[Advertisements⬇️]

YAREEMA KHALEED CHAPTER 8 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

2

YAREEMA KHALEED

CHAPTER 8


[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]________📖* *2MONTHS LETTER.* +

Yau ne aka fito da Raihana daga cikin kurkukun da aka aika da ita, kuma ayau ne dai-dai wannan lokaci su Ammi da suka koma nigeria suka dawo domin tafiya da ɗiyar tasu.

Allah sarki baiwar Allah Raihana abar tausayi,duk ta rame ta ƙanjame tamkar ba ita ba, ga wani baƙi da tayi duk kuwa da tafi Rahinatu haske amma ayanzu kam Rahinatu madara ce akanta.

dukansu a zaune suke acikin fada kowa yana jiran isowar su, zumuɗi duk ya hana Rahinatu nutsuwa so take kawai taga shigowar ƴar’uwar tata.

sai da aka sanar ma da mai martaba kana ya bada izinin shigowar tasu.

hannayenta da ƙafafuwanta duka ɗaure suke da ankwa, kana kallonta kaga wadda ta azabtu, tsabagen wuyar da tasha da ƙyar ma take ɗaga murfayen idonta.

da gudu Ammi ta taso ta rungume ɗiyar tata ajikinta tana kuka, itama kukan ne ya suɓuce mata dama a maƙoshinta yake.

dukansu farinciki suke sose, tin ma Rahinatu data ƙan-ƙameta ta kasa sakinta har sai da mai martaba yay sallama kowa ya watse tukunna.

*4Hrs Leta.*

Rahinatul na zaune bisa katafaren gadon ta na alfarma, jikinta kaya ne masu kyau da kyawun gani, tasha ado mai ɗaukar ido, idan ba saninta kayi a yanzu ba zaka rantse kace ba ita bane saboda yanzu ta koma asalin ƴar sarauta.


waya ce hannunta take dannawa tana yi tana ɗago da ido tana kallon Raihana dake yin sallah.

Bayan ta idar da sallar Rahinat ta sakko daga kan gadon da azamarta tana cire alkyabbar dake jikinta tana faɗin

“yauwa to gyara muci abinci”.

ita dai Raihana kallon ta kawai take tana murmushi har tazo ta miƙo mata hannu tace,

“طيب،ھيا نذھب لنتغذي”.

Raihana ta miƙa mata hannu tana miƙe tace,

“أوکيه”.

Rahinatu ta bama hadimar ta umarnin zubo masu ruwa cikin mazubi domin wanke hannu, suka wanke hannu kana sukai bismilla suka fara cin kubza.

suna gamawa sukai hamdala tare, Raihana tace ma ƴar’uwar tata,

“أشکرك علي إه‍تمامك إياي”.

Rahinat ta sanya mata yatsa saman leɓenta tace,

“شششششششي،إياك أن تقولي ذللك مرة أخرى لك مکانه أفضل بکثير من ه‍ذا”.

farin ciki mai haɗe da ƙwalla ya taho wa Raihana, ta rungume ƴar’uwar tata ga jikinta, lalle ba kowa zai iya abinda Rahinat tayi ba, iya cutarwa tayi mata amma sam bata taɓa duba wannan ba.
suna rungume da juna Raihana tace mata,

“dan Allah Rahinatu ina so ki yafe min laifin dana aikata maki”

“oh ni jikar Matawalle, niko Y Raihana har sau nawa zance maki na yafe maki, ni wallahi tinda nasan ƴar’uwa tace ke naji na manta da duk abinda ya faru, ko bake bace wallahi ni mai iya yafewa kowa ne tinda gaskiya tayi hali bare ke da muke ciki guda, wallahi ko Anty Asma’u da kike gani na yafe mata duk da cutawar da tayi mana”.

