[Advertisements⬇️]

SAWUN BARAWO CHAPTER5 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SAWUN BARAWO


CHAPTER 5

WAIWAYE…
Asalin su yan garin dutsinma neh dake jahar katsina, amma tun kakanni yawancin su yanayin aiki da kasuwanci ya maidosu garin na gwamna(kaduna) da zama, wanda inhar ba kasanu ba zakai tunanin su d’in yan asalin garin neh. 1

Malam ishak mainasara da rukayya mainasara, sune mahaifa kuma iyaye a gurin Ibrahim,nasiru,da sa’adatu.

Ibrahim mainasara wanda yakasance shine uba kuma mahaifi a gurin rukayya(adda) ,Aysha, kabir, safwan, sa’id, salim,ibrahim(khalil), sai auta nabilah.

Yayin da nasiru yake da ‘yaya biyu kacal a duniya, Sulaiman da fa’ iza.

Autar su kuma sa’adatu dama yaya biyar Allah yabata, Fatima, rabiatu, nasiba, fiddausi sai auta salma.

Dukkan su, suna zaune neh a garin kaduna, kuma Alhamdulillah gaba d’aya zuriar malam ishak mainasara Allah ya azurtasu, mussamman alh ibrahim da shi din wani jikakken business tycon neh yayin rayuwar shi, ba shakka yakasance mutum mai matuk’ar kishi da son yanuwan shi

Allah yayi mashi rasuwa bayan haihuwar nabila da shekaru uku, wanda dama mahaifinsu malam ishak bai dade da tafiya nashi gidan gaskiyan ba, hakan yak’ara sanya dalilin dawowar innah gidan babban d’an nata, bayan fad’i tashin da aka sha da ita akan tuntuni ta dawo tak’i. 1

Mahaifiyar su kuma Hajiya saratu mutuniyar Cameroon ce,baffulatanar kamaru wacce ita d’in ta had’u da mahaifin nasu safwan neh wajen bikin yayar su da suka zo nigeria, wanda shi angon ya kasance yaya a gurin abokin ibrahim mainasara dinne.

Bayan aurenta da alh ibrahim dinne, ta taho da tilon kanwarta safinatu gidan auren ta, sakamakon kasancewar ita kad’ai ta rage a gidan a hannun kishiyar Mahaifiyar su da ta dad’e da rasuwa, kasantuwar basa jin dadin zama da ita, yasanya saratun rok’on shi ibrahim d’in akan rik’on da takeso tayi wa tilon kanwar tata.

Alhamdulillahi bata sami matsala daga kowaba na daga bangaren dangin mijin nata, domin kuwa su d’in sun kasance mutane masu dattako da mutunci.

Bayan wasu shekaru masu dan tsayi kadan, ta aurar da safinar ga wani kanin aboki kuma amini a gurin alh mainasaran, alh saleh tafida.

Alh saleh tafida yaya neh a gurin hisham tafida, hisham tafida ya hadu da safina neh a wata ziyara daya kawo wa amini gurin yayan nashi Alh Ibrahim mainasara.

Ba tare da andau dogon lokaci ba, sakamakon duk kusan anzama d’aya, diba da irin zumunci mai karfi dake tsakanin gidajen aka sanya ranar bikin su

Bayan auren na safina da hisham dinne, suka d’aga kasar California inda shi hisham d’in yake aiki, wanda tafiyar sunyi tane da d’aya daga cikin yaran yayan na hisham din “Abu talib”, sakamakon irin son da ita safinar kewa yaron,wanda shi d’in ma tundaga ranar da yafara ganinta a gidan uncle din nashi yake matuk’ar k’aunar ta.

Saida suka shafe kusan shekaru uku batare da ita safinan tayi koda b’atan wata bane, a inda hankalin su yafara tashi duk a tunanin su ko wata matsalar ce ke damun su, hakan yasanya basui kasa a guiwa ba suka shiga ganin k’wararrun likitoci, a inda aka tabbatar masu da lafiyar su kalau lokacine dai beyi ba.Hakan yasanya suka hak’ura gami da fawwala wa Allah dukkanin lamuran su. Cikin ikon Allah bayan wasu shekaru kamar hudu Allah ya azurtasu da samun cikin da suke matuk’ar son samun shi.

Bayan watanni tara safina ta haifi yarinyar ta samb’aleliya mai kama da mahaifiyar sak, sai dai dan duhun fata data dauko na mahaifin ta.

Ranar suna jaririya taci sunan mahaifiyar su safinan Ramlatu, ramlah yarinya ce mai shiga rai tun tana ficiciyarta, tsananin shakuwar dake tsakanin ta da cousin d’in ta Abu talib, ya sanya ko bacci bata iya yi inba a jikin shi, shakuwa ce mai matukar tasiri a tsakanin su, domin kuwa zamu iya cewa kusan shi dinne gaba daya ragamar kula da ramlatun.

Duk da makaranta dayake zuwa, baya hanashi ya bata lokutan shi wajen ganin ya kyautata wa tilon kanwar tashi dayake matuk’ar so da k’aunar, gaba daya dangi babu wanda baisan da irin soyayya da shakuwar dake tsakanin taleeb da ramlah ba.

Wanda har hakan ya sanya darsuwar wani tunani a zuciyar ta safina, a inda batayi k’asa a guiwa ba ta sanar da mahaifiya kuma yaya a gareta haj saratu akan burinta na son ganin ramlah bata da wani miji a duniya inba talib ba, wanda hakan yazama kamar wasiyya take bar wa yayar tata kamar tasan rai zaiyi halin sa

Maganar tazama kamar wani sirri neh tsakanin ita hajiya saratun, safinan da kuma shi kanshi abu talib din, wanda gaba daya rayuwar shi yataso neh da burin mallakar rai d’aya tak a matsayin abokiyar rayuwa a gareshi, gaba d’aya burin shi da tsarin sa ya gina su neh bisa so da k’aunar ramlah tafida, wacce a lokacin da’ake maganar ma bata mallaki hankalin kanta ba, ma’ana bama tasan da maganar ba, diba da kankantar shekarun ta a lokacin.

