[Advertisements⬇️]

WANENE SHI CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WANENE SHI

CHAPTER 1
Nanne! nanne! nanne!!…ki tashi nace koh?”

Yarinyar da aka kira da nanne ta motsa sannan ta cigaba da baccinta,

“Zaki bude ido ko sai na tashe ki da ruwa…”

Inna ta fada tana dad’a girgizata, jin haka yasa ta zumb’ura baki sannan ta mike tana murza ido ta cikin dogon gashin kanta daya hargitse ya rufe fuskarta.

“Ki tashi ki wanke ido ki fita tun kan salisun ya tafi, kin san tun jiya muka yi haka dake.”

Nanne ta dago ta kalli agogon dake kafe a dakin, k’arfe takwas da kwata na safe, gabadaya baccin da tayi bayan sallar asuba ma bai kai fi na awa biyu ba. Kwata-kwata ta manta sunyi da inna cewar yau zata je da safe ta gayawa salisu irin audugar da zai d’ebo mata a gonar baffansu wajen daza’a fitar da auduga yau kafin masu siyen kamfani su d’ebe masu kyan ciki, wai da ita zata yi sak’ar mayafan da amare zasu yafa ranar wankan amarya (Hakan wata al’adarsu ce ta wata kabila daga nijer)

“Allah inna da kin san gajiyar da na kwanta da ita da kin hakura wani daga cikin su yaya umar kawai ya fad’a masa.

“Kema kin san ba ganinsu zanyi kafin su fita ba don haka ki tashi ki d’auraye ido kije tun kan salisun ya tafi na san zasu fara yin gaba, don tun dazu nake jin dirin motoci zasu fara tafiya.”

Nanne tasa hannu ta tattara gashinta baya sannan ta tufke shi, ta shiga band’akin dake jikin d’akin ta zuba ruwa a buta ta wanke bakinta da fuska sannan ta fito, inna ta miko mata hijabi daga inda take zaune.

“Haba dai, wannan ya cukurkude, bari in duba wani.”

Ta bud’e wardrobe ta janyo wani mai d’an tsaho ta zura sannan ta karbi k’atuwar ledar da innan ke nuno ta dashi.

“ki masa bayani kamar yadda na fad’a miki jiya dan Allah.”

Yadda ta marairaice murya yaso ya bata dariya sanda ta fita daga dakin, da yake a hawan farko suke tana iya hango k’aton tsakar gidan da ba mutane sosai saboda safiya sai daidaikun ‘yan aikin dake wucewa akai akai.

Ginin gidan nasu dake cikin wata unguwa a katsina, dad’ad’d’e ne da akayi shi da dakakken gini da ko k’usa ba kasafai take huda shi ba, sannan gabadayansa hawa uku ne, daga bakin gingimemen gate din dake jikin zungereriya katangar data zagaye gidan, faffad’ar haraba ce da tsaf zata d’auke bikin masu dangi, akwai manyan rumfuna na ajiyar motoci da kuma shukar fulawowi data zagaye filin gabadaya.

Daga can jikin ginin gidan kuma doguwar baranda ce data bi tsawon fad’in wajen inda d’akunna ne a jere guda shida na yayyansu maza, a tsakiyar su kuma k’atuwar kofa ce data shigo ciki zuwa bangaren baffansu dake daga dama, inda ya had’a da k’aton falo na saukar bak’insa da kuma d’akuna biyu a ciki da bandaki, daya gefen hagu kuma k’aton kicin din gidan ne wanda shi kansa waje biyu ne dashi, da b’angaren da aka kafe da durowoyin ajiya, sai madafi inda ake jibge tarin itace da kuma manya-manyan tukwanen girkiB2


Bayan shi babu komai a k’asan sai manyan sito guda biyu, da ake ajiyar kayan gona, matattakalar hawa sama mai fadi ce data d’auka daga tsakiyar katon tsakar gidan kuma ta rabu hagu da dama saboda kowanne b’angare a zagaye yake da d’akunan matan baffansu su hudu ras!, inda kowacce take da falo da kuma manyan dakuna guda biyu kowanne da band’aki a ciki, sai wajen inna wato mahaifiyar baffansu inda itama take da katon falo sai dai daki daya ne da kuma band’aki.

Hawa na biyu kuma na karshe faffadar baranda ce inda wajen yafi ko’ina a gidan girma, a d’an zagayeta da gini daidai misali yadda in ba d’age mutum yayi ba ba zai iya gano k’asa ba, a nan suke shanyar kaya, kayan miya da kuma zaman shan iska kasancewar akwai kujeru kala-kala harda ‘yan furanni na tukwane. Kuma daga nan kana iya hango gabad’aya kewayen unguwar da tsilli-tsillin gidaje ne kawai wanda da yawansu ba mutane a ciki, wasu ma ba’a gama ba.A kaftanin ‘ya’yan baffansu Nanne ce ta goma sha bakwai, sannan akwai mutum biyu mata ‘ya’yan aunty amarya data girma a k’asanta.

Uwargidan baffa ta farko, hajiya Nasiba da ake kira da hajiya babba, ‘yar maigidansa ce dake can cikin garin katsina, kasancewar baffansu d’an asalin nijer ne ya shigo katsina. tana da ‘ya’ya shida, Ahmad, Nasir, Muhammad, ishaq, farida da kuma Aisha. Maza hudu mata biyu, kuma ‘ya’yanta sune manya a gidan, don Ahmad da farida sunyi aure saura maza uku da mace daya Aisha.

Sai Mama Rabi wadda ita kuma ‘yar uwarsa ce ya auro daga nijar, ita ‘ya’yanta hudu, Ibrahim, sulaiman, umar da macenta daya jamila. itama ta aurar da babban d’anta ibrahim. Sai Mama halime wadda itama ‘yar nijar d’ince amma ba ‘yar uwarsa ba, ‘ya’yanta hudu duka mata, khadija, maryam, nafisa, da kuma zainab. Khadija ce kawai tayi aure a cikinsu.

