[Advertisements⬇️]

TSANANI CHAPTER 13 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TSANANI


CHAPTER 13
Karaf naji a kunnena Innah na bawa Adda labarin zuwan doctor wajenta wai yana neman aurena, ba ƙaramin dukan zuciyata maganar tayi ba, zuciyata ce ta fara tafasa naji kamar na fashe da kuka, mamaki ne ya kamani ko ya aka yi ma ya gano gidanmu har ya samu ganin Innah, tambayar kaina na shiga yi, anya Baba ya san abinda ya kawo doctor gidanmu kuwa? Na san ko ya faɗa masa ma baxai amince da aurenmu ba, tunda abubuwa marasa dad’i sun faru tsakaninsu. tsayar da abinda nake nayi na cigaba da sauraren abinda suke fada, shawarar Adda saratu ta nema a kan ta bashi izni yaxo wajena ko kuma a dakatar da shi zuwa wani lokaci? Wani radadi da zafi zuciyata ta hau yi min, a gaskiya yanxu babu niyya ko shirin aure a tare da ni, hasalima ni tsoron maxan nake ji gani nake yi kamar irin halinsu daya da malam Jibo, yaushe har na fito daga tarkon malam jibo da har za a sake kokarin tura ni a wani, a yanxu dai bana burin auren kowane namiji idan ba izuddeen ba, na san shi kaɗai xai iya rike ni amana ba tare da ya cutar da ni ba, ji nayi hawaye na ƙoƙarin fito min, a hankali nasa gefan mayafina na share, har cikin zuciyata ban jin don doctor ballantana har na aure shi, sbd babu wanda na yiwa tanadin soyayyata sama da izuddeen, da wannan tunanin nawa naji innah ta sake cewa, zata sa yaxo wajen mijin Addata su tattauna yadda abin namu xai kasance, amma a yadda na lura ita innar tawa taji dadin xuwansa kuma tana so mu kasance tare, don a maganarta na gane tana cikin farin ciki sosai
Tambayarta Adda saratu tayi ko yaya aka yi ya gano gidanmu, sai da ta mayar da ajiyar zuciya sannan ta karanta mata yadda aka yi ya san inda nake, faɗa mata tayi cewa. +

Tare suka yi karatu da makocin mu Dr mukhtar, don haka yaxo wajensa don ya kawo masa ziyara, sai yaga mahaifina zaune a kofar gida, shi ne yake tambayarsa dama makocinsa ne, nan yake bashi labarin babana da irin halinsa, don shi kansa a lokuta da dama yana taimaka mana da abinci da kudi don ya san irin rayuwar da muke yi ni da innata, doctor bai yi mamakin jin halin mahaifina ba sbd shi ma ya gwada masa irin halin nasa ya gani, a nan yake faɗa masa cewa yana sona da aure, amma bai san inda xai ganni ba kuma baya tunanin cewa Babana xai bari alaƙarmu ta kullu ballantana har ya aure ni, karfafa masa gwiwa yayi a kan ya aure ni, sbd kyawun halin da muke da shi ni da innata, ya kuma labarta masa wuyar da muka sha a hannunsa Baba da innah salamatu, washe gari da ya dawo shi ne ya raka shi wajen kanin mahaifina baban su salim yayi masa bayanin abinda ke tafe da shi, yayi farin ciki sosai da jin xancen kuma shi ne yake labartawa innah ya kuma gargadeta da taja bakinta tayi shiru kada ta ɗaga Maganar kowa yaji, shi ne yau taxo wajen Adda saratu take bata labarin abinda ya faru.

Jikina a sanyaye na fito ina jan ƙafa duk jijiyoyin jikina sun yi sanyi, yadda naji Innah ta karbi xancen ne ya daga min hankali sbd bana so hakan ya zama sanadiyyar rabuwata da izuddeen, wannan yar maganar ba ƙaramin tada min hankalina tayi ba, sbd bana son abinda xai katse min karatuna duk da dai na san cewa doctor mahmud mutum ne mai fahimta kuma ya san halin da nake ciki, baxai katse min ilimina ba

Kama hanyar shiga daki nayi, Adda ce ta kwala min kira a hankali na waiwayo ta lura da yanayina sosai kamar ina cikin damuwa, jikinta ne ya bata cewa naji dukkan abinda suke tattaunawa shi yasa yanayina ya canja, zuba min ido tayi tana girgixa kai tare da cewa ba ki da lafiya ne Sa’adatu naga yanayinki ya canja.