Zuwan su ganin gida nijeria neh suka hadu da mummunan hatsarin mota, a hanyar su ta dawowa daga airport zuwa gida, ramlan ce kad’ai ta tsira, domin kuwa mahaifanta da drivern gidan alh saleh tafidan dayazo daukar su gaba d’ayan su basu tsira ba.

Mutuwa ce wacce ta girgiza kafatanin family din biyu, wanda zamu iya cewa babu wanda yafi jin ciwo da radadin mutuwar irin talib.

Fadar irin kukan da talib yayi bata baki neh, domin kuwa hakan har janyo mashi kwanciya asibiti yayi, a inda daga k’arshe ya nuna son kasancewar ramlan a hannun shi domin ta karasa karatun firamare dinta da ta fara a can kasar ta California, wanda shima a can din yake karatun shi na engineering a fannin civil.

Dak’yar da ya Allahu aka samu ya hak’ura yabar zaman ramlan a hannun hajiya saratun, wacce ta dauki gaba daya son duniya ta daura akan ita ramlan, wanda k’warai da gaske ko yaranta da ta haifa a cikin ta ba nuna masu irin so d’in.

A ranar da zaman ramlan zai dawo gidan nasu safwan din, talib d’in dakanshi ya kawota gidan na su safwan duk kuwa da irin b’urarin kukan da takeyi akan ita bataso bazata zauna da kowa ba inbashi ba, da lallashi da komi suka iso gidan nasu safwan zukatan su cike da kuna da alhini na rabuwa da junan su, duk kuwa da cewa a lokacin ita ramlan bata wuce shekaru takwas ba a duniya, hakan ya sanya bata da masaniya da irin rungumar da talib din yayi mata ba lokacin da zai bar gidan.

Kuka take da iya qarfin ta, wanda hakan yak’ara tasiri neh bisa irin marin da safwan d’in ya falleta da shi tun bayan shigowar su gidan nasu, a cewar shi ba’a tab’a sanya shi faduwar gaba ba irin yau din, dad’in dad’awa idanuwan ta masu.kama da na mayu sun sanya kirjin shi bugawa.Wannan marin da safwan d’in yayi wa ramlah shine musabbabi kuma dalilin tsanar da talib d’in yakewa safwan, yayin da shi kuma safwan din ya tsani talib d’in diba da irin yanda ya rungume ramlan yana lallashin ta, lokaci guda yana zubar da hawayen takaici ta gefen idon shi guda, a lokaci guda kuma yana mai yi kanshi fatan yagama abibda yakamata yayi domin zuwa ya dauke abar son shi daga mugaye irin safwan. +

Tun bayan tafiyar yaya kuma masoyi irin talib, ramlan ta fuskanci sabuwar rayuwa a gidan nasu safwan mainasara, hak’ik’a idan ka fidda safwan, a duk kafatanin gidan babu mahalukin da baya ji da ita, k’auna ce irin ta yan uwantaka suke nuna mata, wanda hakan yataimaka wajen mantawa da rashin iyaye da yayan ta da tayi. Amma fa kullum ta Allah tana kan waya gaisawa da yayan nata, wanda har a lokacin bayan shudewar wasu shekaru bai samu damar furta mata sirrin zuciyar shi, abinda yasani shine ramlah ta shi ce shi kadai, domin kuwa shida haj saratun sun san da hakan

A tunanin shi lokaci guda zaizo ya amayar da abinda keh ranshi gameda kanwar tashi, wanda a lokacinne kuma zaiyi k’ok’arin ganin ta zama mallakin shi gaba d’aya.

***
TEN YEARS LATER.

Da dukkan farin ciki da murnar shi yadira kasar tashi ta haihuwa (nigeria) bisa kammaluwar dukkan wasu al’amura nashi masu cike da nasarori.

Shekaru goma kenan rabon shi da tako koda k’afar shi ce cikin k’asar tamu, wanda yayi hakanne bisa tsoron kasa yin komi a yayin dazai sake sanya idanuwan shi cikin na ramlan shi.

Duk kuwa da cewa, sunan baya tare da itane a gaske, domin kuwa komi nata yasani, haka itama yayan nata na nan tsaye cikin ranta, shakuwar su na nan kamar koda yaushe, diba da hanyoyin sadarwa da muke da su a yanzu masu sanya nesa ta zamanto kusa.

Bayan kammala karatun shi na degree neh yajona da had’a masters din shi, bayan kammaluwar karatunne k’asar ta California suka ri’ke shi yayi masu aiki na shekaru uku, a inda dukkan nasarori da alfarmar rayuwa suka wanzu gami da samun gurin zama a rayuwar tashi.

Domin kuwa shi d’in karan kanshi yazama wani d’an matashin tycoon,duk kuwa da cewa a shekarun shi na haihuwa bazai gaza shekaru talatin da biyar zuwa da shidda ba.

Shi d’in kyakkyawa neh mai matuk’ar kwarjini da nasibi, kalar fatar shi data kasance mai duhuwa kamar ta ramlah wacce hutu da jin dadi yasanya har wani shek’i da daukar ido take kaamar irin latin Americans d’innan. 1

Ba shakka shi d’in mutum neh mai yawan barkwanci da sanyin zuciya, mutum neh mai matuk’ar kirki, zaka gane hakanne a karo na farko da zaka fara sanin shi. A lokaci guda kuma mutum neh mai tsanin fishi idan ranshi ya b’aci, wanda hakan ka iya janyo mashi kwanciya asibiti, diba da irin rashin k’warin zuciya da yake da ita. 1

***
CIGABAN LABARI

Hankali kwance hajiyr ta fito daga dakin nata, domin kuwa inda sabo, yaci ace ta saba da irin kiran mafarautan da innar ta saba yi mata a cikin gidan, koda kuwa ba bisa wani dalili mai karfi bane. 1

“Inna ince dai lafiya, har kundawo daga wajen su safwan d’in kenan? “

“Yooo tun yaushe mu muka dawo, ai dauko rablatun nayi ta k’arasa warkewa a gida, domin kuwa da’alama dambanzan yaron nan ba hak’uri neh da shi ba, gaba daya ya hana yarinya sakewa, inbanda k’wak’umarta babu abinda yake.” 2

Ta numfasa kana ta cigaba…….

” Tsakani da Allah kije kitaka wa danki burki, bana ciki da iskancin nan nashi, tunda ni baya jin maganata… Au ni ba ma wannan ba, wannan yaro dalibi d’an wajen Alh saleh neh naganshi zaune a falo sai rabza kuka yake harda su majina, (kuji sharri irin na kakus😂)….. Ince dai ba wani abin akai mashi ba? Keh yaushe ma yazo k’asar neh? ” 4

Gaba d’aya notikan kan hajiya neh suka ja burki gamida daina aiki na wasu sakanni, idan ba kunnuwanta keh jiye mata qarya ba, to hak’ik’a taji inna ta ambaci suna makamancin na talib, wanda kaf zuri’ar tasu babu wani mai irin sunan da yawuce shi talib d’in.Dam… Dam… Dam… Gabanta yacigaba da luguden bugu, lokaci guda kuma ta rik’a ambatar innalillahi wa’inna ilaihirraju’oon.!

Ba shakka tayi mantuwar da bata tab’a yin irinta a rayuwar ta ba, haka zalika tayi aika aikar da batajin zata samu rangwame ba yayin daidaituwar al’amuran.

Take ta runtse ido gamida dafe kanta da hannuwan ta biyu, lokaci guda tanajin wani gagarumin al’amari na tunkaro ta.

Hak’ik’a sauri da k’ok’arin ganin ta gyara al’amura yasanya ta manta da tsohon alk’awarin dake binne a k’asan zuciyar ta, hak’ik’a a yau ta tabka kuskuren da gyara shi zaiyi matuk’ar wahala nan kusa.

Galala innah tayi da baki tana karewa hajiyar kallo, domin kuwa rabon da tace ta ganta a irin yanayin nan har ta manta, kai bama zata iya tunawa ba, domin kuwa wani shimfidadden tashin hankali neh bayyane bisa fuskar ta, wanda hakan yajanyi har wasu tsabi tsabin gumi neh suka fara bin goshin ta. 1

“Yau nake ganin abu iri iri a gidan nan, keh kuma meiyasameki haka saratu? Ince dai ba kunama kika had’iya ba kike irin wannan mashahurin gumin?” Inna ta watso mata tambayar cike da al’ajabi shimfide bisa fuskar ta. 1

“Innah waye kuka ce zaune a falo yana kuka?” Hajiyr ta sake tambaya cike da tsoro.

“Yooo waye ba wannan dalibin ba dan waje alh saleh namu dai dakika sani?inbanda sakarci ina nataba ganin zabgegen ingarma namiji irin shi na kuka sai kace mace?”

Tai tsaki gami da qara cewa……

“Ni wuce muje ko kya jimana abinda ke sanya shi kuka har haka.”

Take hajiya ta juya da sauri tayi hanyar falon, gaban ta na cigaba da bugun talatin, talatin.

***
Koda hajiya ta shiga palon bata ma bi takan safwan dake k’wak’ume da ramlah ba, domin gaba d’aya hankali ta baya jikin ta, burinta kawai ta tabbatar da bayyanuwar taleeb d’in a gidan. 3

Zaune yake inda innar ta barshi, lokaci guda kuma yanayin data tafi tabarshi a ciki, shi dinne a tattare dashi har a wannan lokacin, ba shakka kallo guda zaka masa ka hango bayyanannen tashin hankali bisa fuskar tashi dake jik’e da ruwan hawaye. 1

“Taleeb?”

Hajiyan ta kirayi sunan shi cike da wani irin tsakurarren kuzari, ba shakka bata san daga inama zata fara da wannan gingimemen al’amarin ba. Hak’ik’a ita kanta tasan ba aiwa talib d’in adalci ba, amma ya aka iya da k’addara? Wacce ta riga fatah! 3

A kasalance ya bud’e idanuwan shi dasuka riga suka canza kala, diba da irin yanayin da ya shiga a dan lokuta kadan dasuka shige.

Bin ta da kallo yacigaba dayi,lokaci guda kuma yana bibiyar yanayin ta, domin son gasgata zaton shi. 1

“Hajiya” ya furta maganar a wahalce, lokaci guda yana k’ok’arin dakewa bisa al’amarin dake wanzuwa a can d’ayan sashen na cikin falon. 1

“Taleeb yaushe ka dawo neh? Babu sanarwa kuma?” Ta jero masa tambayoyin lokaci guda.

“Kuyi hak’uri hajiya, dama surprise naso yiwa baby.” ya ida zancen yana mai sake kurawa sashen nasu safwan ido, hakan yak’ara sanyaya wa hajiya jiki, a lokaci guda kuma hakan ya k’ara ingiza wutar kunya zuwa ga ramlan, dominnkuwa cigaba da sunkuyar da kanta tayi bisa rashin sanin abin yi. 1

Gogan ku kuwa, kai kace baisan da wasu halittu ba a falon, diba da yanda ya maida hankalin shi wajen son yin bacci sakamakon wata nutsuwa dayakejin na ratsa sassan jikin shi, duk sanadiyar cusa fuskaar shi da yayi cikin wuyan na ramlan. 2

Shiru neh ya ratsa falon na wasu yan dak’ik’u, a inda kowannensu da irin tubanin da yake sakawa a zuciyar shi.

Shigowar inna a karo na biyu falon ya katse yanayin shiru da falon ya dauka, batare da b’ata lokaci ba kuma tasami guri gami da fara rattabo zance sakamakon ganin har yanzu jikan nata bai sarara ba daga abubuwan da yake. 1

“Halan yaron kirki yau wani abunne ya hau kanka? Wace iriyar jaraba ce haka tak’i ci tak’i cinyewa saboda Allah?” 1

Batare da ya dago ba yabata amsa, “Nifa sweetheart bana son sa’ido, matar ki ce ko tawa?” 1

“Shikenan.” Hajiya ta ambata a zuciyar ta, lokaci guda kuma tanajin wata sabuwar kunya na lullube ilahirin jikin ta.

Sai da ta gallara mashi harara kana tace “Rasa kunya beran tanka, basai ka gaya mani ba sukari ba, tashi maza kadauki akwalar matarka ku k’ara gaba, aikin banza nafasa jinyar.” 1

Ta numfasa kana tacigaba, “Kuma inka gadama karik’a had’iyarta, ina abinda ya shalleni mtsww.”

“Ke kuma…” ta juya kan ramlan.”Keh dad’i miji koh? Ana k’ok’arin kintsa ki kina k’ara manne mashi, Allah baku sa’a, inkin gadama ki ratattake ba ma rub’ewa ba, ko a jikina.” 2

Ta ida zancen tana d’age kafad’a alamun bata da damuwa.

Gaba daya falon shiru ya sake dauka, inbanda saukar nunfashin taleeb babu abinda akeji a falon, ta wani bangaren kuma hajiya ce ta shiga wani irin yanayi na kubcewar dukkan kuzarin ta, diba da yanda gaba daya yanayin na talib ya bata tausayi gami da tsoro.

“Hak’ik’a baya bukatar wani sauran karin bayani, zantukan innah sun wanzar da duk wasu amsoshin daya ke nema tun Shigowar shi gidan, sai dai kuma tabbas yana son jin miyasa hajiya zatai mashi haka?” 1

Kallon dayake bin hajiyar da shi yasa tanemi sauran kuzarin data ta k’ok’arin tattarowa ta rasa, gaba d’aya komi ya kwance mata,shin tayaya zata fahimtar da talib cewar gaba daya al’amuran nan sun wanzu bisa tafarkin qaddara wace tariga fata?

A hankali ta sauke ajiyar zuciya, lokaci guda tai k’ok’arin saita dukkan nutsuwar ta, ba shakka yaron nan na bukatar k’arin bayani, domin kuwa har ga Allah ba’a kyauta mashi ba. 2

“Talib inaso kabani aron hankalinka nan, and dafatan komi zan fada maka zakai k’ok’arin fahimtata tare da yiwa al’amarin kyakkyawar fahimta

Cigaba yayi da kallon hajiyar yayin da sababbin tashin hankali ke cigaba da bayyana bisa fuskar shi, hakan yai mata zuru yana cigaba da kallon bakin ta, lokaci guda kuma yana fatan inama ace mafarki yake, yai maza ya farka.

A hankali hajiyar ta warware mashi dukkan abubuwan dasuka faru cikin dan kankanin lokaci, tare kuma da kara tabbatar mashi dacewa har ga Allah mantuwa dakuma son ganin ta gyara b’arakar data doso su yasanya ta yanke dukkan hukuncin data yanke. 2

Ta k’ara da cewa, “Sabida haka don Allah taleeb ina rokon ka dakayi hak’uri gamida yi mani uzuri bisa kuskuren danayi bisa mantuwa, hak’ik’a ni nasan antauye ka, haka zalika bancika burin yar uwata ba kamar yanda dukkanmu muka so, wanda hakan ya faru neh bisa ajizanci na dan adam, amma kayi hak’uri taleeb, kayi hak’uri mu rungumi wannan k’addara da hannu biyu. “

Ta ida zancen cike da kulawa gamida son ganin ta tausashe shi, duk kuwa da yanda jikin ta ke amace sakamakon yanda taga hawaye na cigaba da zarya bisa kuncin sa, ba shakka da tana da ikon gyara bisa lamarin nan datayi. 2

Tunda hajiya tafara zancen ramlan keh surfa kuka, kuka take mai cike da dimbin bak’in ciki da tashin hankali, miyasa za’a boye mata abu irin wannan? Miyasa yaya talib bai tab’a bayyana asalin k’aunar shi a gareta ba, gashinan shirun shi ya wanzar masu da tashin hankali.

Kuka take da dukkan karfin ta, wanda dama ta dade da zamewa daga kafafun na safwan d’in, sai yanzu take tariyo tarin k’aunar abu talib din zuwa gareta, sai yanzu ta k’ara fahimtar dalilin kulawar shi ta mussamman a gareta akan sauran kannenshi!

“Shin miyasa hajiya zata manta da dukkan al’amarin nan ta mik’a ta gurin mutumin da baya k’aunar koda ganin ta, miyasa hajiya zata wargaza rayuwarta bayan tasan akwai wanda zai iya amsar ta, a dukkan halin data ke ciki?” 2

Taciga da gurza kukan da ko lokacin datake tsakiyar wancan tashin hankalin bata yi ba, ba shakka kodawa safwan yake yawo sai ya saketa ta koma wajen mutumin dayafi kowa k’aunar ta kaf duniyar nan. 1

Ta cigaba da k’ura mashi ido, yayin da k’aunar shi dake binne a kasan ranta ke cigaba da ratsa dukkan sak’o da lungu na jikin ta, lokaci guda kuma yanayin dayake a yanzun ya taimaka wajen k’ara assasa wutar tsanar safwan d’in a ranta, tsana ce sabuwa dal takejin na shigarta, domin kuwa a ganinta shine ummul haba’isin d’in sanya tazara da kantangar karfe tsakanin ta da duniyar farin cikin ta.Komawa yayi ya lafe bisa kujerar, hakanan yana k’ara dangana bayan shi da kujerar da yake zaune, lokaci guda kuma yana maison k’ara tabbatar da irin kallon da ramlan keh mashi, ba shakka hajiya ta rabashu da farin cikin daya dade kaf rayuwar shi yana ginawa, hak’ik’a komi ya wargaje mashi. 1

Zuciyar shi ce ta cigaba da tafasa, hak’ik’a safwan ya cuce shi, ya rasa inda zai sauje akuyancin sa, sai kan tilon yarinyar dayafi k’auna kaf rayuwar shi, ya runtse ido sabbin hawaye na cigaba da wanzuwa bisa kuncin shi…. Hak’ik’a bashi da masaniya akan abinda zai iya yi wa safwan bisa wannan zalunci daya yi wa ramlan shi. 1

Ba tareda damuwa ba bisa fuskar shi ya mike, bayan yagama jin dukkan zantuttukan dasuka wanzu cikin falon, hakan yasa ya k’ara daure fusa tamau domin ganin ya kuntata wa taleeb d’in, ba shakka gayen ya dade yana shigar mashi hanci da kudundune, amma ko abinda ya farun yanzu ya isa ya wargaza sauran kuzarin daya rage wa gayen.

“Keh get up and let’s go.” ya ida zancen yayin da ya maida sauran kallon shi zuwa ga ramlan dake yashe a tsakiyar falon tana kuka.

Banza tayi dashi kamar ba da ita yake ba, lokaci guda tanajin inama tana da ikon dazata mikke ta wawwanka wa wannan fuskar tashi mari.

Mamaki neh yaso ya d’an kamashi, domin a iya saninbshi da ramlah bata tab’a yi mashi musu ba koda sau d’aya neh, hakan yasa ya k’ara kullatar taleeb d’in a ranshi, domin daga dukkan alamu ganin shi da kuma jin wannan sabon al’amarin yasa take nema tafara yimashi fitsara.

Ganin bata da niyyar mikewane su tafi kamar yanda ya bukata yasanya shi yanke shawarar daukar ta kacokan d’in ta.

Da dukkan karfinta ta tatttakura ta tureshi gamida rugawa a guje ta boye bayan hajiyar, lokaci guda tana mai cigaba da rafsa kuka.

Kowa na falon binsu da kallo yake, hatta inna mai bakin iya magana tsit tayi tana raba ido had’i da rik’e hab’a, domin kuwa gaba daya nema suke su kwance mata notikan kanta. 1

“Hajiya wallahi zannkarairaya yarinyar nan, ni sa’anta neh da zanke mata magana tana mani yawo da hankali?” Ya ida zancen yana hararar ramlan.

Gaba d’aya hajiyan jitayi bata da wani kuzarin yin fad’a, hakan yasa cikin lallami tace wa ramlan tayi hak’uri ta tashi tabi mijin ta, amma ga mamakin ta sai ramlan ta make kafada gamida kara sanya kuka, lokaci guda kuma ta furta zancen daya sanya talib da safwan d’in dago kai da sauri.

“Innalillahi, yau nake ganin bala’i, aure kwata kwata yau kwana d’aya shine har kin fara batun neman saki rablatu?”

Cewar inna kenan yayin data kejin tamkar taje ta doddoke talib d’in, a ganinta bayyanuwar shi a gidan neh keh k’ok’arin wargaza rayuwar jikanta da take fatan ta kintsu sanadiyar auren nan. 1

“Yaki zonan ramlah.” Hajiyan ta jawota daga bayanta, kana lokaci guda ta zaunar da ita tana mai fuskantar ta, ba shakka idan har akwai sauran hanyar dazata iya gyara lamarin nan, to hak’ik’a a shirye take da tayi shi.

“Ki nutsu ki gaya mani gaskiya ramlah, dagaske bakyaso kicigaba da zama da safwan a matsayin mijin ki.?”

Da sauri ramlan ta d’aga kai alamun eh, lokaci guda kuma ta k’ara da cewar hajiyar ta taimaketa ta rabata dashi da gaggawa.

Sauke numfashi hajiyan tayi, kana ta sake jefo mata tambayar data ke ganin itace ta k’arshe daza ta iya yi mata, kuma matuk’ar ta gamsu to hak’ik’a safwan dole neh yanzun nan ba anjima ba tasa ya sakar masu yarinya ta auri maisonta da gaskiya.

“Ramlah safwan d’aura maki idda neh? Kigaya mani gaskiya karki boye mani komi don Allah.”

Sunkuyar da kai ramlan tayi, domin bata tsammaci wannan tambayar ba daga hajiyan, lokaci guda kuma ta rik’a jin yanda idanuwan safwan da taleeb d’in keh hora ilahirin jikin ta.

” Inajinki ramlah yi magana. ” ta tsinkayi muryar hajiyan a karo na biyu.

Da sauri ta girgiza kai gamida cewa “Ah ah mammy, ni babu abinda yayi mani.”

Ta ida zancen muryar ta na dan rawa, diba da yanda gaba d’aya yanayin fuskar ta inna ta canza zuwa kalar masifa da bala’i. A yayin da dayan bangaren wata sassanyar ajiyar zuciya da ta kufcewa talib, lokaci guda yanajin yanajin tamkar babyn shi ta dawo gareshi neh tagama. 1

Ilai kuwa tana rufe baki innar ta amshe cike da zallar jin haushi.

“Lallai yarinyar nan, amma baan tab’a ganin yarinya me shegiyar karya ba irinnki,bakiji kunyar ganin ido na ba kika karkace kika sako wannan shegiyar karyar taki da ko sallah baza tayi ba ko rablatu? “

Da saurin ramlan ta amshe gami da cewa “Na rantse da Allah inna babu abinda ya faru fa,kuma ku tambaye shi tsakanin shi da Allah ya fad’i gaskia.” ta ida zancen yayin da take maida kallon ta kan safwan d’in gamida fatan zai fad’i gaskiyar. 1

Wata uwar harara daya banko mata ai bata san lokacin da ta sunkuyarda kanta ba da mugun saur, a ranta kuma ta rik’a roqon Allah kar safwan d’in yaki sakin ta, domin tasan kodan ya kuntatawa talib d’in yaqi yin sakin.

“Kai ka dubeni nan ba wasa neh a gabana ba….” cewar hajiyar a yayin da take fuskantar da kallonta zuwaga safwan d’in.

“Kadaura wa yarinyar nan idda ko kuwa?” Ta tambaye shi in a serious tune.

Shiru yayi yana nazarin maganar, hak’ik’a wannan wata dama ce dazai yada kwallon mangoro ya huta da k’uda, diba da yanda ya tsani yarinyar kuma dama yake neman hanyar da zai rabu da ita tuntuni batareda hajiyar taga laifin shi ba.

“This is an opportunity which comes but once!” wani sashe na zuciyar shi ya kitsa mashi.

A yayin da wani sashen kuma ya tuna mashi dacewar kenan taleeb yayi nasara a kanka? That means he is now the winner? Da sauri ya dakatar da tunanin, lokaci guda batare da yasake barin wata baraka ta shiga tsakanin shi da tunanin nasa ba yace….

“Yes na daura mata idda idda,in short jikina na bani akwai cikina ma zaune a mahifarta daga daren na jiya.” 10

Ya ida zancen yana mai sakin murmushin mugunta , lokaci guda kuma yana kallon yanda fuskar talib d’in ta jirkice zuwa zallar bak’in ciki da kishi mabayyani. 1

Tafin da inna keh ta rafkawa neh yamaido da kallon shi safwan d’in daga sashen na talib zuwaga innar, batare da yasani ba yaji dariya nason kufce mashi sakamakon jin abinda kakar tashi keh fad’i.

“Da kyau yaron kirki, da kyau, haka nake sonji d’an albarka.” ta ida zancen tana mai kyalkyala dariyar jin dad’i.Gaba d’aya falon kallon ta suke, kowanne da yanayin abinda kallon nashi ke nufi. +

Ganin dukkansu sun Sanyo mata na mujiya neh yasanyata dakatawa da yin tafin, kana lokaci guda kuma ta had’a rai alamun bafa wasa take ba yanzu. 1

“Toh madallah, tunda dai yanzu angane cewa yaran nan sun riga da sun zama abu guda sai kowa yaja please ya rungumi sorry abama yaro matar shi su k’ara gaba, ko kuwa?” 2

Ta waiga tana kallon hajiyar da tayi shiru kawai tana binta da idanu.

“Kika tsareni da ido ina magana saratu, halan yau na canza maki kamanni neh?” Innar ta fad’a tana mai hararar hajiyan 1

Da sauri hajiyan ta girgiza kai gami da cewa “Ai shikenan tunda abin yazama haka, keh ramla tashi kibi mijinki kutafi.” 6

Tun kafin ta rufe baki, ramlan tasake tsanyara ihu gamida zubewa kasa tana mai riko kafafun na hajiya akan lallai lallai ita batason safwan bazata bishi ba.

Ganin da gaske dai ramlan take yasanya ta kallon safwan din tace mishi yaje kawai, daga baya za’a maido ta.

Hakanan ya tsinci kanshi da son kin amince wa zancen na hajiyar tasu, hak’ik’a baya da tabbacin zai iya katabus idan har yatafi yabar yarinyar nan a gidan nan, lokaci guda kuma wannan d’an feleken yayan nata na gari, inaa bama zai yiwu bane. 1

Yana shirin bude baki yayi magana neh wayanshi ya dauki kiran neman agaji, fasa maganar da zaiyi yayi ya dauki wayan sakamakon ganin mai kiran wayar.

“Bilal Tofa neh”

“Hello man, safwan mainasara on the line.” ya furta kamar ko wanne lokaci.

Shiru neh ya d’an biyo baya, alamun yana sauraren d’ayan bangaren.

“Yes just come in.” Daga haka bai kuma cewa komi ba ya datse kiran.

Da sauri ya waiga gurin hajiyar da niyyar shawo kanta.

“Yawwa hajiya, as i was saying… Gaskia nikam bazan iya barin matata a cikin gidan nan ba, ko wanne qaton banza idan ya shigo ya rik’a kalle mani mata, i can’t tolerate that, coz wallahil azim za’a iya samun matsala dani.” 2

Galala sukai da baki suna kare mashi kallo, qmmq banda taleeb a cikin ayarin ‘yan kallon, domin kuwa gaba d’aya tunanin shi yagama karkata ga irin hukunci daya kamata ya yanke bisa mutumin nan, ba shakka duk wanda yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake.

Inna ce ta cafe gamida cewa “Da gaskiyar ka yaron kirki, aini kaina na kan rasa wannan shegiyar gaddama irin ta saratu, ayi mata sam baki san zuru ba.” Tai kwafa cike da jin haushin hajiyar a ranta, a ganinta tsabar rashin sanin ciwon kaine yasa take neman raba auren jikallen ta duk sabida wani can daban. 1

” Haba inna wai ya kuke magana hakane, kamar baku san abinda keh faruwa ba? Kuma ma sabida Allah bafa wani abu naceba, cewa nayi yatafi gobe nasanya a maida mashi ita,meyene abin jin haushi anan.?”

Itama hajiyar taba innar amsa cike da gajiya da halin son kai irin na inna, ita indai abinda ya shafi jikanta neh toh kuwa kiri da muzu zata take gaskia babu abinda ya shalleta da wata jin kunya.

“Kedai kika sani, nidai abinda nasani yarinya ta tashi tabi mijin ta kawai…. Yoo inama amfani, haka kurum kijanyo mana kwasar zunubai? Halan bakida masaniyar cewa yanzufa aljannar ta tana k’alk’ashin k’afar yaron kirki neh? Toh nidai babu ruwana, Allah ma yasani wallahi.”Ta ida zancen da zallar gaskiyar ta.

Mamaki neh yakusa kashe hajiya a zaune, kai ba ita kad’ai ba hatta jikan nata jinjina kalar wulakanci irin na kakar tashi yake… Wai yau innah ce keh wa’azin aljannar mata na qafar mijin ta! Oh oh inna manyan gari. 2

Bata damu da irin kallon da taleeb d’in keh binta dashi ba, wanda tun dazu yayi shiru kurum yana binsu da idanu, yau yake ganin son kai kiri kiri da rana tsaka. Girgiza kanshi yayi cike da neman hukuncin daya kamaci duk wani mai bak’in fentin daya nemi yakawo mashi cikas. 1

“Hak’ik’a da sannu zasu san ko shi waye.”

“Keh dan jakar ubanki tashi kibi mjinki, yau ga shegiyar mata.” Innar ta buga mata tsaw harda k’ok’arin kai mata gabza.

Da sauri ta tashi da niyyar rugawa waje, domin kuwa Allah ma yasani bazata tab’a komawa wannan otel d’in ba da sunan gidan miji.

Garaaam kakeji sunkai wa juna karo,yayin data ke sanya kai domin fita, shikuma yake sanyo kai falon domin shigowa, da sauri ya rikota ganin tana shirin kaiwa k’as, wanda hakan ya taimaka wajen baiwa hudojin hancin ta damar shak’o daddad’an turaren nan dai da bazai tab’a mantuwa ba cikin jerin shafukan rayuwar ta. 1

Da hanzarinta ta d’ago kai tana mamakin miya fitar da taleeb waje, in fact inba rudewa tayi ba, ita tasan ya taleeb na zaune a cikin falo inda ta baro shi. 2

Karaf suka had’a ido, bakin shi dauke da murmushin gefen labb’a.

“Bilal Tofa neh.”

Ko kafin tagama watsatsakewa daga rudewar wucin gadin data shiga har safwan yak’araso inda suke, lokaci guda yasanya hannuwan shi ya janye matar shi daga rikon da aminin shi yai mata. 1

“Aboki sorry fa, kasan yarinyar ba nutsuwa neh da ita ba,i hope karon bai janyo maka headache ba?” 1

Murmushin dai bilal d’in yasakeyi gamida cewa, “Haba d’an wannan minor abin, babu komi fa… Ina take shirin zuwa neh haka take irin wannan gudun?” 1

Bilal din ya tambaya yayin da suke karasawa cikin falon.

“Kasan idan akace maka mutum psycho neh.” Cewar safwan d’in a takaice. 4

Gaba daya ma ita ramlan bawai jinsu take ba, dandagaryar tunaninta tuni ta wulla da ita wani sashe na duniyar.

“Shin miya had’a abokin ya safwan Bilal tofa da qamshin turaren nan?kamshin da koda wasa bata tab’a jin wani mahaluki na cikin gidan nan da irin shi ba.”

Kwakwalwarta taciga da tseren gudu cikin kwanyar kanta, ba shakka cike take da rudu da shakku bisa wannan lamarin dake tunkaro ta.

Abinda tasani shine, koh mutuwa tayi ta dawo, babu yanda za ai ma ta dangana abinda yafaru da ita ga bilal tofa, domin kuwa zata iya cewa wannan shine kusan zuwan shi na hud’u cikin gidan nan, duk kuwa da irin amintar shi da safwan.
Asalima, mutum neh wanda ba mazaunin garin kaduna ba,asalin mutumin kano neh, can yake aikin shi dakuma sauran wasu al’amura na rayuwar shi. +

Banda ma haka,Ko giyar wake tasha bazata tab’a danganta ta’addanci irin wannan ga kamilalle kuma nutsatsen mutum irin bilal tofa ba,Ina hankali ma bazai dauka ba! 1

“Toh ko dai turaren neh yazo iri daya? ” tasami kanta da kara tambayar kanta a karo na biyu, domin kuwa take yanke ranta ya amince mata da cewar turaren neh yazo iri d’aya kamar yanda yazo iri d’aya dana yaa taleeb d’in ta

“Me matar mu keh tunani neh haka, da har batajin gaisuwata a gareta?” cewar bilal bayan yagama gaisawa da kowa dake falon.

Firgigit ta dawo hayyacinta, tana mai zare idanu, kai kace sarki taiwa karya.

Murmushin yak’e ta hau yi, duk don kar a fahimci rudewarta.

“Au sorry yaa bilal, wallahi banjika bane, ina yini?” 1

“Lafiya kalau amaryar mu, dafatan kina cikin koshin lafiya”? Ya bata amsa yaa mai sake sanya idanuwan shi cikin nata.

Sunkuyar dakai tayi kasa tana d’an murmushi, kana a hankali tace “Eh”.

Ba shakka bilal tofa ba tun yau ba yake mata matuk’ar kwarjini a idanuwanta, he has that effect almost akan kowa.

A kaikaice taleeb keh k’ara bin bilal d’in da kallo, zuciya da gangar jikin sa naso ta tuno masa inda yasan fuskar nan, amma sam hakan ya faskaru,duk da hakan bai gushe ba ya cigaba da binshi da kallo a kaikaice batare da sanin kowa ba dake falon. 1

“Ba shakka the guy looks familiar.” ya ambaci hakan a ranshi.

Ganin bilal dinne yasanya inna k’ara tsugewa da labari, domin k’warai da gaske takeyin jika da kakar da bilal d’in, domin kuwa acewar ta nagartaccen yaro irin bilal tofa abin so da k’auna neh.

Gaba d’aya sungama kular da taleeb d’in, hakan ya sanya yamike da niyyar barin gidan, dagaske yana bukatar sassauci bisa kuncin da mutanen nan suka aza mashi. 1

Mikewar shi yayi daidai da mikewar ramlan itama daga jikin safwan din zumbur, lokaci guda kuma idanunta suka sakeyin raurau alamun son fashewa da kuka.

Bai bari yak’ara kallon sashen ramlan ba, domin kuwa idan ya cigaba da kallon nata za’a iya samun gurguwar matsala dashi, hakan yasa yaiwa hajiya wacce tundazu hankalinta ma baya tare dasu ta lulak’a duniyar tunani.

Da yak’en ta bisa labbanta take amsawa taleeb d’in sallamar da yake yi mata, lokaci guda kuma cikin hikima ta rik’a bashi hak’uri bisa rashin adalcin da akai mashi.

Hannu ya. Mik’a wa su safwan d’in, wanda yin hakan ba karamin tattaro dukkan courage din sa yayiba yayin afkuwar hakan.

Ganin dagaske yayi hanyar ficewa batareda yako k’ara had’a ido da ita bane yasanyata sulalewa kasa tana gunshekar kuka, lokaci guda kuma tana kwala kiran sunan shi da dukkan iyawar ta.

Runtse idanuwan shi yayi, yana mai jin tamkar ya aikata wani babban zunubi neh zuwaga masoyiya kuma kuma mafi soyuwar kanwar ta shi.

A zuciyar shi yake bata hak’uri gamida yimata alk’awarin shi d’in nata neh, domin kuwa an halicce sa neh sabida ita kad’ai, ba shakka da sannu mai guri zaizo, mai tabarma kuwa zai sami damar nad’e yar guntuwar tabarmar shi ya k’ara gaba.

Da wannan tunanin ya karasa cikin Lamborghini din shi dake girke a inuwa tana jiran shi, batare kuma daya k’ara bari wani abu ya gifta tunanin shi ba yaiwa motar giya, lokaci guda kuma SAMEERAH na fad’owa a ranshi! Ba shakka akwai bukatar ya tunkari samira din a yanzun nan.!

“Shin garin yaya tayi failing dinshi? Upon all the promises

Zuciyar shi tacigaba da azalzalar shi domin ganin ya cimma inda yafi tunanin zai samu sameeran.

***
” Kigama birgimarki kuma ki tashi kibi mijin ki ba, ita tsohuwar soayyar taci uwata.” cewar inna kenan dake kallon yanda ramlan keh rafza kukan tafiyar taleeb d’in.

Haushi yagama cika hajiya, wanda maganar ma nema take ta gagareta, gaba d’aya al’amarin yaran nan nema yake ya shallake tunanin ta, haba daga wannan sai wancan. Kai tashi kutafi, kar insake ganin kafafuwanku a gidan nan nan kusa, kana jina koh?” +

Daga mata kai yai gamida cewa”Your wish is my command maa!” Ya amsata da murmushi samun nasara a fuskar shi.

” Wallahi mammy ni bazan koma wannan hotel d’in ba, sai dai in gawata za a kai mashi.” ta ida zancen tana gumshek’an kuka.

Da sauri yace “Don’t worry dama daga yau na yanke hukuncin gama zaman hotel d’in nima, from here gidanmu zamu wuce.”

Kai daga jin yanda yake bata amsa kasan akwai kamshin mugunta a maganar tashi.

“Dakyau yaron kirki, Allah dai yai maka albarka.” Inna ta cafe.

Janyota hajiyan tayi ta hau lallashin ta da dukkan iyawarta, wanda dakyar da jibin goshi ramlan ta yadda zata bishi, amma duk da hakan da wani burin cikin zuciyar ta.

Ganin tayi nasarar shawo kan ramlan neh yasanyata cigaba dayiwa ramlan nasihihi tareda sanya mata albarka, domin ita kanta harga Allah jikinta na bata ramlan ce sanadin shiryiwar yaron nata in Allah ya yarda.

Baki zumbure a gaba ta mike tabi bayan su safwan d’in dasuka rigata ficewa sakamakon sirri da hajiyar ta bukaci yi da diyar tata.

Ko kallon innar batayi ba, bare tasa ran zatai mata sallama, domin kuwa gaba daya haushin innar neh keh mamayar ta, hakan yasa ta gallara mata harara ta fice tana kunkuni.

“Inkin gadama ki had’i yi zuciya ki mace karewar jin haushi,aure neh dai daram dakau keda yaron kirki, duk bakin cikin ki sai kin haife mana wannan cikin da jikana ya kunsa maki, ‘yar banza lange lange mai ramar k’eta.” 8

Tai gaba tana cigaba da mita,ai ita dai burinta yacika saratu bata samu nasarar raba jikanta da matar shi ba.. Ko banza d’an koli yaci riba. 3

Kallon bayanta hajiyar taciga dayi har ta b’ille hanyar dakinta, hakan yasa hajiyar ta sauke ajiyar zuciya gamida k’ara godwaAllah bisa irin surukar daya bata.

“Allah abin godiya!”

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]