Sai aunty Amarya mai ‘ya’ya biyar kasancewar haihuwarta ta farko tagwaye ne maza, salim da suraj, sai mai bi musu sadiq, safiya da kuma surrayya.

A duk cikin ‘ya’yan baffan, nanne ce kawai bata da uwa a gidan, mahaifiyarta bafulatanar adamawa ce kuma tana can tare da ‘yan uwanta, baffansu ya aureta ne lokacin da wani sab’ani ya shiga tsakaninsu da mama Rabi har ya sake ta, toh a wannan lokacin ne yaje adamawa halartar wani taro na manoman nijeriya da akayi kusan sati ana gudanarwa, anan yaga mahaifiyarta a d’aya daga cikin masu goge-gogen wajen da suka kwanaB2


Farko abokananshi ne suka fara tsokanarshi da cewar ya kamata ya koma gida da bafulatanar adamawa tun lokacin da suka ganshi yana tambayarta wani abu, shikenan kuwa zance ya koma gaske inda a satin basu baro adamawa ba sai da suka je har gidansu nuratu aka tabbatar musu kuma an bashi ita, anan suke ji ma ashe bazawara ce ta taba aure harda yara biyu.

Ko da ya dawo, ya sanar da inna mahaifiyarsa, bata hana shi ba sai dai matansa da suka nuna rashin son abin, hankalin mama rabi yafi na kowa tashi tunda a lokacin tana ta yawon bin ‘yan uwa kan a bashi hakuri ta koma darajar ‘ya’yanta.

Sai dai ubangiji ya riga ya tsara al’amarinsa don ba’a fi wata daya ba aure ya tabbata tsakanin baffansu da nuratu, ta kuma tare a b’arin mama rabin, duk da kasancewar nuratu bazawara, amma baffa ya nuna mata so wanda har hakan ya dinga b’atawa matansa rai, kasancewar baya b’oyewa koda kuwa a gaban ‘ya’yansa ne.

Shekarar nuratu daya da rabi a gidan, ta haifi diyarta mai kama da ita, sai dai ta d’auko hasken fatar baffan tunda ita nuratu ba fara bace, baffa ya sanya mata Sa’adah nuratu kuma ta lak’aba mata Nanne wanda shine ya bita.

Tun daga haihuwarta ne kuma nuratun ta sauya hali, ta fara rashin mutunci kala-kala a gidan, rashin kunya tun daga kan baffan har inna ba wanda ta kyale. Nasiha da kyaliya ba wadda baffa baiyi ba amma a kullum abin gaba yake. Ganin haka, ya sawwak’e mata saki d’aya ba da son ransa ba, don har a lokacin yana k’aunarta, tayi niyyar tafiya da nanne amma ya hana. Saboda haka ta dire ta ta koma adamawa, daga baya ne suka samu labarin cewa ashe gidan tsohon mijinta take son komawa kuma ta koma d’in bayan ta gama idda.

A lokacin da hakan ta faru, mama halime tana shayar da autarta zainab, baffa ya roki da ta hada da nanne amma kiri-kiri ta rantse ba zata shayar da ‘yar kishiya ba sai dai in itama ya saketa.

Aunty amarya ma da bata dad’e da yaye d’anta na biyu sadiq ba tace bata san zancen ba. Hajiya kuwa ba mai tunkararta da irin haka, kasancewar ba shirgin kowa take shiga a gidan ba har dashi baffan kuwa, kuma ma ‘ya’yanta duk sun riga sun girma a lokacin. Daga karshe dai inna ce ta dauki nanne, duk da cewa da farko itama bata shiga zancen ba don tana cike da d’acin abinda nuratun tayi musu.

Da taimakon tatacciyar madarar shanun da a kullum ake tatsowa daga gonar baffa nanne ta girma a hannun kakarta, inda kuma innar ta dauki son duniya ta dora akan nannen, ya zama tamkar bata da jika ko d’aya a duniya sai ita, har ta kai ma in kana son farin cikinta to ka yiwa nannen wani alkhairi.Sannan tun tashinta sau uku baffa yasa aka kaita adamawa wajen mahaifiyarta, sai dai ita nuratun tana yawan yi mata aike ta hanyar turo ‘yan uwanta. B2


Gabadaya ilahirin jama’ar gidan baffa, har kuwa da tulin ma’aikatan dake cikin gida da gonaki, nanne zata iya kirga masu nuna mata kulawa a cikin ‘yan yatsunta kawai, don daga wad’anda suka tsane ta sai masu nuna cewa Allah baiyi halittar ta a cikinsu ba, saboda kuwa dalilai biyu, na farko ta tashi a cikin bakin fentin mahaifiyarta daya shafeta, don da yawansu tsanar da suke mata ta samo asali ne daga irin abinda nuratu tayi a gidan bayan haihuwarta, sai kuma saboda tsananin rashin kunyarta da ba ta kan wanda bata bi in abinta ya tashi, harda manyan mazan gidan kuwa da take d’an shakkarsu.

Hakan kuwa ya samo asali ne daga rashin kwab’ar data samu daga inna, don duk gidan har baffa ba wanda ya isa yayi mata tsawa akan wani abu in tayi ba daidai ba sai anga b’acin ran inna, wani lokacin ma ta yini tana sababin cewa don anga yarinya bata da uwa a gidan ne.

Shi yasa ta tashi kusan a sangarce, saboda kowa a gidan na shakkar bacin ran inna, don in bata yi da kai shi kansa baffan baza ka samu fada a gunsa ba. Mutane da yawa in suka kalli fuskar nanne baza su ce tana da magana bama balle rashin kunya, tafi kama da irin miskilan nan dake takama da wani abu nasu, amma yini d’aya tare da ita zai rusar da wannan ma’anar.

Duk cikin jama’ar gidan, babu wanda nanne take ganin tsana b’aro-b’aro a wajensa irin mama rabi da ‘ya’yanta, kasancewar baffa bai dawo da ita gidan ba sai bayan an yaye ta. Amma hajiya babba babu ruwanta da ita in ba aiken inna ne ya kaita wajenta ba, haka ma ‘ya’yanta, shi yasa su take ganin mutuncinsu.

Mama halime kuwa nunawa take yi Allah bai halicci inuwarta a gidan ba, bata ko ambatar sunanta balle tabi ta kanta a duk harkokinta, tafi karkata ga yadda baffa zaifi fifita ta a cikin matansa, hakan yasa suma ‘ya’yanta basu damu da ita ba, sunfi damuwa da samun harkar kyale-kyale kamar yadda ta d’ora su akai, sai dai kuma duk randa wani abu ya had’o su da nannen, kowa sai ya san ana tashin hankali a gidan kasancewar da sauran ‘yan uwansu ma ba mutunci suke ba.

Aunty amarya ce mai kyararta da kuma hantara in bata ga idon inna ba, wanda ita kuma nannen in dai babu ‘yan biyunta da take shakka a wajen zata rama ne da irin maganar data fito bakinta kafin ta bar wajen, ita kuma ta bita da zagi.

Ma’aikatan gidan ma basa shiga harkarta, don data had’a ka da inna hanyar samunka a wajen baffa ta fara rawa kenan.Nanne na sauka k’asa taci karo da Baba Azumi shugaban ma’aikatan dake kula da girke girke. Mace daya a cikin kalilan d’in ‘yan aikin gidan dake nuna mata kauna. +

“A’ah uwata ce da sassafen nan?”

Ta sake turo bakin daya zame mata jiki.

“Wallahi ba yadda na iya ne inna ce ta taso ni, ya akayi Kema kika fito da sassafen, wani abun za’ayi yau?”

“Yo, mu ai fitar safe yanzu ta ganmu, kin san masu kawo lefen jamila da safe suka taso, kuma kila wajen azahar zasu iso tunda a gobe zasu koma, ga aikin tarbar tasu da yawa.”

Nanne ta d’an zare idonta tace.

“kice yanzu gabad’aya gidan zai tashi.”

Don lefen jamila shine na karshe da za’a kawo kuma wanda kowa yafi d’okin gani a cikin na yayyen nata hud’u da za’a aurar, kasancewar wanda zata aura din a can nijar yake, d’an wata yayar baffan nasu ne da suke kamar cousins ita da baffan, kuma k’anin mahaifin baffan ne ma ya had’a auren, a cewarsa sunyi nisa da danginsu hakan zai dad’a kusanci tsakaninsu ya kuma sa zumunci ya d’ore.

Shine da akace baffan ya bada ‘yarsa ya had’a da jamila ‘yar gidan mama rabi, wanda zuwan yaron d’aya wajenta, aka tsaida maganar auren tare da nasu Aisha d’iyar hajiya babba da zata auri cousin d’inta, da Nafisa da maryam ‘ya’yan mama halime.

Dama kusan duk sa’anni ne su hud’un, har ana zasu tafi su bar ita jamilan kasancewar ta dorawa kanta akidar sai mai kudi zata aura, don kowa shaida ne a gidan bata saurayi sai d’an wani babba ko mai nauyin aljihu, to sai abin yazo a daidai, don wanda zata aura d’in mai suna Al’ameen, mahaifinsa shahararren mai kudi ne a nijar d’in, shi kansa baffan ma bai sanshi sosai ba saboda gabadaya karatunsa a k’asashen waje yayi, shi yasa ma da akayi had’in babu wanda yaji bakin jamilan ko ita mama rabi akan basa so.

Wanda da ace bashi da kudi, kowa a dangi sai yaji masifar da zasu yi wadda zata sa a fasa auren. Amma yanzu mama rabin bata da magana sai habaicin cewa ana yiwa ‘yarta kishi.

Kuma kusan hakane, don hajiya babba ce kawai bata sa ido akan auren ba, saboda ita irin k’ananan abubuwan nan wani bata ma sanin anyi, danginta na uwa da uba kaf! masu arziki ne, shi d’an wan nata ma da Aisha zata aura in bai fi su Al’ameen d’in kudi ba zasu iya karawa.

Amma mama halime ba wanda ya kaita kishi, ganin ita har ‘ya’ya biyu zata aurar, amma duk cikin mazajensu ba wani mai shahararren arziki sai dai rufin asiri, duk da cewar kuwa ‘ya’yanta sunfi kowa gayu a gidan.

Don a lokacin da taji zancen ma cewa tayi kamata yayi tunda itace mai ‘ya’ya mata baffa yayi had’in da zainab, wai ai jamilan tana da tarin samarin dake sonta. Sai dai sanin kanta ne baffa ba zai taba yin hakan ba, tunda jamilan itace gaba da zainab.

Ita kuwa Aunty amarya bak’in cikinta bai wuce na cewa ‘ya’yanta sune k’anana a gidan ba basu kai minzalin da za’a fara damawa dasu ba, tunda ‘yan biyunta manya sai yanzu suke jarabawar fita daga sakandire, Kuma ko a cikin mazan sune k’anana, don muhammad da nasir ma ‘ya’yan hajiya babba aiki suke yi banda Ahmad ma da yayi aure, ishaq ne kawai ya koma k’aro karatun masters, suma ‘ya’yan mama rabi bayan ibrahim da yayi aure, sulaiman da umar duk aikin suke yi. 1

****

“ke don uw**ki ina zaki da sassafen nan?”

Muryar sulaiman ta katseta a daidai barandar waje, d’a na biyu a wajen mama rabi, yana tsaye daga jikin ‘yar karamar katangar data raba k’ofofin d’akunansu da hanyar shiga gidan yana danne-danne a wayarsa, har tayi tunanin me yasa bai tafi aiki ba ta tuna cewa duk ranar da za’a fitar da kaya a gonar baffa tare da mazan gabadaya yake zuwa, har da masu auren ma kuwa, ita ko kadan bata kula ta wuce shi bama, a ranta tace.

