[Advertisements⬇️]

YAREMA KHALEED CHAPTER 3 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

YAREMA KHALEED
CHAPTER 3
Hankalin Khalid inyayi dubu ya gama tashi sai kaiwa yake yana komawa saboda yanda yaga Raihana bata ko motsi wadda duk tinaninsa ke basa Rahinat ce.
+

duk yabi ya gigice banda uban gumi ba abinda ke kato mashi, sai kuma cigaba da safa da marwa da yake da mafisa yana bugawa likitoci tsawa yama hanasu nutsuwa suyi aikinsu, ganin yanayinsa kaman wani mayunwacin zaki mutanen dake ciki sukai tsit, wata nurse kuwa harda sakin stethoscope ɗin dake hannunta wanda drctr ya bata riƙo.

shi kanshi likitan so yake yay magana amma ya gagara yinta bare ya samu damar yi mashi bayanin abinda ke faruwa akan ciwon daya ɗaga hankalinsa wanda ba wani babba bane

yanda yaga likitan yay lakato yana dubansa wanda shi tsantsar mamakin irin wannan soyayyar ya sanyashi tsayawa yana duban Khalid, to randa akace kuma raine babu atare da yarinyar ya zaiyi kenan, ƙwalla ce ta tarar masa azuciyarsa yake cewan Allah sarki Allah yasa dai kai ka rigata ba ita ta rigaka ba.

ganin haka Khalid ya doka masa razananniyar tsawa data firgita shi yay saurin dawowa dga duniyar thinking ɗin daya cala, kwalar rigarsa Khalid ya damƙa yana kora masa woring na idan har ya kuskura wani abu ya sami matarsa to wlh bazai barshi ba.

suna haka saiga Papi ya ƙaraso wanda saukarsu kenan shida su Mami, shi yayo asibiti da akace Khalid nan su kuma su Mami sukai masarauta.

kafaɗarsa Papi ya dafa yana dubansa, ransa duk ba daɗi domin kuwa shi sam baya son wannan zafin zuciyar na jikan nasa, shi kuwa ƙasa yay da kansa cikin zuciyarsa faɗi yake to mai kuma ya kawo wannan tsohon, shifa a rayuwa sam baya ƙaunar yana abu tsohonnan na wurin duk sai ya hanashi abinda yaso

da ƙyar da siɗin goshi Papi ya lallasheshi har zuciyansa yay cool drctr ya sami daman yi masa bayanin abinda ke faruwa.

drips aka sanya mata haɗe da allurai, a hankali yay maganar ko za’a sanya mata jininsa sukace a’a ai bata buƙatar komi sai wannan ,yanzu haka cikin mintina 20 nan gaba zata farfaɗo.

duk dayaji daɗin albishir ɗin likitan amma kuma still fargaba da tashin hanƙali basu barsa ba har sai lokacin da Angel ta farka, shi kansa Papi so yake yay masa maganar Mami dake can hankali tashe ita da Abie da kuma kakansa Abou Mourad shima da yay matuƙar ɓata masa rai amma sam yaƙi sauraronsa, daya fara magana zaice dashi Plss Papi ka bari ta farka sai muyi magana.

Papi ko girgiza kai yay cikin ransa yake cewan lalle yaro bai san wuta ba sai ya taka, wato maƙiyiyarsa yarinyar data ɓata rayuwarsa tai masa sharri amma ita yake kira yanzu da masoyiyarsa.ɗago da ido yay ya kalla Papi da kansa ke ƙasa ya hango damuwa a fuskar tsohon wadda shi kuma baya so, hakan ya sanya ya miƙe ya kama hannun Papi sukai waje ya sanyashi mota yace akaisa hotel ya huta kar asoma akaishi waccen baƙar masarautar wadda yanzu yake mata kallon masarautar azzalumai.

bayan ya dawo room ɗin still Raihana bata farka ba, kujeran dake kusa ya zauna tare da kamo hannunta ya sanya nashi ciki yana shafawa a hankali kaman yana shafa ɗanyan ƙwai.

idanunsa da suka gama ƙanƙancewa saboda tsananin damuwar da yake ciki da fargaba ya baje kanta yana kallonta, muryarsa a raunane kaman zaiyi kuka yake kiran,

” My Heena, my Heena, Heena Angel plss ki taimaka ki buɗe idonki bana son ganinki a haka, nasan bazaki mutu yanzu ba saboda zamu rayu ne tare kuma mutu tare amma ni bana son ganinki cikin jinya”

ya ɗora ɗayan hannunsa saman fuskarta wadda ya jita laushi, yana shafawa yake ci gaba da cewa,

“wlh Angel ina sonki, wlh ina sonki, ki tashi dan Allah, na maki alƙawarin koda ƙasar libya zata ƙone gaba ɗaya saina ɗauka fansa akan abinda azzaluman masarautarta suka maki, babu wanda zan taɓa bari duk wani hannu ciki saina hukuntasa”

yay shiru kamin ya ƙare mata kallo sannan kuma da wata muryar raunin yake faɗin,
“amma fa dan Allah kar haƙurinki ya hanani aiwatar da komi kinji Queen of King”

ya runtse ido gam tare da jinginar da kansa jikin ƙarfen gadon, zafin zuciyarsa na daɗa kamuwa, tsoro da fargabar kuma yanda zata karɓesa na damunsa, gefe guda kuma har yau ya rasa wanna hukuncin zai ɗauka acikin wanda zuciyoyinsa ke bashi shawara dan duk basuyi mashi ba

jin kaman motsinta ya buɗe idonsa, da sauri ya ɗago kansa daga jinginar da yay yana dubanta.
ƙasusuwan hannayenta dana ƙafarta da sukai nauyi take ƙasƙas dasu haɗe da yin ƴar ƙaramar miƙa gami da yamutsa fuskarta.

a hankali kuma ta buɗe idonta da suka kumbura sakamakon daɗewar da sukai a rufe dan ciki har yay taruwar jini.
ɗayan side ɗinta ta kalla sannan ta kuma waigo da kanta a hankali ta kalla ɗayan side ɗin nata da Khalid ke zaune riƙe da hannunta kaman ance masa za’a ɗauketa.

rufe ido tai kaɗan ta kuma buɗewa dan tabbatar da abinda ta gani, jikinta ta mintsila taji zafi, tabbas ba mafarki bane gaske ne, bum bum zuciyarta ta buga ciike da tsoro shikenan ta gama kaɗewa.

gaba ɗaya ta gama tsarguwa da irin kallon da Khalid ke mata wanda yay mata kama dana tuhuma.
a tsorace ta ɗauke idonta daga kansa ta maida kallonta ga yatsun ƙafarta.

_innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, asirina ya tonu kenan?._
cikin zuciyarta tai maganar amma kuma ba wanda zai bata amsa

Khulaid shine wanda ya faɗo mata arai, wani nisan tinani tai kan nan ta zare ido, shi ya tona mata asiri kenan, dama maci amana ne shi, ta tabbata babu wanda ya san komi kuma babu wanda zai faɗi saishi.

ɗayan ɓangaren zuciyarta tace mata to idan kuma bashi ɗin bane bafa, kai dole ma shine tinda har ga Khalid yazo inda take…kyarma jikinta ya ɗauka ta shiga uku ta gama lalacewa watan azabtuwarta kaman yanda taiwa 2wins ɗinta ya kama tare dana mutuwarta.

hankalinta kam duk ya gama tashi haka ma mamaki ya mamayeta ya kanainayeta, satar kallonsa tayi a tsorace kamin ta ɗan ja kaɗan.

saurin riƙota yayi, juyowa tai ta dubesa taga yanda yake kallonta da fuskarsa abar tausayi, girgiza mata kai ya shiga yayi da sanyin murya yake cewa,
“plss dont be upset wit me Angel, ki manta da dukkan abinda ya faru a baya”abinda dama yake ta tsoro kenan idan ta farka, marairaicewa yay ya hau lallashinta. +

ita kuma sai ayanzu ta shiga tinanin karfa ta aikata saɓo tinda ita ba muharramarsa bace ba kuma ainihin matarsa bace amma kuma ya kamata tai amfani da wannan daman ta ɗauke zuciyar data jima tana jira

to tayaya zatai hakan, tasan ayanzu dole 2wins zatana fushi koma ta tsaneshi tinda dole zatai tinanin halin da take ciki a yanzu shine.

amma kuma dole tai wani acting ɗin kamin a sami ɓacin rana, ƙwacewa tayi daga riƙon da yay mata ta miƙe zaune ta ɓata rai, daga kan kujeran ya tashi ya dawo gefen kusa da ita ya zauna.

zata matsa yasa hannu ya kareta tare da kamo fuskarta, cikin faɗa tace dashi, “abeg leave alone”

“kiyi a hankali allura ke ajikinki karki ji ciwo”

“sai kuma mi ya dameka da wannan, mima ya kawoka inda nike, ko kuma hukuncin duk da kakanka yay mani bai isa ba kaima sai kayi naka”

ta sanya kuka wanda yajisa har ƙarƙashin zuciyarsa, bazai iya sauraronsa ba ko kaɗan domin wani sabon sonta ne ke daɗa ratsa shi, ji yake tamkar ya haɗiyeta.

rumgumeta yaje yi ta dakatar dashi d’auke da b’acin rai a fuskarta, kallonta yay nan ya kuma shiga damuwa.

bata shirya ba taji ya rufeta da faffaɗan ƙirjinsa kamin kuma yay mata hot runguma.

lallaminta yake tare da kalallameta da kalamai masu ratsa zuciya akan laifukan da yayi mata, ji tai zuciyarta ta tsinke da irin kalamansa, lallai Yarima abin so da ƙaunane, kuma haƙiƙa babu macen da zata so ta sameshi ta kubce masa

tin shigarta masarauta ta kamin da sonsa har kawo iyau, bata tinanin zata iya barma 2wins shi.

wani tinani datai ta saki murmushin da ita ɗaya taji sautinsa, itama watan jin daɗinta ya kama, koda zata nemi iyayenta to ba yanzu ba har sai lokacin data mallaki Yarima.

ɗan turesa tai ajikinsa zata ƙwace, sakinta yay yana kallonta gami da sakar mata kyakykyawan murmushi.fuska ta kauda gefe tana turo masa baki gaba.

murmushi mai sauti yayi ya sanya hannu ya juyo da fuskarta tana kallonsa, a hankali yayi maganar, “kina son Prince ɗinki shima ya kwanta a irin wannan gadon ko”?

bata basa amsa ba sai bugu da zuciyarta take gami da jin kuma abinda take shirin aikatawa fa bashi da kyau.

“wai ka manta ka sake ni ne”
tai maganar da ɓacin rai.

