[Advertisements⬇️]

YAREEMA KHALEED CHAPTER 9 THEND KARSHE - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

YAREEMA KHALEED


CHAPTER 9 THEND KARSHE
*__________📖* yanda ya tsamke ta ajikin sa tsam tini ta kuma yunƙura wa domin ƙwace wa daga jikin sa sakamakon abinda taji ya tsarga mata.
+

“uhm-uhm ni ka rabu dani dan Allah”.

ƙaramin bakin ta ya kafe da idanun sa da suka gama sauya yanayi saboda sha’awa.

“ki faɗi mani mi zan yi ki huce fishin da kike dani wanda yake azabtar dani”.

“to ni ban yi niyya ba sai ka rabu dani, ni dan Allah ma ka sake ni na huta….”.

ɓacin rai ne ya bayyana a fuskar sa saboda jin furucin ta, yatsan sa ya ɗora saman laɓɓan ta ya danne,

“kar na sake jin kin mani wannan mummunan furucin idan ba haka ba ranki zai ɓaci”.

“to baka na da wata matar ba miye naka idan ka rabu dani”.

tai maganar tana shagwaɓar da fuska.

ƙaramar dariya yayi, ɗayan hannun sa ya ɗauke daga bayan ta ya dawo dashi fuskar ta ya ɗago, cikin ƙwayar idon ya kafe da ido yana kallo, ita ɗin ma shi take kallo da wani irin yana yi, jin baza ta iya jure ma kallon nasa ba ya sanya ta saurin sadda idanuwan ta ƙasa tana kallon ƙirjin sa.

sakamakon hango kishin sa ƙarara cikin idanuwan ta da kuma fuskar ta da yake a shimefiɗe yasa shi sakin murmushin leɓe wanda ya fitar da sauti.

kanta ya kwatar bisa faffaɗan ƙirjin sa yana shafa gashin kan ta.

ta gefen kunnen ta ya raɗa mata, “mi yasa kike zaluntar zuciyar ki akan haramta mata abinda take so take kishin sa”.

“ni ba kishin ka nike ba, kawai dai na faɗi maka ne ka rabu dani ka koma can wurin matar ka ku ƙara ta”.

“ni banda wata mata sama dake, ke ɗaya nasan zuciya ta na so na ƙauna, kece kawai mai maƙullin zuciya ta”.

ya ɗago kanta tare da mata nuni da saitin zuciyar sa yace, “kinga nan, mallakin ki ne ke ɗaya”. sannan ya mata nuni dashi kan sa yace, “ni kai na naki ne, ke ɗaya kike da wannan jikin ta ko’ina, ruwan ki ki bari kuyi shairing da wata ruwan ki ki hana wata kusantar shi”.

ɗago idanu tayi karab nata ya sauka cikin nasa,wani murmushi ya sakar mata haɗi da kashe mata ido guda, baki ta turo gaba tasa hannu ta bugi gefen ƙirjin sa tana tsuke fuska.

“ni ka daina mani wannan kallon”.

cikin sigar kwai-kwayon ta shima yace, “ni ka daina mani wannan kallon”.bata san lokacin da dariya ta subce mata ba dan yanda ya kwai-kwaye ta yasa ta dariya, wani sabon abune ya sake tsarga hudojin jikin sa sakamakon muskuta jikin ta data yi anasa, ido ya lumshe for second kana ya buɗe yana sake kallon asalin kyawun dake tattare da ita, manuniyar yatsan sa ya dora ta gefen dogon hancin ta yace, +

“Angel na ke kyakykyawa ce sose, haka duk lokacin da kika ƙawata wannan fuskar taki da dariya har sai kifi kyau kyau, plsss ɗago ki kalla cikin ido na ki sake min dariyan ki mai kyau kin ji”.

“taya zan maka dariya bayan ina fishi da kai ko ka manta ne”.

langwaɓar da kansa yayi cikin shagwaɓa tamkar ƙaramin yaro yace, “umhmmmm wai har yanzu baki haƙura ba?”.

kai ta ɗaga masa alamun ehh, miƙewa tayi a jikinsa tana gyara ɗaurin towel ɗin ta, zaune tayi kan gadon tana so ta miƙe taje ta ɗauko kaya amma yanda ya kafe ta da mayatattun idanun sa yasa ta kasa.

“kaga ka tashi ka fitar mani a ɗaki zan saka kaya, bazai yiwu nida ɗaki na ba kazo ka hanani sukuni ba, kaje idan na dai na fushin da kai zan neme ka amma ba yanzu ba”.

ko motsawa bai yi baranta ne tasa ran zai fita sai ma kyawawan eyes ɗin sa daya lumshe, ƙun-ƙuni take cikin ranta, ajiyar zuciya ta sauke ta yunƙura zata miƙe taji ya kamo hannun ta ya dawo da ita ta zauna, zaune shima ya miƙe kusa da ita, murza tafin hannun ta ya shiga yi tare da ranƙwafo da kansa ya cusa cikin ƙirjin ta yana goga fuskar sa, gaba ɗaya nema yake yasa jikin ta yin weak, dan haka da sauri tasa hannu ta ɗauke kansa.

shagwaɓa da rigima ya hau yi mata kaman ƙaramin yaron dake neman nono, ganin ba sauraron sa za tayi ba ya sakko ƙasa yay kneeling a gaban ta.

in a cool and slow motion voice yace da ita, “plsss my Angel”.

da hannu biyu ta katse sa, “naji ya isa, oya hold your lips”.

magana zai yi tai nodding kan ta tace, “shikenan ashe baka so na haƙura”.

saurin kama bakin sa yayi wanda hakan ya sa ta ƙyal-ƙyale da dariya sose, dariyar shima yaso yi dan akaran kansa ya bawa kansa dariya da yanda ya jawo laɓɓan sa gaba ya damƙe.

“kana yin dariya punishment ɗin ka zai sauya better hold on”.

marai-rai ce fuska yayi yana “unhm”.

kunnen sa ɗaya ta kama ta murɗa da zafi sannan tace, “aha take promise”.

kansa ya ɗaga alamun ya ɗauka.

lakuce masa hanci tayi tace, “magana zakai ba ɗaga kai ba”.

da ido yay mata nunin kama baki data sashi.
binsa tayi da sexy eyes nata tana kallon sa kamin ita ma ta sakko zuwa gaban sa da yay kneeling.

hannayen sa ta sauke daga bakin nasa daya kama, haɗawa da nata tayi gam tace dashi,

“idan har kana so naci gaba da kasance wa matsayin matar ka to kayi min alƙawarin zaka daina mu’amalantar dukkanin abinda yake haramunne shan sa a musulunci, zaka kaucewa shan duk wani abu da yake sanya maye gudun saɓawa mahallicin ka, zaka nisan ci duk abinda zai illata lafiyar jikin ka”.”i promise you my lady, bazan sake ba, nima ba son kai na yasa nake sha ba, halin da aka jefa ni shi ya jawo na kasance cikin masu shan kayan maye domin na samu sukuni acikin zuciya ta na ƙazafin da akai mani, sai kuma azabar da kike mani na nuna cewan baki sona, amma na maki alƙawari daga shan ɗazu da nayi ba zan kuma sha ba in har zaki barni na rayu cikin ɗumin jikin ki”.

ya ƙarasa maganar ya matsowa tare dasa hannu ta weast ɗin ta ya janyo ta zuwa jikin sa.
harar sa ta ɗanyi tare da ɗauke hannayen nasa tace, “to ai baka ce min ka yafe ma Ya Raihana ba”.

“ni bani ke da kaina ba, umarnin ki nake jira abar ƙaunata”.
ya faɗi yana shafa gefen fuskar ta da bayan hannunsa.

“ka zama mai yafiya domin Allah ma muna masa laifi kuma mu roƙe sa ya yafe mana, dan haka ka yafe mata har abada, kace ka yafe wa duk wani wanda ya zalunce ka a rayuwa, kayi masa fatan shiriya”.

” ehhh nayi , har wanda ma zasu yi min laifi nan gaba duka na yafe masu”.

yayi maganar yana ƙoƙarin cicciɓar ta.

“a’a ka ƙyale ni mana ,kace so kake na haƙura to na haƙura komi ya wuce, ka barni naje nasa kaya kaga ko mai ban shafa kasa duk na bushe”.

bai saurare ta ba ya ɗauke ta tana masa zillo, a kan gado ya kwantar da ita shima ya kwanta kusa da ita tare da ɗora kanta saman hannunsa.

karkato ta yayi sukai facing juna, ƙayataccen murmushi ya sakar mata ya zagaye weast ɗin ta da ɗayan hannun sa yana murza mazaunan ta.

“um-um ni ka bari”.
ta faɗi a shagwaɓe.

“hmm to na daina, oya tell me about my love”.

fari tayi da ido tare da juya ƙwar idon ta, hira ta fara masa wadda ta sanya sa ya nutsu yana sauraron ta, tin daga farkon faɗawar ta tarkon son sa har kawo ya yau, ji tayi yay shiru kamar babu shi a wurin, ta ɗago ta dube sa, hankalin ta ne yaso tashi ganin yanda launin idon sa ya sauya yayi jawur, gashi yay mata ƙuri ko ƙiftawa bai yi ba.

hannu ta aza bisa kumatun sa tana shafawa tace, “Husby whats wrong?”.
ta faɗi da damuwa.

ajiyar zuciya ya sauke with pity face yace mata, “am so sorry for all my wrong deed to you”.

“no worry Husby nah, ya zama past”.
kansa ya gayaɗa tare da ce mata, “all thanks to you Angel”.

murmushi ta sakar masa tare dayi masa kiss a cheeks nasa
“nima tell me about my love”.

leɓensa ya motsa ya lumshe idon sa tare da jan dogon numfashi ya sauke sannan ya buɗe idon sa ya ware su akan ta, hannun ta ya jawo ya ɗora a saitin zuciyar sa, yanda taji zuciyar na harbawa sai data ɗan tsora ta.

“haka son ki yake a kowanne bugu na zuciya ta tare da fitar numfashi na”.

motsa fuska tayi cike da jin daɗi cikin zuciyar ta, tinawa da Nadeeyah yasa farin cikin ta ya tsaya annushuwar ta ta ɗauke, ido ta ɗago tana duban cikin ƙwayar idon sa da ɓacin rai a maganar ta tare da faɗa take kora masa bayanin,

“kaja wa waccan lusarar matar taka kunne akan shiga hurumina in ba haka walla sai na maida wannan dogon goshin nata ciki, ta bar ganin ina mata shiru ina ƙyale ta tayi tinanin ko tsoron ta nike ji, ina raga mata ne kawai saboda ni ba mai son tashin hankali bace amma idan bata saita hankalin ta ba to ni zan koya mata hankali…….”.

shiru yay yana sauraron masifar tata, sai dai ta nisa har tana ƙulle ido kawai ya rufe bakin sa da nata da kisses, kasancewar kowa a desire yake so she was enjoying abinda yake mata.*__________📖* Khaleed sam baya fahimtar abinda Rahinat take faɗi masa, baki ɗaya ya ɗimauce da jin sa a wata duniya ta daban, lokaci guda zazzaɓi ya rufe mata jiki sai kuka take ta na basa haƙurin ya ƙyale ta da zafi, bai bar ta ba sai daya tabbatar daya maida ta cikakkiyar mace tukunna shima kuma ya dawo hayyacin sa
+

gefe ya koma yana maida nunfashi idon sa a lumshe, wani sanyin daɗi ke ratsa ilahirin jikin sa, ita kam banda shashsheƙar kuka babu abinda take, sai daya gama maida nunfashi kan hankalin sa ya dawo kan kukan da take yi, jikin sa ya jawo ta ya shiga lallashin ta yana bata haƙuri, ƙin sauraron sa tayi tana ture sa, shi ko kukan da take gaba ɗaya ya ɗaga masa hankali duk ya duburbuce, tsam ya matse ta jikin sa yana shafa gashin kanta yana afkin lallashi har bacci ya ɗauke ta.

kwantar da ita yay ya shiga yayi wanka sannan ita ma ya haɗa mata ruwa kana yazo ya cicciɓeta ya kaita toilet ɗin ya dire ta cikin bath-tub, take kuwa ta farka a baccin ta fashe masa da sabon kukan shagwaɓa.

murmushi yayi ya mata raɗa a kunnen sannan ya fice ya bar toilet ɗin domin ta samu tayi wanka, sai data gama kukan ta sannan ta gasa jikin ta ta samu tayi wanka.

shi ko tini ya gyara kan gadon ya kimtsa wurin, tsabar rashin kunya ta Khaleed har Mami ya kira ya sanar mata cewar yau ya maida ƴar’ta mace dan haka tayi adu’an samun jika a wannan rana.

murmusawa kawai Mami tayi tace da shi, “Allahumma yahidika mara kunyan yaro kawai, ina fatan baka wahalar mani da ita ba?”.

tamkar yana gaban ta ya ɗan sosa ƙeya yace, “ehh Mami sai dai raguwa ce ƴar’taki, sai kuka take yi”.

“tana ina bani ita”.

“tana toilet”.
“oak to ka tabbatar ta gasa jikin ta yanda ya kamata kamin na shigo anjima”.
“tom Mami”.

koda ta fito sai ɓata fuska take yi, shi ko yana ganin fitowar tata ya miƙe ya nufo gare ta, kauda fuskar ta gefe tayi tana ce masa,

“ni kar ka taɓa ni”.
tayi maganar a shagwaɓan ce.

hannu yasa ya ɗauke ta yana faɗin, “haba Angel nah, am sorry kin ji, daɗin nan fa bani ɗaya naji sa ba kema kan ki kin ji
.

kanta ta ɓoye cikin ƙirjin sa, dariya yayi ya sauke ta kan stool ya ɗauka mai ya shiga shafa mata, ita kam kunyar sa duk ta gama cikata, sam ta kasa kallon sa, dan haka yana gama sanya mata kaya ta masa wayo ta turasa parlo ta rufe ƙofan ta dawo gado tana murmushi.

_BAYAN WUYA SAI DAƊI._

shine abinda ta faɗi cikin ranta.


*3 MONTHS LETTER.*

Nadeeya ce zaune akan gadon ta ta cika tayi fam kawa zata fashe.

Jakadiya tazo gaban ta ta duƙa tace,

“ranki ya daɗe ina fatan dai lafiya ko?”.

a hasale Nadeeya tace mata, “ina fa lafiya Jakadiya wannan matsiyaciyar yarinyar ta rabani ta Sultan, kwata-kwata hankalin sa bai kaina gaba ɗaya ma mantawa yake da cewar ni matar sa ce, har kawo tsawon yanzu fa babu abinda ya shiga tsakanina da shi, ya bar ni da tsananin son sa d sha’awar sa”.


Jakadiya ta gyara zama ta numfasa, cikin murya ta magulmata tace mata,

“hmmm ai ranki ya daɗe ba haka ɗaya ta bar sa ba, buzaye ai zama da su haɗari ne, mugwaye ne da kike ganin su, na tabbata ta asirice Yarima ne”.


“haka kike gani Jakadiya”.”ƙwarai kuwa ranki ya daɗe, amma ai na banzar tayi domin muma baza mu barta haka ba taci gaba da yin nasara akan mu, dole mu miƙe tsaye musan abin yi”.

+

“tau yanzu me kike ganin zamu yi?”.

Jakadiya tayi shiru tana nazari can tace, “tana da ciki ne?”.

Nadeeya ta ɗanyi tunani tace, “da kamar wuya, domin da tana da ciki da kinji a fada yanda Mai martaba keji da ita ɗin nan, kuma shi kan sa Yarima da zan gani daga gare sa”.

“to masha’Allahu, dama da tana ciki abin farko da zamu fara shine zubar da cikin saboda kar tazo ta haife mana baƙar kadarar da zai gaji kujera, amma yanzu matso da kunnen ki kiji”.

nan Nadeeya ta bata kunnenta ta guntsa mata magana, dariya sukai tare sannan suka tafa, ran ta fari ƙal, nan take kuwa suka shirya yanda zasu je wurin boka.

****
“Aayan abinda yasa na kira ka shine, ina so na tinatar da kai cewar kamar yanda Rahinatu take matar ka haka Nadeeyah take mata a wurin ka, yanda kake fita hakkin waccan haka ya kamata kake fitta hakkin wannan ma domin dukan su matan ka ne kuma ko wacce nada hakki akan ka, kar ka bari Allah ya kama da tauye hakkin ɗaya daga cikin su, ka zama adalin namiji a wajen matan ka kaman yanda muke fata ka zama adalin shugaba a wannan masarauta”.

“Mami nifa bana son wannan yarinyar kin fi kowa sanin haka tun muna yara jinin mu bai zo ɗaya ba, kuma ni mace ne da Jad zai ce ya aura min ita ba tare da sani na ba bare neman izini, ni na yanke shawarar kawai zan sallame ta domin bazan iya zama da ita ba, totally ba ta ɗaya daga cikin irin matan da nike ra’ayi, Angel kawai ta ishe ni nayi rayuwa ta cikin jin daɗi”.

duk yanda Mommy taso ta nusar dashi sam ya burki ce yace mata ba haka ba, ransa a ɓace ya miƙe ya fita daga ɗakin ta, kai tsaye sashin mai martaba ya nufa, shi ɗaya mai martaba ya yarda da shigowar sa ba tare da neman izini ba.

a kishingiɗe ya sami mai martaba hadimai na masa firfita yana kuma cin kayan itaciya, gefe da shi ya zauna ya gaida shi cikin girmamawa, fuskar mai martaba sake yana mai murmushi ya amsa masa.

sunkwi da kai ƙasa Khaleed yayi yay shiru har sai da Mai martaba yace dashi,

“ya dai sarkin gobe, da wata matsala ne naga ranka a ɓace haka, ina fatan ba acikin masauratar nan aka ɓata maka ba domin ko wane bazan raga masa ba, duk cikin jikoki na kai nafi so kaine wanda bana ƙaunar ganin ɓacin ransa ko kaɗan, zan kuma iya aiwatar da komi domin ganin ranka ya faran tu na kuma ci zarafin duk wanda ya nuna cewar baya son ka”.

“Jad kai ne ba kowa ba”.

jin haka mai martaba ya miƙe zaune yana mai kallonsa, yana kuma mamaki da jin cewar shine ma yayi laifin ,kodai har yanzu bai daina fushi dashi ba a game da abind aya faru a baya.
“matso kusa dani nan Aayan”.
ya faɗi yana mai masa nuni da kusa da shi.

ya taso ya dawo inda ya umarce shi, fuskar mai martaba ɗauke da damuwa yasa hannu ya dafa kafaɗun sa yace da shi

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


“laifin mina maka Aayan, mi kake so na maka wanda zai gusar da laifi na daga zuciyar ka?”.

“ina so kamar yanda ka haɗa aure na da Nadeeyah, a yau ka raba wannan aure domin bana son ta kuma bazan iya zama da ita ba”.

“haba Aayan, kar kayi haka mana, Nadeeyah fa ƴar’uwar ka ce duk da a baya baka son ta ayanzu ya kamata ka sota kodan matsayi na zama matar ka data samu, ka tausaya wa maraicin ta ka zauna da ita”.

“bana son yin jayayya dakai,bana son yin musu da maganar ka, Jad idan har ka tursasa mani zama da ita to lalle zan bar maka masarautar ka da ƙasar ka kaman yanda ka umarce ni dayi a baya”.

hankalin Mai martaba ya tashi da sauri ya tari numfashin sa yace, “baza ayi haka ba Aayan, kai da zaka amshi ragamar mulki nan bada jimawa ba, a wannan karon idan kayi nesa dani lalle zan shiga mawuyacin hali, dan haka domin kasancewar ka farinciki na yarda da abinda kake so”.

nan take Mai martaba yasa a kira masa maga-takarda yace yana buƙatar takarda da biro, ana kawo masa ya miƙawa Khaleed yace ya rubuta duk iya adadin sakin da yake so yay mata, nan take kuwa Khaleed ya rubuta mata cika biyu yace idan ta gama idda ta dawo zai zai cika mata sauran ɗayan ta. +

koda Mai martaba ya kirayi Nadeeyah ya bata takardar ta ta buɗa taga maike ciki, take a wurin ta yanke jiki ta faɗi, amma yayin data farfaɗo ba Khaleed kaɗai ba shi kansa Mai martaban zagin sa take, uwa uba kuma Rahinatu.

zuciyar ta a hasale ta miƙe tana huci tayi turakar Mami tace ayau bata ga mai hanata kashe Rahinatu ba, da ƙayar aka samu ƙartan fadawa suka rirriƙe ta aka kaita ɗakin horo aka kulle.

