[Advertisements⬇️]

YAREEMAH KHALEED CHAPTER 6 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

YAREEMA KHALEEDCHAPTER 6

da zallar ɓacin ran kalamanta Abibi ya nufi inda take, yana zuwa ya tsinketa da marin da saida taga hasken wuta.

“ƙarya kikeyi munfuka, wallahi baki isa kin ɓata mana suna ba domin kuwa muɗin mutanen arziƙi ne kuma kowa ya shaida hakan, wace ke? nawa aka biyaki?, to bari kisan abinda baki sani ba daga ke har jahilan mutanen da suka aiko ki domin kici zarafinmu kunyi kaɗan” ,

“nida Sa’adatu ba irin shaiɗanun mutanen nan bane marasa imani masu butulcewa ni’imar ubangiji da zai ɗauki kyauta mai girma ya bamu mu wulaƙantata ba, Ƴaƴa da kike ikirarin mun haifa tabbas wannan haka yake komi kin faɗi dai-dai sai zance ɗaya da kikai kuskure akai, bamu saida ƴarmu ba, Allah’n daya bamu shiya amsa abarsa, bawai dan baya sonmu da ita ba sai dan yafimu sonta, da hannuna na ɗau gawar RAIHANA na kaita maƙabarta, amma ni ban saida ƴata ba saboda wani abin dubiya, kuɗin dana fi ƙarfinsu tin kamin zuwan RAHINAT da RAIHANA duniya”


ta ɗago idanunta suna masu zubda hawaye tace, “to Abbi ni kuma wace? mine matsayina a wurinku? miye asalina? dan Allah ka fitar dani daga ruɗani domin kuwa a yanzu inada buƙatar jin ɗumin iyayena, ina son na sami kusancinsu koda babu soyayyarsu kamin na koma ga Allah”


Abii yace, “mu bamu sanki ba, hasalima bamu da wata masaniya akanki, wala’Allah su macutan da suka sauya maki kamanni zuwa irin siffar ƴarmu suke son yin amfani dake ta wata hanyar, yanzu gashi suna neman saki a wuya, domin kuwa ni Abdullahi bazan ƙyaleki ba kuma bazan yafe maki ba har sai na ɗaukarma ƴata fansar wuyar da kika jefata aciki….”


ta katsesa da faɗin, “to Abii idan kuma nice Rahinatu fa?”


wani irin juyowa yayi da jin zancen nata, ya daɗe yana ƙare mata kamin ya koma kan Rahinat ma ya ƙare mata kallo,wani tsoro yaji ya ziyarce shi, karfa aljanu su buɗe masu ido.

ta kuma katse tinaninsa, “Abii baka tinanin nice salahar Rahinat ɗinka waccen kuma ƴar basaja….”

itama bata kai aya ba Khaleed ya nunata da yatsa yace,

“ƙarya take Abii, ba itace Rahinat ba, ga Rahinat kusa dani…kamar yanda na gaya maki ni ba mutum ne mai son a ɓatawa lokaci ba, dan haka karki kuskura gaskiya ta fito daga bakin waɗanda nike tsare dasu domin bazaki ji da daɗi ba…..”

shima maganarsa ce ta tsaya lokacin da Mami ta jefo masa tambaya.

” kai taya kake da tabbacin cewar wannan ce Rahinat Aayan?”

STORY CONTINUES BELOW

ɗan saukar numfashi yayi ya miƙa hannunsa zai kamo hannun Rahinat tai saurin janyewa tana jifansa da harara.

kuma miƙawa yay zai kamota ta sake janyewa, gira ɗaya ya ɗaga yana kallonta, Allah sarki magana ce fal a bakinta take son fitar da ita amma ta kasa, yanda yake kallonta ɗin yasanya ta tsuke fuska ta kauda kai gefe.


_My Angel, kina son kice min zamu buga dramer dake bayan war-warewar wannan al’amarin kenan._

yay zancen cikin zuciyarsa yana mai murmushin saman leɓe

kowa Khaleed yake jira ya nuna evidence nasa na cewan Rahinat itace real one, dan haka kowa ya kafa masa ido yana kallonsa.

Raihan ko cike da ƙosawa da rainin hankalin daya ke ganin Khaleed zaiyi yace,

“shima munafikin karku yarda dashi domin ko ƙarya…..”

sai kuma yay shiru tinawa da cewan fa da Rahinat ai bata magana, ita kuma wannan gata harda zayyano bayanai.

Ammi tace, “Allah ya taimaki sarki ƙarasa faɗin abinda zaka faɗa dan Allah, kai ɗaya nake da tabbacin kasan ƴata a wurin nan, ba don kaiba ma bazamu san inda take ba”


“ehhh Ammi hakane, Rahinat bata magana”

“a’a ƴata ni tana magana, bata taɓa kamuwa da ciwon rashin magana ba…. dan haka indai har wannan ta hannun mugun sirikin nawa itace bata magana to tabbas itace ƴar basaja, wannan kuma itace Rahinatu nah

ta ƙarasa maganar tana mai tafiya ta rungume Raihana tsam ajikinta.


Abii ma ya sauke ajiyar zuciyar kamin yace, “ƙwarai kuwa zancenki haka shike Sa’adatu, ƴarmu tana magana so ba wani rainin hanƙali da za’a kawo mana na cewar bata magana”

Ammi cikin kuka take cewar, “Allah ya isa tsakanina da duk wanda yay silar shigarki wannan halin Rahinat, tinda kika faɗa ƘADDARAR SO kika haɗu da jarabta”
+

ta saki Raihana ta nufi inda Rahinat ke tsaye ta ɗaga hannu ta zabga mata mari,

“muguwa macuciya ,Allah ya isa cutar mana da yarinya da kikai kuma bazamu yafe maki ba sai munyi shari’a dake”

ta ƙarasa faɗi tana mai tankaɗa Rahinat baya ta faɗi a ƙasa.

tana zubda hawaye tayi saurin miƙewa ta kama Ammi, tana kuka tana kwatanta yanda kurame ke magana take ma Ammi bayanin, “wallahi nice Rahinat Ammi, karki yarda da waccen muguwar ,rashin maganata ma itace sila amma wallahi Ammi nice Rahinat”

kuma tankaɗata Ammi tayi ta faɗi ƙasa, “keni karki yaudaren da wannan zancen naku mai ban tausayi”

ta kuma miƙewa ta nufa Abii ta kama rigarsa tana ta masa bayanin bebaye amma shima saiya ƙara hankaɗata gefe.

kuka sose ta sake fashewa dashi tana tsugune, jinta take tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu ta huta da wannan sauyin rayuwa daya sameta,tinda ta haɗu da Khaleed zuciyarta ke cikin wuya har kawo iyau.

“ban san ta yanda zan masu bayani ba su yarda dani Rahinat, baki da wani abu da zan nuna masu su shaida kece ɗin tasu?”

taji maganar Raihan akanta, bata ɗago ta basa amsa ba kawai ta girgiza masa kai.

baki ɗaya ko su Uncle Badamasi dasu Suwaiba sunyi can kan Raihana, daɗi duk ya cikasu Abii har ya kira asibiti yace abama Hajiya ga Jikalle.


albishir ɗin kaɗai da aka mata ya farfaɗo da ita daga kwanciyar jinyar da take.

Maganar Waziri ce ta miƙar da Rahinat a razane tai wurin Khaleed.


“ai shiru mai martaba zai yanke hukunci”

hannu ta haɗa tana roƙon Khaleed ya taimaka mata, kafaɗa ya ɗaga mata ya kauda kai, hannu tasa ta juyo da fuskarsa tana murza hannayenta, cikin yanga ya kuma kauda kansa gefe.

ganin alamun shi wasa ma ya ɗauka abin ta dunƙule hannu ta dakeshi a ƙirji, sose yaji zafin dukan dan har saida ya shafa wurin.


kwai-kwayar yanda ta haɗe gira tai sama shima shima yayi, ganin hakan yasa ta kuma kai masa bugu a ƙirji d duka hannunta biyu.

“ashhhh dafa zafi”
ya faɗi yana mai kallonta, cikin kuka tasa tafukan hannunta ta turasa ta juya zata tafi ya janyo hannunta.

ƙoƙarin fizgewa take amma ya hanata.

“kina son su Abii su gasgata ke ɗin tasu ce?”

da sauri ta juyo tana ɗaga masa kai alaman ehh.

sautin muryarsa a ƙasa yace, “to karki kuma janye hannunki idan nazo kamaki, kuma kin yarda daga baya saina rama wannan dukan da kikai mani?”

fizgewa tayi zata tafi taji yace, “wallahi tallahi summa tallahi Abii idan har kuka kama zancen wadda kuke tare da ita to kun kama gaibu, ga real Rahinat nan amma wannan fek ce, idan har kuka tafi kuka bar Rahinat to baku mata adalci ba”

“zancen banza, babu wata magana da zan kuma yarda da ita ,yanzu haka ina jiran kotunku ta yanke mata hukunci ne kamin nima na haɗata da nawa hukumar su hukuntata a bisa basaja da tayi a matsayin ƴarmu harta sanyata cikin wuya


“rantsuwar da kai rantsuwa ce babba kuma rantsuwa mai haɗari, kasan hukuncin wanda yay ƙarya a bisa wannna rantsuwa, miye hujjarka akan hakan Khaleed?”

mai martaba ya jefo masa wannan tambayar, wani daɗi Khaleed yaji cikin ransa da kiran sunan da Mai martaba yay masa, domin kuwa yau shekara 7 kenan rabon dayaji sunansa a bakinsa.

“su matso data wurinsu kusa tukunna domin shaidar da zan nuna tana jikinta”

harsu Abii zasu musa mai martaba yace zai hukuntasu akan hakan tinda acikin kotun fadarsa suke dole subi umarninsa.

Ammi da Abii suka kamo hannun Raihana suka kawota tsakiyar fada, shima Khaleed kamo hannun Mami yayi dana Rahinat suka hauro zuwa tsakiya.

umarni ya bada da abashi kujera, cikin hanzari kuwa aka kawo lafiyayyiyar kujerar girma aka aje.

zaunar da Rahinat yay akai, da sauri ta yunƙura zata tashi yasa ƙafarsa ya danne tata, hannu tasa ta janye ƙafar da iya ƙarfinta, zata kuma yunƙurawa yay mata wani kallo daya bata tsoro, dan tana son kawai ya fittadata ne ta koma ta zauna amma bawai dan tana tsoron nasa ba.


fadawa yasa dasu miƙo masa Raihana,Ammi zata hana waziri yace mata “kul”

magana Khaleed ya fara, “Abii kaman yanda bayananta da naka suka fita tabbas haka komi yake, itama ƴarku ce amma ba ba asalin ƴarku Rahinatu ba, bayanin ta yanda gawa ta dawo mutum zatai maku daga baya domin ni yanzu burina na ceci rayuwar matata” ,
+

ƙasa ya zauna bisa carpet ɗin da aka shimfiɗa masa, “Abbi na faɗa son Rahinat batare dana son kowace ita ba, sannan na zauna da ita har na wahalar da ita cikin rashin sani duk batare dana san itace wadda zuciyata ke muradi ba, Abii wannan itace asalin ƴarku Rahinat zan kuma baku hujjar da zata gamsar daku hakan”

ya ɗaga ido ya dubi Rahinat data ƙura masa ido yace, “zo nan”

kaman bazata taso ba sai kuma ta taso ta taho, kusa dashi ya mata nuni data zauna, har zataƙi sai kuma tai saurin zama dan ita tana tsoron dogarai.

tana zama ya kama fuskarta tare da juyar da fuskar tata gefen hagu, wata tusar jaki ce a wurin mai ɗan girma yace dasu Abbi,

“Abbi ka duba ta wajenka ka gani, bayan baiwar tusar jakin da Allah yay masu ta gefen ido akwai wata a fuskarta?”

Abbi ya duba yace, “a’a bata da ita”

ya ɗago da fuskarta ya masu nuni da wata tusar jakin dake haɓarta domin maganar da yay harya gaji,


nan ma Abii ya duba yace, “a’a”

nan Khaleed ya ɗan kwanto da Raheenat jikinsa ko kunya ya kamo hannun damanta dake gefe.kai-kaicewa Rahinat keyi tana son janye jikinta amma sai wani ƙara kwantota jikinsa yake, yatsunta ya kamo yay ma Abii nuni dashi.

+

a cikin ƙasaitar maganarsa yake cewa, “ya matsayin wannan yatsan yake a wurin Angel?”

da rashin fahimta Abbii yace, “wace kuma Angel ko wane?”

yanda kasan ta ɓarar da Khaleed haka taji, ƙwacewa tai ajikinsa ta ɗago kunya duk ta gama cikata,Raihana kam ji take inama itace da ba abinda zai hanata sake lafewa jikinsa, gaskiya Rahinat tayi sa’ar miji, kuma matsawar ta rasa *SULTAN AYAN* wato mijin ƴar uwarta haƙiƙa zata iya rasa ranta.

Nimrah ce ta bama Abbi amsar , “Abbi yana nufin Rahinatu”

“auho” Abbii ya faɗi yana gallawa Khaleed harara, saboda duk gidansu Rahinat kowa haushinsa yake ji.

Abbii ya duba Raihana yace, “miƙon hannunki”

ƙin miƙa masa tayi har saida ya kama da kansa tukunna, ganin yatsan cindo a hannunta ya saketa ba shiri, hannun Rahinat ya koma kallo.

“inaa wannan aljana ce ba ƴarmu bace, domin kuwa cindon yatsan dake jikin ƴarmu tin tana shekara 7 aka mata aikinsa aka yankesa, dan haka Sa’adatu ta wurinsa itace Rahinat ɗinmu”

kamin ɗaya daga cikinsu ya kuma magana Raihana ta ɗauka.

“niba aljana bace Abbii mutum ce mara gata mara asali tinda ban san iyayena ba, haƙiƙa da ace nasan da wannan sheda da Sultan Khaleed zai nuna to itama dana bi hanyar da muka zama iri guda da Rahinat”

ta duba iyayen nata tace, “Ammi! Abbii! ku amsa laifinku ko karku amsa amma saida ƴarku kukayi ba mutuwa tayi ba…”

idan da lafazin dake ƙona ran Abbii ya biyo bayan wannan, yatsa ya ɗaga yana nunata ta kama ta sauke , kamin yay magana ta ɗora,

“Ammi! Abbi! ku yarda ko karku yarda nima ƴarku ce”

ta zira hannu cikin rigarta ta fito da hoto ta ɗaga ta nuna masu.

“wannan shine hoton da aka bani akace sune iyayena, kuna so shima kuce min yanda kuke da kokonto kanmu haka abin yake?”

hannun Abbii na rawa ya fizgi hoton yana kallo, mamakinsu duka ko a yanzu basu da ajiyar pix ɗin nan saboda tin na amarcinsu ne.

ta kuma ɗauko wani shima ta ɗaga, fizgarsa shima Abbii yayi yana kallo, hoton da sukayi a england ne suda yaran, lokacin tin Rahinat batai aure ba.
“dan Allah ki faɗa mana tsakani da Allah wace ke kuma aina kika sami waɗan nan hotuna?”

_”ni yarinya ce wadda ta taso agidan marayu batare da iyayen da suka haifeta ba, na taso cikin kulawa da ɗawainiyar wadda aka saidani a wurinta, ta bani ci ta bani sha ta kuma sanyani a makaranta harna girma na kai shekara 12 wanda alokacinne nasan ainihin wace ni” ,_

_”yanda naga wasu marayun suna samin ziyara daga ƴan’uwansu shiyasa na tambayi Mama wato uwar marayu wadda ke ɗawainiya damu, ina kuka nake roƙonta data taimaka nima asamo mani ɗan uwana koda mutum ɗaya ne na gansa tinda Mamana da Babana sun rasu, tana lallashina take shaida mani na kwantar da hankalina soon zanga jinina, ina murna na share hawayena naita mata godiya” _

_”faruwar haka da sati guda saiga wata dattijuwar mata ta kawo mani ziyara da kayan hidimarta masu yawa,naji daɗi matuƙa saboda tinda nake ban taɓa samun kaya irin wannan ba kai kace ma ba gidan marayu nake ba, da zata tafi kuwa ina kuka nace mata dan Allah ita ɗin wace a wurina? ta gyara tsayuwarta kamin ta sami wuri ta zauna ta fara faɗa min tarihi na, ta dafa kafaɗa cike da tausayawa tace dani” ,_Raihana, ni ba kowanki bace,ni da kike ganina sunana Hajiya Safna kuma agarin niger nike da zama, watarana kwatsam na kai ziyara asibitin gamkalley sai naci karo da wasu bayin Allah mata da miji sun sami arziƙin haihuwar ƴaƴa biyu duk mata, muka gaisa dasu na tayasu murna na wuce inda zani, to bayan na shiga ciki na gama abinda zanyi na fito saiga wannan matar tazo min da son in taimaka mata, nace mata mai take so tace dan Allah suna so su sayar da ƴarsu guda ɗaya ne, cikin ɗimbin mamaki nake kallonta da kuma haushi kamin na watsa mata tambayar dalili, nan mijinta yake cemin suna da kuɗi iya kuɗi sai dai bazasu iya rainon ƴaƴa biyu alokaci ɗaya ba dan haka suke son sayar da ɗaya cikinsu, ni kuma batare dana kuma bari maganar tasu taja ba na tambayesu babu matsala dama nima ina biɗar ƴa saboda Allah bai nufeni da haihuwa ba amma nawa zan basu na amshi ƴar, matar tace dani ko nawa ne suna so indai zasu rabu da ƴar saboda ita raino yana mata wuya, na rubuta masu check na naira million goma na miƙa ma mijin, da mamakina sai naji yace sunyi yawa saboda ƴarsu bata kai tsadar da zasu saidata haka ba, kai infact ma shi yafi ƙarfin wannan kuɗin dan haka kawai idan da kuɗi jikina na basu, na buɗe jaka na ɗauko dubu ɗari uku na basu, sai mahaifinki ya rage dubu ɗari yace sun barmi a dubu ɗari biyu, daga nan matar ta sakko mani dake daga bayanta ta miƙo mani mukai sallama dasu sunata farinciki. to dana koma gida ni kuma anan na tarar da ƙalubale daga wurin mijina na cewar bazan shayar dake ba saboda bai amince ba wanda ba ɗan cikinsa ba yasha nono na, naita bashi haƙuri amma fafur yaƙi haƙura, ni kuma alokacin tausayinki da ƙaunarki sun addabi zuciyata ina jin har saidai mu rabu dashi amma bazan iya barinki ahaka ba, ya kafa ya tsare bazan zauna masa agida ba na tashi na maidaki inda na amsoki, kinata tsala kuka abin tausayi na koma wannan asibiti, koda naje sai mukaci karo da iyayenki an basu sallama zasu wuce gida, nan nayi masu bayanin komai amma sukace su basu san wannan ba ƙarshema basu kuma saurarata ba suka shiga danƙareriyar motarsu suka tafi suka barni anan, to na rasa ya zanyi na rasa mafita kawai saina yanke shawaran kaiki wurin mahaifiyata dake a garin Jigawa, a daren wannan rana na kawowa mahaifiyata ke domin ta kula dake to amma itama sai muka sami matsala ta rashin ruwan nono da bata dashi, ƙarshe dai muka yanke magana akan kawai akaiki gidan marayu, washe gari da asuba na kaiki asibiti saboda kwana da kikai da zazzaɓi aka dubaki tare da baki magunguna sannan na kaiki gidan marayu na nan jigawa state, duk ƙarshen mako ina zuwa na ganki domin tabbatar da irin kulawar da ake baki har zuwa lokacin da kika fara girma ni kuma ayyauka suka mani yawa alokacin bani samun daman zuwa jigawa akai-akai shine na barwa Hajiya Saddiqa amanarki, to kinji labarinki Raihana”_
+

_”lokacin da Umma nah ta gama bani labarin kuka nake sose, tambayar da nayi mata shine waya raɗa min sunana? tace dani iyayena, su suka shaida mata an mani huɗuba da Raihana ƙanwata kuma Rahinatu, na kuma tambayarta dan Allah kota san sunan iyayena tace mani ehh Alhji Abdullahi Matawalle da Hajiya Sa’adatu, tambaya ta uku dana mata shine kozan iya samun hotonsu, take tasa hannu ga jakarta ta ɗebo mani hotuna biyun nan, anan na san inada wasu ƴan’uwan bayan Rahinatu, tin daga wannan lokaci kuma a wannan rana naji na tsani iyayena da kuma ƴar’uwata da aka haifemu tare, naji na tsani garin da aka haifani na kuma ji na tsani garin jigawa wanda ban san dalili ba…bayan tafiyar Umma nah da wata ɗaya nai satar kuɗi a jakar Mama na bada aka sayo min rago nzan sauya suna to kuma saina fasa, Umma Nah naima waya nake faɗa mata ni zan bar ƙasar nan baki ɗaya zan koma wata ƙasar na fara
sabuwar rayuwa, nan ta bani haƙuri har saida tazo gidan marayu, to anan mun taho hanyarmu ta niger sai muka tarar da wasu mutane masu sayan bayi suna kaiwa ƙasashe da garuruwa, anan Mama ta saidani muhallina ya sauka anan ƙasar Libya cikin masarauta, daga wannan rana na zama baiwa nake aikace-aikace sai daimi, tinda nazo zuciyata ta kamu da son mutumin da bai son hayaniya baison mutane sam, kyakykyawan namiji jinin larabawa, son samun duk wace mace datai tozali dashi, mai tsananin tausayi da kyautatawa, domin duk aikin da mukesha idan yazo zaice a barmu mu huta, wasa-wasa sai ƘADDARAR SO ta afakamin domin banda tabbacin zan sameshi tinda ni ɗaya nake kiɗi da rawata, mai gaba ɗaya ma dai bazan sameshi ba saboda babu gami auran SULTAN da kuma BAIWA, kwana atashi ciwon ƘADDARAR SO na SULTAN AYAN ta nemi taimin illa, uwar ɗakina SULTANA YASMEEN ita ta lura da irin wahalar ciwon da nake fama dashi saboda na koma baci babu sha, tasa likitan masarauta ya dubani nan ya bata tabbacin na kamu da ciwon zuciya tare da hawan jini sose, ban damu ba kuma hankalina ko kaɗan bai tashi ba saboda nasan dalilin ciwona kuma koda cutar data fisa zan kamu da ita” ,_
_”agaba uwar ɗakina tasani da tambayar kan dole sai na gaya mata meke damunwa har ya haifar manida waɗannan ciwon, gaskiyar magana ban ɓoye mata son Sultan Aayan daya kamani ba har ya haddasa min ciwon zuciya sai dai kuma ban gaya mata ciwon da iyayena suka haddasa mani na hawan jini ba, da taimakonta da taimakon magungunan da nake sha na fara samin lafiya amma kullum zuciyata da ruhina basa barin tinanin ɗan gatan masarautar Libya da kuma abinda iyayena suka mani, kowanne dare mafarkina da tinanina yana ƙarewa ne akan hanyar da zanbi na sami Sultan Khaleed kota halin ƙaƙa sannn kuma na ɗauka fansar zaluncin da iyayena suka mani, kwatsam ina zaune watarana na mun gama hidimar cikin gida ina ɗan hutawa saiga jakadiya tazo kirana inji Sultana Yasmeen, naje na sameta take shaida min ga maganin damuwata, zasu haɗa sharri wanda suke son na bada gudunmawata akai to tana mai tabbatar min da zan sami auran Khaleed, ina zare ido nake tambayarta abinda zna aiwatar, abinda tace mani shine basu so Sultan ya sami sarautar da Mai martaba yake son bashi a gobe, MAKIRCI shine abinda kawai zai dakatar da Mai martaba ya fasa aiwatar da abinda yaso, zaiji ya tsani Khaleed amma ke kuma zaki sami Khaleed a wannan lokacin, ina farin ciki ina murna nake tambayarta me zan aiwatar na sami auran Sultan duk kuwa acikin zumuɗi nike tambayar tata, abinda ta shaida mani shine zasu sanya abu cikin drink nashi ni kuma alokacin zan aiwatar da nawa aikin” ,_

ta numfasa kamin nan ta ɗago ta kalla Maimartaba da yay kasaƙe yana sauraron zantukanta, taci gaba da faɗin,

_”kaman yanda na shaida maku a baya abinda ya faru tsakanina da Sultan Sharri ne, ehh tabbas haka yake sharri ne domin kuwa babu wani abu daya faru, kawai dai sun sanya masa abinda zai kawar da tinaninsa ne tare da tada sha’awa, sam abinda kukaga yana aikatawa bai cikin hayyacinsa kaman yanda duk nayi maku bayani a baya, wallahi tallahi dana san abinda zan aikata bazai sa na sami Sultan Khaleed ba to da ban aikata ba, da banyi abinda zaisa a nisanta idanuwana daga ganinsa ba saboda ina tsananin sonsa, hankalina bai kuma tashi ba sai bayan tsawon shekaru da aka ɗauka baya tare damu najin labarin auransa, ko alokacin ciwon zuciyata sai daya tashi,Sultana Yasmeen ita tayi ɗawainiyar maganina saboda a lokacin lallamani take gudun karna tona mata asiri, na kasa jurewa har saida na samo hoton bikin Sultan da matar daya aura, daga lokacin dana ga fuskar mai kama dani a wannan lokacin na ɗaura ɗamarar ɗaukar fansa mai tsauri, bayan tsanar da naima 2wins ɗina gashi yanzu tazo ta aure farinciki na wannan ya nuna min tabbacin ita da iyayena Maƙiyana ne basa sona ko kaɗan, take anan na fara tinanin abinda zanyi kala-kala wanda zansa rayuwar Rahinatu acikin ƙunci da wuya, wanda zaisa taji inama batazo duniya ba, take nan na yanke shawarar tonama take nan na yanke shawarar tonama kaina asirin ƙazafin dana ma Sultan domin Rahinat ta maye gurbin azabar hukuncin da za’a mani saboda inada tabbacin Mai Martaba bazai yi hukunci mai daɗi ba”_
+

sai kuma ta fashe da kuka sose mai cin kamin ta kada baki tace, _”Allah sarki Khulaid shine abokina a wannan masarauta, tinda mukazo muke tare har muka fara soyayya dashi, yana matuƙar sona sai daini kuma soyayyar da nake nuna masa yaudara ce, shine wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin na ɗauki fansar abinda iyayena suka mani da kuma aure mani miji da Rahinatu tayi, ƙarshe azzaluman cikin masarautar nan saida suka kasheshi kisa na walaƙanci kuma duk saina tona maku asiri, Allah ya jiƙanƙa Khulaid…..”

bakinta ne ya rufe sakamon jin muryar Khulaid yace, “ban mutu ba in araye Raihana”

ta ɗago da sauri ta kallesa, ya ɗaga mata kai da kuma cewan, “ƙwarai kuwa ina raye ban mutu ba, gawar wancan bani bane potocopy nane”

kukanta ne ya maye gurbin dariya, “ni kaina nayi mamaki da akace waɗan nna ƙananun ƙwarin sun kasheka, nai mamaki sose dan nasan wane kai ɗin”

police prisoner ɗin dake tare dashi ne ya ƙarasa cire masa ɗaurin fuskar da aka masa, nan ya fuskanci Ƙhaleed dake masa wani irin kallo, ya ɗora da maganar Raihana daga inda ta tsaya.

_”ka kamani ne Sultan Aayan dan kawai jin yanda akai mukaje gidanka har muka sauya maka mata, tabbas munyi hatsabibanci sose a rayuwa nida Raihana, saboda yanayinmu yazo ɗaya, ni banaji itama bataji, kuma sai abin yazo da ƙaunarta da nakeyi wanda komine zan iya aikatawa domin samar mata da farinciki da jin daɗi, tin lokacin data yankewa kanta shawara da dabarar zata tonama kanta asiri a wannan lokaci ta shiga damuwa saboda bata san ta yanda za’ai ta ɗauko Rahinatu ta maye gurbinta ba, ni kuma ganinta acikin wannan damuwa na fito mana da wannna hanya, nasa ta ɗauko kuɗaɗe da gwala-gwalan da Sultana Yasmeen ta bata muka saida muka haɗa kuɗin mukai jirgin zuwa nigeria, kwananmu uku a nigeria muka fara neman inda kuke, ta hanyar address naka dake goggle muka sami bayanin komi, watarana mun dawo daga hotel muna ƙofar gidan mahaifiyarka sai gaka ka fito akan bike naka, Raihana ta fita da sauri taje wurinka saika sanya ƙafa kai fatali da ita a ƙasa ka ƙara gaba kana zuƙar siggaret, kamin na fito nazo na ɗauketa akan hanyar daka wullar da ita saiga Nimrah ƙanwarka ta fito zata fita anguwa sai ta ganta da sauri ta fito a mota ta nufeta tana kiran Ukhty, cikin rashin sani na cewar ba Rahinat bace ta kamata suka shiga gida, a zaman da sukai Nimrah na lallashinta da bata haƙuri anan Raihana ta fahimci cewar ba auran soyayya kukai da ƴar’uwarta ba kuma inda wadda ka tsana shine Rahinatu, ta nan muka ƙara samun more idea na gabatar da aikinmu, Mahaifiyarka da kanta ta kai Raihana har gidanka ni kuma ina biye da ita a baya, Allah ya taimaka bata shigar da ita har cikin gidan ba ta ijjeta kawai a bakin gate ita kuma ta koma gida, tana juyawa Raihana ta dawo ta shigo motata daga nan muka fara tinanin abu na farko da zamuyi, anan ne muka saye mai gadinka da maƙudan kuɗin da muka sata acikin wannan masarauta, bayan kwan abiyo mahaifiyarka ta wuce saudiya zuwa gidansu a wannan rana muka sami damar shiga gidanka”_mun saye mai gadin gidanka da million biyu, hakan ya bamu damar kutsa kai ciki a dai-dai lokacin daka damƙo matarka kan cewar lalle saita faɗi maka yanda akai ƙazafin data maka ya faru”._
+

Raihana ta amsa, _”lokacin daka fito waje da ita domin sata cikin ɗakin karnuka dan horata, ka juya ka shiga gida ni kuma a lokacin nasa ɗankwalin dake hannuna na rufe mata baki, wata allurar da muka yo odarta mai karayar da lafiyar jiki ita muka mata a maƙogaro sannan mua tusa mata wani ball acikin baki har sai daya kai maƙoshinta, wanda wannan likita ya tabbatar mana da zai hanata magana har sia lokacin da akai aikin ciresa shima sai an taki sa’a mutum zai dawo da maganarsa, kamin fitowarka na maye gurbinta shi kuma Khulaid ya kinkimeta ya fita da ita, nasan saboda baka ƙaunarta yasa baka gane ban-bancin dake tsakaninmu, domin da zaka gane da kayan dake jikinmu, a son samu na na kashe Rahinat har lahira to kuma saina tina da ƙuncin rayuwar dana kasance aciki tin ina jaririyata, hakan yasa nace da Khulaid ya maida ita Libya ta maye gurbina domin itama ta ɗan-ɗani wahalar rayuwa…hakan ko akai ita tana can wanda ban san a halin da take ciki ba kasancewar babu waya hannuna, ni kuma inan ɗakin karnuka kana ta azabtar dani iriri har na fara kasa jurewa raɗaɗin azabar da kake mani, bayanan dana rattabo maka a wannan lokaci duk nice ba Rahinatu ba saboda ita bata san komi game da hakan ba, nayi hakanne domin ka ƙara jin tsanarta aranka ,saboda ina so yanda na rasaka itama ta rasaka,shiyasa nayi amfani da damar cewar ka sake ni wanda naso alokacin ka furta min kalmar saki ko kuma ka rubuta takarda”._ ,

_”ranar dana ji bazan iya bane duba daka na neman halaka ni na faɗi maganar da zata ɗaga hankalinka saboda nasan duk duniya babu abinda kake so sama da mahaifinka, daga nan na sami damar dana gudu daga gidanka, ina cikin wannan gudu kuma mota ta kaɗeni, wasu bayin Allah suka ɗauke ni dasu da wanda ya kaɗeni, na kasance cikin kulawarsu tsawon watanni shida duk da cewar ƙalau nake bawai cuta nake ba amma saboda wata manufa tawa yasa nayi lamfo har tsawon wannan watanni, ban farka ba sai ranar dana ji ana ƙishi-ƙishin fitar dani ƙasar waje domin binciken lafiyata”_. ,


ta ɗago ta kalla Raihan da yayi lakato yana kallonta yana sauraron irin rashin imani nata, ƴar dariya tayi sannan tace ,

_”Sultan Raihan kayi haƙuri domin kaima na nuna maka nawa hatsabibancin, wayarka da kake tinanin ta faɗi alokacin daka na ɗawainiya dani a asibiti ba faɗuwa tayi ba ni na saceta saboda ina da buƙatar yin waya da Khulaid naji halin da ake ciki, ya shaida mani Rahinatu na cikin mawuyacin hali dan yanzu haka ma farfaɗowarta ake jira daga dogon suman da ake tinanin tayi wanda a zahirin gaskiya ba suma tayi ba, ni da kaina na zuƙe jinin jikinta gami da mata allurar bacci ta tsawon wata guda, ya shaida mani Abu Ayan wato shugaban ƙasarmu ya sanar ma da mai martaba abinda ke faruwa, shi kuma yasa an kafa an tsare Rahinatu zuwa lokacin data tashi ta zayyano masa magautan cikin wannan masarauta, ranar da muka dawo ƙasar Libya bayan Khulaid ya ɗauko ni koda na shiga harabar Sultana Yasmeen abinda na jiyo shi ya ɗaga min hankali, tin ranar da Umma ta faɗa min tarihi na naji zuciyata ta ƙeƙashe da tausayi ko so na iyayena da kuma ƴar uwata da muka fito duniya a tare, amma ranar sai naji tausayin Rahinatu ya kamani har bazan iya barin su Sultana Yasmeen su aiwatar da abinda suke sonyi ba na ƙudirin kasheta”._ ,
ta maida kallonta ga Abie dake zaune kan kujera kusa da mahaifinsa wato Mai martaba.

“Abie gidanka shine gidan shugaban ƙasar nan wanda ke kewaye da dakarun tsaro na tashin hankali, wanda tinda nake ban taɓa ji ko labarin inda ake bawa tsaro ba irin wannan gida, amma sai gashi a hatsabibanci na dana Khulaid sai da mukayi mafakar da zamu dinƙa shiga cikin gidan, ta bayan gidanka muka haƙa ramin da zai dinƙa sada mu da shiga ciki a duk lokacin da muka so, duk wasu jami’an tsaro dake mutuwa ba kowa ke kashesu ba saimu, hatta ranar da muka saki
harbi aka tada tiergas mune ba kowa ba shine a wannan lokacin na koma asalin wurina da Raihinatu ta maye gurbinsa, su Sultana Yasmeen sunzo gidanka a wannan lokaci, inda suka rigamu sa’ar ɗauke Rahinat suka gudu, gudun kar a sami ɓacin rana na maye gurbinta, tare da taimakon likitanmu ya min allurar bacci ta wata guda, Khulaid kuma ya bini da duk wani bandage”._

+

Khulaid ya amsheta, “bayan fitowata a wannan lokaci shine nabi diddigin inda su Sultan Dameer suka nufa ta wurin jakadansa wanda duk abinda ke faruwa yasan komi bayan na sayesa da gwala-gwalai, a lokacin da suka kai Rahinat asibiti sonsu a kasheta sai Allah ya kaini kamin lokacin, a zahirin gaskiya bani bane, Jakadan Sultan Dameer na sanya akama plastic surgery zuwa irin kamannina, shiyasa koda suka kasheshi suka ɗauka nine, ban san taya har suka ɗauke Rahinat ba ta dawo hannun masarauta saboda ni tin a wannan lokacin da naje asibitin naga ba ita kawai sai nayi tafiyata sbaoda nima na fara tsoron tonuwar asirinmu domin bazanji da daɗi ba a hannun wannan masarauta, sai a shekaranjiya da na gaji da jin labarin irin halin da Rahinat ke ciki na fito domin faɗar gaskiya, koda naje station sai na tadda Inspecter suna bincike akan hakan wanda Sultan Ayyan ya umarce su da suyi, ta haka aka kamoni aka kawo ni hannunsa”._

“Ya Mai Martaba duk fitinar data faru acikin wannan masarauta ta faru ne silar ƴaƴanka, basu kowa bane magautan wannan masarauta face ƴaƴanka, ba kowa ke son ganin bayanka, bayan ɗanka Morad, bayan jikanka Aayan face ƴaƴanka guda 6 wato Sultan Dameer,Sultan Baheer,Sultan Salman, Sultan Abid da Sultana Yasmeen”._

Raihana ta faɗa.

Khaleed take kallo wanda yake mata kallon jin haushi da tinanin irin fansar da zai ɗauka kanta na cutar masa da Angel.

“Sultan Khaleed nayi matuƙar mamaki da ka gane cewar wace ni, taya akai kai mani basaja, kuma ya akai kasan ni ɗin ba matarka bace?”.

bai bata amsa ba sai neman hukunci daya buƙaci Mai Martaba yayi, ba akan ƙazafin da aka masa ba, akan cutar da akaima Angel ɗinsa.

nan take Mai Martaba ya bada izinin a shigo masa dasu Sultan Salman kaf ɗinsu, aka kawo kowa amma babu Sultan Dameer, hankalin Raihan a tashe yake ƙololuwa, ya rasa wanna irin hali mahaifinsa yake dashi na hassada da ƙyashi, yanzu gashi ya gudu, ko inya gudu ina zashi.

yana wannan tinani yaji Khaleed na bada umarnin a kuncewa waɗanda yasa aka zo dasu fuska, da mamakin kowa fuskar Sulatan Dameer ta bayyana da kuma Mai gadin gidan Khaleed.

doguwar ajiyar zuciya Raihan ya sauke, gefe guda ya juyar da fuskarsa yana runtse ido.

jin saukar hawaye jikin Khaleed ya waigo daga kallon Dameer da yake, Rahinat yaga tana kuka sose, ido ya runtse yana mai jin zafin zubar hawayenta, ƙaramar rigar dake saman jallabiyar daya sanya ya cire, fuskarta ya tallafo ya shiga goge mata fuskarta da wannan rigar.

hannu yasa ya kwantota jikinsa yana mai shafa kanta alamu na lallashi, ƙwacewa tayi tana galla masa harara, tashi tayi a wurin nasa ta nufa inda Raihana ke zaune tsakiyarsu Abbi.

kamo hannunta tayi ta wani ƙwace a fusace.

cike da tsantsar tsana take kallon Rahinat tace, “du faɗin duniya babu wanda na tsana sama dake Rahinatu, karki ƙara kusantoni, ki barni nima yau naji ɗumin azzaluman iyayena da suka gujeni duk da cewar ba sonsu nake ba”.duka da mamaki su Ammi suke kallonta da jin ɗacin kalamanta, Abbi banda sarawa da kansa yake babu abinda yake ji, wacce macece wannan tayi munaƙisar raba shi da ƴarsa harta ɓata masu suna a wajenta, mai suka mata ita kuwa a rayuwa. +

Ammi tana hawaye ta jefowa Raihana tambayar, “Raihanatu idan har kin gasgasata cewar Allah ɗaya ne kuma haƙiƙa babu wani abin bautawa da gaskiya sai shi, to ki yarda wallahi summa tallahi bamu sai daki ba, duk abinda aka faɗa maki sharri ne, amma munji mun yarda a yanzu mun amsa laifinmu mu kamin gaskiya tayi halinta”.

Ammi ta sakko ƙasa ta haɗa hannayenta biyu tace da ita, “na roƙeƙi da Allah ki faɗa min matar data gindaya maki wannan ƙaryar, ki faɗa min azzalumar matar data rabamu dake”.

cikin tsawa Raihana ta dakatar da Ammi da cewan, “Ammi karki sake kuma karki kuskura ki ƙara gangancin kiran Umma na da azzaluma, duk wata azzaluma a duniya to ta biyo bayanki amma badai Umma nah ba”.

bata ankare ba taji saukar wani lafiyayyaen mari saman kuncinta.

a ɗimauce ta ɗago ta kalla Abduljjabar wanda ke tsaye kanta yana faman huci, wani marin ya ƙara mata wanda yay silar sata suman zaune.

“dan kutumar ubar uwar data raineki duk irin haukan da kike ji dashi na taka ki na dameki, banza jahila kawai”.

juyawa yayi ya amsa wata lafceciyar dorina a hannun dogari, take ya shiga lafta mata tana ihu, duk yanda aka so a hana shi kuma a ƙwaceta amma abin ya gagara.

sai da Ammi cikin kuka tace dashi, “Abdul ko k aƙyaleta kona maka baki”.

ta faɗi masa domin tsoratarwa saboda taga yana neman yin kisan kai, sai wani tattake ta yake yana laftarta da iyaka ƙarfinsa.

daktawa yayi yana huci, da yatsa ya nunata yace, “karki kuskura kice min baki dashi, in kuwa ba haka billahillazi wannna haƙora talatin da biyun dake bakinki saina zubar maki dasu yanzu anan”.

ya miƙa mata hannu yace, “ki bani hoton shegiyar uwar taki da kike wa uwar data haifeki gargaɗi akanta”.

ai duk ta gama tsorata da yanayin Abdul, dan haka kuwa ba shiri ta zira hannu cikin rigarta ta ɗauko hoton ta miƙa mas ahannu na rawa.

fizga yayi ya warware shi yana dubawa, hoto ne daka rubuta my swt mother ajiki, duban fuskar hoton da zaiyi yasanya sa sakin dukkan abinda ke hannunsa ya kuma ware ido yana kallo.

ganin haka duk su Abbi suka yo kansa suna tambayarsa wace, Uncle Badamasi ya kalla wanda daka kalla fuskarsa kaga wanda ɓacin rai ya gama cikata da kuma tausayi.

a hankali cikin tashin hankali ya furta, “Anty Asma’u”.

suma su Abbi da Uncle Badamasi suka haɗa baki, ” Asma’u kuma, kana nufin Antynku?”.

ya ɗaga masu kai alaman ehh, amsar hoton daga hannunsa Ammi tayi ta kalla, itama da ɗimbin mamaki da al’ajabi ta furta, “Na shiga uku Asma’u”.

sai kuma ta fashe da kuka, “Asma’u dama ƙiyayyar da kike min har ta kai haka, Asma’u me nayi maki a rayuwa ni kuwa”.

ta zube gwiwoyinta a ƙasa tana mai zubar hawaye.

Uncle Badamasi ya kalla Raihana yace, “kin tabbata itace matar data sayeki a hannunmu?”.

ta ɗaga masa kai tace, “ehh, kuma bani da kamarta a duniyar nan”.

ai take jiki na rawa Uncle Badamasi ya ɗauko waya a aljihunsa ya dannawa Nawwara kira.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]