[Advertisements⬇️]

YARIMA KHALEED CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 1. YARIMA KHALEED
 2. CHAPTER 1
 1. ••••••••LUXURY HOTEL NEW DELHI,suite ne sanye jikinsa wanda suka matuƙar masa kyau, a hanƙali yake sakkowa cike da ƙasaita daga matattakalan benen
 2. Securities ne ke biye dashi baya da gabansa da gefensa, fitowarsu haraban hotel ɗin ya miƙa hannu tare da amsar baƙin glass ɗinsa ya saka.
 3. ɗaya daga cikin haɗaɗɗun fararan motocin dake pake ƙirar benz ya nufa, buɗa masa akai ya shiga, bayan tabbatar da zamansa ya daidaitu driver yaja motar yabi bayan biyun motocin dake gaba sannan ukun bayansa suka biyosa shima.
 4. hawansu titi jiniya ta karaɗe ko’ina,DLF mall New Delhi india suka tsaya,
 5. inda motoci ke aje sukai park,tsayuwar motarsa da sauri aka kewayo aka buɗa masa.
 6. sai daya ɗanja time sannan ya ziro da ƙafafunsa dake sanye cikin fararan takalma waje.
 7. tsaye yayi tare da lumshe ido inda ya shaƙi sanyayyar iskar data kaɗo zuwa hancinsa.
 8. doguwar ajiyar zuciya ya sauke, takawa yay yana tafiya a hankali zuwa inda wasu resting chairs suke.
 9. glass ɗinsa ya zare yana kallon wurin jiki duk a mace.
 10. goshinsa ya shafa tare da ɗaga kansa sama yana kallon gajimaren dake yawo sannan ya sauke gami da fuzgar da iska mai ɗumi daga bakinsa
 11. wuri ɗaya ya ƙurama ido wanda yakai kusan 3hrs a tsaye batare daya ɗauke idonsa ba, Angel ɗinsa kawai yake hanga a wurin tana kai da komowa.
 12. imagination ɗinsa daya basa kaman itace a wurin sai ya tsaya tamkar wani solo da sakin laɓɓa yana fitar da wani malalacin murmushi.
 13. fitowarta daga ciki tai ƙasa zata zame, agigice yay wurin da gudu domin ruƙota, wayam yaji yayin daya ƙarasa zai kamata.
 14. numfashi yake saukewa alokacin daya ɗago suka haɗa ido da matar da itace ta fito.
 15. ɗan dukan goshinsa yayi haɗe da cije lips sannan yace da matar,
 16. “am sorry plss”
 17. ganin kamar ba’a hayaccinsa yake ba ta kaɗa masa kai kawai ta wuce.
 18. juyowa yayi da sauri ya nufa mota ya shiga, basuyi 30mints ba a titi suka isa indira gandhi international airpot.suna isa ya fito ya shige jirgin da dama isowarsa yake jira.
 19. +
 20. shigarsa ya kwantar da kansa saman kujera,isowa akai aka sanya masa belt sannan jirgin ya ɗaga.
 21. mandiri zuciyarsa kawai keyi,a kullum soyayyar yarinyar sake kashe masa jiki take.
 22. ɗan buɗe idonsa yana juyi da kansa kaman zaiyi kuka.
 23. saurin dafe ƙirjinsa yayi daya ke jin zuciyar tamkar zata fito saboda raɗaɗin zafin data ke masa.
 24. _why?why My Angel? miyasa kika kwaɗaitarwa da idanuwana son ganinki bayan kin san bazaki kasance kusa dasu ba akullum._
 25. ƙirjinsa ya daɗa damƙewa saboda yanda wutar soyayyar ciki ke daɗa balbala.
 26. _come 2me Angel,plss come,haƙurina ya ƙare, bazan kuma iya jurewa ba na tsawon wani lokacin._
 27. shi ɗaya yasan irin azabar dayake ji, gabaki ɗaya ya kasa sukuni sai juyi da kansa yake.
 28. baisan da saukar jirgi ba har time ɗin da guard ɗinsa yazo yana magana dan tini yay zurfin tinani cikin wata duniyar.
 29. sai da guard ɗin ya ɗau kusan mintina 15 tukunna Khaleed ya buɗa idanunsa a hanƙali wanda suka sauya launi.
 30. fitowa yay a jirgin ya shiga mota suka wuce gida.
 31. shigarsa ɗaki ya tsaya gaban ƙaton enlargmnt ɗinta daya kafe ya tsaya yana kallo zuwa wani lokaci sannan ya miƙa hannu ya ciro.
 32. numfashi ya sauke ya sanya hannu yana shafa hoton, gefen gadonsa ya zauna time guda ya saki wani ƙayataccen murmushi
 33. kiss ya bama hoton tare da furta, “i love you Angel, i love you more than any word i can express,u’re my life my world, ki dawo gareni Angel, my eyes are all missing you”
 34. sauke dogon numfashi yayi tare da manna hoton a ƙirjinsa gami da lumshe idanunsa.
 35. “bayanki kaɗai ya zama mai kyau ina kuma ga fuskarki, ina tsananin buƙatar sake ganinki Angel, karki azabtar dani da rashinki my Queen”
 36. shida hotonsa kawai yake magana har zuwa lokacin daya ji kiran sallah sannan ya miƙe zuwa gabatar da ibadarsa.
 37. koda ya dawo bayan sallar isha’i kasa cin abinci yayi, wayoyinsa duka ya kashe ya kwanta kan gado.
 38. rufuwar idanuwansa da buɗuwarsu itake yawo aciki, yamutsa sumarsa yayi tare da dafe kansa.
 39. bazan gaji da zuwa inda idanuwana sukai tozali dake ba har sai ranar da kika gaji kika gama ɓoye mani, ni nasan kinan tare dani domin inaji ajikina.
 40. tsoki yay, miyasa ma tin alokacin bai mata magana ba.
 41. wani haushin kansa ne ya kamasa, pillow yaja ya rungume a ƙirjinsa hannunsa damƙe da rimbom ɗinta.
 42. bacci yake so ya ɗaukesa amma yaƙi samuwa, tinanin Rahinat ne ya faɗo masa kuma.
 43. da sauri ya miƙe zaune yana ƙara nazarin kalaman yarinyar, shap ya manta da ita sai yanzun.
 44. ji yay zuciyarsa ta wani buga bummm, da sauri ya runtse ido ya miƙe ya ɗauko kwalban giya ya kafa kai.
 45. ****
 46. bafadawan dake dukanta duk sun game mata jiki da jini, tin tana ihu harta daina sautin kukanta ya daina fita
 47. “bazaki faɗa mana waɗanda suka saki ba”
 48. babu ikon magana domin duk ta gama galabaita, kiran mutuwa kawai take aranta dan tafi mata sauƙi akan wannan azabar da take sha.
 49. mugun cikinsu ya buga mata kulka aka ba shiri ta dawo a hayaccinta, kallonsa ta kama ta haɗa hannayenta biyu tana roƙonsa daya yi haƙuri saboda ayanzu bata da bakin magana tin a wuyar farko bakinta ya rufe da magana.
 50. haka suka gama lugudarta suka tafi zuwa hutu kamin su dawo su ɗora daga inda suka tsaya.
 51. macen da itace shugabar gidan yarin ta shigo bayan fitarsu.
 52. tana zuwa ta damƙi gashin kanta ta barƙalar mata da wuya, “watanni shida ana fama dake amma magana ta gagareki ko, zaki faɗa mana waɗanda suka saki ko kuwa”
 53. matar ta ƙarashe maganar cikin tsawa gami da gwara kanta a bango.
 54. _ita kam ya zatayi da rayuwarta, sai yaushe mutanen nan zasu fahimci cewan ta daina magana ne kota sami sassauci._
 55. dungure mata kai matar tayi tasa ƙafa ta mangareta, “macuta, azzalumai,ku rasa wanda zaku cutar sai PRINCE KHALEED, baki fara ɗanɗanar wuya ba yanzu sai lokacin da mai martaba yaji zancen sannan zaki dana sani mai girma”
 56. tsaki matar taja ta fita a ɗakin ranta a matuƙar ɓace,sun rasa ya zasuyi da wannan gardamammiyar yarinyar, ta sanar dasu abu da bakinta amma kuma faɗan waɗanda suka sata ya gagara, wannan ƙin maganar tata duk wasan kwaikwayo ne.
 57. kanta na kallon sama hawaye na sakkowa tana tinani taji an kira sunanta.
 58. 1
 59. da sauri ta ɗago, da ƙyar ta iya miƙewa saboda ciwon da ƙasusuwanta keyi mata ta nufa ƙofar dan amsar abincin da aka miƙo mata.
 60. kallon ɗan sandan daya kawo ta tsaya tanayi, fuskanta yayi kamar tana son cewa wani abu,ɗaga mata kai yayi alamaan mi take da buƙata.
 61. ba ƙaramin daɗi taji ba daya fahimta, saurin ajiye kwanon abincin tayi ta shiga masa bayani da hannu.
 62. harta gama bai fuskanceta ba, duk juyajuyen da take da hannu bai gane komi ba, gajiya yayi yaja tsaki ya tafi yana faɗan mutane sai iskanci, kamin asirinku ya tonu duk kuna magana raɗau sai lokacin da kuka zo hannu sannan ku rainawa mutane wayo da bakwa magana, to wahala duk zata tinatar daku yanda ake maganar
 63. yana tafiya ta durƙushe ta fashe da sabon kuka.
 64. aina zata sami biro da takarda ita kuwa.

 65. murɗawar da cikinta yayi ta tashi zaune ta buɗa kwanon abincin da shiga ci kamar wadda ta shekara dubu bataci ba.
 66. ****
 67. shiru tsohon mutumin yayi yana kallonta, tausayin yarinyar yake har cikin ransa.
