[Advertisements⬇️]

WANENE SHI CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WANENE SHI





CHAPTER 7



Nanne ta bud’e idanunta a hankali tana jin kamar ta tashi daga bacci. K’amshin turare da warin izal ne suka fara shiga hancinta kafin hayaniyar mutanen d’akin ta ziyarceta. Idanunta suka ci karo da silin fari, a jikinsa kuma akwai fanka wadda ke juyawa da k’arfi. +

A ina take ne? Don tabass nan ba d’akinsu bane. Sai kuma kwakwalwarta ta tuno mata da dukkan abinda ya faru kafin sumanta, tun daga tahowarsu titin Al-karsma gar zuwa sanda tazo tsallaka titin nan da sanda wata mota da bata san daga ina take ba tayi sama da ita.

“Ta farka ne?” wata murya da bata san kota waye ba ta kutsa cikin kunnenta.

“Ai kuwa kamar idonta a bud’e yake.”

Wata ta matso jikin gadon sannan ta kira sunanta, a lokacin maganganun mutane daki suka fara raguwa, saboda haka ta yunk’ura sosai sannan ta ware idanunta, ai kuwa fuskar Aunty nafisa ta fara cin karo da ita, sai ta Rahma sannan kuma Inna.

Tayi k’okarin mik’ewa amma gabadayansu suka dakatar da ita. A sannan ne inna ta fara kuka tana fad’in.

“Sannu Nanne, ke dai kina ganin jarabawa daga Allah, ba don da sauran numfashinki a duniya ba, da yanzu wani zancen ake…”

“Inna dan Allah karki fara kukan nan, tun da ta farka ai godiya zamu yiwa Allah kawai.” mama Azumi dake gefe ta katse ta.

“A kuma yi fatan samun sauki ba.” mama rabi ta k’arasa.

Daga nan dukkan ‘yan d’akin suka shiga matsowa ana yi mata sannu, wanda yawanci ‘yan gidansu ne sai kuma k’alilan daga cikin matan layinsu. Ita dai bin kowa take da kallo don ba wani ciwo da take ji a jikinta…Bata kuma yi magana ba don ta tsinci muryar Aunty maryama na fad’in ba lallai ne ta gama wartsakewa ba.

Yaya Ahmad da ya umar suka shigo sai kuma suka juya don kiran likita ko nurse. A lokacin nanne taji wani irin fitsari ya cika mararta saboda haka ta kalli Rahma dake gefenta tace.

“Ke fitsari nake ji, raka ni toilet.”

Rahma ta kalle ta sosai.

“Ai baza ki iya tashi ba, ban san ya za’ayi ba.”

Sai kuma ta juya gayawa aunty nafisa. Nanne ta yunk’ura da karfi ganin abinda zai hanata, anan ne idanunta suka ci karo da suntumemiyar k’afarta d’aure cikin plasta an rataye ta a jikin wani abu. Mamaki ya kamata, ta motsa ‘yan yatsun daga ciki taji suna motsi kuma ba wani ciwo, toh me zaisa a d’aure ta haka?”

“Nanne…” muryar aunty nafisa tasa ta juya. Tana magana k’asa-k’asa daidai saitin kunnenta.

“Baza ki iya tashi ba, akwai robar fitsari a jikinki saboda haka in kina ji kiyi kawai.”

“Kamar yaya?” ta tambaya don a baiyane yake bata gane ba.

“Kin tuna me ya faru dake koh?”

Ta gyada kanta.”Toh kin samu karaya ne a k’afarki, don haka baza ki iya tashi ba, amma an sa miki robar yin fitsari a jikinki.” +

Kanta ya kasa d’aukar zancen a lokacin d’aya, ta sake kallon k’afar tata, dama haka karaya take babu zafi ko kad’an. Sai kuma ta tuna da wanda ya kade tan, indan har ya karyata ai bai kamata ace baya nan ba. Kamata yayi yazo ya biya duk wani abu daza’a biya na asibitin nan, tunda ba akuya ya buge ba.

Ta juya da niyyar tambayar Aunty nafisan, sai kuma likita ya shigo tare dasu ya Ahmad, don haka kowa ya matsa ya basu guri, ya d’anyi mata tambayoyi akan yadda take ji ita kuma ta tabbatar masa ba wani abu da take ji a jikinta, amma da alama bai gamsu ba, don har allura ya sake mata a k’afar sannan yayi ta zuzzura mata wani abu a baki yana reading daga jikinsa.
Daga k’arshe yace a bata wani abin taci sannan tasha tulin magungunan dake zube a side drawer. Kafin ya fita ya sake tab’a kafar tata, sannan yace gobe zasu sake dressing.

Bayan sun fita aka mikar da ita zaune, ta jingina da filon bayanta sannan mama Azumi ta shiga bata abinci a baki. A lokacin ne ta tambayi inna dake zaune a gefensu ina mutumin da ya kad’e ta yake. Ga mamakinta sai ji tayi innan tace.

“Yaro d’an Albarka, Nanne ki gode Allah, tun jiya d’an nan dashi ake ta fafutukar komai…yana tsaye anan wallahi har safe, sai d’azu sulaiman ya takura masa ya koma gida ya huta, amma anjiman nan na san zaki ganshi ya dawo.”

Kafin ta amsa mama Azumi ta k’arba.

“Wallahi dai kuwa an samu d’an kirki, a wannan zamanin wani ai guduwa zai yi.”

Zata yi magana inna ta sake katseta.

“Ai kowa yaga k’ok’arinsa wallahi, har su hajiya babba zuwansu d’azu saida suka yita yaba masa, banda tsautsayi ya gifta ai yaron da alamun hankali, bai kamata ace yana wannan gudun ba.”

Ganin abinda zata fad’a ba zaiyi tasiri akansu ba yasa ta maida bakinta tayi shiru. Ita taso taji inna ta fara fad’a ta kara tunzura ta akan a damk’e mutumin sai ya biya komai da za’a tambaya na asibitin.

Wajen k’arfe uku, rahma ta matso kusa da ita.

“Kin san me?”

Ta gyara kwanciyarta sannan tace.

“A’ah me ya faru?”

“Kin san waye ya kad’e ki?”

“Ta ya zan san d’an rainin…”

“Kar ki karasa…Wannan mutumin ne fa.”

“Wanne?”

“General topic d’in islamiyya.”

Ba tare da wani tunani ba bakinta yace.

“Imran…?”

“Au sunansa kenan? Wanda dai muka tab’a gani a jikin gidansu walida kafin su tare.”

A lokaci d’aya Nanne taji komai ya tsaya mata, imran ne ya kad’e ta? Ta yaya hakan zata faru? Me zai kaishi Al-karama a wannan lokacin? Taji zuciyarta ta shiga bugawa kamar lokacin da yaje gidansu, anya kuwa shi din ne, ko dai gizo idon rahma ya mata. Taya in shine zai tsaya kamar yadda inna ta fad’a…Amma me zai hana shi? Wata zuciyar ta tambaya, laifinsa ne ya kad’eta dole ya tsaya yaga samun lafiyarta, sannan ma ai ya santa.Sai kuma tayi saurin goge hakan, ta nemo zahiri tasa a zuciyarta, ya taimake ta ne kawai sau d’aya ya kuma tambayi sunanta amma ba lalkai bane ya iya rike saninta har yanzu.

“…Na san abubuwa game dake fiye da cikin yatsu…”

Ta tuno abinda ya fad’a wancan karon. Idan har yana nazarinta ne a da, yanzu ya daina don rabon data ganshi a layinsu kusan wata uku kenan.

“Shi yasa nace miki kar ki k’arasa don duk sanda akayi zancensa, sai kin fad’a irin wannan tunanin.”

“Ta gallara mata harara da gefen ido.

“Me kike nufi?”

“Ke zan tambaya me kike nufi tunda har sunansa kin sani.”

Har ya yamma duk wanda ya shigo sannu yake mata, ita kuma ta tabbatar musu da ba wani ciwo a jikinta. Amma ko sau nawa ta fad’a babu alamun cewa suna yarda da ita saboda haka ta kwanta kawai ta rufe fuskarta.

Bayan sallar la’asar, wajajen karfe biyar mutane da yawa suka tafi, sannan masu zuwa ma aka dakatar dasu, sai da kyar ma aka bar Aunty maryama tare da inna don su kwana a wajenta, don a yadda aka tsara Aunty maryaman ce kad’ai zata kwana amma inna ta kafe cewa baza ta bar asibitin nan ba tare da Nanne ba.
Wajen karfe takwas saura, Nanne taji wani irin bacci ya fara fizgarta saboda haka ta rufe idonta, ta daina saurarar hirar da Aunty maryama keyi ita da mijinta wanda ya tafi aiki can abuja, tana bashi labarin dukkanin abinda ya faru. Inna kuma na daga k’asan d’aya gadon da ba kowa, tana nafilarta.

A lokacin ne suka ji an kwankwasa k’ofar dakin a hankali, inna da tayi sallama ta bada izinin a shigo, don dukkansu sun zata nurse din da tace zata dawo da daddare akan x-ray d’in da akayi a kai ne, wanda nanne ta kasa gane alak’arsa da karyewar k’afa.

“Assalamu Alaikum.”

Wannan muryar, wannan muryar mai taushi ta ratsa kunnen Nanne. Kafin tayi wani tunani inna ta amsa.

“Wa’alaika salam, har ka dawo? Sannu da zuwa.”

“Eh na shigo wallahi, munyi waya da sulaiman ne yake gaya min ta farka shine nace bari inzo inga jikin nata.”

Muryar ta sake ratsa kowacce kusurwa ta d’akin, cikin amonta a hankali, Nanne ta bud’e idonta da sauri ta kalli bangon dake fuskantarta, A lokaci d’aya tunaninta ya dawo mata da sanda taji muryar ta kira sunanta kafin idanunta su rufe, da kuma muryar imran sanda suka yi magana har sau biyu.

Da gaske Rahma take kenan, da gaske ne shine ya kad’e ta ba wani, ta yaya k’addara zata sake had’a ta dashi a haka?

“Ai wallahi da kayi zamanka ma sai gobe ka shigo, don tunda ta farka ba kukan ciwon da take, da alama abun da sauki ba kamar yadda muka zata ba.”

Taji numfashi ya zarce cikin kirjinta sanda ya sake magana.

“Toh Alhmdlilah, Allah ya k’ara afuwa.”

“Ameen Ameen, k’arasa wajen gadon ku gaisa ai inajin idonta biyu.”

A daidai lokacin Aunty maryama ta gama wayar da take, ta mike daga kujerar da take kai sanda ya karaso suna gaisawa. Sai kuma ta sunkuyo daidai kunnenta tace.

“Sa’adha juyo ku gaisa, mutumin d’aya hadu da tsautsayin buge ki ne.”

Nanne taji duk wani silin gashi na jikinta ya mike tsaye, ta gyara zaman d’ankwalinta a hankali sannan ta juyo, k’amshin turarensa ya cika mata hanci sannan zuciyarta ta k’ara girma a cikin kirjinta.Yana nan dai yadda ta sanshi, yadda ta fara ganinsa, yadda take hango shi daga nesa da kuma yadda ta ganshi ranar da ya shigo har gidansu. Shi kad’ai amma kwarjininsa ya cika ko’ina na dakin. Taji ta zama wata ‘yar mitsitsiya a gabansa. +

“Sannu Ya jikin naki?” muryarsa kamar yana rera magana ne.

Ta had’iye wani abu a cikin makogwaronta kafin ta iya amsawa.

“Da sauki, bana jin kowanne ciwo.” amsar da take fad’awa kowa kenan.

Ya kalli kumbuarriyar k’afar tata sannan yace.

“I’m sorry, tsautsayi ne ya riga ya faru amma banso muka k’ara had’uwa a haka ba.”

Idonta ya kai inda Aunty maryama ke tsaye sai taga bata nan, gwara da Allah yasa hakan, don baza ta so daga baya ta tsare ta da tambayar yaya akayi ya santa ba.

Amma duk da haka sai ta kasa amsawa, saboda kamar yadda ya faru ne sau biyu a baya, sanda ya fara mata magana da kuma sanda ya shigo gidansu, ji take yi ta takura a gabansa, balle kuma yanzu da yana tsaye a jikin gadon da take ne, babu wata tazara tsakaninsu.

“Allah ya k’ara miki sauki, na tabbata kafarki zata warke nan da k’ank’anin lokaci.”

Ya tabbata? Shi likita ne dama? Abinda inna ke nufi kenan da tace yana tsaye akayi mata komai? Ko shi yasa ma maganarsa take da sanyi da taushi? Tunda ance da baki ma likita kan warkar da mutum.

Kamar ya karanci zuciyarta sai taji yace.

“Ni ba likita bane, daga dai yadda kika ce bakya jin ciwo ne, kowa zai iya cewa da alamun sauki.”

Ta gyad’a kanta alamun ta fahimta.

“Ina k’awarki? Da safe tana ta kuka anan.”

“Rahma?” ta tambaya kai tsaye don ta san itace.

“Sun tafi gida sai gobe kuma.”

Daidai sannan nurse d’in ta murd’o k’ofa ta shigo.

“A’ah sauki ya samu kenan, har ana hira haka?”

Ta fad’a da dariya sanda ta nufo gadon.

“Alhmdlilahi ai, taji sauki kam.” Aunty maryama ta taso daga gefen inna tana fad’a.

Ganin haka yasa Imran ya d’an ja baya kad’an sannan yace.

“Toh ni zan tafi Aunty, sai gobe in Allah ya kaimu, Allah ya kara sauki.”

“Toh mungode fa, mungode Allah ya kaimu.”

Nanne ta juyo ta kalle shi sanda ya tsugunna yana wa inna sallama.

“Da fatan bakya kukan Allura don ita zamu yi yanzunnan.”

Nurse d’in ta fada sanda ya d’ago shima ya kalleta, kawai sai tayi murmushi ta juya d’aya gefen.

*****

A cikin sati d’aya da kwanaki, Nanne ta maida ‘yar k’ibar jikinta data rasa a baya na rashin lafiya, mutane suna ramewa a asibiti amma banda ita, don ciwo kanta baya mata balle kuma k’afar da aka daure, sannnan ga kulawa da take samu kota wane b’angare.

Sai dai ranar da aka fara mata dressing da taga wani dogon yanka a kafar tata, ga kuma k’ashinta tana lilo, ita kanta ta tsorata ace bata ji ko d’igon zafi a wajen. Su kansu likitocin suka rikice da tunanin ko wajen ya zama paralysed ne amma duk yadda aka taba tana ji, saboda haka a next dressing suka gaiyato wasu likitocin akayi ta bincike akanta, sai daga baya suka tsaya kawai akan cewar jijiyoyin wajen ne suka daina aikin d’aukar zafi zuwa kwakwalwarta.

Suka kira Baffa da zancen za’ayi mata aiki a wajen amma ba wanda ya san ya amince ne ko A’ah, don sadiq da yazo ya gayawa Nanne cewa yaji su ya ibrahim na fad’in wai ba zancen aikin kad’ai suka yi masa ba.

Ita kam! tun lokacin da taji ance jijiyoyinta ne suka daina aiki ta hutar da kanta da tunani. Fatanta ma kar su dawo da aikin don ba wanda ke son ciwo. Shi yasa ma da taji baffan baice komai ba ta mike k’afafunta ta cigaba hutawarta.

A cikin kwana biyar imran yazo sau hud’u. Kuma a duk sanda yazo gaisuwa zata shiga tsakaninsu har da ‘yar hira. Shi yasa a kullum take tashi da kwarin gwiwar ganinsa. Wanda itama a lokacin bata san me yake faruwa game da ita ba, bata iya wani tunani mai kyau ba tare da fuskarsa ta shigo ba. Da gaske ne abinda Rahma ta fad’a ya kamata ta tambayi zuciyarta me take nufi? Me take nufi da yawan damuwarta akansa?

Amma ya zata yi? Fad’ar manzon Allah ce cewa zuciya na son wanda yake kyautata mata, tun da aka kawo ta asibitin nan, daida da kud’in magani Imran bai bari sun biya ba, yace shi yayi laifi kuma alhakin komai na wuyansa, saboda haka kullum ‘yan uwanta da ita kanta cikin ganin k’ok’arinsa suke, a gefe d’aya kuma zuciyarta na k’ara rugurgujewa da tunaninsa. +

Kullum tana tashi da fatan cewa zai baiyana a d’akin da zarar ya dawo daga aiki, da wannan annurin fuskar tasa mai k’ara masa kyau da kwarjini, hakan yasa ba’a tab’a karanto gajiyarsa, a kullum ka ganshi, zaka iya rantsewa a lokacin ya fito daga wanka bayan ya tashi daga baccin hutu.

A cikin sati biyu kawai, Nanne ta yardarwa kanta ta fad’a cikin yanayin da bata taba kawowa kanta ba. Yanayin damuwa da wani bayan harkokin gabanta, ta ayyana a ranta abubuwa baza su taba dawo mata daidai ba. Rayuwarta baza ta taba komawa kamar da ba, don ta d’auko wani abu ne da ba zai tab’a faruwa ba.

Ta fahimci cewa ta fad’a son IMRAN, ta shiga k’aunarsa ba tare da sanin me take yi ba! Wasu mutane ne da Allah ya hallice mu daga b’angare na jikinsu, soyayayarsu wani abu ne da tun farkon halitta aka manne jikinmu tare da ita, shi yasa komai irin halinsu, komai tarin laifinsu, akwai wannan d’igon k’aunar da zai sa kaji cewa kaga wani naka. Nakan da har abada baza ka tab’a samun irinsa ba.

Nanne ta tsirawa matar dake gabanta ido, matar da ta ajiyeta tun bata kai shekara guda a duniya ba ta kama gabanta da sunan aure. A kullum ta ganta sai ta nanatawa zuciyarta wannan laifin, don ta samu ta iya jin haushinta ko sau d’aya ne amma ta gagara hakan, duk sanda ta ganta sai zuciyarta ta tsinke, gwiwoyinta suyi sanyi, taji kamar taje ta rungumeta ta lalabo duk wannan k’auna da d’umin uwar data rasa a baya.

Suna zaune ne daga cikin bedroom d’insu, a lokacin anyi wani ruwa mai yawa an d’auke. Saukarsu kenan daga adamawa ana dab! da fara ruwan.

“Inata magana kamar kina tunani, duk sunce a gaishe ki.”

Ta sunkuyar da kanta a hankali sannan tace.

“Ai ban sansu bane Addano.”

Ta kira ta da yadda taji ‘yanuwanta na kiranta duk lokacin da taje.

Ta d’anyi tsaki kad’an.

“Shi yasa nake ta nacin a kawo ki ai, kwanaki nayi aike ya kai sau uku daga ace min baku yi hutun makaranta ba, sai a bada uzurin wai za’ayi biki a gidan ne.”

“Da gaske ne ai, anyi bikin su yaya Aisha kwanakin baya.”

Bata ce komai ba sai ta juya ta kalli k’afarta da a yanzu aka kwance sannan tace.

“Ance bayan karayar wai akwai wani ciwon ma koh?”

“Eh bayan anyi aikin ne bana jin zafi a wajen, shine likitocin suka yi bincike suka ce jijiyoyin k’afar ne keda matsala, suka yi magana da baffa akan za’ayi aiki a wajen.”

“Ya yarda kuma?”

Ta girgiza kanta. “Bai yi magana ba dai tun bayan nan.”

“Ai gwara a kyale ki, in waje ya warke me yasa kuma za’a tafi neman wani ciwon.”

A sannan wata mata da suka zo tare ta shigo rik’e da ‘yar karamar ‘yarta da take goyo. (k’anwar nannen kenan.)

“Addano gata ta tashi yanzun nan.”

Ta mik’o mata yarinyar wadda ke ta mutstsuka ido, nanne ta kalleta, k’anwarta a suna amma bata ma san sanda aka haife ta ba, ‘yar kyakkyawar bafulatana da ita, mai dogon gashi kamar nata. Sai dai kuma an b’ata fuskarta da bille. Ta kai hannu ta tab’a ‘yan kafafuwanta.

“Yaya sunanta?”

“Miryam. Koda haihuwarta ai na aiko kizo baffanki yace jarabawa kuke.”

Bata ce komai ba ta cigaba da murza k’afar yarinyar.

“Gobe in Allah ya kaimu da safe zamu koma.”

Sai ta d’ago ta kalle ta. “Baza ku biyo ta nan ba kenan?”

Nuratu ta girgiza kanta.

“Toh ai basu fad’a min da wuri ba, sai shekaranjiya fa aka aika, kuma gobe Babansu miryam zai dawo daga china. Kinga dole in koma da wuri.” 1

Sai ta gyada kanta kawai tayi shiru. Don mijin nata d’an kasuwa ne dake yawan tafiye-tafiye, bai cika zama a gida.

“Nanne wai ajinki nawa ne?”

‘SS3…wannan shekarar zamu gama insha Allah.”

“Toh meye a ranki game da nan gaba, kema karatun zaki biye musu kiyi, koko zaki rufawa kanki asiri kiyi aure?”Kalmarta ta k’arshe taso bata dariya, tayi aure a yanzu? Toh ta auri wa?

“A’ah zan fara karatun dai, idan auren yazo ina cikin yi, sai ayi.”

Nuratu tayi ajiyar zuciya kafin tace.

“Na san dama sun cusa miki irin ra’ayinsu, idan zan baki shawara a matsayina na mahaifiyarki kuma ki d’auka, gwara kiyi aure tun yanzu ki samarwa kanki ‘yanci. Karatu zaki iya yinsa koda aure goma akanki, kuma shine ma zaki fi yinsa cikin ‘yanci.”

Tayi shiru tana juya maganganun. Ba wai tana shirin yarda dasu bane, don ta san abu ne mai kamar wuya saboda haka sai kawai tace.

“Toh Addano ni a yanzu ma ba wanda nake kulawa ai.”

Ga mamakinta, sai taga ta fuskanceta sosai, sannan ta gyara zaman miryam dake kan cinya tana shayar da ita.

“Wannan ba matsala bane Nanne, dama akwai zancen dana taho dashi tun daga gida, idan kin amince zan turo d’an wata yayata Nura, yaro ne mai hankali kuma shima d’an boko, don har ya gama karatunsa ma yana aiki a cikin adamawa, na tabbatar miki in kika amince dashi zaki ji dad’i nan gaba, kuma ta hanyarsa zaki dawo cikin ‘yan uwanki.” 1

Nanne taji kanta ya daure ta kasa fahimtar farko da k’arshen zancen, amma abun da yafi daukar hankalinta da tace zata dawo cikin ‘yanuwanta.

“Addano wadannan su ba ‘yanuwana bane?”

“Yan uwanki ne amma bana uwa ba, kuma ke mace ce, duk girmanki dangin uwa sune martabarki, yanzu ki duba fad’in gidan nan kaf! Duk randa akace babu ran inna wallahi ko kinyi aure kika zo sai dai kiyi ta kame-kamen wajen zama. Amma inda cikin ‘yanuwana kike sai inda kike so zaki jefa k’afarki.” 1

Tayi shiru kawai tana jinta, don ta san abinda take fad’a wani abu ne da ba zai tab’a yiwuwa ba, ita a yanzu kwata-kwata ma harkar aure bata cikin lisaafinta, abinda ke gabanta daban ne.

Kuma ko zata yi auren ma, ba zai yiwu da wani wai shi Nura ba, mutanen da basu santa ba, basu damu da saninta ba, sai a yanzu ne zata yi musu amfani?

Baza ta iya musa mata ba, sai kawai ta dinga binta da kalmar toh, a k’arshe kuma tace mata zata yi tunani, ita kuma tayi ta jaddada zancen akan ta kira ta duk lokacin da ta gama amincewa zata turo Nuran. Da haka aka zo d’aukansu daga can gidan da zasu kwana bayan garin ya d’an sha.

Bayan sallar magriba Nanne ta kwanta akan bargon inna dake shimfide a k’asan window na falo, yanayin garin na yadda iskar damina mai sanyi take kad’awa da kuma k’anshin jik’akk’iyar k’asa ya taimaka mata wajen ture duk wani tunani a kanta, ta janyo abinda ke cin ranta. Tunanin Imran! 3

Tun bayan sallamarta da akayi daga asibiti sau biyu kawai yazo, na farko ma bata ganshi ba tana bacci. Sai a na biyu shi kuma bai dad’e ba yana ta sauri. Gashi har yanzu bata fara fita ba balle ta ganshi a hanyar islamiyya.

Kuma a kullum, a kowacce rana tana jin zuciyarta ta k’agu da son sake ganinsa. Sai a yanzu take sake tabbatar wa kanta da gaske son Imran take, kuma ba tun yanzu ba, tun ranar data fara ganinsa ta kasa manta shi, har zuwa yanzu da komai ya cakud’e mata.

Ta san koda ta ganshi d’in ma, ba abinda zai faru ko ya canja, sai dai ta k’ara d’aukarwa kanta wahalar da zuciyarta ta jawo mata. Wahala mara yankewa, wahalar da a ‘yan shekarunta bata san zata fad’a ba.

Wani b’angare na zuciyarta ya fad’a mata cewa ta taimakawa kanta tun yanzu ta cire imran daga ranta, donshi matsayin daya d’auke ta daban ne. Ya taimaka mata a farko kuma ya taimaka mata a yanzu da tsautsayi ya had’a su, kuma babu komai bayan hakan. Amma duk sanda tayi wannan tunanin sai maganar daya tab’a fada mata tazo ta ture komai.

“Abubuwan dana sani game dake, suna da yawa….”

Ko ba komai akwai lokacin da shima ya damu da ita.Ta lumshe idonta a hankali tana kallon yadda iska ke turo labulen windon, su inna na daga gefenta suna firfito da kayan da Nuratu ta kawo ana gani. A lokacin ne rediyon inna dake kunne ta fara playing wata wak’a sakamakon gama wani shiri da akayi.

….Sitting wide eyes open behind this four walls hoping you’ll call,
It’s just a cruel existance i guess no point hoping at all.
Baby,Baby..
I feel crazy, up all night! All night!
Everyday, you give me something…but you said nothing.
Whats happening to me?! 1

(if u can relate dix moment, Allah muku albarka!)

*****

BAYAN SATI DAYA.

Tana zaune tana jiran isowar Rahma, yau a gidan zata kwana don haka ta tafi siyo musu wainar fulawa a can bayan layinsu, inna ta fito daga d’aki sanye da hijabinta a karkace.

“Baffanku ne ke kiranmu tare dasu hajiya, da sune ma zasu zo nan nace A’ah gwara mu zauna a can falon nasa.”

Haka kawai Nanne taji gabanta ya fad’i ta juyo ta kalli inna.

“Ke dasu hajiya? Har dasu mama rabi kenan.”

“Eh mana da duka matan nasa, na san dai wani abun ne ya taso, in ba haka ba yaushe rabon da ayi irin wannan zaman…tun lokacin da tsautsayin nan ya fad’a kan muhammad daya kad’e yaro a mota.”

Nanne ta tuna lokacin, ya muhammad na wajen hajiya babba ne ya tab’a kad’e wani yaro a mota bisa kuskure, abinda yasa bata manta ba saboda azumin da yayi tayi har sittin, kullum su mama Azumi suyi ta hidimar kayan shan ruwansa. Tabass kafin baffa yayi irin wannan kiran sai abu mai muhimmanci ya taso tukunna. Ta had’iye yawu cikin makogwaronta sanda inna tayi hanyar k’ofa.

“Inna ki gyara hijabin naki.”

Bayan kamar minti biyar Rahma ta shigo d’auke da leda da kuma faranti.

“Na dad’e ko? Wallahi layi ne da ita kamar me.”

Ta sauko k’asa ta karbi plate din. “Baki ma wani dad’e sosai ba…juye mana ita a ciki.”

Rahma ta zauna tana zubawa. “Kin san har na taho na tuna bata bani yaji ba, saida na koma.”

“keh na tuna Amina ta bani wani flash da film d’in india a ciki, bari in d’auko in sa mana.”

Ta tashi da sauri ta nufi d’aki, da fatan film d’in zai d’auke mata hankali daga tunanin dalilin meeting d’insu inna, don haka kawai take jin jikinta wani iri.

Ta dawo, tasa flash d’in a jikin TV sannan suka zauna cin wainar. Sai dai tana kai lomar farko bakinta, sadiq ya d’age labulen d’akin ya shigo.

“Ai tunda naji dama kina cewa anan Rahma zata kwana na san wani abin kuka shirya, wato ga waina fulawa mai zafi da zob’o ga kuma TV kunsa a gaba.”

Nanne tana kallonsa tace.

“Kai kuma gulma na cinka sai kazo kaga me akeyi…Rahma dan Allah san masa ya bar nan wajen.”

Ya tab’e baki.

“Allah ya kiyaye inci wannan abar, ni baffa ne ya aiko ni yana kiranki.”

A lokaci d’aya taji k’arar wani abu ya tarwatse a k’irjinta, shikenan abinda take tsoro ya faru, akanta za’ayi meeting d’in nan shi yasa dama tun d’azu jikinta ya bata.

“Da gaske kake dan Allah?”

Ya langwab’e kai ganin ta tsorata a lokaci d’aya, ya sami abinda yake so.

“Da gaske nake ‘yan mata, kije ki girbi abinda kika shuka.”

Ta d’auki kofin robar dake gabanta ta jefe shi dashi, yayi saurin kaucewa sannan ya fita yana dariya.

Sanda ta tura k’ofar falon baffa ta shiga da sallama, jikinta gabad’aya yayi sanyi sannan zuciyarta ta sallama cewa duk abinda zai faru bai zai mata dad’i ba kuma dole ne ta karb’e shi hannu biyu, tunda wad’anda ke cikin d’akin sune da iko da ita da kuma duk wani abu nata.

Inna tana zaune daga k’asan labule hajiya Babba na gefenta, sai Aunty Amarya, mama halime da kuma mama rabi.

A d’aya gefen, ya Ahmad ne da ya ibrahim wanda bata san yaushe suka zo daga gidajensu ba, sai kuma sauran, ya sulaiman, muhammad, ishaq, Nasir da kuma ya umar. ‘yan biyu ne kawai basa nan, inda ta fahimci daga kansu aka tsaya kenan. Toh me zai sa a tsallake su, a tsallake sadiq a taho kanta?

D’akin ya mata girma, ta rasa inda zata zauna sai da Baffa dake tsakiya ya yafito ta da hannu ya nuna gefensa. Ba yadda ta iya haka ta tsallake kowa ta nufi inda yake zaune a k’asan kujerarsa.

“To tunda kowa yazo, Babban yaya sai kayi kayi mana addu’a koh.” ya fad’a yana kallon yaya Ahmad wanda yayi d’an murmushi kafin ya fara.

“Salati goma ga Annabi(SAW)….”

Har aka shafa Nanne bata tabbatar duk abinda aka fad’a tayi dukka ba, don zuciyarta lugude kawai take kamar wadda tayi gudu mai nisa sannan ta tsaya a lokaci d’aya.

Cikin nutsuwa Baffa ya bud’e baki ya fara magana!Cikin nutsuwa baffa ya bud’e baki ya fara magana.

“Dalilin taruwarmu anan akan matsala ce data shafi Nanne, kowa ya san irin rashin lafiyar data fuskanta kwanakin baya, wanda bayan anyi duk wani k’ok’ari da kuma taimakon Allah ta samu sauki na ‘yan kwanaki. Daga baya kuma ciwon ya sake tashi, bayan an kuma warkar dashi ya sake dawowa dai a cikin k’ank’anin lokaci.

Toh a zuwan da malaman suka yi na k’arshe ne suka same ni da zancen cewar har a lokacin basu iya gano ainihin abinda ya same ta ba, duk da rashin lafiyar tata tayi kama da shafar aljanu amma basu ga wani abu na alamar aljani a jikinta ba.

Saboda haka dasu da sauran k’arin malaman da suka zo a ranar, suka bada tabbacin cewa bak’ak’en aljanun ne ke son shiga jikinta, bana irin shafar aljanu da aka saba gani ba, saboda duk wani alamun hakan ya baiyana a jikinta. Sunce su irin wannan aljanun suna da wahalar fitarwa in dai har suka riga suka shiga jikin mutum, sannan suna mu’amala ne da mata da basu da aure kawai.

A lokacin sun bani shawarar cewa da za’a samu tayi aure nan bada jimawa ba, toh da tabbas aljanun baza su sami k’arfin cigaba da bibiyarta ba balle har su iya shiga jikinta. Toh tun daga wannan lokacin sai nayi ta bibiyar malamai wad’anda suke da ilimi akan irin wannan abin, amma kowa magana d’aya irin tasu dai yake maimaita min, in zan sami k’ari ma bai wuce wani yace anyi sa’a ma da har yanzu aljanin bai gama shiga jikinta ba.

Ana cikin haka ne kuma ta gamu da wannan tsautsayin, kuma wani abu ya sake faruwa na cewa taji ciwo a k’afa har an sami karaya amma bata jin zafi a wajen. Suma likitocin suka kira ni bayan sunyi duk bincikensu akan cewa jijiyoyin k’afarta ne keda matasala basa iya aikawa da wani abu zuwa kwakwalwarta, sannan ita kanta wai kwakwalwar tata akwai wani abu da suka gano a ciki kamar k’ari wanda basu tabbatar da menene ba.

Suka bani takardu gasu can a kujerar can akan inje insa hannu za’a sa ranar yi mata aiki. Sai dai ni tunda na karb’o su hankalina bai kwanta ba. Bayan kwana biyu sai d’aya daga cikin likitocin ya kira ni a waya. Yace yana so ne ya fad’a min gaskiya akan zancen aikin nan, duk wani abu da na gani a rubuce basu tabbatar dashi ba kawai hasashe ne, amma shi yana danganta rashin lafiyar Nanne da shafar aljanu don haka yake bada shawara a fara gwada magungunan hausa tukunna.

Da naji haka sai naga an sake dawowa kan dai zancen malaman nan ne, saboda haka sai na tafi wajensu da kaina sulaiman shi ya kaini, suka kuwa sake tabbatar min da abinda suka fad’a a baya, magunguna zasu bata sauki na d’an lokaci amma babu tabbacin cewa nan gaba aljanun baza suyi nasarar shiga jikinta ba sai dai in har tayi aure.

Don haka na yanke shawara cewa yi mata auren a yanzu shine kad’ai mafitar da muke da ita, wadda zata sa ayi fatan dacewa.”Ya juya a hankali ya kalli inna.

“Inna wannan shawara tace kawai, amma ina so inji ra’ayinki duk abinda kika fad’a a yanzu dashi za’ayi amfani.”

Inna ta gyara zamanta sannan tace.

“Yo ni dama ai ka san me zance. Shekara biyu kenan harda watanni ba zan manta na tako k’afata har d’akin nan akan zancen auren uarinyar nan, nace maka ni a tsarin da iyayenmu suka raine mu, ‘ya mace daga sha uku, hudu, biyar an kawar da ita. Amma ba irin zancen da baka kalailayeni dashi ba akan kai a cikin ‘ya’yanka baka tab’a aurar da d’a bai gama sakandire ya fara ta gaba ba saboda haka inyi hakuri.

Nace maka sam! Ni ina yiwa yarinyar nan kallon ‘ya ne tunda nina ci kashinta da komai ba zan yarda tayi ta zama a gabana ina kallonta haka ba, toh Inace a yadda muka tsaya da kai cewa data k’are sakandiren zaka aurar da ita ne koh?”

Baffa ya d’aga kai. “Haka ne inna.”

“Toh yanzu me ya rage a gamawar da har zakayi ta wannan dogon bayanin kamar mai shirin laifi? Koko kana tunanin bata isa auren bane?”

“Ba haka bane inna, shawara ce kawai na nema don kece da iko akanta.”

“Toh in haka ne ko gobe ka tara jama’a ka d’aura mata aure, Allah ya hore min abinda zan had’a nan da sati d’aya a kaita gidanta.”

Ya Ahmad yayi saurin gyara zama yace.

“Toh Baffa zancen karatunta fa? Tunda yanzu SS3 take, bai kamata ai ace ta tsaya kenan ba.”

Inna ta gallaro masa harara.

“Ai zancen kenan, karatu…karatu ko uwar me yake muku oho.”

“A’ah inna da gaskiyarsa shima, nima kuma nayi wannan tunanin. Zata cigaba da karatunta insha Allah, in lokacin yin WAEC da NECO yazo za’ayi mata registration tayi kuma ta cigaba har jami’a da yardar Allah.”

“Toh amma Baffa…” Mama halime ta fad’a daga gefe.

“…Nace ana ta zancen aure, dama ita Nannen ta kawo wani tsayayye ne ko kuwa ya za’ayi?”

“Wannan dalilin shi yasa nasa aka kirawo ta nan itama, dan taji komai da kunnenta kuma in bata dama nan da wata guda ta gabatar min da wani, in har akayi bincike akansa babu matsala shikenan, idan kuma ba haka ba dama akwai tarin mutanen dake min magana akanta, don ak’alla abokaina uku suna min zancen nemawa ‘ya’yansu kuma na tabbata kowanne a cikinsu ko nan da wata gudan nace baza a sami matsala ba.”

Hajiya Babba tayi gyaran murya sannan tace.

“Toh Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa, kowannenmu kuma sai ya taya da addu’ar nema mata sauki. Sannan kema Nanne sai kin kula sosai da kanki, tunda kinji duk abinda akace koh?”

A lokacin kowa ya juya ya kalli Nannen, wadda fuskarta ta jik’e sharkaf da hawaye da kuma gumi.

******

“Me suka tattauna?” Imran ya tambaya yana kallon jaamil.

“Komai ya tafi daidai, na gama nawa aikin saura naka.”

Imran ya ajiye wayar hannunsa a gefe sannan ya kalle shi.Kana nufin dukkansu sun amince?” +

“Na gaya maka komai ya tafi daidai, yanzu kai ya rage ka fara naka.”

Ya ciji k’asan lebbensa yatsunsa a sark’e yana kallon ‘yar vase flower dake can jikin tv-stand. Zuwa can kuma ya maida yatsun kan hab’arsa sannan ya huro iska daga bakinsa.

“Ta ina zan fara kenan?”

“Yarinyar ta riga ta fara sonka, kuma a yanzu bata da isashshen lokaci, saboda haka baka da matsala, inaga kai kad’ai ne zab’inta.”

Imran ya juyo ya kalle shi, yana zaune daga kan two seater dake gefe yana kallon tvn dake kunne tana nuna tashar News, sun kashe fitila sai hasken tvn ne kad’ai a d’akin yana reflecting akan fuskarsa. Har wajen dining ba fitila sai hasken switches kawai da kuma na fitilar kitchen.

“Meye ne kake kallona?”

“Tunowa nayi da yadda kake damuna akan na rabu da yarinyar lokaci kadan daya wuce, yanzu kuma kaine me cewa inje wajenta.”

Bai kula abinda ya fad’a ba yace.

“Ya kamata ka saba fad’ar sunanta tun yanzu. Don bana son abinda zata gane cewa kamar akwai wani dalilin da zaisa ka aureta.”

Kafin ya bashi amsa wayarsa ta fara haske da vibration akan kujerar. Ya kalli screen d’in sannan yaja tsaki.

“Waye?”

“Maryam.” ya amsa a tak’aice.

Jaamil ya juyo ya kalli wayar sannan yace.

“Kar ka damu, idan ka zama ANGO zata kyale ka ne.”

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]