[Advertisements⬇️]

YAREEMA KHALEED CHAPTER 4 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

YAREEMA KHALEED

CHAPTER 4

••••• firgigit Raihana ta dawo daga dogon tinanin data tafi wanda tayi tin a lokacin data ga mutuwar Khulaid a TV.

yanda ta haɗa zufa kace damben gaske tayi ba tinani ba, Khalid dake gefenta ta kalla wanda ke cikin tsantsar mamaki,al’ajabi da kuma ɗarsuwar firgici a zuciyarsa.

dogon numfashi ta sauke wanda ya sanya Khalid dawowa daga tinaninsa yana kallonta.

hannunta ta maƙale da nasa, zufa kawai take haɗawa domin tabbas idan har asiri ya tonu ayanzu to kashinta ya bushe.

duk da jarumtar da yake tare da ita amma hakan bai sashi jin tsoro a cikin zuciyarsa ba domin gani yake tamkar aljanu ne suka buɗe masa ido.

ta gefen ido guda Raihana ke kallon Rahinat dake duban tv tana goge hawaye.

itama sai yanzu ta maida baki ɗayan hankalinta kan Tv ɗin dan sake tabbatar da mutuwar Khulaid shin gaske ce.

ganin gaskiyar lamari duk sai jikinta ya mutu, take tausayin bawan Allahn ya kamata saboda sadaukarwar da yay akanta.

amma taya akai hakan ta kasance? amsar da bata da wanda zai bata ita sai dai kuma idan har ta gano cewan su Sultana Yasmeen ne sila to itama sai taga bayansu.

jitai Khaleed ya kama hannunta ita da Nimrah sun wuce zuwa room ɗinsu, suna tafe Rahinat na bin bayansu da kallo har sukai cikim ɗakin.

baki ɗaya Rahinat acikin tashin hanƙali take, ita bata damu da baƙin mugun mijin da ƘADDARAR SO ta haɗasu ba, babban burinta wannan baƙar azzalumar da take basaja matsayin ita ta fitar da ita daga wannan mawuyacin halin data jefata.

ko yanzu a wanna hali mahaifanta ke ciki oho gashi bata da wayar kiransu idanma ta samu to da wannan bakin zatai masu magana bayan azzaluma mai kmaa da ita sun nakasa ta.

Ammi,Abbi da Hajiyanta kawai ta tina ta sake fashewa da kuka.yanzu taya zata koma garesu bayan bata da kuɗin jirgi bata da hanyar komawa nigeria tinda bata san ko’ina ba.

jin saukar hannun Raihan tayi akan nata, da sauri ta zame tana kaɗa masa kai.

yatsunsa ya sanya ga kumatunsa ya motsa wanda yay mata nuni datai murmushi.

tana kallonsa ta ɗan murmusa sannan ta haɗa hannayenta biyu tai masa godia, ta juya zata tafi yasha gabanta yace,

“dan nabiyurrahmati ki tsaya”dakatawa tayi da tafi ta ɗaga masa hannu alaman mi zaka mani

“kince baki san inda kike ba, to yanzu idan kin tafi ina zaki?”

murmushin tai wanda ya taho tare da hawaye ta kuma bashi amsa da hannu “nima ban sani ba”

ya juya ya kalla room ɗin dasu Raihana suka shiga, “kin san wadda naga kina nunawa ɗazu ne ,wannan mai kama dake ɗin?”

tai saurin kaɗa masa kai alaman a’a saboda bata son ya shigo rayuwarta ya rasa ransa shima kaman yanda Khulaid ya rasa nasa a garin taimakonta.

“cikin su ukun duk ba wanda kika sani?”

ta sake ɗaga masa kai. yace, “oak to shikenan, amma idan ba damuwa kizo muje gidana mana ki zauna kamin Allah ya baki lafiya”

ta girgiza masa gami da haɗa hannayenta mai nuna alamun godia sannan tasa ƙafa ta wuce.

tsaye yayi yabi bayan poor girl ɗin da kallo cike da tausayawa, shin ko mike damunta oho?

kai bazai iya barinta ta tafi haka ba dan haka da sauri yabita, gabanta yasha ya dinƙa mata magiyan dan Allah ta barshi ya sami ladan taimakon wallahi bazai cutar da ita ba in kuma hakan ta kasance Allah yay mata sakayya tin aduniya kamin aje ga lahira.