 68. tsawon watanni har yanzu bata farfaɗo ba,haƙiƙa duk wanda ya zalunci wannan baiwar Allahn sai Allah ya saka mata.
 69. kwanciyar kanta ya gyara mata sannan ya ɗau mahuci ya shiga yi mata firfita.
 70. Inna dake fitowa daga ɗaki take cewa, “ai Malm Allah baya barin wanda yaci zalun yarinyar nan saiya saka mata, ka duba fa daga dukkanin alamu an mata horo da yunwa ,shiyasa nice maka wannan azabatarwar kishiyar uwace”
 71. “keko Jummala zancenki kennan, tokoma yane fatanmu ta samu ta farfaɗo, Allah kuma ya bata lafiya, komi ne zamuji”
 72. hankalinsu suka maida ga ƙaramin yaron daya shigo, amsa masa sallamarsa sukayi tare da tambayarsa lapia.
 73. shaida masu yayi cewan ana sallama da malam Hardo inji wanda ya kaɗe baƙuwa.
 74. da sauri kuwa Mlm Hardo ya miƙe ya fita,
 75. da fitarsa ƙafafunta suka shiga motsi, hamdala Inna Jummala tayi haɗe da murna.
 76. kamata tayi ta ɗagota, dafe kanta tayi saboda wani ciwo dataji yana mata kamin nan ta buɗe ido tana duban ginin gidan ƙasan.
 77. juyowa tayi ta kalla tsohuwar matar sannan ta murza idonta.
 78. ƙwaƙwalwarta ce ta shigo tariyo mata abinda ya faru, a razane ta miƙe tsaye, zugin dataji a ƙafarta yasata cije fuska da faɗin,
 79. “wash”
 80. “kinga dawo zauna da ciwo ajikinfa, karaya ce a ƙafarki dawo”
 81. “no i have to leave, na gode da taimako na da kukayi”
 82. tana jan ƙafa ta fice da sauri ko takalmi bata sanya ba. Mlm Hardo na waje duk maganar da yake bata tsaya sauraronsa ba tayi gaba fatanta ta isa inda take son zuwa.*_FLASH BACK:_* 🎯 +
 83. ••••tin alokacin da Rahinat ta baro gidan Khaleed take gudu batare data san inda take jefa ƙafarta ba.
 84. haka Khalid ya fito ya gama bulayinsa bai sameta ba harya gaji ya koma cike da damuwar zantukanta.
 85. daren ranar barinta ya wuce delhi.
 86. tsalleken titi take tsallakewar rijiya da baya, shigowarta wata anguwa da babu jama’a ta hangi wasu tsaffi zasu wuce.
 87. ƙwala masu kira ta shiga yi har Allah yasa suka jiyota, saboda rashin yarda ta yanzu tsohuwar matar dake tare da mijinta tace dashi,” anya kuwa ma tsaya, duba fa ayanda take, Mlm shige mu tafi”
 88. “a’a bazai yiwu mu wuce mu barta cikin wannan halinba na tsananin buƙatar taimako, karfa ki manta keda kanki kike tinatar dani wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimakeshi, yanzu duba kiga fa yanda take a wahalce ,kiyi haƙuri ki bari mu sami ladan wannan taimakon kinji”
 89. matace dake tsananin yima mijinta biyayya babu musawa a tsakaninsu hakan yasa tace dashi, “tom Malm mu jira isowarta, Allah ya jiyartar damu alkhairi atare da ita”
 90. tsaye sukai suna jiran ƙarasowarta, duk ta gama galabaita da ƙyar take takawa, tangaɗi take kaman wata ƴar maye daka ganta kasan ta wahala dole kuma ta baka tausayi ,murfayen idonta saboda nauyin da idonta yay da ƙyar suke haɗewa wajen rufuwa.
 91. tin tana takawar har ta kasa saita koma jan ƙafa ɗaya, dai² da zuwanta tsallakawa wani mai mota yay awon gaba da ita.
 92. ƙara ta ƙwala mai ƙarfi buguwar da tayi yasa ta dogon suma.
 93. dukansu a ruɗe suka kinkimeta akasa a mota suka wuce asibiti.
 94. tsawon watansu guda bata dawo hayyacinta ba,wani tinani yazo ma Mlm Hardo alokacin da suke zaman jinyarta yace da matarsa suce da mutumin daya kaɗeta ƴarsu ce karsu nuna basu da wata alaƙa a tsakani.
 95. kyakykyawan matashin saurayin daya kaɗeta kullum sai yay zirga akanta ba dare ba rana,kuɗaɗe masu yawan gaske yake bawa su Mlm Hardo duk lokacin daya zo, duk zuwan nasa kuma saiya kawo sayayya mai uban yawa.
 96. alokacin da aka basu sallama zasu wuce gida su ƙarasa jinyarta acan wasu mahaukatan kuɗi Raihan ya zube masu yana mai daɗa basu haƙuri akan abinda ya faru.
 97. bawai dan lokacin dischrge ɗinsu yayi ba aka basu sai dan takurawa da sukai aka masu hakan, duk yanda likita da Raihan sukai akan su haƙura aci gaba da jinyarta a asibiti sukace a’a su gida zasu wuce domin suna so su haɗa dana hausa.
 98. hakan da sukayi Inna Jummala ce ta ɓullo da dabaran, domin idan suka koma gida kulawan Raihan zai ninku akan na yanzu, dan da haka zasu samu su tara abinda zasu tara har zuwa lokacin da yarinyar zata sami sauƙi, saboda ta lura yarinyar hanyar arziƙinsu ce, in ta zamace su zauna tare da ita dan dama basu taɓa haihuwa ba in kuma ta wucewa ce to shikenan.
 99. driver Raihan yasa ya kaisu har gida tare dayi masu alƙawarin wataran zaizo dubiya saboda yanzu zai bar ƙasar ne,nan suka ta masa godia tare da fatan alkhairi tukunna suka wuce.
 100. karaya guda Rahinat tayi a ƙafa sai buguwar goshi da kuma kukkurjewa ajikinta, kullum nurse na zuwa ta bata abinci ta robar da aka sanya mata su kuma su Mlm kullum suna adu’ar samun farfaɗowarta.
 101. tsawon watanni shida anata magani na asibiti dana gida amma abu ya faskara gatann dai kaman mai rai kaman matatta, dan ko numfashinta samasama yake fita.
 102. Raihan dake zaryar zuwa dubiya duk bayan kwana biyu ya sami Mlm Hardo da maganar yana ganin kawai su fita da ita waje domin yin bincike mai kyau.kuka Mlm Hardo yasa yace a’a ita ƙwallin ƙwal gareshi ya taimaka masa bayason wani abu yasami ɗiyarsa.
 103. +
 104. “ka yarda dani Baba, wlh bazan cutar maku da ƴa ba domin nima kuwa ina da aure kuma har da ƴa”
 105. da ƙyar Raihan yasha kan Mlm ya amince shima sai dayace to kawai su shirya su duka su tafi wannan ba wata damuwa bace.
 106. ranar asabar yazo ya sanar masu cewan visa ɗinsu ta kammala zuwa ƙasar england dan haka su zama cikin shiri ranar litinin zasu wuce da ƙarfe goma na dare.
 107. ranar litinin kuwa tin asuba Inna Jummala ta gama kintsa masu duk wasu kaya nasu da zasu tafi dashi duk kuwa da Raihan yace basu da buƙatar hakan idan sunje can duk sai a saya masu wani.
 108. murna fal ranta yau zata hau jirgi lalle wannan yarinyar alkhairi ce a garesu.
 109. da yamma suna kan Rahinat suna tattaunawa sallamar Raihan ta iso da sauri Mlm Hardo ya tashi ya fita.
 110. fitarsa ko mintina biyu ba’a ƙara ba Rahinat ta farfaɗo, bata tsaya duban halin da take ciki ba shine tai wannan fitar aguje har Mlm da Raihan na kiranta bata tsaya bin ta kansu ba ta wuce da sauri Raihan ya shiga mota yabi bayanta.
 111. abinda kowa bai sani ba acikinsu Mlm duk kwanciyar da Rahinat tayi na tsawon wannan watanni tana sane, dan ciwo ciwo kam na damunta sai dai tayi zamanta hakane saboda wani abu nata.
 112. to jin ana niyyar fita da ita ƙasar waje yasa ta farfaɗo domin bazata so zuwa a wannan lokacin ba wannan lokacin nata ne.
 113. ****
 114. wasu haɗaɗɗaɗun marika har 4 Mami ta zube masa a kunci wanda yay sanadiyar fashewar gefen bakinsa da sauri ya sanya hannayensa biyu ya dafe wurin.
 115. “yaushe ka zama maƙaryaci ban sani ba Khaleed, yaushe ka daina bin umarnina ba tare dana gane hakan ba, dama har nakai matsayin da zaka iya cin amanata Khaleed, ina murna ina alfaharin na haifeka ashe ban haifeka ba tinda gashi har kana raina mani wayo, ahaka zaka shugabanci wasu”…..
 116. saurin ɗagowa yayi daga sunkuyan da kansa yake yana kallon Mami wadda zallar ɓacin rai ke shimfiɗe a fuskarta.
 117. buɗe baki yayi da son yin magana tai saurin tarar numfashinsa inda ta dakatar dashi da hannu.
 118. “bana son jin zancenka ,bana da buƙatar sake sauraron duk wata ƙarya taka Aayan, ka riga kayita ta kuma ƙare, buƙatata dakai ayanzu kawai itace ka bani amsar ina ƴata”?
 119. shiru yayi kansa ƙasa ya kasa magana, hannu tasa ta damƙi rigarsa tana girgiza shi “tambayarka nake ina Rahinatu”
 120. “Mami ban san inda take ba…..”
 121. tsinkesa da mari tayi sauran maganarsa ta tsaya.
 122. zata ƙara masa Nimrah tayi saurin riƙa hannunta.
 123. tana kuka tace, “dan Allah Mami kiyi haƙuri, ki danna fishinki ki tsaya ki saurari maganarsa”
 124. “mi zaice mani Nimrah banda ƙarya, duk tsawon watannin dana ɗauka muna waya da Rahinat ashe ƙarya yake mani duk yaudarata yake”
 125. _tin tafiyarsu Mami saudia a kullum saita kira Khaleed da Rahinat domin taji lapiyarsu,Khaleed bai taɓa nuna mata cewan bai tare da Rahinat ba, idan ta tambayeshi ina ƴarta da rawar jiki yake miƙewa yace bari yakai mata.abu ɗaya da Khaleed yayi shine haɗin na’ura mai sauya maganar mutum kasancewarsa ƙwarrare kuma gwani, duk wata gaisuwa da Mami zasuyi dashi sukeyi sai dai wannan haɗin da yay muryar Rahinat ke fitarwa bakuma ta taɓa gane hakan ba._bazaka faɗan inda Rahinat tayi ba, shin waiko ma ka saketa ne ban sani ba? ko kuma kasheta kayi ne?” +
 126. shiru yayi batare dayace komi ba hakan ya sake ƙona ranta dan sai faman magana take masa yaƙi bata amsa
 127. cikin tsananin ɓacin rai tace dashi, “baka zama kurma ba tukunna, nace baka zama kurma ba Aayaan sai lokacin da bakina ya furta maka kalma mara daɗi”…..
 128. “kiyi…..”
 129. ta katse shi da, “mi kajeyi a delhi?”
 130. babu jan lokaci wajen bada amsa yace da ita, “neman Angel”
 131. “uhmmm tumsanaye Aayan, to yanda ka tafi neman wata wadda ba matarka ba a wata uwa duniya haka yanzu nike son ka fita neman matarka ta sunnah, karka kuskura ka dawo mani cikin gidann ba tare da ita ba”
 132. zaro idonsa yayi da cewa, “6ix month fa Mami, yanzu ina zan ganta,plss ki tsaya ki fahimceni muyi magana, you should forgt about dat girl Mami let discuss……….”
 133. “bafa wai ina shawartarka bane ka gane, umarni nake baka idan har na cika wadda ta tsugana ta haifeka to ka shige ka fita ka nemo mani ƴata, kuma karka kuskura ka dawo cikin gidann ba tare da ita ba ko kuma ka dawon da ita ba’a matsayin matarka ba, duk yanda zakayi kayi kasan ka dawo da ita, ka dawo da ita koda kuwa mizai sameka”
 134. farucinta na ƙarshe ya daki cikin kwanyarsa, tafiya yayi domin kama ƙafafunta taja da baya tare da daka masa tsawa.
 135. tamkar Mami zatayi kuka saboda ƙololuwar ɓaci da ranta yay,
 136. “ka cuceni Aayan nace ka cuceni, daka faɗi mani da wnn abinda zaka saka mani kenan da banyi maka gardama ba daka nuna baka son aurenn na ƙyaleka kayi duk abinda kaso, saboda kasan mahaifanta bazasu nemeta ba yasa ka cutar masu da ɗiya ko, yanzu ka faɗan mi zance da kakarta data bani amanarta da wanna ido zan kalleta, mi zan gaya mata, ta ina zan fara mata bayani”
 137. “Mami wlh…..”
 138. “kayi mani shiru” ta faɗa a yayin data daka masa uwar tsawa.
 139. “ka fita ka nemo Rahinatu, ka fita ka memo mani ita a duk inda ta shiga koda kuwa kai zaka mutu ita ta dawo a raye”
 140. daga haka ta juya ta fice masa a gidan nasa gaba ɗaya.
 141. fitarta Nimrah ta yunƙura zatayi masa magana,mugun kallon daya wurga mata yasa ta fice da sauri itama kamin ya sauke fishinsa akanta.
 142. zama yay kan kujera yana birkita cikakkiyar sumar dake kansa,ya zaiyi ne?dama abinda yake ta tinani kenan tinda Mami tace zasu dawo ta yanda zata tsaya ta fahimce shi…..
 143. miƙewa yayi ya buɗa friedge ya ɗauko ruwan sanyi a gora, gaba ɗaya ya juyesa akansa tare da girgiza kan nasa.
 144. zarar keyi yayi ya tashi ya fita,tinda ya fita yake tinanin ta ina zai fara,shiga hanyoyi da fice kawai yake yabi tanan ya fito ta nan,maganaganun Mami nata sake yawo cikin kansa.
 145. driving ɗin yake hannunsa ɗaya dafe da goshinsa sai idonsa ɗaya da yayi jaa, shin dami zaiji, da neman wannan shegiyar yarinyar ko Maminsa ko kuma da rashin Angel ɗinsa.
 146. jin yanda zuciyarsa ta wani buga yayi saurin taka burki ya tsaya, dafe ƙirjinsa yayi yana sauke numfashi, shi ɗaya yasan irin raɗaɗin da yakeji akan son Angel.
 147. gam ya runtse idonsa ya kifa kai akan stearing, ji yay kansa na masa wani mugun sarawa kamar zai cire ga gabansa sai faɗuwa yake.
 148. alarm ɗin daya saita a wayarsa ne ya hau ruri, waƙar Angle am so lonely ita ke tashi akai,fuskarsa abin tausayi ya ɗago ya miƙa hannu ya ɗauka wayar, bai katse alarm ɗin ba ya barsa ya katse da kansa.
 149. hoton bayanta dake kan screen ɗin wayarsa yama kiss sannan ya buɗa glove box ya ɗauko magungu nansa yasha,sauke idonsa da zaiyi ta cikin glass ya hangi Angel tsaye a titi mota bayanta na neman bugeta.
 150. a sukwane ya fito acikin motarsa yana ƙwala kiran sunants Angellll, supa yayi yayin daya ƙarasa gareta zai kamata mai motar daya kasa taka burgi ya kaɗeshi.
 151. ****
 152. tinda Rahinat ta fito agidan gudu kawai takeyi bako waige,jin motar Raihan bayanta yana binta yasa ta yanki wata hanyar da mota bazata shiga ba, aiko da sauri shima ya kashe motan ya fito yabita da gudun.
 153. yana danna kai layin ya miƙe ita kuwa dama tana shiga ta raɓe a wani wuri, ganin wucewarsa yasa ta fito, gona ta hanga ta gefen damanta nan ta kutsa ta shiga bata tsaya ba sai data zo cikin rugar fulani sannan ta tsaya tare da sassaita kanta saboda makiwatan da suke wucewa da shanu. +
 154. numfashi take maidawa ga ƙishi dake cikinta, wayar Mlm data sure ta soke ajikinta ta ɗauko,nambobin banki ta danna ta sayo credt sannan tayi dialling ɗin wata numba ta kira.
 155. sai da wayan ta kusa katsewa sannan aka ɗaga,basu jima suna wata magana ba ta ajiye wayan ta nemi wuri ta tsuguna.
 156. takai kusan rabin awa a wurin saiga wata baƙar mota ta faka, da sauri ta miƙe ta shiga, tana shiga ta miƙa hannunta baya cikin aljihun jaka ta ɗauko faro water ta ɓalle murfin ta shiga kwankwaɗa.
 157. bata ajiye goran ruwan ba sai data kusa shanyewa tukunna ta sauke. ɗan numfashi taja sannna ta juyo ta kalla Khulaid dake kallonta ta ɗaga masa kai da faɗin “muje”
 158. “ina kenan?”
 159. “muje dan Allah Khulaid, mu tafi kar lokaci ya ƙure,yanzu idan har mutann suka gano inda nike to zasu gano inda yarima yake kuma kasan kasheshi zasuyi wanda ni kuma bani son hakan ta faru na ƙwammaci ni su kasheni”
 160. ta ƙarasa maganar alokacin da hawayen daya taru cikin idanunta suka zubo.
 161. da sauri kuwa Khulaid yaja motar suka ɓace a wurin, suna tafiya ta kunce ɗan kwanlinta, cikin damin gashin kanta ta ɗauko ƙatuwar wayar Raihan data ɗauke a asibiti, gidan sim ta buɗe ta zazzare nasa ta watsar ta window sannan ta amsa wani sabon layi hannun Khulaid ta saka ta kunna wayar.
 162. amsar wayar Khulaid tayi ta kunna hostpot tayi connecting ɗin wifi.play store ta shiga tayo downlod ɗin imo app, nan danan ya sauka ta buɗe account.
 163. numban Khaleed tai saving wadda dama tini tayi muguwar hadda akanta.srching ɗinsa tayi ta shiga,30mints kenan da saukansa,guntun murmushi ta saki sannan ta lumshe ido ta kwantar da kanta saman kujera, sai data sauke doguwar ajiyar zuciya tukunna wasu hawaye masu ɗumi suka biyo kuncinta.
 164. awa guda ta kawosu garin kano, sai da suka tsaya a wani chemist aka bata maganin zugin da ƙafarta keyi sannan suka wuce Aminu Kano International airpot
 165. da zuwansu suka fito zuwa wasu lokuta da suka ɗauka a wurin jirginsu ya tashi.
 166. ****
 167. aruɗe Raihan kema Mlm Hardo magana,
 168. “yanzu Baba kana so kace mani na rasata kenan”?
 169. “to hakane mana Alhjin Allah, tinda dai ta tafi, yanda muka sameta aguje gashi yanzuma ta fafi aguje kuma bamu san inda tayi bare mu nemeta”
 170. “da gaske ba ƴarka bace Baba?”
 171. “bazan kuma maka ƙarya ba Alhj,wannan haɗuwa da mukayi a lokacin daka abugeta alokacinne muka haɗu da ita amma ba ƴata bace”
 172. maganar Baba ta saukar masa da rashin kuzari, juyawa yayi batare da yayi masa sallama ba ya shiga mota ya wuce.