“na jima da dawo da matata ai”

ta gyaɗa masa kai, “ni ban yarda ba, kuma bazan yarda ba har sai an sake mana sabon aure”

sauke ajiyar zuciya yayi da tambayanta, “ta hakanne kawai zaki yarda da cewan zuciyar Yarima taki ce kuma shi mallakinki ne”

kaman bazata basa amsa ba kuma ta gyaɗa masa kai, idonta ƙasa tana wasa da diamon ring ɗin dake hannunta tace dashi, “ka yafe min laifin dana maka dan Allah”…

bata ƙarasa ba ya rufe mata baki, “4gt about d past Angel”

fashewa da kuka tayi ta rugumoshi.
cikin tashin hankali yake tambayarta reason ɗin yin kukan, da muryan kuka take basa amsar ita ta tsani masarauta ta tsani ƙasar libya da duk mutanen dake cikinta, indai har yana sonta to ya ɗauketa su bar ƙasar gaba ɗaya su koma wata ayi masu sabon aure suyi rayuwarsu su biyu. +

yana shafa bayanta yake cewa, “to is oak daina kukan bana so, zanyi dukkan abinda kike so amma saina fara ɗaukan revenge akan waɗanda suka cutar min dake”

girgiza masa kai tayi tace, “a’a ni duk na barsu da Allah kawai mu tafi”

domin ya kwantar mata da hankali yace to shikenan, abincin dayasa aka kawo ya janyo ya zuba ya shiga bata tana ci,banda aukin kallonsa ba abinda take duk wani abin burgewa na rayuwa ya biyo bayan Yarima wlh, zancen datai a zuciyarta.

****
B’angaren su Sultana Yasmeen kuwa bayan sun bugawa Khulaid abu a bayansa jini ne ya ɓalle sharshar sai zuba yake, zuciyoyinsu bako ɗison imani saboda kar asirinsu ya tonu su Sultan Baheer suka sake dannesa da pillow, tin Khulaid na motsi har numfashinsa ya ɗauke gaba ɗaya ya daina koda motsa yatsa ne hakan ya basu tabbacin ya mutu.

ajiyar zuciya suka sassauke, sun gama da ɗaya saura ɗaya.
Sultana Yasmeen ta ƙara damƙe gashin Rahinat sose tace, “mai baƙar zuciya da taurin rai, wlh ko baki mutu ba sai mun binneki da ranki domin kuwa bazamu taɓa bari ki tona mana asiri ba, masarautar Abou Mourad tamuce ta iyaka ƴaƴanmuce kawai wlh, bazamu taɓa bari a nuna mana son kai ba”

kallon rashin fahimtar zancen nata Rahinat tayi, ita duk zatonta har yau tuhumar da ake mata akan sharrin data ma Yarima ne kuma sai taji wani zance yanzu na daban wanda bata gane inda ya dosa ba.

maida kallonta tai gasu Sultan Salman da suka shigo da drcter zasu ɗau gawar Khulaid a sanya a carpet a fita dashi.

kukan kura tai ta warci kanta daga hannun Sultana Yasmeen tai wurin da sauri ta ruƙo gawar tana girgiza shi.
babu ikon ihu bare magana sai buɗe baki da take tana ɗora hannu saman ka hawaye duk ya wanke mata fuska

Allah ka tsinewa azzalumi Khalid abinda take cewa cikin zuciyarta kenan, mashayi macuci abin ma ya koma har kan wanda yazo taimakonta.

daɗa girgiza Khulaid take amma ina ai rai ya jima da yin halinsa, kifawa kansa tayi tana kuka mai cin rai sose, fizgarta Sultana Yasmeen tayi sukai waje, ambulance ɗin da aka sanya gawar Khulaid suka shiga akaja.

sai da suka isko tsakiyar wani daji wanda babu mutane sai kukan tsuntsaye sannan suka dakata, su kansu jejin badan sun sakawa ransu mugunta ba bazasu iya shigansa ba.

Rahinat ɗaya suka bari cikin mota su kuma suka fito da gawar babu ko tsoron Allah, tsayawa sukai kan gawar suna tinanin yanda zasuyi da ita, zasu binneshi ne ko kuma su jefar dashi haka kawai wanda Allah ya kawo ya ɗaukesa.

kowa na kawo shawararsa Sultana Yasmeen tace, ” mai zai hana kawai itama waccen munafukar yarinyar suyi mata haka, su danneta har lokacin da numfashinta zai ɗauke ta hakane koda anyi bincike baza a ganosu ba.”

Sultan Baheer yace, ” aishi lamarin yarinyar ɗaure masa kai yake, har yau sun kasa aiwatar da komi akanta, duk yanda suka so sai wani abin yazo ya hana”

tsoki Sultan Dameer yaja ya zaro wuƙar dake jikinsa yace su fito da ita kawai ya aikata da ita lahira, danshi akan dai ya rasa wannan sarautar daya ƙwallafa rai tsawon shekaru masu yawa to komine zai iya aikatawa sai dai in baya numfashi sarautar gaba ta ɗansa Raihan ce kawai bata kowa ba

ayanzu haka jira yake kawai wannan asirin nasu ya rufu yaje ya aika da Mourad da ɗansa.