Ɓangaren Rahinatu kuwa tunda ta labari yaje mata ta ɗauka fushi da Khaleed saboda ya mata alƙawarin zai yi haƙuri ya zauna da Nadeeya kuma bazai taɓa sakin ta ba kamar yanda yake faɗi amma yau sai ya saɓa mata wannan alƙawari.

sose ta ɗauka dokin fushi da shi ,tin Khaleed na ɗaukan abin da wasa har yazo ya fara damun sa ganin da gasken-gaske dai fushi take sose.

takai yanzu gaba ɗaya ta kulle sashen ta duk sanda yaje a rufe yake samun sa, idan kuma yaje ɓangaren Mami domin ya ganta tana jin sa zata miƙe ta bar wurin, ta kulle duk wata hanya da zata sada su ta juna, shi kuwa baya ganin zai iya dawo da Nadeeyah sam.

****
tashin yau yana dawo daga masallacin asuba ya nufa sashen ta dan yasan da wuya idan ta rufe ƙofa, saboda tana idda sallar asuba take zuwa gaida Mami da Mai martaba da Kakar sa.

yana ko zuwa ya tadda ƙofar parlon ta a buɗe, har dakawan da ke tsaye zasu isar da saƙon shigowar sa ya dakatar dasu nan yace duk su tafi

ita kam data dawo daga gaida su Mami baki ɗaya ta manta da batun rufe ƙofa ta koma ta kwanta sai dai ta rufe ƙofan ɗakin ta, daya murɗa handle yaji a rufe kamar zai kuka, ya dawo ya nemi cushion ya kwanta.

sai 8 ta farka ta shiga wanka, yana kwance yaji motsin buɗe key, da hanzari kuwa ya miƙe ya nufa ƙofan, yana zuwa ya murɗa handle a hankali ya tura ƙofan ya shiga, hamdala yayi da godema Allah daya sanya har ya shiga bata san ya shigo ba.

kai tsaye ya nufa inda take yana takawa saɗaf-saɗaf, tana tsaye a gaban tangamamen closet tana ciro kaya, jikin ta ɗaure da ƙaramin towel fari iya ka cinyar ta, baki ɗaya jikin jiƙe yake da ruwa da alamu daga wanka ta fito, sam bata ji motsi na alaman mutum a bayan ta ba dan hankalin ta baki ɗaya na kan zaɓar kayan da zata sanya.

lumshe idon sa yayi tare da furta Alhamdulillahi a cikin ransa, duk wata nustuwa da samun farin ciki nasa tana tare da Rahinatu, buɗe idanuwan sa yayi ya sauke su kan santala-santalan cinyoyin ta masu ɗaukar hankali, maida ƙwayar idon sa yayi daga saman kyakykyawar sumar kanta yana sauko da idon sa har zuwa tudun ƙafar ta.
gaba ɗaya suran jikin ta sura ce mai firgita sha’awar duk wani lafiyayyan ɗa namiji, cikin sanɗa ya ƙarasa takawa har ya kai gab da ita, dai-dai lokacin ita kuma ta zuge closet ɗin ta juyo, a firgice ta waro ido taja da baya zata kurma ihu nan take towel ɗin jikin ta ya zame ya faɗi ƙasa, saurin jawota yay jikin sa ya manne ta da ƙirjin sa yasa hannu ya rufe bakin ta.

“shiiiii!”. ya faɗi yana tsurawa ƙwayar idoon ta kallo, “matsoraciya nine to ba wani ba zaki mani ihu yanzu kisa azo a rufe ni da duka, mai martaba yasa a kulle ni”.

hararsa tayi ta shiga sauke ajiyar zuciya haɗe da runtse ido, ba ƙaramin tsoro ya bata saboda tasan ita ɗaya ce a ɗakin kuma babu wani mai shigo mata, ko hadiman ta iyakar su parlon ta da ɗayan ɗakin ta amma ko ƙofar wannan ɗakin basa zuwa, shi kuma data san yana shigowar yanzu fushi take da shi tasan koya zo zai ga wurin a kulle ya koma.

shi kam wani sanyayyan murmushi ya saki mai sauti yana bin kyawun fuskarta da kallo, a iya ka kwanakin nan da suka ɗauka tana hora sa ba ƙaramin kewar ta yayi ba, ƙugunta ya kamo da kyau haɗe da kai bakin sa saman kumatun ta yay mata light kiss.

gaba ɗaya hudojin ilahirin jikin ta sai da suka amsa, ji tayi wani abu ya tsirga mata zuwa tsakiyar kan ta, ita kanta tasan tayi kewar sa sai dai tana so ta hora shi domin ya dawo da Nadeeyah ɗakin ta, sam sakin bai mata daɗi ba duk da ba zaman lafiya suke da ita ba.

ɓata fuska tayi haɗe da ɗauke idon ta daga gare shi, hankalin sa ya tashi ganin har yanzu dai fushi take da shi, tace da shi, +

“ka rabu dani tunda dai ka koyi saɓa alƙawari”.

murmushi yayi yace da ita, “ban koya ba kaman yanda kike tunani, kawai dai bazan iya sirka soyayyar ki data wata ƴa mace ba, Angel ki fahimce ni wallahi bazan iya haɗaki da wata ba, jikina iya mallakin ki ne anyi shi domin kene kawai”.

lumshe idon sa yayi ya fara yawo da yatsan sa guda a ƙashin bayan ta, ita ma lumshe nata idon tayi taja numfashi ta sauke kamin nan ta buɗe ta sauke su a kan nasa da suka sauya kala, sun rune sun yi jawur ,ga kallon da yake mata jin sa take har zuciyar ta, baki ɗaya zallar soyayyar ta data hango cikin ƙwayar idon sa ta kulle bakin ta, ga shi ita kuma a gaskiya bata shirya saukowa ba a yanzu.

“My Heart Beat”.
ya kira sunan ta cikin muryan raɗa, hannun ta ya kamo ya ɗora a saitin zuciyar sa tana mai jin yanda take harbawa, ganin bata amsa masa ba ya shiga yawo da tafin hannun sa a jikin ta yana ma gadon bayan ta shafa mai tafiyar da hankali, nan take taji tsayuwar da take ajikin sa na neman gagar ta, yunƙurin ƙwacewa tayi, take ya maida kansa saman wuyan ta ya shiga sumbatar ta sumba mai tada duk wata sha’awa.

yana yi yana goga gashin sajen sa a gefen fuskar ta yana kuma yawo da halshen sa cikin kunnen ta, take ta soma fita hayyacin ta, daga ita har shi jikin su ne ya ɗau rawa lokacin daya maido da hannun sa ga ƙirjin ta, wata iriyar ajiyar zuciya ta sauke tare tasa hannayen ta ta kewaye shi, kanta ta ɗago sama tare da haɗa lips ɗin ta da nasa kamin ta buɗe baki ta kama nasa laɓɓan duka ta shiga tsotsa kawa ta sami sweet, gaba ɗaya babu wani kuzari ko ƙarfi a tare da su, sauran guntun kuzarin daya rage masa ya ɗauke ta ya aza saman gado nan suka shiga romancing juna, abubuwan da suke ma juna tuni Rahinatu ta mance da wani fushi da take da Khaleed, har suka lula babban birin maji daɗi.

*AFTER 1 WEEK.*

Bikin Raihana da Khulaid ya ƙara to ,hakan yasa Rahinatu shirya wa domin tafiya Nigeria ita dasu Mami.

kamin tafiyar tasu Mami tace zasu fara zuwa gidan amarya Nimrah dake zaune a saudia, Khaleed yace da Mami ai Rahinatu ba yanzu zata tafi ba sai ana gobe biki sai su taho tare.

mangare sa Mami tayi tace, “ka isa ma ka bimu, ai anan zaka zauna har muje mu dawo, kai kenan baza ka barta zuwa wurin ba kullum kana naniƙe da ita”.

“Mami ita ma ki tambaye ta kiji”.
“bazan tambaye ta ba ɗin, tafiya dai bazamu da kai ba”.

ranar da zasu tafi jin yake ina ma yana da abinda zai hana tafiyar, baya jin zai iya wata guda ba tare da Angel a tare da shi ba.

zama yay tana shiri yana mata kukan shagwaɓa, ita kam sam bata bi ta kansa ba don idan ta biye masa zai kuma ruguza tafiyar yaune kamar yanda yayi a jiya.

sai data haɗa komi nata ta bada akai mota kana ta juyo gare shi, zama tai bakin gado tana masa ƴar dariya tana tsokamar sa.

kansa ya kwantar saman cinyar ta yana neman mata kukan gaske.
“Angel kin fi kowa sanin wane ni, kin san bazan iya zama ba tare da ke ba har tsawon wata guda, dan Allah kice ma Mami kin fasa wannan tafiyar”.

ido ta zaro waje, sumar kansa ta shigar da yatsun ta ciki tana yamutsawa, “lalle Husby kana son kanka da yawa, bikin Yaya Raihana kake nufin baza ni ba, tabɗi kai ma kasan abinda ba zai yiwu ba kenan”.

“ni bamce ki haƙira ba, kice kin haƙira da zuwa gidan Nimrah, ita tayi tafiyan ta idan ya rage 2dayz bikin sai mu tafi tare, amma yanzu ace sai kinje saudia kin yi 2week kin kuma zuwa nigeria kinyi wweeks ,haba Angel nah ina kike so nasa raina”.

cike da tsokana tace da shi, “kaga amfanin mata da yawa kenan, da yanzu idna bana nan sai ka tafiayr ka wurin Nadeeyah”.

“ai dama ban sake ta gaba ɗaya ba, kamn nasan da zuwan wannan ranar, kinga yanzu idan kika tafi saina dawo da abata musha amarcin mu kamin ku dawo”.

wani malolon takaici ne ya kamata, mugun kishi ya tokare mata maƙo shi, ture kan sa tayi a samna cinyar tata ta yunƙura zata miƙe ya dawo da ita ya zaunar yana mata dariya ita kam ta bone fuska har tana neman fashewa da kuka.

“Allah ya huci ran gimbiya, nida wasa nike maki, ramawa nayi nima, amma kema kin san ai ƙaryar wata mace tace zatai gogayyar miji da ke”. +

da ƙyar ya shawo kan ta, Mami nata kiran wayar ta ta fito amma bai barta ta tafi ba sai daya lalata kwalliyar ta gaba ɗaya, sai daya sha zumar ta ya ƙoshi kana ya barta ta tafi cike da kewar ta.*__________📖* masha’Allahu anyi bikin amarya Raihana an gama lafiya sai fatan zaman lafiya da kuma zuri’a ɗayyi ba. +

duk waɗan da suka je biki suna zuwa su diba Anty Asma’u wadda ciwon paralize ya kamata, ta zama abar tausayi duk wanda ya ganta sai ya zubar mata da ƙwalla, shi yasa aka ce a rayuwa ka shuka alkhairi, bada ban darajar ƴaƴan ta da taci ba Uncle Badamasi ce yay baya dawowa da ita.

ranar da su Rahinatu zasu baro nigeria harda kukan ta domin tasan yanzu kamin ta sake zuwa sai anjima, tunda tana komawa school zata ci gaba da zuwa.

wannan karan ma sai da suka fara zuwa saudiya gidan su Mami kana suka ɗauko hanyar Libya.

tun suna can Mami ke lura da yanayin ta na kwana biyu da take fama da zazzaɓi, jikin ta duk yayi wani colaps ko abinci ma bata fiya ci ba.
sai dare suka sauka, lokacin da Rahinat da shiga ɓangaren Khaleed bai nan sun fita wata gayyata shida mai martaba.

ji tayi ba zata iya komawa ɗakin ta ba saboda rashin ƙarfin jiki da take ji,toilet ɗinsa ta shiga ta yi wanka ta fito, ko mai bata shafa ba ta ɓingile anan kan gado bacci yay awon gaba da ita.

koda ya dawo ya ganta murmushi kawai ya saki ya gyara mata kwanciyar yaja blanket ya rufe ta, stool ya janyo gaban sa ya ɗauka system ya kunna ya hau aiki.

sai kusan 11 ya kammala ya turawa mai martaba saƙon sannan shima yayi shirin kwanciya, jikin sa ya jawo ta ya hugging nata very tightly, yasan duk gajiya ce ta sata wannan baccin banda haka da Angel sai ta jira dawowan sa, cikin zuciyar sa yake ta mitar an wahalar masa da ita, ahaka har bacci shima ya ɗauke shi.

asuba nayi kusan tare suka farka, yay alola ya wuce masallacin fada ita kuma tai tata sallar a ɗaki, sai dai fa wannan ma tana iddawa ta kife da bacci a wurin.

shi ko tun bayan daya idda suka zauna tattaunawa a game da ɗaurin ratayar da za’ai ma Sultan Dameer, shi ba shi da matsalan komi sai da yace da mai martaba ayi komi kamin gari ya waye Angel ɗin sa ta sani.

Raihan nata kuka lokacin da aka rataye mahaifin sa, yana ji yana gani aka zuge shi, duk da Dameer ba mutumin kirki bane kowa ya shaida hakan a masarautar ,amma da yawa sai da suka yi kukan mutuwar sa sai dai Khaleed ya jaddadi kowa daya ja bakin sa yay shiru, idan har suka bari matar sa ta sani to lalle zai masu hukuncin da bazai masu daɗi ba.

suna zazzaune anan fada Mami ta kira Khaleed take shaida masa yayi sauri yazo matar sa b….
lafiyar da bata ƙara faɗi ba ya yanke wayar ya taso da sauri ya fito, a hanya sunkai kiciɓis da Abbas, tambayar sa ya shiga yi,
“ranka ya daɗe lafiya dai ko na ganka a hargitse haka”.

ba tare daya kalle shi ba yace, “maza tada mota”.

yana shiga yaga Rahinatu kwance saman cinyar Mami, gaban ta ya duƙa saitin fuskarta ya shafo wuyan ta nan yaji jikin ta zafi kawa garwashi.

“Heartbeat mike damun ki baki faɗi mani ba?”.

kasa ba shi amsa tayi ta bisa da idanun ta da suka kawo ruwa, saboda sose zazzaɓin da ke jikin ta ke shigar ta ga wani azababban ciwon kai na daban.

ai a ruɗe ya ɗauke ta daga saman cinyar Mami ya fita da ita, ko tsayawa sauraron abinda Mami kece masa bai tsaya ji ba.

ita kuwa cike da shagwaɓa ta narke masa ajiki tare da fashe wa da kukan shagwaɓa wanda jinsa ya sake ɗaga hankalin Aayan.

yana fita Abbas ya buɗe masa gidan baya ya shiga sannan shima ya shiga yaja su, direct asibiti suka wuce, suna zuwa likita ya mata gwaje-gwaje nan yay ma Khaleed congratulation ya sanar da shi Madam na ɗauke da cikin wata 3.

ina ai musalta farinciki a wurin Khaleed ba zai faɗu ba, nan take ya kira Mami ya sanar mata ya kuma sanar ma da Mai martaba, kan kace wannan masarauta ta ɗauka tun kamin su dawo.

tini mai martaba yasa aka soke raƙuma domin ai sadaƙa da su.

ɓangaren Nadeeyah kuwa tunda Jakadiya taje mata da labarin ta nemi natsuwar ta ta rasa, hankalin ta ya ta shi, safa da marwa kawai ta shiga yi a duk ta haɗa zufa.ganin haka yasa Jakadiya kwantar mata da hankali akan cewar ta bar mata komi a hannun ta, ba zubda ciki ba ko ciwon hauka take so a ɗora mata sai anyi yanda take so.sai a lokacin zuciyar Nadeeyah ta sami nutsuwa nan ta cika Jakadiya da kuɗaɗe masu yawa tace ta aiwatar da duk abinda ya taga ya kamata.

Rahinatu kuwa tun samun cikin nan samun kulawa daga wurin Khaleed ya nin ka na da, riritata yake tamkar ƙwai, ko da za shi course itally ce yay da ita zai tafi sai da Mami tai masa da gaske sannan ya haƙura amma ba don ya so ba, son samun sa ya tafi da abar sa shi zai fi kulawa da ita acan.

haka ya tafi bada son ransa ba, da sukai masa rakiya airprt kawa ya janyo ta su tafi, ga cikin ya wani ƙara mata kyau ƙirjin ta ya ciko sose yayo sama, haka suka rabu da kewar juna, a system kam kullum suna cikin vedio calling shida ita.

a daddafe ya samu yayi 2weeks acan ya saito hanya dan sam ba zai iya wannan wata gudan ba babu Angel kusa da shi, jin sa yake tamkar ya shekara dubu bai gan ta ba, da murnar sa ya nufi ɓangaren ta sai dai yana zuwa ya tadda bata nan hadiman ta suka ce masa tana ɓangaren Kakar sa Jadda.

yana zuwa ya tarar da abinda yasa shi kurma ihu ta zubewa ƙasa yana jin zuciyar sa kamar zata fito, domin cikin da yake marari ya zube, Nadeeyah tayi nasara akan hakan, sai da su Jadda suka lallame shi da tasassun kalamai tukunna ya sami nutswa cikin ransa tare da roƙon Allah ya ba su wani mai albarka.

kwana biyu da faruwan hakan yay masu visa zuwa america domin a asibiti su sake kula masa da ita daga nan kuma su sha honeymoon ɗin su.

cikin jirgi Rahinatu kwanciya tayi ajikin sa shi kuma yana aikin shafa bayan ta kamar yana lallashin yaron da zai bacci, a hankali a hankali take masa hira mai daɗi duk wanda ya ɗaga ido ya kalle su yaga cikakkun masoya, a haka har tayi bacci.

har sanda suka isko america bata tashi ba, shima kuma bai tashe ta ba ya ɗauke ta suka fito, koda ya fito tuni motoci har sun zo ɗaukan su.

gidan da suka sauka mai kyau da tsari, tunda suka sauka wanka wannan baya barinta tayi da kanta, shi zai mata ya naɗo ta a towel ya shafa mata mai yasa mata kaya ya kuma bata abinci baya barin ta yin komi da kanta.
sai da sukai wata biyu cif sannan suka kamo hanya suka dawo, satika kaɗan da dawowar su Rahintau ta fara rashin lafiya sose.
a wujugace akai kaita asibiti, ana zuwa aka jona mata drip jikin ta sannan likita ya aunata nan ya tabbatar wa da Khaleed tana ɗauke da juna biyu na tsawon wata biyu da sati guda.

ai wannan karon murnar har tafi ta farko, don take Khaleed ya durƙusa ƙasa yayi sujjada ga Allah yana mai nuna tsananin farincikin sa da godiya ga Allah.

yana miƙewa ya zura hannu aljihun sa ya ciro damin kuɗi ya damƙa ma Dr Abid, kallon kuɗaɗen Dr Abid yayi ya kuma kalla Khaleed da alaman tambayan na minene.

“thank you so much Dr da wannan albishir ɗin da kayi mani, wannan ita ce kyautar ka”.

murna sose Khaleed keyi baki yaƙi yaƙi rufuwa, waya ya ɗauka ya kira Mai martaba ya sanar masa, yana fitowa ma ya sanar da Mami abinda likitan ya shiada masa, murmushi kawai tayi tace alhmdl Allah ya raba lafiya amma ita dama tuni tasan menene, haƙiƙa ita ma ba ƙaramin farinciki ta kasance ba aciki Allah yasa an sami tsayayyae shine abinda take roƙon Allah, dama ga Nimrah ma da ciki farincikin sai ya zame mata biyu.

room ɗin da take kwance suka ƙarasa, cire mata drip kenan suka shiga, babu kunyan Mami bare ta nurses ya ƙarasa da azarɓaɓin sa ya rugumota jikin sa tsam yana faɗin,

“i rilly rilly love you Angel nah, another gift from God, na gode na gode, Allah ya sauke mani ke lafiya”.

ya ƙarashe maganar da bata sumba a kumatu, ita kanta nurses sai data ji kunyan abinda yayi kasancewar ta budurwa.

murmushin jin daɗi tayi ta ruƙo hannun sa, “da gaske Husby ina ɗauke da wani sabon cikin?”.

“ƙwarai kuwa, abinda Dr ya shaida mani kenan yanzun haka”.

ya faɗi yana mai shafo cikin ta.runguma ita ma ta kai masa tare da kwantar da kanta saman ƙirjin sa.

“kayi namijin ƙoƙari Husby nah lalle kai ba ƙaramin gwarzo bane, cikin watanni uku ka sake saka ƙwai”.

fuskar sa ya kwanto saman gashin kanta da babu ɗan kwali, “ai daga kene Heartbeat, kogin madara da zumar ki daɗin sa daban yake…..”.

Mami kam bazata juri ganin wannan rashin kunyar ba don haka ta saki gyaran murya, sam Rahinatu ta manta da cewan tana wurin, shi kam dama yana sane, wata uwar kunya ce ta lullɓueta tana jin kawa ta nutse cikin ƙasa.

ita wata kunyar ma ta daban data kamata Mami fa tasan yanda ankai ta samu cikin, ai ina ji tai kaman tai tsuntsuwa nan ta ɓoye fuskar ta a bayan Khaleed.
sai dare aka sallame su suka koma gida.

a wannan cikin kam zo kuwa ga sabuwar tarairaya, Lallami, So, Da kuma Ƙauna da Khaleed ke bawa Rahinatu, motsin ta ma sam bada son ranshi take ba don aganin sa motsawa ma wahalar ta yake, ita kuwa banda narkewa ba abinda take masa.

babu inda yake zuwa ko da yaushe tana maƙale jikin sa ita ma tai ta zuba masa shagwaɓa.
haka ɓangaren kowa ma samun kulawa take kowa ƙara son ta yake.

sai dai fa shima wannan karan abin sam baima Nadeeyah daɗi ba, nan sun kai ƙulla-ƙullar su da Boka akan ai mata kurciya ko a haukatata.

yanda suka so haka akai, wata rana Rahinatu ta fito da tirtsitsin cikin ta don lokacin yana wata bakwai, tana gab da shiga turakar Jadda Nazneen Nadeeyah ta hange ta da sauri ta cilla mata layar dake hannun ta.

jikin ta har wani tsuma yake yana ɓari ,burin ta kawai tazo ta taka wannan layar ko ta wuce ta kusa da ita burin ta ya cika, sai dai tana gab da nufar wajen sai ga Khaleed ya sunkuce ta ta baya ya juya da ita saboda bai son ta fito ba, daga shigar sa toilet ta sarfo don ta gaji da zaman wuri ɗaya.
wani malolon takaici da baƙin ciki ya turnuƙe maƙoshin Nadeeyah, ranta a ɓace ta nufi inda layar take zata ɗauke kawai bata ankara ba ta zame ta faɗi akan ta, ba wata-wata asiri ya koma kanta tamkar yanda boka yace da ita, hauka tuburan sai ihu take tana faman tsalle-tsalle.

abin ya bawa kowa tsoro da mamaki, dake Jakadiya ita ma baƙar munafukar kanta ce nan ta je ta sami mai martaba ta feɗe masa biri da wutsiyar sa akan ƙulalliyar da Nadeeyah tai ta zame kanta.

hukuncin da Mai martaba ya ɗauka akan Nadeeyah yaso ace lafiyar ta ƙalau da gobe aka ce ta kuma abinda tayi ba zata yi sa ba, sai can bayan gida aka mata wani ɗaki aka sanya ta aciki, nan take kashi tai fitsari haka kuma taita wani irin kuka kamar na jaki, sai dai ana ta mata magani da kuma adu’oi.

cikin hukuncin ubangiji cikin Rahinatu ya shiga wata tara cif, zuwa wannan lokacin ta gama yin nauyi domin tashi da zama da ƙyar take yin su bare uwa uba tafiya, ƙafafun ta sunyi mugun kumbura ita kanta cikin ya kumbura ta, ba ƙaramin tausayin ta Khaleed keyi ba, motsi kaɗan zatai zai shiga jero mata tambayoyi wani bin ma har tsokanar sa take don taga yanda zai ruɗe.

daren alhamis ta tashi da tsananin ciwon mara ga bayan ta ma, jikin ta duk ciwo yake mata, dauriya da cijiya kawai take saboda kar ta ɗaga hankalin Khaleed dake bacci, tun tana dauriyar har abin yafi ƙarfin ta, nan ta kamo Khaleed ta shiga girgiza shi, wani ikon Allah ya jima bai irin wannan baccin ba, duk baccin sa kuwa tana motsi zai buɗe ido ita har mamaki ma yake bata amma yau kam ta shin sa take yana sake gyara kwanciya.

yana farkawa ya ganta yaga yanayin da take, ai a kiɗime ya sakko daga gadon ya nemi jallabiya ya zura, sannu yake ta faman jera mata ya sunkuce ta suka tafi asibiti ba tare da sanin kowa ba don lokacin ƙarfe 2 na dare.

suna zuwa likita yaga halin da take ciki yace a wuce da ita labour room, farko ƙi Aayan yayi yace shi ta haihu a gaban sa, ganin abu yaƙi ci yaƙi cinyewa haihuwa har akai asuba bata zo ba ya ɗau waya ya kira Mami ya shaida mata hankalin sa duk a tashe.

nan da nan ko suka ɗunguma mutan gidan suka taho asibitin, lokacin da suka iso yana daga tsaye kusa da labour room ɗin ya kifa kansa, Abie ne ya taɓo sa, yana ɗagowa ya rungume Abie tare da fashe da kuka, kukan sa yake sose babu ƙaƙƙautawa tamkar ƙaramin yaro, babu abinda ya shalle sa da kallon da mutane ke masa, gani yake tamkar zai rasa Angel ɗin sa, idan ya jiyo ihun kukan ta har zabura yake yay ƙofan shiga labour roon ɗin su Jad su ruƙosa.
+

da ƙyar suka lallashe shi Abie ya zaunar da shi kan kujera ya dafa kafaɗar sa, yana mata adu’a yana zubar hawaye, iya jigata da wahaltuwa Rahinatu ta sha don bata haihu ba sai yammacin wannan rana awa goma sha biyar tana abu guda, 19:00 na dare ta haifo santalelen Baby boy ɗin ta, yaro fari ƙal kyakykyawa da shi jinin labarabawa, kamar sa sak ta kakan sa sarkin Libya.

tunda Rahinatu ta yunƙura ta fiddo da shi ta fitar da nishin ƙarshe bata kuma sanin a duniyar da take ba.
nan da nan ko aka shiga gyaran yaron aka tsabtace shi sannan ita ma aka shiga gyara ta, amsar yaron Dr yayi a hannun nurses ɗin ya fita da shi.

yana fitowa kuwa suka yo kansa da tambaya ɗauke a bakin su, sai dai abinda suka gani a hannu’n sa maganar kowannen su ta tsaya, farinciki duk ya lulluɓe su kowa murna fal a ransa.

murmushi yayi ya miƙa masu Baby’n yana taya su murna, duk abinda ke faruwa Khaleed bai san abinda ake ba yana can duniyar kuka ya kifa kai kansa a cinyar Abie.

jin kukan jariri yasa shi ɗagowa, yana ɗaga ido ya hango Mami riƙe da jariri a hannu, ai bai san lokacin da ya wani zabura ba ya miƙe yay wajen su, kallon kowa ya hau yi yaga babu ita, Dr Abid ya nufa yana kallon sa.

“Dr ina matata?”.
yayi tambayar a hargitse hankalin sa na neman barin jikin sa, don ganin jariri kaɗai ba ƙaramin fargaba ya shiga ba.

sai da Dr yay murmushi sannan yace masa, “tana ciki”.
ai bai jira wata cewar ba ya matsar da Dr daga bakin ƙofan yay ciki, yana zuwa ya tadda ita kwance kawa matatta, bacci take tana maida numfashin wahala, ƙarasawa yayi ya zauna gefen ta tare da ruƙo hannun ta cikin nasa, tsabar tausayin ta bai san sanda sabuwar ƙwalla ta cika idon ba ta zubo.

dai-dai lokacin kuma su Jadda suka shigo suma, kowa hankalin sa ya tattara kan yaron ana ta yaba kyawun sa, Jadda kema Jad tsiyar ita ai ta sami sabon miji tunda dama shi ya tsufa.

Khaleed kam sam hankalin sa bai jikin sa saboda rashin farkawar Angel, bai sami natsuwa ba sai da Dr Abid ya shaida masa ƙalau take babu wata matsala an mata alluran bacci ne don ta huta.

cikin ƙanƙanen lokaci masarauta da gari ya ɗauka, kafafen yaɗa labarai da ko’ina abinka da haihuwar ɗan masu ƙasa.
tunda Rahinatu ta farka sabon farinciki ya lulluɓe Khaleed, ƙaunar ta da saoyayyar ta ƙara ratsa cikin ƙashi da ɓargo na zuciyar sa.

kasancewar bata da wata matsala a daren aka sallame su suka koma gida.
hadimai da fadawa nata kai komo, tun kamin shigowar su busar serewa da algaitu ke ta shi duk da kasancewar dare ne, kowa ƙoƙarin sa so yake ya zama mutum na farko da zai fara taya Sultan Aayan murna domin samun babbar kyauta.

sose Rahinatu da Boy ɗin ta ke samun kula daga ɓangaren mijin ta da ƴan’uwan sa, trolly set biyar yasa aka judo masa da kaya na jariri daga saudiya aka kawo masa a washe gari.

ƴan’uwa da abokan arziƙi kuwa koda yaushe cikin tururuwar zuwa barka suke, kwana biyu da haihuwa Raihana ta diro garin itama lokacin ɗauke da jaririn cikin ta, ana kwana huɗu kuwa sai ga su Hajiya da Ammi suma sunzo har Yaya Suwaiba.

kamin suna akwati set goma sha biyar Aayan ya dire ma yaron sa da Maman sa, yau ta kama ranar suna inda yaro yaci sunan Kakan mahaifin sa sarkin Libya wato Suhail suke kiran sa da Arman.

zo kuga ruwan kuɗi da kyauta a wannan rana, sai da Aayan ya ƴanta bayi 100 banda waɗan da sarki shima ya ƴanta, haka nairori suka dinƙa kuka a wajen taron shagalin suna, sama ta ka ake ɓarin su, duk wanda yazo wurin nan sai an masa kyauta ta musamma mai tsoka, don mutane biyar ɗin farko da suka fara halarta wajen da maƙullin mota aka bisu ciki harda su Yaya Aisha tah da su Khaleesa, Nusy Gidaɗo kuwa dama ita ce uwar buɗe taro don sallar asuba ma a wannan hall na cikin masarauta tayi ta saboda kar a rab tayi ta saboda kar a raba wani abun ba ita.
+

sha’ani ake ta gudanarwa namomi nata kuka a bakunan mutane, Maman Husnah na hango loko can ta kwashi nama cikin wata kula tasa agaba sai ci take tana suɗe hannu, data ga an kuma shigowa da abun rabo zata taso da gudu tazo ta shige gaba saboda kar ai rabo babu ita, ƙarshe ma mayafin ta cire shi tai ta dunƙule a hannu, ɗaurin ɗankwali kuwa tsabar zalamar nama ya kunce an maida shi irin na tsaffi.

su My Zee,SisNah,Precious,Maman Abdallah,Uwar biri Hanash, sai ɗaga selfie ake ana ɗasa hotuna a inda ba’a taɓa zuwa ba, a ƴan gayyar soɗi kuwa harda ƴan xumunt@ Novell@ suka yo ayari nida ko katin gayyata ban kai masu ba, duk sun zauna akan kujerun da aka jera na alfarma sai ƙwalala ido suke suna jiran akawo masu nasu kason niko na rufe taro nace an ta shi, ina ta masu dariya ciki-ciki nace waya kawo ku gayyar soɗi gobe kwa kuma zuwa ba abinda zan bari a baku.

haka aka sha taro masha’Allahu taro tamkar naɗin sarauta, an tara jama’a babu ƙarya kuma duk wanda yazo sai yay hani’an yake tafiya.

Sultana Yasmeen dake prison a kulle ji take da zata sami damar fitowa da ba’abinda zai hanata banka ma gidan nan wuta shegu kowa ya rasa ran sa a banza, banda rashin adalci ƴar’ta na cikin wani hali amma su farinciki ma suke akan haihuwar shegen yaron nan da taso mutuwar sa aciki kamin ya fito.

tunda Khaleed yaji cewar Rahinatu wurin Jadda zata koma ransa ya matuƙar ɓaci, sam bai so hakan ba don wannan an ƙware shi ne kawai, yana ta faman kumbure-kumbure ya miƙe daga ɗakin nata ya wuce sa shin sa kamar zai kuka.
Mami nata masa dariya tace kuma kar ta sake ta dinga ganin ƙafar sa har sai anyi arba’in, a zuciyar sa kuwa yace da ku kanku sai kun gaji kun bani a bata, haka yake zuwa kullum babu ko kunya don ma in ya tashi wani abin Rahinatu bata bi ta kansa.

ranar kuwa data dawo ai Khaleed kawa zai tsaga ƙirjin sa ya sanya ta, tunda ya ƙure ta da ido yana kallon ta kawa yau ya taɓa ganin ta, shi kam wani kyau ta daɗa masa na musamman tamkar an sake halittar ta da zallar madarar kyau, ƙirjin ta dake ɗaukan hankalin sa duk sun daɗa cika.

Arman dake hannun ta ya amshe ya fita da shi ya kaima Jadda, yana dawowa ya tarar da ita tana ƙoƙarin zuge zip ɗin rigar ta, daga zuwa taya ta kuma ai nan salo ya sauya, lokaci guda ya gama burkita mata tunani, shi kansa nemna fita hayyacin sa yake, burin sa kawai ya jisa cikin ƙoramar zumarta, shi sam baya gajiya da ita ko kaɗan, kullum sake zama masa sabuwa take ga uban daɗi da take ƙarawa, wannan dare kam an gwangwaji sabon amarci saboda Mami da Jadda gyara suka mata na musamman, ƙamshin ta duk ya susutar da shi bai sami nutsuwa ba sai daya ji sa a duniyar data fi komai daɗi… Rahinatu na ganin so da ƙauna a wurin mijin ta da bata taɓa zato ba.

wani bin har haushin kanta take ji da raɗawa soyayyar su ƘADDAR SO da tayi a baya.
haka rayuwa tai ta tafiya shaƙuwa na daɗa shiga tsakanin su, kullum tamkar ana ƙara masu son juna.

shekarar Arman uku aka haifa masa ƙanne 2wins duk mata, shima wannan lokaci anyi bisha-sha, yara suka ci sunan Mami da Ammi ana ce masu Mahnoor da Maisha, Arman na son ƙannen sa, haka zai zo yake ta leƙen sj ta cikin cot nasu yana kaɗa masu abin wasa, wani lokacin ko in har akan gadon ta ta bar su to har ƙoƙarin ɗaukan su ya ke, sai ta kore shi ya tafi wurin Abie yana kuka, in ya tambaye sa yace Ammi ce.

ɓangaren Raihana ma nada yara uku a lokacin, mace ɗaya Jannat sai tagwayen mazan ta biyu Fadil da Fahad.

haka Nimrah ma a lokacin tana da ɗiyar ta Jasmeen.


*ALHAMDULILLAHI ANAN NA KAWO ƘARSHEN

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]