 173. driving ɗin yake hankalinsa duk bai jikinsa, ikon Allah kawai ya fito dashi titi da tin a ruga zai faɗa wani rami saboda sai da stearing ya ƙwace masa.
 174. kansa ya cika da tinanin ina zai sameta,wayarsa ya ɗauko ya kunna yana duban hoton da yay mata a gadon asibiti tana kwance.
 175. love at first sght,ajiyar zuciya ya sauke yay parking da motar gami da murza goshinsa.
 176. bai san da cewar yarinyar ta shiga zuciyarsa da yawa haka ba sai yau.
 177. yana ta tinanin kiran matarsa ya shigo wayarsa,bai ɗaga ba yaja tsoki ya kashe wayan gaba ɗaya tukunna yaja motar a wani fige ya tafi sai jan tsoki yake.
 178. ****
 179. hannayenta barƙale suke ta baya an ɗaure mata su da ankwa hakama ƙafafunta, duk wanda ya kalleta sai yay mata ƙwalla, daka kalleta kasan tana cikin tsaka mai wuya mutuwarta kawai take jira.
 180. yanda take tafiya a hanƙali kamar mara laka ajiki ɗan sandan prison ɗin ya daka mata tsaya, sam yanzu tsawarsu ko dukansu sun daina firgitata ko tsoratarwa hakan yasa ko gezau batayi ba.
 181. cikin mota suka sanyata aka wuce da ita zuwa president guest house. fitowarsu kawai ta sani banda ƙarasowarsu sai ayanzu da taji kulki a bayanta sannan ta buɗe idanuwanta dake buɗuwa da ƙyar.
 182. fitowarsu kewaye ƴan sanda suke da ita motsi kaɗan suke jiran tayi su bindigeta.
 183. tsakiya suka sanyata suna tafiya, gabanta ƴan sanda bayanta ƴan sanda sai guda biyu dake riƙe da ita a tsakiya.
 184. ABU AAYAN shine abin da aka rubuta a saman ƙofar shiga ƙaton palace ɗin dake gidan.
 185. cikin palace ɗin suka shiga da ita ragowan ƴan sandan prisoner suka ƙarasa da ita su kuma sauran suka tsaya daga bakin ƙofa. +
 186. kyakkyawan dattijo ne zaune saman wata farar kujera ta alfarma sanye da siririn farin glass yana rubutu bisa wasu takardu.
 187. rawanin kansa yay masa matuƙar kyau, daka kallesa kaga baƙin balarabe mai tsantsar kyawun halitta, motsa fuskarsa kawai yayi amma sai ta zama kamar yayi murmushi ne.
 188. girgiza kai yayi ya miƙa takardun dake saman table ɗin gabansa aka amsa, “ɗago mani da fuskarta”
 189. shine abinda yace ma ɗan sanda dake tsaye akan Rahinat, cikin saurin amsa umarnin his Excellency yasa hannu ya barƙalo da kanta dake duƙe.
 190. rufe ido Abu Aayan yayi saboda tsabar tausayin yarinyar daya kamasa, miyasa mutanenn suke haka, sam shi ba irin wannan horon yasa ayi mata ba.
 191. umarni ya basu nasu kunce mata ankwar dake jikinta sannan ya ɗaga masu hannu alama nasu tafi. da fitarsu ya taso shida kansa ya ɗauketa ya kwantar ta ita akan ɗaya daga cikin luntsuma²n kujerun dake wajen.
 192. wayarsa ya ɗauko ya danna numban likita yace yay maza yazo batare daya ja dogon lokaci ba.
 193. ba’ai minti biyar ba saiga doctr yazo,shi kansa saida ya girgiza da ganin halin da Rahinat ke ciki.
 194. kaminma Abu Aayan yace wani abu ya sanya mata oxygen nan da nan kuma aka shigo da gadon asibiti aka ɗauketa zuwa asibitin cikin gidan.
 195. buƙatar farko da likita ya nema shine jini domin kuwa babu jini ajikinta, tsammaninsu za’a sayo ne sai sukaji Abbi yace aɗeba nasa asanya mata.
 196. nan ya kwanta bisa gado akai connecting jininsa zuwa jikin gawar Rahinat.
 197. ****
 198. maƙil fadar mai martaba take da jama’a.
 199. daka kalla fuskar farin tsohon kasan akwai ɓacin rai a tare da ita hakama kowa na wurin.
 200. Nadeeyah dake tsaye daga gefe ya kalla yace, “har yanzu ina sake tambayarki, kin yarda kin amince zaki auri mazinaci fasiƙi matsayin mijiki”?
 201. hawayen dake fuskarta ta goge ta amasa da “ehhh”
 202. “shikenan, gobe za’a ɗaura maku aure sai dai ki sani kamar yanda ya fita yabar mani fadata haka kema zaki fita ki barta sannan kuma ki riƙe cewar bakya ɗaya daga cikin jikokina kuma babu wanda zai tayaki yawon nemansa, na baki awanni shida kacal kije kice dashi ya aiko magabatansa”
 203. yana gama faɗin haka ya miƙe ya fita ya barsu zaune a wurin.
 204. mamaki ya kama Nadiya,to Khaleed nada wasu magabata da suka wuce sune.
 205. kai wai mai yasa Papa yake hakane.
 206. Zaune Nadeeyah tayi shiru bisa katafaren gadonta tayi tagumi, baiwar dake tare da iita ke tambayarta, +
 207. “ranki ya daɗe naga kamar kina cikin damuwa, ko lafiya?
 208. bataji ta ba har saida ta sake magana a karo na biyu sannan Nadeeyah ta ɗago ta kalleta.
 209. kamar bazata bata amsa ba can kuma tace,
 210. “babu komai,kije kawai ina son hutawa”
 211. “tom ranki shi daɗe,ahuta lapia”
 212. daga haka ta fice tabar ɗakin.
 213. fitarta Nadeeyah ta miƙe ta shiga wanka, bayan ta fito ta gabatar da sallolinta kaman yanda ta tarasu akanta over dan rabonta da sallah tin shekaranjiya.
 214. bayan ta idar ta kwanta domin yin bacci amma sam yaƙi zuwa.
 215. yanzu ya zatayi idan har Papi ya koreta itama a wannan masarautar? ina zata nufa dan neman Khaleed bayan bata san inda yay ba? toko saudia zataje,amma idan taje tabbas babu mai saurarenta tinda sun san anwa jikansu laifi,wurin Abbi shine abinda ɗaya zuciyar tata ta sanar mata.
 216. aikam da sauri ta miƙe zaune,saukowa tayi daga saman gadon ta nemi doguwar rigarta baƙa ta sanya sannan ta ɗora blue ɗin hijab, kasancewarta fara ƙal sai tayi masifar kyau acikin hijabin.
 217. kallon fuskarta take cikin madubi,duk ta faɗa kaman mai jinya, ko dayake jinyar take wadda tafi ko wacce jinya zafi, tabbas rasa khaleed shine ƙarewar rayuwarta.
 218. tsaye tayi tana saƙawa da warwarewa akan zuwa wurin Abbi,tinawa da bai cikin masarautar yana can president house yasa ta koma ta kwanta haka har bacci ya ɗauketa.
 219. washe gari bata sami daman farkawa sai kusan 12 ta tashi da ciwon kai.
 220. wanka tai ta fito tai shirinta mai kyau tare da sanya rantsetsiyar alkyabbarta.
 221. zama tayi ta sanya wayarta gaba tana kallon hoton Khaleed dake kan screen ɗin wayarta,murmushi tai ɗan ƙarami tare da lumshe ido taja gajeran numfashi.
 222. _ko yanzu ya ya koma,nasan tabbas ya ƙara kyau fiye dana da,insha’Allahu yau zaka zama mallakina Aayan kuma da yardar Allah saina sami matsuguni a zuciyarka._
 223. gabanta ne ya faɗi ras lokacin data tina fa yana da aure wataƙilan yanzun ma yana da yaro ko yarinya,hawaye masu ɗumi suka shiga bibiyar kuncinta, wannan wacce irin ƙaddara ce ta so ta kamata,ta rasa wanda zata so sai wanda inuwarta bai ƙaunar gani a rayuwarsa sunan wai tana ƴar’uwarsa.
 224. ƙaramar ƙwafa tayi lokacin da tinaninta ya katse, “hmmmm wlh wlh saina ga bayan duk wadda tashiga tsakanina da kai,ni ɗaya zan zauna bani da kishiya al’adar masarauta zata sauya daga kaina, babu da shegiyar da zan zauna matsayin kishiya wlh, zuciyarka tawa ce ni ɗaya Aayan”
 225. buguzunbuguzun ta miƙe ta fita a ɗakin, tana fita aka take mata baya.
 226. ɗaukar hanyar garden tayi sai ta hangi ɗumbin mutane na fitowa daga cikin fada, a iyaka saninta babu wata matsala data danno kai,to mai akai aciki haka yau ba sanarwa.
 227. jakadiyar dake kusa da ita ta kalla, rissinawa jakadiyar tayi tace, “da girmanki ranki shi daɗe, ina mai farin cikin sanar dake an ɗau auranki yanzunn tare da Yarima Khaleed”
 228. zaro ido waje tayi tana kallonta jin zancen nata wani banbarakwai wai namiji da suna Hajara, “me kika ce?”
 229. “ƙwarai kuwa ranki shi daɗe, yanzunnan ma mai martaba ya fita daga fada ransa a matuƙar ɓace, kuma naga su Sultana Yasmeen nata masa magana babu wanda ya saurara acikinsu, amma tabbas an ɗaura aurenki ɗazu da aka idar da sallah Galadima shi ya zama waliyinki….”dakata” ta katse mata maganarta da daka mata tsawa. +
 230. fuuuu ta tafi kaman jakin da aka figa,tini hawaye ya wanke mata fuska,sashin mahaifiyarta ta nufa inda tana shiga ɗakin ta faɗa jikinta da fashewa da kuka.
 231. “haba Mama, wannan wanna irin rashin adalci ne aka mani, yau koda baiwa ce ni acikin gidannan ai ban kamaci haka ba, wannan aurena akai ko sadaƙa akayi dani”?
 232. tsoki Sultana Yasmeen tayi ta hankaɗata gefe, tai kan tumtum ta zauna itama ranta a ɓace yake domin zuciyarta wani irin suya take.
 233. “dan ubanki komi ya faru aike kika jawa kanki,yau da ace shegen alaƙaƙan yaronn yana cikin masarautar nan saiki nace sai kin auresa tinda ke mayyace, amma da bayannan saiki haƙura ,yanzu wa gari ya waya, to dan bakiji mai martaba yace ba da kukan da zakiyi sai yafi wannan, rabin awa kawai ya baki ki bar masa masarauta kuma keda ƙara shigowarta koda bayan ransa”
 234. ƙasa ta zube ta fashe da kuka, “na shiga uku,wai Papi wanna itin mara adalcin mutum ne…”
 235. bata ƙarasa ba Sultana Yasmeen ta sharara mata mari, “uban nawa kike kira da mara adalci”
 236. tamkar zararra ta hargitse tana faɗin,
 237. “to mine banda mugun mutum wanda bai san yafiya ba a rayuwarsa, mufa jikokinsa ne amma ya ɗau karan tsana ya ɗora mana, ina cikin gidan sarauta amma a ɗaura mani aure kamar wata bazawarar data tara ƴaƴa da jikoki sunan kuma wai ɗan sarkin gobe na aura…wlh abinn bazai taɓa yiwuwa ba ,bazan bar masarautar nan ba, babu inda zanje kuma wlh sai an sake min ɗaurin aure anyi shi tamkar na kowacce ɗiya maiji da kanta”
 238. sakato Sultana Yasmeen ta tsaya tana kallonta,lalle abin Yasmeen ya girmama wato rashin mutuncinta ƙara gabagaba yake.
 239. tsaki tayi zata wuce Nadeeyah ta ruƙota,
 240. cikin kuka take faɗin, “wlh wlh Mama idan har na gano dasa hannunki acikin waɗanda suka cutar da Yarima bazan taɓa barinki ba kema, dole saina tona asirin dukkaninku ki bar ganin kina mahaifiyata”
 241. inaa Sultana Yasmeen bata tsaya bata amsa ba saboda kyarmar da jikinta ya ɗauka ta fizge daga riƙonta data mata ta fice da sauri jikinta duk ya jiƙe da gumi saboda mummunan labarin daya iso mata.
 242. da Sultan Dameer suka fara haɗuwa a hanya wanda shima yana kan hanyarsa ta tahowa wurinta, kamar ita shima ɗin jiƙe yake da gumi,numfashi suka tsaya saukewa suna haɗiyar yawu.
 243. kamin suyi wata magana Sultan Salman ya iso shima duk a hargitse.yana zuwa yace dasu, “ya zama dole kamin mu ɗauki ran Khaleed mu ɗauki na mahaifinsa”
 244. “ka faɗi abinda kake tinanin zai iya yiwuwa Salman, kashe Mourad ba abu ne mai sauƙi ba, just think of another way”
 245. Sultan Abid da ƙarasowanshi shima kenan yay maganar.
 246. a hargitse Sultana Yasmeen tace, “ni duk ba wannane gabana ba, babban burina ayanzu mu kashe yarinyar nan kamin ta tona mana asiri”
 247. “itace kawai mafita, sai kusan abinyi yanzu,amma tayaya zamu sami yarinyar da akace yanzu haka tana gidan shugaban ƙasa”
 248. Sultan Baheer da shima a hargitse yake yay maganar.
 249. dogon tsoki Sultana Yasmeen taja kamin ta yarfe hannu tace, “na rasa Mourad wanna irin mutum ne, wato yanda yake bawa kowa tsaro ashiga gidansa haka muma da muke ƴan’uwansa bai yard adamu ba….”
 250. tasa yatsanta a baki tana cija tare da tinanin taya zata shiga gidan Mourad.
 251. “ki haɗa baki da ɗaya daga cikin ƴan sandan prison ya ɗauko mana ita”
 252. shawarar da Sultan Salman ya bada kenan.
 253. cikin tsoro Sultan Abid yace, “bakwa ganin iyanzu yarinayr nan ta sanar da komai game damu, idan har muka ɗauketa tabbas zargi zaiyo kanmu”
 254. wannan yace wnanan,wannan ya faɗi wannan haka suka dinga daga ƙarshe kowa ya tafi cike da takaicin rashin samun mafita.
 255. ****
 256. a ruɗe Raihan ya fito acikin motarsa yayo kan Khaleed.
 257. ɗagosa yay daga sujjaddar wahalar da yayi,ba ƙaramin gigicewa yayi ba ganin yanda jini ke zuba a goshinsa.innalillahi wa’inna ilaihi raji’un,sannu bawan Allah, kayi haƙuri wlh bana cikin hayyacina ne ban san lokacin da stearing ya ƙwace mani ba duk da ƙoƙarin da nayi,yanzu tashi muje asibiti kaga kana zubda jini” +
 258. nauyayyun idonsa ya ɗago ya zubesu akan Raihan da duk ke a firgice daganin yanayin Khaleed ɗin.
 259. idonsa ya mayar ya rufe tare da daɗa dafe goshin nasa wurin ciwon,banda yana cikin mayen Angel da sai dai uwar wannan guy ɗin ta haifi wani bashi ba.
 260. yunƙurawa yay zai miƙe ya kasa,Raihan ne ya taimaka masa ya miƙe,zai kamasa zuwa mota ya hankaɗasa gefe guda yaja lanjaran ƙafarsa da aka kusan markaɗewa zuwa mota.
 261. a ƙufule Raihan ya miƙe daga kifawar dolen da Khaleed yasa shi.taye yayi yana faman huci yana bin Khaleed da kallo,badan karya zama azzalumi ba da saiya koyawa wannan gayen hanƙali dan iskanci anama bashi haƙuri yana sake fusata.
 262. zai koma mota sai kuma yaga baiwa kansa adalci ba idan ya ƙyalesa ya tafi duba dashine da laifi,tsallakawa titin yayi da sauri yaje ya buɗawa Khaleed motar ya sanyashi aciki.
 263. Khaleed yaso yimasa gardama amma duba da halin da yake ciki na rashin ƙarfi sai ya haƙura,bisa ga kujera Raihan ya kwantar dashi, gaba ɗaya baya ganin komi sai ɗishiɗishi.
 264. emergency Raihan ya nufa dashi,suna zuwa aka masa dressing ɗin ciwon dake masa raɗaɗi sose.
 265. magunguna aka bashi amma baibi takansu ba bare yabi takan Raihan dake magana ya fita ya bar room ɗin.
 266. saboda buguwar daya samu a ƙafa da ƙyar yake takawa haka harya ƙarasa motarsa.
 267. Raihan dake bin bayansa ya ƙaraso da sauri yana kiransa, “brox kaga daka tsaya tukunna an wanke maka raunukan dake ƙafarka”
 268. “no need”
 269. abinda yace dashi kenan ya shige cikin motarsa yay mata key.
 270. barowarsa asibitin ya kuma tafiya bulayin neman da Mami tasa shi.ya kai kusan awanni huɗu yana yawo daga wannan titi zuwa wannan sannan ya sami wuri yayi parking don hutawa
 271. bai koma gida ba sai 12 saura na dare,koda ya koma gidansa kewaye da ninki baninki securities ɗinsa da’a tinaninsa Mami ta kawo masasu tin zuwansa delhi.
 272. _tinda bayanan da Raihana ta rattabawa Abbi bayanin cewan ana neman rayuwar ɗansa hankalinsa yay matuƙar tashi, nan da nan yasanya aka binciko masa inda masoyinsa yake sunan da yake kiran Khaleed dashi kenan, koda aka binciko masa aka sanar dashi yana delhi ba tare da wani sanya na ɓata lokaci ba ya aika masa da matakan tsaro haɗe da dakarin sojoji jirgi guda suka tafi domin kula da rayuwar ɗansa._
 273. shigarsa ɗakinsa yay watsi da abeben da duk yaci karo dasu.yana sauke numfashi ya zube ƙasa yana mai jin wani raɗaɗi a ƙasan zuciyarsa wanda ya alaƙantashi da abu biyu,rashin Angel da kuma fishin Mami.
 274. yakai kusan mintina goma sha biyar kansa sunkuye yanata fitar da zazzafan numfashi sannan ya miƙe ya ɗauko kwalban giya har biyu ya zauna ya kwankwaɗesu,idanunsa na rurrufewa haka yajanyo stool ya ɓare kwalin sigari ya kunna yana zuƙa har bacci ya ɗaukesa.
 275. tsawon kwanaki uku Mami batabi ta kan Khaleed ba wanda a ɓangarenta hakan ya bata mamaki tare kuma da shigarta damuwa, Khaleed baya fishi da ita gashi batasan inda yay dan neman Rahinat ba.cikin hanzari ta miƙe ta sanya ƙaton hijab ɗinta ta fita zuwa gidan nasa.
 276. koda ta shiga komi na gidan a hargitse yake, direct ɗakinsa ta haura ta wuce.
 277. tana shiga ta sameshi kwance kansa nannaɗe da gammon bandage. hanƙalinta tashe ta ƙarasa wurinsa gabanta na dukan taratara tana kiran sunansa.
 278. baccin da bai samu ba 2dayz shi ya samu yake ramawa a yanzu da baifi minti 5 da kwanciya ba.
 279. tamkar Mami zatayi kuka take kallonsa, kwalban giyoyin dake baje birjik ƙasan ɗakin take kallo kallon takaici, banda warin sigari babu abinda ɗakin yakeyi kaman bai taɓa maraba da wani abu waishi ƙamshi ba.
 280. kanta ta kwantar jikinsa tana faɗin, “kayi haƙuri yarona banyi dan muzguna maka ba, hakan da nayi shine dai², domin ina gudun fishin Allah ya tabbata akanka na kasancewarka azzalumin miji ga salihar matarsa,kayi haƙuri ɗana nayi dana sanin furucin dana maka cikin fushi”
 281. gaba ta sanyashi tana hawaye,yanzu rabin ran nata ne a wannan hali bata sani ba, fushi da ɗa ma baiyi ba, shi yasa ma’aikin Allah yace ku danna fishinku ga zuciyoyinku.
 282. tinaninta ne kuma ya koma ga Rahinat ƴar mune riƙon amana data amsa, yanzu mai zatace da Hajia dake faman kiranta tin ashekarnjiya kan ta kawo mata jikalle su gaisa ita tana fama da ciwon ƙafa bazata iya zuwa ba, tashi tayi ta gyara masa kwanciyarsa da yayita akaikaice.
 283. wayarta ta ɗauka ta danna kiran Nimrah tace ta aiko mata mai aiki dan ta lura cikin gidan babu wani mai aiki da alamu ya kori kowa.
 284. ba’a ɗau lokaci ba Noor ta ƙaraso, tana zuwa ta hau gyara kamar yanda uwar ɗakinta ta bata umarni.
 285. tana cikin yine ƙasan gadonsa taga ƙaramar vedio camera ta ɗauka ta miƙawa Mami.
 286. amsa Mami tayi,har ta aje sai taga kamar hoton Rahinat ne ajiki.
 287. maida hannu tayi ta ɗauka ta kunna vedion dake ciki.
 288. ganin Rahinat a hali na ha’ulai yasa ta buɗe ido tana kallo tare da faɗin innalillahi wa’inna ilaihi raji’un lalle Aayan ya cika mugu.
 289. ita kanta da take kallo sai data dafe fuska saboda jin saukar marin da Khaleed ya bama Rahinat tayi kaman atata fuskar.
 290. cike da tausayawa yarinyar ta girgiza kai tare da komawa zaune tana ci gaba da kallon vedio.
 291. rasras gaban Mami ya amsa,take ta zaro idanuwanta waje kaman zasu faɗo jin kalaman Rahinat da tayi.
 292. “ƙwarai babu ƙarya aciki, ka daina shakkun nice koba ni bace, yanzu zan sanar maka ko wace, BAIWAr daka jima kana lalube itace yanzu agabanka, nina sauya farincikin rayuwarka na mayar da ita zuwa ƙunci, gani gabanka ka ɗau duk matakin daka ga ya dace dani amma fa sai dai in har matsawar zan kasance matsayin matarka”
 293. mamaki da al’ajabi ya hana Mami rufe bakin data saki wangalalo tana sauraron zantukan da duk ya wakana tsakanin Khaleed da Raihana.
 294. jefar da camerar tayi a ƙasa ta fita da sauri zuwa temporary, tana zuwa ta kira mai lura da wurin ya buɗa mata ta shiga, ajiyar laptop ɗin da Khaleed yayi ta ɗauko ta kunna.
 295. sai ayanzu ta kuma yiwa vedion ɓatancin da’aka alaƙanta ɗanta dashi kallon ƙurulla.
 296. innalillahi wa’inna ilaihi raji’un abinda ta ambata kenan kamin ta furta “RAHINAT”
 297. _kin shigo rayuwar ɗana a karo na biyu domin ki sake cutar minshi ko,to abinda bazan taɓa bari ya faru ba kenan, na tsaneki na tsaneki Rahinatu,Allah yayi wadaran masu hali irin naki,macuciya azzaluma sai naga bayanki_.
 298. ta fito daga ɗakin da sauri ta koma ɗakin Khaleed zuciyarta a harzuƙe tana tinanin wanna irin mataki zata ɗauka akan Rahinat.jirginsu na dira a ƙasar Libya suka fito,basuyi minti biyar ba tsaye a airpot ɗin driver ɗinsu ya ƙaraso nan suka shiga yaja masu motar zuwa emir palace. +
 299. cikin boot Raihana ta shige hakan yasa koda aka zo shiga ba’a lura da ita ba duba da Khulaid ne agaban motan shi kuma yana matsayin ɗan cikin masarautar ne.
 300. tacan ɓangaren garden sukai parking, da sauri Khulaid ya fito ya buɗe mata boot ɗin ta fito duk ta haɗa uban gumi.
 301. ƙatuwar layafar dake naɗe ajikinta taja ta rufe fuskarta da ita yanda baza’a ganeta ba.
 302. kallon juna sukai ita da Khulaid ya ɗaga mata kai, gaba da bayanta ta kalla tukunna tayi sauri tai hanyar turakar Sultana Yasmeen.
 303. revers tayi alokacin datake ƙoƙarin shiga cikin turakar jin tattaunar da Sultana Yasmeen take da jakadiya.
 304. da gudu ta dawo baya a ruɗe take kiran sunan Khulaid,juyowa yayi jin kiran da take masa yasan ba lafiya.
 305. duk ta firgice ta kasa tsayawa tayi masa magana sai daya kamata tukunna ta iya buɗa baki ta fara masa magana hawaye na zuba a saman fuskarta.
 306. “sun kasheta….”
 307. shima ɗin firgici ya shiga da sauraron maganarta da yayi, “mi kika ce”?..yay maganar cikin in-ina.
 308. kanta ne ya ɗau juwa tai ƙasa zata zube yayi saurin kamota tare da ƙwala kiran sunanta, “Raihanaa…”
 309. ••••• a ruɗe Khulaid ya miƙe ya buɗa mota ya ɗauko ruwa a mota yazo ya yayyafa mata.
 310. a hankali ta buɗa idanunta tana kallonsa, hawaye ne suka shiga zuba ta gefen idonta sam ta kasa magana.
 311. “aina kika ji cewar ta mutu”?
 312. miƙewa zaune tayi tace, “zancen danaji gimbiya Yasmeen nayi kenan”
 313. “bata mutu ba” yace da ita kai tsaye.
 314. da sauri ta zuba masa  ido tana kallonsa,
 315. “taya kasan hakan”?
 316. “wannan wani sabon shirinsu ne kawai da suka haɗa ,amma ni ina da tabbacin bata mutu ba sai dai suna da niyyar kasheta”
 317. miƙewa tai duk tabi ta ruɗe, “ka tashi muje mu gani”
 318. tashi yay yabi bayanta suka bi ta bayan fada,sai da sukazo fita  da cikin masarautar sannan ya ɗebe hanƙalin masu tsaro ta fice da sauri tukunna shima yay masu sallama ya fita.
 319. direct president house suka wuce,securites ɗin dake zagaye da gidan bazai basu daman shiga ba sai dai dake su ɗin ƙwararrune kuma hatsabibai tintini sukai hanyar da zata sadasu da duk inda suke son shiga acikin gidan batare da kowa ya sani ba.
 320. ta bayan gidan suka koma ya ɗaga murfin ramin da suka haƙa wanda in basu ba bamai lura da wurin, kamin Raihana ta shiga saiga wani security yazo yana heyhey ya saitasu da bindiga.
 321. “maza maza ki shiga”
 322. Khulaid yace da ita, tana shiga ya juyo kan security ɗin daya saitoshi da bindiga, kamin yay wani yunƙuri Khulaid ya ɗana masa kibiyar dake hannunsa take anan ya faɗi ya mutu.
 323. gidane wanda suka yishi acikin ƙasa komai na buƙatarsu akwai aciki.tsaye ya sami Raihana tana warware lafayar dake jikinta.
 324. wasu riga da wando ta ɗauka ta sanya ta gyara parking ɗin kanta ta ɗaura hula akai, wata ƙatuwar baƙar jaka ta ɗauko ta shiga fito da wasu kayan aiki acikinta.
 325. cikin ƙwarewa take haɗa gskyer telescope ɗin data fito dasu wanda shi kuma Khulaid na daga gefe ya kunna laptop yana dubedube aciki.
 326. cikin mintina kaɗan suka hattama abinda zasuyi nan ta kunce ɗaurukan telescope ta maida cikin jakar shima ya kashe laptop ya maida ma’ajinta.
 327. ƙatuwar cardboard paper ya ɗauko ya miƙo mata ita kuma ta zaro biron dake saƙale ajikinta,a bisa ƙaton bench suka shimfiɗe cardbord paper ɗin nan Raihana ta shiga zana blueprint ɗin cikin gidan.
 328. bayan ta gama shi kuma Khulaid ya shiga bayanin ta yanda zasuyi subi inda suke son zuwa.a tare suka sauke ajiyar zuciya bayan da suka gama tsara bayanin nasu sannan suka kashe light ɗin wurin suka shiga ta ƙasan wani wuri wanda guri ne tsukuku da iska ma bata shigarsa sose babu kuma haske sai touchlight ɗin dake maƙale a goshinsu.
 329. tsayawa Raihana tayi,yay gaba sai juyo ya ganta tsaye dafe da goshi.
 330. dawowa yayi da baya ya kama hannun nata ya sauke daga saman goshinta.
