[Advertisements⬇️]

TSANANI CHAPTER 10 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

TSANANI


CHAPTER 10


A hankali ta xare sakatar kafin ta bude har sun ‘kagu sun hankado kyauran saura kaɗan ta fadi a kasa, cikin kasalalliyar murya take tambayar innah salamatu “Haba Hajiya ya xaki turo min kofa da karfi haka, idan kin yi hakuri xan bude miki, yanxu da ina da rabon wahala karya ni xa kiyi saura kiris na fadi”
Wani kallon wulakanci ta watsa mata “to menene dan kin karye, ai da xaki karye din ma haka nafi so, da xamu fi samun sassauci a kan masifar da kike kokarin jefa mu a ciki”
Cike da mamaki ta dube su
“Ban fahimci abinda kike son faɗa ba wani abin ne ya faru, ni dai na san ban yiwa kowa komai ba?”
Matsowa tayi kusa da ita “Au tambayata ma kike?? Ki fada mana inda malam yake kafin mu fara canja miki halittarki, don na fahimci sai mun fara gyara miki xama a gidan nan xaki daga mana kafa

Da jin wannan kalaman nata sai taji ta warware daga dukkan kasalar da take ji, murmushi tayi gami da kallonta ido cikin ido.
“wannan ne kuma baki isa ba, ba ki da wannan ikon, dakata kiji salamatu shiru fa ba wasa bane gudun magana ne, kada kiyi tsammanin dukkan abinda kike yi ina kyale ki tsoronki nake ji, ina kyale ki kawai ba don komai ba sai don gudun tashin hankali, amma ba wai don ina tsoronki ba ko dan kin fi karfina, magana ta fatar baki don kin yi min bai zama lallai na tanka miki ba, sbd karya baxa tayi min haushi na rama ba, amma matuƙar kika yi kuskuren taɓa jikina da sunan duka a ranar xaki gane halina da yadda nake, ko an fada miki hakuri hauka ne? To ki shiga hankalinki kin san idan ‘kura ta kai bango dan adam baya iya jurewa”

Jin kalaman Innah da tayi da yadda ta ɗau zafi ne ya sanyaya jikin Innah Salamatu amma sai ta daure, bata nuna cewa taji tsoro ba, ita ma zazzaga mata masifar ta shiga yi.
“Dama ai ban ce kiji tsorona ba, amma dai tabbas dole kiyi abinda muke so ki fada mana inda kika boye mana mijinmu, tunda dama ke ya sallama ki ba ki daga cikin matansa sbd halinki na tsiya

Murmushin takaici innah tayi “Banda abinki daga sallamar sai me na mutu ne ko kuma kinga na ragu?? Ina nan yadda nake sai ma cigaba da yake ta xuwar min”

Kwashewa tayi da dariya “Tabbas haka ne cigaba yaxo tunda gashi nan an dakko ‘ya daga gidan mijinta an kai ta bariki karuwanci, tabbas cigaban mai hakan rijiya yazo”

Wannan maganar ba ƙaramin sosawa Innah rai tayi ba sai dai kawai ta share ta kyaleta sbd idan ta tanka mata abinda xata fada mata sai ya fi haka”

Matan Malam Jibo ne suka mayar da kallonsu ga Innah “Dan Allah Hajiya ki faɗa mana inda maxajen mu suke, kinga tun safe da suka fita basu dawo ba kuma uwar gidanki ta faɗa mana cewa kece kika boye su

Rausayar da kai Innah tayi “wlh ban sani ba, sannan kuma ban san dalilin da ya hana su dawowa gida ba, amma idan baku yarda ba shikenan baxan rantse muku a kan hakan ba”

Tana gama faɗa ta mayar da kallonta ga Innah Salamatu “matsa na kulle kofata malama”
Kafin tace mata wani abu tuni ta tunkud’eta ta kulle kofarta, haka ta bar su cikin mamaki, musamman Innah Salamatu da bata taɓa tsammanin innar Sa’adatu xata rama cin zarafin da take mata ba.

Jikinsu a sanyaye suka kama hanya suka bar kofar dakin, soro suka koma suka fara tattauna yadda xasu samowa kansu mafita.

Haka suka riƙa tattaunawa ƙarshe dai suka yanke shawarar washe gari xasu fita nemansu, tare da bada cigiya gidajen radiyo.

*********
Zaune nake bayan na idar da sallar walha ina addu’a, Adda saratu ce ta shigo hannunta rike da flask din abincin karin kumallo, gefena ta samu ta xauna tare da ajiye flask din abincin a gabana, sai da na shafa addu’a sannan ta juyo da kallonta gare ni
“ga abincinki nan kiyi maza ki ci ga maganinki nan kuma ki sha saura kuma ki bar min ragowa, yanxu nan Baban su ihsan ma xai koma asibiti ya sake karbo miki wani maganin” +
Murmushi nayi tare da cewa “Ai baxan bar ragowa ba yau na ƙara jin ƙarfin jikina sosai”
A hankali na ja kwanon abincin na fara tsakuwarar doyar da ta soya min, bai fi guda biyu naci ba na ajiye kasancewar bakina babu dandano ko kaɗan, da kyar nake iya cin abincin, haka dai ta takura min sai da naci da yawa

Hira muka fara yi da Adda saratu tare da taya ni murnar yadda na samu kaina daga hannun malam Jibo, muna cikin maganar ne mijin Adda saratu ya shigo, ƙoƙarin tashi nayi xan fita na bar ɗakin sbd su samu damar yin maganarsu.

Har na mike yayi min magana
“kiyi xamanki mana Sa’adatu ba xama xan yi ba”

Mayar da kallonsa yayi ga Adda saratu “ina takardar nan da aka rubuta mana magani bani na tafi yanxu na siyo”

Cike da nutsuwa ta tashi ta mika masa sallama yayi mana ya fita
Dawowa tayi kusa da ni ta xauna tana fuskantata “Oh Allah mai iko Sa’adatu kin yar da kwallon mangwaro kin huta da kuda, da tuni yanxu kina gidan malam jibo kina fama da warin hammata”

Kwashewa muka yi da dariya a tare “wato abin ma har da cin fuska Adda sweetyn nawa kike fadawa haka”

Murmushi tayi “tunda sweetynki ne ai sai mu mayar da ke, ku cigaba da shan soyayya”

Da sauri na dakatar da ita ina murmushi
“Ina baxa ai ba a yi haka ba Adda, wato baxan iya mislata miki irin daɗin da nake ji ba a xamana a gidan nan, ji nake kamar an saka ni a aljanna, tunani ɗaya nake yi kawai ya xan yi da Baba”

Cike da kulawa ta dube ni.
“ki daina wannan tunanin ko yace baza ki koma masa gida ba a kan Malam Jibo xan riƙe ki har lokacin da Allah xai baki miji kiyi aure, dama ai zaman kuncin kike yi a gidan banda wahala babu abinda kike sha”

Wani sanyi naji a raina “to amma kuma Adda Inna fa?”
Dan tabe baki tayi “Innah ba matsala bace ita ma xata samu mafita insha Allah”Hirarmu muka cigaba da yi cike da farin ciki da annashuwa babu abinda yake damunmu, don ni tuni na cire tunanin Malam Jibo a raina +

Bayan fitar mijin Adda saratu daga gida kai tsaye asibiti ya wuce, office din likita ya shiga don ya gaishe shi ya kuma faɗa masa yadda jikin Sa’adatu ya kasance.

A hankali ya bude kofar office din ya shiga tare da sallama, yana ganinshi ya fara murmushi tare da yi masa sannu da xuwa, kujerar da ke gefensa ya samu ya xauna, hannu ya mika masa suka gaisa sannan ya xauna, ya mai jiki yayi masa.
Fuskarsa a sake ya amsa masa da.

“Jiki alhamdulillah yayi kyau sosai, don har ta kusa shanye maganinta yanxu wannan da ba a siya ba naxo na siya mata shi ne nace bari na shigo mu gaisa”

Cike da farin ciki ya amsa masa “Ai kuwa ka kyauta kuma naji dadin xuwan da kayi, dama ina ta tunanin ina xan sake ganinka na baka labarin matsalar da ta taso”

Gyara xama yayi tare da bashi hankalinsa “me kuma ya taso doctor”
Sauke gilashin da ke idonsa yayi “kada ka damu ba wani abu ne mai xafi ba naga kamar hankalinka ya ɗan tashi”

A tare suka murmusa
“to ai dole ya tashi ni da nake da mara lafiya ai sai na xaci ko wani ciwon ne ya samu”

Girgiza kai likitan yayi “ba ma a kan wannan matsalar bane a kan wadannan mutanen ne da ka fada min cewa ɗayan mahaifin mara lafiyar ne dayan kuma mijinta ne, to su ne suka dawo nan suka min ba dai-dai ba”

Da sauri ya dube shi “me suka yi maka doctor?”

A nan ya kwashe ya bashi labarin yadda suka yi da su malam Jibo, da irin cin mutuncin da suka yi masa, da kuma matakin da ya ɗauka a kansu.

Ba ƙaramin dadin hakan mijin Adda saratu yaji ba sbd shi ma ya samu damar da xai kwatarwa Sa’adatu hakkinta, sbd idan kai tsaye ya kai su ƙara sai abin ya xama abin magana, a ce ya shigar da mijin yayar matarsa ƙara. A lokacin ya nuna damuwarsa, ya kuma nuna bai ji daɗin abin ba sbd kada likita ya gane akwai rashin jituwa a tsakanin su.

“Da ka sani ba baka kai su ba doctor ka kyale su da halinsu”
Cike da nutsuwa likitan ya sake dubansa.
“To ai kyale su da ake yi ne yasa suke yin haka, ɗaukan matakin shi ne abinda ya fi dacewa sbd su kiyayi gaba, kuma su san bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane, kuma kaga ko ku kun samu hanyar da xaku warware matsalar da ta taso muku a kan auren yarinyar”.

Sauke ajiyar zuciya yayi “Haka ne kuma to ba komai xan koma gida na sanarwa da iyalansa halin da ake ciki”

Number wayar mijin Adda saratu ya karba shi ma ya karbi tasa sannan suka yi Sallama.

Tunda ya koma gida yake ta tunanin ta wace hanya xai bi ya fadawa Sa’adatu cewa an kama Babanta, yayi ƙoƙarin danne zuciyarsa ya fada mata amma sai ya kasa, sbd baxa ta so a ce mahaifinta yana hannun hukuma ba, duk da cewa ita kanta yana kuntata mata.

Fita yayi ya nufi gidan malam Salisu dan ya fadawa Inna Salamatu inda mijinta ya makale.Ko da yaje bai samu ganin innah salamatu ba kasancewar bata nan, sai ɗaya daga cikin yaranta ya bawa sakon, tare da cewa ya faɗawa innarsa yadda suka yi, shi kuma ya kama hanyar tafiya gida.

Yana zuwa ya sanarwa Adda saratu inda Baban Sa’adatu yake, ya kuma roketa da kada ta faɗawa Sa’adatu don kada hankalinta ya tashi, tunda har yanxu bata gama warkewa ba.

***********

Washe gari ma yawon neman Baban Sa’adatu innah salamatu ta fita yi, ita da matan malam Jibo duk inda suka tsugunna sai sun bada labarin cewa da Innar Sa’adatu aka haɗa baki aka sace su, duk sun bi sun gama yaɗawa a unguwa.

Babu inda basu je suna cigiyar shi ba amma babu shi ba labarinsa, hakan ba ƙaramin tada musu hankali yayi ba, don har ya’yansa na ma’aura duk sun xo daga gidan maxajensu tare da su ake yawon nemansa, gidan a cike yake da ya’ya ana ta jimami kamar gidan makoki, yau tun safe da suka fita basu dawo ba sai yamma.

Dawowarta ke da wuya ɗaya daga cikin ƴaƴanta wanda mijin Adda saratu ya bawa sako ya shigo a firgice, don ko sallama bai samu damar yi ba sbd halin rudani da ya tsinci kansa a ciki, tunani kawai yake yanxu a ce kamar Babansa bai wuce kamun yan sanda ba, Babban abinda ya dame shi bai wuce rashin sanin abinda mahaifin nasa ya aikata ba, addu’a yake Allah yasa ƙaramin laifi ne ba babba ba, tana ganinsa ta miƙe tare da cewa.

“Kaji wani labari ne dangane da mahaifinka?” Jikinsa sanyaye ya nemi guri ya xauna.

“Eh naji innah amma ba labari ne mai daɗi ba”
Gaba daya hankalin mutanen dakin ya dawo kansa kowa yana jiran abinda xai fito daga bakinsa.
Cike da kosawa Innah Salamatu ta kara tambayarsa
“Me ya faru da Baban naku, kuma yana ina yanxu”?

Kansa a sunkuye ya amsa mata da “yana hannun sanda su suka kama shi”
Dakin ne ya rude da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinsa, tare da mamakin jin yan sanda sun kama Mahaifinsu.

Dafe kirji tayi tana salati “yan sanda kuma me ya haɗa malam da yan sanda shi da baya rigima da kowa kuma bai ci bashin kowa ba, don da akwai wata matsala tun a ranar da ya fita xai faɗa min tunda baya biye min komai, mun shiga uku na salame”

Cikin nutsuwa yace “ba tada hankalin ki za kiyi ba innah, komai xai zo da sauki ke dai kiyi addua idan mun je a bamu belinsa”

Kuka take yi kamar wacce ake ce ya mutu, cikin kukan take cewa.
“me yayi aka kama shi kuma wanene ya faɗa maka ma an kama shi, dan ni har yanxu ban gama yarda ba”

Nan yake bata labarin cewa mijin Adda saratu ne ya bashi sako ya faɗa mata, tana ji an ambaci cewa mijin kanwar babar Sa’adatu ne ta fita a fusace, ƴaƴan ne suka fara kiranta tare da tambayar inda zata je amma bata saurare su ba, kai tsaye kofar dakin innah ta nufa hannunta riƙe da muciya, sai dai tana xuwa kofar dakin ta tarar bata nan.

Tsayawa tayi a bakin kofar tana xagi hade da cin mutuncin innah, jin abinda take yi ne yasa ya’yan suka fito suna tambayarta dalilin xagin da take yi.
Cikin sarkewar harshe ta fara magana.
“Wannan munafukar da ku ke gani ita ce ummul abasin shigar malam wannan masifar, da ita aka kulla komai, baku ga bata nan ba ta fita, yanxu haka mijin kanwarta ne yaxo ya fadi cewa an kama malam, sun yi haka ne don su kashe auren Sa’adatu ta samu lasisin yawon karuwanci, sun san idan basu bullo ta haka babu yadda za a yi ya bari auren ya mutu, tunda shi mutum ne mai taurin kai”Rike baki ya’yan suka yi, da yake duk tunaninsu iri daya ne sai suka hau xagin innah da Sa’adatu suna tsine musu, namijin ne kawai bai goyi bayansu ba. +

Gaba daya suka fita dan zuwa police station din, sai da suka biya ta gidan malam jibo suka sanarwa matansa sannan suka tafi tare.

Da farko sun yanke shawarar xuwa gidan Adda saratu don ci mata mutunci, sai kuma suka canja shawara don kada su bata goma ɗaya bata gyaru ba.

Tafiya suke ba nutsuwa kamar an koro su, kai tsaye suka kama hanyar shiga cikin police station din, daga can nesa aka daka musu tsawa, nan da nan jikinsu ya hau rawa, wani police ne ya karaso tare da tambayarsu.

“Me yasa kuna xuwa xaku shige ba tare da kun neman izini ba, kuna tafe kamar an koro ku, mama son rashin da’a a nan, nan waje ne na ladabtarwa ba wajen rashin da’a bane, me ke tafe da ku”??

Bakin innah na rawa ta amsa da “maxajen mu aka kama shi ne muka xo mu gansu mu ji me suka yi aka kama su”

Girgiza kai yayi tare da cewa.
“Shi ne kuma ku ka saɓo gayya haka kamar masu zuwa gidan biki, ku zabi mutum uku waɗanda zasu shiga su ji abinda ya faru, amma baxa ku shiga gaba daya ba, ragowar su nemi guri nan su tsugunna”

Innah Salamatu da danta da matar malam Jibo guda daya ne suka shiga wajen, police din ne yayi musu rakiya suka shiga har cikin office din da ya kamata su je.

Gabatar da su yayi a wajen D.P.O tare da fadin abinda ke tafe da su.

Umarni ya bayar da a shigar da su wajen wanda case din ke hannunsa, sai dai cikin rashin sa’a wanda case din ke hannunsa baya nan ya tashi daga aiki, don haka aka basu umarni da su tafi gida gobe su dawo.

Cikin ladabi suka tsugunna suka yi masa godia, Inna salamatu ce ta dubi police din “dan Allah yallabai ko xamu samu ganin maxajen namu”

Fuskar shi a d’aure ya amsa mata
“baxa ku gansu yanxu ba sai gobe aka ce, ko bakya ganewa da Hausa da nayi magana”

Jikinta a sanyaye ta amsa da “Na fahimta Allah ya kaimu goben”

Cike da bakin ciki suka fito, ragowar waɗanda suka taho tare suna ganinsu suka fara tambayar su yadda suka yi, fada musu innah tayi bata samu ganin su ba ance sai gobe.

Gaba daya bakin ciki da ɓacin rai ya bayyana a fuskarsu, daya daga cikin su ce tace “ya zama dole mu dauki mummunan mataki a kan wannan shegiyar matar duk wannan masifar ita ta janyo mana, ko hakan zai zama sanadiyyar mutuwata wlh yau sai naga bayanta sai dai a hada mu a kulle ni da su Baban”

Goyon baya suka bata tare da cewa xasu taya ta a daki innar Sa’adatu.A fusace suka shiga cikin gidan tare da kiran sunan innah suna cewa kwananta ya kare idan ta isa ta fito wajensu, ji suka yi shiru bata amsa ba don haka cikin fushi, suka hankada kofar dakin har sai da ta karye sbd dukan da suka yi mata, cikin xafin rai suka shiga ciki suka hau duddubawa ko xasu ganta, ganin basu sameta a dakin ba ya sanya su fitowa tare da tunanin ko tana banɗaki ne, leka banɗakunan gida suka shiga yi suna ambatar sunanta suna xagi, duk yadda dan uwansu ya kai ga yi musu nasiha a kan su hakura da dukanta basu ji ba, don haka ya fita ya kyale su, tafiya yayi gidan da aka ce innah taje don shaida mata cewa kada ta dawo gidan tare da faɗa mata abinda suke shirin aikata mata. Dukkan Mutanen gidan ne suka fito kowace mace hannuna riƙe da abin duka.

A hanya suka ci karo da juna cike da kulawa ta kira sunan shi tare da tambayarsa inda zai je, damuwa ce ta bayyana a fuskar sa a nan yake faɗa mata abinda ake shirin yi mata tare da bata shawarar kada ta koma gidan ta nemi wani wajen daban ta kwana har zuwa lokacin da fitinar xata lafa, komawa gidan yayi ya tarar duk sun fito da kayan dakinta suna watso shi waje, sbd takaici ma bai iya yi musu magana ba sai ya fita ya kyale su.

Tunda ya fadawa Innah wannan maganar sai ta nemi dukkan wani ƙarfi ta rasa a jikinta, komai nata yayi sanyi, da har tayi niyyar komawa gidan amma kuma sai ta fasa, sbd bata shakkar dukkan abinda aka ce su innah salamatu za su yi mata, baxa ta taɓa musawa ba sbd dama basa kaunarta.

Juyawa tayi ta nufi hanyar gidan Adda saratu, tun daga nesa Sa’adatu ta ji Muryar Innah da gudu ta karaso tare da rungumeta kasancewar tunda aka yi mata aure aka kaita gidan malam jibo bata sake tozali da innarta ba, kwantar da kanta tayi a kirjinta tana zubda hawayen takaici.

Ita ma innar kukan take yi sai da suka yi mai isarsu sannan suka saki junansu, kama hannunta tayi suka shiga daki, sai da suka gaisa da Adda saratu sannan suka fara magana

Wani farin ciki da walwala naji ya ziyarci zuciyata, naga innata wacce na kusan shafe watanni biyar ba tare da nayi tozali da ita ba, ji na nake tamkar a aljanna, mayar da kallona nayi ga innata sai naga kamar ba a cikin farin ciki take ba, wannan dalilin yasa na ƙara bada hankali wajen nazarin abinda ke damunta, ban iya cewa komai ba a lokacin, kasancewar suna magana da Adda saratu sai a nan nake jin abinda su Innah salamatu suke shirin yi mata.

Cikin firgici na dubeta, kwalla naji na ƙoƙarin fito min a hankali na sa gefen mayafina na goge, muryata na sarkewa na fara tambayarta “me kika yi musu innah da har suke shirin yi miki wannan muguntar”

Cikin ƙarfin hali ta buɗe baki ta fara zayyano mana abinda ya haɗa su, sai a nan nake ji an kama su Baba, ban ji daɗin kamun da aka yiwa Babana ba duk kuwa da irin tsanar da yayi min, shi ma Malam jibo ban so aka kama shi ba tunda yana da iyali, amma na san duk yadda aka yi wannan mummunan aikin suka aikata don ruwa baya tsami banxa.

Mayar da hankalina nayi ga Innah tare da cewa “yanxu Innah wane hali suke ciki, ni baba ma nafi tausayawa wlh, ga shekaru ga kuma zaman kurkuku”

Sauke ajiyar zuciya tayi “wlh ban sani ba Sa’adatu basu fada min komai ba, sbd sun ce ni sa aka kama su don na kashe miki aurenki ban san a inda aka tsaya ba har yanzu, sai dai muna sauraro Allah yasa mu ji alheri” 2

Gaba daya muka amsa da “ameen”

Tausayi tare da jimamin halin rudani da innah ta samu kanta a ciki, ba ƙaramin daga min hankali yayi ba ina tausaya mana sbd irin rayuwar da muke yi, tunda na taso nayi wayo ban san wani abu mai suna farin ciki ba ,kullum da irin matsalar da xata kunno kai, har abin ma ya fara xamar mana jiki.
A ranar a gidan Adda saratu ta kwana tare da mu.************ +

Washe gari bayan mun karya mijin Adda saratu ya kirata a waya tare da shaida mata cewa ana son ganinmu a police station ya kuma faɗa mata zai aiko mana da daidaita sahun da zai dauke mu ya kaimu, jikina ne ya dau rawa sbd ban taba shiga police station ba kuma bana fatan wani abu ya shigar da ni, sai gashi yau ta sanadin malam jibo da Baba xan shige shi.

Rudewa nayi gaba datya na kasa yin komai, tsoro ɗaya nake ji kada su je su shirya mana sharri karshe mu koma hannu, har sai da Innah ta lura da irin halin rudani da nake ciki, kwantar min da hankali ta shiga yi muna wannan halin mai daidaita ya iso.

Jikinmu a sanyaye muka shiga muka tafi, cikin mintunan da basu wuce sha biyar ba muka isa wajen.

A cike muka tarar da office din, innah salamatu da ƴaƴanta gaba ɗaya sun halarci gurin sai bin mu suke yi da kallon wulakanci, matan malam Jibo ba ma duk sun zo, su ma harara suka bi ni da shi gani suke kamar nice nasa aka kama mijin su.
Su Baba da malam Jibo suna tsakiyar kanta a tsaye, ga kuma likitan da ya duba ni xaune a kan kujera, sai kuma yan sanda guda hudu da ke tsaye biyu a bayan su Baba, daya riƙe da littafi da biro, dayan kuma hannunsa riƙe da kulki da bindiga, gaishe su nayi gaba daya amma mutane kadan ne suka amsa. wajen xama aka nuna mana, jikina na rawa na xauna sbd ban saba ganin irin wannan ba, muna xama mijin Adda saratu ya shigo.

Gyaran murya wanda case din ke hannunsa yayi tare da mayar da kallonsa ga likitan, “Doctor ga ka ga kuma masu laifi, ga kuma iyalansu don haka sai ka maimaita abinda suka yi maka kowa ya ji da kunnen sa”

Gyara xama yayi ya fara zayyano abinda suka yi masa daya bayan daya.
Daya police din yana rubuta dukkan abinda ya faɗa sai da ya gama tsaf. Police din ya mayar da kallonsa ga su Baba, fuskarsa a daure ya tambaye su.

“Kun ji dai abinda yace kun yi masa ko, kun tabbatar da abinda ake xargin ku a kansa? Ko kuma kuna da ja”

Cike da ladabi suka dago, ban taba zaton malam Jibo da Baba xasu yi laushi haka ba, har da sunkuyawa. Baba ne ya yi magana a madadinsu “Tabbas dukkan abinda ya faɗa haka yake babu karya a ciki, mun yi kuskure sai dai muna fatan a yi mana sassauci”

Daka masa tsawa yayi “kana so a yi maka sassauci kaje ka aikata, babu makawa sai mun kai ku kotu kun girbe abinda ku ka shuka gobe ma kwa sake cin mutuncin wasu”

Jikin su ne ya hau rawa, suna rokon a yi masu sassauci ni kuwa ban san lokacin da na fara kuka ba, ina taya su rokon likita ya yafe musu.

Tsawa ya daka wacce sai da kowa ya shiga hankalinsa “ku saurara ba ku da hurumin da xaku tursasa wanda aka yiwa laifi a kan cewa dole ya yafe, sai abinda yake so shi xamu yi tunda mu aikin al’umma muke yi, ba son xuciyar wani xamu bi ba”

Dukkan yayan gidanmu kowa kuka yake yi sbd matuƙar aka kulle Baba tamkar mu aka kulle.

A hankali likitan ya dubi police din yace “Albarkacin iyalansu na yafe musu, amma da tasu ne sai kowannensu ya ja sarka tunda ba su da mutunci kuma basu san shi ba.

Da har ɗan sandan ya nunawa likitan kada ya hakura, ya kai maganar gaba amma sai yace ya yafe, haka dai aka turza ƙarshe aka bada belin su a kan dubu ashrin, nan fa ake yinta malam Jibo ba dubu ashirin baba ma haka, haka dai aka yi karo karo tsakanin ya’yan gidanmu da matan Malam Jibo aka biya musu..

Sai da aka gama case din likita tsaf, sannan mijin Adda saratu ya miƙe tare da yin magana.
“Nima Ina da nawa case din da su yallabai”

Cike da kulawa ya bashi amsa da “ina saurarenka”

Gyara tsayuwa yayi tare da nuna Malam Jibo.
“Wannan shi ne mijin Sa’adatu yar wannan bawan Allahn da aka gama magana a kansa yanxu” ya nuna ni tare da nuna Baba Sannan ya cigaba da magana.
“Ya aura mata wannan mutumin a don bata so, shi kuma sai yayi amfani da wannan damar yake musguna mata, bayan haka baya bata abinci baya kula da ita, bai san wani hakki nata ba, satinta kusan biyu tana cuta kaita asibiti ba, a dalilin hakan ne yasa ya ci wa doctor Mutunci, kullum kokarinsa ya xai yaga ya cutar da ita, banda Sa’adatu yarinya ce mai tarbiyya da tuni a tuni abinda muke ji a radio ya faru da ita, amma sai ta danne zuciyarta ta hakura ta zauna, amma duk da haka bai saurara mata ba, kullum sai ya haɗa mata sharri a wajen babanta, har cikin gida mahaifinta yaje ya daketa ya ci zarafin ta, duk a kan wannan mutumin idan ba so suke su tunxurata ta zama mara kirki ba me suke so da ita” +

Sai da ya karanto dukkan abinda malam Jibo yayi min da abinda Baba yake mana ni da innah tun daga farko har ƙarshe sannan yayi shiru, girgiza kai kawai ɗan sandan yake yi shi kansa abin ya d’aure masa kai, dama kuma doctor ya fara bashi labarin halin da nake ciki.

Mayar da kallonsa yayi gare ni “ke baiwar Allah kin ji dukkan abinda aka fada shin da gaske me duk wadannan abubuwan da ya fada sun faru?” da sauri na girgixa kai nace “haka ne abinda ya fada”

Sake mayar da kallonsa yayi ga malam Jibo “kai ma kaji abinda ya faɗa a kanka gaskiya ne”

Bakinsa na rawa yace “Ba haka bane dukkan abinda ya faɗa karya yake min kawai yana so ya kashe min aure ne” 2

Kallonsa police din yayi kawai ba tare da yace komai ba, sannan ya sake mayar da kallonsa ga mijin Adda saratu.

“Ina ganin wannan matsalar kotu ce kawai xata iya rabata, xamu rubuta takarda mu mika ga kotu a saka ranar da za a saurari ƙarar, ina ganin komai zai fi zuwa da sauki, yanxu xan bada belin mutum ɗaya ku tafi, shi kuma wannan malamin xamu rike shi tunda bamu gama da shi ba, ana tuhumarsa da cin zarafin ‘ya mace, dole sai an warware xai koma gida”

Cike da girmamawa yace “hakan ma yayi yallabai Allah ya wuce mana gaba”

Jin an ambaci baxa a sake shi bane yasa malam Jibo yayi saurin cewa “Dan Allah a taimaka a kashe maganar nan yau, wlh ina cikin damuwa na baro yayana da iyalina ban san halin da suke ciki ba”

Wani kallo dan sandan ya bi shi da shi ” kana so a kashe magana amma kake yi mana musu a maganar mu, ka fada mana gaskiyar abinda ke faruwa, idan ba haka ba kuma kotu ta raba ku”

Jikinsa na rawa ya fara cewa “Abinda ya faɗa wani haka yake wani kuma sharri yayi min, amma tunda har yayi magana, ina so ku fadi abinda ku ke so a yi a wuce wurin kawai, xan gyara dukkan halina baxan sake kuntata mata ba, kuma xan kula da ita”

Kallon mijin Adda saratu police din yayi “to kaji abinda ya faɗa me ku ke so a yi, kuna so ya gyara halinsa ne ko kuwa??”

Mayar da ajiyar zuciya yayi “Ni yanxu yallabai ba ni da wani zaɓi tunda ga yarinya nan a zaune ita xata fadi yadda take so a yi”

Kiran sunana yayi a hankali na dago na dube shi.
“Fada min yadda kike so a yi”
Kaina a sunkuye na amsa da “Ina so ya sauwake min”

Kamar na sokawa Baba da Malam Jibo kibiya haka na gani, nan da nan gumi ya fara yanko musu kallona Baba yake yi yana min alamar na janye maganar, ni kuwa na nuna kamar ban ganshi ba.

Bakin malam jibo na rawa yace “Gaskiya baxan iya rabuwa da ke ba Sa’adatu idan kuma xan rabu da ke sai an biya ni dukkan abinda na kashe a wajen aurenki”

Fuskar ɗan sandan a d’aure ya dube shi “kai kada ka kuskura ka sake magana idan ba ni nace kayi ba nan ba wajen hayaniya bane wajen sulhu ne da maganin matsala”

Sake nuna shi da hannu yayi “kaji dai abinda yarinya ta faɗa bata sonka tana so ka sauwake mata, a yanzu kana da zaɓi ko dai ka sake ta ko kuma mu mika ku kotu tayi muku Shari’a”

Wani gumi ne yake ta yanko masa cikin dusashewar murya yace
“Na sake ki saki biyu…….”

Innah Salamatu ce ta xaro idanu tare da cewa “malam kana ganin ana barna a gabanka baxa ka hana ba”

Sai da police din ya dakatar da ita sannan tayi shiru.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]