[Advertisements⬇️]

TSANANI CHAPTER 9 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TSANANI
CHAPTER 9Sun ɗauki lokaci mai tsawo suna jiran dawowarsu Adda saratu amma shiru babu su babu dalilin su, sun yi jira ya kai na awa biyu har sai da suka fara gajiya, ganin ba su da niyyar dawowa ne yasa suka ɗauki hanyar xuwa wajen innar Sa’adatu don jin wajen da suka tafi da kuma inda aka boye Sa’adatu. +

Zaune take a daki ta idar da sallar la’asar tana ta jero addu’o’i a kan Allah ya kawo musu mafita ita da Sa’adatu, bayan ta kammala ne ta janyo Kur’ani ta fara karantawa. Hayaniyar jama’a ta ji a tsakar gidan a yadda alama ta nuna dukkan matan gidan ne suka hallara a tsakar gidan suna jin abinda Baban Sa’adatu yake faɗa musu, gaba ɗaya sun bashi hankalinsu suna sauraren abinda yake faɗa, ganin ba a kirata ba kuma ba a sa da ita bane yasa tayi xamanta a daki ta cigaba da karatunta, daga can taji kamar har da Malam Jibo ake maganar don taji irin muryarsa duk da dai bai fi gani ɗaya ta taɓa yi masa a rayuwarta ba, amma kuma magana ɗaya biyu sai taji an kira sunan Sa’adatu, wannan dalilin ne yasa ta ƙara bada hankalinta don jin abinda suke faɗa tare da addu’ar Allah ya kareta daga sharrinsu da dukkan abinda suke kullawa. Tashi tayi ta fara ninke kayan wankin da tayi, juyowar da xata yi tayi ido huɗu da Baban Sa’adatu a bayanta yana bin ta da wani irin kallo mai cike da alamomin tambaya.

A hankali ta ɗaga baki xata tambaye shi, ganin tana da niyyar yin magana ne yasa ya dakatar da ita “Ba ki da wani abinda xaki faɗa min na yarda da ke, sbd duk sharri da bita da ƙullin da ake yi kece kika shirya shi, ke kika tura kanwarki saratu gidan Sa’a ta kashe mata aure, sbd har yanzu kuna da burin aura mata wancan shashashan yaron”

Cike da gigita ta dube shi tana motsa baki sai taji maganar ta kasa fita sbd ɓacin rai, kafin tayi ƙoƙarin cigaba da magana ya hau kanta da masifa “wannan wane irin wulakanci da cin amana kike son shirya min, me nayi miki da xaki saka min da wannan abin, tunda ban cuceki ba kema baki isa ki cuce ni ba, ina baki shawara tun wuri kafin lokaci ya ƙuri miki, kiyi ƙoƙarin bayyanar min da inda ‘yata take kafin na wulakanta ki nayi miki tozarcin da baki taɓa tsammani ba,wai ke mutuniyar kirki ko da an fara magana sai ki mayar da fuskarki ta muminai bayan ke cikakkiyar munafuka ce, to wlh kiyi gaggawar cika umarnina kafin ranki ya ɓaci”
Yana gama faɗa ya fice ya bar ɗakin bin sa tayi tsakar gida tana tambayarsa.
“Malam ka bani magana a dunkule ban fahimci abinda kake nufi ba?”

A fusace ya juyo yana nuna ta da ɗan yatsa “Ai baxa ki fahimta ba sbd kin san abinda kika shirya, ni dai na baki lokaci kafin nan da faduwar rana ki san abin yi idan ba haka ba kuma kiga wulakanci”
gaba ɗaya idon matan gidan yana kan innah, shi ma malam Jibo bin ta yake da kallo mai cike da tsana kamar xai kwada mata mari.

Har ta juya xata shiga daki Innah Salamatu da jama’arta suka biyo bayanta suna mata magana.
“Ke kuwa baiwar Allah lalacewar da ta same ki kenan kawai sbd kwadayin abin duniya, kina matsayin uwa kina bawa ‘yarki goyan bayan tayi iskanci kowace uwa ta gari tana so ‘yarta tayi xaman aure, ke kuma kina ƙoƙarin wargaza mata rayuwa wlh kin ji kunya ki gyara halinki sbd kwanciyar kabari”

Girgiza kai tayi kawai ba tare da tace komai ba tayi shigarta daki, don bata san amsar da xata basu ba tunda bata ma san a kan me suke magana ba.

Bayan fitar su malam jibo daga gidan su Sa’adatu kai tsaye sake komawa gidan Adda saratu suka yi don ganin ko sun dawo, bai fi xaman mintina biyar suka yi ba sai ga mijinta tare da ƴaƴanta sun dawo daga islamiyya.
Yana ganin su ya miƙa musu hannu da girmamawa don su gaisa, amma abin mamaki sai suka ki miƙa masa, cikin fushi mahaifin Sa’adatu ya dube shi

“Ba gaisuwa ce ta kawo mu ba don haka ka riƙe gaisuwarka ba ma buƙata, kawai abinda ya kawo mu shi muka zo yi”

Cike da mamaki ya dube su “me kuma yayi zafi haka malam me ya faru me nayi maka da har xaka ki gaisawa da ni?”Gyara tsayuwa suka yi gaba ɗaya suna ta faman huci shi kuwa malam Jibo can yayi da kansa yana ta kunbure-kunbure kamar zai kai masa duka, sake jefa musu tambaya yayi “me nayi muku haka ne naga bamu taɓa samun sabani da ku ba, yau kuma kun xo min da wani bakon al’amari wanda ban saba ganinsa ba”

Cikin fushi Baban Sa’adatu ya dube shi “ina ‘yata da aka hada baki da kai aka je har gidan mijinta aka ɗauke ta ba tare da iznina ba ko na mijinta?? Amsa kawai muke bukata”

A hankali ya dube su “Ba nida hannu ko masaniya a kan abinda kake tuhumata da shi sai dai kawai na san mai dakina taje gidan ka” ya nuna malam Jibo “ta tarar da yarinyarka cikin hali na rashin lafiya, ganin halin da take ciki ne yasa ta taimaka ta kaita asibiti tunda kun gaza, kuma ita ma tana da hakki a kan yarinyar shi yasa ma tayi ƙoƙarin ceto rayuwarta”

A fusace mahaifin Sa’adatu ya dube shi “hakkin menene da ita a kan ‘yata, ita ta haifeta ko kuma dawarta taci ta girma, menene dalilinta nayi min katsalandan a cikin rayuwar iyalina, to wlh tun wuri a dawo min da ‘yata kafin hankalin kowa ya tashi”

Cike da nutsuwa mijin Adda saratu ya fara yi masa magana “wannan duk ba wani abu ne na tada hankali ba malam, taimako mai dakina tayi mata, kuma don Allah tayi ba don wani a cikinku ya yaba mata ba, tunda kun nuna bakwa so shikenan yanxu xamu tafi tare da ku asibitin ku ɗauke ta ku tafi da ita gida kamar yadda ku ka buƙata”

Sauke ajiyar zuciya suka yi gaba ɗayansu ba ƙaramin daɗi suka ji ba da yace zai kai su inda suke, buɗe gidan yayi yasa yaran suka shiga sannan ya taho suka tafi Asibitin, suna tafe suna faɗawa Adda saratu munanan maganganu shi dai bai tanka musu ba, sbd idan ya daka ta tasu sai a yi batacciya.

Suna isowa bakin gate suka tambayi mai gadi don ya nuna musu dakin da Sa’adatu take kwance, ba tare da bata lokaci ba ya nuna musu suka shiga.

Tararwa suka yi ana ƙara mata ruwa, don haka suka nemi waje suka zauna, juyowa likitan yayi ya faɗa musu cewa bata san hayaniya don haka su kula, cikin fushi mahaifinta ya dubi likitan.

“Mu ba ruwanmu da bata san hayaniya domin mu hayaniyar ce ta kawo mu, a bamu yarmu mu tafi da ita ko kuma hankalin kowa ya tashi” cike da nutsuwa likitan ya dubi Adda saratu “wadannan mutanen kuma daga ina suke me kuma suke so a wajen yarinyar nan” kafin ya gama magana Malam Jibo har ya buɗe baki ya fara magana

“Au tambayar matsayinmu ma kake yi, to ni mijinta ne wannan kuma babanta ne, wannan matar kuma yar shiga abinda ba ruwanta ce, domin ita ta karya min dokata ta kawo min matata asibiti ba tare da amincewata ba, kuma yanzu dole ne a tsinke ruwan nan a bamu ita mu tafi gida

A hankali likitan ya xare farin gilashin da ke idonsa ya dube su “to ai ba haka ka’idar aiki take ba malamai dole sai ta samu sauki ko da xamu yi wata magana da ku, yanzu dai kun ga halin da take ciki ya kamata a tausaya mata”

Cikin fushi mahaifin Sa’adatu ya mayar masa da amsa
“kai malam dakata kada ka raina mana wayo kai ka haifar mana ‘yar da xaka fada mana abinda ya dace da mu”

Sai a lokacin Adda saratu ta kalle su tare da mikewa tsaye tana musu magana “Duk da kasancewar Sa’adatu ‘yarka kai kuma matarka, a wannan lokacin babu wanda yake da iko da ita a cikin ku, sbd baku bata kulawar da Allah yace a bata ba, kuma baku yi abinda ya dace a gareta ba, don haka a yanxu ni nake da iko da Sa’adatu kuma babu wanda ya isa ya rabata da asibitin nan sai dai idan warkewa tayi sbd Sa’adatu ba ‘yar da aka ciyo ganima a wajen yaƙi bace da kowa zai riƙa sauke masifarsa a kanta, idan ku bakwa so mu muna sonta kuma xamu kula da ita, idan mahaifiyarta tana jin tsoron ku taki tayi magana a kan zaluncin da ake yi mata, to ni lokaci yayi da xan kwatar mata yancinta”

Hannu malam jibo yasa xai mari Adda saratu da sauri mijinta ya riƙe hannunshi “kada ku kuskura hannunka ya taɓa matata, xan iya hakuri a kan komai amma banda iyalina idan ka sake hannunka ya taɓa ta hukuma ce xata raba ni da kai”

Cikin zafin rai malam Jibo ya fara magana “Ni ba a ga abinda aka yi min ba har xaka ce xaka kaini kotu, idan ka kaini nima Ina da abin faɗa a kanku sbd an keta min haddina” +

Murmushi mijin Adda saratu yayi “To ai ko kotu aka je kaine a hannu, kana da abubuwan da za a tuhumeka da su, domin ka tozarta hakkin ‘ya mace ka wulakanta amanar da ka ɗauka, ka hana ta dukkan kulawar da ta kamaceta, ka hanata abinci da suttura sannan ka sa mahaifinta ya aura maka ita a dole kaga kuwa ko anje kotu kaine a hannu”

Jikin mahaifin Sa’adatu ne ya hau rawa “kaga malam baxa ka kashe mun auren ‘ya ba babu ruwanka da abinda nayi mata tunda ba kai ka haifar min ita ba”

Jan hannun malam Jibo yayi suka fita, kara kanshi yayi a kunnesa yana yi masa rada wanda babu wanda ya san abinda suke tattaunawa.Sun yi tsayuwar sama da minti talatin suna tattaunawar sirri, amma babu mai iya jin abinda suke faɗa, sai da suka gama suka shigo dakin da Sa’adatu take, ko sallama basu yi ba suka samu wajen xama suka zauna suna fuskantar likitan, Malam Jibo ne ya fara yin magana “Yanxu dai ina ganin sulhu ya kamata a yi likita bai kamata a ce matata ta samu matsala kuma an barta a nan wajen ba, ina ganin hakan babu maganin da xai yi sai dai ma ya ƙara mata wata cutar, duba da asibiti matattara ce ta shaidanu, kuma ciwon Sa’adatu ba na Asibiti bane maganin gida za a yi mata, don a ganina tana fama da shaidanun da suke hanata jin maganar mijinta, tunda mun gano hakan, to a bani sallama mu tafi gida tunda ina da taimakon da nake bayarwa, kaga ya kamata a bani ita mu tafi kasancewar matar nan mallakina ce, ko musulunci ya yarda na kafa mata doka ta bi, ga kuma mahaifinta ya bani damar yin dukkan abinda naso a kanta kaga kuwa babu Maganar ta sake xama a nan” +

Cikin nutsuwa likatan ya dube shi gami da sakin wani ɗan siririn murmushi “Dadina da kai dawo da hannun agogo baya Malam, yanzu fa aka gama maganar cewa baxa a sallame ta ba har sai ta warke, me yasa kake son tada mana da hankali, idan har da gaske kake kana son matarka ya kamata ka kula da duk wani abu da xai taɓa lafiyarta, dan Allah ku gaggauta fita daga nan sbd bana so ta farka taji hayaniya jikinta ya sake dawowa sabo, tana buƙatar hutu sosai”

Mijin Adda saratu ne ya dubi likitan “ka ma daina haɗa su da Allah tunda sun nuna basa jin kunyar yin abin kunya, mu ma mun shirya yaƙi da su, xamu yi iya bakin kokari wajen ganin basu samu nasara a kanmu ba” nuna malam Jibo da Baban Sa’adatu yayi “ku fita ku bar Wajen nan na riga da na fada muku yanxu Sa’adatu ba taku ba ce har sai ta warke xata dawo hannunku, idan kuma ba haka ba yanxu ku ga hukuma a nan”

Wani kallo malam jibo ya bi shi da shi, xai buɗe baki yayi magana Baban Sa’adatu ya tari numfashinsa “kada ka fara cewa komai idan ka duba xaka ga mutanen nan ba da alheri suke nufin mu ba, tunda kaga muna sa’insa da su akwai abinda suke shirin kulla mana tashi mu tafi, idan sun san wata ai basu san wata ba”

fita suka yi suka bar asibitin zuciyar su cike da baƙin ciki, suna tafe suna tattauna yadda zasu kwato Sa’adatu daga asibitin.

Sai washe gari Sa’adatu ta farfaɗo a hankali ta fara buɗe idanunta tana ambaton Allah, shafa fuskarta Adda saratu tayi tare da yi mata sannu, a hankali ta bude baki tana mata magana “yaushe kika xo Adda saratu, dama ina ta kewarki malam ya hana naje na ganki” murmushi tayi “Da bai bari kinxo wajena ba ai gashi ni naxo ko?”
Yunkurin tashi daga kwanciyar da tayi ta fara yi amma sai ta kasa, a hankali Adda saratu ta dagota tare da jinginata a jikin gadon, a hankali ta sake buɗe ido “Nan kuma ina muka xo Adda”?
Cike da kulawa ta bata amsa “Asibiti aka kawo ki”
Zaro ido tayi tare da gyara zaman da tayi “Asibiti kuma Adda ya aka yi malam ya bari aka kawo ni amma nayi mamaki sosai”
Rausayar da kai tayi”ai dole kiyi mamaki idan kinga tagagarin da muka yi kafin ma ya bar ni na shiga gidanki xaki yi mamaki, ke dai labari sai kin warke kawai”

Suna cikin hirar likitan ya shigo hannunshi riƙe da magunguna, guri ya samu ya xauna yana duban Sa’adatu “lallai jiki yayi kyau matar malam Allah ya ƙara lafiya”

“A hankali ta amsa da “ameen”
Mayar da kallonsa yayi xuwa ga Adda saratu “Hajiya akwai maganganun da nake so mu yi da ke, Hakan yana da matuƙar muhimmanci ga rayuwar yarinyar nan, idan babu damuwa ki same Ni a waje”
Cike da nutsuwa ta dube shi tare da cewa, “to ba matsala”
Tashi tayi ta bi bayansa. Waje suka samu suka tsaya, kallonta yayi tare da neman izinin fara magana, cike da kulawa tace masa
“Ina saurarenka”
“Kiyi hakuri da tambayar da xan miki yanxu, abin ne ya d’aure min kai ina bukatar na san amsar tambayar da xan miki”
Dago fuskarta tayi tare da cewa”ina saurarenka”
Sauke ajiyar zuciya yayi
“Dan Allah da gaske wannan shi ne mahaifin wannan mara lafiyar, ko kuma dai riketa yake yi?”
A sanya
sanyaye ta amsa masa da “shi ne mahaifinta, shi ya haifeta amma me yasa ka tambaye ni?” +

Gyara tsayuwa yayi “Abinda yasa nayi miki wannan tambayar naga kamar bai damu da halin da take ciki bane, duk da cewa tana cikin halin rashin lafiya amma banga ya nuna damuwa a kan hakan ba, sai ma kokari da yake wajen ganin ya tayar mata da hankali kuma ya rabata da asibitin”

Gajeran murmushi tayi “Hmmm likita kenan idan ana sallah ba a magana Allah dai ya rufa mana asiri kawai”
“Ameen” yace
Cike da nutsuwa ya sake kallonta “Sai kuma magana ta biyu ita kuma shawara ce ba tambaya ba”
Hankalinta ta bashi tare da saurarensa.

“Rokonki xan yi a kan duk rintsi duk wuya kada ki bari yarinyar nan ta koma hannun mutumin nan naga alama kamar bai san darajarta ba, ko da xata koma kiyi iya bakin kokarin wajen ganin kin kwatar mata hakkinta na ya mace, sbd auren nan akwai cutarwa a cikinsa”

Sauke ajiyar zuciya Adda saratu tayi “nima tunanin da nake yi kenan amma ina ganin hakan baxai yiwu ba sbd mahaifinta mutum ne mai taurin kai, kuma ba shi da kirki ko kaɗan”
Girgiza kai yayi “kada ki damu kiyi iya bakin kokari Allah xai taimake ki”

Sun jima suna tattaunawa sannan ta koma wajen Sa’adatu tarar da ita tayi tana bacci don haka ta kyaleta bata tashe ta ba.

********

Yau na ɗauki tsawon kwanaki biyar a asibiti, jikina yayi kyau na dawo cikin hayyacina babu abinda yake damuna sai ɗan abinda ba a rasa ba, tun bayan xuwan da Baba da malam Jibo suka yi basu sake dawowa sun duba ni ba, wannan dalilin yasa xuciyata tayi sanyi don alamu sun nuna cewa malam Jibo ya fara fita daga cikin harkata.

Adda saratu ce ta fita ta kira likita inda ya bamu sallama tare da bani shawarwari a kan na rage damuwa, kuma na daina xama da yunwa, godiya muka yi sannan muka kira mai a dai-daita sahu ya kwashe kayanmu muka shiga.

A hankali Adda saratu take min magana “ina kike ganin xamu je Sa’adatu gidana ko na gidan malam Jibo ko gidan Innah”
A xabure na dubeta “Haba dai Adda me xan koma wannan gidan nayi idan kinga na koma sai dai ko gawata aka kai, wannan gidan da ba shi da maraba da kabari, bana so mu je gidan Innah sbd idan naje kamar na koma gidan Malam Jibo ne

Murmushi tayi tare da dafa kafadata “Nima tsokanar ki nake yi, ai baxan bari ki koma ba sai kin warke sosai kuma sai yaxo mun yi da wajewa cewa baxai cigaba da azabtar da ke ba sannan xaki koma”

Hawaye naji suna shirin gangarowa daga idanuna “Dama kina tunanin komawa ta wannan gidan Adda dan Allah ki daina, ina ji a raina ƙarshen aurena yaxo da malam Jibo”

Dafa kaina tayi “Bana so kina wannan tunanin Sa’adatu, kinga dai yadda muka yi da mahaifinki da irin cin mutuncin da yake mana bana so na shiga hakkinsa na raba shi da ke, tunda kinga ya fi ni iko da ke”

Kafin nayi Magana har kwalla ta cika idanuna, “kada kice haka Adda, idan da sabo kin saba da halin Baba bai kamata wannan abinda yake yi ya sanyaya miki gwiwarki ba, kiyi min gata ki kwato ni daga wannan tsaka mai wuyar da nake ciki, idan ku ka kyale ni ban san inda rayuwata xata kasance ba nan gaba, kinga fa malami ne xai iya yi min asirin da ko ku baxan sake kulawa ba, ballantana har nayi tunanin barin gidansa tunda dai ya iya asirin sana’arsa kenan”

A firgice ta dube ni “Haka ne Sa’adatu insha Allah baxa ki koma hannun wannan azzalumin ba”

Sai a lokacin muka lura da har an wuce layin gidanta, fadawa mai a dai-daita sahun muka yi ya dawo da mu baya, a kofar gidan aka sauke mu.

Da gudu yaranta suka taho suna murna da ganinmu. “Yau kuma kece a gidan mu Aunty Sa’adatu yaushe rabon da mu ganki har mun manta”

Takaitaccen murmushi nayi tare da rike hannayensu “To ai gani naxo yanxu kuma kwana xan yi a nan yau ba tafiya”

Tsalle suka riƙa yi tare da karɓar kayan da ke hannunmu muka shiga cikin gidan tare, kai tsaye daki muka wuce don mu huta.

Hirar su Malam Jibo da Baba muke tayi, da hanyar da xamu bi wajen ganin na tsere daga hannun malam Jibo, shi ma mijin Adda saratu tare da shi muke ta hirar.ƙara jaddada min yayi cewa baxan koma ba, ba ƙaramin daɗi xuciyata tayi ba na jin kalamansa, ji nake kamar an gafarta min xunubaina.
+

A ranar da aka sallami Sa’adatu daga asibiti mahaifinta da malam Jibo suka koma, duba dakin da take kwance suka yi basu ganta ba, wannan dalilin yasa suka je har office din likitan don jin inda ya boyeta, ko sallama basu yi masa ba suka afka office din, sai dai ganinsu yayi kawai a gabansa.

Ajiye takardar da ke hannunsa yayi yana dubansu.
“Lafiya ku ka shigo min office babu sallama ba neman izini??

Binsa suka yi da kallon raini “Baka biyo ta hanyar da xamu yi maka sallama ba katon banza munafuki mai cin amanar bayin Allah”

Cikin rashin fahimtar sakon da suke son isar masa ya miƙe tare da cewa “Har cikin office dina xaku shigo ku xageni ba tare da hakkina ba me nayi muku?”

Malam Jibo ne ya nuna shi da hannu “ai baxa ka san abinda kayi ba sbd ana so a hada baki da kai a ci amanata, to wallahi ka fito min da matata kafin mu bawa hammata iska ni da kai”

Murmushi likitan yayi “Allah ya sawwake da mutuncina na hada jiki da kai, umarni nake baku ku fita ku bar min office kafin na nuna muku fushina na nuna muku gaba dayanku baku isa ba”

A fusace baban Sa’adatu ya dube shi “kai har kana da abin da xaka yi mana kuri da shi, mara kunyar karya, shege ka fasa tsakaninmu da kai, sai ka fito min da ‘yata xan fita na bar nan”

Bai tanka musu ba ya fita ya bar office din, kafin su ankara tuni ya kulle su a ciki ya tafi.

Sai da ya ɗan yi mintuna da fita sannan suka lura da ya kulle su.
Xaginsa suka riƙa yi tare da jijjiga kofar ya buɗe musu amma yayi banza da su.Hannu yasa a aljihu ya dakko wayarsa, laluben number ya shiga yi cikin sa’a kuwa ya samu number wanda yake nema, kara wayar yayi a kunnesa tare da yin sallama, cike da ƙasaita mutumin ya amsa tare da yi masa barka da aiki.
Tambayar shi dalilin kiran da yake masa yayi, cikin siririyar muryarsa ya amsa masa da “wallahi wasu ta’kadaran mutane ne na hadu da su, yanxu suka shigo office dina suna ƙoƙarin ci min zarafi a kan abinda ba nida masaniya a kansa”
Gyara xama mutumin yayi tare da ajiye biron da ke hannunsa
“Su wane ne su kuma daga ina suke? sannan wanene ya turo su wajenka” +

Ƙara saita wayar yayi a kunnesa tare da cewa “ban san su ba ranka ya dade, kawai dai an kawo min mara lafiya ne ta kwanta a asibitina, sai suka nuna kin amincewa a kan kwantar da ita da aka yi, wai su a tsarinsu ba xuwa asibiti sai dai a yi maganin gargajiya, shi ne suka zo xasu tayar min da hankali”

Sake jefa masa tambaya yayi “yanxu ina mutanen suke? Ina fatan dai kun rike su baku bari sun gudu ba”

Da sauri ya amsa masa “Eh suna office dina na kulle su, ban bari sun gudu ba”
Murmushi mutumin yayi.
“Yauwa alhamdulillah naji dadin hakan, yanxu xan turo yara su tafi da su”

Godiya yayi masa sannan ya kashe wayar, ta window Baban Sa’adatu ya leko yana yi masa magiya ya buɗe su, shi kuwa malam Jibo sai masifa yake masa xuciyarsa ta kasa yin laushi.

A hankali ya ƙarasa wajen su yana taku cikin nutsuwa ” Ba dai ba ku da mutunci ba kuma baku san darajar mutane ba, kuma baku san irin wajen da xaku rika rashin mutuncinku ba to yau xan koya muku darasi, ko wani aka ce ku sake ci wa mutunci a duniya baxa ku ƙara ba”
Yana gama faɗa ya bar gurin, cikin mintinan da basu wuce biyar ba har yan sandan sun iso, mikawa likitan hannu suka yi suka gaisa sannan ya nuna musu office din da su malam Jibo suke ciki a kulle, mukulli ya mika musu tare da bin bayansu.

Ba tare da bata lokaci ba suka shiga buɗe gurin, su Malam Jibo na ganin yan sanda ido ya raina fata, nan fa suka fara magiya a kan a taimaka a rufa musu asiri a bar maganar, yan sandan basu sauraren su ba suka sanya musu ankwa suka yi gaba da su.

*************

Innah Salamatu ce zaune a kofar dakinta tayi tagumi, tun bayan isha’i ta gama abinci amma ta kasa ci, sai tunani da take yi kwallawa innar Sa’adatu kira ta shiga yi.
“Bak’ar daga iyayen baƙin hali a fito na kammala tuwon tun daxu a zo a ɗauka, tunda dama haka aka saba abinda aka fi iyawa kenan, a ci a ƙarshe a yiwa miji rashin mutunci a kuma taimaka wajen kakata masa yarsa an yi asara” innah na jinta bata tanka mata ba kuma bata fito ta dauki abincin ba sbd takaicin abinda ta faɗa mata, don ita tuni ta sallama abincin gidan ta hakura da karɓarsa, kasancewar kullum idan za a bata sai an gaya mata magana ko kuma an yada mata da habaici, shi kansa mai gidan bai raga mata ba, wannan dalilin yasa a kullum take jan mutuncinta kuma bata yarda wani abu ya haɗa su da ita ballantana har a faɗa mata abinda xai sosa mata rai.

Ganin shiru bata fito bane yasa ta ɗauki kwanon abincin ta bawa almajiri sadaka, daga bisani kuma ta nufi ɓangaren su salim.

Dakin mahaifiyarsa ta faɗa tare da yin sallama, a kwance ta sameta don har tayi shirin kwanciya bacci, tana ganinta ta tashi xaune tana mata sannu.

Ganinta tayi fuskarta bayyane da damuwa, cike da kulawa ta dubeta “lafiya innar A’isha na ganki haka kamar mara lafiya, Allah yasa dai ba wani abin ne ya faru ba”

Rausayar da kai tayi “Dole ki ganni a haka mama, tun azahar da malam ya fita neman Sa’adatu da jin wajen da aka boyeta har yanxu bai dawo ba, kuma shi ba waya ba ballantana mu kira shi, tunda muke tare da shi bai taɓa tafiya irin wannan ya dade ba, ni tunani nake anya ba haɗa baki aka yi da munafukar nan ta daki ake shirin salwantar mana da rayuwarsa ba kuwa, abin ya bani mamaki, kuma ya d’aure min kai don matar nan ba abar a yarda da ita bace”Gyara xama tayi
“To fa!!! Ni har na rasa bakin magana ma, na rasa ta ina xan fara ni dai nasan malam ba gwanin yawo bane ina zai je haka, shi dai ba karamin yaro ba ballantana a ce ko wajen budurwa ya tafi, kuma kin ce ya faɗa miki inda zai je ko? +

A hankali ta dago kai “ya faɗa min xasu fita da malam Jibo su je neman Sa’adatu, kin san ai uwarta ita ta tura kanwarta gidan ta gudu da ita”

Jinjina kai ta shiga yi “kwarai kuwa an yi haka, tabbas waccen munafukar ta daki tana da masaniyar inda malam yake, amma dai kafin mu yanke hukunci bari na dakko hijabina mu je gidan malam jibo mu tambaya ko shi ya dawo, ko Allah xai sa ya faɗa mana inda yake”

Hijabi ta janyo suka fita, kallo daya xaka yi musu kasan ba a cikin hayyacinsu suke ba don tafiya suke gaba daya ba nutsuwa kamar xasu tashi sama, da sallama suka shiga gidan malam jibo, cike da mutuntawa matansa suka karɓe su gami da yi musu shimfida a tsakar gida, bayan sun gaisa innah salamatu ta fara tambayarta su.

“Dama xuwa muka yi mu tambaye ku dan Allah ko malam yana nan”?

Cike da kulawa uwar gidan ta basu amsa “Ai tun rana da ya fita bai dawo ba”
Sake jefa mata tambaya tayi “Dan Allah ko ya faɗa muku inda ya tafi??”

“A’a gaskiya bai faɗa ba, muna tunanin dai ko gonarsa yaje”
Gyara xama innah salamatu tayi

“Hmm Idan kuna wannan tunanin to ku daina ba gona yaje ba, tare da maigidana ya fita, kuma ni maigidana ya faɗa min xasu fita da mijinku ne wajen neman Sa’adatu kinga kuma har yanxu gashi karfe tara da kusan rabi basu dawo ba, a ganina anya ba salwantar musu da rayuwa ake shirin yi ba”

Da sauri matan suka dubeta “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un to ai mu bamu san haka ba, bai kuma faɗa mana ba sbd kwana biyun nan yana fushi da mu a kan mun bari an kai Sa’adatu asibiti yau ku san sati guda baya yi mana magana”

Girgiza kai Innah Salamatu “Ai tun usuli ku kuka yi wa kanku shirme da ku ka bari aka fita da ita, duk wannan rashin lafiyar da take yi na karya ne tana so ne ta kashe aurenta taje ta cigaba da sheke ayarta kamar yadda ya saba yi a baya, shi ne aka hado baki da kanwar babarta aka zo aka ɗauke ta, sbd wanda suke yin abin da shi mai kuɗi ne ya sakar musu kudi shi yasa suka gigice a kan abin duniya”

Salati matan suka fara yi “Dama haka Amarya take ni duk a tunanina yarinyar mutunci ce ashe dai kura ce da fatar akuya, oh ni wannan xamani”

Da sauri innah salamatu ta dakatar da me maganar
“kada ki sake wannan tunani ke dai kawai a bar kaxa cikin gashinta amma idan aka figeta abin baxai yi kyau ba”

Mikewa tayi tare da cewa “yanzu menene abin yi?? xaku tashi mu tafi inda muka san za a fito mana da maxan mu ko kuma xaku xauna a nan ne ku jira har ya dawo?”

Tashi suka yi suna cewa “ina muka ga ta xama ai dole mu taso mu tafi idan ba malam ai ba gida”

Kai tsaye gidan su Sa’adatu suka nufa, tare da tafiya dakin innah, tarar da Kofar dakin suka yi a kulle, don har ta kwanta kasancewar bata ma son wainar da ake soyawa a gidan ba.

Cike da gadara innah salamatu ta fara buga kofar, “fito munafuka ki kwance kullin da kika yi”
Cikin bacci taji ana buga mata kofa a hankali ta fara buɗe ido tare da ambaton Allah, cikin nutsuwa tashi don xuwa ta buɗe musu kofar da kuma jin abinda ke tafe da su.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]