YAREEMA KHALEED CHAPTER 2

Advertisements

_____

YAREEMA KHALEED

CHAPTER 2

sai bayan da yay ajiyar zuciya sannan ya ɗago daga kwancen da yake yana murza goshinsa. +

sabon envelop ya gani mai kama da irin wancan, ɗauka yay ya zaro takardan dake ciki, wannan kuma sabon rubutu ne wanda akayisa da larabci, rubutun na faɗin, _kaje ka taimaki mahaifinka domin shima suna neman rayuwarsa kaman yanda suke neman taka._ abinda yafi bashi mamaki da ɗaurin kai signg ɗin wancan dana wannan duka iri guda ne. to mi yarinyanga ke nuhi.

ya take neman burkita masa tinani kodan tasan babu abinda yafi so sama da Abie shine zata ɓullo ta wurinsa… shiru yay na ɗan lokaci kamin ɗayan zuciyansa tace, “ka manta da maganar datai akan Abie saboda shi bamai yiwu bane kullum kewaye yake da matakan tsaro iriri”

to taya kuma zai yarda da kalaman yarinyar da zata iya kisa ma saboda son zuciyarta? yaushema ta sami fuskar raina masa hankali irin haka? to amma taya akai tasan Angel bayan ko randa tai ganganci taɓa kayan Angel bai faɗi mata ga mamallakinsu ba bare tayi amfani da wannan hanyar.

shiru yay yana tinane tinane kamin ya tashi, jotter da biro ɗin hannunsa yajefar yana yamutsa sumar kansa.

wai shin wanna irin so yakewa Angel haka, yarinyar da baiga fuskarta bama kawai bayanta ya gani amma ya kamu da irin wannan zunzurun ‘kauna tata haka, to idan kuma aljanace fa kaman yanda Mami ke faɗi.

no hakan bazai taɓa yiwuwa ba,mutumce kuma mallakinsa ce…harya taka zai fice a ɗakin wani tinani da yay ya dawo dashi baya.

pix ɗin data ajemasa ya ɗauka ya sake kallo…akwaifa ayar tambaya akan maganarta da kuma evidence ɗin data aje masa… pix ɗin asali da kuma natan ya ɗauka yana sake kallo, sam babu alamun edit ajiki , waige² yashiga yi shifa gaba ɗaya kansa ya ɗaure.

fita yay ɗaga ɗakin, yana zuwa ya haye bike ɗinsa ya fice zuwa gidan Mami.

shigarsa Parlon Mami ya ganta zaune kan kujera ta talbi fuska da hannu biyu da alamu tayi nisa cikin tinani kuma yanayinta yay kama da wadda ke tinanin hukuncin da zata yanke kan abin daya ɓata mata rai.

jikinsa a sanyaye ya zauna ƙasa da ita, ƙafa ɗaya ya miƙe yay tagumi da ɗayan hannunsa, yanzu in ya zama da gaske Angel ɗinsa ce ya kenan, duk abinda ya mata a baya Angel ɗinsa ya cutar bayan irin tanadin da yay akan ko ƙuda bazai taɓa bari ya taɓa masa ita ba ,kai iska ma mara kyau bazai taɓa bari ta kusanci inda take ba.

Mami ta katse tinaninsa da yake “yaushe ka shigo?”

“tin ɗazu” yace da ita da muryar damuwa.

“ina umarnin dana baka”? ta tambayeshi yayin data miƙe tana yafa lafaya.

shiru baice komi, ta kuma yanke tinaninsa, “Aayan da kai nike fa, ina takardar sakin matarka”

“ban rubuta ba Mami”

cikin tsananin ɓacin rai da bazai misaltu ba ta hausa da faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba kamar zata dukeshi..ayanda takeji ko da Khalid zai zama gawa ne ayau sai yasaki Rahinat.

shiko baki ɗaya ya rasa mike masa daɗi, moment ɗin baya yake tariyowa da kuma letter ɗin data aje masa dan sam baima sauraron abinda Mami ke cewa.

cikin tsawar data gama rikiɗa hanjin cikinsa tace, ” bazaka saketa bane ko kuma kana so kace mani kana tausayin mutumin daya tarwatsa farin cikin rayuwarka ya ɓata maka suna a idon duniya…ko kuma ita matar taka ka fara so? to wlh Aayan idan son yarintar nan ka fara to ka ajesa domin bazaka taɓa ci gaba da rayuwa da ita ba koda zaka mutu…takardar saki kuma dole ka rubuta kaje ka kai masu…Aayan duk duniya babu mutumin dana tsana sama da Rahinatu….”

ta koma ta zauna inda ta fashe da kuka.

jiki ba ƙwari kaman wanda yay cuta ya tashi yaje kusa da ita ya riƙo hannunta.

“dan Allah Ummi nah kiyi haƙuri ki mani afuwa….zan saketa kaman yanda kika bani umarni amma ban san mi yasa na kasa ba”

ta miƙe taje ta ɗauko masa takarda da biro ta bashi, tace” idan har na isa da kai kuma ni na haifeka to ka saki rahinatu domin bata cancanci zama matarka ba”

“Mami kar mu yanke hukunci cikin fushi daga ni harke muzo gaba muna dana sani…na roƙeƙi kimin alfarma zuwa na ɗan lokaci domin nayi wani bincike.”

“bincikenka ɗin banza dana hofi, bincike ya wuce wanda ka ɓata shekaru 5 kanayi dan gano wanda ya ƙulla maka sharri har yana neman rayuwarka a hannu…. Aryan koka manta nike auren Rahinata bakai ba saboda ni na auro maka ita, idan har baka aikata abinda na saka ba saina ɓatamaka….in ko bakai wasa ba zaka biyani nono na daka sha, Khalass”

hannu na rawa yay saurin ɗaukar takardar ya fara rubutu gumi duk ya keto masa.

yana rubutun yana tina kalaman Rahinat, kasoni batare daka san koni wace ba haka ka ƙini batare da kasan wa nike a zuciyarka ba….karkayi shakku da kalamaina dan Allah Khalid wlh nima ina sonka kuma wlh bazan yaudareka dan ka soni ba saboda nafi son soyayyarka ta gaskia.

lokacin daya gama rubuta saki ɗaya gaba ɗayansa ya jiƙe da gumi, haƙiƙa son yarinyar badaga shi bane ,sone da tini aka halicce shi dashi a jinin jikinsa.

ya naɗe takardar ya miƙama Mami yace gashi, bata kalle shi ba tace yaje ya kai masu idan ya dawo ya wuce airpot domin zasu wuce saudia.

yaji daɗi da bata amsa takardar ba gudun karta ga cika ɗaya saɓanin yanda tace mashi.

haka ya tashi ya fita har yana haɗa hanya sakamakon blind love ɗin daya kanainaye jijiyoyin jikinsa.motar ma sai sai security ɗinsa ya taimaka masa ya shiga, ƙaƙƙarfa ne a komi amma wck ɗinsa a so yake.sai daya kira Mami ta masu kwatance sannan ya iya zuwa gidan danshi bai san hanyar bama.

koda suka isa mai gadi ya bama takardar ya miƙa cikin gida daga nan kuma yace da driver ya wuce dashi gidan Khalil.

ganin a halin daya shigo Khalil ya taimaka masa da siggaret koya ji sauƙi, kusan kwali guda ya zuƙe cikin ƙanƙanen lokaci kamin ya ɗago da raunannun idanunsa ya kalla Khalil.

gyaɗa masa kai Khalil yay ya tashi ya ɗakko giya ya bashi yasha, yana gama sha bacci kuma ya ɗaukesa, kusan awa 7 yana bacci sannan ya farka,bayan ya farka yake sanar da Khalil halin daya ke ciki.

Khalil yace ya zauna yay nazari da duba sose , yanzu haka yarinyar wuyar data ke sha wurinsa yasata yin tinanin da zata juyar da hankalinsa, haka dai Khalil yay ta bashi shawara akan karya soma ya yarda ya tina fa itace yarinyar daya fi tsana kuma ita mace ta farko data taɓa nuna tsantseni akansa sannan kuma ya tina Angel fa na delhi ba wai nigeria ba.

a daddafe ya ƙarasa gida, shaf ya manta da batun Mami na inya dawo ya wuce airpot, sai daya diba waya yaga tarin miscalls ɗinta tukunna ya tina.

nan yay wanka ya shirya ya fito ya wuce, acanya samesu da zuwansu jirgin nasu ya ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki.

tskanin ɗa da mahaifa sai Allah, yanda Mami taga duk yanayinsa ya sauya sai ta shiga lallashinsa, “Aryan ka saki jikinka dan Allah kasan bana sonka cikin damuwa, ni ina mai tabbatar maka babu dana sani a hukuncin da muka yanke ko kaɗan”

ɗaga mata kai kawai yay, abinda Nimrah tace ne ya juyo ya wurga mata harara sai kace ya tabbar da gaske Angel ɗince.

“nifa wlh Mami na tsani Rahinatu, kuma insha’Allahu barin gidan da tayi ma shine silar mutuwarta, muguwa azzaluma kawai ta ɓatawa Khoyaa suna ta rabashi da Abie”

“kwantar da hankalinki Nimrah ai harma na shigar da ƙara kuma na aikawa da Abie vedion, matsawar ina raye bazan taɓa bari a zaluntar mani ɗa ba sai nabi masa hakkinsa”

ya gimtse idonsa bai buɗe ba har suka iso saudia, haka dai daka gansa kasan yana a damuwa.da suka isa masarautama ana yowa kansa ya dakatar da kowa ya wuce sashinsa ko fadar Abbu bai leƙa ba.

karo sukai da Taysir a wurin shiga, ya kaikaito da kai yace masa, “yi haƙuri dan Allah”. karo na farko da Tasir yaji khalid yabada haƙuri a rayuwarsa.

duk daya san miskili ne amma yanayin daya gansa yasan cewar akwai damuwa tare dashi damuwar ma kuwa babba.

shima bai saurareshi ba yay turakar Maamaa, bai sameta acan ba saboda sun wuce sashin kakan nasa.

ya jima acan suna gaisawa da Mami saboda tin biki rabuwarsu da haɗuwa, anan ya tarar da maganar da suke tattaunawa na game da yarinyar datai ƙazafi ga Khalid kuma yanzu harta na bayyana masa cewar zasu kasheshi.

daya dawo ɗaki kwance ya sami Khalid kan gado yana kallon sama..taɓosa yay yace , “Man wai ya dai naganka yau sai a hankali duk da dama haka kake”mutumin da sai ya ɓata lokaci yake reply amma farat ɗaya yace masa, “Taysir Angel, Angel ɗina…kasan labarin soyyta ka kuma san yanda take…syyta itace rauni na duk mazantakata…. na kasa yarda Angel ɗina ce na kuma kasa ƙin yarda da hakan saboda nasan Angel bazata taɓa ƙarya ba….gaba ɗaya na rasa wanna irin tinani zanyi Taysir “

“Relaxx Man” Taysir ya faɗi yana dafa kafaɗarsa.
“Man believe me itace Angel ɗinka fa”

Khalid ya ɗago yana masa duban ????, Taysir ya ɗaga masa kai yace “ƙwarai kuwa sai dai in karka yarda…kasan ni lauyer ne right? ka kuma san yanda nake zurfafa bincike akan abu ko…to a ɗazu kamin ku iso Mami duk ta aiko mani da recrd na CC ɗin gidanka….am sorry 2say a ɗazu na kalla inda bai kamata na gani ba amma ya kama dole ne tinda ta hanyar bincike ne…Man yarinyar dake mugun tsoronka da shakkarka bazata taɓa wasa da hankalinka irin haka ba…sannan shaidar ƙarshe da zan baka wadda akanta na tsaya itace wannan”

ya miƙamasa vedion daya kunna, time ɗin data shigo ɗakinsa gyara, ta ɗauka bangle ɗin ta saitashi ne da ring ɗin dake ƙaramin yatsanta wanda ya bada tabbacin wannan ring ɗin na bangle ɗinne shine har take cewan wannan ai kaman bangle ɗina daya ɓata tin a delhi saboda jan zaren data gani ajiki wanda Ammi ta ɗaura mata gashi kuma ajikin zoben nata again, sai ta aje kawai ta ɗau haramar aikinta sai kuma can ta tsaya tana tina wani abu shine tazo ta ɗauka ribom ɗin tai tsaye shiru kamin ta fara tina maganar Nimrah….

rigar baccin da take sanye da ita a time ɗin show ne ce, cikin tsananin ruɗu da tashin hanƙali Khalid dake kallon Vedion ya miƙe tsaye sakamakon ganin lafceciyar tawadar Allahn daya gani a bayanta wadda tai circle, babu shakku Angel ce wannan sai ayanzu ya ƙarama tabbatarwa saboda side view ɗin wuyanta ma daya sake gani mai ɗauke da tabon ƙuna.

yatsansa na rawa yakema Taysir nuni yana murmushi, ” wlh itane ,wlh Allah itane, waɗann sune proof ɗin da nike faɗin ko a filin arfa zan fiddo da Angel ɗina, abu guda yanzu ya rage the extra digit finger(postaxial polydactyly) dana ganta dashi amma ita anyi surgery ɗinsa”

maganar yake murna duk ta gama cika shi dama zai sake ganinta ɗin da gaske kaman yanda yake drmng kullum.

vedion yay rewrding baya, fuskarta yake kalla sose baki washe ƙayataccen murmushin fuskarsa kuma ya gaza ɗaukewa, a hankali ya lumshe ido ya buɗe ya ɗan cije lips ya furta, “Cute face queen of king”
fuskar tata tai masa azabar kyau kaman ta lovely tah Ummu Nabil.

can kuma ya dakata jiki a matuƙar sanyaye da fuskar nuna damuwa yace,
” yanzu kana nufin Taysir duk abinda na aikata a baya Angel nayima shi”

“tabbas”

kamar zai kuka ya shiga girgiza kansa,

” i will neva forgive my self har saina dawo da Angel gareni kuma na nemi afuwan abinda na aikata mata sannan ta yanke kowanne irin hukunci taga dama akaina”

ragon namiji a fannin so kenan wato Yarima Khalid??, idonsa ya matse sose ya dafe kai saboda ya daina ganin abubuwan da duk suka faru a baya.

Taysir ya dafasa yace, “kace ta yanke maka ko wanne irin hukunci ko, koda na rabuwa da kaine”…..

ai bai ƙarasa ba Khalid ya kaishi bango, “karka sake cewan zata rabu dani, Heenat will neva leave me saboda tana sona”

“soyayyar da take maka a bayana ne Man amma banda yanzu, ko ka yarda ko karka yarda soyayyarka a zuciyarta a baya ne yanzu babu ita….ko ka manta da maganganun data faɗa maka ne a baya ,koka mance cewan ita ta nemi saki da kanta daga hannunka tin kamin ka furta mata, ko ka mance tace bazata ƙara dawo garekeka ba kuma bazaka ƙara ganin……”

naushin daya bashi a baki ne yasanya shi haɗiye sauran jawabansa.huci kawai Khalid ke akansa ya kasa magana,Taysir da zafin nama ya ɓarar da hannayensa daga shaƙar kwalarsa da yay.

“mtswww ni nace ka aikata abinda zai sanyaka dana sanin da zaka zo ka juye fushinka akaina ko kuma ni na ɓata maka….kai nama faɗa ɗin na kuma na faɗa yarinyar nan bazata taɓa zama mallakinka ba a karo na biyu….ai ita ba jaka bace duk wuyar daka bata a baya sannna ta kuma dawo ma maka” +

Khalid ya haɗiye wani yawu mai zafi sannan ya ɗago da jajayen idanunsa ya kalla Taysir yana nunasa da yatsa.

da muryan ɓacin rai yace masa , “kar dai ka kuskura ka faɗi wata kalma mara daɗi akanta in ba haka ba yanzu ka baƙunci lahira”

Taysir yay shiru bai kulasa ba dan yasan kaɗan daga cikin aikinsa, komawa yay ya zauna yaci gabada binciken da yake akan wani issue na yarinyar da akama fyaɗe aka kasheta.

shikam Khalid ficewa yay ɗaga ɗakin, fadawa na ganinsa suka bi bayansa dan take masa amma duk ya dakatar dasu.

motar da Abbu ke fita acikinta ƙirar rolls royce ya nufa, da sauri dogarai suka zo dan buɗe masa ya ɗaga masu hannu, hannu ya miƙa ya amsa key ɗin,zai shiga muryan Mami ta dakatar dashi.

bai juyo ba ya tsaya yana jiran cewarta.
“ina zaka haka?”

“neman Angel Mami”

ƙarasowa tayi ta juyo dashi suna facing juna, kallonsa take kallo na kamar bai hayyacinsane ko kuma ya haukace.ita fa tsoron wannan aljanar data shigo rayuwarsa take karta zautar mata da yaro,shekaru nawa yau yaƙi mancewa da ita.

“to yanzu da zaka tafi nemanta ina zakaje bayan bakasan taƙameman inda take rayuwa ba…Aayan….”

“Mami Angel ba kowa bace face Heenat”

ta tambayesa , “wace kuma Heenat”?