biro da takarda daya miƙo mata ta rubuta masa, _bawai taimakonka ne bana so ba saboda fuskanka bai kama dana mugwayen mutane ba, da zaka cutar dani bama zaka kawo ni a asibiti ba domin aceci raina ba…kawai dai ina guje maka shiga wani hali ne ata dalilina saboda duk wanda ya kasance tare dani da sunan taimako mutuwa yake, kayi haƙuri na gode da iyaka taimakon da kayi mani Allah ya biyaka da gidan aljanna._

sose kalamanta suka ƙara sawa yaji wani mugun tausayinta ya sake kamashi, har ƙasa ya zube ƙafafunsa ya hau mata magiya har saida ta amince.

sanyi yaji ya ratsa zuciyarsa saboda bayan taimakonta da yake sonyi kuma akwai sonta tin na wasu watanni a zuciyarsa wanda yake ganin idan har babu ita a rayuwarsa to ba lallai yaci gaba da rayuwa cikin jin daɗi ba.

“na gode sose da kika amince kuma ina roƙon Allah ya fitar dake daga cikin ƙangin rayuwar nan da kike ciki…yanzu mu koma ciki mu amsa magunguna dan likita yace akwai drugs ɗin da zai ɗoraki akai”

binsa tayi suka koma ciki duk data dameshi daya faɗa mata me akace yana damunta amma yaƙi, ahi kansa bazai iya ba saboda in har ya faɗa mata zai kuma iya haifar mata da wata matsala

murmushi Rahinat taƴi cikin ranta take cewan, _nasan dai bazai wuce hawan jini ba ko ciwon zuciya…ni kaina in akace banda ɗaya daga ciki to akwai ayar tambaya akaina dan ko kewan mahaifana ma kaɗai ya isa ya haddasa min wani ciwo bare wannan ƙangin rayuwan dana shiga_.

****

kan gado ya zaunar da ita yana shafa bayanta a hankali.

bazata can ƙasa da mura taji yace da ita, ” are you 2wins?”

bum gabanta ya faɗi, _na shiga uku kar asiri na ya tonu, idan Yarima ya gane wace ni wallahi na gama kaɗewa._

ganin tai tsiru tana kallon gaban rigarsa da alamu na tsoro ya talbi fuskanta tare da cewan,

“what happen Angel?”

fashewa tayi da kuka ta faɗa jikinsa ta ƙan-ƙamesa.

sumar gashin kanta yake shafawa yana lallashinta, “minene kuma?”

“ban santa ba tsoronta nike ji”

“to is oak daina kukan”

ta girgiza kai, “nidai kasa a ɗauketa ko kuma mu tafi mu bar garin..kullum fa saita bani tsoro a mafarkina”

kai ya ɗaga mata kawai sannan ya miƙe ya fita a ɗakin tare da cema Nimrah ta kula da ita.

fitowansa ya dinƙa waigen ko zaiga su Rahinat amma baiga ko ƙyallinsu ba.ba.

+

tambayar Dr incharge yay yake sanar masa yanzu aka sallamesu sun tafi.

da sauri Khaleed ya fice, dai² da ƙarasawan fitansa dai² da zagayowan Raihan daga rufema Rahinat ƙofa.

a dabarance ya ɗaga cameran wayan dake hannunsa ya ɗauki Raihan hoto, har lokacin da Raihan ya fice daga asibitin bai bar kallon numbar motan ba daga nan ya fuskanci ta nigeria ce..

zooming pix ɗin yayi ya kalla sose sannan yay backward yay zooming ɗin gefen fuskan Rahinat daya ɗauka ta cikin window wanda bai fito clearly ba.

zuwa ga wata numba ya tura komi sannan ya nemi da akawo masa kujera.

zama yayi ya shiga online Libya TV talk,abinda ya fahimta a ɗazun ya ɗauke hankalin mutum biyun shi ya shiga yay search.

shiru yay bayan daya gama kalla,tinaninsa ya tafi akan to mine alaƙar Angel ɗinsa da wannan mutumin har fuskarta ta bayyanar da tashin haƙali da ganin gawarsa.

tinani na biyu daya fara wancen mai kama da Angel daya gani ita kuma wace daga ina take kuma itama mine alaƙanta da mutumin da yaga har ta zubda hawaye akan gawansa?

ya jima sose yana ta nazarin abubuwa da dama har tinkararsa da Raihan yay da neman faɗa that means kenan ya taɓa saninsa amma shi bai sansa ba.

lalle ya zama dole yay bincike akan yarinyar nan dake neman firgitar masa da Angel,in har ba aljana bace to haƙƙun bazasu rasa nasaba da juna ba domin kallon da ya ƙare masu tsab ya nuna masa da kama ta jini a tsakaninsu tinda baiga ɗaya daga cikinsu da kofato ba.

kansa ya jingina akan rocking chair ɗin da yake zaune akai.idonsa a lumshe yake tinanin kamin wani baƙon al’amari ya danno kai ya kamata ya san asalin Angel ɗinsa kan su Abie suyi nasarar cin wasan da yake ganin kaman tsarawarsu ne akan halitta biyun da yagani a yanzu.

dan yana da tabbacin dan su rabashi da ita suka haɗa wannan plastic surgery ɗin.

ya jima nan zaune har lokacin idonsa a lumshe kiran da Nimrah ta masa ya sanya sa buɗe ido ya saukesu akanta.

“Khoyaa Sister inlaw na son ganinka”

a saraucensa ya ɗaga mata kai da nuna alaman he is coming.

shigansa ɗakin a zaune ya tadda Raihana kishingiɗe da pillow fuskanta ɗauke da damuwa.

gefenta ya zauna yana dubanta kamin ya miƙa hannu ya kama nata ya sanya nasa ciki.

a hankali ta buɗe ido ta zubesu kan halittarsa da kullum ke daɗa rikita mata lissafi wanda take adu’an kullum ya zama mallakinta.

kukan shagwaɓa zata fara ya tsaidata da faɗin, “mu bar nan ko?”

kai da ɗaga masa na alaman, “ehhh”

“zamu tafi amma ki fara bani amsan tambayan da zan maki kinji”

ta gyaɗa masa kai kawai.

“Angel taya akai kika shigo cikin bayin masarautarmu?”

“Yarima na ka manta da tarihina plss bana son tina baya”…..

“just tell me”

ya katseta cikin tsawa.

ido tap da hawayen dake neman gangarowa take kallonsa, duk da tarihinta abin atausaya mata ne amma bazai yiwu ta bashi asalin tarihin rayuwarta ba in har ba iyayenta ne suka nemeta ba to babu wanda zai sna asalinta.

kan tayi wata magana aka buɗe ƙofa wanda sallamar da sukaji ya ɗauki hankalinsu.

Khaleed bai miƙe ba yaci gaba da zamansa amm akansa sunkuye a ƙasa.

Mami ta ƙaraso inda yake zaunen tace dashi, “Aayan lalle so ya rufe maka ido ka manta wace ni a wurinka tinda har ina kiranka kaƙi amsa kirana saboda kana tare da azzaluma wadda ta jefa rayuwarka acikin ƙunci ko”ba haka bane Mami, plss you should just forget about the past, ta rigada tayi kuskure kuma ta tuba sannan nida tayiwa na yafe mata…..”

tas Mami ta sauke masa mari a fuska, “idan kai ka yafe mata toni ban yafe mata ba saboda itace silar rabani da mijina da muke matuƙar sƙn junanmu, ta kuma gurɓanantar da rayuwr ɗana, ta rabasa da mahaifinsa…toni ban yafe mata kuma akan hakan ne zan ɗaukaka ƙararta”

taja numfashi kamin tace, “sannan idan har ka maida igiyar auren dake tsakaninka da ita Aayan to zan tsine maka kuma ni ba uwarka bace sai dai ka nemi wata uwar…..”

bata kai ga idda abinda zatace ba baiwar dake tare da ita ta ɗaga wayanta da aka kira ta miƙo mata.

ganin sunan Abie tai saurin karawa a kunnenta tayi sallama wadda da kaji kasan tana ɗauke da tsan-tsar ɓacin rai.

“Su hana ki dawo yanzu ga yarinyar ta dawo sai dai basa tare da wuldi…shi ki ƙyalesa duk inda yake ma zai dawo ne indai yasan ta dawo garemu tinda ya fifitata akanmu”

tinda Abie ya fara maganar wai tazo ga yarinyar ta dawo Mami ta saki baki da ware idanuwa ne.

jin shirunta Abie ya katseta tinanin da take da faɗin, “Suhana bakiji nane”

“ina jinka Abu Aayan, sai dai zancen naka ne ke neman sani a ruɗani”

“kaman ya kenan?”

