TSANANI CHAPTER 17

TSANANI

CHAPTER 17


Kwance nake bisa gadona ina jujjuya wayata, ba komai nake jira ba sai shigowar text ko wayar izuddeen yau da tunaninsa na tashi, ƙara kallon wayar nayi tare da sakin murmushi ina tuna yanayin da nake samun kaina a duk lokacin da naji muryarsa. +

A dai-dai lokacin ne Adda ta shigo dakina, ɗan dukan kafata tayi a hankali na waigo na kalleta tare da yin murmushi kaɗan.

“Sannu da shigowa Adda”
Ƙarasa mi’kewa nayi tare da xama kusa da ita.

“Yauwa Sa’adatu, da fatan kin tashi lafiya”

Amsa mata nayi da “lafiya lau”
Sake mayar da kallonta tayi gare ni.

“Yanxun nan Babanki ya kira Abban su ihsan, yace xai zo yanxu sai kiyi sauri ki shirya kada yazo ya jira ki”

A xabure na dubeta.
“Me kuma zai zo yace Adda?? Har ga Allah ban san zuwan Baba gidan nan, kin san dai ba….”

Dakatar da ni tayi
“Ki kwantar da hankalinki kuma ki kyautata xato, babu abinda xai faru insha Allah”

Haɗa kai nayi da gwiwa ina tunani, Allah yasa dai ba xuwa xai yi ya rusa maganar aurena da izuddeen ba.
Komawa nayi na kwanta tare da ajiye wayata a gefe guda, ringing ta hau yi ina dubawa naga number izuddeen din, Amma fargaba sai ta hana ni ɗagawa sbd ban san me xai faɗa min ba, sai da yayi min missed calls 5 ban ɗauka ba, haka ya hakura ya kyale ni.

Shigowar text din shi naji, a hankali na kai hannu na buɗe wayar.
*_A lokacin da kika yi nesa da ni, a wannan lokacin nake fahimtar yadda zafin soyayya yake, a wannan lokacin nake ƙara tabbatarwa da kaina, irin matsanancin son da nake yi miki. Kada ki guje ni masoyiyata, idan na rasa ki, babu shakka zan iya rasa rayuwata, ina sonki da fatan gimbiyata ta tashi lafiya, kixo ina kofar gida ina jiranki_*

Wata ajiyar zuciya na saki tare da lumshe idanuna, sake mayar da kallona nayi kan wayar ina ƙara karanta kalaman da ya rubuto min, izuddeen kwararre ne wajen iya magana da kulawa da zuciyar ‘ya mace wannan yasa a kullum nake ƙara narkewa cikin kaunarsa.

A hankali na tashi na sanya hijabina na fita.
Yau ma tsaye na tarar da shi jikin motar shi, hannun shi rike da mukullayen shi yana karkadawa.

Cike da nutsuwa na tako har na karaso wajensa.
sauke ajiyar zuciya yayi wacce take nuna tsantsar farin cikin sake ganina.

“My bride” ya faɗa tare da sauke kyawawan idanunsa a kaina.

Saurin kawar da kaina nayi, yau haka kawai na tsinci kaina a tsananin jin kunyar shi, gaba ɗaya ko amsa maganar shi na kasa yi ballantana na samu damar gaida shi.

Cigaba yayi da kallona yana murmushi.
“Yau kuma yan kunya ne a kanki Sa’adatu naga ko gaishe ni kin kasa yi”

A hankali na d’aga bakina nace.
“Ina wuni”
Ban yi tunanin yaji ba sbd yadda nayi maganar a sanyaye kuma muryata ƙasa ƙasa.

Lumshe kyawawan idanuwan shi yayi yana faɗin
“Tabarakallah”
Tare da sauke kyakkyawan murmushi a kan fuskata.

Duk da kasancewar Sa’adatu bata da kyau na a zo a gani amma tana da baiwar dauke hankalin namiji. Muryata ta Musamman ce mai kashe jiki, sannan tana da matuƙar kyan diri, da wannan baiwar tata take sace zuciyar maxaje da yawa.

Sake mayar da kaina ƙasa nayi ina wasa da yatsuna, haka kawai yau ban son wannan kallon nashi gaba ɗaya yake kashe min gabobin jikina.

“Da fatan kaxo lafiya” na faɗa tare da cigaba da abinda nake yi.

Amsa min yayi da “lafiya lau”
Gyara tsayuwa yayi “My bride sallama naxo mu yi”

Da sauri na d’ago tare da ware idanuna
“Sallama kuma, wace irin sallama?”
babu abinda ya fado xuciyata sai abinda Adda ta faɗa min daxu, game da xuwan Baba, ko dai tunanina ne ya tabbata.