Ba dai uwata ba sai dai taka. 2

“Nace ina zaki?”

“Inna ce take son auduga, shine zanje in yiwa salisu bayanin irin wadda za’a kawo mata.”

Ya d’ago ya kalleta.

“Duk mutanen da zasu je ba wanda zai iya fad’a masa sai ke?”

“Ni ta yiwa bayani ne don zai fi saurarata.”

Ya kalleta da mamaki.

“Saboda ke k’anwar babbarsa ce?”

Tayi kamar tace wani abu amma sanin hakan zai iya zama kamar ta zage shi ne had’e rai ta juyar da kanta gefe. +

“Koma ciki kafin in take ki.”

Dama abinda take jira kenan, saboda haka tun kafin ya rufe baki ta taho fuuu! ta wuce shiB2

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


“Yo, daya dawo min dake shi ya san irin wadda nake so ne koko ma zai fad’awa salisun ne?”

Inna ta tambaya tana kallon nanne dake cin d’umamen da mama Azumi ta kawo bayan fitarta.

Hankali a kwance ta daga kafad’unta.

“Nima ban sani ba…tunda har ya iya zaginki ina ruwansa da wata audugar da kike so.” 1

“Wai ni ya zaga b’aro-b’aro?”

Ta saki lomar data d’auko cikin hannunta.

“Toh inna uwata fa yace, a duniyar nan ina da wata uwar ne bayan ke…” 2

Inna ta sake kwafa tana kokarin tashi.

“Rabu dashi dani yake zancen, Allah zai kawo shi har nan wajen ina zaune, daga shi har tasa uwar kuwa da yake tak’ama da ita.”

Awanni hud’u bayan haka, Sadiq d’an wajen Aunty amarya dake sa’an Nannen ya shigo rik’e da wata k’atuwar leda cike taf! da farar audugar. Ya dire ta a gaban inna wadda ta hau dubawa tana sababinta, sannan ya matsa kusa da nanne dake yankan farcenta ya d’an sunkuyo yace.

“‘Yan mata..!”

Taja wani dogon tsaki ba tare da ta d’ago ba, tun lokacin da ya samu labarin cewa in tana yarinya aka tambayeta ita mace ce ko namiji sai ta fara kuka tana cewa ita ‘yanmata ce shikenan ya addabe ta, dama k’iris yake jira ya samu wani abin da ya san bata so, tunda a duniya burinsa kawai yaga ya tsokane ta.

“ke kika d’aukewa ya suraj kayansa da aka shanya a baranda? tun jiya yake nemansu.”

Jin haka yasa ta d’ago da dara-daran idanunta ta kalle shi.

“Shi yace maka ni na d’auka, a ina zanga wasu kayansa ma balle in d’auka.”

“Na san zaki iya daukar ne shi yasa na tambaya, in ma kece gwara tun wuri ki mayar masa, don wallahi ransa ya b’aci kuma yanzu zasu dawo, nima don yaya sulaiman yace in biyo su Aminu ne da tare zaki ganmu.”

Caraf! kuwa inna ta karbe zancen.

“Kaga ni bana son neman tashi hankali da safiyar nan, daga aiko ka kuma sai ka soma bin ta da sharri, ina nanne ina wasu kayan surajo?”

“Rabu dashi inna, in ma na d’ebo ai dole nan zan kawo kuma zaki gani.”

Sadiq yayi dariya kafin ya juya yana fad’in.

“Ni dai na fada miki, don wallahi kin san halinsa.”

Ta sake jan tsaki sannan ta mike ta shiga bandaki don d’auraye hannunta. sai dai wani b’arin na zuciyarta tsoron kar da gaske sadiq yaje ya fadawa suraj cewa ita ta dauki kayansa ne, don ta tabbata ko muryar inna zata dushe wajen fad’a sai ya jibgeta kamar yadda ya saba, shi yasa ko kad’an basa shiri da inna.

Tana fitowa ta nufi can kasan kayan wankinsu inda ta cusa kayan nasa, kala biyu na shaddar gezna, wadda baffa ya bayar akayi musu aiki tun daga maiduguri, ta sake duk’unk’une su a ranta tana fad’in.

Ba dai ni zaka yiwa tsawa a gaban abokanka ba, wallahi haka zanyi ta kwashe duk wani abun da kake so. 1

Ta fada a zuciyarta.Yana tsaye daga jikin wata tsohuwar container data raba gate din gidajen biyu yana lura da masu aikin feshi da suke yi a k’ofar gidan. +

“Wai dama da gaske gidan nan tarewa za’ayi?”

Nanne ta tambayi rahama dake tafiya a gefenta lokacin sun dawo daga islammiyya.

“Tun jiya naji mama na fad’a, wai har sun fara kawo kaya ma…gwara ku sami makota ai gidan ya dad’e ba kowa.”

Sun iso daidai bakin gate din kenan zasu wuce, d’aya daga cikin masu aikin feshin ya juyo da bokiti cike da ruwa zai watsar a kasa, cikin rashin sa’a sai abin yazo daidai da sanda suka k’araso wajen, ruwan gabadaya ya sauka a jikinsu, tun daga hijabi har kan takalmansu.

“Malama dan Allah kuyi hakuri, wallahi ban san kuna bayana.”

Nanne ta d’ago da mamaki ta kalleshi.

“Kamar yaya muyi hakuri? Ta yaya zaka jika mu da k’azamin ruwan nan sannan kace muyi hakuri?”

“Toh in ban baku hakuri ba me zance?”

“Wallahi ba wani zancen hakuri sai ka biya kud’in kayan nan tunda uniform ne, ko kana tunanin zamu sake saka su ne a haka?”

Ya girgiza kansa rike da bokitin.

“Wannan ma zancen banza ne, ta yaya daga jik’a ku za’ace sai in biya kudin kaya?”

Jin muryar mutumin a sama yasa imran juyowa daga wayar da yake yi, idonsa ya gano masa ita tsaye daga jikakken uniform a kusa da kawarta, ta hade rai tana dallarawa mutumin nan harara sanda yake magana, abin yaso ya bashi dariya ganin yadda take fiffikewa wajen magana kamar zata cakume shi.

“Ka san Allah malam ba wani zance sai ka biya kudin kayan nan….”

“Na rantse da Allah in dai baku hakura sai dai ku san yadda zaku yi.”

Wani daga cikin abokan aikinsa ya juyo yace.

“Haba ‘yanmata ku baku san tsautsayi bane?”

“Bamu sanshi ba…abinda muka sani kawai a biya mu kudin da zamu sake kaya.”

Rahama ta janyo hannunta.

“Dan Allah ki rabu dasu, yanzu in ya baki kudin ma karba zaki yi?”

“Wallahi karba zan, ni da hakkina…?”

Bata kai karshe ba, muryarsa ta katseta mai taushi daga gefe.

“Uhm kaga…” mai aikin ya juya.

“…Ka tambaye su nawa ne kudin kawai.”

Ta juya ta kalle shi, jingine da container kofar gidansu, yasha farar shadda da hula mai kyau, ranar data fara ganinsa kenan, ranar da ya fara shiga cikin tunaninta….

“Baffanki ya fara fad’a kan bakya zuwa gaishe da su hajiya, don jiya yake ce min ya bawa halime shadda a dinka muku ke da zainab tace masa ai ita tafi sati biyu ma bata ganki ba, don haka da kin gama shiryawa yanzu kibi dakin kowacce ki gaishe ta.”Inna ta katse tunaninta tana kurb’ar koko, Nanne ta kalleta sannan ta cigaba da shafa man da take bayan ta fito daga wanka.

Ko kad’an bata so haka ba, don duk cikinsu babu dakin wadda take son shiga, tafi son tayi harkarta kowa ma yayi tasa…in sun hadu a tsakar gida ko a baranda ta gaishe su da kai.

“Inna ni wallahi da wani waje zamu da rahma, in d’inkin ne ayi min iri d’aya da zainab kawai, waccar atamfar ma da baffan ya bayar ai ba’a tuntube ni ba suka yi min wata ‘yar mitsitsiyar riga.”

Zainab itace ‘yar autar mama halime, kuma kusan sa’ar nanne don da watanni bakwai kawai ta girme ta.

“Ni ba ruwana da zancen dinki, in sun ga dama ma su dinke mata shaddar duka, nace dake kawai kije ki gaishe su, in sun ganki ai shikenan ba mai sake zuwa ya fadi wani abu akanki.”

Ta hade rai kan ta nufi wajen kayanta don daga yanayin muryar innan, ta san da gaske take sai taje.

Dakin mama halimen ta fara shiga bayan ta shirya cikin wata doguwar riga ta jan material, sannan ta yafa dankwalin kawai akanta, hannunta rik’e da bak’ar leda mai cike da kanwa wadda inna tace ta kai can kicin wajen su mama azumi.

Maryam kadai ta tarar a falon, zaune akan kujera tana karyawa da alama bata dade da tashi ba, don kuwa akwai ta da son bacci musamman na safe.

“Maman tana ciki ne?” ta tambaya tsaye daga bakin kujera.

Kamar baza ta amsa ba, don sai da ta gama taune abinda ke bakinta sannan tace.

“eh.”

“Gaisheta nazo yi.”

Ta d’ago ta kalleta sarere.

“sai ki jirata ta fito.”

Tana rufe baki kuwa Nafisa da zainab suka shigo, hannunsu rike da wasu manyan ledoji, kallo d’aya nafisa tayi mata ta shige, zainab d’ince kawai ta mata guntun murmushi kasancewarta mai saukin kai, don ba don rashin yawan maganarta ba da sun d’anyi shiri da nannen.

“Kar dai wai an samo?” cewar maryam da saurinta lokacin data sauko tana ajiye kofin hannuta a k’asan kujera. Nafisa ta mik’a mata ledar da take rike da ita tana fadin.

“Zauna nan, ina tashi daga bacci naga sak’onsa wai an samu kayan ba shiri na azalzali idris (direbansu), in gaya miki sha d’aya muna can, mun ma riga shi isa shagon.”

Maryam ta hau zaro wasu tsantsara tsantsaran lesuna masu kalar milk da orange tana fadin.

“Sune kuwa, yanzu guda nawa ne anan?”

“sha tara ne, amma bamu bar shagon ba sai da nasa ya kulle guda talatin da daya a store kinga hamsin din kenan…don kar ma yace mana an siya wasu.”

“Wooo….” ta d’an yi ihu sannan ta had’a da zagi.

“Wallahi kowa sai ya san anyi ankon da har a gama bikin gidan nan baza a sake yin irinsa ba.”

Nanne ta kalli lace din da akewa ihu, don kyau yayi kyau don ba karya sun san harkar gayu, amma ya za’ace har a gama bikin kowa a gidan baza’ayi mai kyansa ba, ta tabbata ma wanda su hajiya babba zasu fitar sai yafi nasu tsada don ba had’i tsakaninsu.

Idonta ya kai kan kofin da maryam ta ajiye, ta juya taga duk hankalinsu ya tafi wajen kirga kayan, zainab kuma ta dauki wayar maryam din tana dubawa, a hankali ta matsa dab! da kujerar sannan ta damk’o k’ura-k’uran kanwa guda biyu, ta dubi tean da yasha madara kamar me, ta jefa ba tare da sun ankara ba.’yan kasuwar ne har suka dawo…” muryar mama halime ta ratso daga cikin d’akin kafin ta dage labulen ta fito, sai dai ganin nanne tsaye daga jikin kujera ya tsaida ta, cikin kissa tayi murmushi tace. +

“Yau bak’uwa muka yi ne?”

Nanne ta kalle ta daga inda take tsaye, sanye cikin wata hadaddiyar shadda data sha aikin dutse, abin yaso ya bata mamaki, don ta san ba wani shiri suke da mama rabi ba da har zata yi wannan kwalliyar don karb’ar lefen ‘yarta, sai dai fa ko don ta cusawa mutan gidan haushi.

