[Advertisements⬇️]

WANENE SHI CHAPTER 9 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WANENE SHICHAPTER 9
Another day…
without your smile.
Another day…
just passes by.


But now i know, how much it means.
For you to stay right here with me.

The time we spent apart will make our love grow stronger.
But it hurts so bad I can’t take it any longer…
I wanna grow old with you….. 1

Wakar ta katse a daidai nan sakamakon kiran daya shigo cikin wayar. yadda ya tallafe bayan kansa da duka hannayensa biyu ya masa dadi, saboda haka bai ko motsa ba har kiran ya katse.

Yana kwance ne akan irin dogwayen kujerun nan na bakin beach, yana jin iskar wajen mai sanyi da dad’i na kad’a kowanne particles na gashin jikinsa, ya mak’ala earpiece a kunne sannan idanunsa a bud’e yana kallon adon taurarin dake haskawa a samansa.

Adonsu mai kyau, yadda suke shining akan black universe d’in samansa. ya had’e dogwayen gashin idanunsa waje d’aya sannan ya sake bud’e su, taurarin na da kyau, idonsa ya gane masa kuma kwakwalwarsa ta fad’a masa, amma hakan ya kasa tafiya cikin zuciyarsa.

Zuciyarsa da ta kasa nutsuwa tun zuwansa k’asar nan. sati hudu kenan, sati hudu yazo da niyyar hutu amma abin ya zama kamar yazo ne don ya samu isashshen lokacin da zai dinga tunaninta. tunanin wadannan idanun nata.

Ya salam! me yasa ne ya dawo da wannan tunanin, a d’azu har a sallarsa yayi wa Allah alk’awarin ba zai sake kawo ta a ransa ba, amma awa biyu kad’ai ta karya hakan.

Fararen idanun nan nata masu kamar an zuba musu madara, su suka fara jan ra’ayinsa gareta. Bayan ya samu ya takura kansa ya rabu da ita kuma k’addara ta sake hada su, a yanzu kuma da k’addarar ke shirin sake had’a su, so yake ya ture wannan intrest d’in daya samu akanta tun baya, baya so ko kad’an ya sake dawowa cikin kansa.

Don abinda zai had’a su d’in na dan lokaci ne kawai, kuma da komai yazo k’arshe zai fita daga rayuwarta ne har abada, Abada wadda bata da k’arshe. Saboda haka yake k’ok’arin hana kansa jawo musu wata matsalar.

Don shi kansa zaman da zasu yi tare ma wani k’alubale ne da sai yayi mutuk’ar taka tsantsan da kansa. halittarta da tasa ba d’aya bace, in dai yana tare da ita dole ne sai koyaushe hankalinsa ya zamo hundred percent a tare dashi, in ba haka ba zai iya mantawa ko wajen rik’e hannunta ko tab’a kyawawan idanunta, ya rik’e ta da karfi irin nasa da zai sa k’ashinta ya rugurguje. 2

Ya salam! me ya same shi ne kuma? yanzu ya gama yiwa kansa fad’an tunanin idanunta yanzu kuma ya koma tunanin rik’e ta? me zaisa ya rik’e ta? auren da zasu yi ba na gaske bane, zai aureta ne don samun kariyarsu su duka biyun ba don wannan shirmen da zuciyarsa ke kawo masa ba.

Dole ne ma tun a yanzu ya nemi hanyar da zai nesanta zuciyarsa da ita, ko don ma jaamil. ya tuno maganganun da suka yi na karshe kafin tahowarsa nan.

Komai zai tafi mana daidai yarima, dama a lokacin da na kawo zancen nan, tsorona d’aya ne na yadda zamanku zai kasance.

Don yadda kake da intrest akan yarinyar nake tunanin zaka iya jawo mana wata matsalar, ko a lokacin zamanku ko kuma a lokacin da zaman zai k’are. amma tunda ka tabbatar min da baka sonta hankalina ya kwanta, na tabbatar baza ku sami matsala ba.

Ya rufe idonsa sanda ya tuno hakan, yasha gayawa jaamil abubuwan da yawa wanda yake nufi da gaske amma baya yarda dashi, sai a lokacin da ya gaya masa wani abu da shi kansa bai tabbatar ba sannan kuma ya yarda.

Don shi kansa a lokacin daya fad’awa jaamil cewa baya son Sa’dha, yayi amfani ne kawai da kalmar don a tunaninsa hakan zaisa jaamil yace ya fasa wannan shawarar. Saboda tun lokacin da ya fad’a masa ita, hankalinsa ya kasa nutsuwa don bai yarda da kansa in yana tare da ita ba, bai yarda da zuciyarsa ba.lokacin daya sake bud’e idonsa akan taurarin, sai yaga kamar ansa hannu ne an jera su cikin wani tsari da yayi kama dana fuska. fuskar mutum d’aya a duniya wadda ya tab’a jin irin wannan abin game da ita. Gimbiyarsa
Sareefa, ‘yar uwarsa kuma ‘yar uwar halittarsa dake can wata nahiya tana jiransa. +

Ya kamata yayi wa kansa fad’a, Sa’adha ba abokiyar rayuwarsa bace, zata shigo ciki ne kawai kuma ta wuce a lokaci daya. kamar mutum ne ya shiga d’aki mai kofa biyu, ya shiga ciki ya fita ta d’ayar kofar ba tare da tsayawa ba.

Saboda haka ya san zai daure, shi ba matsoraci bane kuma bai tab’a tsoron wata gwagwarmaya a rayuwarsa ba, yana fuskantar komai da kwarin gwiwarsa kuma ya tsallake shi. me yasa yanzu zai damu kansa da tunani akan Sa’adha?

K’arar tsinin takalman dake taka floor din da akayi na katako ya ziyarci kunnensa, kuma ya san waye ba tare da ya bud’e idonsa ba. a sati na hudu da yazo wajen nan don hutawa ba zai iya k’irga iya adadin matan da ya ture daga hanyarsa ba, wasu sun hakura wasu kuma har a yanzu suna cigaba da nacinsu.

Wadda take tahowa a yanzu sunanta, Kathy, kwananta hud’u kenan da fara aiki a hotel d’in da yake, kuma kamar sauran tunda tazo take fatan kawo kanta gare shi.

“Hello, my name is Kathy, and i’m the server tonight. What can i get you to drink?”

Muryarta ta fad’a daga gefe, wai bata fahimce cewa ta fad’a masa sunanta wajen sau biyar bane?

Ya bud’e idanunsa a hankali ya kalleta.

“Nothing.” ya fad’a da muryarsa mai zurfi.

Sai da ta d’auki ta wasu sakanni kafin ya lura ta fahimci me ya fad’a, kamar ta tafi wani tunanin daban. Tayi murmushi da sauri sannan tace.