“ehhh to aini na gama shiga ruɗu kuma, bari dai gamu nan zuwa in mun iso ma fahimtar da juna baki ɗaya”

kashe wayan Mami tayi tabi Raihana da kanta ke sunye ƙasa da kallo, ta sanya hannunta ta damƙi kanta ta ɗagota tana sake kallonta.

ita ɗince dai, to a’a ya Abu Aayan kuma zaice mata gata a wurinsu bayan gata ita data rayuwa da yarinya kusan shekara, toko dai yayi ne dan ya kwantar mata da hnakali ganin ta ɗaga hankalinta na son dawo da ɗanta da kuma hukunta shegiyar yarinyar,to amma bata yanda za’ai suyi mata irin wannan wasan.

ta shiga duhu sai kuma ta koma masarauta zata shiga haske.

dan haka da faɗa tace da Khaleed, “tashi kama hannun matarka mu tafi, in kaƙi kuma wallahi yanzu na maka baki”

ba shiri ya miƙe tsaye ya kama hannun Raihana ya sauko da ita daga gadon, suna gaba Mami na biye dasu a baya har suka ƙaras amota aka buɗe masu suka shiga.

koda suka riski can ɗin Rahinat suka tarar a fada an saƙale hannayenta a igiya an kuma ɗaure ƙafafunta sai police huɗu a kewaye da ita, Abie da Papa kuma na zaune bisa kujeran saurauta.

ƙarasa shigowansu cikin kowa sai da yay shock saboda abinda suka gani, wanda suka tsorata duk suka miƙe.

shi kansa mar martaba miƙewa yayi da ganin abin al’ajabi na halittar ɗan adam guda biyu a gansa.

Abie yace da Mami, “wannan kuma fa?”

Mami tace dashi, “ina can asibitin ai ka kirani kuma muna tare da ita, to ita waccen ɗin wace”?

Papa da Abbu suka miƙe, cikin faɗa suke ceda Khaleed, “Aayan karka rain amana hankali domin wannan shirinka ne ,wato kaje kasa anyi plastic surgery ko..to in har baso kake hukunci ya hau har kanka ba ka tantance mana asalin matarka”Abbu ban aikata plastic surgery ba kaman yanda kuke tinani, ni kaina i was shocked a time ɗin dana gansu ɗazu,sai dai na alaƙanta hakan da kamanni ne……” +

cikin doka tsawa Papa yace, “uskutt….”

sannan ya juya ga police yace, “shima ku kama minshi har ita data ke tare dashi ku wuce dasu prisone babu wani mai kawo min wasa cikin masarautata”•••••••ansa masu handcuff zasu tafi Nadiya ta taso da gudu ta zube gwiwowinta gaban Papa cikin kuka take roƙonsa,

“dan Allah Papa kai min rai kayi haƙuri ka ƙyalesa, kar a tafar min da miji dan Allah, tinda laifin bana sa bane ai hukunta su su kaɗai, abarshi yaji da iyaka sharrinma kaɗai da suka masa”

hauka tibirin Nadiya ta kama, kukanta ko kaman an kunna jiniya, koda ta shiga gaban Khaleed ta riƙo hannunsa tana masa surutai ya bata kyakykyawar harara ba shiri ta kauce. +

umarni Papa ya bada da a ɗauketa a wurin, in har kuma ta musa to su haɗa har ita.

kowa na wurin ya nutsu saboda yanda aka ga ran mai martaba yayi mugun ɓaci ,tinda yake cikin wannna masarauta ba’a taɓa kawo masa wasa da rainin hankali irin haka ba.

duk da Mami bata so ba amma taƙi magana tanaji tana gani aka tasa ƙeyar ɗanta gaba aka wuce dasu prison.

bayan fitarsu Papa yasa aka masa magana da Raihan dake tsaye a waje.

gaban Kakan nasa ya zube gwiwoyinsa ya kwashi gaisuwa tukunna Papa yasa masa albarka.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

kallon saurinyin yake da kamanni na sani kuma har yana jin wani ɗan abu game dashi acikin jikinsa.

Papa yace dashi, ” daga ina kake kuma miya kawo cikin wannan masarauta tamu sannan aina ka samo waccen yarinyar?

Raihan ya gyara tankwashewar ƙafarsa yace, “Allah ya taimaki mai martaba sarki,a salina ni ɗan wannan garin ne sai dai tin ina shekara ɗaya a zane mahaifiyata suka sami matsala da mahaifina wannan dalili yasa suka rabu ta koma ƙasarta ta nigeria, inda acan na ƙarasa girmana bayan na gama karatuna a india na dawo kuma nai aure yanzu haka har ina da ƴa ƴar shekara 4 mai sunan mahaifiyata”

Papa ya kaɗa kai yace, “Allah sarki…to yanzu ina shi mahaifin naka?”

“ehhh kaman yanda nace maka mun rabu dashi ne tin ina a zane to sai ayau Allah yasa na fito nemansa domin mu sami ganawa dashi nima naga mahaifina sannan na basa haƙuri ya maida mahaifiyata daga nan mu dawo ƙasarmu da zama, to akan hanyata ne na zuwa Allah ya haɗani da waccen baiwar Allahn acikin wani irin mawuyacin hali na atausaya mata shine na tsaya taimka mata”

maga isar da saƙon maganar Papa dake gefe yace da Raihan, “to duk munji zantukanka, yanzu wanna taimako kake da buƙata wannan masarauta tai maka?”

sai da Raihan ya sauke doguwar ajiyar zuciya sannan ya ɗago ya kalla kakansa sannan ya maida kai ƙasa yace,

“taimako biyu nake so wannan masarauta tayi mani wanda in har tai hakan shine zai tabbatr min kuma ya tabbatarwa da al’ummar datake mulka cewar adalar masarauta ce, na farko ta haɗani da mahaifina sannan kuma ta hukuntasa akan laifin dani ɗansa nake zarginsa dashi na ha’intar wannan masarauta a ɓoye…sannan abu na biyu ta tsaya tayi bincike mai zurfi akan wannan baiwar Allahn dake ta shiga tsaka mai wuya akan laifin da banata ba kamin ta yanke hukunci”

kamin Papa yay magana adalin sarki mai sauƙin zuciya na ƙasar saudiya wato Shaik Walid Ma’aruf yace,

“karka damu insha’Allahu wannan masarauta mai adalici mai albarka zatayi kaman yanda ka roƙa daga gareta….yanzu wane mahaifin naka kuma ya sunansa”?”Sunan mahaifina Dhameer Suhail Albannah……..”
+

ai bai ƙarasa ba Papa ya dakatar dashi da cewan, “kana nufin kai jikana ne Raihan ɗan gidan Hamida?”

Raihan na murmushi ya ɗaga masa kai yace, “ehhh nine Kaka na”

cike da jin daɗi da farin ciki Papa ya buɗa hannunsa yana faɗin, “

“تعال هنا يا بني ، تعال”

tamkar mai sunbatu haka Papa yake maganar duk murna ta cika shi, rabonsa da samun murmushi kaman haka a fuskarsa tin alokacin da Khaleed yay fyaɗe ga baiwar gidan.

Raihan ya tafi garesa ya shiga jikin kakan nasa Papa na faɗin,

“كيف حالك كيف حال امك اين امك؟”

dama ni ɗan gata ne haka mahaifina ya rabu da mahaifiyata, zancen da Raihan keyi cikin zuciyarsa kenan.

har yanzu shafa sumar kansa Papa yake, ya ɗago da fuskarsa yay masa sumba ta kulawa a goshi.

yana kuma shafa fuskarsa yace,

” اين زوجتك?اين عائلتك؟”،

“بارك الله فيك ،و بارك الله في حياتك ريحان”

sai a sannan aka shigo da Asma’u tare da ɗiyarta dake waje.

Ummi yarinya ce mai wayo tana hangensa ta ƙwace a hannun Mominta ta tafi wurin Dad ɗinta.

Raihan ya nuna mata Papa yace, “to yau ga Granny Ummi”

ta ɗan juya masa idanu kamin tace, “rilly Dad?”

ya ɗaga mata kai alamun tabbas, ƙwacewa tayi a hannunsa ta nufa Papa tare da ɗanewa jikinsa tana, “My Granny”

Papa yana ɗauke da ita yake sa mata albarka yana ta mata sumba.

Asma’u ma ta ƙaraso ta zube tana kwasar gaisuwa, itama nan Papa da Papi suka shiga sanya masu albarka baki ɗayansu.

shiko Papa tsabagen daɗi yama kasa sakin hannun Raihan, faɗi yake yau ga jikan albarka ya dawo, ga magajin kujerata, ga adalin shugaba mai jiran gado.

cike da ƙasaita da kuma izza Sultana Dhameer yake shigowa cikin fadar, dan tin alokacin da labari ya riske shi kan cewar ɗansa ya shigo masarauta kuma Papa nata faɗin cewar shine sarkin gobe yake wani jinsa a sama, sarautar ta motsa.

bayan ya durƙusa ya miƙa gaisuwa ga mahaifin nasa ya nemi kujera ya zauna yanata annushuwa.

Raihan ya karkato ya matso ga mahaifin nasa, cike da girmamawa ya gaidashi sukai musabaha.

shima albarka yake sanya masu baki ɗayansu sannan yace da Ummi ta tazo taƙi tace ita sai Granny.

darawa sukai baki ɗayansu sannan Papa yace a sanarma da kowa yana son ganinsa a fada cikin ƙan-ƙanen lokaci domin yana so ya gabatar masu da jikansa kuma sarki mai jiran gado.

Kamal,Toufiq da Yusuf suna gefe suma suna jin daɗi, dan yanda suka fuskanci baƙon ɗan’uwan nasu lusari ne so koda an bashi sarautar sai yanda sukai dashi shiyasa ma bazasu wani ɗaga hankalinsu ba kaman yanda suka ɗaga lokacin Aayan.

to batare da ɓata lokaci ba Papa ya gama gabar dasu acikin wannan masarauta sannan ya faɗi sashe mai lamba 03 da sarki ke hutawa na cikin masarauta aciki ya zama na *SULTAN RAIHAN* ,nan fa aka ɗau tafi ana rairo waƙa cikin yaren larabci cikin farin ciki.Nadiya kaman ta kurma ihu a wurin ganin abinda ke faruwa, shin wannan tsohon wannan irin tsoho ne mara yafiya da mantuwa da kafiya.

yanzu kenan da gaske ya cire Aayan cikin sahun jikokinsa kuma ya bar batun sarauta atare dashi.

to wallahi koda zatai kisan rai saita ƙwato masu sarautarsu dan ba wanda ya dace da zama sarki sai mijinta Aayan.

har da kyautar gwal-gwal Sarki Suhail yasa akama duk wani da yake cikin fadar, banda bayi 20 dayasa aka ƴanta atake alokacin duk na farin cikin zuwan Sultan Raihan.

Sarki da kansa yay ma Sultan Raihan irin shigarsu aka naɗa masa

bayan ko an idar da sallar isha’i aka gabatar da wata ƴar ƙaramar walima ta farinciki, ansha anyi ɗa’ami kowa na jin daɗi, ɓangaren su Sultana Yasmeen ma zuciyoyinsu wasai domin yanzu sun san Papa zai watsar da sha’anin bincikensa tinda har yana ambaton sati mai zuwa za’a naɗa Raihan a matsayin sarkin ƙasar Libya.

su kansu su Sultan Salman ko zuciyarsa wasai take domin kuwa tinda ragamar sarauta ta dawo hannun ɗansu asirinsu ya zamana a rufe, dan zasu san yanda zasu sa ɗansu koda asiri ne ya yanke hukunci kisa ga Khalid tinda dai har yayi fyaɗe..

da daddare Sultan Raihan ya fito fadawa na take masa baya zuwa cikin kurkun dake bayan gidan.

koda yaje kasa gane wace Rahina yayi ganin dukansu sun koma iri guda har sabon raunin dukan da aka masu a ɗazu.

sai da Rahina ta ƙuresa da ido tukunna ya iya ganeta yace a buɗe masa ƙofarta ya shiga.

yana shiga ta kama ɗaga masa hannu tana tari, da sauri ya ƙarasa gareta, nunin da take masa ya fahimci na buƙatar ruwan sha ne.

take ya bada izinin a kawo mata ruwa mai sanyi a gora haɗe da zuma da kubza.

agaba yasa mata yace taci, ce masa tayi bazata iyaci ba dan bata da buƙatar komi na sawa a bakinta.

da ƙyar ya lallamata taci kusan rabi sannan ya umarci mutanen wurin dasu bashi wuri.

kallonta yake wadda kanta ke sunkuye ƙasa tana zubda hawaye.

muryarsa a sanyaye ya ambaci sunanta data faɗi masa a ɗazu yace, “Rahinatu”

ta ɗago da ƙwala-ƙwalan idanuwanta da suka koma tamkar na mujiya tsabar mayuwacin halin da take ciki na rashin nutsu.

kallonsa take tana jiran cewarsa sai taga yayi murmushi.

runtse ido tayi wasu zafafan hawayen suka kuma sakkowa.

“albishirnki?”
yace da ita.

kaɗa kai tayi wanda ta basa amsa da hakan na goro.

yace, “yauwa ko kefa, to smile lemme see”

ta wuya ta ƙaƙaro murmushin da bai mata kyau a yanzu tayi, duk da tana tausayin kanta amma sai taji tafi tausayin Raihan daya damu akanta da yawa yake ta neman hanyar da zai kawar mata da damuwa.

hannu tasa ta karkaɗa a idons aganin yayi zurfi a tinani, juyowa yayi ya kalleta yace, “what happen”?

ta kaɗa masa kai alamun ba komi.

hannu yasa a aljihu ya ciro wayarsa, record ɗin da yay a ɗazu shi ya kunna mata ta kas akunne tana ji.

tsabagen daɗi bata san lokacin data kusa rungumesa ba, baki kawai take buɗewa tana son tayi magana amma babu daman hakan sai sabbin hawaye dake kwaranyo mata.”is ok”

yace da ita ya kuma miƙa mata hansky yace ta goge hawayen.

ta amsa ta goge baki ɗaya murmushin fuskarta ya gaza ɗaukewa.

“kinji duk yanda mukai da Abbi, bayan kin bani numbarsa na kirasa munyi magana dashi, na faɗa masu duk abinda yake faruwa kuma ya shaida mani gobe da yardar Allah zasu dira a ƙasar nan dan a daren yau zaiyi booking ɗin komi na tahowarsu” ,

ya numfasa kan yaci gaba da cewa, “haƙiƙa Raihana ke ƴar gata ce, yanda naji muryar mahaifanki ya bani tabbacin suna cikin tashin hankali…yanzu haka ma Kakarki tin barowarki can take kwance a asibiti,ita ba araye ba ita ba’a mace ba, dan haka ki kwantar da hankalinki gobe ƴan’uwanki zasu kuma zasu tafi dake dan mahaifinki zaiyi komi dan ganin ya fitar dake daga wannan hali”

tsaye Rahinat ta miƙe duk da jirin dake ɗibarta sannan ta durƙuso ƙasa, hannaye biyu ta haɗe tana ta wangale baki tana zubawa Raihan godiya.

girgiza mata kai yayi yace, “ba godiyarki nake buƙata ba, kwamciyar hankalinki nake so daga daren yau zuwa gobe”

ta ɗaga masa kai alamun ya gama samu, takarda ta rubuta masa ya kuma bata wayarsa taji voice ɗin Abbinta.

kunna mata yay tana taji, sai daya tabbata ya ɗauke mata kewa tukunna ya miƙe ya fita a ɗakin.

*****

misalin ƙarfe 2 na dare Khalid ne kishingiɗe akan kujera riƙe da siggaret hannunsa yana zuƙa.

ɗago da kansa yayi a hankali kuma ya ware idanuwansa da sukai jawur wanda kana kallo zaka hango zallar ɓacin rai acikinsu sai fuskarsa dake shimfiɗe da tsan-tsar damuwa.

ranƙwafa yayi yaci gaba da zuƙar abarsa har sai daya zuƙeta tas tukunna ya yarda.

hannunsa ya aza saman sumarsa yana murzawa gami d fuszagar da zazzafar iska daga bakinsa, Angel ɗinsa kawai zuciyarsa ke ambato a duk lokacin data harba.

runtse idonsa yay na ɗan wani lokaci kamin ya buɗesu a firgice kaman mayunwacin zakin daya jiyo ƙamshin nama.

tashi yay yana faman huci ya nufa ƙofa, da sauri dakarun dake tsaron ƙofa suka buɗe masa inda securities nasa kuma suka biyo bayansa har zuwa cikin prison.

tsit masarautar take sai masu tsaro dake kai komo, duk wanda ya jiyo motsi ya taho in yaga Khaleed ne sai ya koma ya cigaba da aikinsa.

tsakiyar ƙofa biyun cell ɗin da 2wins ke rufe ya tsaya, kowaccensu kwance take cikin uniform ɗin prison akan gadon ƙarfe ta takure daga dukkan alamu ba jin daɗin kwanciyar sukai ba dole ne kawai ya sanya.

ɗakunan daban-dabanne amma kuma a haɗe suke, ya kalla wannan ya kalla wannan haka ya dingayi har kusan mitina biyar kamin ya tsaida idonsa kan ɗakin da Rahinat take.

umarni ya bada na abuɗe masa ɗakin, suna shiga ya sanya aka malala wani tattausan carpet a dai² wurin da yake tsaye.

cikin lokaci kaɗan aka kimtsa wurin harda standing fan, aka kuma feshe ɗakin da tirare baki ɗayansa ya hautsine da shegen ƙamshi.

hannu yasa ya cicciɓi Rahinat dake baccin wahala ya sauko da ita ƙasa, zama yay ya miƙe ƙafafunsa ya ɗora kanta akan cinyarsa.

sam Rahinat bata san anayi ba dan a wahalace take duk dake madai ta kwanta da farincikin zuwan mahaifanta a gobe, hular uniform ɗin ya zame daga kanta wanda duk ya gama burkicewa sakamakon rashin kulawa daya daina samu.

shafa kan yake a hankali yana lumshe ido, sunkuyo da kansa yay ya juyo da fuskarta ya saita leɓansa da nata ya haɗe.kusan miti biyu tukunna ya ɗago daga kiss ɗin da yay mata tare da sauke doguwar ajiyar zuciya.

ya bada umarnin ai maza a kira masa likitan cikin gida, ba ɓata lokaci likita ya iso, Khalid yace dashi yay mata allurar ɗauke zugi tukunna kamin ya fara aikinsa.

kaman shi za aima allurar haka yaji dan saida ya runtsu ido ya kwantar da kanta kan ƙirjinsa yasa hannu ya toshe mata kunne sannan yace da likitan yay mata.

zafin data ji kaɗan dan tana motsawa ta kuma lafar da kanta saman faffaɗan ƙirjinsa a dalilin daɗin baccin data keji da iskar fanka ke shiganta ta ko’ina.

kamar za’ai dressing ɗin ciwon kamar baza’ai ba, dan da likitan ya ɗauko kayan aiki Khalid zai dakatar dashi yace wai yayi a hankali karta farka.

da ƙyar dai ya bari aka samu akai dressing ciwukan dake jikinta.

hannunsa da nata ya haɗe ya damƙe inda ɗumin tafin hannunta ke ratsa shi sai faman lumshe ido yake banda zuciyarsa kuma dake mugun zafi.

ɗayan hannunsa yake yawo dashi a saman fuskarta yana bin duk wani tabo dake ajikin fuskarta yana shafawa, tinanin irin azabben hukuncin da zaima Raihana data sanya Angel ɗinsa acikin wannan hali yake.

“soon jin daɗinki zai dawo my Angel, ba zan kuma barinki shiga wani halin ba tinda har na gane cewar kece ainihin Ruhina….kimin afuwa dana barki har tsawon wannan lokaci acikin wannan hali ,nayi hakanne duk dan na gane wace Raihana da dalilinta kuma nayin basaja a mtsayin ke”

shi ɗaya yake maganarsa can kuma ya ɗauka wayarsa ya kira wani D.P.O dayasa suyi masa ƙwaƙwƙwaran bincike.

anan D.P.O ke shaida masa cewarma ai Raihan bai mutu ba yana raye, ya sami wani ne ya maye gurbinsa matsayin shine har aka kashe shi.

amma yanzu haka yana tare dasu zuwa gobe zai fayyace masu dukkan komi kamar yanda ya shaida masu.

suna gama wayar yay ma Rahinat sabon light kiss a laɓɓanta tare da sakar sabon murmushi sannan ya shimfiɗar da ita kan carpet ɗin ya tashi ya fita yana mai waigenta.

da komawarsa ɗakin ƙullensa ya kirayi Tayseer yace ya shirya masa Visa zuwa London.

yana daga kishingiɗe kan kujera yake ƙwafar yana lissafo mugwayen iyayensa cikin ransa.

Dhameer,Baheer,Salman,Abid,Yasmeen amd photocopy of my Angel duk zaku ɗan-ɗana kuwarku, duk sai kun ƙwammaci ina ma ba’a haifeku ba.

da na yanke shawaran Angel da kanta zata yanke maku hukunci amma nasan halin Ruhina da tausayi hakan yasa zan ɗauketa nayi nesa da ita sai dai ta kalla azabar da zan ganawa kowannenku a vedio.

kasa jurema zaman yay ya tashi ya koma ƙofan cell ɗin da Rahinat take, kujera aka sanya masa ya zauna yanata kallon abarsa, har subhi bai runtsa ba,anata kirayen sallah yanaji amma yaƙi tashi sai daya ga ta motsa tukunna ya miƙe da sauri ya laɓe.

ta gefe yake kallon yanda take miƙar wahala kan ta maida hankalinta kan lafiyayyen carpet ɗin data kwana akai ga wata haɗaɗɗiyar standing fan na bayar da iska.

wani ƙayataccen murmushi ta saki cikin zuciyarta ta ambaci, “tanku Brother Raihan”

daga nan ta miƙe tana ɗingisa ƙafa ta shiga toilet.shi kuma dake laɓe sanyayyan murmushin data yi yasa shi suman tsaye harta fito a toilet tukunna shima ya wuce zuwa masallaci.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]