[Advertisements⬇️]

SAWUN BARAWO CHAPTER 9 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SAWUN BARAWO


CHAPTER 9


Ikon Allah sai kallo! ” cewar innah. +

Kana ta rik’e hab’a a yayin da suke bin safwan dake kwance kashirb’an bisa gado da kallo, wanda duba daya zaka mashi ka fahimci dimbin damuwa da tashin hankalin da sukai wa ilahirin rayuwar sa qawanya, mussamamn idan ka diba fuskar shi, babu abin da ya sauya na daga yanayin da ya fada a iya kwanakin da ya dauka a hukumar ta yan sanda. Fuskar nan cunkushe take da damuwa, wanda hakan ya janyo ko burbushin murmushi da fara’ah babu a fuskar tashi, hakan ya faru ne tun bayan artabun da suka buga shi da kabeer din, a inda kabeer din yayi nasarar tserewa ta hanyar rirrike safwan din da akayi ganin yana shirin aika dan uwan nashi barzahu.

Yau kusan kwana biyar kenan da afkuwar lamarin, wand daga ranar da Kabeer din ya samu ya kufce bai kuma gigin kallo gidan nasu ba, dukkuwa da irin kiran d hajiyar tasu ta rika mashi akan yazo ayi maganar fahimta, amma gogan naku yai biris yace baesan zance ba, domin kuwa ya riga d ya rantse da mahaliccin sa babu wand ya isa ya kwace masa Ramlan sa. 1

“Please Safwan, ni a ganina duk wannan tashin hankalin da kake kokarin sanya kanka ba shi bane mafita, just buckle up and be a man, daga nan sai musan abin yi.”

Irin kallon da ya watsa wa bilal dinne zai tabbatar maka da cewar zancen na abokin nasa bai shige shi ba.

“Please let me be, ta yaya kake tunanin zan fara kwantar da hankali na whilst i don’t know the whereabouts of my wife, for gods sake fa bilal.” 1

“Still hakuri zakayi, i believe sannu a hankali zamu shawo kan lamarin, yanzu abinda nake so dakai ka daure muje ko gyaran fuska ne ayi maka mana, kana kallon kanka a madubi kuwa?”

Tsaki yaja, gami da sake mirgina kanshi gefe, ba shakka shi karan kanshi sumar dake fuskar tashi ba karamin takura masa take ba, amma tashin hankalin da Kabeer ya sanya shi yasa baima lura da hakan.

Kakus dake kan gadon tun dazun tana jin hirar ta su ta tsomo baki a karo na biyu.

“Daure d’an albarka kaje a rage sumar nan ta fuskar ka, ni kaina tsoro kake bani inna kalle ka wallahi.” 1

Janye kanshi yayi dake bisa cinyar innar gami da hanzarin mikewa zaune, ido a zare yace

“Wai dagaske kike sweetheart? Shine baki gaya mani ba tuntuni? Ai da tuni naje nayi askin.”

Dariya Bilal yayi ganin yanda kakus din tayi kalar tausayi, ita a dole a tausaya mata a je ayi aski.

“Aboki bari in watsa ruwa ka rakani in gyaro fuskar nan tau, inama amfani in rika baiwa sweetheart dita tsoro, ya ida zancen yayin d ayake nufar hanyar bathroom din dake dakin.

Tuni kuwa innar ta wangale baki gami da fara rattabo mashi kirarin jin dadi.

“Da kyau yaron kirki, namijin duniya an buga dakai anbarka,angon Rablatu ko anki ko an so, Allah yaci uban makiyan ka mu zauna lafiya.” 9

Fadar irin dariyar da bilal yake ma b’ata baki ne, sosai alamarin na kakus zai baka dariya, domin kuwa bilhakki da gaskia ta bud’e mak’oshi ta rik’a kwararo zantuttuka kan jikallen nata. 1

***
“Ko kai fa, just look at you, har ka dawo Safwan dinnka, amma da ka ganka kuwa?dodo kake ji alaji”

Cewar Bilal yayin da suke shiga mota bayan fitowar su daga barbing shop din da akayi wa Safwan din aski da gyaran fuska.

Dariya Safwan din ya danyi, yayin da yake sake lek’a fuskar shi ta side front mirror dake cikin motar, wanda shi kanshi kwarai ya samu relief daga wasu bangare na sassan jikin nasa, bangare mafi rauni da tagayyara a yanzun shine zuciyar sa, a hakikanin gaskia zuciyar sa tana nema ta gaza daga hakurin da hajiyar ta su ta bashi akan cewa su sarara suga iya gudun ruwan Kabeer din, tunda dai yanzu da sauki sauki tunda ansan wajen wa take, matsalar kawai yanzu asan ta inda zaa shawo kan shi ya maido ta.

Bilal dake tuki ne ya juyo ganin yanda yanayin fuskar aminin nashi ta sauya, duk da dai dama ba wai fara’ar ce yakw yi ba tun dama can, amma dai da d’an sassauci a lokutan bayan da suka fito gida, sanin me ya canza mood din abokin nasa yasa bai mayi dogon bincike ba yace,

“Ina rokon ka da kadena sanya kanka cikin damuwa Safwan, by Allah’s grace i promise you komi yakusa zuzuwa k’arshe, let us just keep praying biko.” +

“Bilal ba zaka gane bane, abubuwa da dama na bani mamaki ne, i mean how could someonebe this wicked?sabida Allah fa? A tarihin rayuwar ka, a ina ka tabajin kwamacala irin wannan? Forget about him being jealous of me,why would he interfere my wife a cikin alamarin nan Bilal?

Shiru bilal din yayi kamar mai nazari, zuwa can ya gyada kanshi gami da cewa,

“It’s like kana manta main reason din Kabeer akan aikata abinda ya aikata ba Safwan, duk da cewa Kabeer bai furta dalilin d yasa ya aikata abubuwan da ya aikata ba din ba, yakamata ace common sense dinka ya sanar da kai dalilin yin hakan, all he did, he did them intentionally on purpose, inma dai to destroy you, tarnish your image, ko kuma to reach some of his aims that ain’t pure towards you, misali the rapping issue, why did he used your face in doing that? Yayi hakan ne to destroy you, the kidnapping issue kuma fa? He also did that to destroy you too, sai dai kuma me? Bai san hakan da yayi ba ya taimaka wajen kafuwar sabon mutum ba, baisan hakan da yayi ba ya taimaka wajen canzuwar wasu munanan dabi’u naka ba, bai san hakan da yayi ba ya taimaka kwarai wajen fahimtar da kai irin rayuwar da kake yi ba, infact bai san sharrin sa a gare ka ba wata sahihiyar hanya bace ta kasantuwar ka cikin mutanen kwarai a yanzun ba, madallah da wannan mummunan nufi da ya samu ikon juyewa zuwa alkhairi cikin rayuwar ka Safwan!Godiya ta tabbata ga Allah mai sauya fari ya koma bak’i, ko kuma mummuna ya koma kyakkyawa! Ba shakka Allah mai girma ne da rahamomi masu tarin yawa!” 1

Sauke numfashi Safwan din yayi, a yayin da yagama jin zantuttukan dake fita daga aminin kwarai irin Bilal, ba shakka sai yanzu yake kara fahimtar inda zantuttukan na bilal din suke dosa, wanda hakika ba shakka dukkan abin da ya fada din gaskiya ne, Kabeer Mainasara ya kasance azzalumin da yayi nasarar canzuwar shi daga mutumin da yake a da, zuwa abinda yake a yau! Ba shakka shi din ya kasance baki mai halshe biyu, domin kuwa b’atancin sa a gareshi ya taka muhimmiyar rawa cikin tarihin rayuwar sa, ashe ko ba komi dole ne ya kara godewa Allah bisa jarabawar sa a gareshi, sannan ya fahimci lallai ubangiji mai girma da daukaka ne, sannan mai shiryar da bayin sa a lokacin da ya so, da kuma yanda ya so! Allah abin godiya!

“Alhamdulillah!” Suka furta a tare, a yayin da kuma suke k’ara jinjina girma da ikon Ubangiji cikin kasan zuciyoyin su.

Wata mota kirar Mercedes fara k’al ce tai overtaking din su, wanda har hakannyasa kiris ya rage mai motar ya gogi ta su.

“For Gods sake kaga wani irin banzan driving da fella din can keyi, atleast yakamata yasan wannan titin cikin gari ne ba na high way ba da zai ke zuba rough drive ba anyhow.”

Cewar Safwan yayin da yake sakin tsaki, lokaci guda kuma ya maida hankalin sa bisa hoton Ramlah dake bisa screen din wayan shi, sosai yake shagala idan yana kallon fuskar ta ta da ke matukar sanya shi jin inama zai iya maida hannun agogo baya, da babu shakka sai ya kashe ta da kalar soyayyar da ba’a taba yi ma wani mahaluki irin ta ba.Jin Bilal din ya kara speed din motar da karfin gaske ya sanya shi dago kai domin jin ba’asi, domin a iya sanin shi, babu abin da Bilal din yaki jini sama da tseren gudu bisa titi yayin tuk’i, amma ko kafin yakai ga bude baki domin tambayar shi ba’asi har shi din ya bashi amsa.

“Kabeer Mainasara ne cikin motar can, o spotted him a owners seat.”

“What? Kabeer fa kace? Oya park the damn car and lemme drive.”

“Calm down, mubi su a hankali muga inda sukayi.”

Dafe kanshi Safwan din yayi cikin halin tashin hankali yace…. “Noooo, i said just park the damn car and give me the keys Bilal,i won’t forgive myself in Kabeer ya b’ace wa ganin mu.”

“He won’t i promise, just keep calm muga inda zasu shiga, please.”

Runtse idanuwan shi yayi ba tare da yabaiwa Bilal din amsa ba, ba shakka Kabeer Mainasara ya zalunce shi iya zalunci, don me zai rike mashi mata? Don mi zai so abinda yafi so kaf rayuwar shi? Don me zai ke wahlar da zuciyar shi har haka? Shin bashi da tausayi ne dama har haka? Ko kuwa shi dinne bai taba lura da hakan ba?

Bude idanuwan shi kurum yayi ya tsince su a international airport din kaduna, ba tare da bata lokaci ba Bilal din ya sami wani guri mai dan sirri yayi parking,hakan yasa suka fito daga motar sanye da Calvin Klien hoodies din su d dama tana kawunan su, sai dai yanzu sun janyo hular sosai ta rufe masu goshin su zuwa fuskokin su.

Direct cikin airport reception din suka nufa, ganin nan su kabeer din suma suka bi,yanayin yanda suke sauri zai tabbatar maka da cewa akwai me shirin boarding flight din cikin su, bayan sunyi dukkan abinda yakamata na dangane da visa din su ne suka dawo cikin reception din suna tattauna wasu maganganu a tsakanin su.

Kabeer dinne ya mika wa abokin nashi hannu sukai musabaha yayin da abokin keh juyawa domin ficewa daga cikin reception din, hakan yasa Bilal saurin canza hanya ya bishi, sanin cewar abokin bai san shi ba.

Da sauri ya cimma abokin yayin da yake bude motar domin shigewa.

“Ammm assalamu alaikum, afuwan please for the interruption brother,don Allah ina da tambaya neh, i hope ba matsala?”

Da dan murmushi a fuskar abokin yace, “No its okay Allah yasa na sani.”

Shima murmushin ya jefa masa kana yace “Don Allah wane domestic flight ne zai tashi yanzu, nayi misplacing ticket di na neh.” 1

“Eh to gaskia i can’t say, amma dai abinda na sani shine, flight din lagos zai tashi nan da mintuna ashirin zuwa talatin haka, coz nima i just dropped a friend zai tafi lagos din.”

“Oh okay toh nagode fa,amma can i get another ticket yanzu nima? Coz nima lagos din zanje.”

Jim abokin ya danyi kana yace…. “Well gaskia i can’t say ko zaka iya samu, sabida shi kanshi abokin nawa da nai dropping yanzu alfarma ne muka nema, because shima asalin ticket din nashi ba na yau bane, urgent abu ne ya taso mashi zaije yai settling din shi.”

Da sauri Bilal din yai fuskar tausayi gami d cewa,

“Ayyah i hope lafiya dai, coz nima urgent issue ne yataso mani nake son zuwa lag din a yanzu.”

“Eh toh shima dai iyalin sa ce zaije ya duba,batajin dadi neh… Amma dai kashiga ciki ka bincika may be kasamu ticket din.”

“Okay nagode sosai fa, sai anjima.”

“You welcome, toh sai anjima.”

Suka sake musabaha, Bilal din ya juya da sauri yayin da kirjin sa ke tsallen doki bisa kirjin sa.

Ba shakka ko tantama ba yayi Ramlah ce wacce Kabeer din zaije gani, domin a iya sanin su matar Kabeer din bata ma kasar, tana can kasar Jordan tana hado masters din ta, kenan Ramlah ce iyalin da zai je dubawa? Hakan na nufin can yake boyon ta kenan? 2

Dam gaban shi ya fadi, yayin daya tuno hannun mutumin da ya hango a cikin jirgi yana kallon hoton ramlah, a satin baya da yaje lagos, wand kuma a ranar ya hadu da Rukayyah Sadauki, har tayi nasarar dauke hankalin sa daga son sanin ainihin waye ne.

Ba shakka Kabeer Mainasara neh. 2

***
Ba lallai bane inkai mata kallo daya ka gane ta ba, mussaman in ba ta bude baki tai magana ba, dalili kuwa na irin tsabaragen ramar da tayi akan ta da,sosai kamanin nata suka canza, tsantsar damuwa, tashin hankali sune shimfide bisa kyakkyawar fuskar ta. +

Kimanin kwanaki akalla takwas kenan, tun bayan tafiyar da Kabeeer din yayi ya barta a halin kunci kenan, duk kuwa da cewar babu abubuwan jin dadin rayuwar da sukai karanci a gidan, amma tsananin mamaki da fargaba aun hanata katab’us a cikin gidan da ta kira da kurkuku.

Ba sau daya ba sau biyu ba tai yunkurin guduwa daga gidan, amma daidai d sakan guda bata taba samun nasara ba, domin kuwa gida neh mai kunshe da security locks ta ko ina, rashin samun nasarar guduwar kan sanya ta zaman dirshan ta dirji kukan ta babu mai lallashi, hakan ya taimaka wajen sanya kunci d bakin cikin rayuwa yi mata sallama.

Kamar kullum, tana makure a wani corridor da zai sadaka da dakunan baccin gidan, kwance take tana numfarfashi, mussaman na irin yunwar dake nukurkusar cikin ta, amma tsabar sarewa da rayuwar duniyar ya sanya ta yin alkawarin sai da ta mutu amma tagama cin abincin gidan, mussaman yanzu da babu abinda tafi muradi sama da mutuwar.

Tunda ya shigo main palour din gidan yake kiran sunanta a hankali kamar mai tsoron wani abu, hakan yasa sam bataji motsin shigowar ta shi ba, ballantana kuma sunanta da yake ta kira cikin rad’a, hakan yasa ya durfafi hanyar dakin da yafi tunanin zai same ta,tana kallon shi yazo ya wuce ta ba tare da shir din ya lura ba, ganin bai sameta ba anan yasa ya nufi dayan dakin wanda dama shine nasa, amma can ma bai gantaba,nan kuma sai hankalin sa yafara tashi, duk kuwa da yasan cewa ko da uban wa take yawo bata isa ta gudu daga gidan nan ba.

Zuwa yanzu ya daga muryarshi sosai wajen kiran sunan nata, wanda sosai zaka fahimci tashin hankalin d yake ciki ta sautin muryar shi, tana kallon shi yana ta faman safa da marwa gurin neman nata, amma da yake bayan wani deep freezer kato take makure hakan yasa bai samu ikon ganin ta ba.

Can kuma sai gashi ya nufo inda freezern ke girke, hakan yasa ya hango lebatun hijabin ta ya leko, da sauri ya karasa ta gurin domin tabbatar wa idon sa.

“Sugar! ” Ya ambaci sunan nata cikin wani irin shauki, domin kuwa sosai yai kalar tausayi, sannan shima din a kallon farko zaka fahimci er ramar da yayi, duk kuwa da cewar dama ba kaurin ne daashi ba shima. 9

Dauke kanta tayi, gami da cigaba da kallon dyan sashen da bata ganin sa, yayin da sabon haushi da tsanar shi ke sake ninkuwa cikin zuciyar ta, ba shakka da tana da ikon ganin bayan wannan matsiyacin, da tuni an dade da shallake wajenstyle

Giuwa kasa ya zube a gaban ta gami da sanya hannayen sa ya tallabo hab’ar ta domin ta fuskantoshi, bakin cikin abin yasa ma ta kasa magana, ko yin masifa kamar yanda ta saba in yana taba ta.

Zuru yayi mata da idanuwa kamar tsohon maye, sosai yakejin bacin rai a kirjin sa, mussaman ganin irin ramar da tayi fiye da yand yatafi ya barta, wanda ko rantsuwa yayi bazai yi kaffara ba shine SILA! Amma shi a ganin shi, sai yaushe ne Ramlan zata fahimci cewar shi dinnan, shi kadai ne ya dace da ita, kuma an halitta ta ne mussaman domin sa?

“Sugar miya sameki haka? Kina kallon madubi kuwa?” 1

Galala da baki tayi tana kallon shi cikin mamakin zantukan banzan dake fita daga bakin shi, a duniya kuwa zaa samu tantirin shege sama da Kabeer Mainasara kuwa? Ta tambayi kan ta. 1

“Uhm Sugar talk to me please, kinga yanda kika rame kuwa? Are you sure kina cin abinci? I hope ba zama da yunwa kike ba?”

“Mtswwww.” Taja wani mugun tsaki gami da fizge fuskarta daga hannun shi.

Sake matsar ta yayi,wannan karon har tana iya jiyo numfashin sa, wanda takaicin hakan da rashin sanin abinyi yasa ta fashe da wani irin kukan, sosai ta bude makoshi ta rika sheka kukan ta, domin kuwa harda majina, amma gogan naku sai kawai ya wawurota jikin sa wai yana lallashi, a inda al’amarin ya taimaka wajen kara sautin kukan nata, wand har bata san lokacin da ta hankade shi ba gami da cewa
“Kai wa girman Allah Ya Kabeer ka rabu da ni hakanan, wannan wace iriyar rayuwa ce saboda Allah?”

“Nima ki taimake ni ki daina kukan nan Sugar, kukan ki na k’ona mani k’irji.”

Ya janyo hannyen ta gamida daura su bisa kirjin sa, lokaci guda yana mai sake sanya idanuwan sa cikin nata dake bin shi da kallon Allah wadaran naka ya lalace. 1

“Feel my heart beat Sugar,kinji yanda zuciyata ke bugawa da kaunar ki a kowanne sakan na rayuwata? Kin gane cewa zuwa yanzu bazan iya rayuwa babu ke ba?” 1

“Saboda Allah kan mantawa da cewar ni matar kaninka ce? Kana tsoron Allah kuwa Ya Kabeer?style

Dariya yayi wacce tafi kuka ciwo, sosai yake jin bacin rai idan yatuna igiyoyiin auren Safwan din na rataye bisa wuyar abar kaunar ta shi, amma wannna ba matsala bane, tunda ya riga da ya gama yanke hukuncin yanda zeyi Safwan din ya sakar mashi matar shi cikin ruwan sanyi.

“Forget about him Sugar, ni ne nan nake sonki ba shi ba, you knew everything Sugar,Safwan bai taba sonki ba, ko kin manta ne intuna maki? How he used to bully you, the hate, the everything? Ki manta da shi ki rungume ni, nine mai sonki fisabilillah Sugar.”

Shiru tayi tana kallon shi, yayin da maganganun nasa ke yawo a kwanyar ta, wnada sosai suke son samun tasiri cikin zuciyar ta, hkane fa, ai bai kamata ta manta da bakin mugu azzalumi irin Safwan ba, ko da cewar ba shi ne yai mata fyade ba, hakan ba zai sa ra mance zallar zaluncin sa a gare ta ba, hakika ba’a taba tsanar ta kwatankwacin yanda shi din yayi ba.

Kallon ta yake yana mai fatan samun nasara a wannan karon, mussaman yanda yaga ta nutsu tana sauraren shi, sannan kuma yaga yanda tai shiru tana tunani.

“Baka taba sona ba Ya Kabeer, domin kuwa duk maj sonka ba zai keta maka rigar mutunci ba, hakanne SO a ganin ka Ya Kabeer? SO ka kira wannan? Kenan baku da maraba da kai da Kanin naka, kusan ma ince gara shi bai taba yunkurin keta man haddi ba, kaifa?”

“I did all that because of your love baby,and at the same time i did that intentionally to get ride of him gaba daya amma hakan bai samu ba,i raped you to destroy Safwan’s image a idanun duniya, mussaman hajiya, nayi hakan ne domin na dasa kiyayyar shi a zuciyar ta, sanin cewar babu abu mafi soyuwa a zuciyar ta sama da Safwan,wanda hakan ba karamin illah ni yai mani ba, amma sai dai kash! Tagayyara shin da na so inyi ta hanyar amfani da fuskar shi wajen yi maki fyade beyi rana ba! Domin kuwa a sanadiyar hakan na rasa ki gaba daya! Wanda a da, na dauka idan safwan din ya dage akan bazai amsheki ba Hajiyan zata hakura, nikuma cikin ruwan sanyi in maye burin hajiyar na son kaasancewarki matar Safwan tun ba yanzu ba, amma unfortunately she didn’t back off, sai da tasan yanda tayi ta hada auren ku ke da Safwan, wanda yin hakan ne ya janyo karasa rugujewar nawa sauran farin cikin, a inda na dau alwashin ko ta halin k’aka ne sai na amso ki, domin kuwa na rantse babu wanda ya isa ya rabani da ke, we were meant for each other Sugar, nasani a yanzu bazaki gane me nake nufi ba, amma zuwa gaba hopefully zaki fahimci komi, zaki gane ni din mai qaunarki ne tamkar raistyle

“Shhhhh say no more Ya Kabeer, zuwa yanzun ma ina tunanin nagane hakan,sannan yanzu dinne ma nakejin shin tun da mi ya hana na fahimci dimbin kaunar ka a gareni? Nasani, kuma ban manta ba Ya Kabeer, a dukkan gidan nan babu wanda ya soni ya kaunace ni sama da kai din nan, sai dai a bisa rashin sani na fassara hakan da soyayyah irin ta yan uwan taka, meyasa ka boye mani kanka for this while Yayaa na? Meyasa ka cutar da kaunar mu?”Zuwa yanzu yafara dena fahimtar komi, sosai duniyar shi ke juyawa cikin wani irin yanayi na shauki, shin mafarki yake ko ido biyu? Ramlan shi ce ke jifan shi da wadannan zantuttukan da a mafarki ne kadai ya tabajin tayi masa irin su? Ashe kenan mafarkin nasa zai zama gaskia kenan? Ya ilahiiii…. Ya sauke wata bahaguwar ajiyar zuciya a yayin da wani murmushin farin ciki ke subuce mashi. 7

“Ki gafarce ni Sugar, i was blindfolded by your love shiyasa, and rashin samun damar isar da sakon soyayyar taki ya taimaka waje aikata dukkan abin da na aikata Sugar, amma n roke ki da ki yafe wa wannan masoyin naki, wanda babu komi cikin zuciyar sa da rayuwar sa face zallar so da kaunar ki Ramlatu Naa… “

Murmushinne itama sakaye a tata fuskar, hakan yasa ta langabe kanta suna karewa juna kallo, shin a duniyar ta mi ya hana ta fahimtar masoyi irin Kabeer din ta? Wace iriyar dodaddaiyar kwakwalwa gareta da har ta kasa gane kaunar shi a gare ta? Ba shakka ta so ta tafka kuskure a rayuwar ta.

Sunkuyar da kanta kasa tayi tana cigaba da murmushi, domin kuwa sosai kunyar Ya Kabeer din ke ratsa ta, lokaci guda soyayyar shi taiwa zuciyar ta kawanya, ashe wasa ma take da take cewa tana son Abu Taleeb, yanzu ne takejin asalin soyayya maras algus na bi lungu da sako na sassan jikin ta, hakan ya janyo taji dukkan damuwar ta ta yaye, ba shakka Love is in the air….style 16

Katse mata tunanin ta yayi ta hanyar dago habar ta, lokaci guda ya sanya idanun sa cikin nata, idanuwan nan dauke zalla da azababbiyar kaunar ta, wacce har cikin kasusuwan ta taji sakon da idanuwan nashi ke baiwa nata, hakan ya janyo har wani sanyi sanyi take ji,a yayin da duniyar ta ke juyawa cike da nishadi mai kafirin dadi.

“Yanzu abu biyu nake so kiyi mani Sugar, don Allah ina rokon ki da ki yafe mani fyaden da nai maki, ki sani i did that because of your love, please do find a place in your heart to for……. “

Zancen sa ne ya katse ganin yanda takai hannun ta guda ta rufe mashi baki a hankli, wanda hakan ya janyo har zaman dab’aro yayi ba tare da sanin sa ba, a yayi da yake jin wata wutar sonta da shaawarta na fizgar shi.

“Ya isa haka Ya Kabeer, ni nan da kake gani na dade da yafe maka, in short ni na ma daina ganin laifin ka, you just collect what is rightfully yours ne, i mean I’m glad it waa you who had my virginity.” 12

Ta karasa maganar yayin da take rufe idanuwan ta cike da kunya, wanda gogan naku ya gama suma a zaune, ba shakka this girl will surely be death of him, salon soyayyar ta daban yake da na sauran yammata, bazai yafewa kan shi dogon lokacin da ya bata ba tare da ya sanar da ita zuciyar shi ba, Kambalasti yana matukar kaunar halittar nan ta zaune a gaban shi. 2

Riko hannuwan ta yayi,tare da cewa “Sugar thank you for understanding me, and for loving me back, wallahi ko yanzu na mutu bani da takaici, ko banza naga tsananin so na a idaniyan ki.”

“Babu godiya tsakanin mu Yayaa na, kamanta mu din abu guda neh? “

Ta ida maganar yayin da take kashe shi da ido daya.

Da sauri ya rika gyada kai kamar k’adangare yana fadin,

“Tabbaas mu din abu guda ne Sugar! I love you beyond words matata.”

Baya bukatar amsar ta, domin idanuwa da gangar jikin ta sun gama shaida mashi amsoshin ta. 8

Madallah da masoyan asali. 5

***
Misalin k’arfe bakwai da rabi Kabeer ne da Ramlan zaune bisa teburin dake adane a gidan domin cin abinci(dinning table), kallo guda zakai wa fuskokin su ka hango zallar kauna da soyyayar dake fita daga fuskokin nasu, zaka fahimci hakan ne daga irin kallon da suke watsa wa juna, duk kuwa da cewa a kunyace Ramlan ke bayyanar da tata kaunar, diba da yanda take ta sussune kai k’asa, lokaci guda kuma murmushi yakasa barin labb’anta.

Sosai zuciyar sa ke k’ara d’okuwa da soyayyar ta, mussaman yanzu da yasamu take tayashi, ma’ana take jin abinda ya dade a rayuwarsa yana ji game da ita, ashe ka so a so ka babban b’igire ne na daga sashin kauna?zuciyarsa me raya masa hakan a duk lokacin da idaniyan shi suka samu nasarar shiga cikin nata.

“Sugar kina so in maki d’ure koh?”

A yangance ta rausayar d kanta tana mai k’ura wa siraran labb’an shi kallo.

“Allah yayaah ni na koshi fa.”

Ta fad’a a dan shagwabe, wanda hakan ba karamin tasiri yayi ba ga wanda akayi domin nasa, don kuwa har cikin k’ashi da b’argon sa al’amarin ya shige sa.

Kokarin sanya idanuwan sa ya sake yi cikin nata, kafin nan yace,

“No kar mui haka dake Sugar,kinsan ba zan yarda mu koma gida dake a haka ba duk kin ramar min d kanki, you have to eat as much as you can domin jikin ki ya dan murmure, ko kuwa mu d’aga tafiyar ne zuwa next week?” 1

Da sauri ta soma girgiza kai, lokaci guda ta dauki cokalin dake aje bisa plate din dafadukar cous-cous din d ta shirya masu a daren ta hau kaiwa baki,

“Allah yaya zanci, ka gani ma? Yanzu zan cinye duka na plate din nan, daga nan ma har in k’ara da naka. “

Dariya ta subuce mashi ganin yanda take ta kai loma cikin dan karamin makoshin nata, hkan ya tabbatar mashi da cewar Sugar din tasa a shirye take domin faranta mashi. 1

“Dakyau My love, yi maza ki cinye mu fita shopping, ko bazakiyi wa su Hajiya tsaraba ba?” 4

Washe baki tayi, amma kuma kafin kace me ne ta kuma yatsina fuska gami da zumburo baki gaba,

“Kaima kasan dole ne inyi wa Mammy da Nabila tsaraba, har ma da kakus ba don halinta ba, amma kuma zan iya hana duk wanda zai kawo mana cikas cikin soyayyar mu tsaraban.” 4

Kallon ta yake cike da birgewa, yayin da yakejin zuciyar sa wasai, ba shakka shi din mai sa’a ne, Ramlah ce da kanta take ikirarin batawa da dukkan wani kalubale da ka iya yi masu karan tsaye cikin k’aunar su? Tunanin hakan ya saka shi kasa dena zabga murmushi, wanda hakan yasa itama ta cigaba da aika mashi da sakon nata kallon da murmushi. 1

“Nagode da zallar kaunarki a gareni Sugar, baki bazai iya furta maki irin farin cikin da kika sanya zuciya ta ba, fatana ki rik’e alkawari Sugar!kece burina, rayuwata da dukkan kaina, na rok’eki da ki rik’e mani amanar kanki don Allah!”

Da sauri ta katse shi ta hanyar girgiza kai, yayin da take sake narka idanun ta cikin nasa,

“Na hadaka da Allah Yayaa ka daina doubting kauna ta a gare ka, duk sa nasan abin yazo maka a bazata, amma inaso kagane cewa hkan nufin Allah ne, dukkan tsawon lokacin d kake kokarin fahimtar da ni soyayyarka a gareni ban dauka ba, amma ka duba k gani yanzu cikin ikon Allah komi ya canza,ina mai tabbatar maka da cewa wallahi Yayaa ban taba son wani a zuciyata ba kwatankwacin yanda nake sonka a yanzu, inajinka a raina tamkar wani maganad’isu dake fizgar zuciyata Yayaah, kaine zabina, kaine kuma burin zuciyata, a yau, gobe, jibi, da har gaban abada!domin zuciya da gangar jikina sun gama aminta da cewa ni din an halicceni neh domin kai, kai kadai, ka agaza wa zuciyata ka cire dukkan wani shakku akan soyayyar mu Yayaah.”Ta ida maganar yayin da hawaye ke sulmiyo wa daga kwarmin idaniyanta. 1

Gaba daya ta gama kashe masaa jiki, zantuttukan ta sun sake samun matsugunni cikin zuciyar shi, yayin da yarda, da amincewa suka gama yin nake bake cikin gurbin zuciyar sa, hakan yasa ya rika hango wani yanayi mai wuyar fassarawa dangane da abar son ta shi. 3

Mikewa tsaye yayi ba tare da yace mata komi ba, kana ya zagaya kujerar da take gami da tsugunnawa saitin kafafun ta, lokaci guda ya kamo hannayen ta biyu ya rike gam.

“Sugar inaso na gaya maki cewar ko da a yanzu Allah zai dauki rayuwata, toh lallai zan mutu ne ina mai gode wa wannn yanayin da kika sanya ni, Allah yai maki albarka Sugar, yakuma bamu sa’a bisa dukkan kalubalen dake gaban mu.” 2

Rintse udanuwan ta tayi cikin wani irin yanayi, ahankli kuma labbanta suka furta kalmar ameen ameen. 2

Daga haka ya umarceta da taje ta shirya su fita domin fara siyayyar tsarabar da zatayi wa yan gida.

“Yayaah inace kace sai jibi zamu tafi? Why not mubar tsaraban sai gobe mayi?”

“No Sugar, muje dai ki fara daukar abubuwan da kike so for now, ke kanki you need alot of shopping, kinsan sabbin outfits zaki fara sanyawa, because ban yarda ba ma ki cigab da sanya kayanki dake gidan wancan Yaron koda mun koma ba.” 2

Murmushi tayi gamida girgiza kai a hankali, kana tace,

“Hoo! Yayaah oga sarkin kishi, please na rokeka ka manta da wata halitta wai ita Safwan,abinda nasani shine ko da w a yake yawo sai ya sakeni, in short nasan hakan ma ba wuya zaiyi ba tunda ba sona yake ba dama.”

“Hmmmmm” Kawai yace, tare da turata dakin ta domin shiryawa, a yayin da shima ya wuce nashi dakin domin sake shiryawa shima. 4

Cikin yan mintuna suka kimtsa, doguwar rigar abaya ce mai kalar coffee brown sanye jikin ramlan, kanta yane da siririn mayafin kayan, duk da ba wata kwalliya bace a fuskar ta ta, hakan bai hana bayyanuwar annurin kyawun ta ba, ba shakka ita din mai kyau ce, innka debe ramar d ta danyi, amma hakn bai canza ko digo ba daga kyawun da ta yi.

Shi din ma wani tissue yard ne mai taushi sanye a jikin sa, kasancewar sa mutum ma’abocin sanya manyan kaya(natives) yasa dukkan kayan da zai sa din amsar jikin sa, har hakan na taimakawa waje boye ainihin shekarun sa, domin kuwa duk da b mutum bane mai cakarewa da kwalisa ba, amma shi din mutum ne mai tsafta sosai, da kuma yanayi na jikin sa kan sa ayi masa kallon matashi mai jini a jika, wanda a kalla ba zai wuce shekaru ashirin da bakwai zuwa talatin ba.

Musayar murmushi sukayi kana suka taka a hankali suka fita daga gidan, ganinta a sararin bainar waje tun bayan wasu tsawon kwnaki da take killace a gida ya sanya ta sakin ajiyar zuciya hankali, ba shakka mutane rahama ne, ta ambaci hakan a kasan zuciyar ta. 10

Drop suka dauka na taxi zuwa jnda zasuje,ita dai Ramla in banda kallon yanayin garin na lagos babu abinda take, sosai garin ya burgeta tunda dai ita kam bata taba zuwa birnin na lagos din ba.Domina E-centre mall suka nufa,biyan mai taxi din yayi kana ya musu jagora zuwa cikin mall din, da alama shi din dan gida ne a gurin, ganin yanda yake kutsawa da ita cikin makeken hadadden mall din, tashin farko mutum zai dauka rana ce, ganin yanda aka kawata tun daga harabar mall din da fitulu masu yawa da kyau, sannan ga mutane nan ta ko ina suna shige da fice, mutane ne en gayun gaske iri iri ga su nan. +

Bangaren kayan mak’ulashe suka fara zuwa, shi ke jidar mata kala kalan chocolates da sauran dangin tarkacen kayan zakin, daga haka suka nufi bangaren turaruka,nan dinma hka ya rika zabar mata designers din turaruka masu kafirin kamshi da kyau, daga haka kuma suka nufi gurin suturu na sawa, anan ne wayar Kabeee din ta dauki kiran neman agaji, ganin ya dauka be ji ne ya sanyi excusing kan shi zuwa wani gefe na bangaren mall din.

Tana tsaye tana takawa a hnkali somin kallon kayayyayakin dake zube a gurin, mamakin irin kayayyakin kurum take, domin kam ita har ga Allah batajin akwai wadanda zata iya dauka a ciki, uban ubansun designers din kaya ne a gurin, kuma dukkan su English wears ne sai kuma arebian wears,gasunan birjik iri iri.

Garin kalle kallen ta ta bigi jikin wani mutum, wanda hakan yai hanzarin maidota cikin hankalin ta ta fara bashi hakuri ba tare da ta dago kanta ba bare taga fuskar mutumin.

Kiran sunanta da mutumin yayi a hankali yayi daidai da karasowar Kabeer gurin da sauri.

Dago kanta yayi daidai da hada ido da tayi da mutumin dake tsaye yana fuskantar ta, sanye yake cikin wasu armani suits, kallo guda zaka mishi ka fahimci gajiyar dake tattare da shi.

Wani irin ihu ta saki gami da zabura tayi kanshi a sukwane, lokaci guda bakin ta na furta sunanshi cike da jin dadin sake ganin sa a rayuwar ta.

Abu-Taleeb ne.

Sosai ya rika juyawa da ita cikin jin dadin sake ganin ta a karo ba barkatai cikin rayuwar sa, inbanda kiran sister yaushe mugun nan ya fiddoki babu abinda yake cewa.

“YaTalib ni fa dama babu inda aka kaini, da kaina na gudu daga gidan nazo nan garin inda bazaa ganni ba.”

Ta fada a shagwabe yayin da take sanya idanunta cikin na kabeer dake kalllon su daga nesa.

“Why Ramlah, miyasa zakiyi haka? ko kin manta da auren Safwan kanki kika aikata abinda kika aikata? baki kyauta ba kuwa indai haka ne, kinsaka mun dauki alhakin sa a banza.”

Zumburo baki tayi gami d yin raurau da idanu kamar me shirin kuka, kana tace,

“Toh ni Ya Talib nayi nayi ya sake ni ne yaki! And zuciyata ta gaza hakurin zama da mugun mutum irin sa yasa na yanke shawarar guduwa kowama ya huta,Allah Yaya na tsani Safwan din nan kamar me!”

Dariya yayi jin irin wautar ta ta, kana yace,

“Toh naji kin tsane shi, amma yanzu dole ne mukoma gida, mussaman sanin irin tashin hankalin da kika sanya mu gaba daya, at least to ease everyone’s curiosity about your whereabouts,ko ya ya?”

Zumburo bakin ta sakeyi gami da bubbuga kafa almun shagwaba, lokaci guda tana mai mak’e kafad’u alamun bata yadda ba.

“No kar mui haka dake lil sis, wuce muje gobe kya karasa shopping din kafin mu wuce, Allah kafata kafarki sai kaduna gobe.”

A lokacin Kabeer ya karaso inda suke, domin sosai yake son takawa Taleeb din birki bisa shishshigin da yaje neman yi mashi kan abar kaunar shi.

“Sugar me ke faruwa ne anan?”Sugar kuma?” Talib din ya sake maimaita kalmar, lokaci guda kuma idaniyan shi suka gane masa mai maganar. 1

Cikin zallar mamaki Talib din yace,

“Kabeer Mainasara? Kai ne ko idanuna ne basu ganeman daidai ba, dama tare kuke kai da Ramlah neh?”

Da sauri Ramlan tace,

“Eh wallahi tare muke, shima dazu d yamma muka hadu, yayi mamakin gani na anan garin din kamar yadda kaima kayi.”

Kallon gefen kasan ido kabeer din ya bita da shi, kana cikin kwarewa yace,

“Ashe kaima kayi irin mamakin danayi dana ganta anan din Talib? Sosai tabani mamaki na ganin all this while tana zaune cikin garin nan d bata san kowa ba, could you imagine?”

Ba tare da Talib din yakawo komi a ranshi ba yace,

“Wallahi kuwa Kabeer, ai alamarin ba karamin kulle mani kaj yayi ba,i hope dai ka fada mata abinda tayin be kyautatu ba? Mussaman irin tashin hankalin d ta saka dimbin jama’ah, mussaman mijin ta da ke cikin wani hali, hope dai ka kira gida ka sanar masu da ganin nata?”

Ji yai kamar ya fallawa Talib din mari jin yanda yake danganta Safwan din da abar son sa, amma dake dan duniya ne cikakke sai bai nuna hakan ba ya maze ya ce,

“Kai dai bari Talib, ai munyi barka dai da ganin nata, sam bata kyuata ba ai, tun daga lokacin da muka hadu nake jaddada mata hakan, shiyasa ma nace mata t shirya jibi dole ta komo gida haka nan, inyaso shi safwan din sai ya sallame ta, tunda bata son zaman dashi.”

Da sauri Talib din yace, “Wannan haka yake Kabeer, in ma amfanin ma irin auren nan da sukeyi,atleast su hakura kowa ya auri wanda yake so, ina ganin hakanne kadai solution to every single thing.”

“Kwarai da gaske kuwa,rayuwar duka nawa take? Life ia too short to be living a life like this.”

Cewar Kabeer kenan yayin da suke gungura keken da suka zubo kayayyakkn da suka siya, akn gobe zaa zo a karashe siyayyar.

Anan ne ma yake wa kabeer din bayanin cewar isowar shi kenan daga canada, ko hotel din da zai sauka beyi booking ba tukunna,wasu turaruka yazo dubawa a mall din.

Da sauri Ramlan tace,

“Kazo muje gidanmu ni da Ya Kbaeer kawai ka kwana a can, ba sai kasha wahalar zuwa wani hotel ba ma.”

Da sauri Abu talib din ya dago kanshi, fuskar sa kuma dauke da mamaki yace,

“Gidan ku keda Kabeer? Au har gida gare ku a nan din dama?”

Gabanta ne ya fadi jin irin subul da bakan d tayi. 10

***
Sake maimaita tambayar yayi jin sunyi shiru sun kasa bashi amsa, hakan yasa Kabeer dawowa cikin hayyacin sa, da sauri kuma cikin halin ko in kula yace, +

“Kasan Ramlah akwai shiririta atimes,kasan tun da ta dawo garin take skwatin a gidan wata yar secondary school class mate din ta, hkan yasa nai deciding nabar mata karamin bungalow dina da nake sauka in nazo garin, i think sekaranjiya ne ma tai parking ta dawo gidan.”

Baki sake Talib din ke bin Kabeer din da kallo.

“Kana nufin ka dade da ganin ramlah har haka, shine baka maidata gida ba? Are you kidding me Kabeer?”

Ramlan ce tayi kokarin katse shi ta hanyar cewa,

“Kai Ya Talib ni ce fa na hanashi fada wa kowa, don gaskiya ni bnyi niyyar komawa gidan ba ma kwanan nan, banda ma ina ganin mutuncin Ya Kabeer din ma da babu inda zani ni.”

Ta ida zncen a yayin da take turo baki gaba, hakan yasa Kabeer din kasa dena kallon ta, gaba daya yarinyar susutar da shi take.

Girgiza kai kurum Talib din yayi, da alama ya gamsu da bayanin na su, hakan yasa shi cewa suje shikam a hotel zai kwana,shi ma Kabeer dinne yace ai shima hotel din yake kwana daga lokacin d ya barwa Ramlah gidan, don haka gaba dayan su suka dunguma don kai Ramlan gida.

WASHEGARI.
Kabeer gaban room din da Talib ya sauka yana knocking, cikin yan mintuna Talib din ya bayyana, kugunsa daure da tawul, da’alama wanka ya fito.

Fuskar shi bayyane da mamaki yace,

“Ah! Kabeer kardai har ka shirya?”

Sai da ya kalli agogon hannun sa kana yace, “Wallahi fa, kasan meeting gareni karfe 8:00 to 5:00/in sha Allah.”

“Ah toh ya maganan tafiyan mu yau din? Kasan jirgin karfe biyu da rabi zamu bi.” Cewar Talib.

Yatsina fuska yayi kadan, “Ai dama nasan zaiyi wuya mu iya making yau, coz dama nariga da nagaya wa Ramlan cewa gobe inna gama abubuwan da nake kafata kafarta sai gida.” 2

Sai d Talib din ya dan numfasa kana yace, “Okay toh shikenan, ka dai tabbata babu wata matsala koh?”

“Hbaa babu wata matsala, goben muna nan tafe in sha Allah, ai surprise zamu mas.” Ya karasa maganar yana yak’e.”

“Eh hakan na d kyau ai, sai mun hadu a can gidan gobe din kenan?”

“Yeah in sha Allah!”

Musabaha sukayi,Kabeer ya juya, shi kuma ya koma ciki domin karasa shiryawa.

***
Shiru tayi gami da sunkuyar da kanta, hakan ya hanashi karanto yanayin da fuskarta take ciki, dalilin d yasa shi jin wani iri a kasan ranshi, hakn ya darsa wani guntun zargi a kasan zuciyar tashi.

“Sugar!” Ya ambaci sunanta cikin kakkausar murya.

Da sauri ta dago kanta a yayin d take sakaya fuskar ta ta da wani malalacin yak’e.

“What is that expression on your face Sugar? Kar dai kina so ki gaya mani baki ji dadin rashin tafiyar tamu ba a yau? Are this eager? Uhmm tell me!”

Kanta kawai take girgizawa alamun ah ah b haka bane, hakna yasa d sauri tace,

“Lah ji Yaaya da wani irin zance, wallahi k kadan abinda kake tunani ba haka bane, what i was thinking da kaga har mood dina ya canza shine, sam bana so a sami akasi Ya Talib din yaje ya rusa mana budget, i mean bana so kwata kwata ya samu fadawa yan gida cewar ya ganmu tare.”Murmushi Kabeer din yayi kana yace, “Toh menene a ciki Sugar? I thought gobe komi zaizo karshe, ya fada masu ko kar ya fada masu it won’t stop us from accomplishing our mission, ko ya kika ce?” +

Rausayar d kanta tayi, lokaci gud kuma ta haske shi da wani kyakyawan murmushi.

“Wannan haka yake sweet Yaaya nah,infact he should just go to hell!”

Murmushin shima yayi kana yace, “That’s my gurl, i love you so damn much.”

Ya ida zancen ta hnyar kashe ta da ido daya, hakn yasa ta sanya fuskarta a tafin hannayen ta tana kyalkyala dariyar jin dadi ba tare da ta samu ikon bashi amsa ba.

“Oyaa get up let’s go shopping.”

Da hanzari ta mike suka nufi kofa suna dariya kasa kasa,tunda dama a shirye take. 4

***
“Kayi wa Allah Safwan ka nutsu mana, wai what is all this? Why not mu jirayi feedback din Salis din tukunna? I know he will never disappoint!”

“Bnagane he will never disappoint ba! How sure are you Bilal?”

Safwan din ya katse shi.

Hajiya da tunda suka fara muhawarar ba tasanya masu baki ba sai yanzu tace,

“Kai kam miyasa baka da hakuri ne iyeeeh? Inace yaron nan yace ku jiraye shi zai kira ya karayi maku karin bayani? Why not bazaka saurara ba aji me zai fada din, idan yaso in decision din beyi maka ba sai ka bi jirgin yamma ka isko su a Lagos din d kanka.”

Shiru yayi, domin zuwa yanzu sam baya iya yi wa Hajiyar tasu musu, sosai yake kokarin nuna mata he’s a changed person now, hakn yasa shi sauke ajiyar zuciya gami da sake narka kanshi cikin kujerar d yake kai, ba shakka ba don ba don ba,da tun a safiyar ta yau ya dira a garin lagos din, mussaman da suka samu information akan inda Kabeer din ke boyon Ramlan, madallah da Salis Danja, shi din wani aboki ne gun bilal mazaunin Lagos ne kuma, hakan yasa daga lokacin da suka gano Kbaeer din lagos ya nufa, sai Bilal din ya kira abokin nashi akan yaje airport din domin bibiyar Kabeer din ga yaga inda ya nufa.

Anyi sa’a ya gane Kabeer din ta hnyar hotonsa da Bilal din ya tura mashi, hakan yasa ya rika bin Kabeer din har gida inda mai taxi ya aje shi, sai dai bai samu yi masa magana ba har ya shige madaidaicin gidan nasa mai dauke da security locks ta ko ina, dalilin d yasanya shi bata lokaci zaune a mota yana tunanin abinyi, duk da cewa ya dauki wasu awanni zaune mota yan jiran tsammanin ganin fitowar Kabeer din hakan baisamu ba, har ya tada motar shi da nufin barin gurin, sai kuma ya hangi Kabeer din ya fito shida wata kyakkyawar budurwa, hkan yasashi dakatawa har sai da yaga shigar su taxi, shima ya rufa masu baya.

Anan ne ya fahimci shopping suka zo, daga nan kuma suka koma su uku sakamakon bayyanuwar Talib, haka dai ya rika bibiyar su har suka je gida suka aje Ramla, kan suka nufi hotel djn da suka kwana, hakn yasa iya wadannan informations din yabaiwa su Bilal, amma yace su jirayi zuwa wayewar gari za suji kome ake ciki kuma.Tsaye suke bakin titi suna jiran mai taxi da zai kwashe su da kayan shopping din nasu zuwa gida, kallo guda zakai wa Ramlan ka hango tsantsar gajiya da kuma alamun rashin lafiya a tattare da ita, hakan yasa gaba daya hankalin Kabeer din yake a tashe,ga karin abin haushi babu ko digon masu taxi sin kamar anyi ruwa an dauke, duk kuwa da cewar yanzu ne ma ake idar da Sallar maghriba a unguwnni.

“Washhhh Yaaaya wallahi ba balain gajiya.”

Jikin shi har wani rawa yake waje lallashin ta, inbanda kiran Sorry Sugar babu abinda yake, a yayin da yake cigaba da duba masu mai taxi, domin shi kanshi a gajiyen yake, har wata massage nan yake buqata, ga wasu irin feelings sa yake jin na addabar shi a duk lokacin da ya hada idanuwan shi da na Ramlan, hakna yasa ya kuduri niyyar yau kam dole ne yai quenching thirsty din sh, mussaman da yake ganin yanzu din zai samu goyan bayan Sugar din tasa, domin kuwa sosai yake matukar bukatar son jin dumin ta a jikin sa, tunda dai ai sun riga da sun zama daya. 8

Tunanin sa ne ya datse sakamkon hango wani taxi da yayj yana shirin wuce su, da sauri ya tsaida mai taxi din,cikin yan sakanni suka zuba luggages din nasu suka shiga mai taxi ya dauki hanyar Victoria Island.

Sunfara tafiya ba dadewa Ramlan ta daddage ta sanya ihu, ihun da saida yayi sanadiyar dakatawar mai taxi,jiki na rawa Kabeer din ya hau tambayar ta akan meyafaru? me take so?.

“Yayyaa wlhy kaina kaman zai cire, ga wani irin tashin zuciya nakeji kamar zanyi amai.”

Ta bashi amsa yayin da hawaye ko karasa zirarowa daga idnauwan ta.

Inbanda sannu babu abinda bakin shi ke furtawa, kana da sauri ya umarci mai taxi da cewar in yaga wani chemist akan hanya haka ya tsaya su sai magani, domin kuwa shi kanshi sosai yake adawa da ciwon nan nata dake mashi barazana,mussaman yanda yake da burin angwancewa a daren na yau din.

“Yawwa yallabai ga wani chemist nan.”

Muryar taxi driver ta katse shi daga ambaton sannun da yake ta jero wa Ramlan.

“Yawwa abokina nagode, don Allah jirani mintu biyu in karbo mata maganin.”

“Ah haba babu komi, Allah dai yabata lafiya, ka hanzar ta ko kwaje gida ta dan samu ta kwanta” cewar mai taxi.

“Hakane abokina, nagode fa, ina zuwa yanzun nan.”

Ya ida zancen yayin da yake ficewa daga cikin taxi din da sauri domin shiga chemist din.

Shigar shi cikin chemist din baifi da mintuna goma ba ya fito, amma sai dai me? Yana fitowa yaga wayam babu mai taxi, babu kala kalar irin taxi din, al’amarin da ya dagule lissafin shi ya sanya shi sakin ledar magungunan hannun shi gami da dafe kanshi cikin halin gigita, a inda dakyar labban shi suka iya lalubo kalmar innalillahi wainna ilaihirraju’oon.”Ya Allah, Ya Allah ina rokon ka kasanya mafarki nake, idan har mafarki nake Ya Rabbi ka gaggauta farkar da ni.” +

Zuwa yanzu a guje yake bin titin gurin da yake makare da motocin jama’ah suna ta wucewar su, al’amarin d yasa ya rika bin titi kamar zautacce, inbanda kiran sunan Sugar babu abind yake, sosai zaka dauka mahaukacine a kallon farko da zaka iya yi mashi. 5

Yanzu kam hawaye sungama yi mashi shabe shabe bisa fuskar shi, kuka yake sosai bikhakki da gaskia, domin kuw ranshi yagama bashi yan yankan kai ne suka gudun mashi da Ramlan shi.

Gefen titi ya samu ya zauna gami da hada kanshi da guiwowin sa, kana a hnkali ya cigaba da barza kuka maras sauti, a yayin da gaban shi ke tsanan ta bugu kamar mai shrin shidewa.

“Sugar I’m so sorry i failed you, amma nayi alkawarin nemoki a duk inda kike a fadin duniyar nan, you are mine, just me alone Sugar.”

A sukwane ya mike zuciya d gangar jikin sa suna masu cigaba da ambaton Sunan Sugar din shi.

***
Gudu yake falfalawa cikin talatainin daren, baya ko kallon gefen sa, zamu iya cewa ikon Allah ne kawai ya shigo da da su garin kadunan a wayewar garin.

Tunda Kabeer ya shiga cikin Chemist din ya juyo ya watsa mata wani abu a fuska bata sake sanin inda kanta yake ba, har izuwa yanzu d gari ya waye kuma yayi daidai da shigowar su garin na kaduna garin gwamna bata tashi ba, kallo guda zakai mata ka dauka irin nannauyan baccin nan take.

Shigowar su garin an kaduna yayi daidai da karfe bakwai da rabi na safe, hakan ya sa mammalakin taxi din fiddo da wayar shi me kirar iPhone 7+ ya danna kiran wata lamba mai dauke da suna BILAL.

“Hello Salis how far ne, tun jiya nake jiran feedback dinka shiru, and nayi ta neman layinka a kashe,hope all is well? And dafatan ka samar mana wani information din? Because wallahi Safwan ya rantse yau dinnan a garin na Lagos zai kwana, yanzu haka wanka yake zai wuce airport, mun rasa ya zamuyi da sh.”

“Bilal kazo yanzun nan ta Ahmadu bello way, gani nan dani da yarinyar da kuke nema, isowata kenan daga Lagos din.”

Da sauri Bilal din ya mika, kan da karfi yace,

“What! Salis kana nufin wai yanzu haka kana tare da Ramlah a nan cikin garin kaduna?”

“Ya wuce wai Bilal,karka manta i can do anything for you matukar bai kaucewa addinin mu ba,karamcin ka a gareni mai tarin yawa ne,yanu dai gani nan ina jiran ka.”

“Alhamdulillah, Alhamdulillah,Salis gani nan tafe yanzun nan.”

Datse wayar tashi yayi daidai da fitowar Safwan daga toilet yana ciccin magani, shi a dole baison jin komi daga bakin Bilal, domin yayi rantsuwa yau babu ubanda ya isa ya hanashi tafiya nemo matar sa, haba abin ya ishe shi haka nan.

“Aboki!” bilal din yakira sunan shi, fuskar shi dauke da wani irin farin ciki, amma dake masifa na cin safwan din sam bai lura da hakan ba, saima dauke kanshi d yayi yaciga da shiryawar shi ba tare da ya amsa kiran Bilal din ba.

“Safwan,ga Ramlah can ankawo maka har gi….. “

Kalar cakumar da Safwan din yai aa Bilal dinne ya sanya shi yin shiru babu shiru.

Baki na karkarwa Safwan din yace,

“If you dare joke with me this early morning, i swear, i swear down Bilal zan iya nannausheka a gurin nan…. What the fuck are you saying?”

Ya karasa magnaar jikin sa na wani irin kafirin rawa.

***

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]