[Advertisements⬇️]

SAWUN BARAWO CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SAWUN BARAWO


CHAPTER 2


Da hanzari ya yaye bargon dake lullub’e da ilahirin jikin na su, kana kumaa a lokaci guda ya sanya hannuwan shi ya b’amb’are yarinyar dake k’wak’ume da jikin sa. 2

Hakan ya sanya ta saurin bud’e ido gami da mik’ewa zaune bisa gadon hotel d’in da ya zame wa wanda ya kama d’akin tamkar gidan ubale. Sakamakon yanda yake tsula tsiyar shi a otel d’in hankalin sa kwance. 2

“Na baki minti biyar, ki b’ace mani da gani” 2

Saurin sake waro idanuwan ta waje tayi, sakamakon jin furucin na mainasara.

“But i thought you said we going to spend the whole day and night together “? Tayi kasadar tambayar shi. 2

“You must be very stupid, my friend get down and pack your filthy ass off my bed, kar ki bari na k’ara yi maki magana” ya bata ansa yayin da yake k’ok’arin sanya wandon black jeans a k’ugun sa. 7

Sanin shika shikan rashin mutuncin nasa ya sanya ba tare da tak’ara cewa uffan ba ta hau kintsa jikin ta, amma kuma bata fasa kwashe mashi albarka ba a zucciyar ta, sakamakon biyu babun da ya sanya ta yi a yau d’in. 4

Kusan a tare suka gama kintsawa, sakamkon saurin da yake yi domin ganin ya tsinci kan sa a cikin gidan na su, he really needs to put some senses into those people’s heads. 1

Da sauri ta kwashi d’agogwaragon takalman ta a hannu gami da k’arasa ficewa daga d’akin da gudun ta, ganin ya na shirin gark’ame ta a dakin, wanda tasan yin hakan ba k’aramin jidali za ta janyo wa kan ta ba, domin kuwa idan ya fara cin uban ta, ko mammalakin hotel d’in bai isa ya k’waceta ba. 2

Duk da kasantuwar ta ‘yar gata gaba da baya a gurin iyayen ta, hakan bai hana safwan din jibgar ta ba, matuk’ar ta yi masa abin da bai gamshe shi ba, duk kuwa da irin rab’ar da yake kwasa a jikin nata.

Ko da yake bata cika ganin laifin sa ba, illa laifin shegiyar zuciyar ta, da ta kasa yakice mata k’aunar safwan din tamkar ta zautu, domin kuwa sanadin son nashi neh yasan ya ta maida mashi da kan ta tamkar karuwa, sakamakon yan da ta amince, kuma ta ke bashi dukkan hadin kai a duk sa’ilin da ya buk’a ce ta. 1

Ta girgiza kan ta yayin da take k’arasa saukowa daga benen da room din safwan d’in yake, hakannan kuma tana ci gaba da sak’e sak’en yanda zata mallaki safwan d’in a hannun ta, ita d’aya.

Domin kuwa baza ta tab’a yadda ya subuce mata ba, ko ta halin yaya neh kuwa, “ba zata tab’a sab’uwa ba” ta furta hakan a k’asan zuciyar ta.

Ko da ta k’arasa harabar hotel din har yayi wa motar sa key, da sauri ta nufe shi tana d’aga masa hannu alamun ya tsaya.

“Samira what again, kin san kina da matsala koh”?. Ya furta hakan yayin da ya lek’o kanshi ta windown motar.

“Pls drop me off, kasan na baro mota na a club jiyan” Ta fad’a da alamun marairaicewa, sanin in be gadama ba tsaf zai iya dizgata ya k’ara gaba. 1

Tsaki yayi ganin tana son b’ata mashi lokaci, idanuwan sa yakai bisa agogon dake shimfide bisa kyakkyawar fatar hannun mai cike da gargasa.

Ganin kusan k’arfe shidda saura ya sanya shi tsaki, domin kuwa yaso ace before maghrib yana gidan na su, hakan ya sa shi bata izinin shigowa ganin kawai gara ya fara tsaya wa yayi sallar maghriban kafin ya je ya sauke wa ‘yan gidan nasu abubuwan da ke kan su. 4

Da sauri ta bud’e gaban motar ta shige, haka nan kuma lokaci guda tana mai sauke ajiyar zuciyar samun nasara.

Shiru motar ta dauka yayin da ya dauki hanyar unguwar ta su samiran, sanin in be gadama ba sai ku kwana ku yini tare ba tare da yace maka komi ba neh yasan ya ta kame bakin ta tai shiru, domin kuwa duk wani wanda yake tunanin sanin halayen safwan d’inne baran ita neh.
Isowar su k’ofar gidan na su samiran, yayi dai dai da isowar babban yayan samiran shima gidan, hakan ya saka shi saurin packer motar shi domin ya hanzar ta zuwa yaga wannan tsagerin yaron da’ake bashi labarin cewar shine silar lalacewar tilon k’anwar ta su. 3

Motar ta safwan d’in ta kasan ce tinted ce, ganin hakan ya sanya shi k’onk’osa glass din motar a hankali. Ganin ba’a sauke glass d’in bane ya saka shi k’ara k’onk’wasa wa da d’an k’arfi wannan karon.
Da kyar ya rabe bakunan su dake had’e da juna ana kiss d’in bankwana, hakan ya saka lokaci guda ya saki wani irin tsaki a zuciye ganin an katse masa ‘yar tak’ aitaccen jin dad’in da yake ciki na wannan lokacin. 2

“Who the hell are you for interrupting me” ya furta zancen a yayin da yake lek’o kan sa bayan ya sauke glass din motar. 1

Murmushi yayan na samira yayi, tun bayan yin arba da siffar ta safwan d’in, ba shakka ko wannan surar ta shi ta isa ta sanya kanwar su lik’e ma shi, amma wannan ba damuwar shi bace, fatan su ya rabu da k’anwar su.

“You must be safwan mainasara right? , fitsararren gayen da yayi nasarar tab’arb’arewar tarbiyar k’anwa ta, shin ko zaka iya gaya mani dalilin hakan”? Ya k’ura mashi idanuwa domin jin amsar shi. 2

Amma maimakon ya bashi ansa, sai yajuya ta inda samiran keh zaune sunkuye da kai a k’asa tamkar munafuka yace “Who is this asshole”?. 5

Shiru tayi gaban ta na luguden bugu, amma safwan bai da mutunci, babban yayan gidan na su gaba d’aya yake kira da asshole?. Wanda tasan a k’alla in bai bashi shekaru goma ba, zai bashi takwas.

Mamaki neh ya kama yayan, jin dan iskan yaron ya kira shi da wannan sunanan, dad’in dad’awa kuma bai ma bi takan shi ba balle ya ba shi amsar tambayar shi.

Hakan ya saka shi dakawa samiran tsawa akan ta sakko daga motar kafin yazo ya same ta, jiki a salub’e ta yayimi jakarta tana shirin b’alle murfin motar ta fita.

Ta chan k’asan mak’oshin sa yace “Don’t you dare open that door, I’m not fucking done with you”. 8

Turus ta yi tana jinjina wannan karfin hali na safwan, ga shi kuma ko giyar wake ta sha ba ta isa ta k’i yin abin da yake so ba, hakan yasa ta saki handle din k’ofar motar tana mai tararrabin abin yi.

“Samira ina wasa da keh neh? Isakancin naki da ake bani labari da ma yakai haka,? Maganar saurayi ta fi tawa kenan koh.”? 1

Ko kafin ta yi yunk’urin furta wani abu yayi wa motar key, hakan ya sanya yayan matsawa da saurin shi ganin yana shirin mutsuke mashi k’afafu. 1

” Ba shakka tantirin d’an iska neh yaron nan” zuciyar shi ta cigaba da kitsa mashi. 3

Haka kuma mamakin al’amarin da ya faru yanzu din ya kasa fita da ga kwanyar sa, jiki a sanyaye ya nufi hanyar cikin gidan na su domin jin k’arin cikakken bayani game da wanna mara mutuncin mutumin.

***
Cikin motar ya bar ta ya shiga masallacin dake gaf da shiga unguwar su domin gabatar da sallar maghriba, wanda tun bayan barowar su gidan na su samiran, bai kuma ce mata uffan ba, sai dai hora ta da yake faman yi da matsiyatan idanuwan shi ma su sanya wa mutum kasala yayin kallon su. 2

“Na shiga uku, son mainasara ya zame mani bala’i” ta tsinci bakin ta da furta hakan, Sannan dad’in dad’awa komi zeyi mata baya bata haushi, illa ma sake nink’aya da take sake samun kanta cikin wutar k’aunar shi. 7

Hakan ya k’ara san ya zuciyar ta kwad’ayin samun shi ita d’aya rak ko ta halin k’ak’a neh, sanin cewar shi d’in ba k’aramin dan akuya ba neh ta fannin iya shegen neman mata, sauk’in ta ma d’aya ba kowace jaka yake kwasa ba, sai ha tabbatar da mazaunin ki da yanayin ki kafin ya gayyace ki bisa shimfid’ar sa. 2

Rufe idanuwan ta tayi tana mai fatan kada wata rana kishin safwan d’in da take yazama silar ajalin ta, domin kuwa tasha sanya ‘yan iskan zaune gari banza cin uban duk shegiyar yarinyar da ta samu labarin safwan d’in ya rage dare da ita, ba tare da sanin shi safwan d’in ba. 3

Bata ji shigowar shi cikin motar ba sakamakon zurfi da tayi cikin tunani, hakan ya sanya ta yin firgigi ta dawo hayyacin ta.

Sai da suka sake d’aukar hanya kana yace mata gidan su zai je, wanda sai da yafurta maganar kana ya juya yana k’ara kallon matsiyatan riga da wandon dake jikin ta, sun lafe gami da zaunawa daram a jikin nata, wanda yake a murje kuma mai kyau sosai kuwa, domin kuwa yanayin na jikin nata na daga babban dalilin da ya sanya shi kasa rabuwa da ita. 2

Da sauri ita ma tace mashi “Saf baka ga kayan jiki na bane, haka kake so in fuskanci y’an gidan ku? Pls i still have some shame wallahi”

Dariya ta ba shi hakan yasa ya sa ya k’yalk’yale da dariya ganin yadda take ta ‘yen muskuce muskuce domin ganin komi ya zama intact a yanayin shigar ta ta. +

“No you don’t have a bit remnant of shame, coz if you do, ba zaki fara fitowa a haka ba tun farko, sabi da haka ki nutsu bana son shirme, you are okay like that, in short you look more sexier a hakan.”

Ya ida maganar yana mai kashe mata ido, hakan ya sanya tayi surrender ganin yanda yake k’ara bin jikin ta da kallo tamkar maye, ko banza she has that effect on him, at least it’s a victory” 2

Ganin su a bakin wani tangamemen get ya sanya ta k’ara nutsuwa, hakan yasa ta k’ara jin faduwar da gaban ta keyi na k’aruwa, shin wani irin kallo familyn mainasara za suyi mata? “Slut” wani sashe na zuciyar ta ya bata amsa. 6

Da sauri ta sauke siririn mayafin kan ta ta yafo shi har kafad’ar ta, amma duk da haka beyi nasarar rufe tumulin gashin kan ta ba ma, balle akaiga batun sakkowa bisa kafad’un ta. Inda ta gode wa Allah shine top d’in rigar ta ta, mai d’an tsayi ce, domin ta d’an sakaye kyawawan mazaunen ta kasancewar ta ‘yar duma-duma.

A k’a’ida dama horn guda yake yi mai tsayi in yazo gidan na su, hakan neh zai fara sanar da duk wanda yasamu damar jin horn d’in isowar shi gidan.

“Oyyaaa muje” ya rik’o hannun ta suka nufi cikin gidan, a ranshi kuma yana mai jin dad’in zai jefi tsuntsu biyu da dutse guda. 3

Da nabila ya fara cin karo ta wajen balcony din
gidan tana amsa waya, hango shi da ta yi ya sanya ta datse wayar ba tare da ta yi sallama da wanda take wayar ba, haka nan kuma chan k’asan zuciyar ta tana mai tambayar kan ta wannan mai kama da inyamuran fa, me tazo yi cikin gidan su.?

“Lah ya safwan sannu da zuwa, ashe zaka zo d’in? Dama kakus ta ce kana tafe”

Ba tare da ya tsaya ba yace “Eh… I hope mutanen gidan na ciki?”

“Eh suna ciki” ta bashi ansa yayin da take hararar matar dake tare da yayan na ta, haka kuma sai ta tsinci kan ta da tausaya wa ramlah. “Chaab ina ramlah za ta iya da irin wad’annan gogaggun matan da idanuwan su sun gama bud’ewa da iskanci.” 2

Hmmm ta sauke numfashi ganin yanda yarinyar keh tafiya tamkar tarwad’a sakamakon yanda komi na jikin ta keh juya wa a hankali. “Wayyo ramlah har kin ban tausai”. Ta ambaci hakan a zuciyar ta.

Babban falon gidan babu kowa, sai TV dake faman yi shi kad’ai, hakan yasa direct ya nufi ta side d’in bedroom din na inna.

Bai kai ga shiga d’akin ba ya tsinkayo wata siririyar murya ana gaishe shi, ya riga da ya san mutum guda neh ke da irin muryar kaf gidan, hakan yasa ba tare da ya kalli bak’ar fuskar ta ba yace….

“Perfect timing! Kazar mayu get your small ass over here”. 8

Da sauri samiran ta waiga domin ganin wacece aka kira da “kazar mayun Cikin sakannin da basu shige sittin ba ta k’are wa hallittar yarinyar kallo.

Siririya ce k’warai da gaske, domin kuwa samb’al take kamar sanda, babu gaban balle kuma baya, tana da matsakaicin tsayi, haka nan kuma ba za mu iya sako ta cikin jerin bak’ak’e wulik d’innan ba,kai tsaye zamu iya kiran ta da chakulet kala,doguwar fuskar ta d’auke ta ke da siririn dogon hancin da yayi matuk’ar k’ara wa fuskar ta ta armashi, sa’annan kyawawan idanu da Allah ya hore ma ta, sun yi matuk’ar taka rawa wajen k’awata kyawun fuskar ta ta, labban ta masu kalar duhuwa kad’an, sai kuma kwantacciyar gashin girar ta da na ido da suka k’ara fiddo asalin kyawun ta. 8

Kallo guda zakayi wa salahar fuskar ta ta, ka hango tsabar kyawu da Allah ya hore mata, matsalar ta guda rama da ta yi mata yawa, domin kuwa Siririya ce ta k’arshen zamani, hakan ya taimaka wajen boyuwar wasu halittu na jikin ta, wanda har hakan yake sanya wa ake mata kallon k’waila, diba da yanda inba kayi mata kallon k’urulla bah, zai yi wuya ka fahimci albarkatun k’irjin ta.

Tab’e baki samiran tayi cike da son kwashewa da dariya, ba shakka yarinyar ta ci sunan nata “Kazar Mayu”. Ba tare da ta k’ara kallon fuskar ta ramlan ba ta bi bayan safwan d’in zuwa cikin d’akin innar da ya shiga. 20

“Heyy sweetheart wassup, ba dai bacci kike ba daga yin maghrib” ya ida zancen yayin da yake k’ok’arin zama kusa da innar da ke kishingid’e bisa gado. 2

Wuf ta mik’ e tana mai k’ok’arin saisaita zaman ta bisa gadon, haka nan kuma lokaci guda ta fara washe baki, Wanda ke nuni da bayyanuwar farin cikin ganin yaron kirkin na ta.

“Af yaron kirki ashe ka iso?, yanzun nan nake zancen ka a raina ai” 1

“Toh ga ni ai sai ki bar zancen nawa a ran naki” ya furta maganar yayin da yake zubawa samira harara, sakamakon ganin tana niyyar zama bisa doguwar kujerar dake girke a d’akin na innar.

Ganin mugun kallon da yake watsa mata ya san ya ta yin cak ba tare da ta zauna ba, haka kuma gaban ta bai fasa fad’i ba sanin me kallon na shi ke nufi.

“Haba wlhy mainasara bai da kunya ko kad’an, ta yaya ma yake tunanin fara zuwa ta zauna kusa dashi a cikin gidan su”?

Ta sauke ajiyar zuciya cike da tararrabin abiin yi.

“Samira kar ki fara trying d’ina da yamman nan”

Sai a lokacin inna ta ankare da samiran, hakan ya san ya ta tambayar ko wacece.

“Beb d’ita ce” ya bata amsa yayin da yake cigaba da hora samiran da idanuwan shi, haka nan kuma ya cigaba da tunanin yanda zai hukunta ta bisa taurin kan da take neman yi mishi a yau d’in. 5

Da idanuwanta ta cigaba da rok’on shi akan ya barta ta zauna bisa kujeran, sanin cewar dole ne matuk’ar ta zauna kusa da shi ya rungumo ta jikin shi, ko kuma ya nanak’e ta ya d’aura bisa cinya, kad’an daga cikin ayyukan sa neh. 2

“Kar ki bari raina ya b’aci beb, kin san abin da zai biyo baya”

Sanin in da zancen shi ya dosa yasan ya ta yin shahada ta nufi in da yake zaune tana zuba kwarkwasa, dama dai d’an kawaici neh ta ke yi ganin kakar shi da ke d’akin, amma tun da ya bada go ahead, toh ai shikenan sai a cigaba da gashi, bala’i wa ya kashe! That’s my girl” ya furta hakan a k’asa mak’oshin sa, wanda samiran ce kad’ai ta ji mi yace d’in. +

“Sweetheart ina yini”? 2

Samiran ta yi kasadar gaishe ta, duk kuwa da irin kallon hadarin kajin da innar ke jifan ta da shi k’asa-k’asa.

Banza ta yi ba tare da ta amsa ba, sannan ta juya da kyau ta na mai fuskan tar su.
Idanuwan ta suka cigaba da kallon hannayen na mainasara da ya k’wak’ume hannayen samiran tamkar wani na shirin k’wace ta.

“Allah ka shirya yaron kirki, shi jarabar ma ta shi a ko ina nuna ta yake, anya babu k’amshin gaskiya a maganar ta ramlah”? Ta tambayi kan ta cike da jin takaicin samiran. Sam yarinyar ba tayi mata ba, sai kace tsatson inyamurai, farin ta har yayi yawa.

“Wani shegen yace miki suna nah kenan”? 4

“Kai kakusa beb d’ina ce fa, ya da haka”?

Safwan d’in ya katse ta gami da b’ata rai.

“Toh sai me, ni ina ruwa na” tai tsaki kana ta cigaba.

“In ban da rigima ma irin taka yaron kirki ina zaka kai wannan shirgegiyar matar mai kama da bazawara” ta ida zancen ta na mai rik’e hab’a. 4

“Oh shiiiittt, ai kinji matsalar ki sweetheart, na d’auka kin fi kowa sanin irin zab’ina kenan? Kuma da kike ce mata kamar bazawara, dama mi cece?ai na dad’e da maida ta bazawarar, koh beb”? 11

Ya ida maganar yayin da yake k’ara matse ta a jikin shi gami da kallon cikin idanuwan ta.

Haushi da takaicin jika da kakar neh suka kusa kashe ta a zaunen da ta ke, ba shakka tsohuwar nan bata da mutunci, ta yaya ma zata dubi tsabar idon ta ta ce mata bazawara? Kuma da yake shima jikan na ta shegen saman neh yak’ara da d’ora na shi salon iskancin a kai. 1

“Da sannu zan gyara wa akwalar rayuwar ki zama” ta yi zancen a zuciyar ta, gami da k’ok’arin danne b’acin ran da ke barazanar faso k’irjin ta.

Lokaci guda kuma ta saki murmushin k’arfin hali gami da k’ara damk’e hannun safwan d’in ta ce “Hakane dear” 2

“That’s my gir…. Be k’arasa zancen ba sakamakon bayyanuwar ramla cikin d’akin, siririyar muryar ta da ko a cikin mafarki zazzabi ta ke sanya mishi ya san ya shi saurin tamke fuskar shi tamau.

” You must be very stupid, don ubanki sai yanzu ki ka gadamar zuwa da na kira ki”?

Jikin ta neh ya fara rawa, kana kuma a take bakin ta yaci gaba da karkarwa a k’ok’arin yi mashi bayanin abin da ya hana ta zuwa tun shigowar ta su.

“C’ommon shut that you fucking mouth up” ya katse ta cike da son zuwa ya jibgi abar banza ko zai huce takaicin kallon ta da yake.

“Shegiya mai zubin mayu”

Kukan da take dannewa neh ya kufce ma ta jin sunan da ya danganta ta da shi.

Ita kam a duniyar nan har yau ta kasa gane abin da tayi wa wannan d’an tahaliki ya tsane ta, tun bayyanuwar ta a gidan na su, bayan rasa na ta iyayen. 2

Domin kuwa har ta koma ga mahaliccin ta baza ta tab’a man ta abin da ya safwan din yayi mata ba a tun ranar da aka kawo ta cikin gidan nan a matsayin k’anwar su.

Domin kuwa bata had’a kyakkyawan mintuna biyar ba a gidan, ya wawwanka mata wasu kyawawan maruka guda biyu, a cewar shi kallon ta kad’ai da yayi sai da gaban shi yayi fad’uwar da bai tab’a yi ba, dob haka hukunci saka shi fad’uwar gaba kenan. 9

Ta yi kuka ranar, kuka ba kad’an ba, wanda duk da k’ank’antar shekarun ta a lokacin bai hana ta fahimtar irin rashin da ta yi na iyayen ta duka biyu da tayi a duniya ba, kasantuwar ta ‘ya d’aya tilo da suka haifa.

Tun daga ranar ya sanya mata karan tsana, shekaru kusan goma sha uku kenan tun zuwan ta gidan, amma babu rana guda da zata nuna tace wannan d’an tahaliki ya kyauta ta mata ko da na rana d’aya neh kuwa.

Duk wannan azabar da yake gana mata a iya wad’annan shekarun bai ishe shi ba sai da yabi hanyar da ya bi ya nakasa mata rayuwa, nakasa ta har abada kuwa,amma da yake mugu neh na farkon zamani, ya shafa wa idanuwan shi toka ya ce bai san zance ba.

Hawayen idanuwan ta suka cigaba da bulbula tamkar anbude fanfo, kallo guda zaka yi mata ka hango zallar k’osawa da tashin hankali a ramammiyar fuskar ta.”Keh ramlatu yi hak’uri kiyi shiru, ko dukan ki yayi neh”? innar ta tambaye ta cike da alamun karaya a fuskar ta.

Gaba d’aya ji tayi tausayin yarinyar na neman kama ta.

Sai da ya harari innar kafin ya mik’e ya isa inda take mak’ure da bango kamar b’eran da’aka tsamo daga cikin ruwan zafi.

Tsaye yayi ma ta a ka, ya na mai k’are mata kallon wulak’anci. Hakan yasan ya ta zamewa k’asa gami da k’ara k’ank’ame jikin ta cike da tsoron shi da ya gama girma a zuciyar ta.

“Munafuka wani abu aka yi maki da kike kuka haka? Mtsw ” Kar ki damu yanzu zakiyi me dalili, ina mai tabbatar maki sai kin yi dana sanin yi mani sharrin da ki ka yi. “

” Wanda gaba ko da billions of dollars a ka had’aki ba zaki k’ara kuskuren yi ma wani sharri ba a duniya, matsiyaciya”

Ya sanya kaf’ar shi ya haure ta.

Toshe bakin ta tayi da hannayen ta domin ganin ta maida kukan da ta ke yi.

“Yaron kirki yi hak’uri ka rabu da ita, sharri neh ta riga da ta yi maka, kuma kowa ya hau ya zauna a kai”

Ta numfasa cike da son ganin ta lallashe shi kafin ya fara jibgar ta, sanin yanda tsab zai iya kakkarya masu yarinya yabar su da jinya.

“Kakus idan nace zan daki wannan abar, ai baza ku tsinci komi a gurin nan ba, tsab zan aika da ita barzahu”

“Shiyasa nace kayi hak’uri ka kyaleta karka k’ara wa kanka laihi wajen saratu, kasan ta da shegiyar mita”

Sai da ya k’ara shureta da kabcecen takalmin timberland din dake k’afar shi kana ya koma ya zauna gami da rungumo samiran jikin shi, wacce tun da suka fara maganganun su ta baza kunnuwa ta na nad’ewa, da kuma fatan ta tsinci inda zancen nasu ya dosa. 7

“Ai sai ki tashi kije ki kirawo mani saratun, ba dai kince keh sharri ki ka iya ba? Ke ce shaa wuya ai” innar ta ida zancen ta na mai jin tausayi da kuma haushin ramlar a lokaci guda.

Sumi sumi ta mik’e ta yi hanyar ficewa daga dak’in, ko kafin ta k’arasa ficewa, ya dakatar da ita, sakamakon rad’a da samiran ta mishi a kunne.

“Ki fara zuwa ki kawo ma beb d’ina abin sha tukunna, tunda ku baku iya karrama bak’o ba, useless”

“Kayi hak’uri mantawa nayi” ta furta maganar bakin ta na d’an rawa. 1

“Banson tsirfa, wareh daga nan kiyi abin da na ce kafin na barki kwance, nonsense”

Da sauri ta juya har tana had’a hanya, had’i da fatan Allah ya ganar da wannan d’an tahaliki.

Samiran ce ta bi bayan ta da hararar, Allah ya gani ita kanta ta tsani yarinyar daga zuwan ta yau dinnan, duk kuwa da rashin sanin alak’ar da ke tsakanin su. 1

Amma don son ganin ta yi clearing doubts d’in ta, sai ta langab’ar da kan ta gami da sake lankwashe murya ta ce “Mainasara wai wacece wannan figaggiyar yarinyar? She seems stubborn” 3

Sai da yayi tsaki kana yace “Bansani ba, banson shishshigi ina ruwan ki”? 4

Ai kamar ya wanka mata mari haka taji saukar maganar, wanda sai da tayi maganar kana ta yi dana sanin furta zancen, halin mainasara neh ta manta na wulak’anci da dizgi.

Dariya inna ta saki cike da jin dad’in dizgin da yayi wa yarinyar, ko banza hakan yak’ara tabbatar mata da cewar mainasara bai kyale kowa ba a duniyar nan. 2

“Yaawah kike sweetheart” yayi zancen yana mai hararar innar, a ganin shi baiga abin dariya ba anan.”Naje nayi yawar, d’an nema” itama ta kaikaice ta zuba mishi harara. 1

Al’amarin da yayi matuk’ar baiwa Samiran dariya, ta hau k’yak’yatawa harda guntun hawayen ta.

“Gaskiya dole ne inci uban da ya haifeki yau samira, ni kikewa dariya”? Ya furta maganar cikin wata iriyar kakkausar murya, wacce ta yi matuk’ar tsorata samiran, har hakan yayi sanadiyar kufcewar fitsari a wandon ta. 7

Dukan kawo wuk’ar da yayi mata a satin da ya gabata ya fad’o mata a rai.!

A firgice ta furta “Na bani, na shiga uku, na lalace Mik’ewar shi yayi daidai da shigowar hajiyan,hakan ya sanya shi fasa abin da yayi niyya, amma don son ganin ya baiwa hajiyar haushi sai ya k’ara da janyo samiran jikin shi kamar babu abin da ya faru. 14

Bata kalle shi ballanta na yasa ran zata tanka don ganin display din da yake yi a cikin d’akin, illa sama wa kanta mazauni da tayi a cikin d’akin.

“Inna barka da yammaci, Yanzun nan ramlah ke ce mani kuna nema na”

“Eh baki ga yaron kirki bane yazo? Ai so nake ayi ta ta k’are a yau d’innan saratu”

Jiim hajiyan tayi a ranta tana mai fatan al’amuran su zo da sauk’i, sanin kafiya irin ta innar da tayi, amma da yardar Allah sai ta ga tabbatuwar al’amarin nan zata sarara. 6

“Kikayi shiru kina kallo na” innar ta katse mata tunanin da ta ke yi, hakan ya sanya ta kallon sashen da safwan d’in yake.

Da sauri samiran ta sunkuyar da kan ta tana maijin nauyin dattijuwar, haka nan kuma ta rasa mi ya damk’e bakin ta ta kasa ko da gaisheta neh.

“You must be stupid samirah, so sai nace ki gaishe da mahaifiya ta abi”? Ya furta zance can k’asan mak’oshin sa ba tare da ya kalli fuskar ta,lokaci guda kuma ya sanya k’afar shi mai dauke da takalmin timberland ya mitsike mata ‘yan yatsun k’afa da k’arfin sa. 12

Ai ba tasan lokacin da ta kurma ihun azaba ba, hawaye suka fara tsartuwa daga fuskar ta, hakan ya sanya ta damk’e cinyoyin sa cikin yanayi na jigata.

Inna ce ta balla mata harara gami da cewa “Yau ga er dabar yarinya, lafiyan ki, kike mana ihun y’an gidan yari a gida”? 4

“Sweetheart take mani y’an yatsu yayi wallahi”

Nan kuwa kaka ta k’ara fusata, “Kai yaron kirki idan wannan bazawarar taka ta k’ara ce mani wannan sunan, wa billahillazi zanci uban ku daga kai har ita, yau ga iya shege”. Ta ida zancen tana hucin b’acin rai. 12

Ko kafin yace komi, samiran ta amshe.

“Toh ai ni haka naji mainasara na ce maki,ban san wani sunan ba bayan wannan ba”

“Toh ina ruwa na, kece jika na ko shi? , yau ni naga jaraba.” innar ta katse ta cike da bala’i a muryar ta. 1

Shiru d’akin ya d’auka na ‘yan mintuna, kana da ga chan samiran tayi k’undumbalar gaishe da hajiyan.

Kadaran kadahan ta amsa ba tare da nuna wani abu a fuskar ta ba. Gama gaisawar ta su yayi daidai da shigowar ramlah d’auke da wani k’aramin faranti a hannun ta.

Can gaban samiran taje ta ijje tray d’in, ga mamakin ta sai jin kalmar nagode ta yi daga bakin bak’uwar ta su, wanda shima kan shi safwan d’in sai da ya jinjina kalar munafinci irin na samira. 2

Hanyar fita ramlan ta yi, amma sai hajiyan ta dakatar da ita, gami da yi mata nuni da tazo ta zauna magana zasuyi.

Gefen hajiyar ta zauna a d’arare, diba da irin kallon banzan da yayan nasu ke jifan ta dashi, hakan ya sanya mata sunkuyar da kai k’asa tana mai cigaba da wasa da ‘yan yatsun hannun ta.

“Toh saratu ina so inji dalilin da yasa kike nema ki tilasta yaron nan yin abin da bai yi niyya ba, saboda Allah a’ina aka tab’a haka?” 2

Hajiya ta sauke numfashi kana ta ce “Inna ku fahimci abun da nake nufi akan al’amarin nan don Allah, ku duba mana, rayuwar marainiyar Allah ce abar tausayi, domin kuwa an riga da an kassara mata rayuwar, kuma kun sani cewa a wannan zamanin babu namijin da zai kwashi ramlan a hakan matuk’ar ya san halin da take ciki”Ta numfasa, “idan kuma har munce mu boye wa duniya halin da yarinyar nan ta ke ciki, gaba idan tayi auren dole ne asiri ya tonu, daga nan kuma sai kuga in ba’ayi sa’a ba wani gagarumin al’amari ya faru.”

Tun da hajiyar ta fara zancen yake karkad’a k’afa, haka nan kuma ya tsinci kan shi da k’ura wa ramlan ido ba tare da shi kan shi yasan ya na yi ba.

Muryar innar ce ta maido shi daga halin da yake ciki, hakan ya sanya shi k’ara tsaida idanuwan shi akan ramlan a karo na biyu, sakamakon jin tambayar da innar ta ke yi mata.

“Keh ramlatu idan kin boye mana, ba zaki b’oye wa Allah ba, duk da dai nasan tuntuni ake tambayar ki, amma nima a yanzun zan tambaye ki a karo ba farko, tsakanin ki da Allah yaron kirki neh ya miki fyad’e”?

Dama ta dad’e da fara kuka a hankali, amma jin tambayar ta inna ya sanya sautin kukan nata bayyanuwa ga dukkan mazauna d’akin. 1

A hankali kukan yaci gaba da girmama, hakan ya sanya tausayin ta a cikin zuciyar innar tun faruwar al’amarin.

“Ki yi hak’uri ki yi magana kinji rablatu” innar ta soma lallashin ta, a tunanin ta kukan fad’ar gaskiya ramlan ke yi.

“Keh malama, ina da abin yi, ki musu bayani kafin na b’arar da ke a gurin nan, Allah kuma ya baki sa’a na k’ara jin kin ambaci suna irin nawa a baki ki”

“Toh uban ta” hajiyar ta katse shi,

“Nace sannu uban ta, wallahi tallahi safwan idan baka fita a ido na ba zan yi mugun sab’a maka, shasha maras tunani”

“Ni fa ban son haka saratu, ya zaki tasa yaro ki rik’a zagi? Ai gaskiya ya fad’a, ko keh akai wa irin sharrin nan sai inda k’arfin ki ya k’are, ah ah ina dalili”

Shiru hajiyan ta yi ba tare da ta sake cewa komi ba, domin kuwa al’amarin na inna ya soma fin k’arfin ta”

“ke rablatu ina jin ki, gara ma ki sarara da kukan nan, domin kuwa babu in da zai kai ki.”

Zuciyar ta ce taci gaba da bugawa cike da tashin hankali mabayyani, ita kam ta shiga uku, wacce iriyar jarabta ce wannan Allah ya nufe ta da ita.

Ta sake fashewa da kuka gami da yun istigfari cikin ran ta, kana a hankali ta budi baki ta yi magana domin samawa kan ta mafita cikin lamarin,ta gaji, ta yi matuk’ar gajiya da al’amuran da suka ta so ta gaba.

“Inna kuyi hak’uri na boye muku,ku yafe mani,ba yaya safwan ba ne yayi mani fyad’e ba, asali ma banga fuskar mutumin ba” ta fashe da matsanancin kuka bayan ta gama fitar da zancen da tasan cewa ba gaskiya ba neh, amma da wata azabar gara wata.

Bata gama had’iye numfashi ba taji ta a tsakankanin k’afafun shi ya fizgo ta, ba tare da sanin me zai faru gaba ba ya fara zuba mata ruwan maruka, ta kowanne bangare na fuskar ta. 16

Wani irin kuka take mai matuk’ar ban tausayi, haka nan kuma zafib marukan ba cigaba da wanzuwa a dukkan ilahirin jikin ta, shi kan shi dake marin ba zai iya cewa ga yawan maruka da ya kikkifa mata ba.

Sannan abin mamaki babu wanda yayi yunk’urin dakatar da shi daga marukan da yake shshshinfid’a wa y’ar mutane, hasali ma samira rugawa tayi k’arshen gado gami da k’wak’ume inna ta b’uya sabi da tsananin tsoron da safwan d’in ya bata. Wannan mutumi anyi bak’in mugu! 8

Tausayin ramlan ya kama ta akaro na farko tun shigowar ta gidan.

“Wanna kad’an na miki idan har kika k’ara kuskuren yin irin wasan nan da suna na, wallahi sai na yagalgala ki da hujja a gaban uban kowa inga ta sharri, useless human being” 3

Jin yasaketa ya sanya ta yin baya da rarrafe tana karkarwa, gaba d’aya kamanin ta sun sauya, ba lalle bane ka gane fuskar ta ba a tashin farko da zaka dube ta, sakamakon yanda fuskar ta ta haye tai suntum. 2

Inbanda sheshshek’ar kukan ta baka jin komi a dakin, hatta inna mai bakin iya magana tsit kake ji kamar an lik’e bakin da gam.

Sai can hajiyan ta numfasa kana tace “Masha Allah, ka gama koh? Ka yi hukuncin da kake ganin daidai neh a gare ta koh?, hakan na da kyau”

“Amma yanzu ka bud’e kunnuwan ka ka saurare ni da kunnen basira”

Ta numfasa bayan ta kalli gefen da ramlan keh tsugunne kamar mai neman gafara, tausayi da k’aunar yarinyar suka cigaba da lullub’e zuciyar ta.

Hak’ik’a bata cikawa ‘yar uwar ta burin ta ba na ganin ta inganta rayuwar tilon y’ar ta guda d’aya rak!, Kaico, safina ba ta cancanci haka daga gare ta ba. +

Wasu zafafan hawaye suka kwaran yo mata, da sauri ta sanya hannuwan ta, ta goge su, kana a lokaci guda ta tamke fuska tamkar ba’a tab’a halittar fara’a a fuskar ta ba.

“Safwan, a yau ina so in sanar da kai cewa, zan aura maka ramla ba don al’amarin da ya afka wa rayuwar ta ba, sai don ganin damar kai na, da kuma isa da nake da ita a gare ka.” 9

Ta cigaba “A yau zan nuna maka ina da iko da kai, a yau zannu na maka fifik’on ramla akan dukka in yaran da na haifa da ciki na, haka zalika a yau nake so in tabbatar maka da cewa, wallahi baka da wata mata a duniya sai ramla.”

“Ban buk’aci amincewar ka, ko rashin amincewar ka ba, da yardar Allah gobe da safe sai ramla ta tabbata mata a gunka, daga nan ina fatan idan na mik’a maka ita, ka sanya kan ta gabas ka yanke, na rok’e ka da Allah kar ka bar ta da sauran rai.” 1

Daga haka bata k’ara cewa komi ba ta mik’e gami da jan hannun ramlan su ka fice daga d’akin.

Huci kawai yake, gaba d’aya jijiyoyin kan sa sunyi rud’u rud’u sun bayyana, ba shakka gab yake da yin aika aika a cikin gidan nan.

” Miyasa mammy ta tsane shi neh har haka” yaci gaba da tambar kan shi ba tare da yasami ansoshin tambayar sa ba.

“Da rarrafe samiran ta k’araso bayan shi hankali tashe, tun da suka fara badakalar su sai yanzu aka tab’o inda ko duniya su had’u ba su isa su hana ta tankawa ba. As in me kunnuwan ta ke jiyo mata, wannan shegiyar yarinyar ce ake nufin zata mallaki abin k’aunar ta?

“Nooo, noooo impossible wallahi”

Ta dafa bayan shi da nufin son ya tabbatar mata da abin da taji.

“Babe don Allah me old woman dinka ta ke fad’a neh, gaba d’aya ta kwance mani notikan kaina, is she insane”?

“Is she what”? Ya juyo a fusace yana kallon ta da rinannun idanuwan shi da suke rine da b’acin rai.

Fizgota yayi daga gadon yasanya k’afar shi guda ya harbeta, ko kafin ta fasa ihu ya zare belt din wandon shi ya fara kilar ‘yan kayan shi”

Ihu take da iya k’arfin shi tana ba shi hak’uri.

Shi kuwa fad’i yake “Nooo ba’ a halicci shege da shegiyar da ta isa ta zagar mani mahaifiya ba ta kwana lafiya, my mum? Mama na samira kike kira da mahaukaciya don uban da ya haifi uwar ki, matsiyaciya irin ki” yaci gaba da kafta mata belt da iya k’arfin shi, kai kace k’ato ya samu. 14

Inna gefe ta koma ta sanya mashi idanu, ba shakka bazata ba da hak’uri ba, domin ita kanta da tana da halin taimakwa da nata gudummuwar da ta yi. 5

Ganin abin ba na k’arau ba ne, ya san ya ta sauka tarike safwan d’in gam ta na bashi hak’uri, sakamakon ganin kukan ma nata yazo yadena fita sabi da azaba.

Wurgar da belt din yayi yana maida numfashi, kana a fusace ya nuna mata hanyar fita, “Get the hell out of here kafin na aika da ke barzahu, don Allah gobe ki kwatan ta qara zagar mani uwa ki ga ni”

Kuka ta cigaba da saki a kwance, jikin nan yayi rud’u rud’u, abin ka da farar fata, jini duk ya kwanta tamkar wacce aka sanya a injin markad’e. 13

“Bazaki ta shi ba ‘yar iska sai na b’allaki into pieces”?

Ba shiri ta rarrafa ta dafa banga ta yi hanyar waje, zuciyar ta cike da sak’e sak’e. 2

“Nonsense” yabi bayan ta da harara, kana kuma ya juya ya fad’a toilet a fusace.Ya cigaba da lumshe idanuwan shi a karo na biyar tun wanzuwar shi bisa makwancin sa dake cikin otel d’in.

Hak’ik’a tunda uwar data kawo shi duniya, wani abu bai tab’a nasarar sanya katangar k’arfe tsakanin sa da baccin sa ba, komin tsauri da wahalar abin kuwa.

“Ikon Allah”

Ya sake mirginawa, yayin da fuskar shi keh fuskantar sama, a lokaci guda kuma yana mai cigaba da al’ajabin al’amarin dake nema yayi wa rayuwar shi karan tsaye.

“Aure Manya!” 1

Ya sanya dariyar mamaki daga k’asan zuciyar shi, tabbasa da hajiya na da masaniya bisa abinda zai biyo baya cikin lamarin nan, da tabbas ta janye k’udirinta a kan shi, kwarai da gaske da ta sanya wa lamarin full stop tun lokaci bai k’ure ba.

Ya sauke numfashi bayan dogon nazarin da yayi, a lokaci guda kuma ya furta “Hajiya don’t say i didn’t warned you”. 2

A take kuma ya yanke wa kanshi mafita bisa lamarin dake nema ya girmi tunanin shi.

Daga haka ya janyo wayar hannun shi dake zaune bisa durowar gefen gado, ba tare da b’ata lokaci ba ya danno wata lamba mai dauke da sunan “ABOKI” yayi dialing.

  “Assalamu alaikum, this is Bilal Tofa on the line, wata murya ma’abociyar kamala da nasibi ta amsa. 7

” Mainasara Safwan” ya amsa kamar yanda ya saba,duk da muryarshi a dakushe take kuma da’auke da sautin bacin rai, hakan bai hana bayyanuwar farin ciki na jin muryar aboki kuma aminin shi ba. 2

A duk kafatanin rayuwar shi baya da aboki, kuma amini da yazame masa tamkar wani bangare na jikin shi face Bilal Tofa, hakan na da nasaba da halayen shi mabanbanta da na sauran al’umma.

A tarihin rayuwar shi tun yarintar shi baya aboki, iyakar shi dakai gaisuwa idan ta kama, hakan ya sanya babu mahalukin da ya isa  ya dangan ta tab’arb’arewar al’amuran sa ga abokkan banzaa, duba da yanda ya zab’i tsula tsiyar sa ba tare da kusanci da wasu b’ata gari ba. 3

Asalima ya tsani ko da hanya ce ta had’ashi da irin zaune gari banzan nan ‘yan daba, domin kuwa sam baya danganta kanshi da irin kallon da al’ummar gari ke masa, wanda shi a ganin sa babu shegen da ya isa ya kira shi da d’ an daba, kayi wuta ka danganta shi da baud’add’en mutum mai wuyar sha’ani, a b’angare guda kuma d’an akuya manemin mata. 4

A inda shi sam bai d’auki hakan a matsayin wani abu ba, abinda ya sani kawai shi “Wannan wata k’addara ce daga cikin shafin k’addarorin sa”. 2

Asalin abotar shi da Bilal ta samo asali neh tun zamanin da suke aji d’aya a jami’ah, ajin su d’aya wanda hakan ke nufin kwas guda suka karanta kenan.

Idan kaga Bilal sai kayi mamakin abotar shi da safwan, inda a take yanke zaka k’aryata wannan fad’ar da hausawa ke cewa “Sai hali yazo d’aya a ke abota”. 3

Domi kuwa bilal complete opposite d’in safwan neh, halayen su da yanayin su gaba d’aya mabanbanta neh a fili.

A kallo na farko da zaka yi wa bilal din zaka hango zallar kirki da kamala bisa salahar fuskar shi, mutum neh ma’abocin hak’uri da sauk’in hali, haka zalika mutum neh ma’abocin addini da tsoron Allah.Hak’ik’a ba y’ar k’aramar wahala bilal d’in ya shaba kafin amintar shi da safwan d’in ta k’ullu kasantuwar shi mutum mai matuk’ar wuyar sha’ani.

Wanda bilal d’in ya dage gami da baiwa rayuwar ta mainasara dimbin gudunmuwa don ganin ya tsamo shi daga halakar da yake ciki, amma ina! Haian bai samu ba, duk kuwa da cewa a kullum bilal din ba ya fasa nuna mishi gaskia, tare da bin shi da addu’ar shiriya a kowace sallar farillar shi.

   “Hak’ik’a wannan shi ne amini na gari”. 3

A tak’aice bilal shi ne mutum guda rak da safwan ke matuk’ar d’agawa k’afa, haka zalika shi kad’ai neh mutumin da ke bashi dukkan lokacin shi da kulawar shi baya ga tsohuwa innah. 2

“Aboki ka kalli agogo kuwa? A iya sanina baka ziyartar club aduk duk rana ta juma’ah, and at the same time na san babu ‘Whore’ din dake tayaka kwana a irin rana ta yau d’in (juma’ah).” 2

“What kept you awake har k’arfe biyu da kwata na dare”?. Bilal d’in ya tambaya muryarshi cike da mamaki mabayyani, domin kuwa yafi kowa sanin waye safwan, a k’a’idar shi daga k’arfe goman dare ya rufe ansa waya, ko uban waye kai ka kira bazai dauka ba,sai dai ka jirayi wayewar gari.

A kasalance yace “Aboki ina cikin gagarumar matsala, i need your help”

Hankalin bilal d’inne ya tashi, domin tun had’uwar shi da safwan d’in kimanin shekaru bakwai kenan da suka gaba ta, bai tab’a jin shi ya ambaci wani abu makamancin “Matsala, Help ba”

Domin kuwa mainasara bai san su ba, a kowacce dak’ik’a ta rayuwar shi tana wanzuwa neh cike da yanda yake buk’atar kasancewar ta, kenan Allah ya ara mashi dama a dukkan abinda ya sanya a gaba, ciki kuwa harda kasantuwar shi mutumin da yakea a yau!.

Murya a tausashe bilal yace “Safwan have i heard you right? Matsala fa kace? Shin wace iriyar matsala ce haka take tunkarar amini nah? Yi gaggawar sanar dani domi  ganin na taimaka waje  kauda ta.”

Ya sauke numfashi, kana cikeda sabon b’acin rai yace “Bilal aure hajiya zata mani bisa dalilin taka ‘SAWUN ‘BARAWO danayi”

   Taka SAWUN ‘BARAWO kuma? Aboki ban fahimce ka ba, kamani bayani ta yanda zangane”

Sai da ya furzar da iska daga bakin shi mai nuni da dimbin bacin ran da yake ciki.

“Bilal bansan kalmar da zan fara da ita ba wajen yi maka bayani,wasu shafukan k’ addarori na neh aka bud’e, and wallahi I’m really confused”

“Ikon Allah, safwan this is unlike you, kasan da haka koh? ” bilal din ya amshe.

“Exactly this us unlike me, ni kaina al’amarin ya zame mani bak’o, ban tab’a tunanin akwai abinda zai zo ya sanya ni kasa controlling duk wani issue da ka iya taso mani ba,ina cikin wani yanayi aboki.”

“Aboki kana ji na ko? This issue seems complicated, why not inyi branching kaduna jibi in ina dawo wa daga seminar d’in dana gaya maka zanyi attending gobe a abuja, in yaso sai muyi maganar a nutse, ko ya kagani?.

” How i wish akwai wannan time din, bilal zancen da nake maka gobe hajiya zata idasa kashe mani ragowar rayuwa, while tana k’ok’arin yin hakanne bisa laifi  da ban aikata ba”

“Oh God, wai wani irin laifi neh haka take tuhumar ka da shi?.

” Tana accusing d’ina da yi wa d’iyar ta fyad’e.” safwan din ya bashi amsa.

Ya katse shi” What kana nufin ramlah”? Amma ya akai haka? Ta yaya ma wai? “

Shiru ya ratsa na wani d’an lokaci, kafin daga bisani bilal d’in yace” I thought ramlah was the last person you can share your bed with”?

“Shiyasa nake mamakin yanda yarinyar ta dage iyakar iyawarta tace ni ne mutumin da nayi mata fyad’e, aboki how could i? Iskanci na bai kai wannan hurumin ba”.

“Ikon Allah, akwai sark’ak’ya cikin lamarin nan safwan, dole sai munbi a hankali xamu fahimci komi, amma yanzu meye abin yi? Tunda kace a gobe za’a d’aura maka aure da ita”

“Kafi kowa sanin bazan tab’a iya zaman aure da ramlah ba, apart from rashin son ta da banayi, kai kasan komai, kasan b’oyayyen sirri nah, shin ta yaya zanyi in fahimtar da hajiya ta gane manufata?”Kasan babu wanda zai yadda da abinda zaka kai musu, in fact kowa ma na iya maka kallon mahaukaci idan ka tunkare su da zancen nan, let’s find another way out”. +

“Okay dama this is what I’ve finalized…. Idan sun da’ura auren, ni kuma a a goben still zan saketa ba tare da sanin kowa ba, inya so sai muje munemi wani malamin a maida auren kan ka, a washegari tunda ban daura mata idda ba, amma zancigaba da zama a matsayun mijin ta a idon duniya, while while you will be the real husband to her. ” 3

Bilal d’in ma kasa magana yayi tsabar kad’uwa da jin furucin na mainasara.

Hakan yasa ya budi baki da k’yar yace” Safwab are you out of your mind? “muryarshi dauke da tashin hankali mabayyani.

***
Nabila ta cigaba da bin ta da kallon tausayi , hak’ik’a ramla abar tausayi ce, wannan shine gaba kura baya sayak’i.

“Kiyi wa Allah ramlah ki bar kukan nan haka, for God’s sake ta yaya kike so hankalin mu ya kwanta in kina cikin irin yanayin nan” 3

Bata kulla ta ba, ballantana ta sanya ran zata yi shiru, basu san ya takeji bane, basu san wani hali zuciyar ta taje ba, basu san d’acin da zuciyar ta ke d’and’ana ba, haka zalika ba su san zafi gami da azaba na rasa budurci ba  ta hanya da bata aure ba, k’warai da gaske ba su san rad’ad’in fyad’e ba, haka zalika ba su sab zafin k’ryatawa da tozarci ba. 1

Hak’ik’a da sun sani, da basu haneta da zubda hawaye ba, da sun taimaka mata wajen ganin ta k’ara k’aimi wajen fitar da zafafan hawayen bak’in ciki, da sun bada gudummuwar su wajen ganin ta sami sassaucin halin da zuciyar ta take ciki, ko da kuwa ta hanyar daina bata hak’uri neh, kaico da wannan bak’in ciki maras misaltuwa da take ciki.

Ta sake rushewa da sabon kuka, zuciyar ta nacigaba da yi mata zogin da bata fata ko makiyinta neh ya tsinci kansa a irin shi.

A lokaci guda kuma ta cigaba da ambaton  Allah , tare da fatan inama Allah zai dauki ranta ta huta.

(Wa’iyazubillah, wannan kuskure neh babba, hak’ik’a musulmi na k’warai shine wanda yake rungumar k’addarar shi da hannu bibbiyu, a lokaci guda kuma yayi fatan cin jarabawar da Allah ya qaddare shi da ita , ba ya kyautatuwa ga mumini na k’warai ya sare da al’amuran rayuwar shi, wanda har takai ga mutum na neman mutuwa, don kurum yana ganin hakanne kad’ai hutu da kuma tsira a gareshi. Cikar mumini shine yadda da k’addara mai kyau ko kishiyarta, sa’annan rungumar k’addarar da hannu bibbiyu da kuma jajircewa wajen ganin cimma jarabawa shine cikar Jajircaccen rai mai fatan dacewa, a lokaci guda kuma godewa Allah bisa k’addarorinmu abu ne mai matuk’ar kyau. Allah kabamu ikon yarda da k’addara mai kyau ko akasin hakan, tare da bamu ikon cin jarabawar mu amin ya rabbi). 5

Shigowar hajiya da inna dakin yayi daidai da saukar wasu zafafan kwalla ta gefen idanun ta da suka dade da chanza kamanni.

“Oh ni rakkiya, yarinyar nan ba dai tun dazu kukan nan naki bai k’areba, kina son sanya wa kanki hawan jini neh da k’uruciyar ki”? Cewar inna a yayin da tayi karo da halittar ta ramlan. 1

“Hajiya ta cigaba da bin ramlan da kallo a yayin da itama hawayen ke son subuce mata.

  ” Ramlah ina rok’onki a karo na saba’in da kiyi hak’uri, ki dauki hakan wata k’addara ce cikin shafukan k’addarorin ki, ki rungume su da hannu biyu, ki kuma roki Allah ya kawo maki sassauci da mafita cikin lamarin, hak’ik’a idan kikayi haka bazaki tab’e ba. “

Ta numfasa, kana ta cigaba” Ramla keh yarinya ce yanzu, bazaki tab’a fahimtar cewa abinda nake shirin yi miki gata ba ne sai nan gaba,nasan ya kike ji yanzu, kina ganin kamar bansan mi nakeyi bane zan daukeki in kaiki gidan mutumin da bai dauke ki abakin komi ba koh?. ” 3

” Ramla bazan tab’a kaiki inda za’a cutar da ke ba, kinfi kowa sanin hakan, haka zalika safwan nice nan mahaifiyar shi, hak’ik’a nafi kowa sanin waye safwan, don haka ina hadaki da girman Allah da kiyi hak’uri kicigaba da addu’ah da yardar Allah komi zai zama tarihi. ” 2

Daga haka ba ta k’ara cewa komi ba ta umarci nabila da ta danno mata lambar babban limamin massalacin jumaah da ke nan unguwan su.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]