” رحينة زوجتي “

ta kifeshi da mari, “wai hankalinka ɗaya kuwa, wacce iriyar maganar banza kake yi, shekara nawa ka ɗauka kana neman yarinyar data ɓata ka sannan kuma gano ka barta tasha, ko ka mance ata dalilinta kai zaman prison ka kusa ɓata kyakykyawan tarbiyarka ka sauya ɗabi’unka masu kyau…… oak kana nufin idan itane ɗin zakaje ka nemeta ne”

“ehhh Mami saboda soyayyarta tarin jayi ƙiyayyarta….da ace tin farko nasan itane to dana manta da komi na mance da faruwar komi, zaman prison dama can rubuce yake sai nayi rayuwan ciki…Mami abinda tayi fa b ayin kanta bane kuskure ne kowa na aikatawa, ki barni naje nemanta dan Allah, rayuwata zata cika ne idan har kawai da ita”

“Mami ga kiran Abie ,yace karku wahalar da kanku domin yarinyar yanzu haka tana wurinsu a tsare kuma tana gab da fuskantar hukunci dai² da abinda ta aikata daga masarautar Abu Mourad Albannah , sannan kotu bazata bar fushi da ita ba har sai lokacin data faɗi waɗanda suka sanyata suma an hukuntasu, yanzu haka Sarki yasa a jefeta idan har bata faɗi b a gobe saboda wannan shine mafi girman laifi da aka taɓa aikatawa acikin masarautar dan ta tozarta sarki gobe mai jiran gado….”

“a jefe wa? u mean zasu jefe mani Angel, to kayi gaggawar sanar dasu kar wanda ya sake ya taɓata har lokacin da zan isa idan ba haka ba kowane sai ya kuka da kansa”

ya faɗi yana zazzarewa Taysir ido ga wata uwar shaƙa daya bawa wuyansa kuma yaƙi sakinsa, Taysir ko sai kakari yake saboda maƙurar daya sha banda ɗishi² ba abinda yake gani.

ya shiga girgiza sa da ƙarfi yana faɗin, “ka kirasu ka faɗa masu kar wanda yay yunƙurin aikata mummunan abu akan Angel, su dakatar da shirin abinda suke aikatawa,laifi ne ni akamawa ba wani ba, kar wanda yay gangancin taɓan mata”

kowa ƙoƙarin ƙwatar Taysir yake amma ya kasa , daka kawo hannu zai mangareka, Mami kam gefe ta koma tana kuka saboda kisan da Khalid ke shirin yi gashi yaƙi ji yaƙi gani.

hargitsatstsen marin da Abbu ya saukar masa a kunci ne yasasa sakinsa batare daya shirya ba nan Taysir ya koma gefe yana maida numfashi.

“dama baka da hankali Aayan, ɗan uwan naka zaka kashe da hannunka”

“Abbu bakaji abinda yake faɗi bane akan matata”

“toni na faɗa, ba aikoni akai ba”
Taysir yay maganar shima yana huci cike da jin haushin ɗan uwan nasa.

“shikenan kar Allah ya baka ikon yin shiru ɗora daga inda ka tsaya”

sanin hauka irin na Khalid akaja Taysir baya saboda yanda ya nufosa a fusace yana muzurai.

“ahaka zaka mulki wasu, to bari kaji mai saurin zuciya baya iya zama shugaba… shikenan kaje ka aikata son ranka Aayan tinda kai babu wanda ya isa ya faɗa maka kaji”cikin ransa yake faɗin shifa baya son yana abu tsohonnan ya shiga ciki, ƙwafa yay banda Abbu a wurin da sai ya dagargaza bakin Taysir, yana huci yay motar ya buɗe , zai shiga ya jiyo yana korawa Taysir kashedin, +

“kuma ka sanar masu matsawar aka cutar min da matata koda ƙwarzane saina tashi ƙasar Libya baki ɗayanta.”

yama manta da idanun su wane a wurin ya shige ya banke ƙofarsa yabama motar wuta zuciyarsa cike da zullumin son ganin halin da Angel ke ciki yana kuma tamin ɗin irin hukuncin dazai wanda duk ya taɓata.

yana isa airpot ya wani fito yashige jirgi ya tashi dashi zuwa ƙasar Libya.
kansa bisa kujera daya kwantar yake tina lokatan baya, babu abind aketa faɗo masa sai abu biyun nan ,lokacin datai gudun mage ta shige jikinsa da lokacin fito a toilet da gudu tana ihu kumfa duk jikinta.

wani dadɗan numfashi ya saki sai leɓensa dake motsawa, wato shiyasa yaji ya tsani magensa alokacin har yay sadaƙa da ita duk da bala’in son da yake mata…. murmushi mai kama da dariya yay a hankali ya furta “My Agel fear fear”

ji yay baki ɗaya ya ƙosa ya dira a ƙasar.

ita kam Mami bayan fitarsa kuka ta saka saboda tsoro da fargabar abinda ka iya zuwa ya dawo.

****

ba sakin Rahinat ya ɗagawa Hajia hankali ba, babban tashin hankalinta kalaman ƙarshe daya rubuta watanni bakwai kenan da guduwar ɗiyarsu suje su nemeta.

koda ta kira Abbi ta sanar masa yace shi ba ruwansa ai dama ya faɗa mata duk matsalar data biyo baya to kar asoma nemansa.

ɓangaren Ammi kam kuka ta sanya a lokacin, tana zubar hawaye take ceda Abbi yanzu itama ka yarda mu rasata kamar yanda muka rasa Raihana.

duk da Abbi ma cikin tashin hanƙali yake amma sai ya dake yace , “ai ita Raihana ba bijire mana tayi ba tabi son zuciyarta kamar yarda ƴar uwarta tayi ba ,ita mutuwa tayi, wataƙila da tana nan data kore min baƙin cikin da Rahina ta sanyani ciki, Allah yafimu sonta shi yasa ya amsa abarsa tin tana jaririya”

“duk da haka Abbi, kar fushi yas aka manta matsayin da zuciyarka ta bama Rahinat”

saboda karta sa zuciyarsa ta tsinke ta raunana Abbi ya tashi ya fice a gidan, office ya wuce idan ya ƙulla kansa, hular kansa ya cire cikin zuciyarsa yana adu’ar Allah ya kiyaye masa ɗiyarsa a duk inda take..

*****

Nawwara ke zaune kusa da Anty, dafata tayi tace, “Anty wai lafiya tin ɗazu na ganki cikin damuwa”

Anty Asma’u da duk tabi ta ruɗe ta kalleta tace, “ba komai, kinga sake kira min numbar Hajia Saddiqa”

“wacce Anty”

cikin tsawa tace, “Hajia Saddiqa shugar gidan marayun pataskum mana wanda Engnr Faruq Adam Modibbo ya buɗe”

“O na tinata amma kaman ta sauya numba bari na duba a whatsapp ɗina”

“ke dalla malama kiyi min da jiki ko kuma ranki yay mugun ɓaci wlh…kin san meke shirin faruwa dani ne”

jiki na rawa Nawwara ta ɗau wayarta ta shiga laluban numban Hajia Saddiqa babu tace Anty nifa banda tata saita matarsa ƙawar matarsa Hajia Hidaya.

“dan uwarki wai ni su nake maki magana, ki duba wayata mana akwai numbar ki sake kira kiji, ni na kira bata shiga ba”

nan Anty taci gaba da safa da marwa a tsakiyar parlon, tana jin sallaman Uncle Badamasi ta kuma ruɗewa dan sai taji kaman ta Abbi.

****
tsaye su Sultana Yasmeen suke cirkocirko cikin asibitin Tripoli Central hospital Libya kowa da abinda yake saƙawa cikin zuciyarsa.

tinda labarin ƙullinsu yaje kunnen Sarki Suhail suka shiga tashin hankali, fargabar da suke ciki idan yasan su suka aikata, lalle matakin da zai ɗauka akansu mummuna ne kaman yanda yasha alwashin jefe ko wane.

Sultan Dameer ya katse tinaninsu da faɗin, “nifa bana jin komai, ruɗanin da nake ciki kawai nake so na fita daga ciki”

Sultan Salaman yace, “nima shi kawai nake so a fitar dani saboda dashine kawai zamu tsira…shin wacce yarinyar ce ta asali ,tamu ko kuma tasu?”

Sultan Baheer yace, “tamu itace feck tasu kuma original zasu raina mana hankali ne kawai”

Sultan Abid dake da zurfin tinani yace, “tamu itane bata asali ba tasu kuma ta asali….mafita ɗaya mu kashe wannan ta wurinmu”

Sultana Yasmeen tai caraf tace, “dai dai kenan, muna kasheta kasheta mu yaudaresu da gawarta domin nima nafi tinanin ta wurinsu itane ta gaskian tinda har suka ƙi tsaurara bincike bayan mun ɗauke wadda suka sauyawa kamanni” +

“to yanzu ya za’ayi kenan?”
Dameer daya fi kowa ƙwallafa rai akan sarautar ya fadi.

Sultana Yasmeen ta daki dariya sannan ta zaro wata allura daga jikinta tace, “wannna itace allurar gubar dana daɗe ina ajiya dan kashe Mourad ko kuma ɗansa amma yau zan kashe baiwa da ita saboda bana so asirinmu ya tonu dan daga lokacin da Maimartaba yasan dasa hannunmu to tabbas ranar na lahira zaifi mu jin daɗi”

tana murmushin mugunta tai room ɗin da Rahinat ke kan gado kwance drip na shiga jikinta.

****
Abie da Papi ne zaune kan kujera gaban gadon Raihana dake kwance itama.

gefe kuma police ne tsare da asalin drcter ɗin dake kula da Rahinat lokacin datake hannun Abie.

tsawa sojan ya daka masa sannan ya saita drcter ɗin da bindiga yace masa, “zaka faɗi mana dalilin daya sa ka mata alluran bacci kuma ka faɗi wanda ya saka ko saina ɓula kanka”

jiki na ɓari yace, “wlh ban mata alluran bacci ba tin ta farko dana mata kuma ai ta farfaɗo, ban san wa yay mata ta yanzu ba sai dai idan a lokacin da aka kawo harin nanne”

sai yanzu Abie yay tinani yace, “ƙwarai zai iya zama haka tinda da suka shigo basu mata komi ba kenan alluran kawai suka mata”

Ran maimartaba matuƙar ɓace yace, “bazan taɓa barin wanda ya nemi ya cutar da jikan dana fi so ba….itama wannna ɗin ku kasheta bana buƙatar farfaɗowarfa, su kuma da sannu asirinsu zai tonu suzo hannu na , mai jiran gado ya masu duk hukuncin daya ga yayi daidai dasu”

Abie ya miƙe yana lallashin Papi yana kwantar masa da zuciya kan karsu kashe yarinyar yanzu saboda idan sukai haka sunyi abinda waɗancan suke so.

****
Khulaid yana daga tsaye tin a ɗazun yana kallonsu Sultan Baheer saboda ya jima yana bibiyarsu tinda suka sace Rahina.

yana ganin sun wuce zuwa room ɗin da Rahinat ɗin ke ciki ya saurin zira labcourt tare da face mask sannan ya sanya gloves wuyansa kuma saƙale da stethoscope yabi bayansu zuwa ciki dan yasha alwashin bazai taɓa bari wani abu ya sami Rahinat ba saboda baya son ya rasa Raihana, kamar yanda ita Raihana ke son raba Rahinat da Khalid dan Aayan ya zama mallakinta…
.

yana shiga room ɗin ya tadda Rahinat cikin hali na ban tausayi wanda duk mai imani zai zubar mata da hawaye.

akan gadon take kwance kowanne sashi na jikinta ciwo ne ajiki duk jini ga Sultana Yasmeen ta toshe mata baki da hanci sai ƙoƙarin ƙwatar kanta take shi kuma Sultan Dameer ya fito da allurar zai tsira mata ga Sultan Salman ya riƙe ƙafafunta.

“ku dakata” shine abinda Khulakd yace dasu yana ƙarasawa wurin nasu da sauri.

sakinta sukai suka jajja da baya shi kuma ya ruƙo Rahinat dake miƙo masa hannu.
idonta duk ya firfito waje hawaye na bibiyar kuncinta bakinta sai rawa yake, shi kansa bai san lokacin da hawayen suka zubo masa ba ,ji yayi dama basu bata maganin da suka bata ba na hana magana tsawon lokaci.

hannuɓta dake ta rawa ya riƙe gam yana , “kwantar da hankalinki babu abinda zai sameki kinji tinda har nazo gareki”

taji duk mai yace sai dai babu bakin mayarwa sai kallo data bisa dashi, Sultana Yasmeen taja dogon tsaki tace da Khulaid, “ka matsa a gunnan ko kuma yanzu nasa dogarai suyi min waje dakai

Sultan Abid yace da ita, “a’a ba haka za’ai ba Yasmeen ai tinda ya ganmu asirinmu ya tonu , yanzu mafita ɗaya mu sayeshi shima”

nan gaba ɗayansu suka masa alƙawarin billion ashirin tare da mallaka masa tarin kadarori.

tsaye yayi yana nazari da tinani kamin ya juya ya kalla Rahinat data cikwikwiye a bayansa sai ajiyar zuciya take fitarwa.

tausayinta ya kamasa sose bazai iya bari su kashe baiwar Allahn da bata da laifin komi ba sannan kuma bai iya jin zai sadaukar da soyayyarsa saboda kuɗi ba.ganin yana neman ɓata masu lokaci da banzan tinaninsa suka makeshi ya zube ƙasa, ita kuma Rahinat Sultana Yasmeen ta shaƙi wuyanta. +

****
kamar baƙo yake kallon ƙasar tasa tinda ya fito daga cikin jirgi, ji yay iskar duniyar ta sauya masa gaba ɗaya.

tsaye yay yana kalle kalle, bugun zuciyarsa ne ya ƙaru a lokaci guda fat fat, tinawa da Angel yay saurin nufa mota aka jashi.zaune Raihan yake cikin wani haɗaɗɗen parlo na alfarma kansa jingine da kujera idanunsa a rufe.
wata ƴar ƙaramar yarinya ce tazo wurinsa tare da kiran sunansa, “Dad” +

ɗagowa yay tare da sauke idonsa kanta yana mata murmushi, hannayensa ya buɗa mata ta shige jikinsa tana dariya.

kiss ya mata a kumatu sannan yace, “Ummi nah ya akai

Tana masa shagwaɓa tace, “Dad muje park ka jima baka kaini ba”

“angama ƴar gidan Dad, maza jeki ce da Momi ta shiryaki mu tafi”

“Dad harda Momi zamu tafi?”
“ehh harda ita, kice mata itama tayi kwalliya mai kyau”

da gudu ta tafi tana “tom Dad kaima kaje ka shirya”

ajiyar zuciya ya sauke gami da shafa goshinsa,shin har sai yaushe zai bar tinanin wannan yarinyar ne,wannan shi ake kira da ƘADDARAR SO,haƙiƙa sonta ya masa wani mugun kamu mai wuyar fassaruwa wanda shi kansa bazai iya misaltawa ba, babban tashin hankalin daya ke ciki a yanzu na rasa taƙamaime a inda zai sameta, ya koma ruga yafi sau goma amma kullum labarin da Baba Hardo yake bashi basu sami labarinta ba.

yana tsaka da tinani Asma’u ta taɓosa dan tin ɗazu take wurin amma bai san tazo ba.

kan cinyarsa ta zauna a shagwaɓe tace, “Handsome nah wai dan Allah mike damunka da kake ɓoye mani, ka diba fa yanda duk kabi ka rame saboda yawan tinani, ko wani abin ya faru a office ne?”

ya kaɗa mata kai ɗauke da damuwa yace, “babu komi Swthrt ɗina, karki damu kinji”
yay maganar yana shafo kumatunta.

fuska ta yamutse tana shirin kuka cikin shagwaɓa tace, “ni dai Allah na gaji da faɗin ba komi, ina fa lissafe 7month kenan da sauyawar walwalarka”

kauda zancen yay da ɗaukanta yana, “mutum shidai yafiya shagwaɓa”

ta saƙalo da hannayenta wuyansa tana dariya tace, “to idan ban maka ba wazanma handsome ɗina
tai maganar tana bashi light kiss a lips ɗinsa.

murmushi yay tare da mayar mata nasa a kumatu, a tsakiyan ɗakinsa ya ajeta ya kamo weast ɗinta yace, “Swthrt kin san mine”?

tace dashi “a’a saika faɗi”

ɗan matse ido yayi yace da ita, “swthrt ina son ganin mahaifina, rabona dashi tin ina ɗaure a tsumma, yanzu lokaci yayi da zanje innemesa”

“to kana ganin Hubbi zata bari”
“swthrt idan na daka ta Hubbi bazata taɓa yarda ba, kuma har abada bazata sakko daga fushin da take dashi ba duk da cewan shine da laifi tinda ya ɗauki SON ZUCIYA(sanaz deeyah) ya ɗaurawa kansa bayan ya san cewan mulki da saurata duka na Allah ne, wayonsa ko dabararsa bazasu taɓa bashi ba, koya manta idan ya kashe shima kasheshi za’ayi, ni ɗin dayake taƙaman ya haifa sam bana sha’awan saurauta ko an bani bazan amsa ba, ina son ganinsa koda sau ɗayane Swthrt, ki bani ƙwarin gwiwa kinji matata”

tace dashi, “ina goyon bayanka Handsome ɗina, ya kamata ace kaje ka gana da mahaifinka, kai rayuwa dashi kaman yanda sauran ƴaƴa ke rayuwa dana su mahaifan suji daɗi…. to amma ni tinanina abinda zamuce da Hubbi”

yace da ita, “kawai na yanke shawaran zance mata zamuje london, duk da ban san inane ba amma nasan ƙasar libya ne kuma cikin masarauta”

“hakane kayi tinani mai kyau, yanzu yaushe zamu tafi”?

yay murmushi sannan yace da ita, “baki buƙatan haɗa mana komi kin san mu dama already visa ɗinmu koda yaushe a shirya take, zadai muje ne yanzu muyima Hubbi sallama nasan zamu sha faɗan bamu sanar mata da wuri ba”

tai murmushi itama tace, “Allah yasa dai kar tace tare zamu tafi dan kasan bata son muyi nesa da ita”miƙewa tayi taje ta shirya cikin ƙanƙamen lokaci, data dawo ɗakinsa shima harya shirya cikin haɗaɗɗen farin boyel mai kyau wand aya amsa farar fatar jikinsa. +

Ummi ce ta ƙarasa wurinsa da ɗan gudunta tana “Dad mun shirya kazo mu tafi”

itama Asma’u da kwaikwayon ƴar tata ta ƙarasa garesa tana “Dad kaifa muke jira”

yay dariyar farin ciki ya rungumeta jikinsa yana shafa ƙaramin cikin data ke ɗauke dashi yace, “Swthrt kiyi min adu’a Allah yasa na sami abinda zuciyata take nema domin ina jin ajikina tafiyar nan da zanyi alkhairi ne agaren, dmauwar da nake ciki zata yaye”

da rashin fahimtar zancen nasa ta ɗago ta dubesa kana tace, “kaman ya abinda zuciyanka ke so da kuma damuwan da kake ciki?”

sam ya manta yay wanan katoɓarar, cicks ɗinta ya kama yace, “kewar mahaifina na mana”

nan ya kama hannunta dana ƴar suka fita dgaa sashensu zuwa na Hubbi wato mahaifiyar Raihan.. suna mata bayani ta gamsu musamman ma da Raihan yace mata ai zasuje duban lafiyan Unborn ne dna 2dayz yana takurama Mamansa.

adu’an Allah ya kiyaye hanya tai masu duk da tafiyan ba’a son ranta ba, sam bata ƙaunar abinda zai nisnata ta da ɗanta kaman yanda mahaifinsa ya nisanta dashi saboda wata aba sarauta.

****
dakatar da driver yay dayaga sun ɗauki hanyar masarauta yace ya juya ba can zasu ba gidansu zashi.

juya akalar motar drivern yayi zuwa president house
wata faɗuwar gaba Khalid yaji lokacin da suka isko bakin gidan, tangamemen gate ɗin gidan aka wangale masu suka shiga ciki.

runtse ido Khalid yay yana mai murza karan hancinsa ,ji yake inama baizo ba saboda tinawa da korar karen da Abie yay masa, ya jingina kansa da kujera yana mai jin raɗaɗi da zugi acikin zuciyarsa.

juyi yake da kansa kamin ya yanke shawaran komawa kawai dan sam bai cancanci zama cikin mutanen da suka ƙisa ba akan gaskiyarsa.

haushin kowa da komi yake, umarni yabama driver daya juya ya maidasa airpot dan ayanzu zai koma saudia, ɗayar zuciyarsa ta tinatar dashi idan ka tafi Angel kuma fa?

ido ya buɗa da sauri zuciyarsa na harbawa, can kuma ɗayan zuciyar tasa tace masa kenan ka mance da komi ya sameka itace maƙusidi harta walaƙantar da kai a bainar jama’a.

ya dafe kansa da ƙirjinsa, ya rasa asalin zafin da yake ji cikin zuciyarsa, SO ko kuma ƘIYAYYA,kansa dake neman sarawa yana mai jin kaman zai faɗo ya dafe, a hankali murya a sanyaye yake cewan,why angel,miyasa kika aita hakan akaina bayan kin san ni mai tsananin sonki ne?

umarni ya bama driver ɗin daya juya kawai, yay alƙaawarin mantawa da ita gaba ɗaya a rayuwarsa, driver na tada motar saiga Abie da sauri ya fito domin kuwa ayanzu ya amsa kira daga Mami cewan Aayan yazo kuma tasan da wuya in yazo ya isko inda suke saboda yanayin daya taho ba kyau.

security yasa dasu dakatar masa da motar, da ɗan gudunsa ya ƙarasa inda motar take, buɗewa yay farinciki duk ya isheshi yau gashi ga ɗansa duk da komi ya faru nasa laifinne.

ciki ya shiga ya ɗago Khalid dake daga kishingiɗe wanda duk abinda ke wakana yana ji sai dai yay shiru dan baiko ƙaunar buɗe ido yaga wannan gidan.

jin daɗi duka ya rufe Abie, muryarsa harna rawa yace, “Aayan wuldi

kibiyar ƙaunar mahaifinsa ta soki zuciyarsa, yana cike da kewarsa sai dai kuma yana fushi dashi.

Abie ya kamasa suka fito a motar, tallafar fuskarsa yay yace, “Aayan ka buɗe idanunka ka kalleni, shekara shida bama tare yau kaga gani amma bazaka kallemi ba”

sma ƙin buɗe ido Khalid yay sai dayaji muryan Abie ya sauya kaman zai kuka sannan ya buɗa idanunsa ya zubesu a ƙasa still dai yaƙi kallon Abie.Abie yace dashi, “nasan har yanzu kana baƙin ciki da abinda ya farune shiyasa, amma karka damu asiri ya riga ya tonu domin yanzu haka ita baiwar data maka ƙazafi tana tsare zamu walaƙantata kamar yanda ta…..”

Abie bai ƙarasa ba Khalid ya damƙi kafaɗarsa cikin tsawa yace, “tana inaaaa”?

shiru Abie yay yana dubansa da mamaki saboda abinda ya masa.
cikin wata tsawar Khalid ya sake ce masa “ina tambayarka tana inaaa”

“Aayan ni kake ma tsawa, koba komi fa ni mahaifinka ne”

sai a sannan ya saisaita fushinsa ya ɗago ya duba Abie, Allah sarki rayuwa harya ƙara tsufa dan furfura sose ta fito masa, wani sabon tausayi da ƙaunar mahaifin nasa ne ya shigeshi, fashewa yay da kuka ya kaima Abie runguma yana roƙon yafiyarsa.

“nizan roƙi yafiyarka bakai ba Aayan, haƙiƙa duk girman sharri gaskia sai tayi halinta wataran, yanzu gashi nida kakanka muna danasanin abinda muka aikata na yanke hukunci acikin fushi”

hannu yasa ya sharema Abie hawayen daya zubo masa yace, “ya mahaifina ina so ka manta komi domin duk abinda ya faru a baya ya wuce, bakuyi laifi ba domin irin wannan hukuncin ya cancanceni sai dai laifin ku ɗaya da kuka yanke hukunci batare da bincike ba”

“hakane Aayan amma duk da hakan ka yafe mani kaji masoyina… insha’Allahu kaman yanda mai martaba yace yau za’a yankema yarinyar hukuncin don yanzu haka ana fada an taru gaba ɗaya ,jiran farkawarta kawai ake wanda nan da minti 30 allurar dake tasiri ajikinta zata barta”

ya zaro ido yana kallon Abbie kamin ya maida idonsa kan diamond wristwatch ɗin dake hannunsa.

saura mintina 28 ya rage,Abie ya matsar daga kusa dashi ya ture driver ya shiga ya tada mota. datse haƙoransa kawai yake yana mai jin kaman ya tashi sama saboda nisan dake tsakani zuwa masarauta.

yankar motoci kawai yake, banda securities ɗin dake biye dashi da ƴan sanda zasu iya kamashi saboda ya saɓa ƙa’idan tuƙi.

tabbas wani abu ya sami Angel bazai ƙyale kowa ba, mugun gudun da yake a minti ashirin ya iso ƙofar masarautar, bai jira da an wangame masa ƙofa ba ya fito da sauri ya faɗa gidan da gudu.
kasancewar Abie yayo waya ya sanar tini dogarai suka bi bayansa, kai tsaye fada ya faɗa, wata supa yaja ya tsaya lokacin daya shiga ciki, numfarfashin dake fita daga jikinsa kowa na iyaji.

hango Raihana dake kwance kan carpet dake shimfiɗe ƙasa yasanya ya ƙarasa wurin da sauri, zaro ido yayi duba da yanda ya ganta da uban tabbuna ajiki da dukkan alamu ta jibgu da duka.

ɗagowa yay ya dubi dubban al’ummar dake cikin fadar, tini jijiyoyin jikinsa suka bayyana tamkar zasu fito waje idonsa ko launin daya sauya baza’a kirashi da ja ko kore ba sai buɗa hanci yake yana fitar da zazzafan numfashi.

leɓensa ya cije ya daki ƙasa wanda saida wurin ya amsa gaba ɗaya…cikin ɓacin rai mai martaba ya miƙe tsaye yace, “kaiii”

kansa na ƙasa bai ɗago ba dan bin tabbunayen jikin Raihana yake da kallo yana ƙirgesu, tabbas babu wanda zai hanashi yima wanda yay ma Angel ɓalliɓalli a duk sassan jikinsa.

“Khaleed Bin Mourad”
Mai martaba ya kira sunan nasa muryarsa ɗauke da ɓacin rai.

bai amsa ba kum abai ɗago ba yasa hannu ya sunkuci Raihana, miƙewa yay da ita yaƙi ɗago ya kalla inda mai martaba ma yake.

cike da jin haushin kowa na wurin ya juya yay hanyar fita ,yasa ƙafa a ƙofa ya dkaata da fitar tare da faɗin, “idan har wani abu ya sameta ,to bazan bar kowa ba, zan tada ta’addancin da aka sami salamarsa shekaru biyar da suka wuce”

dagama faɗin haka ya fice, bai bari an tuƙasa ba dan yana ganin ɓata masa lokaci za’ayi.

yana tuƙi yana dubanta yana kiran sunanta ,”Angel open your eyes plsss, dan Allah karki ce mani wani abin ya sameki ,ki farka gani gareki, wlh na maki alƙawarin babu wanda zan bari acikinsu “cikin ruɗewa da tashin hankali yake maganar yana faman girgiza fuskarta, ƙiris ya rage yay accident saboda sakin stearing da yay ya taɓa artery ɗinta yaji ko tana motsawa amma sai yaji shiru. +

ƙara ya ƙwala tare da ƙara kiran sunan nata, “Angellll ” ya fashe da kuka yana damƙe da hannunta

duk nisan Alkhalil hospital amma cikin kaɗan ɗin lokaci ya isa, ragaraga yay da motarsa saboda bai tsaya jiran an wani buɗe masa gate ba banka motar kawai yay kaman a film.

ko kashe motan baiba ya fito ya ɗauketa yay cikin asibitin da ita sai kiran sunanta yake ba ƙaƙƙautawa.

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

YAREEMAH KHALEED CHAPTER 6

Advertisements _____ YAREEMA KHALEED CHAPTER 6 da zallar ɓacin ran kalamanta Abibi ya nufi inda …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *