ABBAS CHAPTER 13 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ABBAS CHAPTER 13

ABBAS CHAPTER 13

- - Post a Comment
ABBAS
CHAPTER 13
Cikin firgita Teemah ta matsa baya ka'dan tare da furta _" Yah Abbas "_ asaman la66an ta.

Ganin yanda idanuwan sa suka koma tare da irin kallon da yake mata ma ka'dai abin tsoro ne ballantana kuma irin ihun da ya daka mata aka.

'Kasa tayi da idanuwanta da har sun fara 'ko'karin tara ruwa shikuwa sai ya tako ahankali zuwa gabanta tamkar wani abin arziki zai mata sai kuma yasa hannu ya 'dago habarta zuwa sama dolenta ta 'dago kannata batare da taso ba dan ita yanzu tsoro ya Abbas yake bata sak ya juya mata wani irin halitta daban mai abin tsoro

Rintse idanuwan nata tayi da 'karfi jikin na rawa saboda lokacin da ya 'dago kannata tayi zaton sau'kar mari zataji amma kuma sai taji shiru.

Shikuwa Abbas kallon fuskar tata ya tsaya yi, sosai yaga yarinyar ta rame masa amma be tsaya yabi takan ramar tata ba sai hankalin sa ya tafi ga rintse idanuwan da tayin, haushin hakan yaji, shi tunaninshi tayi hakan ne dan bata so taga ko da fuskar ne while bahaka bane ita ta rufe idanun ne saboda tsoronsa, tsoron ha'da idao takeyi dashi.


Sake mata fuskartata yayi sai yacigaba da 'kare mata kallo, be kawar da idanun sa daga kannata ba yace _" lover girl !_, _" kin zaci saurayin ki ne yazo ko"?_

Be jira jin amsarta ba yajuya mata baya ya fara taku ahankali hannunsa 'daya har yanzu na acikin aljihunsa kamar an ce kuma yajuyo, sai ya dawo inda take tsayen ya cira hannunsa yaja hannunta da 'karfi.

Be zame ko'ina da ita ba sai a wajen kujera ya wani jefata da 'karfi ya tsaya akanta yana huci, ita kuwa sai ta kudun dune jikinta wuri 'daya yayin da hawayen da ya taru acikin idanunta 'dazun yasamu damar gangarowa abinsa, ci gaba tayi da zubda hawayen helplessly kanta acikin tafin hannunta.

Sau'kan duka kawai take jira awurin yah Abbas 'din dan zuwa yanzun gaba 'daya ta saduda da wannan alamarin, bata san laifin data yi masa ba, dan ita bata masa laifin komai ba a iya saninta amma ga dukkan alamu ranshi a6ace yake da ita.

Ko kuma cewa da taji akeyi anawa sojoji allura wata'kila gaskiya ne, gashi yau tashiga hannunsa Allah ne ka'dai zai 'kwace ta yau ahannunsa, ahankali cikin kukan ta fara fa'din _" Yah Abbas... dan Allah.....dan Allah kayi ha'kuri, wallahi bazan sake ba, dan Allah karka dake ni, in ka dake ni_ _mutuwa zanyi Yah_ _Abbas........"_

Ahankali take maganar dan in ba akusa da ita kake bama bazaka ta6a fahimtar me take fa'di ba saboda cikin shashsheka tayi maganar.

Shi kanshi Abbas yanda tayi sai da ta bashi tausayi amma sam yakasa jin nutsuwa acikin azuciyarsa, yakasa bawa kansa ha'kuri akan abinda yakeji, aganinsa ai shi rani masa hanakali kawai take shirin yi kamar yanda tasaba abaya, azahiri shikanshi be san laifin data yi masa ba she looks innocent, amma shi aransa ji yake tamkar wani babban laifi tayi masa da babu wanda yata6a aikata masa irin laifin akaf fa'din duniya.

Story continues below


Da 'kyar yasamu ya 'dan sassauto ya 'daidaita nutsuwar shi, sai ya yun'kura da niyyan zama agefenta akan kujeran daya jefa tan.

Teemah kuwa na ganin haka ta zamo da sauri ta dawo 'kasa akan carpet kusa da kujerar taci gaba da rera kukanta

Gira 'daya Abbas ya 'dage da mamakin abin da tayin yana kallonta.

_"meke nan wai "?_
Ya tambayi kansa azuciyarsa.

Teemah kuwa tana sau'ko wa taci gaba da bashi hak'uri " _Nifa banyi laifin komai ba Yayah dan Allah kabarni na tafi, inbaka yadda ba ka tambayi mummy kaji Allah banyi mata laifi ba "_

Rashin sanin amsar da zai bawa tambayar tasa yasa ya watsar da tambayar kawai ya dawo da dukkan hankalinsa gareta yaci gaba da sauraransa ha'kurin nata tana dasa aya yayi murmushin takaici tare da 'dan rankwafo da kansa daf da ita
" _Fatima_ " ya 'kira sunan ta cikin natsuwa.

Shiru tayi bata amsa ba duk da tayi mamakin hakan domin ayanda taganshi 'dazun batayi zaton zai sau'ko so soon haka ba, yau de _" Allah kai ka'dai zaka fitar dani_" ta fa'di aranta sai ta 'dan 'dago kanta ka'dan amma bata kaiga duban fuskarsaba.

Shima be takurata ba wannan karan dan zuwa yanzun ko ba'a fa'da ba dakansa yafara fahimtar irin tsoratan da tayi dashi, ya gane cewa duk abinda takeyi atsorace take yinsa.

_" Waye yace miki bakiyi laifi ba"?_

Shiru tayi masa wannan karan ma dayaga bazata yi magana ba sai yaci gaba da tashi maganar _" anyway,_ _ki bani_ _labari"_.
Yayi maganar yana duba agogon dake 'daure da tsintsiyar hannunsa sai kawai ya 'kara da fa'din

_" ki ban labarin yanda kike so auren ki yakasance"!._

Ko yanzun ma shiru tayi batayi masa magana ba, kawai sai ta 'kara maida kanta 'kasa kamar yanda yake da farko ko ka'dan bata yi alamar zata bashi amsa ba _" toh_ _me yake so_ _ince masa, har akwai wani yanda nakeso aure na ya kasance ne?.

Muryarsa tajiyo yana fa'din _" idan nayi magana banason ashare ni Fatima wata'kila kin manta da wannan ko?"_ 

Yayi maganar tare da komawa baya ya jinginu da jikin kujerar tamkar wani basarake. 


Kai tayi niyyan jijjiga masa amma da tuno da warning 'dinsa daya ta6a mata abaya akan hakan shiyasa sai ta bu'di bakinta da 'kyar kamar ma bazata yi maganar ba tace " ban manta ba".

Shirun shima yayi idanuwansa nakan la66anta datayi maganar, kukan da tayi gaba 'daya sai yasa suka zama jajir, zuba mata idanu yayi shi ka'dai yasan me yake sa'kawa aranshi.

Tsawon mintina biyu suna ahakan, motsi Teemah tafara sanadiyyan gajiya da 'kafafunta suka yi dayake lan'kwashe su tayi ta zauna akansu, zogi taji sun fara yi mata take sai ta sake yamutse fuska tare da daidaita su yanda zata 'dan ji dama-dama.

Motsin data yin ne ya'dan ankarar dashi daga zuba mata idanun da yayi, sai da ya 'dauke idanunsa ya kawar gefe kafin daga bisani ya dawo da kallon shi gareta.

" kina jina" 
Ya tambayeta. 

Sai itama ta bashi amsa daidai da yanayinta a'kasan ma'koshi ta amsa masa da " uumm" tare da 'dagowa a'dan sace ta dube shi.

Bata san meyasa ba amma wani 6angare acikin zuciyarta na kwa'daita mata son kallon fuskar sa yayin da 6angare 'dayan kuma tsoro ya rinjayar shi kuma sai tsoron yafi mata tasiri saboda idanun ya Abbas tsoro sosai suke bata ayau 'din aduk lokacin da yake yanayin da ba dai-dai ba ko ada ma da take masa iskanci son ranta dan be ta6a ritsata bane shiyasa, amma duk da haka de sai da ta 'dan saci kallon san wannan karan dan yadda yayi mata maganar cikin natsuwa sai yasata har ta samu 'kwarin gwiwan 'daga kanta  ta kalleshi, idanunsa 'kur akanta ita kuwa bazata iya sar'ke idanuwanta acikin nashi ba dan haka sai tayi gaggawan maida idanuwanta ga tafukan hannunta dake kan cinyarta luguden da zuciyarta ke yi mata ma ka'dai ya isheta.

_" dagaske ne wai aure zakiyi Angel 'din daddy"?_ 

Muryarsa asanyaye yayi maganar cikin nutsuwa sai kace bashine ya daka mata uban tsawa 'dazu ba, sai ta 'dago da kanta ka'dan itama amma bata kaiga fuskarsa ba sai ta sau'kar da idanun nata akan hannunsa 'daya dake ajiye akan hannun kujera, a irin yanayin da yayi maganar itama sai tace
_" Daddy ne nima ya_ _fa'da min haka"._ 

_" toh meyasa ni baki 'kirani kin gaya min ba a lokacin"._ 
Sai tayi saurin bashi amsa da fad'in " _Wallahi Yayah mantawa nayi kayi ha'kuri"._ Ta 'karashe maganar da karkata kanta gefe harma ta daure ta sanya idanunta cikin nashi.

Yanda tayin ba'karamin birgeshi tayi ba sai kawai ya tsaya yana kallonta kamar baze sake magana ba.

Ita kuwa har godiya takewa Allah dayaga yayi shiru yana kallontan, _"Allah kasa ya ha'kura ya barni na tafi"_ 
duk zaton ta laifin da tayi masa kenan shiyasa yayi maltreating 'dinta 'dazu har tana tunani aranta " ashe dama akan 'dan wannan abin ne, toh ai in de wannan ne harda kai a laifin, kaima ai baka ta6a 'kirana ba, toh ni meyasa zan 'ki......

Tana cikin tunanin taji ya sake fa'din " _kin_ _manta kika_ _ce_ "?

Ga mamakinta wannan karan atsaye yake hannunsa 'daya cikin aljihunsa harma ya juya mata baya kamar me shirin barin 'dakin.

Mamakinta be wuche na har yaushe yabar nan 'din ba batare da tasani ba.

_" Fatima toh dani kika manta ko kuma da 'kirana a waya?_   

Yana gama fa'dan hakan ya juyo ya fuskance ta ga dukkan alamu amsar tambayarsa yake bu'kata gamsashshiya daga bakinta.

Ita kuwa rasa abin da zata ce masa yasa tafara in ina domin ta kamamman abinda zata furta wanda bazai zama laifi ba take so dan ta kar ta 'kara yi masa wani tunda tasamu ya sau'ko, kuma sai tarasa, sai da 'kyar tasamu ta furta _" da wayar"_.

Murmushin takaici yayi inda murmushin ya tsaya masa a iya saman la66ansa sannan ya juyo ya dawo kusa da ita kanta ya 'dago zuwaga kallonshi wannan karan kam jitayi zata iya kallon idanunsa tunda taji ya 'dan sau'ko daga masifar da 'daina shayin ha'da ido dashi aikuwa takalleshin idanun su suka 'sarke cikin na juna 
_" ki gaya min gaskiya, ke ma kina son auren nan ko?._ 

Ita kanta bata san lokacin da har kanta ya motsa ta bashi amsa ba saboda wani bug...bug take jin zuciyarta kamar zata fa'do waje.

_" Fatima kina son Mahmud"_?
Ya sake tambayarta.

Yanzun kam shiru tayi masa sai da ya sake maimaitawa da 'dan 'karfi kafin ta sake 'daga masa kai alamar _"ehh_"
Yagane me take nufi amma dan yasake tabbatarwa yace mata be fahimceta ba dolenta ta bu'di baki ta bashi amsa da " _ehhh"._

_" kin tabbatar "?_ 

kai ta 'daga masa yanzun ma dan ji tayi bakinta yayi mata nauyi koda zai doke tane bazata iya bashi amsa da bakinta ba.

Yana gama fahimtar ta take sai yasake mata kanta ya koma ya zauna da kyau akan kujera ya lumshe idanunsa tare da jingina bayansa tsawon mintina biyu.

Tashi yayi cak kamar an mintsine shi ya nufi 'kofar fita daga 'dakin, yanda ya buga 'kofar ma ka'dai abin ka juya ka kalleshi ne domin da 'karfinsa ya bugata tamkar tayi masa babban zunubi.

Teemah tana inda ya bartan har ya bar 'dakin bata iya 'daga ido ta kalleshi ba, tana zaune tamkar mutun mutumi, bata san me yasa take jin kamar bata kyauta ba haka kawai sai take jin rashin nutsuwa ga kuma damuwa da tausayin kanta da bata san tushensu ba na ratsata ta ko'ina hakan sai ya 'kara kashe mata jiki tare hana ta motsi agurin banda gudun da hawayen ta ke yi babu abinda ke motsi ajikinta

Yana fita daga 'dakin sai su kaci karo da Hannah da ta taho da saurinta itama ta nufo dakin, dan tun 'dazu tun fitan Teemah take cikin bayi bata san da labarin zuwan shi ba koda ta fito kuma 'kawayen Teemah basu tuna sun sanar da ita 'kiran da Ummah take yi musu akan lokaci ba, sai da ta 'bata lokaci awurin yin shirin tagama kafin Naanah ta tuna da cewa an'kirasu tun 'dazu.

Koda taje gun Ummah kuwa  masifah tafara yimata akan wai ina ta zauna tun 'dazu bata je sun gaisa ba alhalin tasan baya da'dewa akan hanya yake, ha'kuri tabawa Ummahn tare da fa'din ai batasan shine yazo ba"

Mummy ce ta tari maganan da fa'din je ki sameshi ku gaisa kafin ya tafi yana can 'dakin.

Toh ita da suka zo jiya Teemah duk tabi da ita ta nunnuna mata ko'ina agidan da 'dakunan yayun tan, hakan yasa da mummy tace mata yana 'dakinsa sai ta nufi 'dakin da Teemah ta nuna mata jiya amatsayin 'dakin sa, amma sai bata ga alamar ma anbu'de shi ba ( ashe ita kuma mummy key 'din 'dakin Mahmud ta bayar aka sau'keshi aciki), ita kuma sai Hannah tayi tunanin ko bata gane lissafin bane tace bari ta dubo 'dayan tagani tukunna ( abinda ya sa tayi delay 'din zuwa da wuri kenan).

Tana zuwa kuma sai ta ha'du dashi harya fito, _"ah ah_Yayah _har tafiya zakayi_ __ne_ _bayan bamu ha'du ba? 

_"Sauri nake yi Hannah lokaci zai 'kure min"._ 

"_Toh yayah kaci abinci ne ?_ "

Duk maganannan da sukayi akan tafiya suka yi ta, Abbas be tsaya ba koda ya gantan sai yaci gaba da tafiyarsa, itama tana binsa abaya take ta faman jero masa tambayayoyin, ganin kamar zata takura shi. Sai ya ce

_" Hannah naci jeki fito da sauran suna ciki"._ 

Yasan in ya fa'di haka zata koma tayi abinda yace dan yasan Hannah bata ta6a musanta masa magana kowacce irice.

Illai kuwa hakanne, dan yana fa'din haka ta tsaya cak daga binsan da takeyi, ta bi bayansa kawai da kallo daga bisani kuma sai ta juya ta koma 'dakin domin fito da ragowar abincin kamar yadda ya ce da ita.


Tana shiga sai ta hango Teemah a zaune tana zubda hawaye, da sauri ta 'karasa inda Teemahn take tayi zaman dirshan a gaban ta arikice take tambayarta abinda yafaru.

Teemah kuwa bata san da shigowan Hannah ba sai kawai taganta agabanta lokaci guda.

Hawayenta ta fara 'ko'karin gogewa ita adole kar Hannah tagani.

Duk 'ko'karin da Hannah tayi dan taji meyasamu Teemah tayi amma takasa samun gamshashshiyar amsa ko guda 'daya ne daga wurin Teemah

Data gaji da tambayar sai tace mata
_" nasan me ya faru ai kawai baki san sanar dani ne"_ 

Shiru Teemah tayi kawai tana kallonta ita kanta so take taji abinda yasame ta so take taji daga bakin HANNAH, dan  idan zata tambayi kanta da kanta ma bata san meke damunta ba bata san mezata ce yafaru tsakaninta da Yah Abbas ba.

_" wannan sojan ne nasani, nasan shine yasaki kuka domin shi ne ka'dai naga yafita daga 'dakin nan kuma nasan sarai zai iya"_ 
Hannah tayi maganar tare da mi 'kewa tsaye ta nufi inda taga tray 'din abincin.

_" gaskiyarki ne Hannah, Yah Abbas ne !,toh amma me zance yamin har nake kuka"?_ azuciyarta tayi wannan tunanin, sannan itama ta mi'ke tabi bayan Hannah zuwa gurin abincin.

Hannah sai da ta zauna kafin tafara bu'de su 'daya bayan 'daya tana gani.

_" 'kila ya tsaya yi miki mugunta ne ma shiyasa ko abincin be saurara ba harda wani cewa wai inzo in kwashe_ _sauran ashema ko bu'dewa beyi ba"_ tayi maganar dai dai tana 'ko'karin rufe plate 'din daya kasance na 'karshe data bu'de " _muje sai na tambayeshi ai laifin me kika masa da har yasaki kuka, innayi sa'a shi zai gaya min tunda ke kin'ki sanar da ni, problem 'din ma miskilancin tsiya gareshi da 'kyar ma yakulani idan yaga dama, amma nasan me zanyi ai in ya'ki bani amsa Daddy zan 'kira infa'dawa ince in yazo nan dukanki yake yi kullum kafin yatafi "_

Suna kan tafiya Hannah take ta jero bayananta batare da Teemah ta fa'di ko kalma 'daya ba sai da Hannah ta dasa aya sannan Teemah tace 

_" ke nifah bance miki ya Abbasa ya doke ni ba"!_ awani tsare tayi maganar tamkar wata jaruma.

Turus Hannah taja ta tsaya
_"Toh yah akayi? fa'damin_ "!

_" ayaya kika sameni"_ ?

Sai da Hannah ta 'dage gira tukunna tace
_"Azaune mana kina_ _kuka"!_ 

_"Toh abinda yasame ni kenan, gajiya nayi da zaman kuma kafata ta ri'ke sai zogi takemin nakasa ko motsa ta shiyasa ni kawai nafara kuka"_

_" shikuma yatafi ya 'kyaleki ahakan"_?

_"Sai da ya fita sannan na fara jin zafin"_!

_" kin ma rainawa kanki hankali yarinya amma da nazo 'din waye yataimaka miki kika mi'ke?"

Da sauri Teemah tace _" ai lokacin 'kafar ta daina zafi"_

_" kuma hawayen kasa tsayuwa yayi ko"?  ,_

Shiru Teemah tayi ta kauda kanta gefe.

Hannah kuwa sai taci gaba da maganarta _" kekika sani wallahi indai juninki wai adake ki 6oye ne kin shiga_ _ukun ki,_ _Yah Abbas fah bashida kara shikan_ _babu_ _ruwansa muguntarsa intazo yinta yakeyi ako ina indai shine, kicigaba da rufa masa asiri wai ke gaki me_ _yayah ko hmm_ , _jiki_ _magayi ai_ _yarinya"__ 

_"ke kin kasa yadda be min komai ba_ _ko"_ ?

_" ai ko bani ba babu me amince miki Teemah"._ 

_"Allah kuwa Hannah babu abinda ya min idan abu yamin ai zan sanar dake kinsani"!_

" _ke kika sani fah ni babu ruwana_ "
Hannah tafa'da 'kasa-'kasa.

Teemah kuma acikin zuciyarta tace _"kanki akeji parrot_ _kawai."_

Hannah alwashi tayiwa aranta sai ta bincika ta gano abinda ke faruwa saboda tana ganin kamar Teemah na 6oye mata wani abin ne, kuma batason Teemah ta kullaci Abbas saboda idan ya kasance kullum mugunta yake mata dole zata na jin haushin sa aranta,itakuwa tana son yayan ta batason kuma taji ance anajin haushin wani abu nashi daya dangance shima ballantana shi da kanshi, tafi son taji kowa nason shi, shiyasa ko yanzun ma ta damu dataga Teemah na kuka taso Teemahn tasanar da ita meke faruwa dan tayi maganin abin, amma Teemah ta'ki

Abbas kuwa tun kafin ya isa 6angaren da yasan zai samu Ummahn ya 'daga waya ya 'kira Mummy..............


Mummy cewa tayi ya shigo tukunna suyi sallama da mahaifiyarsa mana kafin yawuche 'din, yayi 'ko'karin ce da mummyn ta sanar da Ummahn kawai basai ya shigo ba da 'kyar mummy tayi convincing 'dinsa yashigo koda ya shigonma atsatstsaye yayi musu sallamar yawuche abinsa kafin su Hannah su shigo ma har ya wuche dukkansu sun fahimci 'yar 6oyayyiyar damuwan dake kwance asaman fuskarsa amma basu tsaya sun tambayeshi ba saboda sun san basamun amasa zasu yi ayanda suka san halinsa.

Hannah da Teemah kuwa koda suka shigo 'din ma sai kowa yabi hanyarsa, Teemah 'dakinta ta wuche wurin friends 'dinta bayan ta daidaita nutsuwa da yanayin fuskarta, Hannah kuwa kitchen ta shiga ta ajiye tray 'din da ta 'dauko sannan ta dawo wurin Ummah tazauna agefenta. 

_" Ummah wallahi Yayah ko cin abincin ma beyi ba ya fito kayansa"_ 
tace da Ummahn cikin yanayi na shagwa6a66u. 

Sai Ummahn tace mata
_" 'kila baya tare da yunwa ne shiyasa "._ 

'Kasa-'kasa tayi da murya dan kar kowa yajiyo ta tace _" Ummah kinsan wani abu"?_ 

Kai Ummahn ta girgiza mata alamar _a'a_ sai ta cigaba da fa'din 
_" kukafa nasamu Teemah nayi a'dakin nasa na tambayeta kuma ta'ki ta sanar da ni_ _abin da yasameta"._ 

_" nasan za'a rina"_ 
Mummy tace azuciyarta.
dan duk 'kasa-'kasan da Hannah tayi da muryarta sai da Mummy tajiyo ta batasani ba, dah ita a shirmenta wai ba'a jiyo ta Ummah ce ka'dai kejinta, wannan karan Ummah mantawa tayi da sirrin 'karyar da Hannah take so suyin tace
_" toh me yasame_ _ta"?_ da 'dan 'karfi tayi maganar. 

_" oho nima bansani ba, amma inaga itada yayah ne"!_ 
Hannah ma dolenta ta dawo da muryarta daidai yayin fa'din hakan dan Ummah tariga ta tona ta. 

Mummy naji amma bata tanka ba sai da taga Ummah taciro waya sannan taso saka baki amaganar duk da bata so haka ba amma sai taga yazama dole ne tayi maganar, tana shirin yin magana sai Hannah ta rigata  tambayarta abinda Ummah zatayi da wayar ganin tana shirin nemo wata number, afirgice tace da ita _"wa kuma zaki 'kira Ummah da wayar"?_ 

_"Abbas mana, tambayarshi zanyi abinda yarinya nan tayi masa ya daketa"_ 

Hannu Hannah tasa tana 'ko'karin kar6ar wayar tace _"kai Ummah bazaki ci ribar zance ba kekam, daga magana sai ki 'kirashi kalan yazo yaci 'kaniyata yace ni ce nafa'da miki".?_ 

_" Toh me yasa zai daketa yatafi abinsa, daga zuwa gaishe shi dan_ _neman fitina da rashin ha'kuri sai yakama ya doketa,  yarinyar da ake shirin taron bikin ta shine zai daka tsabar shi_ _ishashshe ko me?"_ 

Sai yanzu mummy tasamu damar saka baki amaganar tasu ganin Ummah ta 'dau zafi tace. 

_" dama kin hutar da bakinki da zuciyarki akan yaran nan, indai Teemah da Abbas ne toh wallahi_ _gajiya zakiyi da magana har bakin ki yayi tsami, haka suke kullum cikin abu 'daya"._ 

Story continues below


_" toh ai wannan duk rashin ha'kurin na sa ne, taya zai rin 'ka biyewa yarinya 'karama har haka"?._ _mthewww_ 

  Ta 'karashe da yin tsaki sannan ta da dawo da kallon ta da Hannah tace " _kinga Hannah je 'kiramin ita Fatiman, maza yi_ _sauri"._
Tafa'da tare da 'dago hannayen Hannah sai da taga ta tashi tsaye kafin tasake ta. 

_" ki sauri mana"_ 
Ta 'kara cewa da Hannah ganin tana 'daga 'kafa ahankali kamar ba son zuwa take ba. 

_" hmmm"_ kawai mummy tafa'di a'kasan ma'koshinta, ganin ko'karin Ummahn takeyi ita. 

Ko bayan fitar Hannah Ummah cigaba tayi da surutu tana mita akan lamarin mummy ce ta dakatar da ita da fa'din

_" wannan abinda kike yi fah duk abanza ne inde akan yaran nan ne, kuma nasan babu_ _wani dukanta da Abbas yayi dan tunda muke dashi agidannan banta6a ji ko ganin yasa hannu ya_ _ta6a_ _lafiyarta ba duk kuwa da irin rashin ji da Fateema keyi_ _agidannan, ko yanzun ma nasan iskancin Teemah ne kawai ki rabu dasu."_ !

Kauda kai Ummah tayi gefe kamar bataji ba ga dukkan alamu maganar mummyn be wani shiga kanta ba, sai mummy ma tayi murmushi kawai ta ta tashi ta bata wuri.

Da Teemah ta tashi zuwa 'kiran da Ummah keyi matan gaba 'dayan su suka taho da sauran friends 'din nata dan cewa sukayi suma zasu wuche gida ganin lokaci ya 'dan ja. 

Da fara'ah dukkansu suka shigo 'dakin saboda ragowar dariyar dasukayi duk be bar kan fuskokinsu ba, Naanah ce take kwatanta rawar da zatayi wai agurin bikin Teemah gashi bata iya rawar ba abin dariya kuma wai ita adole sai tayi ,Fauzee kuwa data kare mata kallo sai tace _wai_ _rawar Naanahn_ _tamkar agwagwa na tafiya_ hakanne yasasu dariya gaba 'dayan su shiyasa suka zowa Ummahn da murmushi akan fuskokinsu.

Ummah idanunta  akan Teemahn yafara sau'ka da har yanzu takasa ri'ke tata dariyar idonta har yana hawaye tsabar dariya, aduk lokacin da ta tuno maganar Fauzee sai kawai taji sabuwar dariya ya kamata.

Mamaki Ummah tayi sosai kuma sai alokacin ta yadda da maganar mummyn data gama fa'da yanzun kafin ta tashi, yanda taga idanun Teemahn badan taga tana dariya ba da sai tace kukan dukan da Abbas din yamata ne amma ganinta tana dariya sai ya wanki ranta ta 'danji wasai.

Sallamansu kawai tayi batare da ta tambayi Teemahn abinda yafaru ba, haka suka je suka yi musu rakiya awurin gate suka musu sallama tare da godiyan ziyaran dasuka kawo musu daga nan su Fauzee sukayi gaba sukace sai nan da kwana biyu kuma idan sunzo shan shagalin biki.


*****
*LAGOS* 

Mahmud kullun addu'ah yake kar Allah yasa Abbah yasake tunowa da maganar zuwa yoben nan dan shi ba son zuwa yake ba, Allah kuwa ya taimakeshi Abbah be sake bi ta kai ba, sai kawai yaci gaba shiryen shiryen dake gabansa.

Anty kuwa zuwa yanzun hankalinta inyayi dubu toh ya gama tashi, dan ganin yanda shirye-shirye ya kankama gashi Anty chideh ta 'ki bata ha'din kai suje gurin neman maganin har yanzu, ta ro'ki Anty Chidehn iya yanda zata iya amma sam ta'ki yadda har Anty ta ha'da da cewa  zata iya samo mata 'yan mata duk irin wanda take so wanda suka ri'ka awannan harkar ko guda nawa ne matu'kar zata amince ta kaita wurin 'dan ogah, amma Anty Chideh ta'ki yadda tace ita kanta zata iya nemowa kanta indai tana da bu'katar su wannan ba matsalarta bane ayanzu. 

Anty kuwa tace ita sam bazata iya aikata lesbian ba, bata ma son ko ka'dan taji ana labarinsa ji take yi kamar zatayi amai tun ranar data ga Anty Chideh nayi ta 'kara tsanar abun bata ma ko san tunowa dashi ballantana ita ta aikata shi da kanta, akan hakan ta gwammaci ganin auren Mahmud da ire-iren 'ya'yan Khadija ko da su nawane aduniyan nan indai har sai ta aikata lesbian zata ga rashin yiwuwar hakan. 

Akan haka kullun suke dramma da 'kawarta Anty Chideh inda kowa ya kafe akan nashi ra'ayin, duk kuwa da wannan abinda Anty chidehn keyi mata hakan besa daidai da 'kwayar zarra taji haushin Antyn Chideh ba ko ka'dan, ahaukarta ita gani take kamar _so ne_ ai har yasa Anty chidehn taza6e ta akan hakan, sai dai rashin sa'ar da Anty Chidehn tayi shine ita Anty bata da ra'ayi.

Maimakon ta 'dan ja baya da Anty chideh a'a sai ma wani sake lalla6a ta data keyi akullum, saboda tsoron kar ta ce zata fita aharkanta ta rabu da ita gaba 'daya wanda take ganin kamar in hakan yafaru ba 'karamin asara tayi ba tana ganain cewa wahala zata sha in Anty Chideh bata tare da ita, gani take zata shiga uku domin Anty Chideh itace idanun ta afa'din garin Lagos, duk wani damuwarta, farin cikinta, ba'kin cikinta samu da rashin ta kafin kowa yasani sai Anty Chideh tasani. 

Inkuwa matsala ce ta kunno mata kai bata san ta tsaya ta kaiwa Allah kukan ta ba, sai de Anty Chideh, zuciyar Anty gaba 'daya ya lalace da zuwa gurin bokaye da 'yan tsibbu harma tana ganin kamar matu'kar kana da 'yan canji toh baka da matsala da komai arayuwa inhar bokaye na existing toh damuwarta ka'dan ce, bata san tasaka Allah a lamarinta ba sai dai bokaye sosai tayi amanna dasu da ayyukansu.

Wata 'kawarta ce ta ziyarce ta asatin bikin tasame ta cikin yanayi na damuwa anan tabata shawaran cewa wai tasaki ranta kawai asha biki agama lafiya duk da baso takeyi ba ta 6oye hakan aranta tunda yanzu tarasa mafita inyaso bayan bikin sai ta shi tsaye ta nemi hanyar 6illewa tayi maganin su gaba 'daya.

Aranar da matar ta fa'di haka Anty kamar zata cinyeta 'danye dan masifah, da 'kyar matar tasamu ta fita ta wuce inda ta fito tana mai dana sanin kawo wannan shawaran datayin, Anty cewa take wai dan me matar zata ce haka, tana nufin ta tsaya kenan har sai angama bikin tana kallo, tana nufin idanu zata zuba kenan tana gani 'danta ya auri waccen _banza_ _dangin mayun_ , tajima tana kunfar baki baub wanda ya tankata agidan, dayake ma Abbah baya nan alokacin, house maid ne ka'dai da ita agidan,  da 'kyar Anty  tasamu ta lallashi zuciyarta tayi shiru. 

Sai dai wani abu da batasani duk wannan dramar da Anty keyi akunnan Mahmud kaf aka yi su har sai da yaga matar tafita sannan shima yakoma 6angarensa, dama shigowar sa gidan kenan yanufo parlour daniyar duba ta, sai kuma yaji suna wannan maganar. 

Hawaye yake ta faman sharewa na ba'kin ciki da takaicin halin da mahaifiyarsa ta cusa kanta 'karfi da yaji, har yaushe Anty zata gane ta dawo kan dai dai, har yaushe zakace a kullum sai kayi jayayya da lamarin ubangiji bayan shike da kai ba kai kake dashi ba. 

Hawaye Mahmud yake sharewa yake wannan tunanin, babban dalilin dayasa tun farko yanuna baya son auren nan kenan, dan bazai iya tsayawa ya juri ganin Fatima awani yanayi ba, dan yasan Anty bazata ta6a saduda taso zuri'arsu ba, wannan wani irin rayuwa ne?, karo na barkatai kenan daya ke jin irin mugun alkaba'in data ke bin danginsa dashi, bayan yasan ako ina zasu tsaya ko suje ita ce abin zagi basu ba ga duk wanda yasan halinsu gaba 'daya. 

Darajar haihuwa kawai Anty take ci amma wani lokaci Mahmud jiyake tamkar ya sha'keta saboda kawai ya huta da ganin ba'kin ciki awanan gidan. 

Duk da lokuta da dama yana tanka mata akan abinda takeyi 'din sai de baya jan maganar sosai sai ya 'kyaleta haushi ma baya barin sa ya 'dau dogon lokaci tare da ita, haka kuma be fiya son suna jayayya da ita ba akan abu.

Bayan fitan matar ne kuma sai Anty ta zauna tayi tunani da kanta akan maganar matar sai kuma taga hakan kuma fah yafi mata, saboda bata san ta ina zata fara ba yanzu kam amma bayan angama biki hankalin munafukai ya kwanta asannan ne ita kuma zata bayyana nata haukan.

Sosai tayi na'am da wannan shawarar da zuciyarta ta batan, takuwa bishi dan Abbah da kansa yayi mamakin yanda farat 'daya Anty ta sau'ko ta zubda dukkan makamanta na ya'ki ta kama shirin biki babu 'ka'k'kautawa, yanda ta nuna tana son auren ma har in baka sani ba zakayi zaton ko tafi Abbah ma burin son ganin anyi auren angama.

Mahmud ne ka'dai yasan dalilinta shikuwa akullum addu'ah yake kar Allah yabata sa'an cutar da kowa, dan yasan ha'ki'ka sihiri gaskiya ne, tsafi gaskiyar mai shi.


Anty da kanta ta 'dauki driver suka je da Abbah gidan abokin Abban ta sake duba kayan da aka harha'da 'din, anan ta nuna cewa wasu abubuwan ai sunyi ka'dan ya kamata a'kara gaskiya saboda wannan bikin na _kai_ _da kai ne_ .

Speechless Abbah ya zauna yana kallon iyayin da Antyn keyi, take kuwa ta sake tura ku'di wa Hajiya Aisha tace a'karo kayan tanaso bikin 'danta ya kasance fitattace wanda za'a jima ana kwatancensa aduniya.

Hajiya Aisha kanta tayi mamakin yanda abin ya dawo, domin ba haka labari ya iso mata ba da farko ganin alokacin Abbahn shine tsaye akan komai, sosai tayi mamakin yanda Mum Mahmud 'din ta canja cikin 'kan'kanin lokaci, dan akwanakin baya ka'dan kafin zuwan yau akullum in suka yi duba da yadda Abbahn yayi ruwa ya kuma yi tsaki akan lamarin auren ba sa cewa komai sai dai suce Allah ya shiryi Mahaifiyar Mahmud 'din, Allah da ikon sa kuwa ashe shiriyar tata na kusa yanzu kam sai dai suce _"ALHAMDULILLAH"_ dan Mum Mahmud tabawa kowa mamaki alokacin da basu zata ba.

Aranar Anty bata koma gida ba kasuwa ta wuce tayi siyayyah sosai ma kanta, kaya tsadaddu ta siya ta bada 'dinkin express a inda tasan bazasu bata matsala ba, bata damu da tsadan 'dinkin ba ita damuwar ta tasamu adai dai lokacin da zata bu'kace su.

Ta dawo gida da sauran ragowar siyayyan data yi ni'ki-ni'ki a hannu.

Tun daga ranar Anty bata 'kara nutsuwa guri 'daya ba akullum tana hanyar fita, kasuwa da sauran abubuwa.

Haka duk mutanen data san zata gayyata duk ta gayyace su daga 6angarenta, 'kawayenta ma wasun sunyi mamakin canjuwarta ta amma koda sukayi magana sai tabisu da murmushi kawai batare da ta basu gamsashshiyar amsar da suke son ji ba.

Akwana biyu kacal da sa'k'kowar Antyn har gida yafara cika da wasu daga cikin 'yan uwa da abokan arzi'ki, hatta 'yan uwan Abbah da suke 'kauye 'kalilan daga cikin su sun samu sun zo hakama yan uwan Antyn.


Abin mamaki Anty duk ha'dasu tayi tai musu sau'kar bangirma, bata nuna mugun hali ba koka'dan bata bari sun samu 'kofara da zasu zageta da ita ba wanda hakan duk yana cikin target 'dinta ne nagaba.

Abbah da kansa ya nemawa Mahmud 'din gida flat house mai kyan gaske ya kuma zuba komai na bu'kata dai-dai da zamani sai 'dan abinda ba'a rasa ba, sai dai gidan babu nisa da gidan Abbah yake duk a area 'daya suke, da farko ma Anty takawo shawarar cewa wai  ko a side 'din Mahmud za'a kawo amaryar, har Abbah yaso ya amince domin shi be kawo komai aransa ba game da canjawar Antyn zatonsa shiriyah ce kawai tazo mata daga Allah, amma da aka sanar da Mahmud shi kam sai cewa yayi a'a shi ba zai zauna a nan ba gaskiya sai de anemo wani guri daban, jin hakan yasa Abbah ya yarda da batun Mahmud 'din dan shi lalla6a shi yake yasamu yaga de an 'daura auren yasan daga lokacin komai zai wuche yazama tarihi.

Hakan yasa ya nema masa gidan da kansa ya biya ku'din lokacin ma Mahmud 'din be sani ba sai daga baya Abbah ya 'dauke shi ya kaishi gidan dan yaga yanayin gidan ko ya masa

Story continues below


Shikanshi Mahmud ya yaba da tsarin gidan, dan shi dama yafison gida flat mutun yafi sakewa aciki sai dai kuma duk da haka sai da yayi wa Abbah complaint cewa wai ai sun yi kusa sosai shi fah bahaka yaso ba yafison yayi nisa dasu.

Ido Abbah ya kwalalo yana kallonsa da mamaki " Mahmud wai lafiyarka kuwa"?
Abbahn ya tambayeshi.

Baiyi magana ba illah 'dago hannunsa dayayi yana duba tsadaddiyar agogon dake 'daure atsintsiyar hannunsa.

Cigaba da magana Abbah yayi.
" Babana dan zakayi aure shine zaka guje mu gaba 'daya har baka son zama kusa damu?"

"Bahaka bane fah Abbah"!

Kwafah Abban yayi kana yace "toh menene?"

Shiru Mahmud 'din yasake yi ya sunkuyar da kansa 'kasa.

"Mahmud karfa laifina ni danasa ka kayi aure alokacin da baka shirya ba yashafi wata daban, inaso kaji tsoron Allah Mahmud adukkan lamuranka , wallahi idan ka kuskura ka cutar da yarinyar nan azaman aurenku da ita bazan ta6a yafe maka ba, sanin kanka ne ni...nine na nemi ha'din auren nan da kaina, kuma kasan inde har hakane kuwa bazai yiwu in zuba ido inga ancutar da ita inakallo ba batare da nayi magana ba, dole zan 'dauki mataki matu'kar hakan yafaru koda kuwa waye ne yata6ata"

Mahmud kansa ya 'dago ya kalli Abbahn nasa sannan yace
"Abbah nifah bani da burin 'kuntata wa ko cutar da Fatima arayuwata ko ka'dan............"!

" toh menene "?
Abbahn yatari maganar Mahmud 'din da sauri.

" Tausayinta nakeji ni Abbah "

" you see......,"Abbahn yafa'di tare da nuna Mahmud da yatsansa yakuma cigaba da fa'din.
"Ai shi yasa nake ce maka akullum kaji tsoron Allah, ina son ka sani cewa daga ranar da akace an 'daura maka aure toh nawi ne babba ya hau kanka bana wasa ba, daga ranar amanar Allah ta hau kanka duk abinda ka aikata kai da mahallici ne kar kayi zaton ko babu wanda yaganka, idan tausayin nata kakeji da gaske tun yanzu zakayi 'damar zama da ita idan kuwa tausayin ta dan zata auri wanda baya son aurent ne toh kasanar dani inji...."

Shiru Mahmud yayi yana sauraran maganganun Abbahn, shi kanshi yasan gaskiya Abbahn yake fa'da masa amma shi koka'dan abinda ke ransa beyi matching da na Abbahn ba, taya Abbah zaiyi tunanin shi zai cutar da Fatima dan kawai ansashi ya aureta bada son ranshi ba, ai ko da ace yana bacci ne aka tashe shi aka ce ga matarka an aura maka ita bazai cutar da ita ba ballantana kuma Teemah,! yasani daman idan yace be son zama guri 'daya dasu dole daga Abbahn har Anty sai sunyi tinani daban kowa da abinda zai zo cikin ransa,shi kuwa manufarsa tayin hakan daban ce da tasu

Har Abbah ya kammala da nasihar tashi Mahmud bai ce masa komai ba shiru yayi yana sauraransa, sai daga 'karshene da Abbah yace masa kar yaga kamar yamanta da batun zuwa Yobe ne dan yaga yayi shiru, yace kawai ya 'kyaleshi dan yaga alamar bason zuwa yake ba kuma dan kar abun ya masa yawa shiyasa ya 'kyaleshi amma hakan bawai yana nufin ya bashi 'kofa bane da zai ci zarafin yarinya 
ba ko da bayan auren dan bazai lamunci hakan daga gareshi ba. 

Aranar akan wannan maganar suka kusan wuni da Abbah dan har suka koma gida Abbah be daina yi masa tuni akan magabar ba haka yake yin ta fa'da-fa'da, nasiha-nasiha, garga'di-garga'di. Tausayintan da Mahmud yace yake jine yafi tsayuwa aransa dan takamamme ya rasa dame zai fassara ma'anar hakan.

  
Koda Anty tasamu labarin gidan da Abbah ya nemawa Mahmud itama sosai tanuna farin cikinta azahiri harma take nuna musu zumu'dinta nason zuwa ganin gidan itama yayinda take jin tamkar wuta ne azuciyarta yake ci dan ba'kin ciki da takaici, taso Mahmud ya zauna acikin gidan da suke saboda zatafi saurin cimmah burikanta akan auren cikin sau'ki amma Mahmud yayi mata yawa, sai de duk da haka ba ta yi 'kasa a gwiwa ba tace de _" su zuba_ _sugani "_ .


Ana gobe 'daurin auran dasafe  Daddy ya 'kira Daddyn Abuja yake tambayar labarin Abbas sai Daddyn Abuja yace ai a kwana kinnan ma yazo amma kwanansa 'daya yakoma bakin aikinsa yace kasan 'dan naka gwani ne wurin bin doka, baya son wasa da aikinsa.  
Dariya daddy yayi tare da fa'din ai hakan yana da kyau shine daidai domin sau'ke nauyin daya rataya akansa, ya'kara da fa'din shima yasamu labari agida sunce masa Abbas 'din yazo amma yakoma, yace amma fah dukda haka kar Abbas yace min bazai zo ya halarci wajen 'daurin auren nan ba"?

Daddyn Abuja cewa yayi
"Ehh toh gaskiya bamuyi maganar nan dashi ba amma bari zan tambayame shi naji ya ake ciki".

" yauwa kace masa injini nace auren fah ahannunsa na dan'kata gaba 'daya shine zai bada auren Fatiman ma'ana shi zai kasance _alwali_ agareta.

Baki Daddyn Abuja ya washe tare da fa'din
"Ahh gaskiya abu yayi kyau bari zan sanar dashi yasamu lokaci ya taho kafin goben, nima anjima da yamma insha Allahu ina hanya"

" Toh bakomai Allah ya tsare ya bada sa'a"
Daddyn Teemah ya fa'di tare da yanke 'kiran.  

Koda daddyn Abuja ya sanar da Abbas sa'kon daddyn Teemah Abbas ji yayi tamkar zuciyarsa zata fita daga 'kirjinsa ta yo waje tsabar yanda bugunta ya 'karu, shiru yayi batare da ya bawa daddyn nasa amsa ba, ha'ki'ka badan daga bakin mahaifinsa yaji maganar ba da cewa zaiyi tsantsar rainin hankali ne yasa aka za6eshi domin yayiwa Teemah wakilcin auren ta, amma sanin daga bakin mahaifinsa yaji da kuma sanin wanda yaza6e shin shiyasa yayi saurin kauda wannan tunanin azuciyarsa, 
Hello!.....
Hellloo Abbas kana jina kuwa?....
hel..... 

Muryarsa asanyaye yace " ina jinka Daddy"! 

" aww toh naji shirune shiyasa"! 

Daddyn Abuja sake maimaita abinda ya fa'din yayi zaton shi Abbas 'din be ji  yace dashi 'dazun ba sai de tunkan ya 'karasa maganar Abbas ya tari numfashinsa da fa'din 
" Daddy abubuwane agabana masu yawa wallahi, yanzu ma shirin tafiya nakeyi zuwa Kogi state bani da wannan lokacin"! 

" toh ya za'ayi kenan"?
Dadyn ya sake tambayarsa.
"Daddy please ka wakilceni ko kuma kasa wani amadadina in babu matsala, zan 'kira Daddy Babban ma nayi masa bayani "

"Toh shikenan ba matsala, Allah ya tsare ya rufa asiri"cewar Daddyn, da "Ameen Ameen "Abbas ya amsa masa sannan sukayi sallama kowa ya ajiye wayar.

Abbas da tsaki ya cire wayar a kunnansa dan ma Daddyn Abuja yariga ya yanke 'kiran badan haka ba babu abinda zai hana shi jiyo tsakin da Abbas 'din yabi bayan wayar dashi.

Baya yakoma ya kwantar da jikinsa tare da 'daga kansa sama yana jujjuya kujerar dayake kai 'din, wani huci yake fitarwa tamkar wani wanda ya dawo daga gudun kilometre. 

" kar Allah yasa a 'daura auren in de har sai ni zan bada shi, mthewww"
Ya 'karasa da jan tsaki kana ya sake 'daukan wayar yayi dialling no. tsawon mintina biyu ne ya 'daukesa a maganar yana kammalawa kuwa ya mi'ke tsaye da hanzari yafara rage kayan jikinsa.

Wanka yashiga sharp-sharp ya watso ruwa ajikinsa ya fito, shiri yayi cikin kakinsa na sojoji gwanin birgewa, dan ba 'karamin kar6arsa uniform 'din keyiba, kamar kar ya rabu dasu har abada idan yasaka su.

Zama yayi dan saka socks da takalmi,  yana gamawa da shirin yafito ya kulle 'dakin ko wayarsa ma be tuna ya 'dauka ba, hularsa ce kawai ya ri'ko a hannunsa ya tafi.

Taku yake cikin ta'kama da 'kasaita duk da cikin hanzari yake tafiyar amma hakan be hana bayyana isarsa afili ba, Abbas 'karshe ne wajen iya tsarawa kansa komai, ciki kuwa harda tafiya be barta abaya ba, musamman idan ya shiryo cikin uniform 'dinsa jiyake tamkar yafi kowa, jin kansa yake kamar bashi ba, alokacin jin kai da miskilancinsa 'karuwa sukeyi sosai.

Ballantana yanda yake samun girma aduk lokacin da ya fito hakan ba 'karamin birgesa yake ba, dan dayawa daga cikin sojojinsu na girmama shi, ciki kuwa harda wa'danda suka girme wa shekarunsa suka kuma fishi da'dewa a akan aikin nasu, shiyasa akowani lokaci yake godiya ga Allah da kuma daya ya tsaya tsayin daka ya jajirce dan ganin ya samu wannan matsayin daya kai 'din ayanzu.

Ko yau 'dinma daya fito daga block 'dinsa hakanne yafaru, dan duk inda ya ha'du dana 'kasa dashi sai de kaga suna 'kamewa suna mishi gaisuwar ban girma, ko kulasu ma bayyi yake wucewarsa dan abin da ke gabanshi ne damuwarsa awannan lokacin, hakan kuwa bazai hana su cigaba da sara masan ba.

Office 'dinsu direct yawuce ya nemi jin batun tafiya Kogi state 'din da aka ce zasu da kuma lokacin da za'a yi tafiyar, aka sanar dashi cewa nan da 2hrs ne tafiyan, da 'kyar ya samu yayi cancelling sunan shi aciki aka maye da wani daban inda da kanshi ya sanar da wancan 'din cewa akwai tafiya nan da 2hrs dan haka ya shirya ya taho kafin lokacin.

Uzuri sosai ya basu kafin yasamu suka cire sunan nashi da shara'din cewa ths is d first and d last da zai 'kara yin irin hakan ya kuma amincewa sannan ya 'kara da neman pass na kwana biyu.

Da yamman ranar ya baro Porthacourt ya sau'ka a Abuja, gidan babu kowa ya samu sai me gadi kawai dan daddyn sama aranar suka wuche kuma dawuri suka tafi, tafiyar motan da zasuyi daga Maiduguri zuwa Damaturu ne yasasu tafiya dawuri dan basu so dare ya same su ahanya saboda dokar da ke wannan yankin alokacin mai tsanani ce. 

  
Kaya kawai Abbas ya canja cikin wani kaftan brown colour bayan yayi wanka tare da gabatar da sallan la'asar dake gabansa daga nan ya fita daga gidan yatafi airport da 'kyar yasamu flight 'din da zashi maiduguri 7:00pm, daga can yashiga gari yarage lokaci tare da ziyartan wani abokinsa.

Koda Abbas ya sau'ka a maiduguri hotel ya nema ya yada zango dan bayajin zuwa gidan oga philip wannan karan, duk dama ba'karamin taimakonsa oga philip 'din keyi ba ko ta wajen ha'da shi da driver ma dayake yi, amma wannan karan ya gwammaci ya hau motar haya kawai yafi masa badan komai ba sai dan ji da yakeyi yanajin haushin kowa ma gani yake kowa damuwa ne.

Abbahn Mahmud da shi kanshi Mahmud 'din already sun iso da sauran abokan arzikinsu da suka zo musamman domin halartar 'daurin auren, suma ganin suna da 'dan yawa sai suka taso da wuri cikin sa'a kuwa basu samu matsala da komai ba suka iso akan lokaci kuma lafiya 'kalau, dan har sun riga Daddyn Abuja ma isowa.

Daddy acan wani guest house 'dinsa dake bayan legislative quaters  ya sauke su harma da wasu ba'kinsa na nesa da suka samu damar amsa gayyatar daddyn,  'dakuna isassu ne agidan so babu wanda ya takuru da wanzuwar 'dan uwansa anan kowa ya sau'ke gajiyarsa. 

Babu wanda yabi ta kan Abbas domin daddy da kansa yayi musu bayanin yanda sukayi da Abbas 'din awanni ka'dan dasuka gabata, zatonsa shi ka'dai ne yasani dan Abbas da zai masa maganan be nuna masa cewa yayiwa Daddynsa bayani ba.

Dukkansu basu damu da rashin sa agurin ba dan sunsan yanayin aikinsa bakamar su bane da su suke sarrafa kominsu yanda suka ga dama.

Mahmud ne ka'dai ya damu da rashin Abbas 'din dan tun safe yake ta trying layin Abbas 'din amma baya samunsa, da farko yayi ta 'kira ba'a 'dauka daga baya kuma not reachable, ko bayan isowarsu ma yayi ta gwadawa amma baya samunsa.

Mahmud bahaka yaso ba, yaso Abbas yakasance tare da shi awannan hidiman dan shike 'kara masa 'karfin gwiwa a kullum. 

Amma dayaga be same shi ba dole ya ha'kura da nemansa fatansa de Allah yasa lafiya yake. Sai dai yasa aransa cewa matu'kar Abbas be halacci wurin 'daurin auran nan ba yace da kansa zai je har porthacourt 'din yaji dalilinsa nayin hakan bayan shine yasashi ya amince da auren tun farko.

*****
Washe gari saturday gari na wayewa kowa yafara shirin 'daurin aure. 

Abbas da safiyar ranar ya iso around 9:30 am, alokacin kuwa shirye shirye yariga ya kankama kowa harkar gabansa yakeyi, ta 'karamar 'kofan dake bayan gidan yashigo dan baya son kowa ya ganshi shi, gaishe-gaishen damuwan nan ma shi baso yake ba, Allah ya taimake shi babu kowa ta bayan hakan yasa cikin natsuwa ya nufi 'kofar dake kitchen wanda ita zata sada shi da ainahin 'dakunan dake cikin gidan.

Koda yashiga ma wasu mata yagani a a palourn kuma ayanda ya lura duk ba'ki ne be wayi ko 'daya daga cikinsu ba dan haka sai yayi wucewarsa ciki ya nufi 6angaren dayayi niyyan zuwa.

Abu'de yasamu 'kofar dan haka kanshi tsaye ya tura kansa ciki ya shiga, sai de yana shiga ya tsaya daga bakin 'kofar dan ganin mutane biyu ne acikin 'dakin. 

Dubansa ya kai kan gado domin ya banbancewa idanunsa cikin su biyu amma tunkan tunaninsa yayi nisa yafara jiyo muryar wacce ke kwance akan agadon kunnan ta sa'kale da earpiece tana bin bakin wa'kar Umar m Shareef mai taken  ( SAQAR ZUCI) ,hakan yasa yayi saurin fahimtar cewa wannan wata dabance bawacce yasani ba, 'dauke idanunsa yayi yah mayar wajen mirror inda ya hango wata kuma azaune amma kallo 'daya yai mata ya gane ko wacece ita, domin yasanta da san zama gaban dressing mirror, dan haka sai ya 'daga 'kafafunsa cikin nutsuwa ya isa gareta.

Zaune take tayi zugum tun 'dazu tana kallon kanta acikin mirror 'din, sai de azahiri ba ganin kan nata take ba, tunani kawai takeyi da bata san inda ya dosa ba.

Dukkan su basu lura dashi ba yanzun, dan ita wancen wayar datake sarrafawa ahannunta shiya dauke mata idanu yayin da ita kuma wannan hankalinta yatafi ga tunani, kuma ma a yadda ya shigo 'din ba lallai ne kasani ba koda kuwa kana daidai cikin hankalinka, ne dan tamkar wani marar gaskiya haka ya shigo ballantana su da kowa hankalinsa yana wani wuri ne daban. 


Da isar sa kusa da itan sai ya tsaya daga bayanta shima yana kallon fuskarta ta cikin madubin gani yayi ta yi kyau sosai fiye da ganinta dayayi na 'karshe, hakama ramarta ta 'dan zarta yanda ya ganta last week.

Dubansa yakai ga hannayenta yaga yadda hannayen suka sha kyau cikin zanan flower baki da ja kamar kar su rabu da hannun nata sukasance haka har abada.
" is it all because of th...............! 
" ohh no bahaka bane"!
Ya fa'da tare da jijjiga kansa.

Be da'de da tsayuwa awurin ba sai ta mi'ke tsaye sanadiyyan tuno maganar Ummah datayi akan ruwan wankan da aka ha'da mata tun 'dazun mai cike da ha'din kayan 'kamshi musamman aka ha'da saboda ita inda Ummahn tace mata karta kuskura ta bari ruwan ya huce batare da tayi wankan ba domin da 'duminsa akeso tayi wanka saboda zaifi kama jikinta yanda akeso idanta gama kuma me shiryata zata zo "
tunowa da wannan maganar ne yasata ta mi'ke tsaye da 'dan sauri domin cika umarnin Ummahn.

Amma mi'kewanta keda wuya sai ta hango mutun tsaye daga gefenta yana kallon ta, bata waiwaya baya ba sai kawai ta kalli fuskarsa ta cikin madubin tayi murmushi, jikinsa sanye yake cikin kaftan mint green 'dinkin ba 'karamin kar6ar sa yayi ba, rigar tsayinta be wuce gwiwarsa ba,  hannun rigar 'daure da links, irin 'dinkin dayafi birgeta kenan acikin 'dinkun maza, yasanya hula wacce ta dace da kalan kayan jikin nasa.

Hannu ta 'dago ta nufi madubin dashi daniyar ta'bashi zaton ta idanunta ne ke hasko mata shi domin taganshi ne exactly yanda tayi mafarki dashi adaren jiya, bayyananniyar murmushi tayi aranta tacigaba da fa'din " da wannan daurarriyar fuskar tashi daba ko yaushe ake ganin sakewarta ba sai lokacin da yaga dama sannan kaga murmushinsa sai inko yana tare da Daddy ne wannan kam har zaka gaji da ganin dariyar tasa alokacin"

Daf da zata ta6a jikin madubin sai taji an ri'ko hannunta daga baya, hannun ta kalla inda aka ri'ke tan tabi hannun da kallo zaton ta ma Hannah ce sai kuma taga sa6anin hakan domin wannan hannun beyi kala koka'dan dana Hannah ba not even from her friends.

A 'dan tsorace ta kuma juyawa takalli cikin madubin sai taga wanda ke bayan tan ne yah ri'ke mata hannun nata, sai alokacin tunaninta yadawo dai-dai sai ta juyo afirgice zuwa inda yake tsaye 'din, gani tayi shi'dinne azahiri ba mafarki ba kamar yadda tasaba ba kuma atunani ba.

'Dayan hannun ta 'dago ta rufe bakinta dashi ta zaro idanu kamar wacce tayi karya tace 
" _huh_! _Yayaah"!!!_ . 

Tafa'da ahankali bada bayyanan niyar sauti ba saboda bata manta irin tsawan daka mata ba ranar dayazo last kafin yau, shikuwa be amsa ba duk da yaji me tace saboda tun 'dazun tsayawa yayi yana kallonta sai ma 'kara binta da idanun dayake 'karayi yana wassafa abubuwa acikin ransa ciki harda irin kyan daya ga ta 'karayi, take sai yaji yana kishin duk wanda zai ganta a irin wannan yanayin.

      Teemah data ga  be yimata magana ba kuma be motsa daga tsayuwarshi dayayi ba har yanzun sai tayi tunanin ko irin mafarkan data saba yine, hakan yasa ta 'danji haushi harda turo baki gaba tana 'ko'karin 'kwace hannunta daga nashi sai shi kuma ya 'ki sakinta.

Teemah bata tsoron Yayanta na mafarki da tunaninta danshi be ta6a yi mata tsawa ba shiyasa bata wani jin shakkansa, ko yanzun ma dataga ya'ki sakin hannunta sai tace
" ka sake min hannuna yayah ni baruwana da kai,  kullum idan naganka baka min magana sai de kayi shiru, inaso ma in baka ha'kuri tun ranar da kayi fushi katafi amma bansan yanda zanyi ba, saboda kullum kinmin magana kakeyi idan naganka"

Rausayar da kai tayi gefe sai taci gaba da magana " kuma fah ba laifina bane dana 'ki gaya maka, ni bansan me zance bane alokacin koda nace zan fa'da 'din shiyasa ban 'kiraka ba".

Sake juyowa tayi ta kalle shi da sanyin murya tace " ka ha'kura yanzu yayaah?

Lumshe idanu kawai yayi ya kuma bu'desu akanta duk tana gani, sai de ita hakan be gamsheta ba sosai tagaji da irin hakan daya keyi ita so take ya bu'di baki yayi mata magana kamar yadda suka saba.

Data ga bashi da niyyan yin magana sai tace " sake min hannu na toh, Ummah fa'da zata min in tazo taga banyi wankan ba har yanzu "

Idanunta akan hannayen nasu tayi maganar.

" me yasa?
Haka kawai Abbas yace shima yana kallon hannayen nasu inda idanun Teemah yake. 

" Baka gani ne?
yaufa za'a 'daura auren yah Mahmud wai....wai.... danii. 
Ta'kara fa'da da jan maganar tare da sunkuyae da idanunta zuwa kasa.

Duk da tana zaton wannan ma Yah Abbas 'din mafarkin ta ne amma haka kawai take jin nauyin sanar dashi maganar aurenta kai tsaye. 

Tun ranar daya tafin nan kusan kullum sai tayi mafarkinsa ha kama tunaninsa yasako ta agaba kuma ko amafarkin ma ba magana yake mata ba, wani lokaci sai de tayi ta masa magana shi ya 'ki bu'dan baki yayi magana wani lokaci kuma sai tace tayi fushi itama sai tayi shiru suta kallon juna amafarkin.

Abbas da kansa ya gane cewa har nzu bata yadda shi 'din bane dakansa, domin yadda take yadda take yi masa magana ma ka'dai shaida ne.

Ga mamakinta sai taji ya mintsine ta ahannun daya ri'ke 'din hakan kuwa yasa ta ta 'dago da sauri ta kalleshi suka hada idanu,  rintse idanun tayi da 'karfi ta kuma bu'dewa a 'ko'karinta naganin ta tashi daga baccin da takeyi 'din, amma ko da ta bu'de 'din ma sai ta sake cin karo da fuskarsa agabanta still yana kallonta, baki ta bu'de da niyar yin magana sai ya ja hannun nata da sauri ya janyo ta zuwa jikinsa, ha'da bayanta da jikinsa yayi sai ya juya ga dressing mirror 'din, sai ya zamana dukkansu suna fuskantar madubin, kwantar da kansa yayi agefen kafa'darta yace
_"_ _oyah tell me now"!_ 


Shiru tayi bata yi masa magana ba illah kallonsa data cigaba da yi sai shine yasake fa'din _" bani ha'kurin yanzu inaji"!_

Post a Comment for "ABBAS CHAPTER 13"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...