Girgiza mata kai nayi almar eh ban koma wajensu ba, na shiga daki na faɗa kan madaidaiciyar katifata na kifa kaina Ina tunani.

Tabbas halin da na samu kaina a ciki yanzu babbar ni’ima ce, domin a da irin wannan baiwar muke nema amma Allah bai bamu ba, sanadin hakan ne yasa har aka aura min malam jibo, godiya nayi ga Allah da ya fara share min hawayena ya azurtani da wanda yace yana sona, tambayar xuciyata nayi me yasa xan shiga damuwa don Allah ya haɗa ni da miji irin doctor mahmud na san matukar na same shi na gama dacewa, duk dukkan abinda nake tunanin samu a wajen izuddeen xan same shi a wajen doctor, to me yasa xan damu kaina da tunani? Babban abinda ya fi a gare ni shi ne nayi addu’a na nemi zabin Allah, tashi nayi xan fita na dauro alwala sai kuma na yi tunanin ashe ba ni da tsarki, don haka na koma na kwanta kan katifata ina cigaba da tunani ban san lokacin da bacci yayi awon gaba da ni ba, ko tafiyar innah ban sani ba sai da na tashi aka fada min ta tafi gida. +

Ko da na tashi Adda bata yi min xancen ba nayi tunanin sai ta fara faɗawa mijinta, abinda suka yanke na shawara sannan sai ta fada min.

Yau na samu kusan sati biyu ina xuwa makaranta kullum cigaba ake samu a harkar karatuna, ku san xan iya cewa duk ajinmu babu daliba kamata, wannan dalilin yasa sunana ya fara zagaye sassan makarantar babu wanda bai san Sa’adatu Salisu ba, don wannan karon musabakar da makarantar zata je ina cikin daliban da xasu wakilceta. 1

Kamar kullum yau ma kawata khadeejah ce ta biyo min makaranta, ciwon kai mai tsanani da nake fama da shi ne ya hana ni zuwa nayi ƙoƙarin na daure naje amma hakan baxai yiwu ba, don haka Adda ta bata sako ta fadawa mu’allim kafin mijinta yaje ya fadi uzurina.

Na ɗauki tsawon kwanaki uku ko tsakar gida bana fitowa, sai a kwana na hudu na samu na ɗan fito, sallamar Rukayya naji da sauri muka rungume juna muna murna, dakin Adda ta shiga ta gaisheta sannan muka shiga dakina

Tare muka xauna na dakko mata ruwa, tayi min ya jiki sannan na koma gefe na haɗa kai da gwiwa, dafa kafadata tayi wai har yanzu jikin ne Sa’adatu.

Girgiza kai nayi ba iya ciwon kai nake fama da shi ba har da ciwon zuciya, a firgice ta dubeni, me ye Haka Sa’adatu, wannan wane irin abu ne xaki sa kanki a matsala.
Tsare ni tayi tana tambayata a kan abinda ke damuna.
Nan na kwashe labarin doctor na bata.
Murmushi tayi wlh kin bani kunya kawata sbd wannan xaki sa kanki a damuwa to albishinki.

Bude baki nayi nace mata goro, abinda ya kawo ni gidan nan kenan na fada miki cewa izuddeen ya kusa dawowa jiya abokinsa yake bani labari, kuma ko da suka yi waya ya fada masa kina ina kinga kuwa kina xuciyarsa bai manta da ke ba

Wani farin ciki ne ya lullube xuciyata naji kamar an yi min kyautar hajji da umara ban san lokacin da na rungume Rukayya ba ina kukan farin ciki idan akwai abinda nafi bukata a rayuwata bai wuce izuddeen ba, na san shi ne waraka daga dukkan matsaloli na…

Ganin yadda nake farin ciki ne yasa Adda ta tambaye ni, Sa’adatu lafiya tun daxu kike murmushi kamar wacce aka yiwa kyauta da aljanna. Labarin abinda Rukayya ta faɗa min na bata amma ga mamakina sai naga ta tabe baki ta tafi ta barni ba tare da tace komai ba.

Jikina ne yayi sanyi xuciyata ta kasa bani amsar abinda take nufi.Samun guri nayi na xauna a tsakar gida ita kuma ta wuce dakinta, kallon mamaki kawai take yi min wanda ni kaina ban san fassararsa ba, nayi jira sosai ko xata dawo na sake tambayarta dalilin rashin saurarar abinda na faɗa mata, amma bata dawo har na gaji na tashi, shiga dakinta nayi tarar da ita nayi tana ninke kayan su husna, karba na fara taya ta, ina mata aikin ina ɗan jefo mata maganar izuddeen ko Allah xai sa ta tanka min, amma sai naga ta share ni ba tare da ta bani amsa ba, da naga bata son zancen sai kawai na kyaleta na shiga harkokina, ina gamawa na koma dakina na kwanta.

Shigata ke da wuya naji sallamar yaro a tsakar gida, wai yana nemana da sauri na fito don jin abinda ke tafe da shi, takarda ya miƙo min rufe take da envelope da dukkan alamu wasika ce aka aiko shi ya kawo, mamaki ne ya kama ni, cikin nutsuwa na tambaye shi ko wanene ya aiko shi? Cike da ladabi ya bani amsa da cewa wani mutum ne shi ma bai gane ko wanene ba, umartar yaron nayi da ya biyo ni naje naga ko wanene, dakin Adda na fara shiga na fada mata abinda yaron ya faɗa min, hijabinta na sanya muka fita tare amma abin mamaki bamu samu wanda ya aiko shi ba har ya tafi, don haka na kyale shi ya tafi ba tare da na cigaba da tambayarsa ba, sbd ko wanene xan gane shi ta hanyar wasikar da ya aiko da ita.

A sanyaye na shiga dakin Adda, tsaye na tarar da ita hannunta rike da takarda bata buda ba tana jiran dawowata, tambayata tayi ko naga wanda ya bani sakon, a hankali nace banga kowa ba.

Miko min tayi, “karbi ki bude Sa’adatu” girgiza kai nayi “a’a ki bude ki gani Adda” hannu tasa ta fara buɗe wasikar, ga mamakin mu sai muka ga rubutun ajami ne da shi aka rubuta wasikar, miko min tayi tare da cewa, “karbi Sa’adatu kece yar makarantar allo ke xaki iya karantawa
Karba nayi na fara budewa.
Ina ganin yanayin yadda aka rubuta wasikar da irin takardar da aka yi rubutun da ita na san sakon malam Jibo ne, jikina a sanyaye na fara karantawa.

_sallama gare ki hasken idaniyata, wacce ta guje ni a lokacin da nake da bukatar kulawarta_
_gaisuwa mai yawa da fatan alkhairi a gare ki amaryata mai share min hawayena Sa’adatu, da fatan kina cikin koshin lafiya,na rubuto miki wannan wasikar ne domin na kara jaddada miki soyayyata da kaunata a gareki,ki sani duk inda kika shiga a fadin duniya kina cikin raina har abada baxan taɓa mantawa da ke ba. Ina dada tunasar da ke cewa kiyi gaggawa ki amince da komowa gidana idan ba haka ba kuma xaki dawo ba tsiya ba arxiki ,don nayi alwashin muddin ina doran kasa babu wani da namiji da ya isa yayi tarayya da ke idan ba ni ba, ina fatan baza kiyi taurin kai wajen bin umarnin mijinki ba,sannan xaki sanar da masu hure miki kunne dangane da kudurina a gare ki_

_Ki huta lafiya daga mijinki mai kishinki mai kaunarki Sheikh Jibo_ 1

Ina gama karanta wasikar na kalli Adda, kallon kallo muka riƙa yi da ita, gaba ɗaya mun kasa magana, kallona tayi kamar xata xubar da hawaye

“Ina so ki tattara nutsuwar ki Sa’adatu kiyi watsi da dukkan abinda yake faɗa a kanki, ki sani babu wanda ya isa ya amfanar da ke ko ya cutar da ke sai da iznin Allah, don haka ki ɗauki wannan maganar tasa a matsayin tatsuniya, ke dai ki kama Allah kuma ki dage da addu’a babu abinda xai miki da yardar Allah”Ban iya cewa komai ba sai girgixa mata kai kawai da nayi, tashi nayi na faɗa dakina na fara kuka, tabbas na yarda da maganganun Adda, amma ina kara jin takaicin abinda ya faɗa min, idan da wanda ya jefa ni a wannan halin bai wuce Mahaifina ba, da bai hadani da malam Jibo ba da baxai yi tunanin yi min wani sharri ba, na san bai isa ya cutar da ni ba sai abinda Allah ya rubuta min amma duk da haka ina jin ciwon abinda yake furtawa zai aikata a kaina don na dade da sanin ba imani gare shi ba, tashi nayi na fara addu’a ina kai kukana wajen Allah tare da neman tsari ga sharrin da ake shirin kunno min.

A ranar cikin baƙin ciki na kwana ban yi cikakken bacci ba sbd damuwa, yau ma da wuri na tashi na shirya don tafiya makaranta, kamar kullum sai da na gama aikin gida na tabbatar Adda baxa ta bukaci komai ba idan ta tashi daga bacci sannan na tafi, ina fitowa kofar gida naci karo da kawata khadeejah. tare muka rankaya makaranta, muna tafe tana min hira sbd damuwar da nake ciki bana samun damar amsa mata, har sai da ta fahimci akwai abinda ke damuna, tambayata ta shiga yi tana min naci na faɗa mata damuwata amma sam naki amincewa na buda mata cikina, haka dai ta gaji ta kyale ni

Ku san yau mun riga kowa zuwa aji har shi kanshi malamin, don haka muka fara muraja’ar karatun mu, rufe fuskata nayi da Alkur’ani ina ta faman kuka yau ko kadan ban ji xan iya karatu, sbd tunani da damuwar da suka cika xuciyata ina a nan halin mu’allim yaxo, ba tare da bata lokaci ba ya fara yi mana kari, shi kansa ya lura da yanayina ba irin yadda ya saba ganina bane.

Sai da aka kammala karatu yake min ya jiki sbd fashin kwanki uku da nayi ban zo makaranta ba, a hankali na amsa da na warke, shi kansa bai iya jin me nace ba sbd kukan da ya ci karfina ya hana ni bude baki nayi magana, har aka gama ƙarin sauran littafai ban dago ba idona rufe yake da littafi ina ta faman kukan da na kasa tsayar da shi, kiran sunana yayi tare da cewa na buɗe fuskata duk a tunaninsa ko surutu nake yi

Muna hada ido da shi yaga idanuna sun yi jawur fuskata har ta kumbura sbd kuka, a razane ya dube ni.

“Lafiya me ya same ki Sa’adatu, ko wani abin ku ka yi mata kafin naxo” yana Maganar yana kallon yan ajin
Da sauri suka bashi amsa “wlh bamu sani ba mu’allim tunda tazo da safe take kuka”

Mayar da kallon shi yayi ga khadeejah wacce take a gefena, ita ma tambayarta yayi ko ta san abinda ya same ni, ita ma irin amsar da yan aji suka bashi ta faɗa masa.

Cike da tausayawa ya dubeni tare da cewa na biyo bayansa, cikin nutsuwa na tashi na bi shi.

office din malamai muka shiga, kujera ya samu ya xauna sannan ya umarce ni da na xauna a ta kusa da shi.

Cike da girmamawa na xauna, tsura min manyan idanunsa yayi yana naxarina sannan ya bude baki a hankali yace

“Fada min abinda yake damunki Sa’adatu tunda kike ban taɓa ganin ki a irin wannan yanayin ba, ki fada min ko me ke damunki nayi alkawarin xan taimaka miki matukar ina da iko a kan haka”

A hankali na dago idona bude baki nayi xan yi magana kuka mai tsanani ya kama ni, maganar gaba daya ta makale na kasa fitar da ita, rarrashina ya shiga yi da kalamai masu sanyaya xuciya.

Lallabani yayi sosai har sai da hankalina ya kwanta na fara dawowa cikin nutsuwata, labarin aurena da malam Jibo na fara bashi da kuma wasikar da ya rubuto min yau da abinda aka rubuta a jikin wasikar.

Cike da mamaki yake kallona tare da tambayata “dama kin taɓa aure Sa’adatu?”

A sanyaye na daga masa kai alamar eh.
Cike da tausayawa ya Girgiza kai.

Cigaba yayi da tambayata dalilin da yasa malam Jibo ya sake ni da abinda yasa yake min haka, ban rufe masa komai ba na bashi labarin dukkan abinda ya faru tsakanin mu, ba ƙaramin tausaya min yayi ba, sannan ya bani addu’o’i yace na dage da karanta LAHAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH indai ina yinta ko asiri ko wani abu bai isa yayi tasiri a kaina ba, ko da kuwa da aljanu aka haɗa ni, sbd LAHAULA taska ce daga taskokin gidan aljanna, kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya faɗa mana, ya kara min da addu’o’i masu yawa yace na dage da yinsu.

Nasihohin da yayi min sai suka zama tamkar waraka a gare ni na daina jin tsoron komai na miki al’amurana ga Allah Cikin nutsuwa na tashi ina tafiya a hankali kamar wacce kwai ya fashe wa a ciki, kallo daya xaka yi min ka san ina Cikin matsananciyar damuwa, don ma nasihohin mu’allim sun fara tasiri a gare ni ne shi yasa na dakata da kukan da nake yi, bi na yayi da kallo mai cike tausaya wa, ina kaiwa bakin kofa naji ya saki wata ajiyar zuciya, tare da kiran sunana, waiwaya nayi muna haɗa ido na sunkuyar da kaina, bai iya ce min komai ba sai nuni da yayi da hannunshi alamar na tafi, kifa kanshi yayi a kan table din har nayi nisa bai dago ba, ko tunanin me yake yi ban sani ba, amma dai yadda na lura maganata ce ta girgiza shi Musamman da nace na taɓa aure. +

Ina shiga aji aka bi ni da kallo, da yawan mutanen da ke ajin na son tambayata abinda muka tattauna da shi amma babu dama, kasancewar bani da sakin fuskar da xasu samu damar tambayata. Mu’allim bai samu dawo wa ajin ba har aka tashi sai wani malamin ne yaxo yayi mana addu’a.

mamakin ne ya kama ni tare da tambayar kaina ko menene dalilin da ya hana shi dawowa? Rashin samun amsar ne ya dagula min lissafina nima sai na tsinci kaina a cikin damuwa mai yawa, yanxu ma haka muka dawo tare da khadeejah taso ta bugi cikina taji abinda muka yi da mu’allim amma ban saurareta ba, hirar ma jefi-jefi nake sanya bakina a ciki.

Ko da na dawo Adda saratu ta gama komai, don haka dakina na wuce na tube kayana na shiga wanka ko xan ci sassauci a xuciyata.
★★★★★★★

A ɓangaren mu’allim kuwa tunda Sa’adatu ta bar office dinsa ya faɗa dogon tunani tausayi da soyyyarta ne suka mamaye masa zuciya, mamaki ne ya cika ransa yanzu a ce yarinya kamar wannan ita ce ta haɗu da kalubale kala-kala a rayuwarta, yana ji a ransa xai iya sadaukar da rayuwarsa kawai don ya faranta mata, ji yayi kaunarta ta kama shi, da xata amince ta bashi zuciyar ta da sai ya aureta, duk da cewa ta taɓa aure shi kuma yana saurayi, amma a hakan zai iya rayuwa da ita, tsanar malam Jibo ce ta kama shi, ji yake kamar ya same shi ya hau shi da duka, sbd irin wulakancin da ya yiwa Sa’adatu, addu’a ya riƙa yi a ransa Allah yasa dai bai mayar masa da mata bazawara ba, da wannan tunanin ya tashi xai tafi gida.

Bai iya yin sallama da kowa ba a salube ya tafi gida yana ta tunanin rayuwar Sa’adatu, ko da ya koma gidan bai kula kowa ba ya faɗa dakinsa, kwantawa yayi rigingine ya cigaba da aikin tunani, wanda a yanzu yake son xama cinikinsa.

Sai lokacin sallar magariba ya fito ya nufi masallaci yayi sallah sannan ya sake komawa gida yayi wanka ya shirya cikin wata brown shadda, wacce aka yi wa aiki da brown din xare, hular da ke kansa ma brown ce haka ma takalmin da ya sanya, kasancewar mu’allim mutum ne ɗan gayu mai tsafta ga kamun kai, wannan dalilin yasa yan mata da yawa ke kawo tallan kansu wajensa amma bai taɓa saurarsu ba sbd shi mutum ne mai tsari da tsaurin akida, a kofar gida ya tsaya yana nazari shib yaje wajen Sa’adatu ya faɗa mata abinda ke ransa ko kuwa kawai ya kyaleta, sbd baya so yayi mata katsalandan cikin al’amarin rayuwar ta, duk a yau ta bashi kwatancen gidan su sbd yace xai zo ya bata wasu addu’o’i.Ya dauki ku san rabin hour yna wannan nazarin kafin daga bisani ya yanke shawarar zuwa wajenta. +

Wuta ya bawa machine dinsa ya saita kansa ya nufi hanyar gidan su Sa’adatu, ya dade a tsaye yana tunanin ta ina xai fara gabatar mata da kansa, tambaya ya jefawa kansa wacce ya gaxa samun mai amsa masa, da wane ido ma xai dubeta yace yana sonta, shi dai tunda yake a tarihin rayuwar sa bai taɓa xuwa kofar gidan su wata yarinya da sunan soyayya ba, amma ga shi yau yaxo wajen Sa’adatu, shi dai bai san me xai ce ba. Ba shi da tabbacin ma xata karbi soyayyar tasa ko kuma xata yi watsi da ita, wannan ita ce fargabar da ta cika xuciyarsa.

Ta maza yayi ya kira wani yaro ya aika shi gidan.

Muna tsakar gida muna shan iska ni da Adda sbd zafi ya fara xuwa, labarin yadda muka yi da mu’allim nake bata da yadda ya nuna damuwa a kan abinda ya same ni, ba ƙaramin burgeta yayi ba sbd ita kanta tana son mutum mai irin halayensa, zaulayata tayi da cewa ko shi ɗin ma yana ciki ne, sunkuyar da kaina nayi tare da bata amsa da cewa shi baya wasa da ɗalibai ma ballantana har na samu dama yace yana sona, kawai dai ya tausaya min ne a matsayinsa na malamina, muna a wannan halin muka ga yaro tsaye a kanmu.

Adda ce tayi masa magana me yasa ya shigo mana gida ba tare da sallama ba, a ladabce ya amsa da cewa ya dade yana mana magana bamu ji ba, tambayar shi ta shiga yi ko me ke tafe da shi, a nan yake faɗa mata cewa wai ana sallama da ni ne.

Cike da mamaki ta juyo ta kalle ni “Kin bawa wani kwancen gidan nan ne Sa’adatu” a sanyaye na amsa mata da a’a, mamaki ne ya cika zuciyata tare da farin ciki, wannan farin jinin da ya fashe min ba ƙaramin mamaki yake bani ba, yanxu nake kara tabbatar da ribar hakuri, a xuciyata nace Allah na gode maka, mayar da kallonta tayi ga yaron “je ka tambaya kace wanene yake kiranta”

Cikin mintinan da basu wuce biyu ba ya dawo yace “mu’allim Mahmud ne yake kiranta”
Gabana ne ya fadi, kallon Adda nayi ina mamaki, ko me yasa yazo wajena a dai-dai wannan lokacin.
Amsa ta bawa yaron da cewa yace masa ina xuwa.
Cike da kulawa ta dube ni “tashi ki kintsa Sa’adatu kije kiran nasa, ashe dai hasashen da nake yi ya zama gaskiya, tunda naji abinda kika fada min dangane da mu’allim din nan na san yana ciki akwai magana a bakinsa”Murmushi nayi tare da mikewa, daki na shiga na canja kaya na shafa yar powder na fesa turare sannan na sanya hijabina na fito, ni kaina nasan nayi kyau duk da cewa ba wani kaya masu kyau na saka ba. +

Kujeru guda biyu na ɗauka na fita da su na ajiye a soro, lekawa nayi don yi masa iso cewa ya shigo ciki, a bakin machine dinsa na hange shi yayi matuƙar yin kyau, kana ganin shigar ka san waje na musamman xai je da ita.

Muna hada ido ya sakar min kyakkyawan murmushinsa, a hankali ya tako ya shigo kirjina sai dukan uku-uku yake yi sbd ban san me ya kawo shi wajena ba.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]