 331. hannunsa yasa ya goge mata gumin daya tsatstsafo kamin yace da ita, “feel free kinji, kici gaba da tsayawa a matsayin jarumarki kar jikinki yay sanyi,insha’Allahu tana nan da ranta bata mutu ba dan basu isa su cutar da ita ba”
 332. manyan idanuwanta ta ɗago ta kallesa ta gyaɗa masa kai shi kuma ya sakar mata guntun murmushi.ɗaya daga cikin bindigogin dake jikinsa ya ciro ya bata ta sanya a bayan wandonta sannan yaja hannunta suka wuce. +
 333. ta cikin ƙaton swimmingpool suka fito, dama tun ba yau ba suka kashe na’urar CCTV ɗin dake bayar da saƙo ta wurin, nan suka rabu ko yay hanyarsa kaman yanda suka tsara ita tayi yamma shi kuma yay gabas.
 334. basu sha wuyar kutsa kai cikin asibitin dake gidan ba domin kuwa Khulaid tantiri ne tini ya bibbige duk wani security daya kawo masa kai.
 335. lokacin da Raihana ta ƙarasa zuwa ga ɗakin da’aka kwantar da Rahinat wasu dakarun sojoji ne kewaye da wurin kowa da bindiga hannunsa,duk da kasancewar dare ne 12:30 amma kap ɗinsu kowa idonsa tar babu mai yunƙurin yin bacci.
 336. saurin laɓewa tayi daga bayan gini tana maida numfashi,runtse ido tai gam wanda hawaye ya gama cika cikinsu, burinta kawai taga halin da ƴar’uwarta ke ciki, daidai da bugawar zuciya ɗaya bata taɓa jin son ƴar’uwar tata ba sai ayau taji ɗiso na tausayinta.
 337. a hankali take jan ƙafa jikinta manne da garu har ta wuce ta bar wurin ta zagaya ta window da zata iya hangota.
 338. window ta ɗan kama ta ɗafe, hangen cikin room ɗin take,gado ɗaya ne aciki kaman yanda telescope ɗinsu ya nuna masu.
 339. gabanta ne yay wani mummunar faɗuwa ganin ba kowa akan gadon,da gaske kenan sun kashe Rahinat na shiga uku,sautin kukanta dake neman fitowa ne yasata saurin saka hannu ta rufe bakinta.
 340. shushu ɗin dataji ta cikin cpu bluetooth ɗin dake maƙale a kunnenta yasa ta gyara masa zama dan sauraron abinda Khulaid yake cewa.
 341. sai data ɗan matsa daga inda take kaɗan sannan netwrk ya dawo mata norml, “what’s happnng?” shine abinda yace da ita.
 342. “Khulaid sun ɗauketa pa, na hanga ban ganota aciki ba”
 343. “kin tabbata bata ciki, gani a ƙofar ɗakin amma ban sami shiga ba”
 344. “ehhh wlh bata ciki, Khulaid kar suyi mata wani abin”
 345. “oak oak, ki nutsu karki firgita zan koma baya nayi harbi domin in ɗauke attention ɗinsu saiki shiga ciki kinji ko”
 346. “to” tace dashi kamin ta saita nutsuwarta ji kake dam dam sautin harbi na tashi.
 347. a tsorace tai ƙasa tare da toshe kunnenta.
 348. jin haka gaba ɗaya securites ɗin dake kewaye da wurin suka bar wurin zuwa inda suka jiyo tashin harbin.
 349. jiyo takun gudunsu ya sanya ta miƙe,tana leƙowa taga guda ɗaya tsaye a wurin yana kai da komowa, bindigar dake jikinta ta fidda ta harba masa a ƙirji kan kace wannan ya faɗi ƙasa nan ta samu ta zaga ta buɗa ƙofar room ɗin ta shiga.
 350. gadon ta ƙarasa tana fashewa da kuka, kanta ta ɗora saman pillow dake da ɗigeɗigen jini ajikinsa, “2wins sis” shine abinda ta faɗi alokacin data kuma fashewa da sabon kuka”
 351. maganar Khulaid a saman kanta ya sanya ta ɗago tana goge hawaye.
 352. miƙewa tai taje ta tsaya gabansa tana faɗin, “ya zanyi Khulaid sun kasheta bayan bata da haƙƙin komi”
 353. “sai yanzu kika san bata da haƙƙin komi bayan azabar da kika sa aka gana mata, duk abinda ya faru ke kika janyo Raihana,sam wannan ba dabara kikai ba ta ɗaukan revenge”
 354. ƙasa ta zube tana kuka mai sosa rai,
 355. “duk abinda nayi nayi shine domin itama ta ɗanɗani wahalar rayuwa kaman yanda nima na ɗanɗana, sai dai babban kuskurenta data tafka shine shiga hurumin da banata ba domin Prince Khaleed nawa ne tin bata san da halittarsa ba a duniya amma wlh ko ɗaya banso ya zama ace nice silar rasa ranta ba” +
 356. ƙasan shima ya tsuguna gabanta yace, “ki kwantar da hankalinki basu kasheta ba, wannan ɗaukan da sukai na ƴan sa’oi ƙalilan ne da suka gabata kamin zuwanmu wurinn kinga kuwa baici ace sun mata wani abuba yanzu”
 357. “to miye abinyi yanzu”?
 358. “ke zaki maye gurbinki na asali”
 359. a razane ta ɗago tana kallonsa,tsaye ya miƙe tare da sanya hannayensa cikin aljihunsa ya juya mata baya.
 360. “hakan kawai shine mafita,shine zaisa mu sameta a raye, domin hankalinsu zai rabu gida biyu, zasuyi tinanin wadda suka ɗauka itace fake ke kuma ta asali, hakan zai sanya hankalinsu ya sake dawowa nan kanki ni kuma zanje na fidda ta acan”
 361. gyaɗa masa kai tayi fuskarta cike da damuwa da fargaba, kai shima ya gyaɗa mata yace, “fuskarki bata kyau da damuwa ki saki ranki ki kwantar da hankalinki i will handle everything insha’Allah”
 362. murmushin yaƙe tai sannan tai saurin sanya irin kayan prison ɗin dake ajikin Rahinat ta kwanta saman gadon.
 363. “dont forgt the fake one bata magana”
 364. shaf ta manta sai yanzu ta tina, gashin kanta ta warware ta baza kan pillow shi kuma drctrn daya ƙaraso yanzu wanda Khulaid yay masa waya yazo ya shiga aikinsa na naɗa mata bandages da connecting ɗin drip tare da mata alluran bacci.
 365. kasancewar jininta baida ƙarfi ana mata allurar bacci ya ɗauketa,na tsawon mintina 5 Khulaid ya tsaya yana kallonta sannan ya duƙa ya mata kiss a kumatu tukunna ya fita da gudu a ɗakin.
 366. da fitarsa Abbi suka shigo cikin ɗakin.da sauri Abbi ya ƙarasa gadon da Raihana ke kwance, taɓata yayi ya tabbatar da itanne sannna ya sauke numfashi.
 367. umarni ya bawa sojojin dake wurin kan a bincika ko’ina da ina na gidan sannan a tabbatar da cewar an kamo masa waɗanda suka kawo wannan hari.
 368. nan da nan suka amsa umarnin oga kowa ya fice aka shiga operation.
 369. gaba ɗaya gidan sun sakar masa tergas wanda ma shi Khulaid tintini ya manta da ficewa daga gidan yaje inda zashi.
 370. hankalin Abbi ne ya tashi wanda gaba ɗaya yayi kan masoyinsa,duka ƙirjinsa ya shiga yi,da sauri ya fice a room ɗin yay office ɗinsa.
 371. zamansa ya danna wasu nombers a landline ɗin dake kan table ɗinsa.ƙarshen wayarsa kawai naji wanda ya amsa da ok.
 372. kanka ce mine wannan jiragai sun tashi zuwa nigeria kaman yanda Abu Mourad ya bada umarni domin aje a kula masa da rayuwar ɗansa.
 373. bacci sam yaƙi zuwa idon Abbi, wato ba ƙaramin kewar matarsa da ƴaƴansa yake ba musamman ma ɗansa, sosai yake buƙatar kasancewa atare dasu.
 374. tsoki ya ɗanyi ya kwantar da kansa bisa katafaren gadonsa,shin maima yasa yaƙi yarda da ɗansa bayan yasan irin kyakykyawar tarbiyar da suka masa, miyasa ya yanke hukunci bai tsaya yayi dogon bincike akan hakan ba.
 375. amma shi da dukkan mamakinsa da yake har yau ya kasa hasaso who is behind all this,ga dai abinda yarinyar tace to amma idan acikin masarauta ne suwa take nufi bayan shi babu wanda yaga yayi kama da munafiki aciki.
 376. ada yayi alƙawarin bazai koma ga ɗansa ba sai lokacin daya kama magautansa a hannu sannan zaije garesa ya bashi damar yanke hukunci da kansa a kansu, amma yanzu bazai iya ba sose yake ya kasance tare dasu ko ya samu ragin damuwar da yake ciki.
 377. ya kamata ayanzu ya sanar da mai martaba amma kuma kamin yay yana kyau ya sanar da wani acikin ƴan uwansa musamman Yasmeen ko Dameer.
 378. da wannan niyar ya kwana wanda kuma yake saka ran insha’Allahu a goben zai dira a nigeria wurin iyalinsa.
 379. ****
 380. a hanƙali ya buɗa idanunsa daga kwancen da yake yana ƙara jin zafin ciwon dake goshinsa.
 381. Mami ya hanga zaune akan beside drower tayi tagumi wadda da alama tayi zurfi a tinani.
 382. da sauri ya miƙe zaune ganin baƙon abu danshi zai iya rantsewa baifi sau uku ya taɓa ganin taguminta ba,farkon rabuwarsu da Abbi, lokacin datazo ta sameshi ya koma ɗan giya sai lokacin da yay yunƙurin illata idiot yarinyar nan.
 383. ƙafarsa da har yanzu bata bar masa ciwo ba ya ziro ƙasa, sai daya taɓota sannan ta san da tashinsa, ɗago da jajayen idonta tayi ta baza masa tana kallonsa cikin tausayawa,shi kuma ɗanta da haka rayuwarsa tazo na kusa dashi suke cutar dashi.