“Okay, but if you ever change your mind…”

Sai ta fito da wata ‘yar paper daga dan k’aramin aljihunta na gaba ta dora akan jikinsa. sannan tayi murmushi ta juya.

Imran ya bita da kallon mamaki, kodayake ba abin mamaki bane inda ya bar kansa tun farko yaji me tunaninta ke cewa. A lokaci daya al’adar bahaushe musulmi ta burge shi, ya hango tarin matan dake damuwa dashi, ko kuma da siffarsa data fi kama da tasu, amma babu wadda ta tab’a fito masa kirikiri da bukatarta, sai dai ‘yan kewaye-kewaye kawai.

Ya godewa Allah da dalilin zuwansa cikin mutane bai kasance a cikin turawa ba, wayarsa ta sake katse sabuwar wak’ar dake playing.

Ya mik’e zaune sosai, iskar dake kad’awa ta d’auki paper tayi wani waje da ita. yana sliding answer button muryar jaamil ta shiga cikin kunnensa.

“Me ya same ka yarima?”

Maimakon ya amsa masa sai yayi murmushi mai k’ara sannan yace.

“Wallahi kullum kara komawa more human kake, its a miracle, yau kaine ke kirana a waya?”

jaamil yaja tsaki sannan yace.

“Ba dole in kiraka ba, na duba duk inda nake tunani ban ganka ba.”

“Kamar yaya? ba na gaya maka inda zani ba?”

“Ko dai ka fada min inda zaka je da farko, don gani a k’asar Bulgaria d’in kuma baka cikinta.

Imran ya cusa yatsunsa cikin gashin kansa da iska ke kad’awa.

“Oh my god, na manta ban fad’a maka bane, ina maldives sanyi ne ya koreni daga bulgaria kwana na d’aya.”

“I don’t care, yaushe zaka dawo?”

“Yaushe zan dawo? gaskiya ba rana. I have almost 2 weeks a cikin leave d’ina fa, meya faru?”

“Komai ma ya faru, lokacinmu ya k’are sannan ciwon yarinyar na shirin dawowa.Sai da numfashinsa ya d’auke jin jaamil ya fara maganar sa’adha, sati hud’u kenan yana hirar ta a zuciyarsa amma bai furta ko sunanta a fili ba.

Daga d’aya bangaren jaamil ya rage sautinsa sannan yace.

“lokaci yayi yarima, ina fata ka shirya.”

*******

From the first time i met you…

There was something about you
I can never forget the way you thief my heart.

I didn’t try to pretend you
I ain’t like gonna send you
But i know like we’re friends too.

Cuz you gave me a spark
I just can’t help myself,
I want be your all
And i see no one else….

“Rahma dan Allah kashe wak’ar nan…”

Nanne ta fad’a lokacin da take goge tv da tsumma a hannunta.

“Me yasa? wallahi ina son wak’ar duk da dadewarta.”

Bata ce komai ba sai ta d’auki bokitin ruwan omon dake kusa da k’afarta ta matsa jikin window ta fara goge shi.

“Anya fa su inna yau zasu dawo, nifa banji kowa yace suna hanya ba?”

Rahma ta fad’a daga gefe inda take jera tarkacen inna cikin wata cupbaord. kwanan inna biyu kenan a niger, tun shekaranjiya suka tafi ita da baffa kuma a yau ake sa ran dawowarsu. A kwana biyun kuma Rahma tana tare da ita, tare suke kwana a dakin kuma tana iya kokarinta wajen ganin ta saki jiki suna harkokinsu tare kamar da amma bata iyawa, ko ta fara sai tunani da yawa yazo ya danne sukuninta.

Musamman a yanzu da tunanin dalilin tafiyar Inna da Baffa yafi damunta, wani abu ne da bai tab’a faruwa ba, in dai za’a je niger toh kusan rabin gidan ake tafiya a tare. amma yanzu daga su sai direban Baffa kawai suka tafi. kuma bata san me yasa ba, tana danganta tafiyarsu ne da lamarinta.

“Dazu kina wanka, Mama halime ta shigo tace sun taho.”

Ta amsa mata a hankali.

“Toh Allah ya kawo su lafiya, in munyi sallah zamu je gidan Sumayyan?”

“Eh zamu je, na gayawa Mama Azumi ma zamu fita.”

“Yawwa kinga sai mu tsaya in kai….”

No one else can do the things that
You do for me…

I wanna be there for you
Baby i really love you.

There is something about you that i cannot explain…

Wak’ar ta sake shigowa cikin kanta ta ture k’arshen maganar Rahman, sai kawai ta ajiye tsumman hannunta da sauri sannan ta nufi kan kujera ta lalubo wayar ta kashe.

“Na gaya miki bana son wak’ar nan.”

Rahma ta juyo ta kalle ta, da gaske ne abubuwa da yawa sun canja game da Nanne, abubuwa da yawa da bata sansu ba bata kuma tab’a tunanin zasu faru kanta ba.

Bata k’ara cewa komai ba har suka gama aikin. ta zubo musu abinci suka ci sannan ta tattare kwanukan da niyyar sauka dasu k’asa. Sai dai bata kai bakin k’ofa ba wayar inna da bata tafi da ita ba ta shiga ringing a kusa da Nanne wadda ta baje magungunanta tana k’ok’arin sha.

Nanne ta kalli wayar a gefenta, bata san number ba, don haka ta barta ta gama rurinta sannan ta tsinke. bada dad’ewa ba aka sake kira, sai tayi tunanin ko inna ce tace a kira ta, tunda basu yi waya ba kuma ance sun taso.

“Assalamu Alaikum.”

Imran ya rufe idonsa a hankali jin yadda muryarta mai sanyi ta ratsa jikinsa.

“Wa’alaikum salam.” Shima ya amsa ba tare da ya bud’e idonsa ba.

A lokaci d’aya bugun zuciyarta ya tsaya, me yasa a kullum taji muryarsa take jin kamar wata murya ce data sani tun farkon rayuwarta, sab’anin sanin data yi masa na ‘yan watannin baya ne kawai?

Mamaki ya kamata, ta cire wayar daga kunnenta ta kalli numbar, da gaske imran ne ya kirata? imran d’in data sani? bayan tarin kwanakin da suka wuce ba alamarsa?

Ta maida wayar a hankali kunnenta.

“Zan iya ganinki gobe?”

Muryarsa ta sake ratsa cikin kanta, ta juya ta kalli kofa inda Rahma take tsaye, babu kowa a wajen.

“Me za’a yi?”

Tana iya jiyo sautin murmushinsa daga daya b’angaren kafin yace.

“Hak’uri zan baki na tarin laifukan dana yi.”

Nanne taji kanta ya fashe a lokaci d’aya. ita zai bawa hakuri.

“Laifin me kayi?”

“Suna da yawa, kuma in kika bani dama duk zan zayyano su duka da reasons d’ina.”