“exactly wat we will do” abinda Sultan Abid yace kenan sukai ambulance ɗin dan ɗauko Raihanat.

ita kuwa dama tin fitowarsu dataga sunyi nesa da ita sose ta fita da gudu, bata tsaya ba sai datayi tafiya mai nisa tukunna ta kunce ɗaurewar hannun da suka mata.

kasa tsayawa hakin tai ta ɗora daga inda ta tsaya sai taka ƙayoyi take da kwalabe ƙafafunta sai zubda jini suke.

tana cikin wanan gudu har Allah yasa ta iso ga titi, ƙarfinta da juriyarta tuni suka ƙare, baya ta waiga da gefenta babu kowa babu komi sai tsirarrun motocin dake wucewa.durƙusawa tai tana haki kamin ta miƙe kuma, zata tsallaka titi k’itttttt kake ji mota tayi awon gaba da ita Allah ya rufa asiri bata kife a ƙasa ba ta kifa kan motar. +

da sauri ya taka burki yana hailala ya fito a motar, ƙirjinsa na bugawa yay kanta da sauri ya ɗauketa daga jikin motar zuwa ƙasa.

tashin hankali ƙarara atare dashi domin gani yake ya kashe rai, mai yasa hakan ke yawon faruwa dashi a duk sanda yake driving anya kuwa bazai aje driving ba, sau goma in zai fita sai yay accident aciki kuwa in bai kaɗe ba to zai kusa kaɗewa

ganin wadda ya buge ruɗu da sabon tashin hanƙali suka dirar masa, dama tin barowarsu nigeria banda tunaninta babu abinda yake yi tare da roƙon Allah ya sake haɗashi da ita dan gani yake babu ita babu rayuwarsa.

a gigice ya ɗauketa har matar shi na masa magana amma bai ma san tana yi ba, ganin haka yasata fitowa daga cikin motar don ganewa idon ta, ƙarasa ɗaukan Rahinat yayi ya sakata cikin mota.

tsaye nan ya bar Asma’u da ‘yarta bakin hanya yaja motar a wani sukwane hankalinsa duk bai jikinsa, tuƙin yake yana duban bayansa daya kwantar da Rahinat cikin jini.

Asma’u Kama k’ugunta tayi tana mai jin haushin hakan tare da bin motar da ido har ta b’ace ma ganinta.

Asibitin Alkhalil ya wuce direct, yana zuwa ya mik’ata emergency, likitan daya amsa Raihana yanzun ma shine ya amsa Rahinat, tsoro abin ya bama likitan har jikinsa na karkarwa, kardai ace aljanu aka kawo masu hospital, ya kasa tab’a Rahinat saboda ɗumbin al’ajabi fal k’unshe kan fuskar shi, yanzu fa ya baro ɗakin waccen kuma tanan zaune har mijinta na bata labari amma kuma yazo nan ya kuma tadda wata, tsawar da Raihan ya doka mashi ita hargitsa mashi ‘ya’yan hanjinsa take ya had’iye wani miyau mai kauri babu shiri ya hau aikinsa.

Shikam Raihan bai samu sukuni ba sai daga bisani daya ga an gyara mata ciwukan jikinta an mata allurar bacci sannan likita ya bashi tabbacin da babu wata matsala sanan ya sauke ajiyar zuciya tare da lumshe ido yana mai godiya da Allah.

nan kuma ya shiga goge zufar dake jikinsa ya matsa kusa da fuskar Rahinat ya mata kiss a goshi yana murmushi, dai dai saitin kunnenta ya rad’a mata a kunne I love u my Sweetheart dama nasan zan sake haɗuwa dake domin ke ɗin mallakina ce…

Ya jima yana kallon kyakyakyar fuskarta can kuma ya tuna da matarshi da ƴarsa, da sauri ya mik’e ya fice daga room d’in bayan daya jaddawa likita da nurses su kular masa da ita yanzun zai dawo.

yana fitowa yazo dai² ƙofan fitowa sukai karo da Khalid har ya kusa zubewa ƙasa.
gaba Khalid yay abinsa dan baima san yayi ba bare yace masa sorry.

ran Raihan ɓace ya ɗago zai bishi ya cakumesa Nimrah ta bashi haƙuri kan cewa dan Allah yay masa uzuri yana cikin matsala ne matarsa ke kwance a asibitin.

bawai dan halin da Khalid ke ciki ba Raihan ya ƙyaleshi sbd ya gane kowane kawai dan dai shima data shi matsalan ne so yake yaje ya ɗauko su Asma’u ya dawo wurin Rahinat, gani yake matsawar wani abu ya taɓata bazai iya yafema kansa ba.

ya taka zqi ƙarasa motarsa sai yaga Asma’u tsaye a wurin.
da mamaki yake cewa, “taya kuka zo nan?”

“mota na hau nace yabiyo bayanka, to kuma da muka shigo banga inda kai ba, na dudduba ban sameka ba nace to bari mu jiraka anan”

“gud hakan da kikai yayi, yanzu amsa wannan key ɗin kijaku zuwa masrauta ai kin gane a map da muka duba ko””to handsome kaifa?
“karkiji komi so nake nai warware wannan matsalan yanzu haka jami’an tsaro na kaina, buƙatata ayanzu bai wuce in ganni cikin gidan da aka haifeni ba, ku tafi idan kinje sunan mahaifina DAMEER”

“to” abinda tace masa tare da amsar key ɗin, bayan ta shiga ta kira sunansa tace ya kula da kansa yace mata i promise u beauty.

nan taja motar suka fita shi kuma ya koma da sauri zuwa ciki, yana isa ya tadda likitan ya fito daga room ɗin yanayinsa ya nuna alamar akwai matsala.

tambayarsa yay yace mai ya faru yace dashi gaskia sai an sanya mata jini zamu sami abinda muke so in kuwa ba haka ba tabbas zata rasa ranta domin tana cikin halin da bashi da kyau.•••••••kai tsaye lab suka wuce, da zuwansu aka gwada jinin Raihan nan aka tabbatar masa da cewan baizai yiwu a sanya mata nasa ba.
+

shi kam duk ya gigice ya shiga tashin hankali ,baya son rasata ayanzu dan jinta yake ta riga ta gama zama ƙashi da tsokar jikinsa..

fitowa yay daga cikin lab ɗin ya tsaya bakin ƙofa ya kifa kansa jikin bango yana tinanin abinyi, duk maganganun da suka faru a kunnen Nimrah suka sauka wadda ke tsaye itama a lab ɗin domin abinda take karanta kenann tazo ta daɗa samun experience

cike da tausayawa take kallonsa, fita tayi a lab ɗin ta wuce zuwa room en Raihana…

da shigarta ta tarar Khalid na bata abinci ita kuma tanaci tana dariya.
daga bakin ƙofa ta tsaya tana kallonsu dan ba ƙaramin burgeta sukai ba, duk cikinsu babu wanda yasan da shigowan Nimrah saida Raihana ta ɗago ta ganta tsaye.

murmushi suka sakarma juna ita da Nimrah, abincin ya kuma ɗebowa yakai bakinta ta kauda fuska, ya kuma miƙa mata ta kauda, dakatawa yay yana dubanta inda yay mata magana da ido.

kaɗa masa kai tayi tare da nuna masa cikinta alamun ta ƙoshi, ya girgiza kai alamun bai yarda ba.

shagwaɓe fuska tayi tare da rausayar da kai tana yamutsa fuska.

tin dawowar Khalid Libya ya koma asalin Aayan ɗinsa, magana wuyar yi masa take sam baya sha’awar yaga ma ya buɗa bakinsa da sunan yinta bare kuma dariya ko murmushi.

motsa fuskarsa yay ya kama kumatunta kamin ya matsar da fuskarsa zuwa ga tata ya haɗe, laɓɓanta kawai yake bi da kallo, ɗan karkatar dakai yayi da son kai nasa laɓɓan su haɗe tare da nata

doguwar ajiyar zuciya Raihana ta sauke tare da saurin runtse idonta, dakatawa yay ya ɗago yana duban kyakykyawar fuskarta dake fitar da gajeran murmushi.

bisa ga kafaɗarta ya ɗora haɓarsa, ta saitin kunnenta yace, “ina sonsu”

_in dai laɓɓana ne ka gama samunsu Yarima, domin yanzu ni mallakinka ce kai kuma nawa ne, lalle burina ya cika domin na rabaka da ƴar uwata , sannan ko anan gaba zan rabaka da duk wata mace dazata raɓeka, kai ɗin nawa ne ni ɗaya,I love you Yarima nah_.

zancen zuci tayi amma sai kalman ƙarshe ya fito fili.

daɗi yaji da abinda tace sannan shima yace”baki tambayi mi nake so ba?”

“hmm to mi kake so Yarima nah”?

“tsoro da tsantsar kunyar dake bayyana a fuskanki idan an kalla kamin kuma akai ga ganin na cikin idanunki…miyasa kika barsu suka kau bayan ina sonsu”

juya idanu ta fara, gayenn fa na gab da ɓaro jirginta, karya tarwatsa mata plan B ɗinta, kash ta ya za’ai taga Khulaid yanzu, gashi sai kiran wayarsa take bata tafiya.

“why u kepp silent umm”?

shiru tai bata amsasa ba dan a duniyar tinani take, kenan twns ɗinta matsoraciya ce kuma tana da kunya, wannan shine kawai abinda ya banbanta su kenan,ya kamata tayi wani abu akai amma ta ina zata fara dan bata san mike ba twins tsoro ba…

tinanin nata ya katse da faɗin, “ni na sani, idan ke kin manta ni ban manta ba”

“umm to mine”
tayi maganar da yanayin jin kunya dan tana so ta fara sabon acting ɗinta a yanzu.

ya murmusa kamin yace,
“i wont tolerate it anymore Khaleed, zan ƙwaci ƴanci na,bana son igiyoyin dake kanka ka sawwaƙe mani”,

“kin tina wannan kalman, daga wannan lokacin d kikai wannan furucin tsoronki ya kau daga gareni, to amma kuma ita ƴar kunya ta ina tabi ta gudu?”

amsarta yake sonji amma sai tai shiru ta kuma kwantar da kanta a bayansa.

gaskia ba ƙaramin dabara tayi ba data maye gurbin ƴar’uwar tata, matsuwarta ɗaya yanzu su bar ƙasar kaman yanda tace masa ya kuma amince, ɗaya ɓangare na zuciyarta kuma na tinatar da ita girman kuskuren datake shirin aikatawa.

zai kuma magana Nimrah ta katseshi da kiran sunansa dan taga alaman wannan soyayyan bamai ƙarewa bane ƙwamma tayi abinda ya kawota kar lokaci ya ƙure.Khoyaa” +

sakin Raihana yay ya juyo yana kallon Nimrah dake tsaye, da ido yay mata maganan “lapia?”

gabansa tazo ta tsuguna ta kamo hannunsa.

“Khoyaa dan Allah taimakon daka saba zakayi”

tasan ba magana zai ba shiyasa ta ɗora da maganarta.

“dan Allah Khoyaa, jini ake biɗa kuma idan aka ɗauki lokaci shi ɗin zai iya rasa matarsa ka taimaka masa”

“are you mad,taya zan bada jinina a yanzu”

“Khoyaa likita fa yace duk da abinda kake sha Allah baisa jininka ya gurɓace ba, cikin ikon Allah ma sai ƙara lapia da jininka yake…plss ka taimaka masa karta mutu”

jin an ambaci mutuwa ya ɗaga ido ya kalla Raihana data tsaresa da ido tsoro fal idonta, yanda baya son rasa tasa matar haka bazai so yaga wani ya rasa tashi ba. idan har yana da halin taimakawa to zai taimaka masa

da sauri Raihana ta girgiza masa kai alaman a’a ita bata so karya je.

ya kama hannayenta gami da tallaɓar haɓarta.