 384. ba ƙaramin tashi hanƙalinsa yayi ba a lokacin daya sanya idanuwansa cikin nata, babu tantama kuka tayi, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un ya ambata a sa’in da zuciyarsa ta shiga suya, miyasa Mami kuka? waya ɓata mata har yay silar zubar hawaye daga idanuwanta? bazai taɓa ƙyale ko wane ba.
 385. cikin ruɗewa ya tallafi fuskarta yana jera mata tambayoyi game da damuwar datake ɗauke da ita wadda ya ganta ƙiri² gatann.shirun data masa ne yasa hankalinsa ya kuma tashi, ƙanin hawaye ne ya cika idanuwansa, kneelingdown yay gabanta tare da kamo hannayenta ya sanya cikin nasa, a hankali kuma cikin sanyin murya ya fara magana,
 386. +
 387. “nasan nine Mami, i know am the reason of your tears,ina roƙonki da girman Allah karki kumar hawaye saboda ni, na maki alƙawarin zan dawo maki da ƴarki, naso ace ranar dana fita na dawo maki da ita kamar yanda kika biɗa sai dai incedence ɗin daya faru shi ya hanani bawai da son raina ba… and even dat i try naga cewar na fita a washe gari sai ciwon dake jikina ya tsananta….”har tarar numfashinsa tayi tace
 388. “ya tsananta ko ka tsananta shi da shan giyarka da zuƙeƙenka”
 389. ta faɗi ayayin data katse sauran maganganunsa tana mai jifansa da wani irin kallo na zallar ɓacin rai mai cike da jin haushi da takaici.
 390. girgiza kansa yayi like wani ƙaton lizerd yace, “no ba haka bane Mami, you know it is the only thing reduce the devastating pain in me….”
 391. “banda adu’a ko?”
 392. sai daya ɗan ja numfashi kaɗan ya sauke sannan ya amsa mata da, “no,itama inayi ai”
 393. ƙaramin tsoki tayi gami da girgiza kai tace, “Allahumma yahdika”
 394. ya amsa da “ameen, amma Mami kin daina fushin ko?”
 395. yayi maganar cikin damuwa.
 396. “ai bana fushi dake Aayan, ko nayi na mitsitsin lokaci ne”
 397. wani daɗi ya mamayeshi nan ya zauna inda ya tankwashe ƙafarsa ya kuma damƙe hannunta acikin nasa.yace
 398. “Ummi nah,idan har shan giyan da nike na damunki to ki daina bcx am gonna meet my Angel soon domin ina jin hakan ajikina, Mami ki tayani da adu’an ganinta,  wlh itace kawai ke ɗauke da maganin damuwar da nake ciki, Ummi ko babu Abbi zan rayu cikin farinciki 100% idan har ina tare dake da Angel”…..
 399. “vedion dake cikin wannan camerar gaskia ne ko kuma shima haɗinka ne dan ka sake raina min wayo”?
 400. jin tambayar tata yayi a bazata nan ya ɗago yana duban camera ɗin dake hannunta fuskarta ɗaure babu alaman wasa.
 401. shiru yayi bai iya cewa komi ba sai data sake katse shirun nasa da faɗin, “ƙarya ne ko?”
 402. ya girgiza kai da faɗin, “a’a Mami”
 403. “to ya abin yake ina magana ka mani shiru ko sabon rainin hanƙali zaka kawon?”
 404. “Mami wallah ba ƙarya bane gaskia ne kuma idan baki yadda ba bari na nuna maki ma ki gani”
 405. ya miƙa hannu ya ɗauko laptop ya aje kan center table ya kunna mata yayi connecting CC nan zahirin vedion ya bayyana.
 406. kallo take cike da mamaki,sai ayau ta yarda da maganar hausawa da suke cewa na jikinka shike cutar dakai kai dai kawai ka kalli mutum yanda ka ganshi.
 407. bata ƙarasa gani bama tayi wurgi da system ɗin ta miƙe tana huci, “haƙiƙa bazanta taɓa yafewa Rahinat ba and she must pay for it”,Sai huci take.
 408. ta ɗora da faɗin, “ina fatan daga ranar da aka kawo maka ita babu abinda ya kuma shiga tsakaninku saboda bazan yarda na sami jika ta ƙarƙashin wannan mayaudariyar yarinyar ba”ta fad’a babu ko alamun wasa atare da ita.
 409. “babu abinda ya taɓa shiga tsakanina da ita Mami”….ya fad’a cikin girmamawa.Sai data gama kallonshi tsaf tukun tace
 410. “daren farkonku fa? shi nike nufi ba bayan shi ba wani abu daya kuma haɗaku?…. wallah koda rabo ya shiga tsakaninku bazan karɓeshi ba Aayan”
 411. ya tari numfashin da faɗin, “babu fa abinda ya taɓa shiga tsakaninmu Mami, duk abinda na faɗi maki ƙarya ne, nayi hakanne domin farincikinki sannan kuma kiyi tafiyarki ki barni da ita……”
 412. nan ya shiga labarto mata dukkan abinda ya faru da dalilin daya sanya yayi hakan.
 413. “na gode Allah, yanzu abinda nake so dakai  ka rubuta mata takardar sakinta saki uku cas ka shirya anjima ka kaiwa kakarta ,daga yau har zuwa ƙarshen rayuwa babu auren da zai kasance a tsakaninku”
 414.  
 415. jin maganar tata yayi ta dakesa duk da bawai damuwa ne hakan ba, shi kansa ko lokacin daya faɗiwa Rahinat ba aure tsakaninsu ya mata barazana da hakan bawai da gaske ya faɗi ba, duk da bai sonta bazai taɓa iya sakinta ba har sai sanda Mami ta bashi izini amma yanzu tunda har ta furta hakan alhamdulillah.hijab ɗinta ta ɗauka ta sanya tai ƙofa zata fita sannan ta juyo tace dashi,
 416. “mintina talatin kawai na baka, ka kimtsa ka rubuta divorce paper ka kawo mani ni da kaina zan kai masu”daga haka bata kuma cewa komi ba tayi waje zuciyarta cike da tunani iri iri. +
 417. tsintar jikisa yayi da yin sanyi wanda bai san dalilin hakan ba.
 418. toilet ya faɗa bayan fitar tata, ya jima tsaye cikin shower idanunshi a rufe yayin da ruwan ke sauka bisa jikinsa  sannan ya fito.
 419. koda ya fito an jere masa lunch, sai daya shirya cikin ƙananun kaya derk blue jeans da kuma army t-shirt, jikinsa ya feshe da wasu mahaukatan turaruka masu daɗin shaƙa, sumar kansa dayasha gyara tayi kyau sai sheƙi take.
 420. zama yayi ya ɗau gurasar da aka mata vegetable souce yaci tukunna ya kora da banana smothie.
 421. bayan ya kammala ya miƙe ya wuce ɗayan bedroom ɗinsa, drower ya jawo ya ɗauko wani file, ƙaramar jotter ce a tsakiya wadda hotunan Abbi ne da Mami na aniversry ɗinsu.
 422. biro ya ɗauko ya zauna bakin gadon ya yagi jotter ɗin, ya ɗora biro kan takardar sai ya tsaya yana tuna yama sunan yarinyar dan shi harga Allah bai san sunanta ba.
 423. karan hancisa ya shiga murzawa ko Allah zaisa ya tuna sunan nata.idonsa dake lumshe ya buɗe, kan wani ƙaramin envelop ya sauke idon nasa, envelop ɗin mai kyau yaji design na heart love ajikinsa.
 424. ɗaukan hanƙalinsa da yayi ya sanya ya miƙe, ɗaga takardun dake kansa yay sannan ya zaro shi. ido ya sake lumshewa gami da shaƙar daddaɗn ƙamshin dake fita ajikinsa.
 425. buɗe envelop ɗin yayi inda yaci karo da takarda ciki daga sama an sanya Angel.
 426. saurin zarota yayi jikin sa har rawa yake saboda yadda yake rumud’in son jin mai yake d’auke cikin wanan takarda ya warwareta dan karanta mike cikinta. wani good hand writing ya gani mai ɗaukan hankalin duk wanda ya kalle shi ido ya zuba yana kuma juya takardar ciki da bai daga bisani kuma ya .rufe ido yayi ya buɗa kamin ya fara karanta abinda ke ciki kaman haka.
 427. _ka soni ba tare daka san koni wace ba, ka tsaneni ba tare da kasan wace ni a zuciyarka ba, I love you Khaleed i love you i love you so much…..nice farincikinka daka jima kana nema, nice wadda idanuwanka keda muradin gani a koda yaushe, nike zafafa zuciyarka kuma nike sanyayata,ina nufin Angel ɗinka, karkai shakku ni Raheenat nice Angel idan baka yarda ba kuma ka sake diban pix ɗin da kake ajiyansa tsawon shekara Shida sannan ka kalla wannan ƙaramin pix ɗin dake haɗe d wannan lettern.
 428. daga nan ta zana hoton imogi mai alaman murmushi.
 429. jiki na ɓari ya sunkuya ya ɗauki envelop ɗin ya zaro pix ɗin dake ciki.
 430. hoton bayanta ne jikinta ɗaure da towel ta ɗan zame kaɗan.abinda ya gani shiya sanya shi zaro ido yana sake duba.
 431. sai daya murza idonsa tukunna ya kuma buɗewa,jiki na kyarma yay ƙasan pilow ya ɗauko pix ɗin angel.
 432. wasu numfarfashi ya shiga saukewa bakinsa buɗe duka sai wani irin murmushi dake fita daga fuskar tasa.
 433. bakinsa na rawa yake faɗin, “my my Angel”
 434. wani daɗi da farinciki ne ya mamayesa ya faɗa kan gado yana kallon sama zuciyarsa sai amsawa take.


[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]