Sai ta gyara zamanta, yatsunta na kanannad’e ledar dake gabanta.

“May be da yamma?”

Wannan karon sautin murmushinsa ya k’aru.

“Baki tabbatar ba?”

Ta lumshe idanunta sannan tace.

“Na tabbatar, Allah ya kaimu.”

“Ameeen…”

Yaja Ameen d’in da d’an tsawo, sannan yace.

“…Nagode sosai.”

Maimakon ta amsa sai kawai tace.

“Sai anjima.”

Har ta cire wayar daga kunnenta, muryarsa ta katse ta.

“Sa’adha…”

Me yasa ne wai ya iya fad’ar sunanta fiye da kowa? bata ce komai ba amma sautin numfashinta ya tabbatar masa tana jinsa.

“Thank you!”

Dib! wayar ta katse.

Ta cire wayar ta kalli screen d’in, da sauri kuma ta shiga call log don ta sake tabbatar ba tunani take ba.

Sannan ta d’ago da ta kalli agogo.

K’arfe uku da rabi.Wajen cikin daji ne, dajin da bata tab’a zuwa cikinsa ba, amma somehow sai take jin kamar ta san wajen, kamar ruhinta ya tab’a zuwa…kamar wani waje ne da yake rik’e da wani tarihi na rayuwarta. +

Inda k’afafunta suke tsaye fili ne kuma daga gabanta akwai tarin bishiyu, tarin bishiyun da take ganin kamar abinda tazo nema yana cikinsu ne.

Sai dai tana motsa k’afafunta, taji muryoyi da yawa na kiranta daga baya, muryoyin da ta kasa tantance su, kuma da yawa sunanta suke kira. ba tare da ikonta ba taji k’afafunta sun cigaba da tafiya wajen bishiyun nan, kamar tana zaune akan wani abu ne ana tura ta gaba.

“Nanne..!”

muryar inna ta fito daga cikin muryoyin nan, daga nan kuma sai ta fara tsintar sauran, akwai ta Rahma, Baffa, Sadiq, Amina, Mama halime, Mama Azumi, ya sulaiman da kusan rabin ‘yan gidansu. kowannensu yana kiran sunanta da alamun gargad’i

Taji tana son juyawa taga kiran me suke mata, don a yadda take jin muryoyin kamar bata yi nisa dasu ba, sai dai kafin ta iya juyawa ta hango shi.

Imran ya fito daga cikin bishiyun nan yana kallonta da lumsassun idanunsa, kamar koyaushe yayi wani irin kyau sanye da light kaya, fuskarsa ta haska, sannan kyakkyawan murmushinsa ya kwanta sosai a gefen fuskarsa, sai da ta shagala da kallonsa sannan ya d’ago yatsansa guda d’aya yayi mata alamun ta biyo shi sannan ya juya ya koma cikin bishiyun. k’arar muyoyin suka k’aru a cikin kanta.

Amma sai taji duk basu dame ta ba, bata damu taje wajensu ba, bata damu ta san kiran me suke mata ba. Tafi son ta k’arasa wajen Imran, ta tambayeshi tarin abubuwa da yawa da suka shige mata duhu, abubuwan da take son sani game dashi.

Taku daya kawai ya shigar da ita cikin duhun bishiyun, amma sai wajen ya zama sab’anin tunaninta, a maimakon duhu wajen mai haske ne da kuma kyau, korayen ciyayi da fulawowi sun baje a koina, ga wani dutse daga can gefe yana zub da ruwa.

Taji wani ya rungumeta ta baya, hannayensa sun zagaye k’ugunta sannan ya d’ora hab’arsa a daidai lungun wuyanta, ko bata juya ba ta san Imran ne kuma zuciyarta ta riga ta nutsu dashi, saboda haka ta cigaba da tsaiwa ba tare da ta juya ba tana jin d’umin jikinsa akan fatarta da kuma yadda numfashinsa ke busawa a k’asan kunnenta.

A lokacin ne abin ya faru, taji an caka mata wani abu mai tsini a wuyanta, abin ya huda tun daga farkon wuyanta ya fito ta d’aya gefen.

Numfashinta ya tsaya cak, sannan jini ya shiga gangarowa kan fatarta, tayi k’asa ta fad’i da baya sannan zafi ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinta, taji ruhinta na barin jikinta a hankali sannan idonta na shirin rufewa.

Amma kafin komai ya d’auke mata, fuskar Imran ta shigo cikin ganinta, yana tsaye akanta da wannan murmushin dake murkushe zuciyarta, sannan hannayensa na d’igar da jini!

Nanne ta farka da wata irin ajiyar zuciya mai k’arfi idanunta a zare, wayar inna dake gefenta ta fad’i k’asa ta gangara wajen dressing mirror.

Ta juya kowanne b’angare ta kalli wajen da take, cikin d’akinsu ne ba wani waje ba, Rahma na kwance a kusa da ita tana baccinta hankali kwance, ta kalli agogon dake saman dressing mirror.

K’arfe uku da rabi na dare.

Ta koma da baya ta kwanta akan filon, sannan ta shiga tofa adu’o’i a jikinta, amma har kusan mintuna ashirin baccin yaki dawowa, Sannan hankalinta ya kasa kwanciya, tunanin mafarkin ya cika kanta, saboda haka ta mik’e ta shiga toilet ta d’auro alwala da niyyar sallah.

Tana fitowa idonta ya kai kan wayar inna dake k’asan mudubi, ta sunkuya a hankali ta d’auka, hannunta ya shiga call log ta lalubo number da Imran ya kirata jiya, tana nan rad’au a rubuce ba’a tunaninta ne komai ya faru ba, idonta ya kai kan time d’in da kiran ya shigo.

K’arfe uku da rabi na rana. 1

A lokacin fuskarsa ta cikin mafarkin nan ta sake haskawa a idonta, da sauri ta ajiye wayar gabanta na fad’uwa, me mafarkin ke nufi? wannan kiran dasu inna ke mata, wannan murmushin imran din sannan yadda ya rungumeta, yadda take jin numfashinsa a wuyanta kamar gaske da kuma sanda ta fad’i k’asa, ta hango hannayensa da jini?Jini? jinin waye? ita dai ta san taji zafi a wuyanta amma bata ga fitowar jini ba. +

Ta rufe idonta a hankali sannan ta bude su akan mudubin dake gabanta, idanunta sunyi zuru-zuru kamar tayi kuka.

Ta k’iftasu a hankali tana k’arewa yanayinta kallo, a sannan ne abin ya faru, a sannan ne gabanta ya fad’i sannan dukkan tsoro ya shigeta.

Ganinta ya koma dishi-dishi, sannan wani hayak’i ya fito daga rabin fuskarta ya tarwatse a iska!Wai Rahman ta tafi ne?” +

Inna ta tambaya tana kallon Nanne dake kokarin sa hijabinta, a lokacin karfe bakwai da kwata na safe.

“Ta tafi tun d’azu kina sallah, zata je makaranta ai.”

Ta fad’a a hankali, saboda kanta dake tsabar ciwo. Tun bayan lokacin data farka daga mafarkin nan da kuma abinda ta gani a cikin mudubi.

Bata san iya adadin sallar da tayi a lokacin kafin gari ya waye ba sannan ta iya samun nutsuwa.

“Amma kuwa Rahma bata kyauta ba, ga tsarabarsu tun jiya na ware tana kallo shine zata tafi bata fad’a ba.”

“Inna zata dawo ai, ga kayanta ma fa bata d’auka ba.”

Nanne na rufe bakinta ta jiyo horn d’in idris daga compound saboda haka ta d’auki jakarta tayi waje tana fad’in na tafi.

“Yau kar ki tsaya wannan lesson d’in naku, ana tashi ki biyo su safiyya ki taho.”

Daga k’afar bene ta amsa da toh ba tare da tayi la’akari sosai da abinda innan tace ba.

A makaranta gabad’aya bata da walwala, duk da cewa kusan kwana biyu haka take amma yau ko hirar da take dagewa suyi da Amina ta kasa, tunaninta ya rabu kashi kashi, ga azabar da ciwonta yake sannan ga tsoron mafarkin da tayi a jiya da kuma fuskar da ta gani a mudubi, don ta tabbata taga wani abu kamar hayaki ya fito daga fuskarta, ta shafa wajen a hankali tana so ta cusawa zuciyarta cewa ba da gaske bane.

Sannan ga Babban abun dake gabanta a yau, zuwan Imran wajenta, mafarkin da tayi ko kad’an bai girgiza zuciyarta akansa ba, ji tayi ma ta k’agu sosai yazo ya warware mata tarin k’ullin dake cikin kanta game dashi. Amma kuma bata san ya zasu had’u ba don ko Rahma bata gayawa zancen kiran da yayi mata ba, amma ta san in har zai zo d’in zai gaya mata lokaci.

Ta kwanta akan bencinsu sanda ajin nasu ya rud’e da surutu sakamakon rashin shigowar malami a last period d’in da suke da ita, wasu sun had’a group-group suna ta hira wasu kuma na daga can gaban ajin suna kid’a da benci suna rawa, a cikin masu rawar harda Amina, saboda haka ita kad’ai ce a row d’insu dake can k’arshe, kowa ya tafi harkarsa.

Ta rufe idonta a hankali tana sauraren wak’ar sa’adu zungur da masu rawar suka had’a baki suna yi. 1

Haba yarinyar nan…dan Allah juya, idan baki juya ba…kinci amanata, mai abin dad’i kawo eh mara abin dadi ko….

Sai da aka kad’a k’ararrawar tashi sannan ta tuna da abinda inna tace mata, saboda haka ta yiwa Amina sallama ta fito tare da wad’anda basa yin lesson d’in. Zuciyarta cike da tunanin me za’ayi a gidan da inna tace ta dawo da wuri, amma har suka koma bata hango wani abu da ake shirin yi ba tun dawowarsu innan a jiya da rana.

Sanda ta shiga d’akinsu, Mama Azumi na zaune suna magana da inna wanda shigowarta yasa dukkaninsu sukayi shiru sannan Mama Azumin ta mik’e tana fad’in wa inna sai anjima zata shigo.

Bata nuna komai ba ta gaishe su sannan tayi d’aki, ta fad’a toilet tayi wanka da ruwan zafi sosai don ta samu k’arfin jikinta, har a kanta ta dinga kwarawa ruwan da fatan zai wanke tunanin wannan mafarkin da tayi.

Ranar Alhamis ne saboda haka ta zura doguwar rigar wani light material ta fito falo.

“Nanne k’araso nan magana zamu yi.”

Inna ta fad’a ganin tana shirin zuba abinci, ba musu ta rufe flask d’in sannan ta dawo ta zauna a kusa da ita.

“Ina so ki nutsu sosai ki saurareni da kyau, abinda zan fad’a ba neman ra’ayinki nake ba ko son jin shawarki, abu ne da manyanki sun riga sun gama yanke komai kuma in ba wani ikon Allah ba, ba abinda zai sa a canja shi.”

Nanne ta tsura mata ido kawai tana jiran kalamanta na gaba, don ta tabbatar ita a yanzu babu wani abu da zai sake girgiza zuciyarta.

“Tafiyar da muka yi nida baffanki akan maganar ki ne.

Ni ban san yaushe kuka shirya da yaron nan ba don baki gaya min ba amma bayan baffanki ya tara mu akan zancen rashin lafiyarki yaje wajensa da sati biyu, ya nemi izinin zuwa wajenki amma baffan yace masa ya dakata tukunna. sai da yayi bincike akansa ya tabbatar da halayensa sannan yace dashi ya turo iyayensa.

Toh wani abu na ikon Allah kuma bayan sun zo, sai suka nuna cewa shi yaron ya shirya kuma da wuri suke son ayi auren duk da haka baffa bai tsaida wata magana ba sai bayan sati guda da suka dawo, anan aka tsayar da lokacin aurenki nan da wata guda kamar yadda shi baffan yace ko kafin nan ko kun k’are jarabawar wane ne term oho… +

Yana gaya min zancen nan na d’aga hannu na godewa Allah, don dama ni inda nake tunanin yin magana sai in har ya had’a ki ne da wanda bamu sanshi ba, toh shine zance a d’an dakata mu dake mu fahimci halinsa tukunna. Amma tunda har Allah yasa an sanshi kuma shima baffan ya yaba da hankalinsa shikenan nayi shiru da bakina.

Don haka zuwan da muka yi niger, mun tattauna ne da duk ‘yan uwan mahaifinki kuma Alhmdlilahi kowa yaji dad’in zancen wallahi.

Abinda yasa nace ki dawo da wuri kenan yau, don yace zai zo ku gana kuma na san kema ya gaya miki.”

Nanne taji ta zama kamar gunki ne zaune a wajen, abu na farko daya d’aure mata kai shine, tana cikin gidan nan har ake jelan zuwa neman aurenta bata sani ba? don ita baffa kawai ya gaya mata cewa yana bincike akan wanda ta turo wajensa ne amma ko Addano bata kira ta tace mata har iyayensa sunzo ba.

Sannan ita ta zaci baffa ko inna zasu nuna rashin amincewarsa akan cewa Nuran daga dangin mahaifiyarta yake sai gashi har komai ya tafi daidai an tsaida ranar aure wata d’aya? wata d’aya kawai?

Sannan zai zo wajenta yau? ita bata shirya ba, tana bukatar lokaci amma ba yadda ta iya, tunda inna ta fad’a mata tun farko cewa bata da zab’i abinda zata fad’a mata umarni ne kawai, muryarta na rawa tace.

“Amma inna ba wanda ya fad’a min duk wannan abubuwan da suke faruwa ko ita kanta Addano bata kira ni ba.”

“Nuratu kuma? yo ina ruwanta da wannan sha’anin? koko bamu da ikon mu yanke abu akanki sai da izininta? tunda ita kad’aice me iko dake? toh bari kiji kalma d’aya akan lamarin nan bata sanshi ba kuma habu abinda zai canja, ban k’i ba dai yanzu da aka yanke lokacin a gaya mata.”

Cike da mamaki Nanne ta kalleta tace.

“Inna na san dole zata sani ai tunda wanda kuke zancen akansa d’an uwanta ne.”

“Ban gane ba, Imranan ne d’an uwanta? toh ni a yadda baffa yace min game da asalinsa banji wata dangantaka data had’a shi da adamawa ba.”

Wani irin bugawa zuciyarta tayi, gabanta ya fad’i, sannan kwakwalwarta ta yanke daga fahimtar komai, me inna ke cewa? wane Imran d’in take nufi? wane Imran d’in ne yazo neman aurenta? watak’ila dai mafarki take irin na jiya, kuma zata iya farkawa a kowanne lokaci, saboda haka ta tsura mata ido kawai ta cigaba da kallonta kamar wadda kammaninta suka canja gabadaya.Sai dai kafin k’arfe biyar na yammacin ranar, inna ta tabbatar mata da cewa da gaske imran ne yaje wajen Baffa neman aurenta kuma har an amincewa iyayensa an bashi ita.

Ta zauna tayi mata bayani sosai akan cewa ba ita ta tura shi wajen baffa ba, ita irin wannan maganar ma bata tab’a had’a su ba amma inna ta kasa fahimtarta, zance d’aya kawai take maimaitawa cewar ai daman abinda ya dace kenan a shari’ar musulunci, a fara tuntub’ar iyayen yarinya kafin ayi mata magana, kuma gwara shi akan baffa ya bada ita ga d’aya daga cikin ‘ya’yan abokansa da bata san ya suke ba, tunda dai ko babu imran aurenta ba zai d’auki lokaci ba.

Ta san cewa a zuciyarta tana son imran, amma yanzu da kawai maganar aure ta shigo tsakaninsu, bata san yaya zuciyarta zata dauki abun ba. bata san me ya kamata taji game dashi ba, tunda shi bai taba fad’a mata yana sonta ba, kuma a tsawon lokacin daya kai kansa wajen baffa bai nemeta ba, yayi amfani yawunta ya gabatar da kansa, sai a jiya daya san zai zo yau sannan ya kirata a waya, ita kuma ta kasa daure zuciyarta ta ja ajinta, kawai ta amince da zuwan nasa.

A sannan ne kuma ta san abinda inna da mama Azumi ke tattaunawa sanda ta dawo daga makaranta, kayan tarba sosai aka had’a masa na snacks da lemo har kala biyu, don ta hango su a hannun lami sanda ta shigo d’akin karb’ar muk’ullin falon waje da aka sa su halliru suka share.

“Nace miki ki maida wannan rigar ko? ina hankalinki yake tafiya ne wani lokacin?”

Inna ta katse tunaninta, ta juya ta kalli rigar da ta d’auko, ash doguwar riga ce mai kama da abaya sannan mayafinta yana had’e da d’an k’aramin hijabi a jikinsa. ita bata ga abinta tayi ba da inna zata ce ta mayar, kuma ma ai ita ta siyo mata a makka, in har bata da kyau me yasa ta d’auko mata.

Kamar tayi magana taga yanzu sai inna ta fassara zancen da wata ma’anar, saboda haka ta cukwuikuye ta mayar, ta d’auko riga da skirt na atamfa coffee da milk da kuma dogon hijabinta mai hannu milk.

“Su zaki sa?”

“Inna meye laifinsu to dan Allah, shifa bata shigata yake ba, tunda har zai iya zuwa neman aurena ba tare da amincewata ba na tabbata shigata baza ta sa ya fasa ba.”

Ta saka kayan kamar gaske sannan tayi waje, ta tsakanin k’ofar gate d’in ta hango shi.

Yana tsaye daga jikin motarsa yana danna waya, sanye cikin wani milk yadi wanda ya kwanta akan fatarsa sosai, yana da d’an shara-shara kad’an don har ana iya hango layin singlet d’insa dake ciki, sannan yasa hula mai kyau kalar brown shigen aikin dake jikin kayan da kuma takalmi k’afarsa, zata iya rantsewa a rayuwarta tab’a ganin halitta mai kyau irinsa ba,

Zuciyarta tayi nauyi da tunanin cewa wannan jiran da yake nata ne, abinda tayi mafarki da tunaninsa fiye da cikin k’irga a baya, sai gashi a yau yake faruwa, yau d’in da komai ya cakud’e mata.

Tunaninta ya tsinke, taji kamar baza ta iya bin shawarar data yanke ba, amma in har bata yi ba, ta san sai tayi regretting  hakan daga baya sau cikin carbi.

Tayi baya ta koma ciki sannan ta kira wani hanif d’an wata mai aikinsu dake wasa a gefe tace masa.

“In ka fita gate d’in nan zaka ga wani mutum a jikin mota kaje kace masa wai ance sa’adhan bata nan.”

“Yaron ya d’an kalleta.

“Wace ce Sa’adha?”

“Nima ban santa ba a gidan nan take kuma bata nan, kaje ka fad’i abinda naka gaya maka.”

Ta tsaya tana kallon tafiyar yaron, kowanne taku d’aya da yake ji take kamar taje ta jawo shi tace ya koma ta fasa ta fita wajen imran d’in dake jiranta. Amma kuma tunanin ya danne-danne abinda zuciyarta ke so, saboda haka tana gani har yaron ya fita ya rufe gate d’in sannan ta juya ta koma cikin falon da akace ta shigo dashi.Bata tab’a tunanin cewa hannun mutum zai iya gyara d’akin ba tunda kusan kodayaushe a k’ulle yake cike da ku’ra, amma a yanzu yasha gyara tas! harda carpet aka shimfida da kuma wasu manyan tin-tin guda uku, sannan daga gefe turaren wuta mai dad’in k’amshi yana tashi a kaskonsa.

A tsakiya wannan farantin ne da ta hango a hannun lami cike taf! da duk irin snacks d’in da take so, a lokaci d’aya taji yawunta ya tsinke.

Ta koma gefe guda ta jingina da bango sannan ta cusa hannunta cikin lallausar sumarta kamar zata tsinto duk wata damuwarta waje. Har a lokacin kanta na ciwo sama-sama.