Katse min tunani yayi da maganar shi.
“Ya naga kamar kin firgita amaryata”

Girgiza kaina nayi alamar ba komai.

Ɗan tamke fuska yayi yana gyara kwantaccen gashin fuskar sa.

“Zan je Lagos ne akwai wani aiki na gaggawa da zan yi, shi ne na xo faɗa miki amma baxan dade ba kwana uku kacal xan yi, kin san baxan iya yin nisa da ke ba”

Sauke ajiyar zuciya nayi, tare da kallonsa idanuna sun yi rau-rau kamar xasu kawo hawaye, xan yi masa magana sai kuma na kasa, sbd mayataccen kallon da yake bi na da shi wanda yake min barazanar faduwa, ya fahimci a tsarge nake amma ya kasa daina bi na da kallo.

Cikin sanyin Murya ya dube ni.

“Menene ya bata miki rai my wife, har yake kokarin saka min ke kuka?”

A shagwabe nace
“Baka faɗa min xaka yi tafiya ba sai yanzu”

Kwantar da murya yayi, cikin wani salo yace.
“Nafi so sai naxo na faɗa miki, sbd ko ranki ya ɓaci na rarrashe ki, kin san ni nafi can-canta na rarrashi matata a kan kowa, ko kaɗan ban san ganin damuwa a saman fuskarki, kiyi hakuri baxan dade ba xan dawo gare ki, amma idan baki amince da tafiyar ba sai na hakura na dawo mu xauna tare”

A hankali na d’ago
“Na amince Allah ya dawo da kai lafiya”

Amsa min yayi da “Ameen”
Buɗe mota yayi ya dakko leda ya miko min.
“Ga wannan naki ne amma kada ki bude sai kin je gida”

Karba nayi tare da godiya har sai da yaga shiga ta gida Sannan yaja motar shi ya tafi.

Komawa ta gida kenan ko kayan da aka bani ban buɗe ba, naji sallamar Baba, jikina na rawa na shiga dakin Adda na fada mata yaxo.

Tabarma na bawa ihsan taje ta shimfida masa tare da faɗa masa cewa ina xuwa.

Fargaba ce ta cika xuciyata sbd ban san abinda ya kawo shi ba, alkhairi ne ko akasin haka?.

Sai da na gabatar da addu’o’ina sannan na fita zuwa gare shi.

Mamakin yadda ya canja min lokaci ɗaya nake yi, kamar ba shi ne baban da yaƙi jinana ba a da, ya kore ni daga gidan sa, ya yanke duk wata alaƙa ta ɗa da mahaifi tsakanina da shi.

Sannu da xuwa nake masa cikin sakin fuska yace
“Yauwa Sa’adatu yar albarka sannunki, ya gida ya Addar taki?”

Kaina a sunkuye na amsa.
“Da suna lafiya Baba ya innah da yan uwana”

“Duk suna lafiya Sa’adatu”

Gyara xama yayi tare da gyaran murya.
“Abinda yasa na kira ki, kuma na tako da kaina wajen ki, naxo ne na tambaye ki game da yaron da ya zo gurina a kan maganar aurenki, na san kin san da maganar shi kuma ya faɗa min yana xuwa hira ko?”

A hankali na girgixa kai alamar “eh”

Cigaba yayi da magana “Alhamdulillah haka nake son ji, iyayensa sun xo sun yi min magana a kan xasu kawo kayan auren ki, shi ne naxo na tambaye ki idan kin amince bana so naxo nayi abinda xai kawo miki matsala a rayuwar ki, amma ni a ɓangarena na amince ki aure shi sbd yaron mutumin kirki ne kuma iyayensa mutane ne na gari”

Shiru nayi ban iya bashi amsa ba, sai dai ya lura da ina son izuddeen.
Cigaba yayi da magana.
“Na fahimci komai Sa’adatu tashi kije xan ce kin amince Allah ya sanya alkhairi Allah ya bada xaman lafiya”Kaina a ƙasa har na shige cikin gida sbd kunyar shi da nake ji. +

Dakin Adda na shiga na bata labarin yadda muka yi, ita kanta tayi mamakin yadda ya canja dare ɗaya kayan da aka bani na nuna mata, fito da shi ta shiga yi, kayan kwalliya ne kala-kala da kayan saka, ba ƙaramin kuɗi izuddeen ya kashe min ba. Godiya tayi masa tare da ajiye kayan a wajenta.Cikin rawar baki ta fara magana
“Malam naxo ne naga ana ƙoƙarin yi maka sakiyar da ba ruwa” +

Cike da mamaki ya dubeta.
“Kamar yaya kenan Hajiya salamatu?”

Gyara xama tayi
“Gobe idan Allah ya kaimu za a kawo kayan auren Sa’adatu ita da wannan yaron da ta sanadinsa ta kashe aurenta”

A zabure ya dubeta
“Ina me wannan ɗanyen aikin zai faru? wato duk abinda nayi don na hana abin nan sai da ya warware, ni da kaina fa nayi alƙawarin baxan taɓa bari Sa’adatu tayi aure ba matuƙar ina raye, amma yanxu ma ban makara ba dole akwai abinda zan yi wannan maganar ta lalace”

Wani daɗi ne ya sauka a zuciyar Innah Salamatu, cike da farin ciki ta fara magana
“Naji dadin wannan matakin da ka ɗauka malam kada ka d’aga ƙafa, abu na ƙarshe da nake so kayi idan ka raba auren ka lalata shi, ina so ka mayar da shi kan wannan diyar tawa”

A hankali ya dubeta tare da sauke kallon shi a fuskar A’isha wacce take xaune kusa da Innah.

Wani kallo ya bi ta da shi yana jin wani abu na yawo a zuciyar shi, cikin ranshi yake faɗin
“Dama malam Salisu yana da wasu yan matan amma ya kyale ni a haka bayan Sa’adatu ta rabu da ni”
Lumshe ido yayi tare da kallon Innah Salamatu
“Dama wannan yar ki ce, ina ganinta amma ban taɓa zaton ita ma taki bace”

Murmushi tayi tare da cewa ” ‘yata ce Malam a taimaka a juyar da auren kanta”
Mayar da ajiyar zuciya yayi
“Indai wannan ne ba wata matsala bace xan yi iya bakin kokarina”

Cikin farin ciki suka hau yi masa godiya, wani turare ya dakko ya basu yace indai A’isha tayi amfani da shi saurayin Sa’adatu yaji kanshi magana ta ƙare aure ya gama komawa kanta.
Da farin ciki suka karbi turaren suka fita.

Fitar su ke da wuya ya bushe da wata irin dariya, shi kaɗai ya san irin muguntar da ya shirya musu, matuƙar A’isha ta kuskure tayi amfani da wannan turaren da ya bata da kanta zata kawo kanta wajensa ya aureta.

Tafe suke suna yaba irin mutuncin Malam Jibo, Allah Allah suka riƙa yi su koma gida su fara aiki da turaren don maganar auren Sa’adatu ta lalace.

***********

Shirye-shirye sun yi nisa a gidan su izuddeen, kowa sai murna yake yi gami da farin cikin ganin auren izuddeen, kowa ya ci burin baje farin cikinsa a duk lokacin da ranar ta zo.

Wayar mama ce tayi ƙara a hankali ta kai hannu ta dauka sunan shi ta gani rubuce a kan screen din.
Murmushi tayi tare da faɗin
“Ango kenan baka gajiya da kiran waya”
Cikin kulawa ta fara magana
” ‘Dana na kaina ya aiki?”

A hankali ya amsa
“Lafia lau mama ya shirye-shirye”

Murmushi tayi
“Ai kai xa a tambaya shirye-shirye”

Siririyar dariya ya saki tare da cewa
“Komai dai ya kammala ko Mama babu wani abu da ake bukata?”

Girgiza kai tayi
“Eh babu abinda ake buƙata, kaya sun yi sai fatan Allah ya sanya alkhairi”

A hankali ya amsa da “Ameen”

Hararar shi mama tayi kamar tana ganinsa.
“Kai me yasa yanzu ba kada kunya ne izuddeen, shi ne har da cewa ameen ko?”

Sosa keya yayi tare da sakin murmushi
“Yi hakuri mama tuba nake”Ita murmushin tayi
“To shikenan ba komai, yanxu yaushe xaka dawo?”

Ɗan dage gira yayi
“Idan aiki yayi sau’ki gobe ma xan iya tahowa”

“To shikenan Allah ya dawo da kai lafiya”

Amsawa yayi da Ameen ta kashe wayar.

*********

Innah ce ta shirya ta nufi gidan su Rukayya, a tsakar gida ta tarar da umma na shara, da fara’a ta karɓeta tare da yi mata sannu da xuwa.

Ajiye tsintsiyar tayi suka shiga d’aki bayan sun gaisa ta faɗa mata cewa gobe za a kawo kayan Sa’adatu, shi yasa taxo ta shawarce ta me ya kamata a yi musu.

Gyara xama tayi
“A ganina idan akwai wadataccen kuɗi a wajen ki a siyo kaji a soya musu, a siyo musu lemo da ruwa, zan bayar kanwata tayi musu kayan snakes sai a haɗa musu gaba ɗaya”

Mayar da ajiyar zuciya innah tayi, yanzu dai babu kuɗi a hannuna sbd na kashe na yiwa Sa’adatu siyayya, yanxu abinda nake da shi bai wuce dubu biyar ba, amma xan tambayi saratu ko akwai a wajenta sai ta ara min”

Dafata umma tayi.
“A’a ba ma sai kin tambayeta ba akwai kuɗi a hannuna sai na baki rance duk lokacin da kika samu sai ki bayar”

Ba ƙaramin daɗi taji ba, godiya mai yawa tayi mata, gidan su Rukayya sun xamewa su Sa’adatu da innarta tamkar yan uwa, domin duk abinda suka rasa matuƙar suka nemi taimakon su ko shawara, basa taɓa juyar da buƙatar su.

A lokacin umma take faɗa mata abin arxikin da Sa’adatu tayi masu na haɗa doctor da Rukayya, da yadda magana tayi nisa har ana ƙoƙarin kawo kuɗi, Innah taji daɗin abinda diyar ta tayi albarka ta shiga saka musu tare da fatan alkhairi.

Sun dade suna tattaunawa sannan ta tafi gida sbd kiran da aka aiko ana yi mata.Washe gari gidan su Sa’adatu ya cika makil da yan uwa da abokan arziki musamman dangin mahaifinta na Bankaura don karɓar kayan aurenta, innah na dakinta ita da Adda saratu sun kammala haɗa komai sbd maxa ne xasu karbi kayan ba mata ba don haka basu fito ba, Innah Salamatu da ahalinta na daki sun kasa kunne su ji yadda xata kaya, babu wanda ya iya fitowa tsakar gida sbd baƙin ciki. misalin sha daya na safe suka iso da akwatinansu, tun daga isowar su kake jin ana sa albarka tare da fatan alkhairi, akwati dozen biyu izuddeen yayi guda ashirin da huɗu kenan, kowacce cike take da kayan arziki har da sarkar gwal, sannan suka dora dubu dari kuɗin dinki, ga buhunan shinkafa da kayan tea da duk wani abu da zasu buƙata idan xasu yi girkin biki.

Mutanen ƙauyen Bankaura gaba ɗaya sun gigice tunda suke basu taɓa ganin kayan lefe irin wannan ba.

Cikin gigicewa mahaifin Sa’adatu ya dubi wakilan izuddeen.
“Duk wadannan akwatunan na Sa’adatu ne?? Ai kayan sun yi yawa haka”

Murmushi yayan shi yayi.
“Ai Sa’adatu ta cancanci fiye da wannan malam duk nata ne fatan mu Allah ya sanya alkhairi”

Gaba daya wajen aka amsa da ameen, an yanke lokacin biki nan da sati biyu masu xuwa sai da aka yi addu’a sannan malam Salisu ya miko musu tukwicin naira dubu hamsin, basu karba ba sbd iyayen izuddeen sun hana a karbi tukwici tunda sun san iyayenta ba masu ƙarfi bane, amma sun karbi kayan snacks din da aka basu da lemo katan goma da ruwa katan biyar, ba laifi innah tayi kokari sosai ta fidda yarta kunya kasancewar innah mace ce mai zuciya.

Fitar su ke da wuya aka fara shiga da akwatunan cikin gidan, ana fara shiga da su Innah Salamatu da ƴaƴanta suka fito don ganin me aka kawo wa Sa’adatu, a tsakar gida aka shimfida tabarma aka ajiye su.

Gani suka yi ana ta shigo da kaya sun ki karewa, sai da aka gama shigo dasu gaba ɗaya sannan suka hau budewa a yatsine, kallo daya xaka yi musu ka san suna cikin takaici da baƙin ciki, idanunsu sun yi ja kamar xasu fashe da kuka, duk akwatin da suka bude sai su ganta cike da kaya babu wani nakasu a cikinta.

Tsabar baƙin ciki basu iya gama ganin kayan ba suka tashi, cikin rawar baki Innah Salamatu ta dubi Baba.
“Burinka na son ka siyar da yar nan dai ya cika”

Cike da mamaki ya dubeta
“Kamar yaya na siyar da yata”

Gyara tsayuwa tayi tana watsa masa wani kallo.
“Gashi nan ka bada ita ga ɗan yankan kai sbd yazo ya toshe maka baki da kudi, duk garin nan wane ne bai san abinda yaron nan yake yi ba, amma sbd abin naka son xuciya ne ka kasa ganewa”

Dakatar da ita yayi da hannunsa
“Kin ga ya ishe ki haka, bana son bakin ciki na san abinda ke damunki kenan da yarki aka kawo wa wadannan kayan ai baxa ki fadi haka ba, amma da yake yar wata ce kinxo kina Maganar banxa, indai baxa ki daina baƙin ciki ba baxa ki daina ganin ba dai-dai ba a rayuwar ki da ta yayanki, duk ba sharrinki ne yake bibiyar su ba ya hana su cigaba, gasu nan a xaune duk samarin nasu sun gudu”

Dafe kirji tayi tana bin sa da kallo
“Ni kake faɗawa haka malam sbd ka samu siriki mai kuɗi shi ne xaka wulakanta ni har kana kirana yar bakin ciki, to Allah ya isa tsakanina da kai idan kaxafi kayi min, menene abin baƙin ciki don xata auri ɗan yankan kai”
Ta karasa maganar tana kuka.

Shigewa daki tayi ƴaƴanta suka bi bayanta suna guna guni.

Shi kuwa Baba ko a jikinsa don yanxu ba ta tata yake yi ba, gaba ɗaya ta fara fita daga kansa daga ita har ƴaƴanta sbd hassadar da take nunawa a sarari.

Taimkawa su Innah yayi suka shigar da kayan cikin daki, godiya Innah take ta yiwa Allah, tunda take bata taɓa tunanin Sa’adatu xata samu irin wannan ba har sai da tayi kukan farin ciki.

Makota ne suka riƙa shigowa suna kallon kaya suna yaba irin kokarin da izuddeen da irin yadda Allah yayi mata sakayya lokaci guda, albarka suka shiga sakawa auren.

Su innah salamatu na komawa daki suka turo kyaure suka fara kukan baƙin ciki don shi ne kaɗai abinda zai saukaka musu damuwar su.

Zaliha ce ta dubeta
“Yanxu Innah irin rayuwar da zamu cigaba da yi kenan, muna ganin cigaba ya fi ƙarfi arfin mu ke kuma kin kasa yi mana wani ƙoƙari, da xamu fita daga wannan damuwar, ni babu tsayayyen saurayi A’isha ma haka, sannan kin kasa kwace mana na waccen shashashar” +

A fusace ta dube ta
“Duk ƙoƙarin da nake yi muku baku gani ba, kin san irin fadi tashin da nake yi don ganin yaron nan ya dawo hannun ku amma duk baku gode min ba”

Cike da tausayawa A’isha ta dubeta
“Muna gani Innah mun san kina yi mana kokari, ita dai zaliha ce bata gani, tunda gashi jiya har wajen malam Jibo muka je ya bani turare kuma har na fara amfani da shi, so nake kawai Allah ya haɗa ni da saurayin nata mu yi ido biyu na san daga ranar ya bar hannunta”

Wani tsalla zaliha tayi ta rungume A’isha.
“Yauwa Alhamdulillah abu yayi kyau Allah ya taimaka”

Amsawa suka yi da “Ameen”

A nan take Innah Salamatu tasa zaliha ta kira saurayinta ta faɗa masa cewa tana so ya fito a sati biyu, kuma tana so yayi irin akwatin da izuddeen yayi, ko ta haya ce ya karbo xata bashi wani kuɗin ya rage.

Shi dai to kawai yace mata, basu gama faɗin abinda xasu faɗa ba ya kashe wayarsa.

Tsaki tayi tare da xaginsa, sannan ta dubi ya’yan nata.

“Ni fa a ganina matar nan bayan maganin bakin jini da tayi muku sai da ta raba ku da samarinku”

Cike da damuwa suka dubeta tare da cewa
“Me kika gani Innah”

Rausayar da kai tayi
“Ku duba fa ku gani ina yi wa na zaliha magana amma to kawai yace ban gama ba ya kashe min wayar, ke kuma ma gaba ɗaya ba labari”

Girgiza kai suka yi gaba ɗaya
“Ba komai innah ko bai yi dan Allah ba xamu haɗa shi da malam jibo yasa yayi dole”

Hirar da suka riƙa yi kenan su tufka wannan su kwance, a ranar wuni suka yi a daki sun kasa fitowa tsakar gida sbd baƙin ciki.

About Ismail

Check Also

TSANANI CHAPTER 16

TSANANI CHAPTER 16 Cikin Wata irin rikicewa da d’imaucewa tare da rawar baki nake faɗin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *