TSANANI CHAPTER 12

TSANANICHAPTER 12


Sake bushewa yayi da wata irin dariya wadda har sai da ya tuntsura, Allah ne kaɗai ya san irin muguntar da yake shirin kullawa Sa’adatu wani abu zuciyarsa ke hasaso masa matuƙar ya samu Sa’adatu a yanxu shi kaɗai ya san irin garar da xai kwasa, domin ya dade da sanin Sa’adatu tana dauke da baiwa mai yawa, ƙoƙari ɗaya zai yi shi ne yayi duk mai yiwuwa ta dawo cikin rayuwarsa, tunanin irin lugwigwitar da zai yi mata yake yi, saboda ya san dole yanzu yarintar ta taqara fitowa tunda ta samu huta tare da nutsuwa. +

Kamar wanda aka zabura ya tashi ya janyo wata adaka da ke ajiye a gefensa, ya fara fito da wasu irin takardu yana ware wanda zai yi amfani da su fuskarsa na ɗauke da murmushin mugunta. Bincike yake yi sosai sai dai har yanxu ya kasa gano wacce xai yi amfani da ita, wacce da ya xuba aiki xai kama Sa’adatu.

Rigingine ya kwanta yana cigaba da dogon tunanin da ya saba.

★★★★★

Salamu alaikum nace sannan na sanya kaina cikin gida. Da murna “Adda saratu ta karɓe nii
Sa’adatu har kin dawo amma kin yi sauri sosai”
Zubewa nayi a ƙasa ina share gumin da ya ɗan taru a fuskata gami da cire hijabin da ke jikina.
“wash Allah wlh na gaji addah ko don na kwana biyu ban yi tafiya ba, ga shi kuma a qafa na taho ban samu abin hawa ba, shi yasa fa bana son fita sbd a gajiye nake dawowa”

Riƙe haba tayi tana kallona
“oh!! ni saratu Yanzu yar tafiyar nan har kin gaji Sa’adatu, gaskiya ki rage lalaci abinda gidan ba wani nisa ne da shi ba, a ƙafa ma xaki iya zuwa, lallai yaran zamanin nan, idan bakwa motsa jiki wlh xaku tsufa da wuri”

Murmushi nayi ina gyara xama, mikewa nayi xan karbi wukar da take yanka salad na Taya ta aiki dakatar da ni tayi.

“A’a ki bar shi na kusa karasawa, shiga ki samu ruwa a fridge ki sha, baki dade da fita ba suka dawo da wuta”
Amsawa nayi da to Adda, dakko ruwan nayi na dawo muka cigaba da hira.

“Ya kika baro innar Ruqayyah da fatan dai kowa lafiya”

“Suna nan lafiya duk suna gaishe ki sosai ashe wai basu samu labarin abinda ya faru ba, sai da naje nake fada musu, abinda yake bani mamaki Adda babu wanda yake baƙin cikin rabuwata da Malam Jibo kowa murna yake min”

“Ai dole a yi miki murna Sa’adatu Allah ya raba ki da ƙaddara Allah dai ya kyauta ya kare ki daga sharrinsa, abinda nake so da ke yanzu Sa’adatu, ba zama za kiyi ki ta bacci ba, dole mu dage da addu’a don kin san wanan algungumin mutumin ba rabuwa damu zai yi ba, sbd ki san zuciyarsa babu alkhairi Allah ya shige mana gaba ya raba mu da sharrin masu sharri.”

Jikina a sanyaye na amsa da “Ameen” tashi nayi na shiga kitchen na kama mata girki, har na fara haɗa miya naji kamar an tsikare ni na fito, daga gefenta na tsaya yana dubanta
“Adda kin ji izuddeen ya tafi training din custom dan Allah Adda ki taimake ni kije gidan su izuddeen ki jiyo min labarinsa”

Sakin wukar da ke hannunta tayi “Ke Sa’adatu ina raba ki da izuddeen din nan har yanxu kin ki karbar shawarata ko, wannan ai Bara a kufai kike yi, tunda kina son mutumin da ya manta da ke a rayuwarsa ya fita daga shirginki, dan Allah ke a tunaninki yanxu me izuddeen xai yi da ke, ai ya wuce ajinki kiyi addu’a Allah ya haɗa ki da wanda ya fi shi, amma kwallafa rai a kanshi ba naki bane”

Hawaye ne suka kwace min baxan iya cire son izuddeen daga raina ba har abada sbd shi ne mutum daya tilo da ya fara koya min soyayya, kuma duk duniya ina ji da shi kadai xan iya rayuwar aure, amma xan yi kokarin bawa xuciyata hakuri kamar yadda tace, kitchen din na koma na cigaba da aikin gabana.

Tun daga wannan ranar na dage da addu’a tare da kiyamullaili ina gayawa Allah ya kare ni daga sharrin malam jibo ya haɗa ni da dukkan alkhairi idan kuma izuddeen alkhairi ne a gare ni Allah ya tabbatar min, ita kanta Adda saratu tana taya ni wannan dalilin ne ya ƙara min nutsuwa na daina shakkar komai tunda ina gayawa Allah kuma na san xai min maganin matsalata.Ranar wata Lahadi ina zaune a dakina ina tsifa, Ihsan yar Adda saratu ta shigo da gudunta ta faɗa jikina, rungumeta nayi ina kallon kyakkyawar fuskarta. Cikin siririyar muryata ta fara min magana. +

“Aunty saadatu kizo inji Abban mu yana kiranki”
Sauke ta nayi daga jikina na mike
“Kice ina zuwa Ihsan” Hijabina na saka na tafi amsa kiran mijin Addah

Cikin nutsuwa na janye labulen dakin tare da cewa
“Salamu alaikum”
Fuskarsa a sake ya amsa min
“wa alaikumussalm”

Jikin kofar dakin na damu na tsugunna kasancewar dakin Karami ne kuma Adda da sauran yaranta duk suna ciki shi yasa dakin cunkushewa har na rasa wajen da xan xauna.
Cike da kulawa ya dube ni
“Shigo mana Sa’adatu”
A ladabce na shiga na samu kusa da Ihsan na xauna, kaina a sunkuye nace
“Barka da dawo wa Abbah ya kasuwa”

“Alhamdulillah Sa’adatu ya zaman hakuri Allah yayi mana jagora, dama wata shawara muka yi da Auntynki naga yana da kyau ki koma skull saboda zaman a haka ba dadi, kinga yanzu rayuwa ta canza sai kana da ilimi za’a tafi da kai, na samo miki wata makaranta a nan kasan layin mu ta manya ce akwai fannin ilimin boko dana islamiyyah kinga riba biyu kenan, tunda kina da haddar Alkur’ani babu wani abu da xai miki wahala, ina fatan zaki mayar da hankalin ki har muga abinda Allah zai yi a nan gaba”

Wani irin hawayen farin ciki ke bin fuskata tare da wani dadi mara misaltuwa daya mamaye ni, ban taɓa xaton wannan ranar xata riske ni da wuri haka ba, ashe burina zai cika Allah kenan mai yadda yaso, wanda yayi hakuri zai ga ribar hakan, wanda yayi gaggawa kuma xai yi nadama”

Ban san lokacin da na xube ina godiya ba tare da yi masa addu’a, tabbas mijin Adda saratu mutum ne mai karamci da kirki, na dade ban ga mutum irinsa ba, iya xamana a gidan bai taɓa banbanta ni da ya’yansa ba, kuma ko a fuska bai taba nuna min bai son na xauna a gidansa ba, wannan dalilin yasa nima nake girmama shi don yayi min rikon da ko mahaifinta bai min irinsa na.

“Na gode sosai Allah ya kara girma insha Allah bazan baka kunya ba”

Yaji dadin godiyar da nayi masa, cikin sakin fuska yace

“Tashi kije kinji insha Allah gobe zaki fara zuwa Allah yayi miki albarka”

Amsawa nayi da Ameen na fita.

Alhamdulillah Allah kalmar da nayi ta maimaitawa kenan bayan na dawo dakina, ina san karatun sosai musamman na boko amma sbd an fi karfin mu aka danne hakkina ko primary ban yi ba, banda arzikin Alkur’ani da ko Hausa baxan iya karantawa ba, sai ga shi cikin falalar Ubangiji, Allah ya dube ni zan yi karatu kamar kowace diya mace.

Kasa cigaba da tsifar nayi sbd farin ciki, fita nayi naje na dauro alwala nazo na fara jero nafil filun godia ga Allah da ya nuna min wannan rana.
Washe gari misalin karfe tara na safe naji muryar mijin Addah yana kirana, fitowa nayi cikin shiga ta kamala sanye nake da atamfa na rufe jikina da dogon hijabi wanda sai da ya kawo min idon sahu, cike da nutsuwa na tsugunna na gaida shi tare da cewa “Abba na shirya” Addah ce ta fito daga daki tana yi mana fatan alkhairi da dawowa lafiya +

Makaranta ce mai girma tare da wadatattun ajujuwa, cike take da dalibai manya da ƙanana, tsarin makaranta yana da kyau sannan akwai cikakkiyar tarbiyya uwa uba kuma ga karatu, makaranta ce da ta haɗa bangarori biyu boko da islamiyya, wannan dalilin ya sanya mutane tururuwar sanya ƴaƴansu a ciki, muna shiga office din shugaban makaranta muka nufa, a hankali mijin Adda yasa hannu ya tura kofar office din tare da yin sallama, da girmamawa aka karɓe mu tare da bamu gurin zama, form din da muka zo da shi ya miƙawa shugaban makarantar, duba form din ya shiga yi tare da kiran wani malami ya bashi umarnin ya tafi da ni ya gwada ni, a nan na bar mijin Adda saratu suna magana, ni kuma na bi bayan malamin ina taku cikin nutsuwa.

Bakin wani aji muka je zaunawa yayi a kan wani benci ya bude file din ya fara tambayata, izifi nawa na haddace yayi mamaki kwarai da nace na haddace Alkur’anin gaba ɗaya, gwada ni ya fara yi duk inda ya janyo min sai yaga na karanta shi dai-dai babu wani kuskure, Kasancewar mun yi karatu mai kyau a makarantar malam Jibo, bangaren littafai muka dawo a nan ne kaɗai na samu matsala, kasancewar makarantar da nayi Kur’ani kadai ake koya mana, don haka ya yanke shawarar sanya ni cikin wani aji da suka bude kwanan nan don na samu karatu tun daga farko.

Raka ni yayi tare da nuna min ajin da xan shiga, a ladabce na saka kai cikin ajin, tarar da su nayi suna ta tilawa ban yi wa kowa magana ba sbd bana so na katse musu abinda suke yi, guri na samu na xauna sai da suka kammala na miƙa musu hannu muka gaisa, wadda nake kusa da ita ne ta juyo ta dube ni fuskarta dauke da murmushi.

“Sannu da xuwa bakuwa, ya sunanki? Ni sunana Khadijah”

Nima murmushin nayi mata tare da bata amsa “Yauwa na gode Ni sunana Sa’adatu”

A hankali muka fara yar hira kafin malam ya shigo, a ɗan hirar da nayi da ita na fahimci Khadijah tana da kirki da san mutane, kwatanta min gidansu ta shiga yi, ashe ma makociyar mu ce gidansu yana kusa da gidan Adda saratu, naji dadin hakan sbd xan samu abokiyar tafiya kasancewar makarantar tana da dan nisa da gidan da nake. Muna cikin maganar malam ya shigo.

Gyara xama muka yi muka bada hankalin mu gare shi, yana shigowa, Ajin yayi shiru kamar ruwa ya cinye kowa da alama dai ana jin tsoron malamin yadda ya kamata, duk da kasancewar sa saurayi hakan bai sa dalibansa sun raina shi ba, kallo daya xaka yi masa ka fahimci mutum ne da baxai karbi raini ba, fari ne sosai yana da manyan idanuwa da dogon hanci fuskarsa kewaye take da saje wanda ya sha gyara, a hankali ya buɗe ɗan karamin bakinsa yayi sallama, cike da ladabi muka amsa gaba ɗaya.Ji nayi yan ajin suna gaishe shi tare da kiran sunan shi da mu’allim Ahmad, a nan na san sunansa Ahmad.

Dora idonsa yayi a kaina da sauri na sunkuyar da kaina, tambaya yayi yaushe aka kawo ni gaba ɗaya yan ajin suka amsa masa da yau naxo, girgiza kai yayi ya samu guri ya xauna.

Ƙarin Bulugul maram yayi mana biyawa biyu naji na iya, don haka da aka xo biyawa gaba ɗaya muryata kadai kake ji a ajin, malamin yayi mamakin kokarina da yadda na mayar da hankali kan karatuna kamar dama can a cikin ajin nake, duk abinda aka biya mana cikin kankanin lokaci na haddace shi, mamakin ƙoƙarina yan ajin ke yi a ranar mutane da dama sun so kulla alaƙar ƙawance da ni, amma ban saki jiki da su ba sbd ina so na fahimci halin kowa, dama ni a halittata ban fiye sakin jiki da jama’a ba, sai na san halin kowa nake sakin jikina.

Da aka tashi tare muka taho da khadeejah muna tafe muna hira har muka xo kofar gidan Adda saratu, sbd gidan su yana ɗan gaban gidan mu, a nutse na saka kai na shiga soron gidan, me xan gani??? Malam Jibo ne jingine da bango ya tsura min ido yana kallona, ban bari mun haɗa ido da shi ba na sunkuyar da kaina sbd na san sharrinsa xai iya saka wani abin a idonsa don na rikice nace sai shi, shan gabana yayi ya tare min hanya, ki tsaya ki saurare ni Sa’adatu nayi nadamar abinda nayi miki a baya yanxu nazo gare ki na gyara kuskure na, ki daure ki kalle ni da wannan kyakkyawar fuskar taki, ina so kiyi min murmushinki mai kwantar min da xuciya, wlh na dade a cikin baƙin ciki da damuwa tun bayan da kika tafi kika barni, wani kululin bakin ciki ne ya tokare min kirjina, ban san lokacin da nayi kukan kura ba na hankade shi da karfina, da sauri yayi kokarin fixgo ni Allah ya bani sa’a na shige gida a guje ina haki.

A firgice na faɗa dakin Adda ina kuka, na shiga ukuna Adda wannan mutumin neman ganin bayana yake ban san wanda ya nuna masa gidan nan ba, kinga yanxu yaxo yana magiya wai sai na koma gidansa, na shiga uku ki taimake ni ki shiga tsakanina da wannan azzalumin kada ya salwantar min da rayuwa.

A birkice Adda ta tashi tana dubana, me kike son fada min haka sa’adatu? kada dai kice wannan masifaffen mijin naki ne ya sake biyo ki.
Girgiza kai nayi alamar shi ne, hijabinta ta dakko ta saka, tare muka fita da ita, duba soron ta shiga yi ko xata ganshi amma babu shi babu dalilinsa don haka muka dawo cikin gida.

Dakina na shiga na faɗa kan gado na fara aikin kuka, na tsani malam jibo ko sunansa bana so a ambata sbd muddin na kasance a ƙarƙashin sa, rusa min farin cikina xai yi na har abada, da na koma gidansa gara na mutu na gwammace mutuwa ba aure a kan dai na aure shi, ganin tunani na ƙoƙarin illatani ne yasa na tashi na dauro alwala na shiga jero nafila tare da karatun Alqur’ani, a ranar daga ni har Adda kasa cin abinci muka yi sbd tunani Allah Allah muka rika yi mijinta ya dawo mu sanar da shi halin da ake ciki.

Mun kasa aikata komai sai aikin tunani, bayan isha’i ya shigo ganin halin da muke ciki ne yasa ya tambaye mu Adda ce ta bayyana masa komai, yaji haushi kwarai sbd shi ma ya tsani malam Jibo, ba ƙaramin bata masa rai yayi ba da har yaxo gidansa.

A lokacin ya fita yaje har gida ya same shi, yau ma a kofar gida ya tarar da shi ya riƙe zungureren carbi yana ta faman muzurai, yana ganin shi ya san ba kalau ba don haka ya mike yana ƙoƙarin mika masa hannu su gaisa, bai karba ba ya bishi da wani kallo yana huci ji yake kamar ya rufe shi da duka, buɗe baki ya hau yi wato sakona ya isa gareka kenan, ai dama Sa’adatu tana sona shiga tsakaninmu aka yi, nayi farin cikin ganinka, na san ko ta qini kai mai tursasata ne ta so ni dole.A fusace ya kalle shi bana son maganar banxa me kake so kace min wannan ya xama na farko kuma na karshe da xan kara ganinka a gidana, idan kuma ba haka ba wlh wlh sai na daureka.

Matsawa kusa da mijin Adda yayi yana masa wani kallo, kai ka isa kaxo har kofar gidana ka fada min magana a kan matar da nake so, duk baƙin cikin ka sai Sa’adatu ta dawo hannuna idan kuma kace baxa ta aure ni ba ,ina mai tabbatar maka cewa ita ma har abada baxa tayi aure ba ko kare bai isa yaxo wajenta ba shashashan banxa da wofi.

Murmushin takaici yayi tare da furzar da numfashi mai xafi, sai me don ka hana Sa’adatu aure ka sani baka isa ka cutar da ita ba sai da yardar Allah, kaine jahili dakiki da har kake ganin xaka iya yin wani abu a kanta, amma babu wanda ya isa ya hana wani aure sai da yardar Allah, yana gama faɗa masa ya wuce ya kyale shi.

Wani tsaki malam Jibo ya buga, dole na dauki mummunan mataki a kanku, a sati biyu nake so yarinyar nan ta dawo hannuna, kafin shekara nayi mata ciki makiya su mutu da bakin ciki Sa’adatu ta zama ta malam jibo har abada, tattara babbar rigarsa yayi ya koma ya xauna..

A fusace muka ji ya shigo don ko sallama bai samu yi ba sai da ya ɗan nutsu, ya zama dole mu yi wa tufkar nan hanci saratu wannan mutumin son ganin bayan yarinyar nan yake yi, a firgice Adda ta dube shi me kake fada min haka Abba, da yake da sunan da take kiranshi kenan

Gyara tsayuwa yayi yanxu daga wajen wannan mugun nake, shi ne yake faɗa min wai idan Sa’adatu bata koma hannunsa ba ko kare baxai zo wajenta da niyyar aure ba, maimakon naga ta bata rai sai naga tayi murmushi.

Lallai sai yanxu na tabbatar da cewa malam Jibo jahili ne da rigar malamai, shi har ya isa yace wani baxai yi aure ba, insha Allah yana ganin Sa’adatu xata yi aure ta haihu kuma ta bar hannunsa da yardar Allah.

Nima ko kadan maganar bata taɓa min zuciyata ba, sbd na san Allah shi ke bayarwa kuma shi ke hanawa, a ranar kwana nayi ina salloli gami da neman sauki a wajen Allah,Washe gari da wuri na tashi na gama aikace-aikacen da zan yi wa Addah sai da na karya sannan na fito daga dakina, a bakin kofar dakin su na tsaya na gaida su tare da yi musu sallama, nace xan tafi makaranta addu’a suka yi min, kafin na fita naji sallamar Khadijah ta biyo min makaranta.

Fuskarta ɗauke da murmushi take min magana kiyi sauri Sa’adatu mu tafi, nasan da kyar ne idan mu’allim Ahmad bai shiga aji ba, kin san dai halinsa sarai baya son makara, ko da yake dai baxa ki fahimci wane ne shi ba tunda jiya kika shigo ajin namu amma sannu a hankali xaki fahimci halinsa, ni har Allah Allah nake yi a canja min aji na huta da takurarsa, yana matsa mana da yawa ragowar ajujuwan makarantar duk ba haka ake musu ba.

Jikina na rawa na dubeta wayyo Allah ban sani ba wlh ai da ko karyawa baxan yi ba xan tafi, amma dai baya duka ko? Dariya tayi baya duka amma abinda xai miki sai ya fi dukan ban haushi ke dai ki taho mu tafi kya ji labari idan mun je aji. Da sauri da sauri muke tafiya kamar xamu tashi sama, bana so daga fara karatuna mu fara samun matsala da malami shi yasa duk na shiga damuwa.

Bayan mun shiga makarantar kuwa shi muka fara hangowa a bakin ajin mu yana janyo kofar ajin, gabana ne ya fadi tare da nunawa khadeejah abinda ke faruwa ku san da gudu muka ƙarasa bakin ajin, tararwa muka yi har ya fara karin Alkur’ani, ja da baya muka riƙa yi aka rasa wanda xai buɗe kofar ya shiga, ni nayi shahada na fara yin gaba ita kuma tana makale a bayana, a hankali ta min rada a kunnnena ke Sa’adatu ba a shiga fa kai tsaye sai an nemi izni, ko saurarenta ban tsaya yi ba na saka kai cikin ajin tare da yin sallama a takaice, babu wanda ya amsa min kasancewar suna karatu, dakatar da abinda yake yi yayi yana bina da wani kallo na tuhuma.

A ladabce na tsugunna tare da cewa mu’allim ina kwana.
A hankali ya dago dara-daran idanuwansa fuskarsa a murtuke ya sake dagowa don ganin wacce zata karya masa dokar aji, ya dade yana nazari kafin yace min wani abu sauke ajiyar zuciya yayi sbd ganin yarinyar da jiya tunaninta ya hana shi bacci, ya dade yana mamakin kansa tare da tambayar zuciyarsa ko menene dalilin da yasa ya tsinci kansa a irin wannan yanayin, shi dai ya san a tsayin lokacin da ya ɗauka a rayuwarsa yau yana da shekara 33, babu wata diya mace da ta taɓa burge shi ballantana har ta hana shi bacci, amma kuma menene dalilin da yasa wannan ƙaramar yarinyar ke san haifar amsa da wani abu dai bai saba da shi a rayuwarsa ba, dakewa yayi ya sake kallona bai ce min komai ba ya mayar da hankali kan Alkur’anin da yake karantawa ni kuma ya barni a tsugunne, sai da ya gama karatun sa tsaf sannan ya waiwayo ya kalle ni.

Kece bakuwar da aka kawo jiya ko? Kaina a sunkuye na amsa masa da eh, murtuke fuska ya sake yi sannan ya cigaba da magana, wannan ajin namu yana da ka’idoji da sharudda wanda na san baki sani ba ko? Cikin nutsuwa na girgixa masa kai, gaba daya idanun yan ajin yana kanmu suna son ganin yadda xata kaya a tsakanin mu. yadda yake min magana ne ya basu mamaki, sbd shi baya yi wa dalibansa magana a hankali ko kadan, hakan yasa daliban ke ɗari-dari da shi, sbd baya sakar musu fuska komai da xafi yake musu.

Cigaba yayi da magana, daga yanzu idan kin xo kin tarar na riga ki shigowa aji to kada ki shigo ki tsaya a bakin kofa har sai na gama na baki izinin shigowa, sannan wannan ya xama karo na karshe da xan sake ganinki da kayan gida kafin wani satin ya kewayo kiyi kokari ki dinka kayan makaranta, duk maganar da yake yi kaina na sunkuye sai da ya sallame ni naje na xauna sannan na dube shi.

Cikin siririyar muryata mara karfi nace “mu’allim da……” Kwarjinin da yayi min ne yasa na kasa ƙarasa maganar da xan yi sbd yadda ya tsare ni da manyan idanuwansa, kamar baya son yin magana yace min, me kike son faɗa min.
Sunkuyar da kai nayi “Akwai abokiyar karatuna a waje tare muka xo”

Kallona yayi ba tare da yace komai ba, bude kofar ajin yayi ya kira khadeejah jikinta na kyarma ta shigo bai ce mata komai ba ya nuna mata guri ta xauna, har muka yi ka yi karatu muka gama gaba ɗaya bai juyo ya tuhumi khadeejah ba, yau ma ku san na riga kowa iya karatu don waɗanda basu gama iyawa ba ma ni na cigaba da koya musu. +

Mutane da dama sun yi mamakin yadda malam ya ɗagawa khadeejah kafa bai ce mata komai ba, wasu har suna xargin ko akwai wani abu a tsakanina da shi, shi yasa har ya kyaleta sbd ni.

Yau ma mu biyu muka dawo daga makaranta muna tafe muna hirar mu, ina shiga gida naji muryar innah, da gudu na ƙarasa na faɗa jikinta ina murna da ganinta, a hankali tasa hannunta ta ɗan ture ni tare da kallon fuskata, ke dai bakya girma Sa’adatu, murmushi nima nayi ya za a yi na girma da hawa cinyarki innata, yadda na dade ban ganki ba ai dole xuciyata ta cika da kewar ki.
Tambayarta lafiyar Babana nayi da sauran yan gidanmu, duka ta faɗa min suna cikin koshin lafiya, kuma ta fada min yanzu tana zaune lafiya babu mai keta mata alfarmarta.

Tashi nayi na shiga dakina don na bar su innah su yi hirarsu ta xumunci, dama irin tarbiyyar da tayi min kenan, matuƙar tana da bako bana saka ta a gaba naji me xasu fada, fita nake yi naje nayi harkokina.
Cire hijab dina nayi sannan na shiga kitchen don xubo abinci.

Daga can nesa naji innah na faɗawa Adda saratu wata magana wacce tasa na xubar da abincin da ke hannuna sbd yadda maganar ta daki kunnena.

About Ismail

Check Also

TSANANI CHAPTER 17

TSANANI CHAPTER 17 Kwance nake bisa gadona ina jujjuya wayata, ba komai nake jira ba …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *