[Advertisements⬇️]

TSANANI CHAPTER 11 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TSANANI
CHAPTER 11Bayan wajen yayi shiru ana jiran umarnin police ya bada damar tafiya ko tsayawa, mikewa Adda saratu tayi tare da cewa ina da magana, damar yin magana ya bata.
Gyara tsayuwa tayi tana mai fuskantar mutanen da ke wajen.
“Ina ganin yallabai kamar mun yi suya mun manta da albasa, domin kuwa akwai wani abu guda daya da muka manta ba mu yi magana a kansa ba wanda barin nasa ba karamin illa bane ga rayuwar waɗannan bayin Allah, yallabai ina so a shiga tsananin yayata da wannan matar” nuna innah salamatu tayi tare da kafeta da ido, dafa kirji Innah Salamatu tayi, xata yi magana kenan Adda saratu ta katseta ta cigaba da bayani.
“Da kuma mijinta sannan da ragowar ƴaƴansu, abinda nake so shi ne yallabai ka jawo hankalin mijinta ya dinga sauke hakkin da ya rataya a wuyansa, sannan ya saurara da cikin zarfinta, ya kamata kuma ya kafawa matarsa da ya’yansa dokoki domin suna take hakkin wadannan bayin Allah ba tare da sun yi musu komai ba, kullum burinsu su zage su sannan su ci musu zarafi, cin kashin da suke yi mata ita da ƴaƴanta yayi yawa yanzu haka kafin mu taho nan sun yi yunkurin dukanta, Allah ne bai sa sun samu damar hakan ba, sannan labari ya iske mu cewa ilahirin kayan dakinta duk sun fito da shi waje sun lalata mata, wannan Dalilin yasa nayi maka magana, don haka a shiga tsakanin su da ita, idan mutunci baxai hada su ba kada su kuskura su shiga gonarta ballantana har su yi tunanin dukanta”
+

Tana gama magana ta koma ta xauna.
A hankali ya juya ya kalli Baba nasiha mai ratsa jiki yayi musa, kasancewar police din mutum mai addini, ya kawo masa hadisai da ayoyi waɗanda suke magana a kan sauke hakkin aure.

Mayar da kallonsa yayi ga su Innah Salamatu da tawagarta.
“Naji dukkan abinda ake xargin ku da shi, don haka wannan ya xama karo na farko kuma na karshe idan muka sake jin wani labari makamancin wannan,to wlh gaba daya sai hukuma ta dauki mataki a kanku, duk abinda ya biyo baya kada ku zargi kowa sai kan ku”

Umarni yayi da a rubuta takarda dukkansu su saka hannu a kan baxa su sake cin zarafin mu ba, haka kuwa aka yi kowa ya saka hannu sannan aka bada su Baba muka tafi gaba ɗaya.

Kallo daya xaka yi musu ka san abinda ya faru bai musu dad’i ba shi kuwa malam Jibo da iyalansa basu biyo mu ba, sai da muka yi nisa sosai sannan suka biyo bayan mu, wani irin kallo Innah Salamatu take mana tana so tayi magana amma ba dama, sbd dokar da aka saka kafa mata.

gidan Adda saratu muka wuce su kuma suka tafi gida.

Zuciyar mu cike take da farin ciki, na dade ban ji dadi irin na yau ba Allah ya kwato ni daga hannun azzalumi Jibo.

shigar mu gidan ke da wuya naji sallamar Baba, don su innah ma basu san yaxo ba gabana ne ya yanke ya fadi, cikin xuciyata na fada “me kuma ya dawo da Baba wajenmu” sai da ya sake yin sallama ta biyu sannan na amsa.

A sanyaye na sanya hijabi na fita, tsugunnawa nayi har kasa tare da cewa “sannu da xuwa Baba ashe kaine kaxo ya hanya?” shiru yayi min ba amsa, jin bai amsa min bane yasa na dago ido don ganin yanayin da fuskarsa ke ciki. Idanunsa na gani sun yi ja da dukkan alamu yana cikin damuwa, a hankali ya daga baki yace.

“Kira min babarki xan yi magana da ita, sannan ina so kuma ku taho tare da kanwar uwar taki duk ina son ganin ku a nan”

A sanyaye na tashi na shiga ciki, abinci na tarar suna ci don haka na nemi guri na tsaya sbd bana so na katse musu abinda suke yi, gaba ɗaya na kasa zama sbd ban san da sabon abinda yaxo mana da shi ba, maganar Innah ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin da na tsunduma a ciki.Tunanin me kike yi haka Sa’adatu kika yi shiru ke kadai, ni fa bana so kike yawaita wannan tunanin kada ki je ki cutar da kanki” A hankali na dago
“ba tunani nake yi ba Innah Baba ne yaxo yace yana so xai yi magana da ku, shi ne ban fada muku ba na bari ku gama cin abinci” +

Xare hannunta tayi daga kwanon da dukkan alamu ita ma jikinta yayi sanyi “Me kuma ya dawo yayi ba yanxu muka rabu da shi ba
Ita ma Adda saratu tayi mamakin dawowarsa, ajiye abincin suka yi suka saka hijabansu muka fita.

Sallama muka yi masa amma babu wacce ya kalla a cikinmu ballantana har mu sa ran zai amsa mana, waje muka samu, su Innah tsayawa suka yi, ni kuma na samu gefe na tsugunna.

Innah ce tayi ƙarfin halin cewa “Malam lafiya naga ka sake dawowa naga yanxu muka rabu ko wani abin ne ya sake tasowa?”

A yatsine ya dago Yana bin mu da wani irin kallo.
“ko ban ce komai ba kema kin san abubuwa sun dade da tasowa, kuma burinki na son toxarta ni ya cika, kin wulakanta ni kin tozarta amanar da Allah ya baki, kin yi sanadiyyar girgizar al’arshin Allah a yau, da sannu xaki girbe abinda kika shuka, ba wani abu ne ya kawo ni ba illa dai na fada miki cewa tunda kika yi kokarin da har auren Sa’adatu ya mutu, to sai ki nema mata wajen da xata koma ta cigaba da rayuwa don ni dai baxan iya rike karuwa a gidana ba, taje duk inda zata je amma ko a hanyar gidana na ganta duk abinda nayi mata ita ta siya.
Sannan abu na biyu kina da xabin da xaki dawo ki ci-gaba da xaman aure da ni, idan kema kin xabi zawarcin ne sai ki faɗa na sawwake miki, kinga yarki ta samu yar uwa kenan, na bar ku lafiya”

A fusace ya fice ya bar mu, bin sa muka yi da kallon mamaki, a cikin mu babu wanda ya iya yin magana sbd mamakin jin waɗannan kalaman nasa.

Murmushin takaici innah tayi tare da kallon Adda saratu “ko kaɗan waɗannan kalaman nasa basu tayar min da hankali ba, sbd idan da sabo na saba jin su, kuma batun komawa gidan sa nima na gama baxan koma ba, Gara na koma ƙauye nayi xamana ina jin xan fi samun kwanciyar hankali a can, amma wannan masifa har ina”

Girgiza kai kawai Adda saratu take yi, cikin nutsuwa ta dube ni “Sa’adatu kada ki damu da wannan abin da yake faruwa jarrabawar rayuwa ce kowa da irin yadda take xuwar masa, ni nayi alkawari xan cigaba da riƙe ki baxa kiyi kuka ba matuƙar kina tare da ni, ke kuma yaya kada kice baxa ki koma, tunda aure ya xama ibada dole kici karo da abinda zai sosa miki ranki, sbd ita aljanna ba a samunta da sauki, kiyi hakuri ki koma sbd rashin komawarki ba shi ne xai warware waɗannan matsalolin ba, kuma idan kika ƙi komawa kamar kin bawa salamatu wata kofa ne na cin karenta babu babbaka, amma xamanki a gidan shi kansa nasara ne tunda baxa ta sake tayi yadd take so ba, tunda dai yanxu an shiga tsakanin ku da ita, nafi tunanin duk wannan abin ita ce ta shirya masa yaxo ya faɗa, don haka ki koma xaman gidan ya xama dole ko tana so ko bata so”

Ni kaina nafi so Innah ta koma sbd baxan so a ce ni ina gida ita ma tana gida ba, abin xai iya zama abin magana, tunda mutane basa raina abinda za a yi ta xance a kansa.

Jikinmu ba ƙarfi muka koma daki, rarrashin mu Adda saratu take yi da kalamai masu dadi sai da Innah ta huce sannan tafi gida.Bayan komawar Innah gida sai da muka kirata a waya muka ji yadda xaman nasu ya kasance tsakanin ta da su innah salamatu, faɗa mana tayi babu wani matsala da take fuskanta sai dai kawai yanxu basa ko kallonta ko magana tayi musu basa amsawa sai dai su bi ta da harara, amma dai ta samu sauƙin cin zarafin da suke mata, wannan maganar ba ƙaramin faranta mana tayi ba, domin kuwa zuciyata cike take da tunanin yadda rayuwarta xata cigaba da kasancewa ita kaɗai a gidan ba tare da ni ba, sai dai har yanzu ina kewar innata kuma ina kewar wajen da nake kwana domin na kwashe kwanaki da dama ba tare da nayi tozali da shi ba sai dai kuma an haramtawa min shiga gidan hakan yasa na ƙara bawa xuciyata hakuri, na fara cire tunanin gidan daga zuciyata

Rayuwa nake yi mai tsananin dadi a gidan Adda saratu, mijinta ba mai kudi bane sai dai yana da rufin asiri sosai, iya xamana a gidan ban nemi komai na rasa ba, yanzu babban tunanin da yake yi shi ne mayar da ni makaranta, ba ƙaramin farin ciki na shiga ba sbd na dade ina son yin karatu amma Baba ya hana ni.

Sakkowa nayi daga gadon da nake kwance kasancewar tun bayan da na farka da asuba nayi sallah ban rintsa ba, sai da na gyara gida nayi abincin karyawa sannan na koma bacci, a hankali na janyo jiki na sakko daga kan gadon tare da duba agogon da ke manne a bangon dakin 12:30 na rana, da sauri na ƙara mutstsike idona gami da yin miƙa, toilet din da ke cikin dakin na shiga na kunna fanfo na hada ruwan dumi nayi wanka, bayan na kammala na shirya cikin wata atamfa ja (red) wacce Aunty saratu ta bani, nayi matuƙar yin kyau Kuma kayan sun karbi jikina sosai, har sake kallon kaina nake yi a mudubi kamar ba ni ba, na fara dawowa cikin nutsuwata amma lokacin da nake gidan Malam Jibo ficika baxa ka siye ni ba sbd yadda na fita a hayyacina duk nayi baƙi na rame.

Jan mayafi na yafa tare da kullo kofar dakin na fita, dakin Adda saratu na shiga tare da yin sallama kwance take a kan doguwar kujera ta tsurawa screen din waya ido tana ta faman karatu, a hankali na ƙarasa wajenta ina mai murmushi “Dadina da ke Adda saratu bakya gajiya da karatun littafi”
Murmushi tayi tare da tashi daga kwanciyar da tayi “Hmm tunda bakya yi baxa ki gane dadin karatun littafi ba da kuma muhimmancinsa, akwai abubuwa da yawa na karuwa da xaki gani kuma xaki koyi xaman duniya da iya zama da mutane”
Gyara xama nayi ina mai fuskantar ta “Nima dai xan fara Adda ko don na san yadda xan kama izuddeen dina”

Murmushi tayi tare da dafa kafadata “ban san lokacin da kika zama mara ta ido ba Sa’adatu ko xaman gidan malam jibo ne yasa kika xama haka?”

Sunkuyar da kai nayi tare da rufe idona “Ba haka bane Adda kawai ke kadai nake iya faɗawa haka, kuma don ma izuddeen din ya shiga raina ne shi yasa”

Cikin nutsuwa ta dube ni “A shawarce ki manta da maganar izuddeen Sa’adatu kiyi addu’a Allah ya kawo miki wani don a ganina izuddeen kamar yayi miki nisa yanxu”Cikin ɓacin rai na tsinci kaina idanuna kamar zasu zubar da hawaye amma sai na daure “Me yasa kika ce haka Adda”
Hannuna ta riƙe “Ni fa ban ce ki tada hankalin ki ba, na fada miki haka ne sbd ina ganin hakan shi ne xai fi sauki a gare ki, kin manta irin abinda Babanki yayi masa da irin cin kashin da ya yi wa iyayensa, a ganina ko izuddeen ya yarda zai aure ki iyayensa baxa su bari ba, sbd xasu tuna abinda aka yi musu sannan xasu dakatar da shi su ce ɗansu baxai auri baxawara ba” +

Ihu ne kawai ban yi ba sbd takaici tabbas abinda ta fada gaskiya ne, amma har yanxu zuciyata bata yarda cewa izuddeen baxai aure ni ba sbd na san irin mugun son da yake min.

Shirun da nayi ne yasa ta gane ina cikin damuwa “Addu’a ita ce mafita Sa’adatu kada ki damu kowace mace mijinta take aure, idan har izuddeen rabonki ne babu wanda ya isa ya hanaki auren shi, idan kuma ba rabonki bane duk son da kike masa haka xaki ganshi ki kyale, to babu damuwa a cikin lamarin aure Allah ya dade da tsara komai”

Naji daɗin maganganunta kuma sun kwantar min da hankali, mikewa nayi ina gyara mayafi “Dan Allah Adda ina neman alfarma xan je wajen Rukayya na ganta kin ga na dade rabona da ita”

Tsura min ido tayi ba tare da tace komai ba “Ni fa bana son fitar nan Sa’adatu idan kina yawan fita munafukai xasu samu damar cewa wani abu, amma tunda wajen Rukayya ne don Allah kiyi sauri kada ki dade”

Naji dadin barina da tayi, sbd a wajen Rukayya ne kaɗai xan samu labarin inda izuddeen yake da matsayin da soyayyata take a wajens

Jikina na rawa na nufi gidan Cike da nutsuwa nake taku a hankali kaina a ƙasa har na isa kofar gidan su Rukayya, da sallama na shiga cikin gidan, tun daga uwar daki ta jiyo muryata da gudu ta taso muka rungume juna muna murna, hannun mu riƙe da na junanmu muka shiga dakin tare da samun guri mu zauna. +

Ina umma na tambayeta, faɗa min tayi tana banɗaki tana wanka,
Sannu da xuwa tayi min tare da jawo min flask din abinci gami da cewa.

“Ga abinci ki ci Amaryar malam don na san kin yi kewar girkin umma”
Murmushi nayi “Ai kuwa dai kamar kin sani”
Plate ta janyo ta fara xuba min abincin, kallonta nayi ina murmushi “kada ki zuba abincin nan Rukayya wlh a koshe nake sai da na ci abinci na fito”
Tsayawa tayi da zuba abincin tana hararata “Tunda malam ya shagwaba ki ai dole kice baxa ki ci irin girkin mu ba, lallai Sa’adatu amarci yayi daɗi, to ko bakya so sai kin ci abincin nan
Cigaba da xuba abincin tayi, sai da ta haɗa komai sannan ta turo min shi gabana.

Cike da kulawa ta dube ni “Sannu da zuwa Amaryar malam kin yi kyau sosai kin canja, kin fi komai a kan xuwan da nayi kwanaki, yaushe rabon da na ganki aminiyata, yau dai wato yaga dama ya bar ki xaki yi zumunci”

Ɗan murmushi nayi wanda sai da hakorana suka bayyana ” Hmm ashe fa baki san wainar da ake soyawa ba ko?”

Kallo ta bi ni da shi “Kamar yaya, yi min bayani kawata”
Rausayar da kai nayi “mun rabu da Malam Jibo fa nayi zaton ma kin ji labari don duk xancen ya baxa gari”

“Ban ji ba wlh, ai kin san baxan ji ba tunda bana shiga harkar yan unguwar nan sbd munafuncinsu”

Nayi tsammanin xan ga ɓacin rai a fuskarta sbd aurena ya mutu sai naga ta daka tsalle tana murna ” Alhamdulillah Allah ya taimake ki kin yar da kwallon mangwaro kin huta da kuda, wannan masifaffen aure ina ranarsa, ai da naga kin yi kyau kin canja na xaci kyallin amarci ne, ashe kyallin yan matanci ne”

Dariya muka sa gaba dayan mu, a dai-dai lokacin ummansu ta shigo, tun daga nesa take ta buɗe ido, da alama tana son tabbatar da gaskiyar abinda idanunta ke nuna mata ne, da ƙarfi tayi magana tare da ajiye abin wankan da ke hannunta.
“Wa nake gani haka kamar Sa’adatu?”

Murmushi nayi “nice umma ba idonki bane”
Da sauri ta karaso “Sannu da xuwa amarya yau an tuna da mu kenan

Rukayyah ce tayi saurin cewa “ki daina cewa amarya umma Sa’adatu sun rabu da Malam Jibo Allah ya taimake mu”

Dafe kirji tayi tana salati “Oh amma ban ji daɗi ba mutuwar aure ba tada daɗi ko kadan Allah yasa haka ne yafi alkhairi”

Amsawa muka yi da ameen.
Sai a lokacin nake labartawa Rukayya sanadin rabuwata da shi da irin azabobin da na sha bayan ziyarar da ta kai min, ba ƙaramin farin cikin rabuwa da shi tayi ba, sbd dama tana cikin mutanen da gaba ɗaya basa son tarayyata da shi.

Tambaya na jefa mata.
“wai kuwa ina izuddeen ne?”
Shiru tayi min tare da tafiya dogon tunani sannan ta dago ta dube ni
“Tun bayan rabuwar ku da shi sau biyu kawai muka taɓa yin waya, sai a wajen abokinsa nake jin labarin cewa ya samu aikin custom yanzu haka yana can yana training”Ji nayi gaba ɗaya jikina ya mutu, tabbas abinda Adda saratu ta faɗa min na cewa izuddeen yayi min nisa gaskiya ne, ban iya cewa komai ba sbd halin da na tsinci kaina.

A hankali ta dago da kaina tana dubana “ya naga kamar kin damu Sa’adatu? Na san dole xaki ji ba daɗi na rashin izuddeen, sbd shi ne mutum na farko da ya fara koya miki SO, amma hakan kada ya sanyaya gwiwarki idan har izuddeen rabonki ne xai dawo gare ki, fatana dai ki cigaba da addu’a sai kiga komai ya zo da sauki”

Sauke ajiyar zuciya nayi tare da cewa”Haka ne insha Allah xan cigaba da yi”

Nayi zaman sama da awa biyar a gidan muna ta hirar yaushe gamo da kuma labarin izuddeen, ban tafi ba har sai da nayi magariba, har gida Rukayya ta raka ni.

*********

Malam Jibo ne zaune ya haɗa kai da gwiwa ya rasa me yake masa daɗi a ransa, tun bayan rabuwar su da Sa’adatu bai sake jin wani abu mai suna farin ciki ba, ko abinci ya daina ci kullum tunaninsa ya zai yi ya dawo da ita gidansa, burinsa yana cika zai ɗauke ta ya mayar da ita kauyensu ta cigaba da rayuwa a can

Ɗaya daga cikin ƴaƴansa ya kira tare da umartarsa ya kira masa ɗaya daga cikin almajiransa, da sauri yaron ya fita ya sanar da shi ya shigo.

Da Sallama ya shiga shagon da malam Jibo ke xaune, tsugunnawa yayi tare da gaida malam din.
Sakin labulen shagon malam Jibo yayi Sannan ya dawo ya xauna yana mai fuskantar sa “wani aiki nake so ka taya ni”
A ladabce ya amsa da “to malam”
Wata farar takarda ya xaro tare da mika masa.
“Ina so kayi min sirrin da Sa’adatu Amaryar da na aura kwanaki, xata dawo wajena da kafafunta, kayi iya bakin kokarinka wajen ganin ka mallake min ita ta dawo gidan nan ko tana so ko bata so, nima ina nan xan bada himma wajen yin wani, na raba aikin ne sbd abin namu yayi sauri”

Tashi kaje, daga yanxu nake so ka fara aiki, nan da jibi kuma nake son ganin sakamako. 1

Jikin sa na rawa ya tashi yana fita malam Jibo ya bushe da wata dariya yana mai cewa “Da kafarki xaki zo kina neman gafara Sa’adatu indai ni ne na isheki riga da wando har da yar ciki

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]