“naga alamar hakan, dan gaskiya koni ace nice ke bana jin zan iya yafe maki ko zan yafe kuwa saina rama abinda ki kai min, amma dake zuciyar ki mai kyau ce wadda tayi silar abin ma kin yafe mata”.

suka saki juna,Rahinat na kallon ta tace,

“yanzu dai mu bar zancen baya tinda ya wuce, muyi wata hirar kuma”.to ni ina naga wani labari Rahinat, ai labari bai wuce labarin rayuwata ba dana kasan ce aciki, cikin wuya da ƙunci kuma duk kin san komi”.

“umm nasan komi, kuma indai akan sane bana son sake ji, ƙwamma muyi baccin dole”.

Rahinat data miƙe tana nufar wadrope take maganar.

wasu abaya ta ɗauko guda biyu iri ɗaya, pink colour masu shegen kyau, sun sha desgn da stones ajiki.

ta miƙama Raihana ɗaya tace ta sanya ita ma ta sanya ɗaya, su kansu kallon juna suka tsaya yi dan in banda kowacce ta san kanta tabbas baza su iya shaida juna ba.

a kan resting chair dake cikin ɗakin suka zauna suna hira, hannyensu riƙe dana juna.

Ammi ce ta shigo da sallama suka amsa mata, wurin su ta nufa kai tsaye, raba tsakanin su tayi ta shiga ta zauna, ta kalle su tana ƙawata fuskarta da murmushi, duban su take ɗaya bayan ɗaya, ganin ta kasa shaida su tace,

“to ni kam dai kamin zuwa lokacin da Allah zai yi na fara gane ku a faɗan ina Raihana, sarai dan ku ruɗar da mutane kukai wannan shigar iri guda”

Raihana tayi caraf ta nuna Rahina ita ma Rahina ta nuna ta, sai kuma dukan su har Ammi suka sanya dariya.

“au to shikenan, bari na kira Aayan ai shi yafi kowa sanin ku”.

Ammi tai maganar da son gano wace Rahinat.

ai da sauri Rahinat ta ɓata fuska ta ruƙo hannun Ammi take ƙoƙarin tashi, baki ta turo gaba, idanuwan ta kawa zatai kuka, kallon ta Ammi tayi tai ƴar dariya tace,

“to kunga ni ta inda zan ke gane ku kenan”.

“nifa Allah Ammi ki daina haɗa ni da wannan mara mutuncin mutumin, da har sai ta silar sa zaki ke gane ni idan ina tare da Y Raihana”.

“hmmm to sai ki daina ɓata fuska idan na ambace shi, banda abinki ma Rahinat ai ya kamata zuwa yanzu ki bar fushin da kike da Aayan, duk cutarwa da yayi maki ai bai kai wadda Raihana ta jefa ki ciki ba, ya kamata ki yafe masa matsayinsa na mujin ki”.

baki ta turo gaba rana tsuke fuska, ita sam bata son ake dangan ta ta da Khaleed.

Ammi ta juya ga Raihana tace, “to Raihana sai ki shirya Abbi’n ku yace baza mu kwana ba tafiya zamu yi yau”.

“tom Ammi ai ni a shirye nike sai dai na fito kawai”.

“Ammi amma dai ai nima dani za’a tafi yanzu ko, dama kin tina wancan karan haka kuka ce nayi haƙuri na zaunar ma Mammy idan kuka dawo ɗaukan Y Raihana sai mu tafi tare”.

Ammi tayi murmushin saman leɓe ta biye mata da cewa, “ehh”. dan yanzu tana cewa a’a Rahinat zata fara daru, dama wancan karan ma da ƙyar ta yarda ta zauna a wurin Mammy dan cewa tayi ai ita tinda dai babu aure yanzu tsakanin su bata ga abin zama ba.
Ammi tayi ma Raihana signa ta ido, dan haka tana fita Raihana ta miƙe tace, “Rahinatu bari naje…..”.

bata ƙarasa ba ta dakatar da ita da faɗin,

“a’a ki bari kawai mu fita tare, ai dama ba abinda ma zamu ɗauka, yanzu bari na shiga toilet kawai na fito, idan ba haka ba kika riga ni fita Abbi ce zai yi ku tafi dan shi mutum ne da bai son jira, ki san halin Abbi ta wannan ɓangaren”.

tana maganar ta nufar hanyar toilet.

da shigarta Raihana tai fit ta fice, sai dai zuciyarta cike da kewan ƴar’uwarta da zata yi, a bakin ƙofan parlo tayi karo da Khaleed daya sanyo kai ciki.

saurin sunkuyar da kanta ƙasa tayi tare da dafe goshinta, ana sa tinanin Rahinatu ce dan haka yay sauri sa hannu ya kwanto kanta ƙirjinsa yana faɗin, “sorry my dear”.

zuciyar Raihana ce ta shiga bugu, ɗagowa take son yi amma yanda ya kewaye ta gaba ɗaya da hannunsa sai ta kasa koda motsi dan gaba ɗaya ya saukar mata da wata iriyar kasala, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, shin har sai yaushe wannan abu dake maƙale a zuciyarta zai fita, yaushe zuciyarta zata gane babu soyayya tsakaninta da Sultan talkless of aure, sai yaushe zuciyar ta zata bar tinanin abinda bazai yiwu ba, har ta shiga kurkuku ta ƙaraci zaman watanni biyu aciki zuciyar ta bata bar tinanin Sultan Aayan ba dan har yanzu tana sonsa.

shi ko ɓangaren sa abinne ya bashi mamaki jin yanda tayi luf ajikin sa, Rahinat da tinda suka dawo daga asibiti banda faɗa babu abinda ke shiga tsakanin su, kullum cikin masa tsiwa take, hanya ma bata bari su haɗa, in ko suna zaune da Mammy yazo wuri tashi take, hannunta bai isa ya riƙa ba bare har ya sami damar haɗa ta da jikinsa.
+

tinanin da yake ya katse lokacin daya ji ta fitar da numfashi mai zafi a jikinsa, abinda yaji kamar ruwa ya zuba ya bashi tabbacin ruwan hawaye ne, zuciyarsa ta raunana tausayinta ya kama sa, yasan sarai tana son sa duk abinda take tana yi ne kawai dan ta rama abinda yayi mata.

ranƙwafo da kansa yayi zuwa saitin fuskar tata yace, “my Angel”.

jin tayi shiru ya ɗago ta ajikinsa, tafukan hannayensa ya sanya a haɓar ta ya ɗago fuskar tata, ƙura mata ido yayi yana son hango reason ɗin daya sa hawaye ke bin kuncin ta.

yasa yatsan sa zai share mata hawayen sai ya daka ta, yanayin fuskarsa ne ya sauya, pin ɗin data matse ɗaurin veil ɗin ta ya ɓalle mayafin ya kunce, tini ya fahimci cewar ba Rahinat bace kasancewar ita tana da yawan saje Raihana kuma bata dashi, gashi kuma ƙamshin daya santa dashi yau babu shi ajikin ta.

ransa ɓace ya sake ta, yamutsa fuska yayi yana watsa mata mugun kallo mai tattare da ban haushi, cikin kakkausar muryarsa yace da ita,

“me ya shigo dake nan?”.
“wa nike dashi anan, banda ita ai baza ka taɓa ganina cikin sashen ka ba, kai cikin masarautar taku ma ba zaka ganni ba”.

dukan hannayensa ya zuba cikin aljihun wandon sa, “koma minene, bana son ƙara ganinki a inda kika san inuwa ta da taki zasu haɗu, dan haka ki gaggawar ɓace min anan macuciya kawai”.

“hmmm dan ka kira ni da haka ko kaɗan bazai dame ni ba, tinda wadda na yiwa ma ta yafe mani, so duk abinda mutum zai kirani ya kirani dashi na banza yayi”.

