[Advertisements⬇️]

SAWUN BARAWO CHAPTER 8 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SAWUN BARAWOCHAPTER 8


Da zafin gaske ya kaiwa bakin nata muguwar capka,kana lokaci guda ya sanya dukkan hannayen shi ya rike nata kam, ta hanyar murk’usheta gaba daya. Sam mutsu mutsunta da kiciniyar kwacewa da ta ke bai dame shi ba, diba da yanda gaba dayan shi ya soma ficewa daga sauran hankalin da yai mashi saura a kwanyar shi,sosai yake kokarin cimma manufar shi haik’am

Ita kanta dake neman dauki gami da kokarin kwace kanta da take sai da tazo ta gaza, karfin ta ya soma karewa sakamakon ciccijewa gami da tureshi da take yi da dukkan iyawar ta da ikkon ta, sai dai kwata kwata hakan yaki samuwa, wanda hakan ba karamin kara bata mamaki abin yayi ba, diba da kasancewar sa mutum mai karancin k’iba amma sai kafirin k’arfin tsiya. 1

Zuwa yanzu jikin nata yayi lakwas gami da yin laushi, karfin ta kuwa gaba daya ya kare, inbanda hawayen bakin ciki da wuya babu abinda ke fita daga jikin ta, wanda kwarai sanyin da rashin kuzarin da jikin nata ya samu ya taimaka gami da bashi kwarin guiwar k’ara hobb’asa wajen son cimma mummunan nufin shi. 1

Sosai ya bada kaimi, diba da yanda numfashin sa ke sauka da mugun sauri,ga wani gurnani da ke fita daga makoshin sa, duk kuwa da cewar bai riga da ya dau gangarar isa inda yake son zuwa din ba,domin kuwa sosai yake son kunna duk wata gab’a ta jikin ta, a ganin shi hakan ne zai taimaka wajen samun galaba da kulawar ta a gareshi. 1

Wayar shi da ya manta a kunne saman gadon ce ta dauki kiran neman agaji, sannan kuma sai akai rashin sa’a wayar na ta gefen ramlan ne ta wajen kanta, hakan yasa da cikin zafin nama ta kai hannunta guda ta danna okay duk kuwa da cewar batasan waye ke kiran ba

“Hello Kabeer?”

Muryar hajiya ta doki kunnuwan ta, wanda hakan yayi sanadiyar maido da kabeer din hankalin shi cikin halin gigita, ba tare da bata lokaci ba kuma ya sanya hannun shi yayi wurgi da wayar da dukkan kuzarin da yai mashi saura, wanda hakan yayi daidai da kwalla k’aran kiran sunan hajiyan da ramlan tayi, sai dai kash ihun nata yazama ihun ka banza, domin kuwa kyakkyawar wayar mai k’irar Samsung galaxy S7 ta dad’e da tarwatsewa a tsakiyar dakin. 4

Sosai ta kara hangame baki ta rik’a kwalla kiran sunan hajiyar da iya karfin ta, yayin da sautin maganar ta ta ke fita da kuka mai tsananin karfi, wanda zuwa wannan lokacin kabeer din ya riga da ya mirgine daga kanta,tsananin tashin hankali bayyananne ya bayyana bisa fuskar shi, domin kuwa har ga Allah jikin shi na bashi hajiyan su ta gama jin muryar ramlah, wanda hakan ke nufi da asirin shi ya tonu kenan?

Ga mamakin shi sai gaban nashi ya daina faduwa, domin kuwa ya riga da ya yanke wa kanshi cewar ko mahaifiyar ta su bata isa ta raba shi da RAMLATUN SHI ba,ko da kuwa hakan na nufin sab’a mata ne! 3

Ihun kukan nata ya cika masa kwanya, hakan yasa shi mikewa yana mai gyara tazugen wandon shaddar shi, lokaci guda yana watsa mata wani shu’umin kallo da murmushin nan nashi mai ban haushi.

“You lucky for today SUGAR,amma still be expecting me anytime, sabida na rantse da Allah sai na tabbatar da nasaka k’wai na a tumbinki zan maida ki gida, kinga daga nan, ko sun k’i ko sun so, dole su aura man ke, ko ya ki ka gani?”Ya ida maganar yayin da yake dage girar shi guda sama,wanda hakan yayi sanadiyar daina kukan da takeyi, ta tattaro gaba daya hankalin ta ta zuba mashi idanuwa, baki sake +

“Ba shakka Kabeer Mainasara tantirin shege ne.”

Ta ambaci hakan a kasan ranta, yayin da shikuma yacigqba da suturta jikin shi domin ficewa daga gidan.

Peck din da ya manna mata a goshi ne ya dawo da ita hayyacin ta, ba tare da bata lokaci ba ta bishi da Allah ya isa, wuta balbal, hakan bai bata mashi rai ba, saima wata dariya mai nuni da zallar jin dadi mabayyani da yake fitar wa a hankali, lokaci guda yana mai gyad’a kai kamar k’adangare alamun jin dadin masifar tata yake.

Maganar ta ta karshe ce ta bugi dodon kunnen shi a yayin da ya rike handle din kofa dominated ficewa daga dakin, hakan ya sanya shi dakatawa yana sauraron ta.

“Allah ya had’aka da dukkan masifun dake cikin duniyar nan Yaa Kabeer,Ya sadaka da dukkan bacin rai kwatankwacin wanda kasanya mu,Ya kuma wulakanta rayuwar ka, kwatankwacin yanda ka wulakanta tawa amin.” 8

Kakkausar muryarta ta cigaba da amsa amo cikin dodon kunnuwan shi, sosai yake sake juya zantuttukan nata da kwarai dagaske suka samu gurbin sosa mashi zuciya, beyi tsammanin zata jefe shi da munanan kalamai irin wadan nan ba, dukkuwa da cewa shi a ganin shi rashin sani ne, da kuma rashin wayo yake sanya ta kasa fahimtar shi din wani halitta ne daga cikin halittu masu tsananin so da begen ta, wanda sanadin son ne yake sanya shi yin duk wani abun da yake ganin shine daidai cikin soayayyar ta, shin sai yaushe ne zata fahimci cewar shi din ba makiyinta ba ne? Sai yaushe ne zata gane cewar shi din masoyi ne mai muradi da kwadayin kasancewa da ita ko ta halin k’ak’a? Infact sai yaushe ne zata gane cewar babu mahaluk’i a nan duniyar da yake mata, ko zai mata irin son da shi d’in yake mata? 2

“Bi’izinillahi kuma sai na zama ajalin ka Yaaa Kabeer, ka rubuta wannan ka aje!” 4

Zuwa yanzu kasa jurewa yayi, hakan yasa cikin zafin nama ya fice daga gidan, yayin da zuciyar shi ke cigaba da luguden bugu, ba shakka yarinyar nan na bukatar counseling, he needs to put everything in order, idan ba haka ba, daga dukkan alamu nema take ta bashi tough time, amma kuma ta yaya?

Yacigaba da tambayar kanshi yayin da yake tsaida cab domin zuwa airport.

***
A cikin motar yayi kokarin hada wayarshi da tayi filla filla a dazun, wanda kamar jira ake wayar tashi ta kunnu call din saleem ya shigo wayar ta shi,be wani b’ata lokaci ba yai picking gami da yin sallama kamar yanda ya saba.

“Wa’alakummussalam, Yaa Kabeer for God’s sake ina kashiga ne haka kasa hankulan mu suka tashi? And why ain’t you picking your calls? Ka diba dimbiin kiran da mukayi maka tsakanin wayewar garin jiya zuwa yammacin yau? Why duk me ya kawo hakan?” 1

Salim din ya jero masa tambayoyin a tare, wanda hakan yasanya shi yin shiru yana mai sauraren kanin nasa, lokaci guda yana mai kokarin shirya karyar da zaiyi domin fitar da kanshi, domin kuwa ba yanzu ya shirya bayyanar masu da SUGAR din shi ba, sai lokacin da ya tabbatu da gina wani sashe na jikin shi cikin mahaifarta. 2

“Saleem calm down, bazan iya yi maka bayanin komi ba a cikin waya, amma in sha Allah gani nan zuwa kadunan, wani urgent issue ne ya taso mani, but will explain everything idan na iso,inafatan kowa na lafiya?” 1

Sauke ajiyar zuciya salim din yayi, kana a hankali yace “Dalilin kiran kenan dama, kasan abinda safwan yayi kuwa? Could you imagine wai zuwa yayi yakai kanshi gurin C.I.D yana mai claiming dukkan abubuwan dake faruwa, i mean how could someone do something recklessly like this?” 1

“Bani da labari, because I’m not in town, amma koma menene in sha Allah within some few hours zan iso gidan, please kagayawa hajiya tayj hakuri abubuwa ne suka taso mani.”Zaune yake a cikin dakin da ake killace masu laifi, yau kusan kwana hudu zuwa biyar kenan da ya kawo kanshi hukumar, amma abun mamaki har yanzu hukumar sunki yin amanna da abinda ya kawo masu,domin kuwa sunce sai sunga k’wararan shaidu da suke tabbatar da abinda yace d’in ko zasu daukaka k’arar shariar kamar yanda shi d’in ya buk’ata.

Abin zai baiwa dan adam mamaki yanda safwan din ya dage, gami da k’in kaucewa hukumar akan lallai lallai sai an hukuntashi gwargwadon laifin sa, a cewar sa shi din mai tarin laifuka ne b’oyayyu, shin meyasa baza su dube shi ba su zartar da hukuncin su akan mai laifi irin sa ba ?

Kafewar da yayi a hukumar ya janyo har sai da aka samu wasu masu zuciya a kusa cikin ma’aikatan lallasa shi, k’warai da gaske sosai suka jibge shi ganin shegiyar kafiya irin tashi, a cewar su shi d’in wani irin mutum ne haka? Ta yaya zaizo yakawo kanshi guri irin wannan? Sannan sun buk’aci shaida yace bashi da ita, a cewar shi Allah ne kadai shaidar sa, sai kuma CCTV camera dake girke a wajen corridor da zai sadaka da shiga falon gidan shi.

A bisa binciken da hukumar tayi, sakamakon zuwa har gidan nashi da sukayi, kana kuma suka diba camera din gami da yin bincike a kai, wanda daga karshe suka samu hujjar rike safwan din a matsayin mai laifi, domin kuwa camera ta nuna masu zahirin wanda ya fita da Ramla Tafeeda ranar da abun ya faru, ba fuskar kowa bace face fuskar Safwan Mainasara.

Runtse idanuwan shi ya sake yi a karo na barkatai, a yayin da yake jin gingimemen gajiya tare dashi, sosai yake son komi yazo ya wuce, ma’ana a zartar masa da hukuncin sa gaba daya ko zai huta, ba shakka shi din gajiyayye ne kuma maras galihu a yanzu, diba da cewar yau kusan kwana hudu kenan bayan bilal, babu wani mahaluqi na daga shak’ik’an sa da suka nemi sanin halin da yake, ba wai don yana bukatar tausayi ko jink’an su ba ne! ah ah yana dai son sanin cewar ko babu shi zasu tuna dashi sui mashi addu’ah,ya kuma tabbatar da yafiyar su ko bayan babu shi

Hawayen da yake boyewa tun bayan tafiyar bilal ne samun ikon fitowa, hakan ya faru ne sakamakon tunawa da Ramlah, wanda hakan ya riga da yazame mashi jiki a yanzu, k’aida ne matukar ba sallah yake ba, baya da tunanin kowa sai ita, a ranshi yakan so ace inama zai sake samun wata dama kwatankwacin wacce ya samu a baya? Toh da hakika ya cire duk wani tsoro da zuciyar shi ke ji game da ita ya nuna mata zallar so da kaunarta da ya rayu da shi, da ya nunawa duniya cewa ita din ce dai wacce ya rayu yana matuwar so da bege, da kuma ya nunawa UNKNOWN d’in nan daya shiga tsakanin sa da duniyar matar shi cewa baya tsaron dukkan threatening din sa a yanzu, a shirye yake da ya bata dukkan kulawar da zata sanya ta mantawa da maraicin ta, she deserves it!

Amma sai dai me? Hakan duk ba mai yiwuwa bane, domin kwarai dagaske damar shi tayi nisan zango wajen sub’ucewa, babu rabon zai rayu da ita, babu rabon zai aake sanyata a idaniyan shi, babu rabon dukkan wasu buruka da ya dade yana shimfidawa a birnin zuciyar shi….”Malam Safwan kana da bak’i.”

Kakkausar muryar wani Sargent din dan sanda ta katse duniyar tunanin sa.

Mikewa yayi tsaye, yayin da zuciyar sa ke kokonton wanda yazo ganin nasa, domin a iya sanin shi, jiyan nan da safe Bilal yazo ya sanar da shi cewar zaije wani workshop Lagos, amma dai bai fada mashi iya adadin kwanakin da zaiyi ba, kila har ya dawo ne, ya ayyana hakan a ranshi a yayin da yake bin bayan dan sandan zuwa inda ake ganawa da bak’i.

“Ni wallahi kakus da nasan bazaki dena kukan nan naki ba, da ban kawo ki ba, dama alkawarin yammatan amarya kikai mani da kikace bazakiyi kuka ba?”

Sosai ya gane mammalakin muryar, ba kowa bane illah Khalil, mamaki yakama shi, lokaci gida yaji wani yanayin farin ciki na lullube zuciyar shi, Allah sarki SWEETHEART ya ambaci hakan a kasan ran shi. 1

“Yi hakuri Khalili nayi shiru ai, yanzun ma jin dadin zanyi idanu hud’u da yaron kirki yasa kaganni ina hawaye, amma nadaina kaji?” 3

Kakus din ta ba wa Khalil din amsa a yayin da take goge hawayen dake ta tseren doki bisa kuncin ta, lokaci guda kuma tana mai cigaba da rarraba idanu domin ganin ta inda jikallen nata zai bullo.

Tun da suka b’ullo ya hangota zaune bisa kujerun da aka tanada saboda bakin, gefen ta kuma Khalil ne zaune shima yana mai kallon bakin kofar da yafi tunanin ta nan Safwan din zai fito, ilai kuwa tanan din suka bullo, da farko bai gane shi ba, sai da ya kara kura mashi idanuwa kana ya kara tabbatar da cewar lallai wannan yayan shi ne, gaba daya lokaci guda ya sauya, banda tsabagen rama da duhu da yayi, ga wani uban k’asumba da ya samu muhallin cika wannan kyakkyawar fuskar tashi,dama gashi mutum mai yawan gargasa, idanuwan nan sun kara yin ciki, dama ba girma ne dasu ba, hakan zaisa ba lallai bane mutum karon farko ya fahimci idanun a bude suke ba. 4

Wasu hawaye ne suka taru a idanuwan Khalil, sakamakon ganin halin da danuwan shi yake ciki, sosai yake tambayar kanshi,shin Ya Safwan ne dan gayu dan kwalisa ya dawo haka? Zuwa yanzu ya mike tsaye domin ganin karasowar yayan nashi, a yayin da yake zungurin Inna akan cewar ga Ya Safwan din nan, baiwar Allah ta rik’a wangale baki tana k’ara rarraba ido,a son sake sanya jikallen nata a idaniyan ta a karo na barkatai na rayuwar ta

“Kai Khalilu ina Yaron kirkin? Ni har yanzu ban ganshi ba.”

Wa da gama maganar ta ta yayi daidai da tsayuwar Safwan din a gaban su yana mai murmushin jin dadin sake ganin su, sabida haka ko kafin Khalil din ya bata amsa, shi din sai yayi azamar bata, domin kuwa ya riga da yasan cewar har a yanzu da yake tsaye a gabanta bata gane cewar shi din bane.

“Hello Sweetheart.” Ya ambaci sunan ta yayin da yake rike hannuwan ta, domin juyo da fuskar ta zuwa sashen sa, juyowa tayi tana mai k’ura mashi ido, ba shakka ko yanayin rayuwa ya sanya fuskar shalelen ta canzawa, toh hakika babu abinda kuma zaisa takasa tantance muryar sa ciki miliyoyin jama’ah.

Murya na karkarwa, ta zame hannun ta guda daga nashi ta kai shi bisa fuskar shi mai dauke da tarin kasumba cunkus, tace, “Yaron kirki, kaine ka koma haka?Na shiga uku ni jikar mutum hudu, Khalilu duba mani nan dan Allah, Yaron kirki na ne dai nake gani haka a gaba na Khalilu?”

Habawa ia sai ta b’arke da kuka gami da fadawa jikin Safwan din, shima din baisan lokacin da wasu hawaye masu dumi suka rik’a saukowa bisa kuncin sa ba, fadar irin kewar da yayi wa wannan tsohuwar ma b’ata baki ne, ba shakka he missed her more than one can imagine. 1

Khalil kam langabar da kanshi yayi yana kallon su, idan da sabo yaci ace kowa na dangin su yasan irin matsananciyar soyayyar dake tsakanin jika da kakar nan, soyayyah ce tsakanin su mai karfin gaske, domin kuwa tun tasowar Safwan idan kana son ganin bacin ran Inna to ka zagi Safwan ko ka doke shi, in sha Allahu yanzu zaayi yak’in basasa na biyu, babban dalilin d ayasa innar bata son Ya Kabeer kenan a duk fadin gidan nasu, a cewar ta sosai take hango hassada mai girma ta yaron kirkin ta a cikin fik’i fik’in idanun shi, duk da cewar a lokacin abu wanda yake kula ta ko baiwa maganar ta ta muhummanci, a ganin su tsabar so ne d atake yi Safwan din shi ya kawo wadannan camfe camfen nata. 9

“Ya isa Sweetheart, ki bar kukan hakannan, ba gani ba kinganni ina nan lafiya ba?”

Ya ida zancen yayin da yake dagota daga jikin shi, kana yasamu ya zaunar da ita shima ya zauna,koda suka zauna din kin yadda tayi ya matsa ko nan da can, gagam ta rike mashi hannuwa kamar mai shirin tashi sama, al’amarin da yabasu dariya da shi da Khalil.

“Kai sweetheart, toh ai kya sakeni in gaisa da Khalil koh? Ko baki lura bane bamu gaisa ba?”

Ya ida zancen yana kallon fuskar ta yana murmushi, k’in sakin hannun nashi tayi, saima kara kankame hannayen da tayi, domin kuw ahar ga Allah gani take zai iya bacewa ne ya gudu ya barsu, wanda ita kuma tayi alwashin ko sama da kasa zata had’e yau kafarta kafarshi sai gida.

“Ku gaisa a haka, inmunje gida kwayi musabahar.”

Sosai abin ya basu dariya, hakan yasa suka dan dara, mussaman Safwan da yake jin tamkar yau ne take sallah, domin kuwa ganin su kawai din nan da yayi ya kwashe kaso sittin na daga k’uncin da zuciyar sa take ciki.

Bayan gama gaisawr tasu ne da Khalil, inna ta bukaci su tashi su tafi gida, ko safwan din yayi wanka, ya huta ya kwanta, furucin da yayi sanadiyar sake baki da idanu da Khali din yayi yana bin tsohuwar kakar tasu da kallo, ba shakka Kakus na da ababen mamaki, shin kowa ya gaya mata masu laifi na tafiya gida domin hutawa? 3

Cikin sigar lallashi safwan din ya fara da cewa….

“Sweetheart ai ni ba yanzu zandawo gida ba, ko baki san nan guri e inda ake tsare masu laifi iri na ba? Kiyi hakuri ina na dawowa nan da wani lokaci k’ank’ani.”

Ya ida zancen cikin son ganin ta lallasu, amma ganin yanda ta fara mini mini da ido cike da alamun masifa yasa guiwowin sa yin sanyi, domin kuwa k’warai da gaske shine mutum na farko da zai bada shaidar Inna in zata zubda ruwan masifa, mussaman idan ya tuna da kafirin kafiyar ta yasan kuwa yau ba k’ananan yan kallo za’a kwasa ba a division din ba.

“Laifin uwar wa kayi daza’a tsareka iyyyeh? Nace ubanwa ka kashe, ko kuwa uwar wa ka satar wa kudi da za’a zo atsareka anan din? Zaka tashi mutafi gida ko sai na sa yan sandan nan sunyi maka kafirin bugu tukunna?” 3

Ba zancen innar bane zai baka mamaki ba, illa yanda ta dage gami da daga muryar ta garas kowa dake shige da fice a gurin na ji ba, kuma hakan bai dameta ba ganin yanda wasu daga ma’aikatan juyowa ba suna k’are mata kallo ba.

Murya k’asa k’asa Khalil yace “Haba kakus haka mukayi dake? Ke kinsan yanda akai muka baro gidan nan, kinfi kowa sanin alkawwuran da kikai man kafin na kawo ki gurin nan, shine tun a yanzu kinfara karya alkawari? Shikenan ai zakiga wanda zai kara kawo ki wajen shi kuma.”

“Shi alkawarin yaci uwar shi, kai kuji mani yaro da tsirfa don Allah, yo dama ubanwa zai kara dawowa wannan shegen gurin me canza wa mutane halitta? Jira nake mukoma gida dama, idan yaron kirki ya nutsu dole ne zai gaya mani wani shegwn ne ya ramar man da shi haka, ji bi nan gefen idon shi har kumbura yayi, ba tantama nasan cikin wadannan shegun mutanen ne wasu suka bugar mani jika, kuma wallahi duk sai sunci uban su yan iska kawai macuta. 4

Fadar irin shahararriyar kunyar da ta lullubesu ma bata baki ne, sosai suka rik’a jin inama kasa zata hadiye su ko sa huta da wannan kayan kunyar da Inna ta jefa su ciki, wacce ita wadda tai abin ko a hab’ar gyalen ta saima harare harare da take faman yi, gashi ta kama safwan din ta kwakume, ita a dole sai ya tashi sun tafi gida.

“Time Up!” Muryar wani kurtun dan sanda ta doki kunnuwan su, hamdala Khalil yayi, a ganin sa kila Innar ta ji kunyar idon dan sandan ta kyale safwan din, amma sai me? Sai tsinatar muryar Innar yayi tana tambayar shi

“Kai Khalilu menene kuma time up ne koma me yace?” Da sauri khalil din yabata ansa cewar sunce ne ta saki safwan din lokacin komwar shi ind ayake yayi.

Kalar kallon banzar da innar ke bugawa kurtun shi zai baka dariya, sosai take hararar sa, kana lokaci guda tace ” Toh Ubanmu sai kazo ka dau dauke shi ingani fitsarrare kayi da katon bakin ka a gurin kamar Shaddaa.” 5

Wayyo kunya ina kika saka da Safwan da Khalil, a inda Khalil tuni ya rik’a danasanin sato hanya ya kawo innar nan gurin din, amma a can kasan ran shi yace dan ba kara ba!

Yanda kurtun dan aandan yai kicin kicin da rai, shi zai tabbatar wa mutum da cewa ba karamin baci ranshi yayi ba, hakan yasashi dakwa Safwan din tsawa akan yatashi su wuce kafin su canza mashi halitta yanzu,kafin ya rufe baki sai jin saukar mari yayi tasssss, lokaci guda ta sanya hannayenta biyu ta rik’a zuba mashi rankwashi a tsakiyar ka, kasantuwar shi dan gajere mai karancin tsawo, kira take 2

“Shege dama kaine ka rika bugar mani jika har yakoma haka? Dan banza da gajarta kamar inuwar alli.” 21

Da kyar aka rirrike inna tana haki tana huci, sai kokarin son sake komawa take ta cigaba da bugun ‘yan kayan ta, wanda tuni gurin hayaniya ta karade, yayin da tuni wasu zaratan en sanda sukayi nasarar capke safwan, al’ amarin da ya kara tunzura innah ta rik’a kwashe masu albarka, kana kuma tai kane kane tak’i bari a tafi da safwan din, inbanda kuka da tsine babu abinda takeyi. 1

“Subhannallahi lafiya me ke faruwa anan gurin?”

Safwan, Khalil da Innah sune suka shaida muryar mai maganar, hakan yasa su juyawa da sauri domin shaida hakan, amma sai me kuma? Mamakin su ne ya hauhawa sakamakon fuskar ganin wacce Bilal din yake tare da ba kowa bace sai RAMLAH! 5

A hankali safwan ya furta KAZAR MAYU? 13

***
Tun da suka baro hukumar ta state C. I. D yake bin kowa dake zaune cikin motar ta bilal da kallo, kama daga kan shi kansa Bilal din, Ramlah wacce har yanzu mamakin sauyawar ta yagaza barin tunanin shi sakat, har izuwa kan Inna dake ta washe bakin ganin sun samu nasarar tahowa da jikallen ta, wanda tsananin murnar bayyanuwar Ramlan da kuma kubutar jikan nata be sanya ta tsaya ta nutsu gami da yi wa Ramlan kallon sauyar ta gaba daya ba, domin kuwa inka debe fuskar su babu abinda kuma ke shige a wasu daga bangaren halittun su. 4

Sake maida hankalin sa yayi kan Bilal dake ta zuba tuki hankalin sa kwance, baya ga haka wani kyakyawan murmushi ne bayyane bisa fuskar shi, wanda kallo guda zaka mashi ka tabbbatar da samuwar farin ciki a tattare da shi.

Sab’anin Safwan da babu komi a fuskar tashi bayan duba na mamaki da yake bin abokin nasa dashi, har yanzu ya gaza gasgata wannan al’amari, tambayoyi ne masu matukar yawa ke tseren gudu cikin zuciyar sa, mussaman wannan bakuwar fuskar dake kama da Ramlan shi, wanda tun bayan kallo na biyu da yai wa fuskar ta ya fahimci cewar wannan ba KAZAR MAYUN shi bace, toh ina Bilal ya samo wannan? Kuma meye dalilin sa na zuwa ya fiddo shi a hukumar? Bayan yasan wannan din ba asalin Ramlan bace, ma’ana dai har yanzu shi din mai laifi ne, tunda kuwa ba wai gaskia bayyanuwar ramlan bane a zahirance.

Bud’e bakin sa yayi da niyyar jefo wa bilal din tambaya, amma sai Bilal din ya dakatar da shi ta hanyar d’aga mashi hannu.

“Save your questions har mu isa gida tukunna buddy.”

Harar Bilal din yayi gami da komawa jikin kujerar motar yana maida numfashi, lokaci guda yana mai maida hankalin sa bisa titin da suke ratsawa, yayin da zuciyar sa ke cigaba da kissimo masa al’amura masu yawa.

Inna dake bayan mota ita da fake Ramlah sai zubo surutu take, yayin da ita kuma Ramlan sai dai ta rik’a bin Innar da kallo, lokaci guda kuma tana mai sakar mata murmushi, domin kuwa tun haduwar ta dasu innar batace k’ala ba, illah murmushi da girgiza kai, a inda wannan din duk yana daya daga plan din bilal din, sanin cewa muryar ta kadai ta ishi ta tona masu asiri, mussaman gurin Innah.

Zuwa yanzu inna tafara k’ulewa da rashin maganar ta Ramlan, hakan yasa ta muskuta gami da sake fuskantar Ramlan da kyau ta hanyar cewa

“Oh ni ‘yan nan, amma yarinyar nan kin auna arziki, ace mutum yai kwana da kwanaki a cikin daji babu ci babu sha, aikuwa dai ba karamin wuya kika sha ba ko Rablatu?”Murmushi Rukayyan tayi kamar ko da yaushe gami da daga kanta alamun Eh, hakan kuwa ya kara tunzurar da inna, a ganin ta wani irin iskanci ne tun dazu yarinya tak’i Umh tak’i Uhm Uhm. +

“Ke ni don ubanki ki bude mani baki kiy man magana, yau ga iya shegw, kya rik’a daga mani kai kamar wata k’adangaruwa, koh zaman jejin ne yasaki daina magana?” 1

Murmushin yake Rukayyan ta kuma yi gami da kara daga kai alamun Eh hakane, amma ga mamakin ta sai ji tayi kawai Innar ta janyo ta, kafin tasan me ake ciki sai ji tayi Innar na zuba mata iyayen dunduna a baya, ai bata san lokacin da ta kwallara k’ara ba gami da cewa

“Wayyooo Allah bayana, Toh ni menayi maki?” 2

Zuwa wannan lokacin su Bilal dake gaba sun maidk hankulan su gurin su innar, lokaci guda kuma suna masu kara mamakin karfin hali irin na kakus.

“Ja’irah ai ni na iya maganin marasa magana, ince dai ba zafi koh?”

Sai da ta zumburo baki gaba tana hararar innar kana ta bata amsa, wanda amsar da ta baiwa innar yanzu yai nasarar ankarar da ita kalar muryar tata, hakan yasa ta sake kallon Rukayyan da sauri tace,

” Ke lafiyan ki? Wani salon iskanci ne wannan haka zaki maida muryar ki kamar ta k’attan farkon zamani? Kai yaron kirki kana jiyi iya shegen da matarka ta dawo mana dashi kuwa?” 4

Shiru yayi yaki kula Innar, yayin da yacigaba da hararar Bilal din, wanda hakan ya sanya Bilal din kin kallon shi, domin kuwa ya riga da yasan me hararar ke nufi, amma bazai ce mashi komi ba yanzu, sai sunje gida sai ya warware masu daga bindi har wutsiya.

“Inna ke baki ganewa ne? Dadewar da tayi a jeji ne yasanya mura kama ta, baki ga muryar ta ta bata bud’u ba sai da kika zuzzuba mata dunduna a baya ba?”

Bilal din yayi kokarin baiwa Innar amsa, wanda hakan kuwa yayi matukar tasiri a gareta, domin kuwa har karawa da cewa tayi akan Bilal din ya kara sauri domin suje gida ta had’awa Ramlan shayin larabawa tare da farfesun kaji masu yaji, mussamman domin su taimaka wajen gyaruwar muryar Rablatun, a cewar ta inama amfanin wannan murya kamar ta garada. 4

Itadai Rukayyan inbanda mamakin furucin Innar babu abinda take, domin ita tun tasowar ta babu mahaluqin d aya taba danganta muryar ta da ta maza, hasalima mutane da dama k’aunar kalar muryar tata suke kaaantuwar ba ko yaushe aka cika samun irin muryar ba a wajen mutane ba, hakan yasanya ta zama UNIQUE a ko’ina ta bud’e baki domin yin magana.

***
Irin kallon da Hajiyar ta su ke bin shi dashi ya sanya shi jin kamar an samu guiwowin shi ne an bibbige, take kuma yaji k’arairayin da ya shirya domin fitar da kanshi na watsewa daga kwanyar tasa, hakan ya sashi jin inama bai zo gidan ba, domin kuwa sosai yake jin wani bak’on yanayi na bin ilahirin jikin sa.

A hankali ya karasa cikin falon gamida hanzarin rik’e mata kafafu, lokaci guda yana mai langabar da kanshi tamkar wani maraya, sanin cewa ire iren d’abi’un nan nasa ne ke k’ara karkato da hankalin hajiyar gareshi, har ma yake ganin da su dinne zaiyi nasarar fidda Safwan daga zuciyar ta gaba daya, domin kuwa zuwa yanzu hakurin sa ya kai mak’ura, sosai yake buk’atar juyo da soyayayr Hajiyar ta su zuwa gare shi tamkar kafin haihuwa da tasowar Safwan din, wanda haihuwar Safwan din ya canza komi na daga cikin k’aunar da Hajiyar ta su ke mashi a da, wanda hakan yataka muhimmiyar rawa wajen dasa k’ iyayyar dan uwan nashi tun kafin ma yasan mecece ma ita kan ta k’iyayyar, hakika bazai mance yanda ya rayu da bakin ciki gami da tsanar dan uwan nashi ba, ganin irin fiffik’on da Safwan din yasamu daga dukkan bangare na iyayen nasu fiye da shi, dukkuwa da kasantuwar sa mutum shiru shiru mai kafirin hakuri da k’awa zuci, yayin da Safwna din ya kasan ce opposite din sa, amma hakan bai sanya iyayen nasu lura, gami da fahimtar cewa shi nan he’s dying inside ba, sun dauki dukkan son duniya sun daura akan Safwan din, duk kuwa da ksantuwar shi yaro mai kafirin k’inji da k’iriniya, wanda tasirin soyayyar iyayen nasu ya kara taimakawa wajen k’ara sangarcewar shi, a inda su din basu ankare da hakan ba sai bayan da al’amuran nashi suka fi k’arfin su, hakan uasa basu takura ba ko nuna mashi tsana ba, sai dai suka rik’a bin shi da nasihohi gami da addu’o’in shiriya,kana kuma soyayayr da suke masa din babu abinda ya ragu daga ciki, mussaman mahaifin su da har yakoma ga mahaliccin sa kowa yason mafificin soyuwa a ran nashi Safwan ne,ga kuma oga kwata kwata Hajiya Kakus wacce duk sai da tace musu su din basu iya ba, kuma ba son Safwan din suke ba tamkar ita din yanda take jin shi a kan dukkan sauran dimbin jikokin ta. +

“Yanzu Kabeer daidai kenan ka d’auki tsawon kwanaki fin bakwai ba tare da ka lek’o gidan nan ba? babu maganar waya dama, domin kuwa kafi kowa sanin irin neman da mukai maka amma ba’a samun ka, yanzu kana ganin abin da kayi daidai ne ko Kabeer?

“Hajiya don Allah kuyi hakuri, ni kaina ba’a son raina ba ne al’amura suka juye haka, amma kuyi hakuri gami da yi mani uzuri sanin cewa hakan din ba halina bane.”

“Ya zanyi da kai Kabeer, hakuri kam ai dole inyi, mussamman inn duba cewar hakan din ba halin ka bane, irin wannan halin ba halin kowa bane sai na Safwan, Oh ya Rabbi ka shirya mani da yaron nan, ka sanya shi ya fahimci cewa ni din nan bana so mashi komi a gidan duniyar nan face alkhairai da dacewa, Kabeer kai kadai ne shaida ta, kuma kai kadai kasan sirri na, kai kasan dalilin da yasa na dage da son ganin na aura wa Safwan Ramlah, kasani Kabeer ko da fyade, ko babu fyade dama can buri na ne in aura wa Safwan dina Ramlatu na, su din rayuka biyu ne mafi soyuwa a zuciya ta, dukkuwa da cewar banji dadin halin banzan da Safwan din ya aikatawa Ramlan ba, har gobe inajin zafin FYAD’EN da Safwan yayi wa Ramlah, amma zafin na raguwa ne inna tuna dole kuma shi dinne ke auren ta, ko banza zata samu sassaucin cin zarafin rashin kawo budurci gidan miji, ko ba haka ba Kabeer? Ta sake yi mashi tambayar da yake jin tazame masa jiki a duk lokacin da zai kebe da hajiyar tasu, domin kuwa har gobe tambayar shi take in abinda tayi na aura wa Safwan din Ramla daidai ne? “

Kamar ko yaushe idan tana irin wadannan zantuttukan nata yakan tsinci zuciyar sa da mummunan bacin rai, wanda hakan yake kara taimakawa wajen assasuwar wutar tsanar Safwan din a can k’san zuciyar sa, wanda ba karamin k’ok’ari yake ba wajen b’oye haka ba, mussaman ga mahaifiyar su da yake ganin duk duniya babu wanda yakai ta k’aunar safwan d’in ba,amma take boye hakan a kasan zuciyar ta duk don ganin ya shiryu.

“Hakane Hajiya, add’uah zamu cigaba da yi mashi, in sha Allah komi na gab da zuwa k’arshe, yaya maganar Ramlan har yanzu babu wani labari?” 1

Ya soko maganar Ramlan duk don son ganin ta dena maganar safwan din, domin kuwa yafi kowa sanin ta, in tafara zancen Safwan din ikon Allah kad’ai ke sanya ta yin shiru.

Sauke ajiyar zuciya tayi, lokaci guda tana maijin inama al’amura zasu daidaitun masu tamkar ba ayi ba, “Kabeer har yanzu shiru babu wani labari game da yarinyar nan, har yanzu zuciya ta ta kasa gasgata cewar Safwan na da hannu cikin b’acewar Ramlah, har ga Allah nayi mashi hakane domin ya dawo hayyacin sa ya kuma san muhimmancin matar sa, ko ba yanzu ba, amma ni nasan iya shegen Safwan bai kai ya salwantar da rayuwar mutum ba, inada wannan tabbacin Kabeer. “Hakane Hajiya, toh amma yanzu meyene mafita, tunda a jiyan da ina tahowa saleem ke sanar dani cewar Safwan din yakai kanshi hannun hukuma yana mai claiming cewar yana da hannu bisa bacewar da kuma fyaden na Ramlan? Meyasa zaiyi hakan? +

Wasu hawaye ne masu zafi suka samu nasarar gangarowa bisa kuncin hajiyar, amma sai tayi hanzarin share su gami da kamo hannun Kabeer din ta zaunar dashi bisa kujerar dake gefen ta.

“Kabeer har yanzu zuciyata ta kasa fahimtar dalilin d ayasa Safwan aikata abinda yayi din, sai dai jikina naabani cewar wani al’amari ne mai girman gaske ke tunkarar mu, har hakan yasa nake jin k’ila fatan shiriya da nakeyi wa Safwan dinne ya fara afkuwa, domin kuwa gaba daya idan ka lura tun bayan faruwar abin nan Safwan ya fara zama sabon mutum, mai yiwuwa hakan nada nasaba da irin burin da nayi na kasantuwar Ramla SANADIN shiryuwar yaro na, kafi kowa sanin abinda na rik’a hange kenan tun farkon zuwan Ramla gidan nan, kasani kabeer, kai shaida ne, nakuma sha fada maka cewar Ina hango wani babban al’amari a idanun Safwan game da Ramla, wanda shi kansa da abin ke tar da shi bai fahimci hakan ba, amma inafatan abinda nake tunani yasa hakanne, yakuma sanya Allah ya bayyana mana Ramlah cikin lafiya da kwanciyar hankali, hakika da na ksance cikin jinsin da suka samu dacewa bisa abinda suke buri da mafarkin samu Kabeer.

“Hakane Hajiya, yanzu menene abin yi?”

Yayi k’arfin halin tambayar ta, domin zuwa yanzu kiris zuciyar sa take jira ta tarwatse, Hajiya na taka muhimmiyar rawa wajen son ganin yaga karshen Safwan ba, har sai yaushe ne Hajiyar zata fahimci cewar Ramlah ba ta kowa bace face tasa shi kadai? Sai yaushe zata gane cewar Ramlah Tafeeda an halitto ta ne mussaman domin shi shi kadai? Sai yaushe zata gane cewar Ramlah bata dace da kowa ba, kuma ba ta kowa bace face shi din nan da ba’a so?

Sallamar su Innah ta maido shi daga duniyar tunanin da ya afka, hakan ya sanya shi mik’ewa da sauri sakamakon ganin fuskar da ta kad’a yan hanjin cikin sa, cikin alamun fitar hayyaci ya ce

“RAMLATU NA WANENE ISASHEN DAYA FITO MANI DAKE?” 12

Gaba daya falon suka maido da dubansu kan Kabeer din, yayin da kowanne cikin su fuskar sa ta bayyanu da wani irin mamaki, a lokaci guda kuma kowa zuciyar sa tafara raya masa wani al’amari mafi girma cikin zuciyar shi. 3

***
Yanayin kallon da dukkannin su ke bin shi dashi, bai sanya ya dawo hayyacin sa ba, bare har yayi yunkurin kare kanshi bisa katob’arar da ya aikata yanzun, a maimakon hakan ma k’ara rikicewa yayi, mussaman da yaga wacce yake nunawa da hannun ta juya da sauri ta boye bayan Safwan, kasantuwar sa shine mutum mafi kusa da ita, sosai Kabeer din ya firgita ta, ganin irin firgici da fita hayyacin da yayi duk sabida ganin ta. 1

Gaba daya idanuwan sa sun rufe, hakan yasashi mantawa da dukkan halittun dake ysaitsaye a falon hangame da bakuna suna kallon shi, mussaman da suka jikin shi har wani irin rawa yake, kana idanuwan nan sun juye sunyi jawur, ga wasu maka makan jijiyoyi da sukayo masa fitar burtu a tsakiyar sanqon kanshi.

Nufar ta yayi gadan gadan, mussaman ganin ta lafe a bayan Safwan din da yafi tsana kaf rayuwar shi, ba tare da b’ata lokaci ba yai hanzarin isa inda take gami da fizgota, wanda zuwa wannan lokacin har ta hangame baki ya fara zuba kuka, domin kuwa bata taba ganin tashin hankali irin wannan ba.

Kifa mata mari yayi, wanda yayi sanadiyar sanya Bilal buga wani irin tsalle ya riske shi, wanda zuwa lokacin kokarin sake kai mata wani marin yake, inbanda ihu da kiran wani shegen ne yasa ta fito babu abinda yake, sosai ya haukace masu a gurin, wanda al’amarin yayi matukar daure wa kowa da ke gurin kai. 1

“Haaba Yaa Kabeer wai kanka k’alau kuwa? meye haka kake yi kamar wani psycho? Wane irin zantuttuka ne haka kake yi marasa kan gado?”

Cewar Bilal kenan yayin da ya samu ya kwaci Rukayyan daga hannun Kbaeer din, amma ga mamakin sa, sai gani sukai Kabeer din ya sulale kasa yana mai rusa kuka, kuka sosai yake, wanda dole in kana kallon shi a gurin abin yabaka mamaki, mussaman irin yanda yake kukan bilhakki da gaskia, a yayin da kuma sambatun da yake zai kara samun nasarar firgitar da mai sauraren shi.

“Ramlah na how could you do this to me? Meyasa kike son guje mani bayan kinsan bako da wani a duniyar bayan ni?Sai yaushe ne zaki gane ni din mai sonki ne tamkar RAI? Sai yaushe zaki fahimci cewar banyi dukkan abubuwan da nayi ba sai a DALILIN SONKI? I mean how could you be this cruel and run away from me? Why Ramlah? Whyyyyyyyyyy? ” 2

Zuwa yanzu jikin kowa ya dauki rawar mazari, mussaman Hajiya da take jin al’amarin tamkar a mafarki, shin me idanuwa da kunmuwan ta ke jiye mata? Ya ILAHEE, idan har mafarki take, lallai kuwa tana bukatar wani mai imanin hanzarta tashin ta, shin wannan wace iriyar rana ce yau a gare su?

Tunanin ta ne ya tsinke, jin falon yasake rikicewa, hakan na da nasaba da kukan kurar da Safwan yayi zuwa kan YAYAN nashi dake zube a kasa yana gumshek’an kukan son MATAR SA! Wane irin kwamacala ne haka? Ta yaya YAYA zaiso matar K’ANEN sa? A ina aka taba hakan?

Irin yanda jikin Safwan din ke kyarma ne zaibawa mutum tsoro, mussaman idan ka dubi fuskar shi da bata riga ta samu gyara ba, hakan ya kara taimakawa wajen sauya kamanin nasa zuwa wata iriyar halitta, mussaman gingimemen b’acin ran da yai wa fuskar shi k’awanya, lokaci guda kuma wani masifaffen hawaye na tsartuwa ta gefen idon shi guda. 1

Irin shak’ar da yayi wa Kabeer dinne zai ba mutum tsaro, kasantuwar Kabeer din mai rangwamen jiki, mussaman idan yazamo kusa da Safwan, wanda shi munsani irin mazan nan ne dogaye masu garin jiki, ma’ana k’akk’arfa giant, hakan yasa ba abun mamaki bane don Safwan din ya d’aga shi sama gami da buga shi da jikin bango, gaba daya ilahirin jikin shi babu inda baya rawa, zallar b’acin rai da bakin ciki ne bayyane bisa fuskar shi.

“So tell me Kabeer Mainasara, just tell me, all this years,all those damn years it was YOU? It was you Kabeer? You son of bitch….. It was you abi? Kabeer it was you? Oh my Goodness Kabeer i mean how could you do this to me? Uhmmm menayi maka da zafi haka? Me nayi maka Kabeer? I said uban menayi maka kake mani wasa da RAYUWATA har haka?

K’arajin da yake yayi daidai da wurgi da Kabeer din da yayi, lokaci guda yabi ta kanshi da kabcecen takalmin canvas din dake sanye a k’afar shi ya take,gaba da take,gaba daya yagama ficewa daga sauran hayyacin sa, hakan yasa babu mahaluk’in da yayi yunk’urin tankawa, bare kuma kai d’auki, baya ga Bilal da yayi yunk’urin yin hakan amma sai Hajiya ta dakatar da shi ta hanyar cewa, +

“K’yale su Bilal, ni kaina nan ina buk’atar jin dalilin da yasa KABEER aikata abin da yayi din.” 1

Amma ganin yanda Safwan din ke k’wallon tamola da Yayan nashi ya sanya Bilal din kasa jurewa, mussaman kukan Nabila, Inna da Rukayyah ya karad’e falon, wanda zuwa yanzu Khalil ma dasu Salim sun hallara a gidan, a inda suka zo suka tadda wannan irin tashin hankali.

“Safwan ina had’aka da girman Allah da ka saurara da abin da kake, ko ka manta waye wannan a gare ka? Idan ka manta bari intuna maka, ba kowa bane nan a wulakance sai Danuwan ka, kuma YAYA a gare ka, wanda a k’alla yabaka shekaru biyar zuwa shidda, don menene zaisa kai mashi irin wannan hukuncin akan koma menene ya aikata a gare ka eyeee Safwan”?

A fusace Safwan din ya dakata daga abin da yake, sosai ya maoda hankalin sa bisa Bilal da yake jin tamkar ya watsa mashi ruwan zafi ne sakamakon magamganun da yagama yi yanzu.

“Bilal Tofa how dare you zaka dubi tsabar idona kana tambaya ta wai me wannan ASSHOLE din yamani?”

Ya saki wata shegiyar dariya mai dauke da sautin bakin ciki, kana ya cigaba…..

“I mean how could you asked me such question? Wannan filthy abin da kake ikirarin dan uwa ne a gare ni, still shi din ne ya sanya katangar k’arfe tsakanina da duniyar farin ciki na,wanda hakan ya faru ne ba tare da sanin ni dinnan me nayi masa da zafi haka ba,i mean Bilal me nayi wa Kabeer zai juya mani rayuwa ta upside down har haka? Me nayi mashi? Me MATATA tayi mashi da a duk duniyar nan zai rasa wacce zai so sai tawa matar? wanda dukkan abubuwan tozarci da wulakanci da nai mata sun faru ne duk sabi da wannan SON OF A BITCH din,just look at him, he have been screwing me for a long period of time ba tare da sanin cewa shi dinne ba, Bilal kai kasan komi, you knew every damn thing, you knew about that fool, that UNKNOWN someone who have been trying my patience for a while, ashe JINI NA ne behind all this Bilal,jini na Bilal……. Ya rabbi! ” 2

Zuwa yanzu bakajin komi a falon inbanda sautin muryar Safwan, wacce sautin ke fita cike da zafi da tuk’uk’in b’acin mabayyani, hakan kuwa bai sanya ya fasa shuri da harbin Kabeer ba, wanda zuwa yanzu baya iya yin komi baya ga ajiyar zuciya, tsabar buguwa da yayi a hannun k’annen nasa, amma kar ku dauka hakan yasa shi ya russuna? Sam ko kad’an babu alamun danasani sassauci a tare dashi, baya ga haka wani sabon haushi da tsanar Safwan dinne yai mashi karan tsaye a birnin zucciyar shi, ba shakka bazai tab’a hakura ba har sai ranar da yaga Safwan ya tagayyara, tagayyara irin wacce bata da madafa, sosai yake burin sanya shi cikin dukkan k’uncin duniyar nan, kuma ba shakka ko duka duniyar nan zasu taru babu wanda ya isa yasan ya shi ya hakura da RAMLAN SHI, shin baza su fahimci cewar Ramlah an halicce ta domin shi kadai ba ne? 1

“Yaa Safwan don Allah ka k’yaleshi haka nan, kayi hakuri don ya rasulillahi.” cewar Nabila cikin kuka, yayin da ta ruga ta k’wak’ume Kabeer din, ta yanda Safwan din dolen shi ya dakata da hauri gami da shurin da yake wa yayan nashi.

Juyawa yayi gami da fuskantar hajiyar tasu, wacce zuwa yanzu hawaye sungama yi mata kace kace da fuska, bata t’aba tunanin akwai rana makamanciyar wannan zata riske su ba, ba shakka kwamacala irin wannan babban abin kunya ne ga ahalin na su.Hajiya, Ina hadaki da girman Allah, da ki tambayi d’anki me na tsare mashi a rayuwar shi da har zai man irin wannan yankar k’aunar, i mean anya JININ KA zai iya cutar ka har haka? Just tell me tsakanin ni da Kabeer waye ne ba jinin ki ba.” 3

Shiru yayi yana bin ta da kallo, sakamakon marin da ta kafsa mai, lokaci guda ta nuna shi da d’an yatsa tana cewa,

” Safwan ka shiga hankalin ka, ka kuma san irin kalmar da zaka rik’a furtawa, yau ni kake kallon tsabar idona kana tambaya ta ko ku d’in jini na ne? Sabida me Safwan zakai mani wannan banzar tambayar? Saboda bacin rai a kan abinda dan uwan ka yayi? Kana tunanin mu din nan gaba daya bamuyi mamaki ba ne akan abin da shi din ya aikata? Ko kana zaton al’amarin k’arami ne a gare mu baki daya? Ba shakka Kabeer ya bani mamakin da tunda uwata ta kawo ni duniya ba’a tab’a bani irin sa ba, ya sanya mani shakku akan shin shi d’in wane irin mutum ne shi? Kuma menene ya sanya shi aikata abin da ya aikata d’in?”

“Son zuciya!” 1

Muryar Inna ta karade falon tun bayan farawar lamarin.

“Bakomi ba ne ya sanya wannan kafirin mazan aikata abinda ya aikata ba illa SON ZUCIYA, wanda kowa yasan son zuciya B’ACIN TA!Kaico!kaicon ka Kabeeru, karasa wa zaka so a duk fadin duniyar nan sai matar kaninka, ka rasa wa zaka ci amana a duniyar nan sai DANUWAN KA SHAK’IK’I! Wace iriyar zuciya ce a kirjin Kabeeru? Shin anya kai din ba shedan ba ne? Babu kunya babu tsoron Allah ka wage gwangwareriyar muryar ka kana kukan Son matar k’anen ka, wallahi kaji haushi, Allah kuma ya shirye ka idan mai shiryuwar ne, amma kamar yanda kasani ne, Rablatu ba ta kowa bace face ta Yaron kirki, shege mai bak’in hali, idan ka gadama ka hdiyi zuciya yanzu kayi mushe, da kuwa mun rage mugun iri a cikin dangin mu! ” 2

“Yaki nan Rablatu” Ta juya gami da fuskantar inda Rukayyan ke rakube tana zare idon ganin tashin hankali kiri kiri, ba shakka da ta san abinda zata riske kenan da batai gigin amsar tayin Bilal ba, wane irin gida ne wannan ta kawo kanta? 3

Da sauri Safwan ya isa inda Rukayyan take ya janyo ta, bai dire ta a ko ina ba sai a gaban Kabeer dake jingine da bango a jigace, ga mamakin su sai gani sukai Kabeer din ya ture Nabilan dake kwance a jikin sa tana kuka, a yayin da yake yunkurin kai hannun sa jikin Ramlan, wanda hakan yasata zabura gami da yin baya, domin kuwa ita sosai Kabeer din ke bata tsoro, kallon mahaukaci mahaukaci take mashi.

Sai da Safwan din ya watsa mashi kallon banza kana yace, 1

“You asshole, nasan dakikiyar kwakwalwar ka dama ba lallai bane ta tantance fari da baki, mussaman idan a kai lura da irin zalunci da bakin hali irin naka, saboda haka for your own information, take a look at this girl, ka kalle ta da kyau, wannan ba RAMLAH ba ce, amma yanzun nan ba anjima ba nake so ka gaya mani inda ka kai mani mata! “

Gaba daya falon inbanda Bilal da Hajiya ai sai suka maida hankalin su bisa Rukayyan, domin kuwa hajiya dama tashin hankali ne ya hanata magana, amma tun kallo na biyu da tai wa Rukkayan ta gane ba Ramlah ba ce wannan.

Ba’a maganar inna wacce ta saki baki gami da cigaba da yiwa Rukkayan kallon kurullah, sai yanzu tsohuwar k’wakwalwar ta ke tantance mata tarin bambamcin dake tsakanin Ramlatun su da wannan.

Wannan din irin matan nan ce masu dan kauri kubul kubul, ma’ana irin chubby dinnan, ga ta kuma fara ce sosai a kan Ramlah, sannan kuma bata da dimple,sabanin Ramlah da ko bacci take kumatun a lotse su ke.. Amma idan ka dauke wadannan ababen toh hakika babu abin da ya bambanta ta da Ramlah Tafida, ikon Allah kenan, mai tsara halittar sa yanda ya so, kuma a inda ya so!

“Aikuwa dai ba Rablatun ba ce, oh ni jikar mutum hudu yau nake ganin ikon lillahi, yaki zo nan yammata, tukunna ma dai yaya sunan ki?”

“Rukayyah Sadauki.” Ta baiwa Innar amsa yayin da take kara sunkuyar da kan ta.Ah ah ikon Allah, ashe jikar tawa takwarata ce, madallah da zuwan Rukayya gidan nan, wanda sanadiyar kamanin ta da tamu jikar ya sa.Allah ya toni asirin munafikin gidan nan, Allah abin godiya!” 3

Ta ida zancen yayin da take cigaba da hararar Kabeer, wanda tun bayan gane cewa wannan din ba Ramlan shi ba ce yake. jin wani nishadi na bibiyar shi, hakan ya sashi mantawa da wani cin kashi da ya fuskanta, koma yake shirin fuskanta a gidan, domin kuwa alkawari ne yanzun nan ya daukar wa kanshi babu su babu sanin inda yakai Ramlan, ko da hakan na nufin fitar numfashin sa ne daga gangar jikin sa.

“Kabeer Mainasara, don’t let me ask you for the fourth time, INA KA KAI MANI MATA?”

Muryar Safwan ta katse masa tunanin sa, jin abinda yake cewa ya sashi watsa wa Safwan din kallon baka da hankali, daga haka ya dafa jikin bango ya mike, bai bata lokaci ba yayi hanyar ficewa daga falon yana layin bugun da yaci ba tare da yabaiwa Safwan din amsar tambayar shi ba, al’amarin da ya kara tunzura Safwan din, wanda hakan yasa shi shan gaban Kabeer din gami da cakumar kwalar rigar farar shaddar shi, lokaci guda yana mai zazzaro wadannan fici ficin idanuwan nashi.

“Where the hell do you think you are going without telling me what i demand to know Kabeer Mainasara? Gidan ubanwa zaka je ba tare da gaya mani inda RAYUWATA take ba? Are you mad”? 5

“Yes Safwan Mainasara i am beyond mad indai akan Ramlatu na ne, i am a psycho, you can call me that,wallahi tallahi kaji na rantse da wanda raina ke hannun sa, ba zaka tab’a sanin inda Ramlah ta ke ba, because she is mine, she’s mine since from day one! Ko baka sani ba ne intuna maka?Nine nan nafara sanin ta ‘ya mace, ni ne nan nayi mata FYAD’E! Just because of what? Just to make her mine alone and alone, and idan duk duniyar nan zasu taru babu shegen da ya isa ya rabani da ABINA! not even you Safwan Maina….. “

“You son of a bitch….” Ya kai mashi wani bahagon naushi, wanda yayi sanadiyar zubewar Kabeer din a k’asa. 14

***


[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]