Komai ya cakud’e mata, kuma ta san ba sai ta fahimce su duka ba, abu d’aya ne kawai ya kasa shiga kwakwalwarta har yanzu, cewa Imran shine k’arshen duk wannan k’addarar tata.

Ta tuno da mafarkin data yi a jiya, mafarkin da su inna ke kiranta kar taje wajensa, a yanzu kuma su ke k’ok’arin had’a ta dashi, sannan wannan jinin hannun nasa sanda ta fad’i k’asa. sai tayi saurin ture wannan shi kuma, mafarki k’arya ne, ba zai tab’a zama gaskiya ba.

Ta dad’e zaune a d’akin kafin daga k’arshe ta janyo plate d’in nan ta cika cikinta dam, sannan ta kulle d’akin ta shigo cikin gida.

*******

Bayan ta idar da sallar magriba, ta cigaba da zamanta akan sallayar tana lissafo dukkan damuwarta ga jalla wata’ala, ta bud’e zuciyarta sosai ta rok’e shi akan Allah yasa duk abinda ke faruwa da ita ya zame mata alkhairi, tunda wani abu ne da baza ta iya canjawa ba.

Tana shafawa wayar inna ta shiga ringing, ta juya ta ga har a lokacin bata idar ba saboda haka ta d’auka ta kai kunnenta.

“Assalamu Alaikum.”

A lokaci d’aya, taji tunaninta ya tsaya cak!

Wannan muryar, wannan muryar  mai taushi ta cika kunnenta. taji tayi kewarta kamar ba’a jiya ne taji ta ba.

Calm down Sa’adha! just calm down!

B’arin zuciyarta mai hankali ya shiga bata warning.

“Waalaikum salam.” Ta amsa a hankali.

“Sa’adha kina lafiya?”

Bani da lafiya kuma hankalina a tashe yake imran, komai ya cakud’e min a lokaci d’aya, sannan ga al’amarinka da na kasa ganewa, ka san irin halin dana shiga a baya? kace min zakazo na jiraka har dukka hope d’ina ya kare ban ganka ba, me ya hana ka zuwa?  me yasa baka fad’a min kana sona  ba? me yasa ka tafi wajen baffa kai tsaye? sannan tsawon lokaci baka neme ni ba? in kowa yak’i fad’a min halin da ake ciki atleast i deserve an explanation from you, amma kaima ka share ni, sai a jiya kawai ka kirani, babu tambayar lafiyata balle wani explanation kace zaka zo wajena, ni kuma banyi tunanin komai ba na biye maka, sai a yanzu ka damu da sanin halin dana ke ciki? me yasa ma zaka damu? bayan ka riga ka samu go ahead akaina? a yanzu ko da yardata ko babu ka san ba zan iya fasa aurenka ba, saboda ko ba komai nima na san har yanzu wani side d’in zuciyata yana sonka…

Maimakon duk wannan sai tace.

“Ina lafiya, Alhmdlilah.”

This is clumsy. ta fad’a a ranta

“I’m sorry, ban tambayeki haka jiya ba.”

Huff. wannan kuma ya wuce.

“I’m so sorry sa’adha, na san ban kyauta miki ba, na san nayi abubuwa da yawa wanda ba haka ya dace ba…”

“Me ya hana ka zuwa ranar da kace min zaka zo?”

Tayi saurin katse shi, in har zata saurareshi gwara ayi komai tun daga farko, tana bukatar bayani da yawa.
Ya danyi shiru kafin a hankali yace.

“Sulaiman ne ya hanani zuwa wajenki sa’adha, ba’a ranar kad’ai bama harda duk sauran lokutan da ban nemeki ba.”

Taji wani k’aton abu ya fad’a daga zuciyarta, ya sulaiman kuma? ta ina ya shigo zancen?

“Tun ranar dana fara ganinki a k’ofar gidanku rayuwata ta canja, duk wani tsari da nake dashi ya ruguje, na zama ba abinda nake iya yi ba tare da tunaninki ba, tun ban fahimta ba har nazo na gane cewa sonki nake yi, irin son da zuciyata bata taba yiwa kowa ba.

Zan so in iya fad’a miki kuma ki fahimci irin son da nake miki sa’adha, duk sanda na rufe idanuna ke nake gani, in na bude su kuma sai inji ke d’in kawai nake son gani, duk da bana iya samun ganinki kullum amma i always feel your presence around me.
Every second, every moment, every hour, my eyes search for you only, call this love, craziness or the beat of my heart… it is all same for me. +

I love you very very much Sa’adha and i don’t want to lose you, ever!

Shi yasa a ranar dana ce miki zanzo naje na sami yayanki sulaiman na gaya masa damuwata, shi yace inje wajen baffa sa’adha, shi yace kar in neme ki na tsawon lokacin nan sai na samu yardar baffa tukunna. a duk tsawon lokacin ba mantawa nayi dake ba, ina ta fad’i tashin neman amincewar baffa ne har na samu ya saurare ni, don da farko yace min yayi maganar ki da wani d’an abokinsa ne.

Da Sulaiman da umar su suka yi ta min kokari a wajen baffa har na samu ya saurare ni, daga nan kuma yace zan iya turo magabata na, ko a lokacin na so zuwa in sanar dake komai amma sulaiman yace in bari inji me zasu tattauna tukunna.

Kamar yadda aka fad’a miki nima haka naji zancen sa’adha, bayan tattaunawarsu, sun yanke mana rana zuwa nan da wata guda kuma wallahi duk da bani na tambaya ba i’m more than happy.

Shi yasa jiya dana kira ki na kasa cewa komai…nace miki laifina da yawa sai nazo zan fad’a miki duka reasons d’ina, kuma nazo kika ce min bakya nan.”

Ya k’arashe zancen muryarsa can k’asa kamar k’aramin yaro.

Nanne taji duk wata jijiya a jikinta tayi sanyi, gabad’aya fushin da take ji game dashi yabi iska, maganganunsa kamar sun sa hannu ne sun yaye rabin duhun da take ji game dashi, bakinta ya k’ulle ta rasa me zata ce. sai ta jingina kawai da jikin gado ta dunk’ule jikinta waje d’aya.

Shiru ya biyo baya ba tare da yayi magana ba.

“I’m sorry Sa’adha, i’m reeeeallly sorrry, dan Allah kiyi hak’uri if i’ve hurt you in anyway.”

Yadda muryarsa ta fita a hankali da kuma zurfi, yasa taji kamar zata narke gabad’ayanta.

I’m so sorry nima da na kasa fahimtarka a baya, i’m sorry da duk wahalar da kasha akaina, i’m so sorry dana kore ka d’azu.

Ta ayyana hakan duk a zuciyarta, sannan ta sake k’ank’ame wayar a hannunta ba tare da tace komai ba.

“Sa’adha…”

Sai da zuciyarta ta buga da k’arfi jin yadda muryarsa ta nannad’o sunan kamar tun asali shi ya bada shawarar a rad’a mata.

“Na yarda kiyi punishing d’ina duk yadda kike so amma dan Allah kar kice kin fasa.”

“Na fasa me?”

“Aure na.”

Kalmar tayi mata nauyi sosai, don duk sauran dauriyarta ta tattare ne wajen yadda muryarsa ke shiga kowanne lungu da sak’o na jikinta.

“Na san ba zaki fad’a ba koh?”

A hankali ta daure tace.

“Baffa ya riga yayi magana ai ba zan iya masa musu ba.”

“Saboda Baffa ne ba saboda kema kina sona ba?”

Ta damk’e k’arshen hijabinta  da k’arfi  sanda sallamar sallar inna ta shiga kunnenta. jin tayi shiru yasa yayi murmushi sannan yace.

“Karki damu, zan koya miki yadda zaki so ni, for now wanda nake miki ma ya ishemu mu biyu.”

Taji maganganun suna shirin yi mata yawa a rana d’aya kawai da komai ya kwance mata saboda haka tace.

“Sai da safe.”

“Zaki kore ni? dan Allah sa’adha kar ki d’auki fushin nan da nisa, so nake mu sake komai afresh, in sanki sosai kema ki san ni.”

Tayi shiru tana cije lebb’enta na k’asa.

“Kinjiii….?”

Da sauri tace.

“Naji, sai da safe.”

“Ya na iya…sai da safe, Allah ya tashe mu lafiya.”

“Ameen.”

Tana shirin d’auke wayar daga kunnenta taji abinda ya d’auke numfashinta gabad’aya.

“I love you!” Nanne…?” muryar Rahma ta kira ta. +

“Mhmmm.” ta amsa halfway cikin barci ba tare da tunanin komai ba.

“Yau baccin me kike yi haka, sha d’aya fa ta wuce.”

Jin haka yasa ta bud’e idanunta da sauri ta kalleta.

“Da gaske kike sha d’aya?”

“Na gaya miki ma fa ta wuce, inna har ta fita asibiti nima shigowata kenan.”

Ta mirgina a hankali ta juya kan bayanta.

“Ni kaina ban sani ba, na dad’e banyi bacci irin haka ba.”

“An kawo miki sak’o yanzu wani yaro ne ya kawo daga waje, shi yasa ma na tashe ki.”

Nanne ta had’e girarta waje d’aya.

“Sak’o? meye a ciki?”

“Sak’o fa nace miki, ta yaya zan bud’e.”

Ta matsa jikin dressing mirrow ta d’auko wata brown leda k’atuwa mai logo d’in hannaye biyu.

“Kamar wani kwali ne a ciki.”

Nanne ta mik’e sosai akan gadon  ta karb’i ledar, tana bud’ewa taci karo da wani pink box medium size a jikinsa akwai large prints d’in flowers purple.

Ba tare da tunanin komai ba ta bud’e cikinsa, idanunta suka ci karo da ledoji na different kinds of chocolate, tun daga kan wanda ta sani harda wanda bata tab’a gani ba, gasu nan fal! a ciki.

“Lallai kayan dad’i ne ashe, daga ina haka?”

Rahma ta fad’a tana zama akan gadon, ita dai tayi turus! da murfin a hannu tana kallon su, daga can gefe idonta ya hango mata wata takarda ta janyo ta a hankali ta bud’e.

Sa’adha….!

Yau ina tashi da safe naji a News wai sugar yana kwantar da anger dake
jikin mutum, zaki taimaka kisha wannan ko zamu samu fushin da kike dani ya ragu?

Bata san lokacin da wani d’an guntun murmushi ya sub’uce daga fuskarta ba.

Bayan ta fito daga wanka ta zauna a gefen gado tana shafa mai tana kallon fuskarta ta cikin mudubi, akan mudubin wannan box d’in alawar yana facing d’inta.

Wayar da tayi da imran a jiya kawai ta wanke abubuwa da yawa a cikim kanta, idan ta tuno cewa duk tsawon lokacin nan ba share ta yayi ba yana ta neman hanyar da zai same ta ne sai taji wani dad’i ya wanke zuciyarta, sannan idan ta tuno kalaman daya gaya mata cewa shima yana sonta sai taji kamar tana daya daga cikin wadanda suka fi kowa sa’a a duniya, don Imran daban yake daga irin mutanen data sani kuma take gani. 2

Ance mutum baya taba zama cikakke, amma ita gani take shi komai nasa perfect ne! komai da ta sani a yanzu, kamar ice cream mai dad’i ayi topping d’insa da m&m’s…

Ta ina za’a sami matsala a cikinsa?

Ta kalli box d’in ta tuno da d’an short text d’in nan, wani dad’i ya ratsa ta, kamar an saka k’ank’ara a cikin zuciyarta.Da gaske Imran yana sonta.

Da gaske ne ba mafarki take ba.

Yace yana so suyi starting komai afresh, kenan zai gaya mata waye shi da duk sauran details d’in rayuwarsa, kamar yadda ya fad’awa baffa har ya yarda ya bashi aurenta, in ma bata san duka a yanzu ba, ta tabbata zata sani nan gaba.

Tunda k’addararsu ta riga ta zama d’aya.

A lokacin ne taji wani abu a gefenta yace zut! tana juyawa taga ashe tana zaune ne kusan akan rabin wayar inna, aikuwa idonta ya gane mata number da taje tana kira, number Imran ce da yake itace ta farko akan call log d’in.

Da sauri tasa hannu ta katse kafin ya kai ga shiga, me zai kaita kiransa a yanzu? tace masa me?

Ta mik’e ta nufi sa kaya, sai dai kafin ta zak’ulo kayan da zata saka k’arar shigowar message ya shigo.

A wayar inna dai ta san banda layin gidan waya babu masu turo da text, sai ko wani lokacin wrong number, amma kawai sai ta samu kanta da matsawa ta d’auko wayar.

Da gaske text d’in ne kuwa, kuma ba daga layin waya ba balle wrong number ba. Daga number Imran.

Missing me already?…ki min afuwa zan kira ki anjima yanzu zamu shiga meeting ne. nima nayi missing d’inki Habibty… 4

…like crazy!

Hannayenta suka shiga rawa, dama kiran ya shiga kenan? ya salam! yanzu me zaiyi tunani akanta? zaice har ta fara kiransa kenan? ta ya zata ce masa toh bata san ta kira ba?

Ta ajiye wayar ta koma wajen wardrobe ta jawo kayan da hannunta ya fara kaiwa kansu, ta saka rigar amma kafin ta zuge zip ta koma ta d’auko wayar ta sake karanta text d’in.

Habibty. Ta fad’a a hankali.

He just call her habibty!

*******

“Toh ina jinka…sai kuma kayi me bayan nan?”

Jameel ya tambaya yana kallon Imran dake zaune a study room d’insa yana signing wasu papers. shi kuma yana zaune ne akan wata couch dake jikin glass wall na d’akin. D’akin triangular ne mai bango uku, bangon k’arshe shine aka yishi da glass gabad’aya inda daga ciki kana hango d’an k’aramin garden d’in gidan mai d’auke da flowers.

“Na kira ta a waya, na bata hak’uri kuma nace mata nima ina sonta kamar yadda itama take sona, sannan nace mata zanyi mata bayanin ko ni waye saboda ni da ita mu fahimci juna.”

“Yarima….”

“Na sani jamil…” yayi saurin katse shi.

“…Ba sai ka tuna min ba, na san bamu tsara haka ba, na san na dawo yanzu ne saboda ciwonta yana shirin dawowa sannan na san bamu yi da kai zan kulata ba har lokacin da za’ayi auren.

Amma idan har muna tsarinmu dole ne mu dinga duba yanayin rayuwarsu suma. ba zai yiwu don iyayenta sun yarda da auren ba kawai ace babu wata alak’a da zata shiga tsakaninmu a yanzu, a tsarinsu dole ne a samu fahimtar juna tsakanina da ita wanda in babu hakan, ba yarinyar kad’ai ba har iyayenta zasu fara suspecting wani abu, kuma babban abinda zai fara rusa mana shiri, shine in har wani ya fahimci cewa akwai wata manufar da yasa nake son aurenta.

Saboda haka dole ne jaamil sai nayi acting cewa da gaske ina son ta ne. kamar yadda ka fada a baya ka gama naka aikin saura nawa, don haka ba sai anyi auren zan fara zan fara part d’ina ba, zai fara ne tun daga yanzu.”

Jaamil ya d’anyi shiru yatsunsa akan lebb’ensa yana nazari, daga can kuma yace.

“In dai zaka tafi da hakan akan tsarinmu ba matsala bane yarima, I’m just afraid kar ka zama so close da ita nan gaba….”

“Na gaya maka bana sonta jaamil, abinda ya faru tun farko ya riga ya wuce, har yaushe zaka yarda dani ne wai?

Sannan ni kaina ina da hankalin da zan san cewa Sa’adha ba abokiyar rayuwata bace, halitta ta da tata daban ce, ko banzo cikin mutanen da wannan manufar ba, ba zan tab’a fad’awa wannan kasadar ba.

Rayuwata daban ce da irin tasu kuma na san a kowacce halitta aure shine cikar rayuwa, to ta yaya zan k’arashe rayuwar da ban fara anan ba?”

Jaamil yayi shiru baice komai, hakan ya bawa imran tabbacin cewa ya d’aure shi ne da jijiyoyinsa.

***

K’arfe sha biyu saura na rana, Imran na cikin office d’insa yana harhad’a takardun da ya gama signing, sha biyu daidai zasu shiga meeting da wani sabon company da suke son fara bussiness dasu.

Wayarsa tayi haske, wani d’an mitsitsin haske da ba don idonsa na kusa ba zai gani ba. ya mik’a hannu ya jawo ta gabansa, mamaki ya kamashi ganin number Sa’adha, ya sake kallon agogo, yau friday…bata je makaranta ba kenan? +

Ya tuno da fuskarta a jiyan nan, sanda ta lek’o tana kallonshi daga cikin gate din gidansu. a lokacin yaji kamar ya shekara ne bai ganta ba, duk da cewa bata canja ba, amma wad’annan fararen idanun nata cike suke da damuwa wanda ya tabbatar masa da cewa abinda ya karanta da ita a sanda yaje don kwantar da ciwonta gaskiyane kenan.

Zuciyarta tana cikin damuwa, damuwa mai yawa kuma rabi akansa ne, ya fahimci cewa in har zasu tafi akan tsarin da suka yi da jaamil kawai to dole zasu fuskanci matsala nan gaba, don ba zata k’i aurensa ba amma zuciyarta baza ta yarda dashi ba wanda hakan dole zai jawo matsala nan gaba.

A daren ya lura kamar kuka take, daga baya kuma ya fahimci mafarki take yi kuma kamar wani abu ya same ta ne a cikin mafarkin, ya san zata iya farkawa a kowanne lokaci saboda haka yayi sauri ya d’ora hannunsa akan goshinta sannan ya shiga kwantar da d’aya b’arin ruhinsa dake tare da ita.

Sai dai kafin alamun cewa hakan yayi, ya fito, ta bud’e idonta da sauri tare da yin ajiyar zuciya, a sannan ya tabbatar da cewa mafarki tayi wanda ya tsorata, yana cikin d’akin har sanda tayi alwala ta fito sannan ta tsaya gaban mudubi, ya matso dab da bayanta ya tsaya don yaga abinda take gani a cikin wayar data d’auka.

Number daya kira yace mata zaizo ce, ita take ta kallo kamar tana so ta tantance ko shima kiran da yace mata zaizo a mafarkinta ya faru, ya lura ta haddace number saboda haka dole ya nemo layin duk inda ya shiga, don bayan ya kirata ba zai iya tuna inda yasa shi ba.

Ta d’ago ta kalli mudubin, a lokacin ne alamun cewa ciwon ya kwanta ya faru, wani hayak’i ya fito daga rabin fuskarta ya tarwatse a iska, kamar yadda yake yi kullum.

Tun daga yadda yaga ta tsorata a lokacin, ya san sai ya kwantar mata da hankali in ba haka ba abubuwa ne zasu k’ara cakud’ewa a cikin kanta.

Shi yasa bayan yazo ta hana shi ganinta, ya san sai yayi amfani da dabararsa don ya saita tunaninta, saboda haka ya kirata bayan sallar magriba.

Amma kamar yadda ya sani ne, bai yarda da kansa in yana tare da ita ba, bai yarda da zuciyarsa akanta ba. Saboda haka tun lokacin data amsa sallamarsa bai k’ara bi ta kan tsarinsu  ba, yayi amfani ne da hanyar daya san zata kwantar da hankalinta kawai.

Bayan nan kuma ya tafawa kansa da shirmen da yayi, shirmen da ya fara tun ba’aje koina ba, shirmen da yayi k’ok’arin lullub’ewa jaamil d’azu cewar ba wani abu bane da zai b’ata tsarinsu, shirmen da yayi d’azu na aika mata da sweets d’in nan, sannan shirmen da yake shirin sake irinsa yanzu.

Ya bud’e cikin wayar ya shiga typing mata message.

Missing me already?…ki min afuwa zan kira ki anjima yanzu zamu shiga meeting ne. nima nayi missing d’inki Habibty…

Ya tsaya ya kalli abinda ya rubutu, sannan a hankali ya k’ara da..

…like crazy!

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]