“ke Sultan kike faɗawa haka, to ki bar ganin kina da alaƙa da Sultana yanzu sai mu yanke maki hukunci mara daɗi”.
Dakarun dake tare dashi suka ɗage labule suna faɗin haka.

ba ƙaramin razana tayi da yanayin su ba hakan yasa ta saita kanta, amma duk da haka dogari ɗaya sai da yayo kanta Khaleed ya dakatar dashi.

cikin miskilar magana yace dasu, “ku ƙyaleta taci darajar Angel nah da yanzu saita koma inda ta fito”.

ficewa Raihana tayi cike da jin haushinsa da kuma sonsa, tana fita Rahinat ma ta fito, kafaɗarta da tasa suka gogi juna ta banka masa harara kamar yanda ta saba kullum tai ficewarta ba tare data kalli inda yake ba.

daga can ta hangi su Abbi sun fito suna tsaye bakin mota zasu tafi, aiko da saurinta ta ƙarasa.

daru ta hau ita alalle sai an tafi da ita bqzata zauna anan ba, Mammy ta ruƙota ta ƙwace tayi wurin Ammi, ganin zata ɓata masu lokaci Abbi ya haɗe rai ya hauta da faɗan ita mahaukaciyar ina ce da auranta da komi zata ce zata bisu, to mijin nata ta barwa wa?.

“nifa Abbi ai banda miji yanzu, niko yana sona ni bana sonsa kuma ai tinda ma ya sake ni, dan Allah Abbi kar kayi min haka wallahi ni bazan iya zama dashi ba na barwa Y Raihana tinda ita dama tin can da tana sonsa, kuma ma ka tambaye ta har alƙawari na mata Allah na bar mata shi ni yanzu bana sonsa”.

tai maganar tana kuka.

Kakus dake tsaye tayi dariya tace, “kinga yanzu karki gaggawar yanke hukunci acikin fushi, tinda kika ga muma mun sakko da fushin mu akan Khaleed to kema zaki sakko ne, yanzu duk wannan hargagin da kike na lokaci ne, idan kuma kin haƙura da gasken kin barma Raihana ɗin shikenan sai mu koma ciki ya baki takardarki ita kuma a ɗaura masu aure, haka ne kawai zai sa mu tafi dake, amma matsawar da auran ki kanki sai dai ki bari kwazo da mijin ki kuwa”.

suna ta fama da ita, Mammy ma na lallaɓa ta sai ga Nadeeyah ta iso wurin cikin takun isa da taƙama gami da sarauta.

a daƙile ta ɗan rissina ta gaida su Abbi, kosu amsa ko karsu amsa ita dai ta gaida su ne dan kar Mammy tayi mata magana ta yarfa ta, a duk faɗin rayuwarta babu mutanen da take jin haushi kaman iyayen Rahinat, haka zalika idan ta tina Rahinat kishiyarta ce ta kan tsinci kanta a baƙin ciki ta takaici, wai wannan bolar gaja wata baƙar aba da ita wai ita ce kishiyarta.gaskiya Yarima yama cuce su daya ɗakko baƙin fata ya kawo cikin ahalin su, to ai ko a nigeria ɗin ma akwai farare amma shi ya rasa da mai zai ɓige sai auran baƙar fata abin tsan-tsani, mahaifiyarsa balarabiya mhaifinsa balarabe amma ya rasa wazai aura sai wannan abar.
+

baki ta taɓe tana yatsine fuska ta matsa kusa da Mammy ta ɗaya ɓarin hannun nata na hagu.

“Mammy kije inji Umti”.
“oaak, kice mata dan Allah ina zuwa, zamu yi rakiyar surukan Aayan ne”.

aciki ta amsa to ɗin ta juya ta tafi dan ko Mammy ma bata bata wani girma, yanzun ma tana cin darajar ɗanta da take aure ne.

tana juyawa Rahinat tabi bayanta da kallo cike da haushi da takaici, ba Nadiya kaɗai take jin haushi ba har shi kansa Khalid ɗin, musamman ma idan ta gansu tare sai taji kawa taje ta sheƙe Khalid, ta kuma rasa dalilinta na jin haushin hakan.

sai data gama harar bayan Nadiya sannan ta maido da hankalinta wurin su Ammi taci gaba da kukanta daga inda ta tsaya

“kin gama harar kishiyar taki?”.

Kakus tace da ita tana ƴar dariya cike da zolaya.

“Allah sauƙa wannan abar ta zama kishiya ta, ai bata da abinda zanyi kishi da ita”.

duk da tausayinta da Mammy keji sai data ɗan dara kaɗan itama, dan kowa tabashi daɗiya saboda maganar data yita cike da kishi.*__________📖* wayo Mammy tayi ma Rahinat kan cewar tayi haƙuri idan zata je sai su tafi tare.
+

“Mammy nafa san ba zuwa zaki yi ba, kawai dai kuna so ku ninke ni ne, haka ma kinka mani wancan tafiyan”.

suka dara gaba ɗayan su ita kuwa ta kuma cukulewa tare da sake son ƙaro wata rigimar.

Abbi ya doka mata tsawa yace ta shiga hankalin ta, ta bar ganin ana lallamata tace zata yiwa mutane iskanci, banda rashin hankali irin nata ina ta taɓa ganin aure ya mutu ba tare da sakin miji ba….

Abbi yay shiru da faɗan nasa jin maganar data yi ƙasa-ƙasa, “to ba sai nace ya sake ni ba”.

kamin su sake wani yunƙurin magana ta juya tayi sashen ta.
tana shiga parlon ta tarar da Aayan tsaye yanda ta tafi ta bar sa tin a ɗazu, tinanin ta dama yake ta yanda zai shawo kanta, duk yanda yaso sai ta kar kace ta koma kamar Nabila @KULLU NAFSIN.

hankalin sa ne ya ɗaga ganin busassun hawaye a fuskar ta, hannu ya kai zai kama haɓarta ta doke masa hannu, katse maganar da zai yi tayi da kama gefen rigarsa ta jashi kawa ta kama ledar kashi har zuwa inda su Mamy suke.

“tin da an dage kai miji nane to ka sake ni na sami ƴan cin kaina”.

tai maganar tana harar sa.ji tayi an bige mata baki har sai da leɓen ta ya daki haƙorin ta, a gigi ce ta ɗago kai tana kallon Ammi da ta ɓata rai tana watsa mata mugun kallo.

“idan na kuma jin wannan furucin a bakin ki saina saɓa maki, ki bar ganin ana ƙyale ki ana shagwaɓa ki, idan shi son ki ya rufe masa ido ba zai iya taking any action akan ki ba to mu zamu iya, shashashar banza kawai, sai kace mai zuciyar kafiran farko ,an baki haƙuri anyi-anyi ki haƙura amma kinƙi, to uwar ma mai yayi maki, ina ce in laifin ne kece dashi tinda ke kika nace masa har sai daya aure ki, hakan da yay ba taimakon ki yayi ba”.


Allah ya sota kusa ba kusa da Abbi da take ba da ayanda ya ta ƙufule shi ɗin nan sai ya faffaule ta, to sai Allah yasa tana kusa da Ammi, jan kunne Ammi tai mata sose tana gama faɗin haka suka shige mota suka tafi ya rage daga ita sai Khaleed a tsaye dan a rakiya har da Mammy da Nimrah, Abbi kuwa ce yay ta yiwa kan ta rakiyar ma baza’ayi da ita ba.

tana tsaye tana tsiyayar hawaye har motar tasu ta fice daga gidan, sannan ta raɓa ta gefen Khaleed ta wuce zuwa ciki

kan hanya sukai karo da Nadeeya suka bangaji juna, dakatawa tai ta ɗago da kai ta kalle ta, harara kawai ta watsa mata taja tsoki, tasan sarai da neman magana Nadeeya ta buge ta.

tsakin ta da harar ta sun ma Nadeeyah ciwo, dan haka ta damƙo kafaɗar ta ta baya, Rahinat ta juyo daga tafiyar da take tana mata kallon mamakin rashin hankalin da take neman mata.

“ke dabbar ina ce da zaki wani bangaje ni ki ƙara gaba ba tare da kin bani haƙuri baka”.

maganar ta mata ciwo amma saboda bata son tashin hankali sai bata bi ta kanta ba, dan ba tin yau Nadeeyah ke neman ta da rigima ba, wani tsokin ta kuma yi ta wurga mata kallon banza, zata wuce ta kuma ce mata,

“aikin banza aikin wofi, banda ma ke jaka ce ina ke ina liƙewa auren balarabe kema ai kin san babu gami, amma saboda tsabagen son kuɗi talauci yayi maku ƙatutu kika naye sai da kika aure sa, to yanzu mai kika tsinta a auren nasa, bari na faɗa maki, yanda tin a farko baki sami soyayyar Aayan ba haka har ki mutu bazaki taɓa samunsa ba”.

tsayawa tai tana kallon Nadeeyah dake faman tattaɓe fuska tana magana kamar wadda take gaban kashi.

hannu Rahinat tasa ta goge hawayen fuskarta kana a hasale ta cakumi kwalar alkyabbar dake jikin Nadeeyah.

kamin tace wani abu Nadeeyah ta wancakalar da hannun nata, “nafi ƙarfin wannan rashin mutuncin naki, dan haka karki kuma gigin sanya ƙazamin hannun ki ajiki na, ƴar mabarata kawai”.

in har ta biye ta Nadeeyah to abin bazai yi kyau ba dan haka tayi juyawar ta, zata tafi taji anma hannun ta mugun damƙa, juyowar da zata yi taga Khaleed ne, fuskar nan tasa a haɗe yana mata wani mugun kallo.

ƙaramin tsoki tai shima ta bashi nasa kason harar, ƙwacewa take son yi daga riƙon da yayi mata amma ta kasa saboda ba ƙaramar damƙa yay mata ba.

“dilla Malami ka sake ni”.

“ki ki fara bata haƙuri kana sai na sake ki, tinda ke bakin ki na rashin kunya ne baki san na gaba dake ba”.

“hmmm” tai murmushin takai ci tace, “to ai ko kai baka isa na baka haƙuri ba bare wata karan kaɗa miya matar ka, dan haka ka sake ni”.

yatsan sa yasa ya ɗalle mata leɓe, sose taji zafin hakan, hannu tasa ta dafe wurin saboda a wurin Ammi ta gwaɓe ta ɗazu.

“mugu kawai”. ta faɗi tana kiciniyar ƙwace hannun ta.
ƙara damƙe wa yayi ya kafa ya tsare akan sai ta bama Nadeeyah haƙuri tinda gaba take da ita, amma duk da zafin da take ji taƙi.

“kasan Allah ko da nice da laifi bazan bata haƙuri ba barranta na kuma bani bace, a haka kake so ka zama sarkin kana take gaskiya, ai komi ya faru kan idon ka ne, kana kallo ita ta bige ni amma shine saboda son kai da rashin adalci irin naka zaka ce na bata haƙuri, to wallahi sai dai mu dawwama anan amma bazan bada haƙuri ba”.

da mamaki yake kallon ta, duk sanda ta rufe ido tana faɗa ba ƙaramin mamaki take bashi ba, gashi in tana yi jijiyoyin ta har fitowa suke, ta iya masifa kace ba Rahinat ɗin baya ba.

ganin bai da niyyar sakin ta ta taƙarƙare ta gartsa masa cizo babu shiri kuwa ya sake ta, duk su biyun ta haɗa ta banka ma wata uwar harara tare da sakin dogon tsokin daya daki kunnen su kana tayi wucewarta.

murmushi ya saki a cikinsa yabi bayan ta da kallo, ran Nadeeyah ko ɓace da rashin hukuncin da baima Rahinat ba ta wuce fuuu zuwa na ɓangaren.

a parlo ta tsaya tama kasa ƙarasawa cikin ɗakin nata, tana tsaye tana saƙe-saƙen matakin da zata ɗauka akan Rahinat, tin kamin tasan wace Rahinat tasha alwashin sai ta raba tsakanin ta da Aayan, bare yanzu data san tafi ta da komi da namiji ke ɓiɗa, duk da kasancewarta balarabiya jinin larabawa amma Rahinat ta fita

ƙugu ta kama tana tinanin mafita, mahaifiyarta ta tina Sultana Yasmeen, lalle ya zame mata dole ta saci lokaci da daddare taje kurku-ku ta sameta domin neman mafita, dan dole ta fitar da Rahinat daga gidan nan.

ya zama dolen ta ta ɗauka mataki tin kamin abinda take gudu ya faru,ji tayi an kama tufkar gashin ta an lanƙwaso da kanta ta baya, Khaleed ne cike da mugunta yay mata hakan.

“me nace maki game da matata?”.

“amma Sultan wannan ai cin zali ne taya zan maka magana ahaka bayan ka damƙen gashi, dan Allah ka sake ni wallahi da zafi”.

tai maganar murya a shaƙe tana daɗa runtse ido.

ƙara damƙewa yayi ya shiga kora mata bayani kamar yanda yake mata koda yaushe.*__________📖* “wanna kashedi nayi maki akan shiga hurumin matata?”.
+

“amma taya zan bari ƙaramar yarinya kamar wannan ta raina ni, gaskiya Sultan bazan iya ba,bazan iya bin umarnin ka ba indai akan haka ne”.

cikin salo na mugunta ya sake barƙalo da wuyan ta ta gefe.

“wannan ya zama kashe di na ƙarshe da zan yi maki Nadeeya, kallon banza kika kuma matata sai kin gane baki da wayo”.

ya sake ta yana binta da mugun kallo.

“amma Sultan wannan ai rashin adalci ne kake nunawa, ya kake fifi-tata akai na, yanda take matar ka nima fa haka nike matar ka….”.

maganar ta tsaya mata sakamakon hannu daya sa ya matse bakin nata gaba ɗaya.

“sau nawa zan faɗi maki ni ba mijin ki bane kar ki kuma alaƙanta aure a tsakanin mu?, ke baki da wani matsayi a wuri na face sharar bola, idan kowa na ɗaukan ki matsayin matata to ni ba komi na ɗau ke ki ba face baiwa ta, dan haka ina mai gargaɗin ki da kije ki sake bin hanyar da kika sa aka ƙulla wannan aure a war-ware shi, ni ba zaki taɓa kasancewa matata ba domin bazan taɓa haɗa Angel da wata ba, idan kuma kin ƙi to ina maki maraba da shigowa ƙoramar wahala”.

ya sake bakin nata yana ƙyasta mata hannu,
“and this should be the last worning da zan yi maki, kar ki ƙara bin hanyar da Heenat take bare har ki saukar mata da ɓacin rai sanadin ganin ki”.

ya ƙarashe faɗi mata yana mai take mata yatsun ƙafar ta da takalminsa, ƙarar zafi ta saki ta shiga bashi haƙuri tare da ƙoƙarin janye ƙafar.


ransa matuƙar ɓace ya fice daga ɓangaren nasa yayi na shi, hana dakawa bin sa yayi, a ƙasan malelen carpet ɗin dake parlo’nsa ya zauna.

hannu ya miƙa saman wani glass table ya ɗauko giya ya fasa ya kwan-kwaɗa kana ya kunna siggaret ya shiga zuƙa.

daga saman kujerar ya kishingiɗar da kansa tare da lumshe ido’nsa da sukai masa zafi.

Nimrah ta shigo ɗakin ɗauke da sallama bakin ta har ta ƙaraso gaban sa bai ma sani ba, tana ta masa magana sam bai san tana yi ba, hannu tasa ta ɗan bibbigi kafaɗar sa, a hankali ya buɗe idon yana kallon ta.

tace dashi, “kazo inji Mami”.

duk da sama-sama yaji zancen nata amma ya gane abinda tace, sai daya ɗauki kusan minti biyar kana ya ɗaga mata kai alamun yaji.


bai tashi ya amsa kiran Mammy ba sai daya ɓata kusan awa ɗaya, a cikin ɗakin ta ya sameta hadima’nta suna mata hidima, daga masu tausa sai masu firfita.

ganin shigowar sa duk suka miƙe suka fita suna masu rissinawa.

yana tangaɗi ya ƙarasa wurin ta, zama yayi ya kwantar da kan sa saman cinyar ta.

hannu tasa cikin sumar sa saboda ganin irin yanayin da yake, kamar yanda damuwa ta bayyana ƙarara a fuskar sa haka itama.
cike da so da kulawa take shafa gefen fuskar sa, tace dashi,

“ba damuwa ya kamata ka sawa ranka ba,ka cire jida kai ka lallashi Rahinat, kai fa namiji ne kasan yanda zakai ka shawo kan kowacce mace, fishin Rahinat akan ka ƙaramin alhaki ne,”.

“Mami bazan iya kuma mata komi ba, bana son zama da mutumin da bai sona dan haka zan mata yanda take buƙata, ni ai ba sa’a’nta bane da zata ke raina min wayo tana bin duk abinda taga dama dan ina son ta”.

“a’a zancen saki bai taso ba, kasan dai yanda zaka ci gaba da shawo kan ta, kar ka gaji kayi fushi kaji Aayan ɗina, ina so naga kun kasance a tare cikin farin ciki”.kai kawai ya gyaɗa mata sannan ya ɗaga kan nasa daga saman cinyar tata ya miƙe zaune.

abinci ya buƙata data ba shi, dama ita ma abincin zata ci dan haka ta zuba masu tare suka ci.

bayan ya gama ya tashi ya fita daga ɓangaren ta ya wuce na Rahinat.

ko da ya shiga ɗakin ta tana cikin toilet, kwanciyar sa yayi a kan gadon, fitowar ta taga mutum sheme kamar wani matacce.

sai da taja tsoki ta cuno baki sannan taci gaba da goge ruwan ƙafar ta saman foot mat, jin wayar ta tayi ƙara da sauri ta nufa beside drower dan ɗauko, baƙuwar numba ce, tana ɗagawa taji Raihana ce ke magana.

tace da ita, “ni Y Raihana bazan kulaki yanzu ba”.

ta kashe wayar ta maida ta ijje.

juyawa tayi zata nufa closet taji ya riƙe hannun ta, a ƙufule ta juyo zata ƙwace, ganin ya kafe ta da shanyayyun idanunsa da suka ƙanƙance sose.

bai bari tayi maganar da take so ba ya fizgo ta ta faɗo jikin sa.
yatsina fuska tayi ta shiga kiciniyar ƙwacewa,

“bana son rashin mutunci ka sake ni, wannan ma ai iskanci ne zaka shigo mani ɗaki ba neman izini kuma ka kwanta min har kan gado,dilla ni ka sake ni”.

“haka kike so naci gaba da zuba maki ido Angel, wallahi bayan azabta ta sonki harda addaba ta sha’awar ki ma,plss ki daina wannan fushin dani haka ya isa, ki daina wahalar da zuƙatan mu, mai kike so nayi maki ki haƙura ki daina fushi dani ummm Beauty nah?”.

kasa wani motsi tayi saboda yanda yake tafiyar da yatsansa a ƙashin bayan ta ta cikin towel ɗin ta daya zame.

wani yawu ta haɗiye a maƙoshin ta, yunƙura wa tayi zata miƙe ya dawo da ita ta hanyar kamo buttocks ɗin ta ya matse ta da jikin sa gaba ɗaya.[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]