[Advertisements⬇️]

SAWUN BARAWO CHAPTER 10 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SAWUN BARAWO


CHAPTER 10


“Hey… Hey, will you please calm yourself down and listen to me.” Bilal din yai hanzarin katse shi daga makarar da safwan din yai masa.

Maimakon ya sake shi, sai sake matsar shi da yayi zuwa jikin nasa, har yanzu kuma jikin nasa bai fasa rawa ba.

“Buddy stop playing with my intelligence and explain the whole damn thing…. “

“Oh my God, toh da shak’ar d kaiman zanji ko kuwa da makurenin d kayi? A hakanne zan maka bayani?”

Sakin shi yayi yana mai maida numfashi, kana a hankali yace “Please tells me what i don’t really know.”

Hararsa Bilal din yayi, ba tare da ya sake furta komi ba kurum ya zari keys din mota yayi hanyar waje da sauri, ko kafin kace me shima Safwan din ya mara masa baya a sittin.

Zaman Bilal din cikin motar yayi daidai da bude kofar dayan side din da Safwan din yayi shima ya zauna, lokaci guda yana maida numfashin gudun da yayi

Jjn shiru Bilal din yaki tada motar ya sashi waigowa yaji ba’asi, amma kalar kallon da Bilal din ke sakar mashi ya snya shi kallon jikin sa a hankali, babu komi jikin s face farin tawul din dake daure a k’ugun sa, saikuma bathroom slippers a kafafun sa, daga haka bazamu rage ba, ba zamu kara ba, babu komi a tattare da shi. 3

“Kai malam inzaka ja mota kaja mota mutai inga matata, meye aibuna a hakan?” 3

“Wait, Dude are you kidding me?” Bilal din ya katse shi, fuskar shi da alamun mamaki.

“Kidding you as in how? Wai don Allah don annabi meke damunka ne Bilal? Wane irin rashin imani ne iri wannn, sati kusan biyar zuwa shidda banga mata ta ba, har kuma kana gaya mani I’m i kidding you?such cruelty.” 3

“Eh ka fadi ko me zaka fada, amma baka bi na a haka wallahi, i still have some shame in me.”

Sanin kafiyar Bilal ya sanya shi fitowa daga motar a fusace ya juya, har yakusa isa bakin kofa ya juya gami da cewa,

“Ka rufa mani asiri aboki ka jira ni, minti uku yanzu zan zura boxers in fito.” 11

Toh kurum yace mashi, domin ya samu ya shige ko yayi wucewar shi, aiko yana ganin billewar shi yai wa motar key a guje, wanda hakan yai snadiyar dawowar Safwan din a guje yana kwala kiran sunan shi

Juyawa yayi a fusace yakoma ciki da niyyar yayi maza ya dauko wani key din ya bi shi, amma kuma shigar sa dakin nashi yayi daidai da kiran wayar shi da akayi, tsaki yayi ba tare da ya kalli screen din wayar ba, hakan yasa bai lura da sunan me kiran nashi ba.

Ji yai gaba daya jikin shi ya mutu tun bayan suturta jikin nasa da yayi, wata iriyar kasala da faduwar gaba ke mamaye ilahirin jikin sa, haka nan kuma zuciyar sa ta kasa gasgata mashi cewa yau din nan zai sake sanyata a idunun sa bayan wasu lokuta masu tsayi, sosai yake jin zuciyar sa na tsalle, lokaci guda kuma wani irin tsoro na baibaye zuciyar tasa, wanda shi kanshi ya rasa gane dalilin hakan.

Turo kofar dakin nashi da akayi ya maido dashi cikin hayyacin sa, kakus ce a tsaye rike da kugu, ga nabila a gefen ta da wayar kakus din a hannun ta, irin yand kakus din ke huci shi tabbatar da bala’in d ke cinta a rai.

Da hanzarin sa ya mike ya nufo ta, kana lokaci guda kuma ya sanya hannayen sa ya janyota ya zaunar kan couch din dake zaune a dakin, zaunawar ta yayi daidai da kai mashi dundu da tayi a gadon bayan shi da babu ko riga.

“What!Sweetheart lafiyanki kike neman karya man baya?”

“Ungo nan” ta sakar mashi dak’uwa, nace “Ungo nan yaron kirki, don ubanka baka ga tarin kiran dana rika yi maka a waya bane?” 2

STORY CONTINUES BELOW

Sai yanzu ya gane aahe itace ke ta kiran wayar tashi dazu kenan.

“Haba sweetheart yawa kike, ya za ai haka nan inki daga kiranki? Kema kinsan its impossible, bana cikin hayyaci na ne time din da kike kiran.

Ya karasa maganar yayi da yake dora kanshi bisa kafafun ta, hakan yasa tace,

“Ni daga ni, aikin bnza nazo da labari na da dumi dumin shi ka kwapsa man.”

Habarta ya rike yana mai jagula tamulalliyar fatar kumatun ta, alamun lallashi, “Haba sweetheart, so kike yan bakin ciki irin su oh oh sui mana dariya,share kawai ki bani labari, nima akwai labarin da zan baki dama.”Hararar Nabila yayi dake zaune bakin gado ta zubo masu na mujiya babu ko kiftawa, itama kakus din maida kallon ta tai kan Nabilar gami da yin kicinkicin da fuska alamun zata gurza RM. +

“Munafuka kika zubo mana wasu idanuwa nan naki masu kama da na mayu, ga wasu kunnuwa nan kin baza kina nade mana zance, zaki fice ki baceman da gani ko kuwa?”

Hngame baki Nabilan tayi, fuskar ta kuma bayyane da mamakin zancen Innar, lallai kakus ba yar goyo bace,ji yanda tai kici kici da rai tana neman gurza mata rashin mutunci, alhalin ita taje har dakinta ta tattagota, amma ji yanzun yanda suke neman wukaqanta ta.

“You must be very stupid, sweetheart din kike wa irin kalllon nan don ubanki?”

Zumburo baki tayi gami da mikewa, “Toh ni Yaya menayi mata? Haka kurum don an tsaneni, ba ita bace tazo da kanta ta tattago ni, shine zaa wulaqnta ni.”

“La’ikahailllahu, kai kuji man yarinya da kafirar karya! A gidan ubanwa na kiraki? Ni da ganinki kawai nayi kina bina, almura mai halin mutanen farko!” 10

Gaba kawai Nabilan tayi, a ranta kuma tan kara jinjina rashin mutunci irin na kakus din.

Fitar ta yayi daidai da ihun ta d suka jiyo, tunkafin ma su fara gulamammakin da suke shirin yi, hakan yasa Safwan din ficewa da sauri domin ganin menene yasa Nabilan kurma irin ihun nan, da niyyar inyaje yaga ba wani genuine abu bane yaci uban ta hanklin sa kwance.

Turus yayi a kofar falon sakamakon ganin abinda ya sanya Nabilan irin ihun da tayi, a inda take jijiyoyin dake sadar da jini zuwa gangar jikin sa dakatawa na wasu yan sakanni, hkan yayi sanadiyar daukewar duk wasu al’amuran rayuwar shi,sosai zuciyar sa ke tsalle bisa allon kirjin sa, a yayin da yake jin tamkar zuciyar tasa na barazanar fasowa daga kirjin nasa ne, he can’t believe it, he really can’t believe what he is seeing right now infront of him!

Bangaje shin da Kakus tayi ne yayi nasarar fargar da shi,jin irin hayaniyar da falon ya dauka ya kara tabbatar mashi da abinda idunwan sa ke hnga mashi kwance kan doguwar kujera kanta bisa cinyar Hajiyar su, yayin da Nabila, Khalil da kuma Bilal sukai masu rumfa a ka.

“Kai ku matsa, ku matsa man ingani, shin wacece nan nake gani kamar Rablatu? Keh Rablatu anshiga uku ni jikar mutum hudu kece Rablatu? Ko dai mafarkin danayi dazun neh nake sake yi? Kai yaron kirki matso kaga labarin da nake son baka na sake maimaita kanshi.”

Gaba daya ta tutture su Nabilan, kana batayi kasa a guiwa ba ta janye Ramlan dake kwance kan kafafun hajiya ta maido ta kan nata kafafun, duk kuwa da cewa Ramlan duk badakalar nan da ake batasan anayi ba, domin kuwa har yanzu baccin take sharba hankalin ta kwance. 7

Bilal ne ke sakeyi wa Hajiyar bayanin yanda aka samu Ramlan, al’amarin da ya sake daurewa Hajiyar kai, kana kuma zuciyar ta take sake jinjina bakin hali irin na Kabeer din,ba shakka Kabeer ya tozarta su, kuma ya wulakanta martabar gidan su, wannan abun kunya har ina? 2

“Oh ikon Allah! keh Saratu anya a danginku babu ahalin shedanu? Don nidai kaf ahali na babu masu bakin hali irin wnanan, kinga kuwa bana ce ta bangarenmu ya debo wannan mugun halin ba.” 11

STORY CONTINUES BELOW

Ta karasa maganar bilhakki da gaskia, domin kuwa kallo guda,zakai mata ka tabbatar da cewa har zuciyarta take maganar.

Haushi da mamaki ma sun sanya Hajiyar kasa ce mata komi, illah kwnadunan hararar da Nabilan ke ta wullo wa innar, domin dama haushin dazu na nan a ranta be barta, dalilin hakan yasa tace

“Ai wallahi kakus ba dan ba dan ba sai ince kusan bakin halin nan na Ya Kabeer ke ya gado, baki ga duk gidan nan babu mai kama dake kamar shi ba?” 5

Tofa! Aifa Nabila ta taro masifa, ta taro match kuma, domin kuwa ida zancen nata yayi daidai da d’add’age k’ofofin hancin ta da tayi ta hau hura su cikin tsananin masifa da bala’i, ba tare da ta kara tunawa da Ramlan dake cinyar ta ba, ta mike tsaye a fusace da nufin tunkarar Nabilan domin yi mata kafirin bugu(kuji tsohuwa da karfin hali), mikewar tata yayi daidai da fadowar Ramlan daga kan kujerar, ji kake tiiiim ta fada bisa carpet din dake mai karancin kauri sosai ya sanya ta buguwa kadan, hakan ya taimaka wajen farkawar ta gigice tana salati. +

Habawa ai gaba dayan su sukai kanta, ana rige rigen dagata,har da kakus me shirin dambacewa, sam ta ma manta da zance masifa, domin kuwa ita din ce gaba gaba wajen daga Ramlan, koda aka dagota hana kowa matsowa tayi kusa da ita,zama tayi bisa carpet din tai kane kane sa Ramlan ta k’wak’ume, inbanda kiran,

“Sannu Rablatu, sannu kinji y’ar albarka, ince dai bakiji ciwo ba? Kai Khalilu kawo mata ruwa tasha”

Ita dai kam Ramlan babu baka sai kunne, gaba daya ta kasa gasgata me idanuwan ta ke gane mata? Shin mafarki da ta sabayi ne take yi ko kuwa gaske ne? Kwakwalwarta ta kasa tantance mata zahirin al’amarin hakan yasa ta rika bin kowa na falon da kallo, bakin ta kuwa yayi matukar yi mata nauyin da takasa cewa ko d tak ne.

Idanuwan ta ne suka sauka kan mutumin da ko a mafarki ne bazata kasa tantance shi ba, ba cikin falon yake ba, hasalima duk badakalar da suke a falon bai karaso ciki ba tun sanyata a idanun sa da yayi, yana nan kafe a jikin bangon corridor din dake kallon cikin falon, shi bai koma ba kuma bai shigo ciki ba,kananan idanuwan nan nasa masu kama da na mashaya neh sauke baro baro bisa fuskarta, tun dazun da yake kallon ta ko kiftawa ba yayi ya tsohon maye, kallon juna suka cigaba da yi, kowannen su da abinda yake ayyanawa a zuciyar sa.

Kusan zuwa yanzu falon kowa yayi zugudi gami da sunkuyar da kanshi yana jinjina wannan kallon kurullah da Safwan din ke bin Ramlan da shi, domin kuwa ita tuni ta sunkuyar da kanta kasa tana godewa ni’imar ubangiji a gare ta, hakika koma ta wani hali ta dawo cikin mutanen da tafi so kaf rayuwar ta, hakika pretending din da ta koyawa zuciyarta don kubuta daga hannun Kabeer din yazo karshe, ashema babu rabon zata sha wahala sosai gurin subucewa Kabeer din, domin kuwa yanzu ko da wa Yaya Kabeer din ke yawo bai isa ya sake guduwa da ita ba kuma…. Alhamdulillah Allah abin godiya, ta ayyana hakan a ranta. 6

“Kai yaron kirki ko maye nan yaganka ya kyale, wannan irin kallon k’urullah har ina?” 6

Muryar kakus din ta katse shirun da falon ya dauka, hkn yasa kowa na falon darawa,amma gogan naku ko a jikin sa, da’alama har yanzu bai k’oshi da kallon kazar mayun tashi ba, domin kuwa zuwa yanzu har wasu ruwa ne suka taru a kasan idanun nasa,kallo guda zakai masa ka hango zallar so, kauna, bege da sha’awar matar tasa a kwarmin idaniyan nashi. 2

“Mammy!” muryar Ramlan ta doki kunnuwan su, da sauri Hajiyar ta matsa kusa da Kakus din ta kama hannayen Ramlan ta damke, yayin da hawaye d take ta boyewa samun ikon zubowa, a hankali tasa bayan hannunta tana sharewa.

“Y’ar gidan Mammyn ta,munyi kewar ki ba kad’an ba, kiyi hakuri da yanayin da kaddarar rayuwa ta kaiki kinji ko? Ki dauka hakan wasu shafuka ne aka bude daga shafin kaddarorinki kinji ko Ramlah? Allah na nan, kuma shine zai sakamaki akan dukkan wani zalunci da akai maki, fatana dai babu wata matsala? Kuma Kabeer din be kuma yi maki komi ba?”

Da sauri ta girgiza kanta alamun babu komi,hakan yasa su jiyo ajiyar zuciyar da Safwan din ya saki a hankali.

A hankali ta maida dubanta gurin su Nabila, murmushi ta sakar musu kana tace “Ya Bilal, Nabila, Khalil na same ku lafiya? Ina su Yaa Salim?

Gaba dayansu murmushin jin dadi suke sakar mata, wanda zuwa yanzu Nabilan ta samu ta rab’i jikin Ramlan da kyar sakamkon bake baken da kakus tayi ta hana kowa matsowa kusa da ita.

“We miss you sister, but Yaa Safwan misses you alot more ” Nabilan ta rada mata a kunne, hakan yasata yin dariya mai dan sauti gami da sake maida dubanta bangaren da Safwan din ke tsaye yana binta da idanu, hakan kuwa ya ankarar da Innah, kafin kace me har ta ture Nabilan daga jikin Ramlan, itama kuma ta mike tsaye, kan ta maida duban ta ga kowa dake falon tace.

“Toh malamai, hamshakai,tunda dai kowa ya gaisa da ita, yanzu kuma lokaci ne da kowa zai kama gabnshi abaiwa Yaron kirki damar ganawa da matar shi, sabida Allah ma dai wallahi bama ku da imani, wata da watanni watanni yaro bega matar shi ba,amma har sai antuna maku ku bashi matar shi su gana? Wane irin bakin hali ne haka en gidan nan kuka koya?” 27

Shiru kowa yayi yana binta da idanu, ba shakka kakus er bala’i ce, kaji ta, kmar ba itace tai bake bake ba ta hana kowa yin katabus da Ramlan, amma yanzu ji abin da take cewa, ganin sun zuro mata n mujiya yasata juyawa gami da daga muryarta yanda Safwan din zai jiyo ta tace,

“Yaron kirki mazo zaka sungumi matarka kuje kuji d’umin juna, da’alma akwai yan bakin ciki a gidan nan,maza maza zoka dauki abarka kafin ka sume mana a gurin nan, wannan kallon naka ya fara fita daga musulunci.” 9

Daga haka ta fisge hannun Ramlan dake cikin na Hajiya, ji kake k’iiii ta ja Ramlan har gaban Safwan dake tsaye yana kare mat kallo, babu ko digon kunya a tattare da shi. 6

“Ungo, maza ku tafi daki, ai kamayi kokari yaron kirki, watanni kusan biyu ai ba was bane.” 23

Zuwa yanzu kunya tagama lullube kowa dake zaune a falon, mamakin su bai kara ba sai da suka ga Safwan din ya sungumi Ramlan gaba dayan ta ya juya ya nufi hanyar dakin sa da ita. 32

Yuuuuuu suka bishi da idanuwa, bakuna a sake, a yayin da tafin kakus ya rika karade ilahirin falon, ji kake raf, raf, raf, raf. 21

“Angaishe ka Yaron kirki, yaron albarka!”

***
Ba shakka ya shammaceta, domin kuwa koda wasa bata taba tunanin sunkutar ta zaiyi haka ba,shin wannan wane irin abin kunya ne Safwan yaja mata?Tanayin dukkan zntuttukan zucin ne a yayin da take ta wutsil wutsil da kafa akan ya aje ta, domin kuwa sosai bakinta yai mata nauyin da ta kasa yin magana.

Bata tunaninma yanajin me take cewa, mussaman da suna isa dakin ya dire ta gami da hadeta da bango,ba tare da saninta ba sai ji tayi duniyarta na juya mata, sosai ta rika ganin wasu taurari na yawo a tsakiyar kanta,a yayin da sakonnin dake fita daga bakin shi zuwa nata ke matukar samun tasiri ga dukkanin ilahirin jikin ta,yanayin matsar da yayi mata, da kuma yanda yake had’ama wajen sumbatar bakin nata, zai tabbatar da tsananin kewartan d yayi, mussaman yanda ko’ina na jikin shi keh rawar mazari.

Tun tana kiciniyar kwacewa har itama tafara amsa saqon, hakn yasa tasanya hannayen ta bibbiyu gamida tallafo keyar shi wajen bashi access ba tare da sanin tayi hakan ba, al’amarin da ya kaisu zubewa bisa makeken gadon dake dakin,tsaya fadar kalar soyyayar da yake gwada mata bata baki ne, mussaman wasu zantuttuka masu wuyar fadi dake fita daga makoshin sa cikin halin fita hayyaci,hakan ya sanyata sanya kuka a hankali. 1

Jin kukan nata ya taimaka wajen dakatar dashi daga shirin cire mata baki da yake,cike da zallar son ta yake kallon idnunta dake kallon nasa suna fidda ruwan hawaye, tsintar halshen sa tayi yana lasar hawayen,a yayin da bakin shi bai fasa furta kalmar “I miss you,i miss you so damn much.” ba.

Ita dai kallon shi take kamar taga sabuwar halitta, gaba daya ya canza mata,sannan ita kanta tirr take da zuciyarta da gangar jikin ta dake jin dadin abinda Safwan din ke mata, gaba daya yagama kashe mata jiki,hakan yasa duk inda yayi da ita nan take bi.

Ganin yana shirin rabata da rigar jikinta ya sanyata hambare shi da dukkan karfint, kasantuwar jikin shi duk a mace ne ya sanya shi kaaa tabuka komi, baya ga rigingine da yayi yana maida numfashi da sauri da sauri, bata b’ata lokaci ba tai hanzarin mikewa ta nufi hanyar waje da gudun ta, hakan yasa ko ta kan d’ankwalin ta bata bi, hakan kuwa ya taimaka wajen bayyanuwar tumulin gashin kanta da yai watsa watsa ya yamutse dalilin Safwan din.

Hanyar bedroom din Hajiya tayi da dan gudun ta, sabida tana ganin nan d’inne kad’ai mab’oya kuma matsira a gare ta,tsabar rudewa da son ganin ta cimma dakin na Hajiya yasa bata lura da Kakus na tahowa ba, hakan ya taimaka wajen cin karo da juna da sukayi. 1

Da sauri tai hanzarin riko Innar, wacce kiris ya rage taci k’asa,kana kuma bata b’ata lokaci ba ta hau baiwa Innar hakuri, sanin halin masifa na kakus din. 2

“Yi hakuri Inna ban lura dake bane,kiyi hakuri.” Ta ida zancen tana mai shafa goshin kakus din da tafi ganin ta bugu a a gurin.

Ture hannayen Ramlan tayi, ta hau zambada mata kallon uku saura kwata, kana a d’age ta kalli Ramlan tace,

“Toh waini Rakiyya, me ma ya fito dake neh yanzu har kike kokarin fasa man goshi? Inace yanzun nan yaron kirki yatafi dake domin ku gana?”

Zumburo baki tayi gaba gami da dauke fuskar ta, yanda zata ji dadin kauce wa tambayoyin kurullar tsohuwar, hakan yasa tace,

“Kaji Innah, toh ai mungama gaisawar, shine zanje in watsa ruwa, in dan huta.”

“Eh lallai kuwa kungama gaisawa, shiyasa naganki a firgice haka kamar wacce aka koro, kai babu ko d’ankwali.”

Ta ida maganar tana yiwa Ramlan kallon karki maida karuwa yar iska mana.

Dan bubbuga kafa Ramlan tayi alamun fara gajiya da tambayoyin na Kakus, hakan yasa tace, “Allah inna shi yace in taho.”
“Ai shi yace ki taho? Yanzu yanzun nan daga shigarku har yagaji dake yace ki taho?” 4

Da sauri ta daga kai alamun “Eh”
“Toh ai inda ba k’asa nan ake gaddamar kokuwa, wuce muje inji daga fatar bakin shi.”

Idanuwa a zare tace, “Haba don Allah Innah, toh waini karya zanyi maki neh?”

“Nidai bance bah, haka nan jikina ke bani k’aryar ce wannan karon, kinga wuce muje inji daga gareshi.”

Daga haka bata jirayi komi ba ta iza k’eyar Ramlan suka nufi dakin Safwan din, a inda Ramlan ta rika jin tamkar ta d’ora hannu a ka ta fasa ihu.

“Gaskia matar nan k’ajaga ce wallahi.” Ta ambaci hakan a kasan ranta.

Yana nan kwance inda ta barshi, da’alama ma baya tare da mutanen nigeria, ganin yanda idanuwan shi ke a lumshe, kana lokaci guda yana sauke wani irin numfashi da dan k’arfi, shigowar su baisa ya motsa ba, bare kuma yasan su waye suka shigo.

Da sauri Kakus din ta nufe shi tana kiran sunan shi.”Yaron kirki, kai Yaron Kirki bude idanuwan ka inji kaine da kanka kace yarinyar nan ta koma dakin su?”

A hankali ya bude idanun nasa gami da sanya su cikin na Kakus din dake ta marin fuskar shi da sunan tana tashin shi neh.

“Sweetheart an tab’a gaya maki cewar kina da hayaniya?” 24

Dakatawa tayi daga abinda take,kana lokaci guda tai kicin kicin da annurin fuskar ta,kana ba tare da b’ata lokaci ba kuma ta daddage iya k’arfin ta ta zuba mashi dundu a bisa kirjin sa da babu ko singlet ballantana riga.

Da sauri ya rauntse idanuwan shi yana shafa gurin, domin kuwa ba shakka kakus din ba laifi kafirin zafin hannu gareta, hakan yasa yace,

“Shiiiit,Sweetheart ba’a tab’a gaya maki cewar kina da zafin hannu ba? You almost break my chest for heaven’s sake.” 4

“Don ubanka ba’a taba gaya man ba sai yau, ni zakai wa iya shege da rana tsaka?”

Juya kanshi yayi inda Ramlan ke tsugunne tana cuna baki gaba, hakn yasa ya shagala da kallon Ramlan, mussaman yanda sumar kan nata take a yamutse, kuuma a zube bisa kafad’ar ta, hakan ya taimaka wajen k’ara mashi tsananin so da begen ta. 4

Sosai ya manta da Kakus dake kusa dashi tana zuba ruwan jafa’in masifa,domin kuwa sam yadaina jin Kakus din,ruhi da gangar jikin sa na can na misalto mashi wani sabon yanayi dashi da Kazar mayun shi.

“Yau ga bakin maye! Kai yaron kirki kanka daya kuwa?” Kakus din ta d’ala mashi duka, hakan yasa yadawo hayyacin sa, gami da maido da kallon shi kan Tsohuwar kakar tashi.

“God! Sweetheart why won’t you let me be neh for goodness sake?”

Dakai da turancin duk kunci uwarku Saratu! Wani irin maitane haka zaka rika kallon yar mutane kamar kasamu talabijin?wannan ai kallon iskanci neh!”

“Ai dama ni dan iskan neh sweetheart, ba’a tab’a gaya maki bah?” 11

“Lah! Yau na shiga uku, ban lalace ba ni Rakiya! Yaron kirki dama dan iska ne kai bamu da labari? To wai tsaya ma yaushe ka zama dan iskan ban sani ba?” 1

“Ai na dade da zama dan iska Sweetheart, tun ranar da kukai man aure da waccan Goddes din nazama tantiri ai, ba’a taba gaya maki ba dama?” Ya ida zancen yana kallon Ramlan da ta dago fuskar ta tana kallon su baki sake.

Harar shi tacigaba da yayi, domin zuwa yanzu tafara gane cewar ita yake nema ya maida yar iska mai shan taba ta k’eyah. 3

“Fitsararre, ni dama tambayarka nazo inyi, dagaske kai kace Rablatu ta koma dakin su? Don gaskia ban yadda da maganar ta ba da tace mani kai ka sallamota.” 1

Kallon Ramlan yake ya d ta rausayar da kai tana rok’on shi da idanu akan ya rufa mata asiri, al’amarin da ya taimaka sosai wajen kara cusa soyayyarta cikin zuciya da k’albin sa. 2

“Eh ni nace taje tai wanka,ta kwanta ta huta, baki ganine tana bukatar hutu sweetheart.” 1

Jin shiru Kakus din bata ce komi ba ya sanya shi maido da idanuwan shi kanta, ga mamakin sa kallon banza kawai take zuba mashi, hakan yasa shi rungumota yan dariya qasa qasa.”Kai ni dalla can sake ni, ubanwa zaku maida y’ar iska? Toh bari in maku gwari gwari kwafi fahimta, tunda naga alamar baku san zuru ba.” Ta gyara zaman d’ankwalin kanta kana ta cigaba…. +

“Eh naga alamar ku sam baku san annabi ya faku ba, ayi ku dake baku san ciwon kanku ba, wata da watanni bakw tare da juna amma ace yanzu mintuna basu fi ashirin ba da haduwarku har kun gunduri juna kuna korar juna? Wace iriyar toshewar basira ce haka yaron kirki?” 7

A can kasan ranshi yake sake jinjina karfin hali irin na Kakar tashi, gaba dayan ta bata da magnitude bare direction, yanzun nan zata ce abu kaza, kafin kuma mutum ya ankare ta canza, kamar wata hawainiya.

“Toh yanzu Sweetheart me kike so ayi.? Yayi hanzarin tambayar ta, domin kuwa sosai Kakus din tafar sa mai ciwon kai, gara tayi tayi ta fita ko ya sarara.

“Yoooh ni kuwa me nafi so da ya wuce inga kun kara gaisawa da kyau da kyau, gaisuwa sosai irin ta sauran ma’aurata nake nufi, shin wai Yaron kirki ko baka so inga jinin ka ne kafin in mutu?” 8

Ramlah dai sake sanya kanta tayi a tsakankanin cinyoyin ta yayin da kunya tai mata shigar burtu, ba shakka sai dai mutum yaga Kakus, amma wane mutum yace zai maganin ta,Kayyasah!

Shi ko gagan naku kamar jira yake ya hau zabga murmushi yana kara jin kaunar Ramlan na bin lungu da sako na jikin sa, ba shakka he really need a baby with this damsel, sake kallon inda take yake, yayin da tunanin sa gaba daya ya raja’a akan son ganin ya dasa k’wan shi cikin mahaifarta. 13

Lumshe idanuwan sa yayi yana imagining dinta dauke da babynsu tana shayar da shi. 7

“Ko bakaji abinda nace bane Yaron kirki?” Muryar Innar ta dawo dashi hayyacin sa, hakan yasa da sauri ya rik’o hannayen Innar yana murmushi yace,

“Sweetheart ai bazaki mutu ba sai idanunki sun gane maki Kazar mayu da jariri na tana shayar da shi, infact hatta kannen sa guda goma sha daya da zasu biyo bayan shi duk sai kin gansu in sha Allahu.” 1

Aifa shikenan Kakus aka hau wangale wawulo ana zuba dariyar jin dadi, kana murya dauke da farin ciki da annuahuwa ta dubi Ramlan tace, 9

“Yawwa y’ar albarka maza tashi ki tafi gurin mijinki ko mafarkina yafara tabbata, Allah dai ya amsa a yau dinnan a samu tattab’a kunne na, maza tashi kinji Rablatun Innah.” 1

Rasa ma abinyi Ramlan tayi, al’amarin na Inna nema yake ya shallake shekarun ta, wane irin zance ne haka sukeyi itada jikan ta? Lallaima Ya Safwan dinnan! Babu mugun dan rainin wayo irin sa, ita dinnan ce yake tunanin zata hada jiki da shi har ta kai ta ga haifa mashi yara? Ba shakka ya zauce idan har abinda yake hangowa a tattare da ita kenan! Such nonsense! 2

Ba tare da ta lura ba Kakus din ta riko hannunta gami da mikar da ita tsaye, ga wani murmushi ne sai zabga shi take, ita a dole ga wacce aka dad’ad’a mawa.

“Yauwa yar albarka, kizama mai biyyayah ga mijinki kinji koh? Tashi maza kije a gaisa da kyau, da kyau, kar inji, kar ingani,nan da wata tara masu zuwa nake so mubawa mahassada irin su Kabeeru kunya!” 5

Ta juya kan Safwan tace,

“Ka dage sosai Yaron kirki, dole ne musha d’amarar takawa wancan kafirin mazan burki, Allah dai yasa ayi a sa’a, ni bari inje nima in dan kwanta.” 13

Tana ganin tabbatuwar Ramlan a hannun Safwan din ta juya tana hamma ta fice daga dakin, bakin ta bai yanke ba wajen kwararo masu addu’ar samun sa’a da dacewa. 6

Fitar ta yayi daidai da Sanya kukan Ramlan a shagwabe, hakan yasa Safwan din rudewa ya hau tambayar ta ko lafiya?

Sai da ta harare shi kan tace, “Ni wallahi ba yar iska bace, Allah ma yakyauta in haihu da kai.”

Ta ida zancen tana mai sake kware baki a hankali tana kuka.

Rumfa yayi mata da faffadan kirjin sa yana mai cigaba da kasheta da idanuwan nan nashi, murya a shake yace,

“Na rantse da Allah yau sai kin tantance nauyi na!i mean its a must to have you all by myself today honey! ” 18

Daga haka ya cafki labbanta cikin wani irin salo mai wuyar fassarawa.

***
KABEER FA?

Farkawa yayi a firgice bisa wahalallen baccin da yasamu kwashe shi a daren na jiya ba tare da sanin sa ba,kana cikin ‘yan dak’ik’a kad’an zuciyar shi ta samu nasarar tariyo mashi abinda ya faru da shi a daren na jiya, al’amarin da yayi sanadiyar zamowar shi daga kan doguwar kujerar da yake kwance a kai, dafe kanshi yayi cikin halin bakin ciki da juyayi, babban tashin hankalin sa shine, lagos ba karamin guri bane da zai mike kanshi tsaye ya fara neman Ramlah, abu na biyu kuma shine, a halin yanzu bashi da ikon da zai kai cigiyar Ramlan kafafan yad’a labarai, mussaman yanda yasan da cewa kaf yan gidansu sun san cewa Ramlan na hannun sa, kenan hakan yana iya zama kalubale ga rayuwar shi babba.

Sauke numfashi yayi cike da faduwar gaba, a ayayin da yake sanya hannayen sa duka biyu yana shafa sanqon kanshi, kallo guda zakai mashi ka hango zallar tsurewa da rashin sanin abinyi bayyane bisa salahar fuskar shi, ba shakka da yasan fitar nan ta su zata zama haka, hakika da ya hakura sun wuce tare da Taleeb, duk da abubuwan da suka faru ba su faru ba,kaico!

Rashin sanin takamaimain abinyi ya sanya shi sake mik’e k’afa yana b’arza kukan takaici, sosai zuciyar sa ke k’una bisa wannan iftila’in da ya fad’a mashi da rana tsaka!kwata kwata kwakwalwarshi tsaya tayi cak, har yanzu tunanin sa yakasa bashi wanda ke da sa hannu wajen dauke masa abar kaunar shi,dama sam tunanin sa bai kawo mashi Safwan ba, sanin irin halin da ya baro su bisa rashin sanin takamaiman inda Ramlan take, toh kuwa idan haka ne me yayi wa wannan taxi drivern da zai dauke mashi abar son sa haka nan siddan? Dam gabanshi ya sake wata fad’uwar sakamakon tunawa da yankan kawuna da ake fama da shi a garin na Lagos.

Zumbur ya mike tsaye yana mai cigaba da sharara kuka cike da tashin hankali, ba shakka ba zai yafe wa kanshi ba idan har Ramlah ta mutu ta barshi, gara kawai yakoma kadunan kawai ya sanar da su abinda ke faruwa, inyaso dole su had’a k’arfi da k’arfe a ceto rayuwar abar son sa.

Gama tunanin nasa keda wuya ya juya ya shige dakin baccin su domin kwaso abubuwan da yake da bukata, ko sauya kaya bai tsaya yi ba, ballantana a kai ga batun yin wanka, daga haka ya sanya wa gidan key,sannan ya tari taxi zuwa airport.

***
“Don Allah ya isa haka kibar kukan nace koh bakyaji na?”

Sake cusa kanta tayi cikin pillow tana hawaye,sosai takejin inama kasa zata iya tsagewa biyu ta had’iyeta, da ta huta da dimbin kunyan dake bibiyar rayuwar ta! Shin wai wannan ma wane irin abun kunya neh? Taciga da tambayar kanta yayin da idanun ta basu fasa kelayar da ruwan hawaye ba.A tarihin rayuwar ta,bata tab’a shan azaba ba kwatankwacin wacce tasha a hannun Safwan jiya da yamman ba,harda kuwa fyden da Kabeer yai mata a ciki,a iya karance karancen ta, da irin labarurrukan da take ji, macen da ba budurwa ba bata sake jin zafi idan namiji na tarawa da ita a karo na biyu, sanin cewar wani ya riga da ya keta mata budurcin ta tun fil’azal, amma sai dai me?Zafin da ta sha a hannun Safwan din bana wasa bane, dukkuwa da cewa shi din ba fyade yayi mata ba, asalima duk bori bori da fizge fizgen da ta rik’a yi sai da ya san yanda ya kashe mata jiki da salon k’aunar shi har bata san lokacin da ta sakar mashi jikin ta ba, ta kuma biye mashi ba tare da sanin tana hakan ba domin ganin sun cimma manufar abunda suka fara. 5

Tashin hankalin ta bai fara ba sai da al’amari yazo kankama gadan gadan, amma sai me kuma?Zance ya sha banban, wanda dukkan su suna sane da cewar ita din ba budurwa bace sabuwa dal! Duk kuwa da cewar sau daya ne hakan yataba faruwa da ita, amma ko yaya ne ya kamata asamu hanya a karo na biyu,al’amarin da ya dugunzuma hankalin ta ta rika mutsu mutsun ture Safwan din, ganin yana neman aikawa da ita lahira, amma gogan naku yayi nisa bayajin kira, dukkan burin shi a wannan lokacin bai wuce ya isa inda ya dade yana mafarkin isa ba,hakan yasa ba tare da sanin sa ba, kuma cikin halin fitar hayyaci ya zage damtse, gami da bada himma domin son cimma manufa.
Ihun da ra kurma sai da ya ratsa lungu da sak’o na kusurwar dakin,kana ta cigaba da rusa ihun kuka cikin halin jigata,a inda al’amarin ya zama biyu, domin kuwa da mai aikin, da wanda ake aikin da ita dukkan su biyun kuka suke, sai dai kukan nasu sun banbamta,d’aya na azaba ne, yayin da dayan yakasance na zallar nishadi da gamsuwa neh.

Bai lura da aika aikar da yayi ba sai bayan ya dawo hayyacin sa,gaba daya inbanda zufa da hawaye babu abinda ke fitowa daga ilahirin jikin ta,idanuwan nan kuwa sunyi luhu luhu alamun shan kuka,gaba dayan ta ya tattaro bisa kirjin sa ya kankame, a yayin da k’asusuwan da tsokar naman jikin sa ke amsa kuwwar nishadin da baiwar Allahn nan ta sanya shi, bayajin yataba, ko kuma iya tuna ranar da wata ‘ya mace ta sanya mashi nutsuwa irin wacce yake jin kanshi ciki a yau!duk kuwa da irin dimbin matan banzan da yai mu’amala da su a baya,kwarai da gaske a duk iya shegen shi da yayi na neman matan shi, ko da sau daya bai tab’a tarawa da wata mace ba batare da yayi amfani da condom ba, yau itace rana ta farko a tarihin rayuwar shi da ya kusanci wata ‘ya mace a asalin namijin shi,ma’ana ba tare da condom ba,al’amarin da ya k’ara taimakawa wajen ficewa daga hayyacin sa, ba shakka Kazar mayun shi babu irin ta a duk fad’in duniyar nan. 9

Hajiya ce ta sake katse mata tunanin da takeyi.

“Ramlah wai bazaki bar tunanin nan ba ki tashi ki sake shiga ruwan zafin nan ba? Ko baki so jikin ki yadawo daidai neh?” 9

Zumbura baki tayi gaba, a yayin da idanuwanta ke sake yin rau rau alamun sake son yin kuka,ganin yanda Hajiyar ta had’e rai yasata mikewa domin shiga bathroom din, mik’ewar ta yayi daidai da shigowar Innah a fusace tana mai k’wala kiran sunan Hajiyar, a yayin da Safwan ke bin ta a baya sumi sumi yana sussune kai k’asa.Ai tana ganin Safwan din tai baya baya ta haye bisa gadon da gudun ta, kana a sukwane ta yayimi blanket ta makure, Allah yasani gaba daya bata ko son jiyo muryar Safwan a yanzu, sosai gayen ke bata tsoro matuk’a. +

Wata uwar harara Innar ta raka Ramlan da shi, kana cike da masifa ta bude baki tace,

“Yau ga shashar yarinya kai, Mijin naki kike ma wannan gudun pampalak’in? Iyyeeh Rablatu? Dodo ne shi da kike boye ma ganin sa tun jiya? Ko da yake ba laifin ki bane, laifin Saratu ne da ta daure maki gindin gujewa mijin ki, tsabar shishigi da cusa kai ba kwarjinj irin nata.” 1

Hangame baki Hajiyar tayi, gamida waigowa tana kallon Innar,tun shigowar su dakin, lallai Innah wulakancin ta ba made in Nigeria ba ne, amma inbanda haka ta yaya zata kira ma mai shishshigi? Sabida Allah ita bata ga irin aika aikar da Safwan din yai wa Ramlan ba ne? 19

“Eh kike kallona, kamar baki tab’a gani na ba, ba shishishgin gareki ba? Kinbi kinyi kane kane kin hana yaro ganin halin da matar shi take sabida tsabar baki da imani Saratu! Ke in ke akai wa haka zaki ji dadi? Nace zakiji dadi?” 1

Zuwa yanzu takaici yagama kama Hajiya, hakan yasa bata ce wa Innar komi ba ta juya inda Safwan din ke tsaye bayan Inna yana mazurai tace,

“Kai fice man daga daki tunn kafin raina ya baci,ko kuwa maganar da nayi maka ce bata shigeka ba?Safwan kana wasa dani a gidan nan koh?”

Narai narai yayi da fuska tamkar mai shirin sanya kuka, baki na rawa yace,

“Please mana Hajiya, minti biyar i just wanna know how she’s feeling neh, kiyi hakuri kiyi man rai!” Ya ida zancen yayin da idanuwan shi ke kallon inda Ramlan take a dukunkune cikin bargo tana jin su. 1

“And i said No! Halan baka da kunne ne? Wallahi ka bace man da gani kafin in sassaba maka a cikin gidan nan Safwan,naga alaman ba…….. “

“Kika ga alamar me?” Kakus din ta katse ta a fusace.

“Nace kika ga alamar me Saratu? Ni naraba ganin vakin zalunci irin wannan? K’iri k’iri kin hana yaro ya sake da matar shi? Toh wai ma una ruwanki ne da al’amarin su? Nifa da kika ganina a nan na tsani shishshigi, haba wallahi baki ma da imani Saratu, ki canza hali.” 16

Bata kula Innar ba, sanin cewa tsayawa kula Kakus tamkar sake bata wa kanka rai ne, hakan yasa ta juya gami da nunawa Safwan din hanyar k’ofa.

“Get out, fice man da gani nace.”

“Hajiya ina hadaki da girman Allah, just two minutes toh, Allah peck guda daya tal zan bata in fice maki da gani, Sweetheart ki bata hakuri mana kin tsaya kina mata masifa.” 15

Ya ida zancen yayin da yake hararar Kakus din.

“Kai tafi can Shashasha, waye ya gaya naka Saratu na jin lallashi? Ai gara in fito mata a mutum, tafi tsorata ta barka kaga matar ka, amma dai tunda haka kace shikenan hakan za’ayi Yaron kirki.” 2

Daga haka ta washe baki gami da Kallon Hajiyar dake kokarin tado Ramlan daga kan gado tace,

“Haba ke kuwa Saratu, kiyi hakuri mana ki bar yaron nan yadan gaisa da matar shi, haba Saratuwalle, farar mace alkyabbar mata, uwargida a gidan ibrahim mainasara, Allah ya jiqan Iro ya gafarta mashi.” 14

Murmushi kurum Hajiyar tayi, a ranta kuma tana mai amsawa da Amin, ba shakka Kakus ta san lagon ta, kuma tasan takan iya hada trap, toh amma ya ta uya da halin surukuwar ta ta, karshen ta dai ko bata barshi ya ganta don Allah ba, dolen ta zata barshi ko don jarabar masifar Innar, hakn yasa ta mike tai ficewar ta daga dakin ba tare da tace musu uffan ba, illah kallon kabini a hankali da ta zabga wa Safwan din.

Ai Hajiyar na bada baya yai wa gadon dirar mikiya kamar walk’iya,wanda nan take Ramlan ta sanya ihun shagwaba, gamida kokarin ture shi ganin irin wawuyar rungumar da yayi mata tare da sakin ajiyar zuciyah da karfi, kana kuma kafin kace mene, ya hade bakin shi da nata yana tsotsa.

Ai da sauri Inna aka juya kai gamida neman hanyar ficewa, yayin da halshen ta bai fasa k’unduma wa Safwan din zagi ba.

“Kai wannan yaro ba dai fitinanne ba,ka dai bi a hankali karka cinye wa yarinyar mutane baki, wannan rashin kunya taka Yaron Kirki har tsoro take bani.”

Murmushi Safwan dun yayi jin kalamen Innar kafin ta karasa ficewa, hakan yasa shi sake balance wajen isar da lodin k’aunar sa zuwa ga kazar mayun ta shi. +

Sai da yagama yamuta son ranshi kana ya sarara, shima hakan ya faru ne ganin ta sanya mashi kuka, ganin yana shirin maimaita abin jiyan, da sauri ya dagata gami da cewa,

“Matsoraciya.”

Shiru tayi tana kallon shi, a yayin da shi dinma kallon nata yake, har yanzu yakasa tantance wane irin so yake wa yarinyar, she us just everything he’s willing to spend the rest of his life with,sonta da k’aunarta a kowacce dakika samun gurin zama take a zuciyar sa.

Hura mata idanuwan ta yayi ganin ynda ta shagala da kallon shi, ba tare da bata lokaci ba ya sungumeta kamar jaririya ya nufi hanyar bathroom din da ita.

Wutsil wutsil ta rik’a yi alamun ya sauke ta, amma bata ga alamar yana sauraren ta ba, hakn yasa ta fara hadashi da Allah akan ya sauketa zata iya yi da kanta, amma yai kunnen uwar shegu ya shige da ita toilet din.

“Calm down Honey,i’ve been dreaming of a day like this some very long time ago, allow me to show you how much you mean the world to me.”

Bakin ta ne ya mutu sakamakon jin ta da tayi a cikin ruwan zafi mai dadin gaske, hakan yasa ta lumshe idanuwan ta tanajin wani al’amari mai girma game da Safwan din na k’ara bin lungu da saqo na jikin ta. 1

Bayan wasu mintuna da basu wuce ashirin ba ya kammala wanke ta, daga nan yasanya k’aton towel ya nadota a ciki tamkar wata jaririya, itama zuwa yanzu inbanda narke mashi babu abinda take, hakan yasa ya sunkuto abar shi sukayo waje.

Turus yayi a bakin k’ofar toilet din yana bin fuskar mutumin dake zaune a bakin gadon Mahaifiyar su dafe da kai, da’alama ma bai san abinda duniyar take ciki ba, ganin yanda yai nisa cikin tunanin.

Gyaran murya Safwan din yayi, kana lokaci guda ta dauke dukkan annurin dake fuskar shi, cikin wata iriyar kakkausar murya yace,

“Mr Kabeer Mainasara can you please do us a favor and respect our privacy?”

A hankali Kabeer din ya bude idanun sa, lokaci guda idanuwan sa suka hasko mashi burin zuciyar sa rungume a hannun kannen sa, kuma mutumin da yafi tsana kaf rayuwar shi. 9

Zafi da sanyi neh suka ziyarci zuciyar shi a lokaci guda, sannan ba tare da bata lokaci ba ya nufi Safwan din gadan gadan domin karb’e abinda yake mallakin sa ce.

***
Kallon rashin fahimta Safwan din ya rik’a bin Kabeer din dashi a yayin da ya tunkaro su, lokaci guda zuciyarsa na kissima masa kalar bugun da zaiyi wa Kabeer din, sai dai kafin Kabeer din ya k’araso har Ramlan dake rungume a hannayen sa ta dire, hakan yasa dirowarta daga hannun Safwan din yayi daidai da karasowar Kabeer din, ba tare da saurare ba ko bashi wata damar magana ta karasa cike da zafin nama ta figi zumbulelen hijabin sallar Hajiya dake ajiye a bakin gadon. +

Juyowa tayi domin fuskantar Kabeer din, a yayin da dukkan annurin fuskar ta yai balaguro,amma duk da haka yanayin nata bai sanya Kabeer din fahimtar kome kenan ba, asalima nufota ya sakeyi da kuzarin sa yana mai ambatar “Sugar” 3

Bai gama rufe baki ba ta kamtse shi da wani bahagon mari, kasantuwarta bahaguwa,ko kafin mamakin hakan ya sake shi ta sake kamtsa mashi wani, wanda hakan yayi sanadiyar fashewar bakin shi. 5

“Da kyau Rablatu,k’ara ma shegen.”

Suka tsinkayo muryar kakus na nufowa cikin d’akin itada Hajiya d Nabilah.

Zuwa yanzu kallon da yake mata ya bambanta da irin wadanda ya saba yi mata, wannan karon kallon “anya kece kuwa?” Yake yi mata, a yayin da bakin sa yayi matukar yi masa nauyin gaza furta ko da kalma guda bace, zuciya da ruhin sa sunkasa gasgata mashi abinda ya faru dashi yanzun din.

“Kabeer!” Hajiya ta kira sunan shi cikin kakkausar murya.

Bashi da alamun amsa mata ballantana ta san ran ya ji, amma duk da haka bata fasa maganar da tayi niyya ba.

“Tukunna ma wai yaushe kashigo gidan, har ka samu ikon shigar mani daki kai tsaye? Ashe rashin kunyarka ta kai har haka Kabeer? Bayan dukkan abin kunyar da dibar akbarkar da ka janyo wa ahalin gidan nan, amma still kana da guts din da zaka shigo mana gid kanka tsaye ba tare da jin komi a zuciyar ka ba? Ashe haka kake? Ashe kai din kura ce sanye da fatar akuya bansani ba?Haba Kabeer me nayi maka a duniyar nan da zaka saka man da wannan alkaba’in?”

Zuwa yanzu muryar ta tafara rawa, alamun gab take da fashewa da kuka, ba shakka Kabeer ya dasa mata bakin cikin da gogewar sa ba nan kusa ba,d’an cikin ta shine da wannan mugun halin, wannan wane irin abu neh?

“Shege munafikin Allah ta’ala,kai tsaye kana zazzare ido,ai nasan baka sa ran zaka ga Rablatun anan gidan ba, a tunaninka kai din me wayau ne koh? A tunaninka Yaron kirki bazai tab’a gano inda kake b’oyon matar shi ba koh? Oh, oh ke duniya ina zaki damu?kiri kiri ba kunya ba tsoron Allah kayi kane kane da matar k’anenka, anya? anya Kabeeru ba shedan bane kai?” 1

Kakus dinnta ida maganar tana mai rik’e hab’a, yayin da takejin tamkar taje ta rufe shi da bugu kawai kowa ma ya huta.

Bai saurari zantuttukan da uwar shi tagama yi ba,domin kuwa cikin zafin nama ya juya ya fuskanci Safwan dake jingine jikin k’ofar toilet yana jin su yace,

“I’m not here for all this,duk da cewar dole ne in gode maka, domin ka gajarta mani wahalar neman Sugar, yanzu ba sai anjima ba nake rok’onka for the last time, ka sakar mani mata, so that all this will be over!” 4

Kalar dariyar da Safwan din keyi ya sanya dukkan su maido hankalin su kanshi, domin kuwa basajin sun taba ji ko ganin yayi irin dariyar a dukkannin rayuwar sa, dariya ce mai dauke da ma’anoni masu dimbin yawa, wanda sosai hakan zai tsorata wanda bai san shi ba.

“Maimaita abinda kace Kabeer.”Safwan din ya umarce shi, bayan ya dauke duk wani sauran annurin dake shimfide a fuskar shi. +

“Safwan you heard me well,amma in abinda kake so kenan, well i said yanzun nan ba sai anjima va nake so ka sakar mani matata, as you were all aware now, ni ne na dace da ita bakai…… “
Da gudu Nabila ta nufi gangar jikin Kabeer din da ta dade da kaiwa kasa, sakamakon wani bahagon naushi da Safwan din yakai wa bakin na shi.

Cikin kuka take ambaton sunan Kabeer din, ganin babu sauran alamaun rai a tattare da shi.

“Hajiya don Allah kizi kigani baya numfashi, Ya Safwan ya kashe shi, mun shiga uku, mun lalace,Innah, Innah kitaimakeni kada ya mutu don Allah.”

“Keh arrrrr d’inki, kada in sake jin kin kira sunana anan guri, yooooh ya mutu din mana, ina ruwana ni? Allah na tuba ai mutuwar irin su Kabeeru ita din ce daidai, domin kuwa ba shakka za’a rage mugun iri.”

Kakus ta katse nabilan. 1

Can k’asan zuciyar Hajiyar ta rika jin wani irin tsoro na lullubeta, ba shakka komin lalacewar naka, naka nakane, hannunka bai tab’a rub’ewa ka yanke ka yar, hakan yasa da sauri ta nufi karamin fridge din dake can gefen gadon ta ta sunkuto robar ruwa, ba tare da bata lokaci ba ta bude bakin robar gami da tuttula wa Kabeer dib dake zube magashiyan tamkar babu rai. 1

Saukar ruwan bisa fuskar shi kenan ya sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya, kana a hankali ya rik’a bude idanuwan shi yana ganin su dishi dishi,idanuwan sa na sauka kan Ramlah dake jikin Safwan tana hawaye a hankali yasa shi ya mik’e a zabure gami da ture Nabila dake rik’e da shi tana hawaye.

“Hajiya, Ki gaya wa d’anki ya sakar mani matata, na rantse da Allah zan iya kashe shi akan k’in sakar mani mata da zaiyi,meyasa baku da imani neh?”

Zuwa yanzu inbanda rawa da tsalle babu abinda zuciyar hajiya keyi, kai hatta Innah ita kanta al’amarin na Kabeeru ya soma firgitata, anya wannan yana cikin hankalin sa kuwa?”

Kwashe shi da mari Hajiyar tayi, ganin yanda ya mike a zabure zai sake tunkarar Safwan din, lokaci guda kuma yana cigaba da sakin soki burutsun zantuttukan sa.

“Innalillahi wa’inna’ilaihirraju’oon, Allah na rok’eka ka kawo mani k’arshen wannan jarabtar, wannan wane irin abu ne? Kabeer ina hadaka da girman Allah da kadawo hayyacin ka kasan abinda kake? Matar k’anen naka kake kira d taka?”

Dakatawa yayi da kukan da yake yi,kana ya kalli cikin idanuwan mahaifiyar ta su dake durkushe a gaban shi tana hawayen tashin hankali yace,

“Matata ce mana Hajiya,baki sani bane?Ni ne nan nafara sonta, amma saboda son kai irin naki, kika kasa fahimtar hakan, kika murza wa idanunki toka kika mikawa wanda kika fi so duk duniyar nan abinda ni kuma nafi so,haba Hajiya! Dukkan irin bambancin da kuka nuna mani keda Alhaji akan Safwan bai isaba, har sai da kika dauki the most precious thing to me kika ba wancan dan iskan, duk kuwa da kasantuwata kamili, amma kika tsallakeni sabida tsabar son kai irin naki kika ba wancan mara mutuncin! Toh let me make myself clear, wallahi ba zan taba barwa wancan dan iskan Sugar ba,coz she’s mine,tawa ce ni kadai Hajiya, sai yaushe zaku fahimci hakan?”

Baki sake haka kowa na dakin ke kallon shi, take kuma zukatan su suka shiga raya masu abubuwa da dama game da Kabeer din.

“Kasan kana son ta meya hana ka nuna mata, me ya hana ka fadawa Hajiyar? Me ya hana ka amsheta lokacin da ni din na bijire? Me ya hana kayi abinda ya dace a lokacin da ya dace?”

Muryar Safwan ta ratsa kunnuwan su.

“Sabida ni nasan dadadden burin Hajiya kenan na ganin ta hadaka aure da Ramlah, Saboda bani da ikon gaya mata cewar ni ne nan ke son Ramlah, Sabida Hajiyar kanta bata bani dama ko fuskar da z an tunkareta da zancen Ramlah ba, abu ba k’arshe kuma shine,bantaba tunanin fyaden da nayi wa Ramlan da fuskar ka zai k’arawa Hajiyar kwarin guiwar hadaka da Ramlan ba,hakan ya nuna cewa kaso saba’in na dafa cikin plan dina ya rushe, domin kuwa naso baknn ciki jin cewa kaine kaiwa Ramlah fyade yasa Hajiya ta tsaneka, ta koreka da gidan nan, ta fiddaka daga ciki zuri’ar ta, daga nan kuma ta nemi shawarata akan yanda zatayi da Ramlan, ni kuma daga nan zan samu ikon mallakar masoyiyata cikin ruwan sanyi, ta hanyar nuna mata zan share mata hawaye in Auri Ramlan!” +

STORY CONTINUES BELOW

“Lahaula wala kuwwata… Lallai akace in baka mutu ba kasha kallo! Keh duniyah! Keh duniya jna zaki damu?” 1

Innah kenan ke ta faman zuba salallami, sakamakon jin zantuttukan da Kabeer din keyi.

A hankali Safwan din ya tako gami da karasowa inda Kabeer din ke zaune,tare da su Nabila sub sashi a gaba, bakunan su a hangame itada Hajiya suna masu jinjina wannan al’amari haka.

Tsugunnawa yayi gaban Kabeer din, lokaci guda ya kamo hannayen Kabeer din ya rike, kana ya saita idanuwan sa cikin na Kabeer din yace,

“Inaso a yanzu ba sai anjima ba,ka gaya mani laifin da nai maka da har nai deserving wadannan sharukka daga shakikin dan uwa na, tell me Kabeer Mainasara, me Safwan yayi maka har haka a duniyar nan?”

“You did alot Safwan, halshena bazai iya lissafo laifukkan ka a gareni ba, k’alilan daga ciki sune, daga ranar da aka haifeka, nayi bankwana da soyayyar iyayenmu, tun bansan me ake nufi da bambanci ba, har nazo na fahimci tarin bambancin da iyayenmu suke nuna mani akan ka,Safwan ka kwace dukkan soyayyar su, ka kwace dukkanin kukawar su daga gareni, duk kuwa da kasancewata mutum nagari abin alfaharin dukkan iyaye,amma hakan bai samu ba, sai kai da ka kasance, kangararre, dan iska kuma fitinanne a cikin zuri’ar mu samu dukkan soyayyah daga iyayen mu, me nayi Safwan, ni ba mutum bane da ba za’a soni ba? Kowa kai, kowa kai dai,zuciyata ba zata taba yake maka ba bisa dukkan zaluncin ka a gareni Safwan.” 1

Kallon shi kowa na dakin yacugaba dayi cike da alhini, sabida Allah meye laifin Safwan a nan?

“Meye laifina anan Kabeer?Ni nasa su hajiya su soni fiye da kai? Ni nasa sweetheart ta soni fiye da kai? Infact dukkan soyayyar da kake magana akai bantaba sanin akwaita ba ma bayaga ta sweetheart, meyasa zaka rikeni a zuciyarka akan abinda banda hakki akai Kabeer?amma kayi hakuri! Zan ari wannan lokacin in baka hakuri bisa laifuffukan dakake tunanin ni din nayi maka ba tare da sani naba, and i will make sure in sha Allah na maye gurbin b’acin ran da na sanyaka da farin ciki, nayi alkawari Kabeer, zan yi maka dukkan abinda kake so, dafatan yin haka zai goge tsanata dake binne a cikin zuciyar ka! Kai dan uwa nane Kabeer,zanyi maka komi domin ganin na faranta maka, wadancan laifukan ma bansan nayi su ba,danayi kokarin gyarawa, amma kayi hakuri please, i will make it up to you.”

Zuwa yanzu, sosai sautin kukan Ramlah da Nabila ke fita, harma da Hajiya da ta koma bakin gado ta zauna gami da rabka uban tagumi, yayin da hawaye ke ta tseren gudu bisa kuncin ta,kaico! Bata taba sanin soyayyar su ga Safwan tayi matukar yin tasiri akan Kabeer ba har haka, abin da mamaki, salihin mutum irin Kabeer ya kangare, gami da k’ek’ashewa har haka, ba shakka idab Kabeer yana da laifi, to kuwa sune manyan masu laifin itada marigayi, domin kuwa basu kyautatu ba wajen fifita son Safwan da sukayi akan sauran yaran su, mussaman shi Kabeer din da sam basa duban shi da irin wannan so din! 1

(Kalubale gareku iyaye, akan fifita wani daga cikin y’ay’ayenku, mun riga munsani cewa su y’ay’a dinnan amana ne a garemu, haka zalika hakki ne a gare mu mu sauke dukkan hakkokin su,mun sani kwarai akwai wanda yakan zama zara cikin yaranmu, wato mu rika jin son shi wannan din fiye da saura yaran da muka haifa, toh hakan ba laifi bane, domin kuwa komi nufi ne da tsari na Allah, sai dai abin lura anan shine kiyayye gami da yin takatsantsan wajen nuna soayyayar, mu guje wa duk abinda zaike iya darsuwa a zukatan yaran namu, muyi kokarin yin adalci a tsakanin su, ta hanyar yin hakanne komi zai daidaita na daga kafuwar nagartaaccen family,family mai tattare da hadin kai da kaunar juna na har gaban abada, Allah yabamu ikon tarbiyantar da yaranmu, dakuma ikon yin adalci a tsakanin su amin.) 5

Muryar Safwan din ce ta sake amsa kuwwa a ciki kunnuwan su.

“Tell me, ka gaya mani abinda zanyi maka wanda zai taimaka waje goge laifuffuka na a gareka Kabeer, nayi alkawarin yin duk abinda kace, matuk’ar bai kaucewa shari’ah ba. +

Zuwa yanzu shima Kabeer din kallon Safwan din yake kamar yanda kowa dake dakin yin zugudi suna jiran jin abinda Kabeer din zai ce.

“Abu d’aya nake bukata daga gareka Safwan, abu d’aya ne tal…. And ina tabbatar maka idan har kai mun shi zan yafe maka dukkan laifukan ka na baya a gareni.”

“Tell me, menene shi?”

Sai da ya kalli gefen da Ramlah ke tsugunne kusa da kakus tana hawaye, kana kuma a hankali ya maido da dubanshi zuwa ga Safwan din dake sauraron shu yace,

“Ka sakar mani Ramlah,divorce her and let me make her mine, yin hakan kadai ne hanyar da komi zai wuce a zuciyata Safwan.”

Kowa ka kallo a dakin ya dago ne cike da mamaki, mussaman Hajiya dake ta bin Kabeer din da kallo tana girgiza kai, a yayin da hawaye ke ta rige rigen sauka bisa kuncin ta.

Inna kuwa hangame baki tayu ta kasa magana, jira kurum take taji me Safwan din zai ce, ba tare da tadawo daga duniyar tunanin ta ba taji wata mummunar kalma na fita daga bakin Safwan din.

“Ni Safwan Mainasara, na saki matata Ramlah Tafida saki daya,idan ta samu miji tai aure.” 34

Daga haka ya mike ya fice daga dakin kamar iskah.

Ihun Ramlan ne ya maido su Hajiyar daga duniayar shock din da suka shiga, hakan yasa gaba dayan su sukayi kanta suna masu ambaton sunan ta.

***

³7

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]