“ki kwantar da hankaliki ba abinda zai sameni kinji, i will be back right now take care”

da ido ta bisa ya miƙe shida Nimrah suka fita.

koda suka ƙarasa ƙaramar fafatawa akai da Raihan daya ce shifa baza a ƙarama matarsa jinin mutumin da bai san darajar ɗan adam ba da ƙimarsa.

juyawa Khalieed yay zai wuce Nimrah ta riƙosa da sauri, “no Khoyaa karka biye ta maganarsa kayi dan Allah ka ceci rai… kayi dan iyayenta badan shi ba”

likita ma yace, “kayi haƙuri yallaɓai taimako ne zakayi, kaga jininka shine exactly wanda ake nema dan iri ɗaya ne da nata”

Khaleed ya ɗago ya kalla Raihan tare da masa kallon banza sannan ya wuce Nimrah da likita suka bi bayansa

ana gama ɗiban jinin nasa ko hutu bai tsaya ba ya miƙe ya fita, bai wuce room ɗin Raihana ba ya fita dan sayo mata popcorn, in bai manta ba ita ma’abociyarsa ce tin a tym ɗin daya ganta a india, dan tana wasa tana cinsa cikin wani madaidaicin bowl. haka time enma data zo wurin Mami tasa shi gaba tanata ci har taƙi cin abinci ma.

daya dawo zai shiga ɗakin wayansa yay ƙara, kiran inspecter ne , picking yayi yace dashi he will call back leta.

in a worried mood ya sami Raihana zaune daga gefen gadon, kamin ya ƙarasa ta taso da sauri ta shige cikinsa tana jan kuka a hankali.

yana shafa bayanta ya kama hannunta sukai gadon ya zaunar da ita,kallon fuskarsa take wadda take ganin kaman da damuwa a tare da ita.

zatayi magana y sanya yatsansa a lips nasa yace, “shhhhh”

small container en popcorn ɗin ya buɗa murfin, ɗiba yay ya kai mata bakinta ta saurin ɗauke kai, inda abinda ta tsana a duniya ya biyo bayansa sam bata sonsa.mamaki abin ya bashi ,duk da bai wani sani sose ba amma yasan ita ɗin mai ƙaunar porpcorn ce. +

Nimrah kanta abin ya bata mamaki tace, “sister inlaw yau kuma Popcorn ɗin kike gudu, tab kice kowa ma zai daina cin abinda yake so”

_kenan wannan ma abinda twns ke sone._
tai zancen a zuci.

“a’a kawai yaune ban son cinsa saboda bakina ba daɗi”

wayarsa ce ta kuma ruri nan ya miƙe ya cire hannunsa daga bowl ɗin ya fita bayan yay ma Nimra nuni data sanyata taci kamin ya dawo.

Nimrah ta ƙaraso kusa da ita tana smiling tace, “sister inlaw da wani abin ya taɓa shiga tsakaninku da Khoyaa to da sai nace ciki gareki”

kauda mamakiyos ɗin dake neman kamata tayi tace, “kinji ko”

ƴar dariya sukai tare, Raihana tace ta tashi su fita ta ɗan taka ta gaji da zama da kwanciya kuma inta biye ta Prince haka zai barta.

kamata tayi suka fita tare suna zaga asibitin, cikin zuciyar Raihana kuwa neman ta yanda zata sarfe take ta nemi waya ta kira Khulaid dan baki ɗaya hankalinta yayi kansa gashi gabanta na tsananta faɗuwa .

ita komi zai faruma ya faru da twins ɗinta amma bada Khulaid ba saboda ya taimaka mata a rayuwa.

ba danshi ba bazata taɓa iya ɗauke Rahinat daga gidan Khaleed ba.
kasadar da yayi alokacin ta tina har ta ɗan saki dariya kaɗan.

lokacin da suka isa ƙofan gidan suka rasa ta yanda zasu shiga, plier ya ɗauko ya datse security wayar dake kewaye da jikin gidan.

ya kama katangar shock ya makoshi ƙasa sai gashi yana rawa a kwance,duk data tausaya masa amma sai datayi ƴar dariya.

shi kuma ganin hakan dan kar tace masa rago ya miƙe yana wani bouncing amma shi ɗaya yasan miyaji a shock ɗinn.

saboda cikakken hatsabibi ne shi haka yaje ya kuma kama pole ya gimtse wutar layin baki ɗaya.

Nimrah ta katse tinaninta da cewan, “sister inlaw yadai? naga kaman mood enki ya sauya”

ta kakalo murmushi tace, “Nimrah wayanki zaki ara mani plss”

Nimrah tace, “haba sister inlaw ba yanzu ya kamata ki kirasu Abbiyy ba ki bari tukunna har lokacin da Khoyaa yace”

“bazanyi magana ba kawai dai zanji muryan Abbiyy ne”

tace da ita to tare da miƙa mata wayan,nan tayi dialling numban Khulaid taita kira ana cewa swrchoff.

ba ƙaramin damuwa ta shiga ba da jin haka.jingina tayi da bango kaman zatayi kuka, idan har wani abu ya sami Khulaid bazata yafema kanta ba.

_I love much more Raihana,zanyi abinda yafi haka indai zaki sami farinciki._ido ta runtse lokacin data gama tinanin maganarsa,a hankali ta furta Allah yasa kana cikin ƙoshin lafiya hubbi nah. +

Nimrah ta dafata tace, “bai ɗaga bane sister inlaw”?

ta goge ɗan guntun hawayen daya tarar mata tace, “inaga ya gane nice shi yasa ya kashe wayansa”

nan Nimrah ta hau lallashinta tana bata haƙuri.

****
a hanakli Rahinat dake kwance ta shiga buɗa idanunta masu nauyi.

jin jikinta tayi ya ƙara ƙarfi da kuzari kaman ba ita ke a wahale ba, ledan jinin tabi da ido tana kallo haɗe da ledan ruwan drip ɗin.

cikin zuciyanta tace na gode maka likita daka taimaka mani, dama tinda naji jikina kaman zan mutu nasan waɗannan abubuwan nike da buƙata duk dana na kusa tafiya.

nurse ta shigo, sannu ta mata ta zare mata drip ɗin daya ƙare a yanzu sannan tace mata mijinta yaje yanzu zai dawo.

bata rufe bakinta ba saiga Raihan ya shigo.

sannu yay ma nurse ɗin ta amsa masa sannan ta fita shi kuma ya tsaya bakin gadon yana ma Rahinat sannu.

da ido take kallonsa domin babu bakin magana,shi kuma wannan fa ko daga ina.

ganin tana masa kallon alamun ayar tambaya yace da ita, “amm kin sami accident ne shine na kawoki asibiti”

miƙewa zaune tayi ta masa alamun daya taimaka mata da biro da takarda,miƙo mata yay ta rubuta masa,

“na gode da taimakon da kayi mani Allah ya biyaka, sai dai ka nisanceni saboda kasancewarka tare dani akwai haɗari,kamin kai wanine ya taimaka mani dalilin haka suka kasheshi, dan haka kaima ina roƙonka ka bar inda nake dan bana so na kuma zama silar rasa wani ran”

mugun tausayinta yaji ya kamashi daya gama karantawa, ashe cikin tsaka mai wuya take shiyasa koda yaushe take a firgice.

dan karya barta cikin damuwa kaman yanda yaga fuskarta ya nƴna ya naɗe takardan ya jefa a aljihu.

bakin gadon ya matso ya zauna ya miƙa hannu zai taimaka mata ta sakko ta dakatar dashi.

dubanta yake, hakan yasata ɗan sakin murmushi, ƙasa tayi da kanta tana tinanin ta yanda zata masa bayani.

yanzu ya tabbatar da tinaninsa akanta na cewan bata magana, biron ya kuma miƙo mata da takarda ta amsa.

_am married_.
abinda ta rubuta ta miƙa masa kenan.

bohot-bohot zuciyarsa ta shiga lugude jikinsa har na ɓari, ƙalu innalillahi ya shiga karnatawo a zuciyarsa ,kenan da matar wani ya faɗa soyayya.l, kai da sake, hakan bazai taɓa yiwuwa ba ta faɗi ne kawai dan ya ƙyaleta.

sakkowan ƙafafunta ƙasa ya sanyasa ɗagowa gami da goge zufan daya tara.
tsaye tayi tana dube-dube, kaman yasan mi take tinani ya tashi ya ɗauko ledan daya shigo dashi yanzun ya bata.

buɗawa tayi ta ɗauko hijab ɗin dake ciki ta ware ta sanya..sose take jin ƙwarin jikinta ba kaman kwanakin da suka shuɗe ba sai dai gabanta dataji yana faɗuwa wanda bata san dalili ba amma ta alaƙanta hakan da mutuwarta dake kusantota.

“ina zakije? da kin zauna kin daɗa hutawa”

girgiza masa kai tayi ta wuce ta barsa tsaye yana sose kansa daga bisani shima yabi bayanta.

dakatawa tayi da tafiyan ta juyo tana kallonsa, da hannunta ta shiga masa nunin lalle idan harya ci gaba da binta to zai rasa ransa kaman yanda wancan bawan Allahn da yay yunƙurin taimaka mata ya rasa nashi.goge hawayenta tayi taci gaba da tafiya, taƙamaimai batasan inda take ba tsawon wannan lokaci, shin har sai yaushene zata bar wannan rayuwar ƙuncin da ƘADDARAR SO ta jefata RASHIN BIN UMARNIN IYAYE yaja mata. +

haƙiƙa bazata taɓa yafewa Khalid ba har abada, tasan bata da iko ko hanyar hukuntashi amma zata barsa da Allah maɗaukakin sarki ya saka mata dukkan zaluncin da yay mata akan laifin da bataji ba bata gani ba.

a iyaka rayuwa ta tsani Khalid, tayi dana sanin faɗawa sonsa da tai, tayi nadamar bijirema maganarsu Ammi.
wani kukan ya kuma ƙwatarta, ko a wanna hali yanzu Hajianta take, shikennan ya bar kowa nata cikin jimami da tashin hankali.

ƙasa ta durƙushe tana kuka mai sosa zuciyar mai saurarensa, cike da tausayawa Raihan ya duƙa ƙasa da ita ya miƙa zai kama hannunta tai saurin janyewa tana kaɗa masa kai.

ɗaga kan da zatayi dan maida sauran ƙwallar idonta sai taga picture ɗin Abie kafe a wurin, tana gani ta firgita lokaci d’aya ta ruɗe.

_Khaleed_.
sunan data fadi cikin ranta kenan.

tuni fa faɗa cikin tunani yaushe ne tsawon rabuwarsu dashi da har ya sake girma haka harya tara furfura…

hannu Raihan ya sanya ya kaɗe idonta tuni ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi.

ya tambayeta, “tinanin mi kike?”

girgiza masa kai kawai tai ta yunƙura ta miƙe, da hannu ta masa godia ta tafi.
yabi bayanta da tausayawa, turus taja ta tsaya lokacin data ƙaraso reciption, kallon kallo suka shiga ita da Raihana, ita a firgice Raihana a tsure.

tsoro,mamaki tare da ɗumbin al’ajabi suka kama Khalid shida Raihan da isowarsu kusan tare wurin kenan, Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un shine abinda Khalid ya faɗi a zuciyarsa inda Raihan kuma ya faɗi a fili.

_photocopy of me_.
zuciyar Rahinat ta faɗi, hannunta na karkarwa ta shiga nunata da tsantsar mamaki.

takawa tayi zata je wurin kawai taga Khalid a wurin.ganinsa ba ƙaramin firgita tayi ba da sauri ta koma bayan Raihan ta maƙalƙaleshi dan ita tsoron Khalid take gaba ɗaya.

_bata mutu ba kenan?to ina Khulaid ɗin? wane kuma wannan suke tare dashi?”_

tambayoyin da zuciyar Raihana keyi kenan amma bata da amsarsu bata kuma da mai bata su.

ita kuwa Nimrah suman tsaye tayi dan ta tsorata sose, in ba’a film ba bata taɓa ganin irin haka ba, wannan kaman tayi yawa harta ɓaci.

ƙafafunsu tabi da kallo dan taga wace aljana acikinsu.
shikam Aayan yama rasa ta cewa ko matsawa ya kasa saboda ɗimbin al’ajabi.

ya rasa wanna irin tinani zaiyi, inma zaiyi ta ina zai fara…vedio evidemce ɗinsa ya tina, rufe ido yay yana kallon lokacin daya wulla Rahinat ɗakin ajiyarsa.

yatsu yasa yana murza idonsa, ganin ya tafi wannan tinanin Raihana ta tabbatar da zai shiga zargi ya kamata tai wani abu.

da sauri ta ɓoye bayansa ta cikwikwiyesa hakan ya sanyasa buɗe ido, shikam Raihan ya zaton sufar da Rahinat ta gani shi ya tsoratata daga baya kuma sai ya gane ba haka bane mutumin dake tare da waccen take tsoro.

topa zuciyar maza ta harzuƙa, hannun Rahinat ya damƙa ya fito da ita daga bayansa yana huci ya nufa wurin Khalid da ita.

yana zuwa ya bugi ƙirjin Khalid, ido Khalid ya buɗa ya ɗaga masa gira alaman ya akai?

“wane kai?”

hannu yasa ya ɗauke hannun Raihan daga jikinsa, al’amarin ya gama ɗaure masa kai.

karkatawa yay ya kalla Rahinat ya kalla Raihana waɗanda duk suke a tsorace cikin firgici da tashin hankali.

cikin ƙanƙanen lokaci computar kansa ta gama warware masa lissafi, ya tabbata waccen yarinyar biyu ce kenan, ta asali kuma itace baiwar ta ƙarya kuma matarsa da aka liƙa masa. to wacece Angel aciki?

ta tsoro da kunya kawai zai gane hakan dan ƙaryar mutum yace zai tantancesu ta sufar jikinsu.

su biyun ya haɗewa hannye yana kallonsu yana son tantance abinda yake amma saboda Raihana ta gama sanin komi taƙi barin haka, duk abinda Rahinat tayi sai tayi shi babu banbanci.

salatin da jama’ar asibitin suka fara ya maida dukkanin hankalinsu ga TVn da suke kalla.

tare suka fizge hannayensu daga hannun Khalid sukai bakin TV ɗin idon kowacce a waje ganin ana nuna gawar Khulaid da aka tsinta an masa kisan gilla wanda ba’a san kosu wane bane.

wata ƙara Raihana ta saki ta zube ƙasa tana kuka, itama Raihinat duk da mutuwar ba sabuwa bace agareta amma yanda taga gawar tashi ta zama sai ta kuma shiga tashin hankali ta zube ƙasa itama tana kuka.

_tinda har ya rasa ransa ata dalilinki to tabbas kema saikin baƙunci inda ya baƙunta, na tsaneki Rahinat na tsaneki bana sonki, duk dake ƴar uwatace amma banda wata maƙiya sama dake, na rasa farincikin mahaifa saboda ke yanzuma na rasa masoyi saboda ke, to kuwa bazan taɓa barinki ba saina kasheki kema jin daɗin rayuwarki ya ƙare, kuma bazan taɓa barin Yarima ya gano gaskiar lamarin tsakaninmu ba ni zanci gaba da rayuwa dashi a matsayin daya ke ɗaukata yanzu._

Raihana ke wannan maganar cikin zuciyarta inda ta ɗago a fusace tai kukan kura ta danƙo wuyan Rahinat, itama a ƙufulan take dan so take taji wace ita da take kwaikwayonta har ta jefa rayuwata a haɗari, dan haka itama ta bata wata maƙura a wuya nan suka shaƙi juna.

🤣🤣🤣wayyo abin dariya abin tsoro tinda suka haɗe an rasa gane wace tazo daga wurin Raihan da wadda tazo daga wurin Khalid gashi kowa ya kasa zuwa wurinsu sai Khalid dake tsaye zuciyarsa na tafarfasa.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]