[Advertisements⬇️]

YAREEMA KHALEED CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

YAREEMA KHALEED


CHAPTER 5

da marwa Anty Asma’u keta faman yi a tsakar ɗakinta duk ta gama jiƙewa da gumi, nadama fal ranta.
+

murɗa handle na ƙofar yasata juyowa a tsorace tana duban mai shigowar.
ganin Hajiya Saddiqa yasata sauke doguwar ajiyar zuciya.

itama Hajiya Saddiqa ganin yanayin ƙawartata yasa tai saurin ƙarasawa wurinta.

“Asma’u lafiya, mai ke faruwa ne naga duk kin fita a hayyacinki haka?”

“hmmm Saddiqa ba dole ki ganni cikin wannan yanayin ba, ai fiye da haka ma zaki sameni, wato sai yanzu na yarda da zancen mutane da suke cewa rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak ta mai kaya…Saddiqa asirina na tsawon shekara ashirin da ɗaya shike neman tonuwa a yanzu”

“ban gane inda zancenki ya dosa ba, fahimtar dani”

“toki gane Saddiqa ba sai najaki da nisa ba, jariryar yarinyar dana sace a asibiti na musanya da gawa ita nake nufi”

“ehhh to miya faru yanzu kuma, ba tana wurinmu ba kuma ai ba wanda yasan da zancen?”

Anty Asma’u ta runtse ido ta buɗe tace, “kina cemin tana wurinku bayan yarinyar ta jima da guduwa daga gidan marayu a lokacin da muka sanar mata da rashin kyautawar da iyayenta suka mata muka dasa mata ƙiyayyarsu cikin ranta, ko kin manta ne Saddiqa?”

“ehh kazalika anyi haka, kin san sha’ani irin wannan dayake faruwa da yawa saika mance da wani…yanzu dai miya faru akan hakan?”

“daren jiya mummunan labari yazo gareni kan cewar ƴarsu Rahinatu data ɓata an tsinceta acan ƙasar libya cikin masarauta kuma tana cikin wani hali ta kasa ƙwatar kanta bisa wata da aka samu mai kama da ita…kai ni ban san ma tayanda zan maki bayani ba Saddiqa saboda ni kaina tashin hankali bai tsaya na maida hankali naji kan zancen ba, ni dai roƙona agareki yanzu ki fiddani daga halin da zan shiga ana gaba bisa wannan SON ZUCIYA dana aikata

Hajiya Saddiqa ta murmusa tare da gyara zama tace,

“na fitar dake ko kuma Allah ya fidda ke Asma’u, ni ai ba kowa bace da zan war-ware maki matsalarki, shawarar zuciyarki kika bi kika aikata Son Ranki dan haka ta inda kika samo shawarar farko ta nan zaki bi yanzu ma kisha kan abinki tin kan yay tsamari ya zame maki ba kyau”

“na shiga uku ni Asma’u”

“ya kike ambaton kin shiga uku, adu’a ai ya kamata kiyi”

“ai inda dubu ma na shiga Saddiqa, wallahi matsawar Alhaji yasan kanin zancen nan abakin aure na sannan kuma nasan Alhaji Abdullahi bazai taɓa barina ba sai nayi zaman prison saboda mutum ne wanda baya barin ta kwana akan ƴaƴansa”

Nawwara dake tsaye kansu da basu san da shigowarta ba tace, “to Anty ke dacan me yakaiki aikata haka?”

“Son Zuciyawa kawai Nawwara da kuma wata manufa tawa, gashi yanzu hakan zaija min nadama ,dama ƙarshen alewa ƙasa, yanzu gashi *NASHIGA HALAKA*(Na Mrs Abdousalam)”

ta fashe da kuka.

“hmmm Anty bakiga komi ba sai Abba yasan komi tukunna yanda dama yake jin haushinki akan yadda baki son ƴaƴan Abie”

“na shiga uku yanzu cikinku bame tayani neman mafita, bame kwantar min da hankali, wallah duk nayi ne saboda kuɗi da kuma baƙin cikin Mardiyya ta sami albarkar ƴaƴa biyu ni kuma bani dasu,anawa tinanin asiri na rufe ashe ƙarshe sai ya tonu wayyoni Asma’u Allah kaɗai gatana sai Babanku yanzu idan na rabu dashi ina zani bayanni ba kowa bace”

“kinga ki saita nutsuwarki sai asan abinyi amma kinata haka wane cikinmu zai sami ƙwarin gwiwar kawo shawara”
Hajiya Saddiqa tace da ita.

“to ya kike ganin za’ai, ni da cene kawai aje a saceta ko kasheta ne ayi wallahi”

“tab lalle Asma’u kin cika mara imani, yanzu banda zaluncin da kikai mata na rabata da gatanta shine yanzu kike kiran akasheta, karki manta fa ke kika saidata matsayin baiwa kika amsa maƙudan kuɗi kuma shine yanzu kike cewa akasheta dan baki da tausayi maimakon ma kice a satota ai mata kurciya…to indai kisa ne nikam badani ba bari kiga ma tashina”da sauri Anty Asma’u ta riƙo hannuɓta tana, “kiyi haƙuri Hajajju duk shawarar da kika bada zan yarda nabi, na daina zancen kisa nidai ki taimakawa aurena da sauran raina”

“ki bari zanje nasa abincika min yanda cikin masarautar yake ,idan ta iya shiga ce ta ɓarauniyar hanya sainasa gogawana su satosu duka ai masu kurciya….amma fa zaki ɓarin kuɗi Asma’u

“wallahi naji ko nawane zan baki indai zaki taimaka min”

“to shikenan baki da matsala akan hakan, amma shi Alhajin da yaushe jirginsu ya tashi?”

“ai suna idar da sallar asuba suka tashi ƙilama yanzu sun sauka sai dai tinda basu san gidanba ba lalle sun isa ba, nidai yanzu kije da sauri ki wani abu akai”

“to bayan kuɗi da zaki bani Asma’u zaki biyani da abu guda akan ƙoƙarin da nai maki, ina so ki bani kanki”

zaro ido Anty Asma’u tai tana kallonta cike da fargaba, “Saddiqa me kika ce?”

“ehhh matsayina na mace ina nemanki idan kin amince dan najima ina sha’awarki”

cikin tsanin tashin hankali Anty Asma’u taiwa Saddiqa nuni da ƙofa tana zaginta.
dariya Saddiqa tayi tace, “lalle kuwa kamin kowa ya toni asirinki ni zan tona maki asiri”

“na shiga Saddiqa karki min haka wallahi bazan iya aikata wannan mummunan saɓon da kike nemana dashi ba,ki tina girman laifin dake ɗauke da haka ki tina lahirarki”

sa kai Saddiqa tai zata fita da sauri Anty Asma’u tasha gabanta tace, “na amince maki…..”

*****

ƙarfe biyu na ƙasar nigeria jirginsu Abie ya sauka a tripoli international airpot Libya.

suna dira Abie yasa aka masa oder ɗin motoci biyu kasancewar shida Uncle Badamasi ne.

da tambaya suka ƙarasa har masarautar ta Libya.

zuwansu bakin gate ƙememe masu tsaro suka ce bazasu shiga ba, rigima ce ta ɓarke tsakanin Abdul da masu tsaron gate ɗin, zaginsu kawai yake yana ambaton azzalumai macuta wallahi matsawar naga abinda ya sami ƴar’uwa wanda bai gamsar dani ba saina bankama masarautar taku wuta.

“ku bani hanya na wuce nace”

ya faɗi cikin ƙaraji inda jijiyoyin kansa duk suka fito sukai raɗau.

duba da haukan da yake tuburan na son ƙusa kai cikin gidan sojan dake tsaye yasa masa binɗiga aka.

dariya yay yace, “harbeni, ka ɓula min kai, an gaya maka ina tsoron wannan abar taku ne, billahillazi indai ka bari aka yanke hukunci baka matsamin na shiga azzalumar masarautar nan ba kamin ka kaini lahira ni zan kaika

inaa hankali Ammi da Suwaiba tashe sukayo kan sojan suna roƙonsa Allah da Annabi yayi haƙuri, dan sun san taurin kan Abdul bazaisa ya haƙura ba.

shiko Abie tsaye yay jingine da mota yama rasa wannan irin tinani zaiyi.

anahaka Uncle Badamasi ya ƙaraso tare da tawagar ƴan sanda.

dukan ƴan sanda a tsorace suke dan sun san wane Shaik Suhail Albanna, zafinsa da kuma kafiya da rashin tsoron kowacce hukuma.sai daifa a zunzurutun maƙudan kuɗin da Uncle Badamasi ya dire masu wanda Abie ya bada yasa su biyoshi tinda bazasu iya ganin banza su ƙyale ba.

“idan har baku da AP da mai martaba to kuwa baku da damar shiga cikin wannan masarauta”

faɗar bafaden dake tsaye daba bakin ƙofa yake ceda ƴan sanda.

kan suyi wata magana wayar Abie tai ƙara inda numbar Sultan Raihan ta shigo.

ɗagawa Abie yay suka gaisa yace da Abie, “Abie up to now baku ƙaraso bane? maimartaba fa na neman yanke hukunci ayau wanda zai yanke hukuncin ɗaurin rai da rai ga Rahinatu”

dakiya kawai Abie yay ya basa amsa amma zuciyarsa har saida ta harbawa saboda fargaba.

“Raihan ka ganmu kusan rabin awa bakin masarautarku amma an hanamu shigowa munata fama da masu tsaro saboda sarki baisan da zuwanmu ba”

“oak,oak bari nai magana azo ashigo daku, naji daɗin wannan zancen

nan take ya aika saƙo daga system ɗinsa zuwa ta masu tsaron gida.

saƙon na isa garesu da hanzari aka wangamewa su Abie gate suka nausa motacinsu ciki yayin da ƴan sanda kuma suka juya.

Raihan ya bada umarnin a shigo dasu sashensa, koda suka shiga dukansu a ƙagauce suke da sukaga ƴarsu banda ma Abdul daya kasa zaune yay tsaye sai waige-waige yake dan gani yake ma shi kamar gidan tsafi ne nan ɗin duk da cewar yana shiga ƙasashe yana ganin dandatsa² gininsu amma wannan yasha ban-ban danasu.

Ammi kuwa gogar ƙwalla kawai take dan ta matsu taga ɗiyarta.

da faɗa yake ceda Raihan, “kai dalla malami karka tsaya ɓata mana lokaci ina ƴar’uwarmu take?”

Abie ya tsawatar masa yace, “kabi komi a hankali mana Abdul,Raihan ba mutumin da zai cutar damu bane dan sai dana bi diddigi nai bincike akansa tukunna ma na yarda da zancensa wanda shima bai san da haka ba”

Raihan yay mirmushi yace da Abie, “ai bakai laifi ba Abie,hakan da kai yayi kyau saboda ba kowane abin yarda ba a rayuwar yanzu dan gaskiya tayi ƙaranci”

Ammi tace, “hakane ranka ya daɗe, mu ai ba abinda zamuce dakai sai dai fatan alkhairi ga rayuwarka da kuma sarautarka Allah ya baka ikon riƙeta bisa gaskiya da amana”

ya amsa da ameen ya dubi Abie yace, “Abie dan Allah ku ɗan ƙara haƙuri saboda saina aika da takardar saƙon zuwanku ga maimartaba tukunna zaku sami daman shiga”

Abie yace, “to amma baza dai a aikata komai ga ƴata ba har zuwa lokacin ba ko?”

yace, “ehhh insha’Allahu dan ina saka ran ya buɗe takardar tawa batare da ɓata lokaci ba ,kuma suma su Rahinatu ɗin ba’a fito dasu ba tukunna”

****
zaune Khaleed yake cikin ɗakin tsaron da aka bada umarnin tsaresa har zuwa ranar hukunci.

gefensa na dama mutum biyu ne hagu kuma ɗaya zube da gwiwoyinsu ƙasa fuskokinsu ɗaure da baƙin ƙyalle an ɗaure hannayensu ta baya, koya suka motsa za’a zabga masu lafceciyar bulalar dake hannun dakawan sojojin dake tsaye kansu banda wanda keta gefen hagun Khaleed.

ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yay ya kuma ɗora kansa bisa hannayensa ta baya yana lilo da kujerar da yake zaune akai idonsa a rufe.

da sauri mai isar da saƙo ya shigo da sauri dan isarma da Khaleed saƙo.

“Allah yaja zamanin Sultan Aayan, mai martaba ya bada umarnin a shiga da masu laifi domin yanke masu hukunci yanzu bada jimawa ba”

wani mugun bugawa zuciyar Aayan tayi saboda tsoron yanda zaiga Angel ɗinsa.

sai daya ɗau lokaci kamin ya buɗa baki yace a kunna masa saitin CC dake cikin fada.

nan da nan suka aikata umarnin daya bada, tar saiga abinda ke wakana ta cikin fada duk ya bayyana aciki.

zaman ƙasaitarsa ya gyara yay ma TV ɗin ƙuri yana kallo.
a tare aka shigo dasu Raihana,duk da kowaccensu fuskarta rufe take amma Khaleed na kallon Rahinat ya ganeta.

tsinkayar zuciyarsa yay da yin wani irin zafi,da sauri ya runtse idonsa kamin ya bada umarnin a kuncewa waɗan nan dake tsare wurinsa fuska.

ana kuncesu dukka suka sauke numfashi suna shaƙar iska.ɗaya bayan ɗaya ya dubi Khulaid,Sha’aban da kuma Sultan Dameer.

sabon zama ya gyara lokacin da aka kuncema su Rahinat fuskokinsu.

cikin idon Rahinat yabi da kallo wanda tsabar kumburin da galabaitar da sukai harda taruwar jini acikinsu

yana huci ya juyo gefen hagunsa da Sultan Dameer yake yace, “ni kaina ban san wannan irin hukunci zan yanke agareka ba shugaban azzaluman duniya yayin da Angel ta bani umarnin hukuntaku… in amai maka albishir Kawuna daka shiryama baƙuntar lahira nan bada jimawa ba dan bazaka ga sarautar ɗanka ba”

jin ƙarar ihu ta cikin TV yay saurin ɗago da kansa ya maida hankalinsa kai.
Raihana ce aka zabgama wata lafceciyar bulala a baya ana tambayarta wace ita.

itako Rahinatu idonta runtse yake tana jiran a zabga mata bulalar datai sabo da ita zuwa wannan lokaci.

an ɗaga za’a zabga mata Khaleed ya miƙe da sauri yana, “انتظر”
inaa ba’asanma yanai ba da iyaka ƙarfi aka labtawa Rahinat wanda har yasa buɗe baki tai ihu sai dai ba sauti.

take kuwa shima ya bada umarnin cewar a labtawa Sultan Dameer guda goma idan kuma har yay ihu su fille masa kai.

“kai Aayan ni wan mahaifin naka kake bada umarnin a sarewa kai”

“hukuncin daka can-canta dashi kenan, zaima fi kyau ni da kaina na yanke maka akan maimartaba yasan abinda ka aikata…da ace zaluncinka bai shafi matata ba to da babu ruwana da taking any revange akanku matsawar an wankeni daga laifin da ban aikata ba, amma sai kukai gangancin saka matata farincikin rayuwata acikin hatsabibancinku babban kuskuren da kuka tafka kenan wanda ni kuma i cant spare you anymore i must purnish you at anycost”

cikin tsawa ya bawa sojan kusa dashi umarnin yay ta laftarsa.
haka aka dinga zabgama Sultan Dameer bulala tin yana ihu yaga azabar ba ƙarma bace ya san yadda yay ya toshe ƙarar bakinsa daga cikinsa tukunna aka ƙyalesa.

bisa shigowar Sultan Raihan cikin fada maimartaba ya bada izinin a dakata da dukansu Raihana tukunna zasuyi magana da Mai jiran gado.

duk da sarki bai gamsu da saƙon Raihan ba amma sai yace ya yarje su Abie su shigo.
shigowarsu Ammi ta ƙarasa wurin ƴarta da sauri, tana zuwa taga halitta biyu gabanta babu ban-bancin koda ɗigo atare dashi zubin kukansu ma iri guda ai a tsorace taja da baya tana salati.

shima Abie daya ƙaraso wurin sai daya firgita, ja yay d baya bakinsa buɗe cike da tsan-tsar mamaki da al’ajabi da kuma ruɗu.

nunasu yake duk su biyun yana kiran sunan Ammi, “Sa’adatu wacce Rahinatu aciki?”

“bazan iya ban-bancewa ba kamannin sunyi yawa, sai dai ina jin wani abu atattare da hakan Abdullahi”

Khaleed dake kallon abinda ke wakana da mamakinsa yake kallon Abie,taya akai suka zo nan dan yasan Abie sai dai bai san Ammi ba.

yanda ya gansu duka a tsorace yay ƴar dariya, “ni ɗaya zan iya tantance RAYUWATA”

gabansu Ammi ta zube ƙafafunta ta ɗaga hannayenta tace, “Allahn daya halicceku yay maku kamanni iri guda shi ɗaya zai iya tan-tanceku dan ni kaina bazan iya fidda ƴar dana haifa da cikina ba kuma na rayu da ita tsawon shekara ashirin ba acikinku…amma na roƙeki baiwar Allah, ki ƙyale min ƴata ki bayyanar da asalin kanki karki mutu da hakki da yawa akanki…. dan soyayyarki da fiyayyan halitta ki barmin rayuwa ƴar ki tausayawa ƴa da uwarta ki barta taci gaba da jin daɗin iyayenta ta mutu cikin gatanta”

runtse ido Raihana tayi wasu zafafan hawaye na zubowa daga idanuwanta, tausayin kanta takeyi,yau gata ga iyayenta amma bata gatan da zasu kirata ƴarsu,a saboda Rahinat gata zube a ƙasa tana roƙon ƴar cikinta har tana hawaye, ashe dama haka iyaye suke da daɗi….ɓangaren Rahinat ma ido ta runtse tana zubda zafafan hawaye,so take tai magana amma ba dama, jin hawayen Ammi take har cikin ƙashin zuciyarta.

a tare suka buɗe ido suka sauke kan Ammi suna kallonta,kowacce motsa baki take tana son tai magana amma ta kasa, ɓangaren Rahinat saboda rashin baki ta kasa samun wannna damar amma ɓangaren Raihana zafin da zuciyarta keyi yasa bazata iya cewa komi ba.

“innalillahi wa’inna ilahi raji’un” shine abinda Abie yace.
“yanzu duk gatan da kike dashi Rahinatu kece acikin wannan halin, kiyi ƙoƙari ki nuna mana kanki dan Allah, bazamu iya jurar ganinki cikin wannan halin ba, sanin kanki kin san irin zazzafar soyayyar da muke maki, ki tausayawa zuciyoyinmu da kamuwa da ciwo ki wani motsi da zamu gane”

tana jin haka ta shiga gilu-gilu da kanta tana kallon Abie, tsorata kowa ya ƙarayi sboda duk abinda ɗaya tayi sai ɗaya tayi.

_bazan barki ke ɗaya kiji daɗin rayuwa ba Rahinat, matsawar basu suka ganemu ba to wallahi sai dai komi zai faru ya faru amma bazan barki kita jin daɗin iayayenmu ke ɗaya ba banda ni._

****
wani gigitaccen mari Khaleed ya zubewa Khulaid a fuska,damƙar kwalar rigarsa yay ya shaƙi wuyansa a tsawace yace,

“ka faɗa min mai kukaiwa Angel ta daina magana”?????…..___📖* yanda Ammi ke tsugunne tana kuka haiƙan sai daya taɓa zuciyar duk wani mutum dake a wurin.
+

Ace ƴar data haifa da cikinta ta raine ta tsawon shekaru 20 amma yau ta kasa gane ta koda da wata alama.

_ya ubangiji ina roƙonka daka bani ikon cinye wannan jarabawa taka._

ta kuma ɗago kai ta zuba ma duk su biyun ido, koda za’a ɗora mata wuƙa a maƙogaro sai dai a feɗeta amma bazata taɓa iya cewa ga Rahinat ba.

miƙewa tsaye tayi taje gaban mai martaba ta zube gwiwoyinta gami da haɗe hannayen ta tana roƙonsa.

“dan Allah ina roƙon wannan masarauta data yi haƙuri karta zartar da hukunci, tayi yafiya akan abinda ya faru….”

“babu yafiya a game da hakan domin ƴarki ta aikata babban kuskure wa wannan masarauta… taci zarafin Yarima a ranar da ake ƙoƙarin ɗora masa rawanin sarauta, sannan ta kuma kasancewa ɗaya daga cikin masu son ganin bayan wannan masarauta, to a dan haka zamu yanke mata hukunci gwargwadon abinda ta aikata, ta hanyar da addinin musulunci ya tanadar mana……”

bai ƙarasa faɗin abinda zaice ba ya dakatar da maganarsa sakamakon ganin Khaleed ya shigo a fusace sannan fuskarsa da sigar fad’a acikinta.

idon kowa ya koma kansa dan ganin mizai faru,saboda yanda yake huci ya kuma nufi inda su Raihana suke.

“kai…..”
Mai martaba ya faɗi amma sauran zancen nasa ya tsaya sakamakon ganin abinda Khaleed ya aikata.

mugun kallo ya watsa wa masu tsaron dake tare da Rahinat su biyu, ba shiri kuwa suka saketa dan ayanda yake ɗin nan zai iya wanzar da komi akansu.

igiyar dake ƙulle da hannun Rahinat ya warware ya janyota jikinsa, ɓangare ɗaya kuma yasa hannu ya ɗago da fuskar Raihana ya sheƙe ta da zazzafan marin daya birkita mata lissafi lokaci ɗaya.

a gigice ta ɗago dara-daran manyan idanuwanta da Allah yayi ta dasu tana kallonsa yayin da wasu hawaye masu zafin gaske ke sakko mata a kunci.

zai ƙara mata wani Marin, zuwan Raihan wurin ya dakatar dashi, da mugun kallo yake kallon Raihan ɗin kamin ya nuna sa da d’an yatsa yace dashi,

“idan har kayi gigin taɓa mani mata a wannan karan, billahil-azeem sai na datse maka hannu, ba muharramarka bace dan haka ka nisanta da ita tin wuri”

Raihan ya duba Rahinat da tai wurƙi-wurƙi da idanuwa tana sake maƙalewa jikin Khaleed saboda ta gama jure irin azabar da ake gana mata, ta ko wanne hali mafita take nema ayanzu tunda taga wannan mai kama da ita ɗin tantagariyar mara imani ce.

shi kansa Raihan ɗin ya kalleta ne bawai dan ya shaidata ba, maganar da Khaleed Yayi ne kawai yasa yake kokonton ko itace.

cikin izza da jin sarauta shima Raihan ɗin yace da Aayan, “taya zaka kirata matarka, wacce ƙwaƙwƙwarar shaida ce da kai akan hakan munafiki azzalumi”

Khaleed yace dashi, “banda lokacin ka at this time Sultan Raihan, amma ka jirani zuwa lokacin da zan gama ɗaukar fansa akan zaluncin da akayi wa matata”

tsoki Raihan ya buga, ya kamata yayi wani abu tin kamin Khaleed ya kuma wargaza lissafin da yayi, ya duba Raihana ya duba Rahinat haka yake, gaba ɗaya abin ma tsoro yake neman bashi. Don kamanin fa yaran nan sai Allan daya haliccesu, wani tunani yayi ya ƙarasa wurin Raihana yace da masu tsaronta,”ku saketa.”yana da tabbacin itace Rahinat dan yasan Khaleed bai san komi akai ba, so wadda ke hannunsa itace ƴar basaja.

ita kuwa Raihana ganin haka zuciyarta tayi wasai tunda ga wata damar ta samu.

“Rahinat ko?”
Yayi zancen a saitin kunnenta ta yanda ba wanda yaji mi yace.

sai data kalla Rahinat ta wutsiyar ido cikin ranta tace, _”har yanzu twins kashinki bai gama bushewa ba, tunda ganina ma baisa azzaluman iyayena sun tuna da ƙazamin abinda suka aikata ba”._

kana ta ɗaga ido ta kalla Raihan ta ɗaga masa kai alamar itace.

Rahinat na ganin hakan ta fara kiciniyar ƙwacewa a hannun Khaleed daya wani riƙeta gam.

so take Raihan ya juyo ya kalleta ta shaida masa ba ita bace ita gata anan amma ina hankalinsa Yayi can yana warwarewa Raihana ɗaurin igiyar da akayi mata.

hannu Khaleed yasa ya kamo fuskarta ya juyo da ita gareshi.

wani walaƙantaccen kallo tayi masa kana ta wurga masa banzar harara, sarai tasan badan yasan ita bace yazo ya cece ta sai dan tunaninshi yana bashi waccen muguwarce.

dukan al’amarin dake faruwa ya bama jama’ar wurin mamaki.

jan hannun Rahinat Yayi da sauri ya ƙarasa wurin Raihana, dai-dai lokacin kuma da aka shigo dasu Sultan Dameer fuskoki duk a ɗaure da baƙin abu kowa an sanya masa bindiga aka.

mai martaba ya miƙe tsaye zaiyi magana amma zancen daya ji Khaleed nayi ya kuma tsaida maganarsa.

da hannu Khaleed ke nuna Raihana yace da ita, ” nasan baki san ko su wane waɗan nan ba, amma idan har kika bari suka faɗi gaskiyar lamari daga bakinsu, to ba makawa saina sanya an datse maki ƙafa da hannu”

ba shakka ta tsorata da jin zancensa dan haka zuciyarta ta shiga tunanin abinda ya kamata data aikata, ita ta gama ƙudurar bazata taɓa faɗin gaskiya ba kuma bazata yarda a ganesu ba har sai iyayenta sun tuna ƙazamin aikin da suka aikata a baya, amma har yanzu sun gaza hakan saima ido kawai da suka baza suna kallon abin al’ajabin dake faruwa.

wawayen marikan da Khaleed ya sake zube mata a fuska wanda suka gigita ta tare da ɗaukewar jinta na wucin gadi, zai ƙara mata Raihan ya riƙe hannunsa, a kiɗime ita kuma ta ɗago ta buɗa baki tace,

“karka sake marina Sultan, karka kuma marina dan nan gaba bazan yarda ba saina ɗauki fansa, ka barni naji da raɗaɗin da zuciyata kemin mana”

“innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”
shine kalmar da Ammi,Abie da Yaya Abdul suka faɗi a tare.

“kenan da gaske Rahinat ce ta aikata abinda ake zargi na ganin bayan masarauta da kuma yin ƙazafi, to taya hakan ta kasance kenan? har ayaushe ta sami damar shigowa ƙasar libya ta aikata wannan ta’asar”

abinda ya fito daga bakin Suwaiba lokacin data ɗora ido kan Raihana tana kallonta.

“banyi tunanin bayan bijirewa maganata da Rahinatu tayi ba again kuma tarbiyar da muka bata ta gurɓace ba sai ayau”
Abie ke wannn maganar yana sharce gumin daya keto masa.

“Allah Yayi wadaran……”
Ammi da tai mutuwar tsaye tin ɗazu tai saurin katse maganar Abie.

“yasalam, haba Abdullahi mikake shirin aikatawa ne, kaida zaka nema mata shiriya kuma sai kayi mata baki ta ƙara lalacewa, kar kayi haka, ka barta da iya rayuwar wahalar data gani ma ta isheta ta hankalta”

Uncle Badamasi dake tsaye yana nazari yace, “nifa har yanzu ina da shakku akan yarinyar nan, anya Rahinatun mu zata iya aikata wannan ƙazamin aikin, karmu manta bafa irin tarbiyar da muka bata ba kenan, sannan ko mun manta komi karmu manta wacece ita, yarinya dako yatsa aka sanya mata ga baki cizawa ke mata wuya”

“mai Yayi saura wanda kake son kaga hujja Badamasi banda muryarta daka ji a yanzu, ga sautin ta nan rangaɗaɗau kana zancen cewa kana da tantama”

gadan-gadan Abie Yayi kan Raihana ransa da ruhinsa a matuƙar ɓace, kan ya ɗauketa da mari ta fashe da sabon kuka inda ta rissinar da kai ƙasa.

kamar Abie zai kuka cikin rawar murya yace, “Rahinatu kin cuci kanki domin kuwa bamu kika cuta ba tunda har a wurin Allah mun fita haƙƙinki wurin baki ingantacciyar tarbiya, miyasa kika aikata haka Rahinatu, har ayaushe hakan ta faru ba tare da saninmu ba, yanzu a dalilin haka ga Kakarki can kwance agadon asibit “Abie ba Rahinatu bace kaman yanda kuke tinani ,ni dabance, ba kowa bace ni face baiwa mara gata mara galihu, Rahinatu nada gata ni kuma banda shi domin banda maraba da tsintacciyar mage”
+

ta ɗaga yatsa tayi masu nuni da Rahinat kan tace, “waccen itace Rahinat ni kuma ƴar uwar Rahinat, Abie nima ƴar kuce tamkar Rahinat sai dai ni ban sami soyayya da gata daga wurinku ba matsayinku na mahaifana, Sunana Raihana Abdullahi Matawalle kaman yanda take Rahinat Abdullahi Matawalle…..”

aiba Abie dasu Ammi kaɗai ba, shi kansa gogan gayyar Khaleed sai daya girgiza banda Rahinat da Suwaiba da sukai suman tsaye.

Maimartaba daya gaji da kallon shirmen da ake masa yace, “ku dakata gaba ɗayanku, mun shigo cikin kotun wannan fada ne domin yankewa mai laifi hukunci badan kallon wasan kwai-kwayo ba, ya kamata ku shiga nutsuwarku kusan a inda kuke”

Raihana ta dubi Maimartaba tace, “ranka ya daɗe kamin a yanke hukunci agareni, ina neman alfarmar wannan kotun masarauta data bani dama na fara sanar dani ɗin wacece, in yaso daga nan ko jefeni ne sai ayi”

Sultan Raihan shiya bama Maimartaba baki har ya aminta da hakan.

ta saki guntun murmushin yaƙe mai ɗauke da takaici taci gaba da cewa,

“nasa ku cikin ruɗani ko iyayena, karku damu zaku fita daga duhun da kuke tunanin na sanyaku ciki yanzun nan in har baku manta shekaru ashirin baya ba” ,

ta sauke numfashi sannan taci gaba,
” safiyar ranar asabar 9/8/1999 da misalin ƙarfe 9, acikin asibitin gamkalley clinic niamey, Allah ya azurtaku da samun haihuwar tagwaye biyu mata a lokaci ɗaya, amma saboda rashin godia da imani irin naku kukayi butulci agareshi, Ammi kika manta da rainon cikin da kikai tsawon watanni goma atare dake, saboda kawai son abin duniya wanda bai taka kara ya karya ba” ,

“nice ɗayar jaririyar ƴarku da kuka saida akan ƙalilan ɗin kuɗi naira dubu ɗari biyu…..”^^^^^^^^^^^^^^

_Tofa Yau Akeyinta,Fire on The Mountain😂, kosu Ammi zasu iya tina wannan rana da Raihana ta karanto masu🤔..

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]