“Ya kika tsaya daga nan, zainab baku ce ta zauna ba, shigo ciki mana.”

Kamar gaske. Ta ayyana a ranta kafin tace.

“Nan ma ya isa mama, dama zuwa nayi in gaishe ki, ina kwana.”

“Lafiya kalau, ya innan da k’afa jiya na fita tun safe ai bamu gaisa ba.”

“k’afarta da sauki, tace a gaidaku kuma.”

“Muna amsawa, zauna mana.”

“Ba komai mama, tafiya zanyi ma sai anjima.”

Har ta juya maman tace.

“A’ah dawo kici abinci mana, maryam kina kallon kanwartaki ba kiyi mata tayi ba?”

Abin ma yaso bawa nanne dariya, wai a cikin gidansu ake mata tayin abinci kamar taje wani bak’on waje, abincin da a yanzu in ta tuburewa inna bashi take so ba, dole ta fad’awa mama azumi a canja in yaso wanda ba zai ci ba, ya nemi wani abin.

Ta girgiza kanta.

“A’ah mama taci abinta wallahi, a k’oshe nake.”

Tana fadin haka ta juya ta bar dakin, sai dai kafin ta gama zura takalmanta taji sanda maryam ta furzar da wani abu sannan cikin muryar fushi tace.

“Meye wannan?”

Da murmushinta ta nufi falon aunty amarya, inda ta tarar gabad’aya yaranta na nan banda ‘yan biyu da suka tafi wajen fitar da auduga, safiya da surrayya sun baje suna kallon wani film d’in larabawa, ta tab’e baki ganin yadda hankalinsu ya tafi gabadaya akai, ita abinda baya gabanta kenan kallo, don tvnsu ta dakin inna sai tayi kusan sati biyu bata kunna ba, tunda itama inna ba kallon take ba, sadiq dake can kan dining ya d’ago daga cin abincin da yake yi bayan su safiya sun amsa sallamarta.

“Kayan kika kawo a ledar? don wallahi na tabbata suna hanya yanzu.”

“Sadiq na gaya maka kafi harkata, don wallahi daga kai har kayan gabadaya sai in had’a in zage ku.”

Ya kyalkyale da dariya harda buga table din gabansa.

“Na zata ai zaki ce harda mai kayan, tunda baki ji waccan shawarar dana baki ba bari in sake miki wata, kije ki canja kaya kisa masu nauyi-nauyi da zasu kare miki duka ba wannan fale-falen ba, don jawur zaki koma yanzun nan.” 1

Taja tsaki kafin ta juya wajen surayya ‘yar autarsu da bata fi shekara tara ba tace.

“Ina Aunty?”

“wanka take yi.”

Kamar ta jira ta fito kuma ta tuna sadiq yace yanzun nan su suraj zasu dawo, kuma ba lallai ma ta samu wata tarbar arziki daga wajen Auntyn ba don haka tace.

“In ta fito kice nazo gaishe ta.”

Har ta juya safiya mai bin sadiq ta tsaida ita.

“Yaya Aisha tace zata samu a gad’ar da cousins dinta zasu yi ranar kamu, in kina so ki fada mata kema ta saki.”

Kamar tace mata eh kuma ta tuna rawa ce, daya daga cikin abubuwan da bata iya ba, saboda haka tace.

“Gaskiya bana jin inna zata barni.”

Safiya ta gyada kanta sannan ta maida hankalinta kan tv. Dad’in nanne dasu kenan ita da surrayya basa taba mata rashin kunya ko wani abu, duk ko da cewar mahaifiyarsu bata sonta. Shi yasa itama take jin dadinsu musammam ganin sune kadai wad’anda ta girma a gidan.Tana isa falon hajiya Babba ta tarar kanwarta mai suna Aunty hadiza da wata mata da bata sani ba sunzo ana lissafin adadin labulayen da za’a siya na gidan Aisha kasancewar sunje sun gano gidan. +

Ta gaishe su suka amsa mata ba yabo ba fallasa sannan ta tambayi inda Aishan take, hajiya babba ta shaida mata tana dakinta, tayi zaton zata kirata ne don haka ta cigaba da zama a wajen, sai dai ga mamakinta kai tsaye hajiyan tace ta tashi ta shiga dakin.

STORY CONTINUES BELOW

Tun daga kofa take k’arewa dukiyar da aka narka a dakin kallo, tana iya tunawa shigarta ta karshe komai na dakin lemon green ne amma yanzu an canja zuwa milk and ash, gaskiyane da inna ke cewa ita kanta hajiya babba mai kudin kanta ce, su mama rabi kawai haukansu suke a gefe.

“A’ah daga nan, karaso mana.”

Aisha dake kwance a gado tana waya tace da nanne.

“…zaka d’an ara min miti biyu?” ta tambaya cikin wayar, wanda suke wayar da ba tantama nanne ta fahimci wanda zata aura ne ya fadi abinda ya sata murmushi kafin ta katse kiran ta mike zaune.

“kina lafiya? Kwana da yawa?”

“Lafiya kalau.” Nanne ta amsa da murmushi, a ranta tace ‘ya’yan hajiya babba kenan, ko basa sonka baza su taba nunawa ba shi yasa a duk sanda ta gansu gaisuwar mutunci ke hada ta dasu, duk ko da kafin ta gansu din aiki ne, don ko ita Aisha da take mace sai tafi sati bata ganta ba don kusan kullum a makaranta take yini, balle kuma mazan dake aiki, kuma yawanci ma sunfi shiga dangin mamansu.

Daga nan bata ko kalli hanyar d’akin mama rabi ba wanda ke cike da mutane tayi kasa ta nufi kicin. Anan ta tarar gabadaya ma’aikatan gidan harda wanda ba b’angaren girki suke ba anata hada hadar abinci kala-kala da kuma snacks fal duk cikin umarnin mama rabi.

Ta wuce can karshe inda mama azumi dasu lami ke packaging wasu snacks d’in a foil paper.

“Farar mace alkyabbar mata, balle kuma in tasa jan kaya, haba wa!.”

“Kai mama azumi, kema ai jan kayan ne a jikinki.”

“Yo ke kya had’a fatar budurwa data tsohowa irina.”

Tayi murmushi sannan ta mik’a mata ledar.

“Gashi inji inna.”

“Me muka samu….kinga kanwa mai kyau wallahi, a ina ta same ta haka?”

“Wa ya sani….” ta fada tana d’anewa kan durowar data zagaye k’aton kicin d’in, bata ko kalli su lami ba dake ta faman d’auke kai suna maganganu don su nuna kamar basu ganta ba.

“…Naji kamar tana kawo mata akayi. Mama azumi a d’an zubo min kad’an yunwa nake ji.”

“Kai uwata, na san fa tare kuka ci tuwon nan da inna, ina yunwa ta isa ta kamaki?”

“Toh dan Allah a d’an bani ladan k’anshin da naji.”

“Haka dai zaki ce, kuma wannan ai ko baki fad’a ba.”

Ta yago foil paper dake hannunta ta shiga zubo mata su samosa da meatpie wadanda ke cike taf! da nama bisa umarnin mama rabi. Tana ci suna hirarsu da tare, don dad’i sai shilla k’afafunta take yi tana zuba santi wanda kesa mama azumin dad’a tsokanarta.

“Toh ga fa ‘yan gona nan sun dawo.”

Mama azumi ta fada tana duban windon dake bayanta, nanne na juyawa ta ci karo da samarin gidansu kaf! Su tara, har kuwa da yaya Ahmad da yaya ibrahim masu aure, sun sako baffa a tsakiya kowanne cikin shadda mai kyalli da hula kalar kayansa, baffan sai murmushi yake yana yiwa ya Ahmad magana, idonta ya kai kan ‘yan biyu da suka yi ankon shudiyar shadda daga gefen yaya umar, kamar kodayaushe suraj ya had’e girar sama data k’asa kamar me shirin lailayo zagi, ta inda ake gane su da salim kenan don shi ba laifi yana da d’an sakin fuska.

Cikinta ya bada k’ara lokacin da tayi saurin juyowa don kar su ganta, mama Azumi kuwa sai fadi take.

“Masha Allah, masha Allah…Allah ya bawa kowannen ku zuri’a irin haka kuma.”

Ta had’iye abinda ke bakinta kafin tace.

“Haba dai in kowannensu ya sami ‘ya’ya irin haka, ai ina jin sai mu shiga tarihi a matsayin zuri’ar da suka fi kowacce yawan haihuwa.””Yo ai ba abin gudu bane uwata, ‘ya’ya fa suna d’aya daga cikin rahamomin duniya.” 1

Daga nan ta juya tana bawa su lami odar a shiryawa ‘yan mazan abinci don ta san yanzu kowannensu zai fice ganin mata sun fara cika gidan.

Nanne ta dad’e a kicin d’in tana ta ganin hada-hadarsu kafin Rahma tazo ta tarad da ita.

Rahma ita kadai ce k’awar da take da ita bayan kawarta ta makarantar boko Amina, jikar d’aya daga cikin tsofaffin ma’aikata gidan ce wadda ake kira da hajiya, a yanzun haka ita hajiyan ta rasu sai babar rahman ce ta maye gurbinta kasancewarsu masu k’aramin hali, wanda a yanzu shekara biyar kenan tun rahman na ‘yar karama take zuwa da ita har ta fara wayon da take d’an kama mata wasu abubuwan, dalilin da yasa ma kenan ya zama kullum tare suke zuwa, don gidansu ba nisa daga nan.

K’awancen nasu ya fara ne tun suna k’anana lokacin da kowannensu bai san ciwon kansa ba, in sunzo za’a had’u dasu zainab da nannen ayi ta wasa wani lokacin ma har da sadiq da yazama sune sa’anninsa. Sai dai tsakanin nannen da rahma ne kawai abotar ta d’ore saboda ita rahman tana da tsananin hakuri, tana jure duk wani rashin mutunci da abubuwan da nannen ke saka ta har zuwa yanzu da don kanta take ragwanta mata ganin irin hak’urin da take yi da ita.

“Wai tun d’azu dama kinzo ina nan inata jiranki?”

“Kiyi hakuri yau aikin gidan ne da yawa, kin ganni ko hijabi ban cire ba wallahi tun zuwanmu.”

“Toh ya zancen zuwan? Zamu je fa.”

“Ki bari dai zuwa d’an anjima in anci karfin aikin, yanzu in na tafi mama zata iya yin magana.”

“Saboda ke sai a kasa yin wani abin, kin san fa anjima ‘yan kawo lefe ne zasu zo, gidan k’ara cika zaiyi.”

“Toh bari in gaya mata inji.”

“Ki dai wanke hannunki bari inje in d’auko mayafina.”

Ta mik’a mata ragowar meatpie da samosan hannunta kafin ta diro k’asa.

“Nagode.” Ta k’arb’a da murmushi.

Nanne na d’age labulan kofar d’akinsu tayi turus! Ganin ‘yan mazan gabadaya sun baje a cikin falon, inna na daga tsakiyarsu tana ta washe baki, kowannensu kuwa ya d’ago ya kalli kofar d’akin harda yaya sulaiman dake maitar danna waya.

Ta had’iye yawu lokacin da yaya Ahmad ke fad’in.

“Ke dama kina nan?”

Duk da da gabanta dake fad’uwa a ranta saida tace.

“Ina zani nida gidan ubana.”

Tayi kamar ta juya ta koma amma muryar hadiza ta katse ta daga baya.

“Zamu wuce.”

Ta juya ta gansu kusan su biyar d’auke da manyan-manyan tire shak’e da kayan abinci.

Ba musu tayi cikin d’akin, sannan ta dan durkusa ta gaishe su lokacin da ake ta faman dire musu abincin.

“ke zo nan!”

Tar! muryar suraj ta kirata a cikin hayaniyar da aka fara ta zuba abincin, ba damar tace bata ji ba don saboda wani tsautsayi yana magana ta kalle shi.

“An shanya min kaya a baranda jiya kuma daga nan ba’a gansu ba.”

Ya fada kamar mai bata labari bayan ta isa gabansa, zuciyarta cike da tsoro ta daure tace.

“Toh ni meye had’ina da kayanka?”

A cikin hayaniyar nan suka tsinci muryar innan na fad’in.

“Surajo me tayi maka ne?”

Bai ko bi ta kanta ba yace.

“Kije ki d’ebo min su yanzu kafin in mik’e in fasa kanki.” ya fad’i kalmar fasawar kamar zata fashe da bakinsa.
“Ban gane ba, kana nufin ni na d’auka? Toh ni ba barauniya bace, kuma ko zanyi sata ma sai in k’are a kayanka…”

Kafin ta rufe bakinta kuwa taji saukar wani azababben mari a fuskarta wanda ya taho tare da salatin inna.

“Kai meye haka?”

Yaya Nasir da yaya umar suka had’a baki wajen fad’a, nanne ta rusa wani irin kuka da rabinsa na k’arya ne.

“Me tayi maka?” ya muhammad ya tambaya, kafin ya amsa kuwa inna ta karbe.

“Me ko zata yi masa banda tsananin azaba irin tasa.”

“Nace me tayi maka?” ya muhammad ya sake tambaya.

A dak’ile ya amsa.

“Yaya kayana na shanya a courtyard ta d’ebe.”

Kafin a tambayeta nanne ta k’ara rushewa da kuka tana fadin wallahi tallahi k’arya yake ita ba abinda ta dauka.Kai dama tana d’aukan kayan ka ne?” yaya Ahmad ya shigo zancen. +

“Ba wai tana d’auka bane, na san ita ta d’auka don ita kadai ce a wajen lokacin da aka shanya.”

“Toh ai hakan baya nufin ita ta dauka…ke kuma kar in sake ji kince k’arya yake, tashi ki tafi.”

Dama abinda take jira kenan, saboda haka yana fad’a ta mike tayi ciki.

“Guda nawa ne kayan?” Taji yana tambayar suraj bayan ta shiga d’aki.

Ta wanke fuskarta sannan ta yafa d’an karamin mayafi lightbrown akan doguwar rigar, ta nufi wajen kayan wankinsu ta janyo kayan suraj d’in dake can k’asa ta cusa su a bak’ar leda tana fadin..

“Kai da kayan nan har abada wallahi.”

Ta fito har a lokacin suna hayaniyarsu ana ta dariya, kanta a mik’e ta fita, Allah yaso idon inna bai hango ta ba lokacin ta juya tana ganin adadin abincin da yaya ibrahim ke zuba mata.

Tana sauka k’asa ta tarar Rahma na jiranta a bak’in k’afar bene.

“Me tace?”

“Tace dai kar mu dad’e, don wai an tafi markad’en Alala zamu yi k’ulli.”

“Ai dama ba dad’ewa zamu yi ba, abinda ya kaimu kawai zamu yi.”

Ko dai abinda ya kai ki. Rahma ta fad’a a zuciyarta.

Don inda zasu je d’in gidan wata ‘yar islamiyarsu ce Hafsa, a sati biyun da nanne bata je makaranta bane hafsan ta tada ballin cewa nanne na neman kwace mata saurayinta, wanda kullum aka tashi zai zo ya raka ta gida. Ta dinga masifar cewa wai duk sanda aka tashi sai ta dinga binsa da kallo wani lokacin ma harda murmushi. 1

Abin ya zama topic d’in ajin nasu kullum sai an tada zancen da za’a zazzage ta, ganin ma taki dawowa yasa suka rubata takarda aka gaya mata bak’ak’en maganganu sannan aka bawa safiya ta kawo mata shekaranjiya da yamma, jiya kuma ta titsiye rahma sai da ta gaya mata dukkan abinda yake faruwa da bata nan.

“Zamu biya ta shagon khalid kafin muje.”

“Wane khalid?”

“Mai shagon bakin titi mana.”

Khalid irin ‘yan karyar samarin layin nan ne da ba abinda suka sani sai d’aukan wanka, iyayensa masu rufin asiri ne daidai nasu, amma shi inda yake kai kansa yafi haka, shagon da yake dashi ma na soft drinks da recharge card wani Alhajin layinsu ne ya bud’e masa. Dalilin haduwarsu da nanne kenan wajen siyan lemo.

Suna isa kuwa ya tsuke bakinsa yana murmushi, kafin ya fito ya fara shafa sumar kansa irin ta fulani.

“Kin b’uya fa, kwana wajen shida kenan ban ganki ba.”

“Shida?”… Ta zare ido tana kallonsa.

“Har wani kirgawa kake?”

“Sosai ma, ke d’in ai ta daban ce.”

Ta tab’e baki kafin ta mika masa ledar hannunta.

“Kaga rik’e, kaya ne na kawo maka ban sani ba ko zasu yi maka?”

“waww! Ai ko nagode sosai zasu yi ma insha Allah…”

Ya d’ago ya kalleta, idonsa d’aya a kanne.

“Thank you, har na hango ni a ciki.”

“Wai me yasa kika damu da Khalid d’in nan ne.”

Rahma ta tambaya bayan sunyi gaba.

“Saboda bashi da matsala, kuma yana yin duk abinda nace.”

Ta amsa kanta tsaye wanda kuma hakan ne, in dai mutum zai jure halinta ya kuma dinga yi mata biyayya toh fa zasu yi shiri dashi.

Rahma bata kara cewa komai ba, tunda ita ta san abinda khalid ke tunani daban ne, don har ya fara yad’awa a unguwa cewa nanne sonsa take yi, zaiyi auren jari.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]