[Advertisements⬇️]

YAREEMA KHALEED CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

YAREEMA KHALEED


CHAPTER 7

*__________📖* ko bayan da Nawwara ta ɗaga abinda taji mahaifin nata ya faɗa ne ya ɗaga hankalinta, da sauri kuwa ta faɗa ɗakin Anty.
+

zaune gefen gado ta ganta ta rafaka uban tagumi, ta dafata tace, “mi Hajiya Saddiqa tace maki?”.

ai gaban Anty sai daya faɗi jin ambatar sunan Hajiya Saddiqa, bata taɓa sanin da shaiɗaniyar mace take mu’amala ba sai data nuna mata halinta, to kome zai faru da ita ai sai dai ya faru da ita amma bazata taɓa iya mu’amala da mace ƴar uwarta ba.

saɓo mai girma a wurin Allah, mai aikata shi Allah ya tsine masa, da sauri ta girgiza kanta tace da Nawwara, “babu komai tace dai zata je ta dawo”.

Nawwara tace, “oak, to Anty Baba ne ya ƙirani yace wai mu shirya yanzu yasa Yaya ya gama booking zamu wuce ƙasar Libya”.

a firgice Anty ta zaro ido dan zancen ba ƙaramin razana ta yayi ba, kamin tayi wani yunƙuri na magana suka jiyo ƙarar jiniya a harabar gidansu.

da sauri suka miƙe su duka suka fita, suna isa parlo suka ci karo da Hajiya a tsaye fuskarta da zallar ɓacin rai

tana ganinsu ta bama ɗan sandan dake tsaye umarnin ya sama Anty ankwa, take kuwa aka sanya mata ankawa.

rau-rau idanuwanta sukayi, zatai magana cikin tsawa Hajiya ta dakatar da ita da hannu tace,

“dakata karki ce dani komai, munafukar banza kawai maciya amana, muguwa, mai hassada da ƙyashi, toki sani makomarki bazatayi kyau ba, domin bazan taɓa yafe maki ba kuma bazan barki haka ba”.

tini Hajiya ta bawa Ƴan Sanda umarni suyi gaba da ita zuwa airport.

*2Hrs 53Mints Letter.*

cikin wannan lokaci jirginsu ya sauka a ƙasar ta Libya, suna sauka motar data iso domin su ta ɗaukesu zuwa masarautar ta Libya.

tin kamin a shiga gaban Anty ke faɗuwa, lokacin kuwa da sukai sallama cikin fada jinta tayi kaman tayi mene saboda kunyar data kamata.

ƙasa tayi da idonta ta kasa haɗa ido da mijinta, cikin tsawa ƴan sandan dake tsare da ita suka ce ta zube gwiwonta ƙasa.

Hajiya na shigowa daga bayansu tace da Uncle Badamasi, “kai yau idan harni na haifeka na baka nono, to kamin na ƙifta idona ka saki wannan makirar, ka mata cika biyu ranar data gama idda ka cikashe mata na ukunta”.

take kuwa ya kalla Anty da mugun tsanar halayyarta yace, “Asma’u na sakeki saki biyu”.

Rahinat na ganin Hajiya ta ƙwace daga hannun Khaleed daya wani damƙeta kawa ance za’a ƙwaceta tayo wurinta da gudu ta rungumeta.

tsam itama Hajiya ta rungumeta tana hawaye farin ciki fal ranta, “Rahinatu kece”.

kai kawai Rahinat ta ɗaga mata tana murmushi, tausayi ta bawa kowa na wurin tinawa da cewan fa da tana magana amma a sanadin muguwar ƴaruwarta yau ta zama sai kallo.

ɓangaren Raihana ma tana ganin Anty ta taso da gudunta tayo wurinta tana kiran,

“Umma na mai jin ƙaina, ki bar zubda hawaye matsawar ina raye babu wanda ya isa yay maki wani abu wai shi ɗaukan hukunci saboda baki da hakkin kowa”

“ni ba mahaifiyarki bace Raihana kamar yanda na faɗa maki, duk labarin dana karanta maki ƙarya ne gaibu ne, babu wani abu ɗaya daya faru daga ciki, tabbas ɗaya nake sanar maki dashi cewan waɗan can sune iyayenki na gaskiya kaman yanda na shaida maki, amma sam zancen sun sai daki ƙaryata ne, zance ne da shiri na son zuciyata”.wata muguwar damƙa Raihana ta bawa kafaɗar Anty, jijjigata ta hauyi kawa ta sami reshe, manyan idanuwanta ta firfito mata dasu waje, numfashi mai zafi take sauke mata aka tana huci, yanayin data koma ya tsorata Anty dan sai ta ganta kawa aljana ko wata horo.
+

cikin in-ina tace da ita, “kika ce mene? kika ce mene?, ina tambayarki kin min shiru kika ce mene?, dama sharri kika haɗa domin ki rabani da iyayena?, kikai wa iyayena ƙarya”.


duk maganar da take a tsawace take mata su tana wani jijjigata, kan kowa na wurin ya ankare cikin zafin nama Raihana ta ɗaga hannu ta ware zara-zaran yatsunta ta bawa Anty tas tas a fuska.

“ki gaya min duk dalilin shirinki na yin haka?, ki faɗa min dalilinki na sanya rayuwata cikin wahala bayan ina da gata”.

ta faɗa tana maƙure wuyan Anty, tana soka mata farcinanta zaƙwa-zaƙwa.

kakari Anty ta fara ,tini aka taso aka yo kan Raihana ana ƙoƙarin ƙwatarta amma kawa wata namijin zaki sai data watsar da kowa ƙasa.

“zaki gaya min ko saina feɗe ki”.

tai maganar cikin ƙaraji tana nuna Anty da wuƙar data warta hannun wani dogari.

“kiyi haƙuri ,wallahi son zuciya ne, hassada duk ita ta jazamin, na kasance tin auren Sa’adatu da Abdullahi nake baƙin ciki ,haka kawai nake ƙinta bata re data min wani laifi ba, saboda ta kasance mace mai farin jini kowa sonta yake, haka dangin mazajenmu duk sunfi sonta, shiyasa ni kuma na tsaneta, lokacin data haifi ƴan biyu ji nayi kamar na kasheta saina kasa samun wannan damar shine kamin ta farka Abdullahi yazo nazo na saceki nai replacing da wata gawar jaririya dana sato, kema so nayi na kasheki sai Allah bai bani wannan damar ba, shine na bada rainonki har kika girma nai maki wannan karatun ƙaryar, amma wallahi iyayenki mutanen arziƙi ne….”

ai bata ƙarasa ba Raihana ta soka mata wuƙar dake hannunta take jini ya shiga shatata.

salati kowa ya saka aka mimmiƙe tsaye.*__________📖* Khaleed ne ya miƙe da sauri ya isa wurinta, yana zuwa yay saurin ƙwace wuƙar da take neman sake daɓawa Anty, yanda take huci shima haka yake huci, wani fincikarta yayi daga kan Anty yay cilli da ita gefe guda
+

“Arrest her”.
mai martaba ya faɗi yana daga kan kujerar mulkinsa a zaune.

take aka ɓama Raihana handcuff a hannu, hawaye kawai take zubarwa tana bin Rahinatu da mahaifanta da kallo, dana sanin abubuwan da tayi kawai take,soyayyarsu da ƙaunarsu gami da tausayinsu lokaci ɗaya sukai wa zuciyarta mugun kamu,shin ta inama zata fara neman yafiyar Rahinatu.

bayan an fita da Anty Asma’u zuwa asibiti aka samu hayaniyar dake fada ta tsagaita, mai martaba ya buƙaci da a kawo masa biro da takarda, miƙo masa akai yay rubutu ajiki kana waziri ya miƙa hannu ya amsa.

abinda ke jikin takarda ya fara karantowa bayan yace saƙo daga mai martaba,
“wannan kotu tana buƙatar da a kamo mata waɗan nan mutane, Baheer Suhail Albanna, Dameer Suhail Albanna,Salman Suhail Albanna,Abid Suhail Albanna da Yasmeen Suhail Albanna”.

baki ɗayansu acikin minti uku aka gabatar dasu gaban mai martaba, kowanne cike da kunya da dana sani banda Sultan Dameer wato mahaifin Raihan.

ba wani ɓata lokaci Mai martaba ya yanke masu hukunci.

“haƙiƙa kunyi kuskure mafi girma, laifukanku suna da yawa ƙwarai, dan ku ƴaƴana ne hakan bazai hana ni yanke maku hukunci mai tsauri ba, tambayar da zanyi maku shine wane yay kisan wannan gawar?”.

shiru sukai dukkaninsu ba wanda yay magana, har saida yay sau uku tukunna Abid da shine ƙarami ya buɗi baki yayi magana cike da tausayin mahaifin nasu, dan yanayinsa kawai ya nuna yana cikin ƙunci ,takaici, gami da kunyar abinda ƴaƴan cikinsa sukai duk a saboda kujerar sarauta

“كان ضمير هو الذي قتله.”

Khulaid ne ya nemi izini da abashi damar yin magana.
aka bashi ya miƙe ya bada wani flash, aka soka jikin laptop, take dukkanin abubuwan daya faru na sirrin tattaunawar su Dameer ya bayyana aciki.

su kansu mamaki sukai sose, taya akai har aka sami wannan, Khulaid yace saboda wannan rana yay ƙoƙarin yaga yana bibiyarsu domin samun hujja.

Waziri yay gyaran murya yace, “bisa wannan taƙaitattun hujjoji da kuma shaidu da suka gabata a gaban wannan fada da kuma al’umma, muke fatan kotu zasu saurari irin hukuncin daza’ai ma waɗannan azzalumai, bisa ga cutarwar da suka yima ɗan gatan wannan masarauta wato *SULTAN AYAN* na ɗora masa laifin da baiji ba bai gani ba, sannan kuma suka nemi da suga sun cutar da wannan masarauta domin amsar kujerar mulki d akuma gawar ɗaya daga cikin jakadan da suka kashe”.


STORY CONTINUES BELOW

Mai martaba yace a janye Dameer gefe, su kuma duk a sanya masu ankwa aje a ɗauresu a gidan kaso, zasuyi rayuwa ta tsawon shekara 40 aciki kana a fito dasu.

“kai kuma Dameer kaida kayi kisa to ka sani a muslunci wanda ya kashe a kasheshi, dan haka za’a horaka tsawon shekara guda agidan Yari kana daga bisani a akaita maka abinda ka aikata”.

sannan Waziri yaci gaba da cewa, “bayan yanke hukuncin waɗan nan bayin Allah, yanzu hukunci zai koma kan Raihana bintu Abdullahi wadda tayi mummunan *ƘAZAFI* akan *SULTAN AYAN*, bisa shaida data gabata zamu bi hukunci ta hanyar da Addinin musuluci da shari’a ta tanada ga duk wanda yay *ƘAZAFI* ,kamar yanda Allah maɗaukakin sarki ya faɗa acikin qur’ani mai girma cikin suratul nur aya ta huɗu zuwa biyar, kamar yadda nassi ya tabbatar wanda yay ƙazafi yana da hukunci bulala tamanin, a don haka yanzu za’ai wa wannan yarinya bulala tamanin agaban al’umma domin su zama shaida na cewan an yanke hukunci kamar yanda Ubangiji ya umarta”.

ana gama faɗin haka Raihana ta zube gwiwoyinta ƙasa tana mai kuka sose, zuciyarta take ji tamkar ta fito waje.

sose itama Rahinatu dake jikin Hajiya take kuka, haka zalika Ammi ma kuka take, bazata iya kallon wannan hukunci ba dan haka ta sauke kanta ƙasa kan cinyar Abbi.wata sharfaɗeɗiyar dorina aka shiga laftawa Raihana, tin tana juriya har ta kasa, ihu take zundumawa sose tana roƙon ai mata afuwa, ba’a ƙyaleta ba sai da aka hattama wannan bulala guda tamanin ajikinta, farar rigar uniform ɗin prison dake jikinta duk jini ya ɓata sakamakon fashewar da jikinta yayi. +

bayan an gama mata kotu ta kuma shaida cewan zata tsare Raihana acikin gidan yari na tsawon watanni biyu domin bata horo mai tsanani duba da irin abubuwan data aikata.

daga nan mai martaba yay bayani da kansa akan tsayawa a tabbatar da bincike kamin yanke hukunci, domin ita kanta wannan masarauta a yanzu tana dana sanin abinda ta aikata a baya, domin data tsaya tayi bincike da duk haka bata faru ba


bayan gama gabatarwar bayanai daga bakin mai martaba, aka ɗauka su Sultan’s akai gaba dasu.

gabansu Ammi Raihana ta zube , tana kuka take neman yafiyarsu akan abinda ta aikata masu, sannan ta dawo gaban Rahinatu ta rungumeta tsam jikinta, kuka suke duk su du, roƙonta take da magiya cikin yanayi mai ban tausayi tana cewan ta yafe mata abinda tayi mata na cutarwa.

“na yafe maki 2win sis, dama tin a lokacin dana fahimci ke jinina ce na yafe maki”.

“na gode sose, sannan dan Allah ina roƙon ki tayani neman yafiya wurin mijinki shima ya yafe mani Ƙazafin dana masa, domin na jefe rayuwarsa acikin ƙunci”.

sakin juna sukai Rahinat ta maida kallonta ga Khaleed, harara ta watsa masa, gabansa tayi tattaki taje ta tsaya, da yaran kurmaye take masa magana akan ya yafe ma Raihana.

yanda take bayanin ya daki zuciyarsa, bai san lokacin daya rungumota jikinsa ba yana kaɗa kansa idonsa a runtse.

“duk abinda kike so shi nake so, idan kin yafe mata na yafe mata, kece mai controllng ɗina so you dont have to ask me”.

ya ɗago da fuskarta yana kallo idansa jawur yace, “Angel kiyi magana mana”.

fincikewa tayi taje gaban Raihana dake kallon Khaleed, wadda daka kalli irin kallon da take masa kaga kallo mai cike da soyayya.

murmushi Rahinatu tayi ta kamo hannunta da suke cikin ankwa, takardar data yi rubutu akai ta bata ta karanta.

zaro ido Raihana tayi bayan ta gama karantawa tana duba Rahinatu tna kaɗa mata kai, wannan abu ne da bazai yiwu ba kar muyi haka dake.

abinda ta rubuta mata shine, _daga wannan lokaci na sadaukar maki da soyayyata 2wins, ke mai son Khaleed ce ni kuma ayanzu mai ƙinsa ce, dan haka zuwa lokacin da zaki fito a prison Sultan na nan yana jiranki, Rahinatu na mallaka maki shi ya zama naki har abada._

lokacin da aka ɗiba masu ne ya cika, dakawa da ƴan sanda sukai gaba da ita zuwa gidan kaso.

adu’a akai sarki ya sallami kowa, jama’a duk suka watse, sarki ma ya tashi ya wuce cikin gida, wurin dai ya rage daga su Ammi sai Khaleed.

Khaleed ya nemi kujerar dake kusa da Hajiya ya zauna, kallonsa Hajiya tayi tasa yatsa ta dungure masa kai.

ƴar dariya yayi yace, “sai yaushe zamu wuce?”.

“sirikina na gode maka, kayi ƙoƙari sose da kayi bincike cikin ƙanƙanen lokaci har ka gano kan wannan ƙulallen al’amari, banyi tinanin zan iya ƙyaleka batare dana yi shari’a da kai ba sai sanda ka kirani kake shaida min bayani akan komi, lalle kai mai ƙaunar Rahinatu ne ba maƙiyinta ba, halin da aka sanya ka shi yasa ka tsaneta, yanzu ya kamata mu tashi mu tafi domin na ƙagu Rahinatu ta sami lafiya”.


Hajiya ta kirayi Rahinatu, ta shaidawa su Abbi cewan su zasu wuce egypt aima Rahinatu aikin maƙogaro domin a cire mata wannan abu da suka sanya mata.Uncle Badamasi su Nawwara suka ƙirashi suna kuka akan Antynsu, yace shi ba ruwansa babu wani abu da zaiyi akai.
+

suka kira Abbi suka faɗa masa shima yace bazai taimaki maƙiyiyarsu ba.

jin haka Ammi ta zabari jiki tabi bayansu zuwa asibiti, tana zuwa ta tadda har anma Anty ɗinkin wurin da Raihana ta daɓa mata wuƙa, tana kwamce akan gado tana ta kuka.

Ammi tace wallahi duniya da lahira ta yafe mata, ta manta da faruwar komai, Allah ma muna masa laifi mai girma kuma ya yafe mana.


Anty tayi ta mata godiya.

*2hrs 27mints letter.*

saukar jirgin su Hajiya a ƙasar ta Egypt.

Cleopatra Hospital, shine asibitin da suka wuce domin aima Rahinatu aiki, ba ɓata lokaci aka shiga da ita surgery.

a wanni biyu kacal aka ɗauka likita ya fito yay ma su Hajiya congrat domin an samu nasaran aiki.

da gudu Hajiya ta faɗa ɗakin cike da murna, tana zuwa ta tsaya tana kallon Rahinatu dake dariya, tace, “Hajiyata”.____📖* rungume suke tsam da juna cike da tsantsar farin ciki.
+

Kakus sai tattaɓata take kawa Rahinat ta koma sabuwar halitta.

“Jikalle yanzu dai ina fatan ƙalau kike ko?”.

tana ƙayataccen murmushinta data saba tace, “ehhh Kakus ɗina, sai dai ɗan zafi kaɗan da wuyan nawa ke yi mani amma likitan yace zai warke a hankali idan ina shan magani”.

“to Alhmdl Allah ubangijin girma ya ƙara maki lafiya, wannan yarinya kinsha wuya”.

“ai Kakus aka ce dama bayan wuya sai daɗi, yanzu ba gashi daga ni har Y Raihana’n komi ya wuce mana ba”.

“haka ne kam, itama yanzu tana fitowa a prison zata ɗan-ɗani jin daɗin rayuwar da bata yi ba har ta iya cutar dake akai”.


Rahinat tasa hannu ta danna idonta dan mayar da ƙwallar data taru, ta duba Kakus tace,

“Hajiya na tausayawa Y Raihana halin data tsinci kanta, wai Hajiya har mai muka yima Anty Asma’u a rayuwa da bata son ganinmu cikin farinciki take mana hassada?”.

“to Jikalle koma mene ai a gabanki tayi bayani kuma duk kinji, ba kiga shi Khaleed ɗin mai gaba ɗaya ma so akai a kasheshi shi da iyayensa”.

cikin zuciyarta tace, _to ni ina ruwana da wani Khaleed,can tasu damuwar._

a fili kuma tace,

“Allah ya kyauta kuma ni na yafe mata komai ta mani Allah ya yafe mu baki ɗaya, itama Y Raihana ɗin zance mata ta yafe mata, amma dai Kakus Anty’n tana nan ko, wuƙan da Y Raihana ta daɓa mata bai haifar da wani matsala ba ko?”.

“umm toni ina na sani, ni dama hankalina naga lafiyarki ita ne nake so kuma kin samu yanzu hankalina ya nutsu ya kwanta, komi na farin ciki na zai dawo”.

ta kuma shafo fuskar Rahinatu tace, “yanzu mai kike son ci?”.

“Tsire lafiyayye da kuma fura”.
tai maganan tana ɗaga manyan idonta waje.

“an gama Sarauniya yanzu zaki ci ki ƙoshi kuwa, bari naje na dawo”.

ta kamo hannun Hajiya dake ƙoƙarin miƙewa tace, “sarauniyan wa?”.

“sarauniyan Hajiyanta mana,sarauniyan kuma Abbi da Amminta”.

ƴar dariya tayi ,Hajiya ta miƙe da hanzari ta fita, koda taje ƙofa kallon Khaleed tayi wanda tin ɗazu yake tsaye yana kallon, kai kawai tayi ta girgiza kai ta wuce tana murmushi duba da yanda ya ƙurawa Rahinat ido bako ƙiftawa.

STORY CONTINUES BELOW

Rahinat kuwa na ɗago da idonta ta kalla ƙofa taga Khaleed take tai kicin-kicin da fuska ta ɓata rai.

hakan da tayi ba ƙaramin ƙarawa fuskar tata kyau yayi ba, ajiyar zuciya ya sauke ya zare hannunsa daga cikin aljihun wandon jeans ɗinsa, sannan ya nufeta yana ta fitar da azababben murmushi mai kyau.

yana zama kan gadon gefen kusa da ita tayi saurin kauda fuskarta gefenta.kansa ya ɗan barƙala kana ya kewaya hannunsa ta ƙugunta, a hankali yake kewayawa yanda bazata ji bare tai yunƙurin hanasa, jin saukar hannunsa a shamulokin cikinta yasa tayi wani zillo har tana haɗawa da ƴar shaƙuwa.
+

kwantar da kansa yayi saman kafaɗarta yana goga fuskarsa a hankali.

cikin cool voice nasa yake rera waƙa a hankali hannunsa kuma yana shafa cikinta da wani irin salo.

“Am so lonely broken Angel,am so lonely listen to my heart,you,you are the one i miss so much”.

tsaki ta buga ta ture kansa a kafaɗar tata sannan tasa hannu tai ball da hannunsa dake cikinta.

a ɗan shagwaɓe ya yunƙura zai kuma yin jikinta ta ɓata rai sose ta miƙe zata bar ɗakin yay saurin fizgota ta faɗo jikinsa,gudun karta miƙe ya kewayeta da hannayensa gaba ɗaya a faffaɗan ƙirjinsa.

sai da tasan yanda tayi ta tattaro ƙarfi a kiciniyar da take ta ɓalle hannun nasa ta ƙwace ajikinsa.

“tashi ka fita tinda ba wurin zamanka bane”.

tayi maganar da ƴar ƙaramar muryarta ita alalen dole da faɗa tayi, wani ko ya jita ma ce zai shagwaɓa take bama faɗa ba.

“ka tashi ka ɓace min a waje nace”.

shima kwai-kwayon yanda tayi ɗin yayi yace, “uhmm uhmm idan naƙi fa Angel nah”.

haushi sose ya ƙara bata, tana baƙin cikin wannan sunan da yake kiranta dashi.

“karka sake kirana da wannan stupid name ɗin naka,asalin sunana ma ka faɗi bazan yafe maka ba, kuma nayi niyyar fita na baka wurin amma yanzu na fasa tinda wuri nane ba nake ba, Allah idan baka tashi ka fita ba saina cijeka”.

ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka.

Ya Allah,wani Sonta da ƙaunar ta ne suka ƙara yiwa zuciyarsa dirar mikiya, sai daya lumshe idonsa kamin ya buɗe ya ɗora ƙafafunsa kan gadon,akan pillow ya jingina kansa kana ya naɗe hannayesa a ƙirjinsa, jinsa kusa da ita a zabure ta miƙe ta sauka ƙasa,waigo da kai yayi ya zuba mata narkakkun idanuwansa yana mai jin kawa ya haɗiyeta saboda tsan-tsar ƙaunar da yake mata.

Murmushi yayi yace da ita, “Angel nah mi yasa kike kora na, idan kin koreni a wajen ki ina zani bayan kin san zuciyata bata da kowa sai ke?”.

“tambaya ta ma kake, to oho?”.

ta basa amsar tana galla masa harar tana duban wani gefen.

ganin da gaske dai take da azama ya sauko daga gadon yaje gabanta ya tsaya,duka tausassun hannayenta ya kamo ya sanya cikin ɗumammun nashi.

still fuskarta na kallon wani gefen guda, ta fizge a riƙon ta ɗan ja da baya.

“Hayatee nah kina so na mutu ko?”.

kalaminsa ya sanya tai saurin runtse idonta.

ya sake matsawa gab da ita yasa hannu a haɓarta ya juyo da fuskarta tana facing nashi amma idonta a ƙasa.

“am asking you ki amsa mani, kina so na mutu ko?”.

“zanfi kowa farin ciki idan hakan ya kasance domin kana nema ka addabi rayuwata wanda ni kuma bana so”.kauda kai yayi da sauri, kamar zai mata kuka yace mata, +

“kina so kice min kin daina sona yanzu?”.

tambayar da yayi mata babu shiri ta ɗago manyan idanuwanta masu daɗa narkar masa da zuciya ta watsa masa su.

cikin idonsa take kallo tace, “ai ba daina sonka kaɗai nayi ba, har kai kanka bana so ba kuma na ƙaunar gani da duk wani abu daya dangance ka, Khaleed ko acan baya dana so ka *ƘADDAR SO* ta afka mani, amma a yanzu babu wata ƙaddara makamanciyarta da zata kuma samuna, idan kana tinanin cewar har yanzu ina sonka ko kuma zan so ka anan gaba, to kayi gaggawar farka daga dogon barcin da kake domin abu ne da bazai taɓa yiwu ba, Khaleed ina so na faɗi maka ka daina bibiyata ka barni na buɗe sabon shafi n afara rayuwar soyayya….”.

“dani ba”.
yace da ita yana kallonta cikin ido kaman yanda ita ɗin ma ke kallonsa.

“ko mai kama da kai bana fatan Allah ya ƙara haɗani rayuwa dashi bare kuma kai, kai Khaleed idan baka sani ba yanzu ka sani a duk duniya idan da wani abu da zuciyata ta tsana to ya biyo bayanka, wallahi bana sonka bana sonka ko kaɗan…..”.

sam bai jin zai iya jurema jin sauran kalamanta dake masa zafi cikin zuciya, hakan yasa yay saurin haɗe bakinsa da nata wuri ɗaya,cikin wani salo na daban yake kissing nata.

duk yanda taso ta ƙwace ta kasa har sai da ta samu dabarar da ta danƙara masa cizo a leɓe babu shiri kuwa ya sakar mata baki.

yatsansa yasa yana shafa wurin da har jini ya ɗan fito dan ba ƙaramin cizo tai masa ba.

halshensa yasa yana lasar leɓen nasa daya gama jiƙewa da yawun bakinta, ya shaƙi doguwan iska gami da sauke dogon numfashi kana ya lumshe idonsa ya buɗe yana kallonta yace,

“so sweet more than honey”.

tsukar da tayi har cikin dodon kunnensa, duƙawa tayi ta ɗauka ɗan kwalinta daya saɓule mata, ƙwalla duk ta tarar ma idonta amma dan kar tai kuka a gabansa ta dake, raɓawa tayi ta gabansa tana watsa masa harara mai cike da ban haushi.

kamin ta kai ƙofa taji shi ya rungumota ta baya ya tsamke ta tsam sai faman hura mata iska yake a wuyanta daya saƙalo kansa.

“Hayatee (Rayuwata), ki daina wannan fishin naki dan Allah ban sonsa, in kika ci gaba zaki rasa ni”.

kamin tayi magana Hajiya ta turon ƙofan ta shigo, turus tayi daga inda take ta riƙe haɓa.

“ahhh lalle sannu mara kunyan zamani”.

tace da Khaleed tana kallonsa.

sam ganin Hajiya ko maganan da tayi baisa ya saki Rahinatu ba sai ma ƙara matse jikinsu da yayi yana murmushi.

Hajiya ta cire takalimin dake ƙafarta tayo kansa zata ƙwala masa yay sautin juyar dasu, da sauri Rahinat ta sauke kanta ƙasa dan saura ƙiris akanta.

“sannu fitsararre, ai sai ka bari idan mun bar asibitin kayi iya shegen naka, amma anan ko bani ba likita zai iya shigowa, ba kowa zaka bari da kunya ba sai ita”.

“Hajiya kice ya sake ni”.

“to kaji ka sake ta”.

ya saki Rahinat kans aƙasa yana sosa gashin girarsa.
Hajiya ta harare shi tace, “kamin kayi min abin kunyar daya fi wannan ƙwamma mu tarkata mu tafi tinda dai lafiya take, sai kaje ka mana booking”.

Rahinat tayi tsalle ta dire ta doki ƙafa a ƙasa tace, “Allah Hajiya indai tare dashi zamu tafi sai kuyi tafiyanku ni na taho ko a ƙasa ne”.

zaro ido waje yayi jin abinda tace, ya matsa daga kusa da ita yace da Hajiya,

“manatun amana,ki kula min da ita sose da sose,irin sose ɗin nan fa Hajiyata, zanyi gaba sai kun taho”.

Hajiya ta mangare shi tace, “bazan kula da ita ba ɗin mara kunya”.

yana ƴar dariya ya fice a ɗakin bayan yay ma Rahinat blowing kisss.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]