[Advertisements⬇️]

KANDALA CHAPTER 11 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

KANDALA

CHAPTER 11

..

Kuka ta saka tace Anty please kicewa dady yaushe zan fara zuwa makarantar? +

” wallahi wannan fuskar taki akwai damuwa..?

” kuka tasaka tace baya kaunata wallahi, Allah Anty baya sona..

Cikin mamaki darashin fahimtar zancen Nata mama farida tace wanene baya sonki?

” Cikin shashekar kuka tace yaya haruna, bakiga abunda yakeyimin ba…

” yanzu wata hudu baki fada ba kande ke wacce irin ‘ya ce? Ai wannan zaman ke yake kwara haba dan rashin imani..Tashi ki shirya mutafi gwara araba auren..

” wallahi banaso iyah habu taje zancen nan domin nayi miki imani zata iya tsine masa akaina, nikuma Allah yana gani inason mijina domin abunda yakeyi bayin kansa baniba…

” ina daman ai bayin kansa Amma yarinyar nan batada imani wallahi, Ne nayi tunanin ciki ne yaramar dake ashi kina nan kina kunsar takaice…

   ” Anty kenan ai ne nayarda babu wanda zaiyi min wane abu sai abunda Allah ya kaddara, shiri inkika anyi sababine Sai Allah ya kaddara, Nasan bata isa tayimin abunda Allah bai kaddara ba..

     ” hakane kande amma kema kina sakaci, ki dage dayin azkar, zama da Alwala da kuma yawaita ambaton Allah…

      ” Tabbas kwanaki nema anso kamar Ahanani amma cikin ikon Allah dana dage da Addu’a naji dadi..

   ”  Ne wallahi duk kin sakar min da jikina wannan abu danaji Bari natashi natafi ko sadakace adage dayi da addu’a…

     ” Tohm Anty Amma ina rokonki kada kigayawa wane Dan Allah….

    ” wallahi abu ya cigaba dole nafada wallahi baza’a dinga cutar dake ba…

        ” inshaa Allahu zai karye kwanan nan…

      ” To ga dubu goma inje Dady…

Bayan ta rika’ta sukayi karo da haruna ko kallonsa batayi ba tace sannu da zuwa..

     ” Tsaki yayi yace ina kuma kikaje gantalalliya?

    ” Babu inda naje nadai ra’ka mama farida ne..

      ” Toh ki shirya Nan da wane satin zanyi Aure domin ina bukatar mace, kamela mai tarbiya akusa dani….

    ” To Allah ya sanya Alheri yabamu zaman lafiya…

     ” karma kice zaki hada kanki da’ita domin Nafi sonta…

      ” Batasan lokacin da tafara hawaye ba, sannan ta shiga ciki addu’a kawai takeyi sai taga wayarta tana ringing A hankali tace ina yini mukhtar?

    ” lpylou Aisha, yagida?

      ” lpy kalou!

” Da kyau kina tofa masa addu’a dai ko?

    ” wallahi da sauki ma yanzu har yakan tsaya yayimun magana babu kuma zage sai dai yasanar dani zai kara aure ta fashe da kuka.

     ” ki daina damun kanki, kafin ya aureta sai mun warware duk wane sharrin data kulla, Nasanar da wane kakana malamin allo ne to yace ki yawaita saka suratul bakara kokuma ki dinga karanta saboda annabi saw yace duk gidan da ake karanta ta, shaidanu baza su zauna ba ballanta na suyi ‘yaya, kuma ki dage da ambaton Allah..

    ” Tohm inshaa Allahu  Nifa abun yana bani mamaki wallahi ace kawai azo arabaka da mijinka…

     ” Ai da sauki ma nake in kinajin nawasu wallahi sai kin koka musu , dan ma Allah yasa ke kina da Dan ilimine, da wata yarinya ce ba zata yarda ba,Dan haka idan kinajen tsoronsa har ita yarinya ke koma wa kike tsoron zai cutar da ke sai ki karanta wannan addu’ar أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لَا يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولَا فَاجرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ
Wannan addu’a lokacin da aka koyawa annabi ita yatafi wa’azi ne sai shaidan ya gangaro daga kan dutse zai kona manzon Allah (saw) sai ga mala’ika jibrilu nan yace maza kakaranta wannan addu’a , Annabi yana karantawa sai shaidan din ya kone, in kana tsoron wane yana kulla maka sharri ko makirci to ka dinga karanta wannan addu’a…

    ” Amma Nagode mukhtar wallahi naji dadin Addu’ar nan domin na dadi ina nemanta….

     ” yauwa Akwai kuma ganyen magarya guda bakwai da dutse guda biyu suna cikin motar haruna kije ki dauka…
me zanyin dashi? +

        ” yauwa zaki Nemi ruwa mai kyau sai ki dauki ganyen magarya guda bakwai sai ki daka da wannan duwatsun inkin nukasu sai ki zuba acikin ruwan….

     ” kande cikin jindadi tace sai kuma Nayi yaya?

     ” Na farko sai ki karanta suratul fatiha gaba dayanta aciki, in kina karantawa ya kasance Numfashi yana shiga ciki, sai ki karanta ayatul kursiyu cikin suratul bakara aya ta 255, Na uku sai ki shiga cikin suratul a’araf sura ta 7 a alqur’ani ki karanta daga kan aya ta 106 zuwa aya 122, sai ki karanta su acikin ruwa kije cikin suratul yunus sura ta 10 ki fara karantawa tunda kan aya 79 zuwa ta 82 , sai kuma ki karanta suratul (kafiruna) sai ki karanta falaki kafa uku Nasi kafa uku sai ki tofa aruwan inshaa Allahu in kika bashi yasha yayi sau biyu arana ya kuma dinga wanka aguri mai tsarki inshaa Allah komai najikin zai karye…

   ” Mukhtar banda bakin yimaka godiya tabbas kacika aboki nagari, yanzu to tayaya zai karba agurina?

    ” ki daiyi dan dabarar ki bari naji nayi sallah Allah ya taimaki mu yakuma bamu sa’a..

      ” Ameen Nagode, Tashi tayi Nufi palour a zaune ta tarar dashi yaba kallo a mbc action hucewa tayi ta gaban sa…

    ” Dawa kike waya tun dazu?

     ” Da iya muke waya!…” ina zakije to yanzu?

     ” Abu zan duba a, uffan bai karya cemata ba bakinta ciki da addu’ar da mukhtar ya koya mata har tazo ta shige ta tafi dak’inta sai da tayo sallah sannan ta huce kitchen ta gado ruwanta sai data daka ganyen magaryar sannan tafara karatun tana gamawa Ta juye acikin jarka….

     ” Ko sallam baiyi ba ya shigo dako ita kuma tasa kayan bacci zata kwanta yace me iya habu tace kibane?

     ” Wane dadi taje tace ga sunan…

      ” roba daya ya dauka yace yaya zanyi dashi?.
     
     ” sau biyu zakasha sai ka wanke jikin ka dashi…

    ” Toh yace sannan yayi ficewarsa…

●●●●●

    Hamza ne ke rungume da farida yana shafa kanta, baby kinsan inason twins fa!…

    ” cikin turo baki tace dafa wahala rainon twins! Nidai kabarni da guda daya na!…

     ” shafa cikin yayi yace karki damu dear ai zan tayaki rainonsu…

      ” Murmushi tayi..

  ” Allah ya sauke ki lafiya!…Firdausi ce tayi b’ari Dazu…

     ” subhnlhi Allah yabata wane, sai kishirya gobe Na kaiki…

     ” Tohm Allah yakaimu..

   ●●●●●

Wai sau Nawa zan sanar daki kidaina damun kanki ne? Haba firdausi me kikeso Nayi ne? Allah fa shi yabaki kuma zai baki wane..

     ” rungumesa tayi tace sweety ina son babys wallahi…

    ” Nema inaso burina bai huce in ganki cikin farin ciki da Annashuwa ba, Yanzu kikwanta kiyi bacci Ne zan tafi kasuwa…

     ” me zan dafa maka?

” yau Na hutashi ki zan tawo dashi…

     ” I love you dear…

●●●●●

   Yauwa dady wai yaushe kande zata fara zuwa skul din?

     ” ran thursday zataji screening…

     ” Tohm zan sanar da’ita…

      ” Nasamar mata driver zai dinga kaita ma, ina fatan tana lafiya lou dai?

    ” Anty dai tayi kamar ta sanar dashi, sai kuma tace eh to lafiya za’ace…

     ” Ran jumm’a zanje musu gaba dayansu…

     ” Allah ya kaimu..

●●●●●

    Da safe da Abunda haruna bai tabayi ba, ya shigo dak’in kande Tana kwanci bacci ma takeyi..

    ” hannun sa ya saka yace ina sauran sak’on nawa…

    ” Addu’a tayi tare da murza idon ta, ina kwana?

     ” lpya, ina kika ajiyemun?

     ” Yana cikin durowar mudubi…

     ” Dauka yayi sannan ya fita, Sujjadar shukur tayi sannan ta shiga wanka, Tana fitowa taga wayarta na ringing ina kwana Anty?

    ” lpya lou! Yaya haruna..

     ” Alhamdulilahi yanzu yafita ma..

     ” Toh Allah ya daidaita, Dady yace ran thursday zakike skul scrn..

    ” jibe kenan to Nagode bari Na dura Abinci…

    ” ki daure kije ki duba firdausi tayi b’are jiya..

   ” Subhanallahi Allah ya bata lafiya yasa hakan yafi alheri zanje ISA….

Da daddare bayan sallar isha’i tana zaune tana karatun Al’qurani a palour…

   ” Assalamu alaikum ya samu kujera ya zauna..

    ” wa’alaikas salam sannu da zuwa..

     ” yauwa, Naje zuwa.. +

     ” yauwa, Naje wane company ne shiyasa nadade sunyi wane sabon tahil masu kyau ina tunanin acire Na gurin gate asaka su…

   ” Ita dai shiru tayi masa kada tayi magana ya cimata mutunci…

    ” jiyowa yayi yace yanaga kinyi shiru?

     ” To me zance?

” jiyowa yayi yana fuskantar ta Amma dai a matsayin matata Ai kya bani shawara ko?

    ” To gani nayi babu abunda gurin gate yayi kabarshi kawai..

    ” Tohm shikenan, Amma fa kin rame meke damunki?

     ” bakomai, gobe inason zuwa gidan firdausi tayi b’ari..

    ” Shiru yayi yace okay gobe laraba zandawo 4 sai nakaiki..

    ” Tohm

” Dakko min ragowar maganin nawa, tunda Nafarasha Nakejin dadin jikina wallahi Ga wayata ki sakamin application Na azkar…

     ” tohm, Tasaka masa sannan ta dakko masa ragowar ta mika masa!…

    ” Sannu nagode..

       ” Mek’iwa tayi ta nufi dak’inta, har takai kofa yace ina zakije?

     ” Bacci zanyi dare yayi…

     ” To tafiya zakiyi kenan? Toh shikenan..

     ” Tausayi ya bata sai kuka ta shige dak’inta…

      ” A k’an kujera ya kwanta sai Asuba yatafi masallaci, Yana dawowa ya shiga cikin kitchen yana ferayi dankali…

    ” kande ta fito hada tea taganshi, Tsugun nawa tayi ta gaida shi, kawo nayi maka..

   ” Tohm, bari Na share gurin..

    ” Aa kabarshi zangyara!

     ” kallonta kawai yakeyi yana murmushi..

●●●●●

   Wai muneeba meke damunki? Haba tun jiya waya ahannun ki..

     ” ke asirin nan fa ya karye haruna rejecting  din wayata yakeyi ke yanzu ma yayi blocking dina, Ke wallahi zan iya hallaka matarsa wallahi…

    ” kafin ma mukoma gurin boka tashi muje muyi mata kashide…

    ” Bar idiot tashi muje yusrah kinsan gidan nasa ko?

     ” Nasane mana!..

” gown suka saka sannan suka nufi unguwar motar sukayi parking a kofar gida!

     ” Directly babban palour suka isa suna shiga muneeba tace wai ina malamar gidan ne?

    ” Ah sannun ku ku zauna mana!

      ” ke bakar taraka mahaukaciya, wato nayi asiri kin karya ko? To let me tell you ko kinaso ko bakyaso sai na Aure haruna…

    ” yusrah tace ke kikaye mata imani ai kisa a haukata ta kokuma akasheta…

     ” murmushi kande tayi tace bana shakkar ace kice muneeba domin naga dumbun jahilce a tattare dake, Na kuma godewa Allah da mijina ya tsira da shedancin ki…

     ” muneeba ce ta rike hannun yusrah ki tsaya ki gane sai nasa an batar dake ko an kasheki…

    ” Dariya Kande tayi sannan tace haba wanda yariki Allah ai baza’aga bayansa ba, Ni ban isa nakare kai naba nasancewa Allah swt zai iya kareni kuma dashi Na dogara…

     ” Fita sukayi, binsu tayi tace malam adamu kafin ashigo gidan nan ka dinga sanar dani…

     ” Toh hajjaju..

●●●●●

     Da safe Ta shirya cikin abaya tayi kyau, sai sauri takeyi Tana shiga dak’in haruna tace yaya Na tafi makaranta!.

    ” Tashi tsaye yayi yace makaranta yan tun karota?

  ” Eh makaranta yau zamuyi…

     ” hannun ta ya riki yace wallahi banason ki da makaranta, Aisha dan Allah ki hakura…

     ” matsowa takarayi daf dashi kayi hakuri Yaya dady ya samar min driver yana jirana, kuma kai da zaka kara aure kwanan nan…

     ” Yadda bakin ta yake moving shiyasa jikinsa yayi sanyi bai san lokacin da ya kai nasa cikin nata ba ya fara kissing din ta….

     ” Turashi tayi tace kark….Turashi tayi tace kar Ka kara tabani kabarni natafi… +

    ” yadda yaga ta tureshi yaje baiji dadi ba tayi saurin hankada shi…

    ” Tana kokarin bude kofa kenan ya fisgota sai kuwa ta wada jikinsa cikin murya mai cike da tausayi tace Ne kike gayawa wannan kalaman? Ne fa mijinki Ne….

    ” kafin Tayi magana wayarta tafara ringing tana dauka ta fashe da kuka Anty…

    ” fizgar wayar haruna yayi yakara akunnen sa Nan yaje mama farida tana cewa Haba kande tun dazu driver yana waje yana jiranki mikikeyi? Haruna ne yace kuyi hakuri domin matata bazata cigaba da wata makaranta ba…

    ” Haba haruna karkace haka duk yan uwanta sun gama kuma suna da takardun su kada kace haka…

       ” bazanyi magana biyu ba anty, bazatayi ba wanda tayi abaya ma ya isheta…

     ” kashe wayar tayi batare da tace uffan ba…

     ” kande dataga yanaso ya hanata dagaske jakarta ta dauka tabude kofa zata fita, cikin jan idanuwan sa yace indai kika fita ban baki izini ba…

      ” kuka tafashi dashi sannan ta huce dak’inta kayan jikinta tacere sannan ta kwanta maganganun mahaifinta taketa tunawa da lokacin da yace haruna mutumin kirki ne kuma Alheri ne agareki Dan haka kada wata yar kaddara ta huce kimanta da maganata! Sautin kukanta takara sannan bacci barawo ya saceta….

   ” shikuwa haruna yakasa sukune tunanin sa daya tayaya kande zata fara sonsa har ta yarda dashi? Yana cikin wannan tunanin wayarsa tafara kara yana dauka yakara akunnen sa sai da yadan jima sannan yayi sallama …..

    ” Yanzu abunda kayi min haruna yadace kayi blocking dina? Abun taikaice ma baka kulani karfa kamanta gobe kace zaka kawo kudin auren mu why haruna why???

     ” kada kikara kirana kije kinemi dai dai ke domin ne Kinfi karfina yaudarata da ha intata dakikaye abaya kije Allah ya shiryeki Amma inkika kara kirana sai Na cemiki mutunci i have tell you! So stay away from my life..yayi off din called din….

   ●●●●

Yusra i have already tell you asirin nan yadade da rugujewa so dear ki tashi mu koma gurin bokan known…

    ” muny this guy ba kalarki baniba u better forget about him, ga sugar dadys manyan harka malama kikoma gidan jiya….

     ” see this idiot.. let me tell you this is the first and last da zakice Na daina son haruna cuz he’s already in my heart kuma saina aureshi in bazaki karane ba i should go by my self!…

    ” muje to but muny matarsa fa?

    ” forget about that rat, lokaci daya zamuyi squeezing dinta so just watch me….

    ” muny i cant drive sai dai ke kiye…

    ” okay..

●●●●

Karfe hudu haruna yau zai fita gashi yunwa yakeji har 3 baiga fitowar kande ba, hakan zuciyar sa taraya mishi kodai ta tafine, Tashi yayi ya Nufe dak’in ta budewar da zaiyi yaganta akwance ta bararraje sai baccin ta takeyi, A hankali ya tabata my Aisha?

     ” cikin fadafada tace menene?

    ” yunwa nakeji fa, kitashi ki duramin ko taliya ce…mikewa tayi ta manta vest ce ajikinta ta ja zanin gadon.. +

    ” baisan lokacin da Haruna ya fixgeba tayi maza ta saka hijjabinta….

    ” murmushi yayi yace hmm..

    ” ince abinci kace in dafa maka ba kallona ba?

    ” Dan Na kalle matatah haramun ne? Ai so ne yajawo haka..

” Sai ka jera Amaryar ka tazo in cinyeta zakayi sai kayi…

    ” binta yayi da kallo sannan ya tashi ya bita kitchen din.

    ” Taliya ta dafa masa da Dankali Lokacin data kai masa dining table yana zaune ta zuba masa ta miko masa drinks dinsa…

     ” hanyar Dak’inta tayi…

          ” my humairat  kitawo muci!..

        ” Nakoshi..

” ko 2spoon ne please kizo kiyi! Tunawa tayi lokacin da takeso suce abincin Tare Amma kwata kwata babu dama jiyowa tayi ta dau fork tafara ci…

   ” wallahi har naji dadi baby esha Nazata fushi kikeyi dani Akan skul, tun agida kin san banason cigaban skul fa! Yakara gyara zamansa kinsan kowa da irin ra ayinsa…

    ” Kallon sa tayi tace Amma ai amaryar dazaka karo ai Nasan tayi phd ko?

   ” kallonta yayi daga sama har kasa yace wai wane aure kike fada?

     ” spoon din hannun ta ta ajiye, Naje An fara kiran sallah bari naje…

    ” tana shiga dak’i wanka tayi sannan tayi alwala tayi sallah..

    ” Shima hakan yayi sannan yasaka shaddarsa ya shiga dak’in kande tayi kyau sosai tsayawa yayi yana kallonta…

    ” Tunda fita zakayi please ka ajiyeni a gidan firdausi…

    ” okay tawo muje, but ki tsaya karki tawo har sai nazo…

●●●●●

   Kai yusrah ina fa ganin nisan gurin bokan nan kiga fa sai yanzu mukazo..

   ” kuma yanzu 5 ma kedai taho mukarasa gurinsa, Tafiya sukeyi kowaccen su da abinda suke sakawa kafin su karasa yace kuuuuuu kuuuuu ku dakata ku dakata zuwanku sharri ne….

   ” boka kai kadai zaka taimaka mana kayi mana afuwa…

     ” Karku karaso domin yaron nan sai da ya kona mana aljannu 7, Ada ma da kuka ga nayi nasara akansa toh ya kasance mai wasa da sallah bayayinta akan lokaci mafi masifar abunda yakeyi shine baya tasbihi in ya idar kuma ya kauracewa kur’ani Amma yanzu babu wane da zai iya yimasa asiri domin yana fadan wasu kalmomi safe da yamma kuma yayi imani da Allah cewa shi zai karesu….

   ” muneeba ce tace too boka matarsa fa??

     ” Ki daina bibiyarta domin ta kasance mai ibada ga tsoron Allah kuma bata nufin kowa da sharri Ku tafii ku bar gurin nan…

    ” yusrah ce taja hannun muneeba tana tafi tana ki kyaleni ya taimaka min boka please…

    ” ke muneeba ki dawo hayyacin ki mana akan wane banzan yaro kin susuce…

    ” Ina sonsa ina kuma kaunarsa yusrah zan koma india domin ayimin sabon asiri…

     ” Hmm mudai je domin idonki ya rufe ruf….

   ●●●●

   A hanya yatsaya yasiya mata lemoka, suna isa mai gadinsu yazo yayi cike dasu, kiyi mata sannu…

    ” zataje, katawo min da case din wayar in kasamu…

     ” Nawa zaki bayar? ” Dubu daya tazaro ajakarta to gashi….

      ” wai me isa kika k’i fahimta ta ne? Inafa sonki dear kuma bakya…

     ” motar ta bude sannan ta shiga gidan tana karasawa palour ta tarar da ya Aliyu rungume da matarsa yanata bata hakuri….

     ” Dariya kande tayi tace ohhh ne yar nan darana ma sai kun soye!…

     ” Ya Aliyu ne ya cillomata pillow ina mai gidan naki…

     ” cikin raha tace karka jimin ciwo dan nima mijina bazai yarda ba…

    ” To Ai sai ku daure ne, bari naje Nadawo…

     ” kande ce ta rungume firdausi tace ashi haka abu yafaru?

     ” ke dai bari sister wallahi inason baby’s…

     ” hawaye ne ya zubowa kande Tausayin kanta takeji da ko shirrin kwana nan suka shirya, oh ne kande dubi yadda kika rame firdausi..

    ” firdausi tace ke ai yanzu inaje da babyn ki aciki shiyasa kike fadin haka…

    ” hmm wallahi banida komai, Amma inaso kisane babu macen datafi matsaye agurin Allah sai wacce take da’a agurin mijinta inya bata umarni, sau nawa yana baki hakuri? Komai fa zai huce…

     ” Tohm firdausi komai ya huce, inshaa Allahu Nadaina zancen…

     ” shiru tayi tace Firdausi kenan Allah daya baki wannan shi zai baki wane!.. +

    ” Tohm yar’uwa yakike ya gida?

     ” Wallahi gida babu dadi kullum shiru..

    ” Au baki fara zuwa skul din baniba?

    ” Hmm ki dai ayi sha’ani! Yaushe zakuje kauye ne?

    ” Gobe zamuje, yaya zai barki Ne?

    ” wallahi inason zuwa ganin goggo, Amma zan gwada naga ko zai barne…

    ” To Allah yasa tashi muje muyi sallah sai mu shiga kitchen kema kyatafi da Abincin…

     ” mu daije ki dafa ne bazan tafi dashi ba in nakoma zan girka…

   ” Sai gurin 9 sannan haruna yazo bayan ya shigo mun gaisa, firdausi tace yaya gobe zamuje kauye har kande!..

     ” tohm yace mata sannan suka Nufi hanya…

Tunda ta shiga take jansa da hira saboda bataso ya hanata suna isa gida tace me zan dafa maka yaya?

    ” ga takeaway nan nayi mana kisa Plate kikawo mana daki…

      ” wanka tayi sannan tasaka kayan baccin ta ta zura hijjabin ta tana shiga daki ta tarar dashi daga shi sai gajeran wando kasa shiga tayi sai shi yace mata karaso mana!.

   ” kanta a sunkuyi ta ajeyi A gaban sa sannan ta huce…

    ” Me isa kikemin Abunda kikaga dama? Me isa kike nunamin tsana da kiyayya kara kara? Me isa kikeso ki cucene?

    ” kafin yakarasa maganar sa hawaye ya zubo mata cikin shashekar kuka tace shekarar mu daya kana kunsamin Takaice ko kana tunanin zan manta zaman kashin da mukayi da kai? Menene baka kirane ba? Wanne irin bakin cikine ba kunsa min ba? Kakirane jahila kakirane mahaukaciya ko duk suma acikin so ne? Kaso wata har kana ikrarin kara aure to ka kara mana ko na hanaka? Ko ajikina ingaya maka domin ko mata 3 zaka karo sai dai nazuba maka ido..

    ” Amma yakamata ki tsaya ki saurare ni kuma…

    ” basai ka karasa ba nima mutum ce ina dakuma feeling ina kuma da zuciya inda banyi hakuri ba Ai da tuni mun rabo, ina sonka saboda Allah shiyasa nace gaba da zama dakai…

      ” mikewa yayi kafin ya karaso ta shige dakinta tana kuka!

     ” Ki daina kuka duk abunda nayi miki sharrin shaidanu ne da shaidan ba kuma Na cikin hankali na…

    ” sautin kukanta kawai yakeji can kuma yaje tayi shiru dakin ya karaso ya rungumeta shima hawayen ke wanke masa fuska!…

  ●●●●●

  Dady yakamata kayiwa haruna magana fa?  Yaza’ayi ya hanata makaranta!

     ” Matarsa ce ya fimu hakki yanzu akanta, kuma kinsan komai ra’ayi ne bakomai in da rabon zatayi gaba sai tayi…

   ” mumy tace hakane kam Allah yasa mu dace ya kuma basu zaman lafiya…

    ” Ameen sukace ..

●●●●●

   Da Asuba ta ganta rungume ajikin shi taje dadin kasancewa dashi amma sai kuma tayi wane tunani ta zame daga jikinsa…

     ” rungumeta ya karaye my esha Nasan nayi miki laifi Amma Allah ma yana yafeya ga bayinsa.. If you ask me about the love, I can’t answer you. But if you ask me who I love, the answer is you…
    
   ” har cikin ranta taje dadi sannan ta mik’i zata shiga bandaki…

    ” What else can I say ……. I love you and then again love you and this goes on and on…wane dadi yaje sannan ya fita zuwa masallaci…

    ” Tana fitowa bayan tayi sallah ta gyara dakin sannan ta huce kitchen…

   ” Yana dawowa yace kishirya ne zan kaiki kauyen!..

   ” tsalle tayi tace Are you serious ???

    ” kada kansa yayi sannan kowannen su ya shiga wanka suka huce har kauyen suna isa ta rungume goggo…

    ” sai tunanin ki naketayi ‘yata yagida yasu dady?

    ” wallahi Duk suna nan kalou, haruna ne ya shigo gidan suka gaisa da goggo….

    ” sadiya ce tace aine yaya nayi fushi sai yau zakuzo…

   ” murmushi yayi yace ayimana afuwa, ya kira kande mik’ewa tayi sannan ta huce zuwa gurinsa…

   ” karfe biyar zanzo dan haka ki shirya kinje?

   ” Ne gaskiya kwana zanyi..

    ” bazaki kwana ba so ba 5 ki shirya..

   ” cikin gida ta shiga tanata kumbure kumbure..

    ” Goggo ce tace mekuma yafaru?

     ” wai bazan kwana ba?

    ” meke damunki kande wallahi kije tsoron Allah kisan hakkin mijinki, Dama inson ingaya miki, ita rayuwa ba abace da take da tabbas ba!  Allah yayi Aljanna tun kafin ya halicce ki, ki, Allah kuma yayi wuta tun kan ya halicce ki, tun kan kizo bayan kasa wuta tana nan Aljanna tana nan… +

    Wanda ya kafircewa Allah ya aikata munanan aiyuka to zai saka ta a wuta…

      ” mafi mune abunda ‘ya mace zatayi shine ace ta cutar da mijin Auren Allah, komai zakiyi kisane cewa zaki mutu kuma abunda kika shuka shi zaki girba…

    Kuma ita rayuwar aure ta kasance zo mu zauna zo mu saba, Dan haka sai kinyi hakuri yanzu zakuyi fada anjima sai aganku tare…

    ” ki dinga ibada gyara jikinki da kuma fahimtar abunda yakeso arayuwa…

    ” in namiji ya nuna yanason abu kika hanashi ayayin da ya fita yaga wata dashi to tanan zata janye hankalinsa…

   ” Duk lokacin da yace zaimiki kishiya karki damu domin kowa da halinta zata zauna, akan wata kishiya zakije gurin boka? Dame tafiki dame tafiki tazo mana ai indai zuciyar ki bata mutu ba babu abunda zatayi da bazaki iyaba, wane dauren zane ni ta iya baki iya ba? Wane kwalliya ce zatayi baki iya ba? Sai dai in zuciyarki ta mutu, har yanzu mata basu fahimce matsalar karen aure ba, Ba dan ya gaji dake bani ba, bakuma kiyayya bace Jarrabawa ce da Allah swt ya jarrabi mata dasu, wacce zataje gurin boka tayi asara domin ta rabu da ubangijinta kuma ta rabu da aljanna domin wasu bukatun ta Na duniya, bayin Allah bakwa tunanin kwanciyar kabari ne? ..

     Dan haka kiriki mijinki ki maidashi dan uwanki ku zauna lafiya…

     ” Nagode goggo Allah yasaka da alheri yakara girma zanyi duk abunda kikace…

    ” yauwa yata Allah yayi miki Albarka…

    ” suka nufe gidan iya habu tana shiga ta wada kanta yar tsohuwa barkanki da rana…

    ” a’a yar albarka saukar yaushe?

     ” Dazu mana, kaddai yaya bai shigo ba?

    ” tsokanarki Nakeyi ya shigo kuna dai lafiya ina fatan babu wata matsala dai?

     ” Babu komai iya habu..

     ” to mashaa Allah sai ki lika gurin sumayya tanata cigiyarki…

    ” sumayya ce tace kaga Amaryar haruna koma kin kusa haihuwa ne???

    ” ke anty sumayy ya haka, Ne bari natafi ma…

     ” Aa karbe wannan ki shanye kinsan sai ana gyara kidinga yawaita shan kayan itatuwa kuma…

     ” Tohm nagode…

   ●●●●●●●●

    Yusra ce tace muny goben zamu tafi?

      ” nop fa inason Na saka wannan matar cikin bala’i?

   ” wa kenan?

       ” matar harun mana so nakeyi Nasaka mata poison a abinci so ta yadda zan shiga gidan nake tunani…

     ” Bare nagama da Alhajin nan sai mu tattauna…

     ” yauwa kawata kina kawo huta fa…

  ●●●●

   Tun karfe 6 suka isa gida, Tana zuwa ta dura abinci sannan tayi sallar isha’i , Dinning table ta dura musu sannan ta saka atamphar ta datasha stone ko ina ya zauna ajikinta…

   ” Sannu da kokari baby esha…

      ” Menayi ake yimin sannu?

    ” Da wainiya da kiketayi dani mana..

     ” murmushi tayi tace ai hakki ne Gareni dana kula da mijina…

     ” Amma naji dadin maganar nan!

     ”  gyara zama tayi tace when kishiyar zata karoso ne..

   ” So kikeyi tazo ne yana dariya yana fadar haka?

    ” hmmmmm

          ” bari naje Nayi wanka bacci yafara kamani…

     ” yau dawuri haka tohm sai da safe…

     ” Itama wanka tayi sanna ta saka wasu fitinannun kayan bacci sannan ta kwanta…

    ” Haruna dake faman zagaye a dak’insa daga karshe kawai ya shige dakin kande a hankali ya shiga bargon ya rungumota….

    ” bude idonta tayi tace kai da kace bacci zakayi?

    ” ta yaya zan iya bacci bayan farin cikina Tana nisa dani…

   ” Hmm ” to tashi muyi sallah suna  i dar wa ya dura hannunsa  akanta yace اللّهُـمَّ  إِنَّـي أَسْـأَلُـكَ خَيْـرَها، وَخَيْـرَ ما جَبَلْـتَهـا عَلَـيْه، وَأَعـوذُ بِكَ مِنْ شَـرِّها، وَشَـرِّ ما جَبَلْـتَهـا عَلَـيْه…
   
  ” Mik’ewa tayi sannan taje ta kwanta bakinta ciki da Addu’a… +

    ” bAyan ya gama abunda yakeyi ya rungumeta sannan ya sumbace ta Alokacin tafara kuka mai sauti tana kokarin tureshi ….

   ” rungumeta yayi yana kokarin sumbatar ta yace ki taimaki ne my esha in bahaka ba haukaciwa zanyi please dear, sallon nashi soyayyar Na da banne ya karanta addu’ar saduwa da iyali yafi sau goma daga Nan yafara kokarin rabata da kayanta tana tureshi tana kuka Amma ina baima san tanayi ba, ko ta’ina kissing dinta yakeyi…

   ” Yadda ta wahala hakan yasa muryarta ta durshashe kukan datakeyi baya fita kwata kwata ma!…

    ” Haruna da ya shiga wata duniyar bai barta ba sai kusan asuba sannan ya barta…

    ” I danu wanta da sukayi jajir ta bude…

     ” rugumeta haruna yayi sannan ya sumbace goshin ta.. Barakallahu fiyki am in with you my baby, banda bakin godiya..directly toilet ya kaita sannan ya huce nasa toilet din yayi wanka ya huce masallaci…

    ” Lokacin daya dawo tana kan dadduma bacci ya kwasheta tsugunnawa yayi ya dauketa ya kaita wane dak’in ya kunna mata Ac sannan ya sumbace goshinta ya huce kitchen…

    ” cike da Addu’ar Allah ya barsa tare da matarsa ya kuma saka mata sonsa Da kaunar sa ya bars….
Lok’acin daya dawo tana kan dadduma bacci ya kwasheta tsugunnawa yayi ya dauketa ya kaita wane dak’in ya kunna mata Ac sannan ya sumbace goshinta ya huce kitchen… +

    ” cike da Addu’ar Allah ya barsa tare da matarsa ya kuma saka mata sonsa Da kaunar sa ya bars osu mutuwa ta rabasu, cikin murmushi da Annushuwa ya hada tea sannan ya dauki cups ya kai kan dinning table, wanka yaje yayi sannan yayi walha yasaka wasu kayan ball…

   ” Sai karfe 9 sannan kande ta farka cikin murmushi tare da godewa Allah daya barta tare da mijinta, burgon jikin ta take kokarin yayewa sai kuma taje wata muguwar gajiya hawaye ne ya zubo mata sannan ta mik’i ahankali ta huce zuwa toilet ruwa ta hada sannan tayi wanka tayi brush, Tana fitowa tasaka brown din gown wacce duk tabi lafiyar jikinta wata karamar hula tasaka sannan ta samu humrah ta saka, addu’a takeyi aranta cewa Allah yasa ya fita domin kunyar haduwa dashi takeyi, cikin sakin fuska takarasa palour babu wanda tatarar hakan yasa ta zauna a kasan kafet dinta…

    ” kamshin turaren ta ne ya tabbatar masa da cewa ta tashi kuma tana palour a zaune Sallama yayi mata…

     ” cikin kunya da sunkuyar da kanta ta Amsa guri ya samu yazauna kusa da’ita…

   ” kanta a sunkuye tace ina kwana yaya?

    ” dago fuskarta yayi yana murmushi yace am ur husband fa why kike kunya ta, kuma ni yakama Na gaisheki baki ba!..

    ” sauri tayi ta kalleshi lokaci daya taje bazata iya sauke idanuwanta daga fuskarsa ba bakaramin kyau ne da haruna ba babu ma sajen da ya kwanta a fuskarsa jitayi kamar ta rungume mijin nata can kuma ya katseta da cewa….

    ” i hope baccin ya isheki dai?

      ” kasa bashi amsa tayi yadda yakeyi mata kwarjini…

    ” hannun ta ya dauka ya dura kan kafadarsa sannan yace shirun dakikeyi shi yake tabbatar min da cewa kina fushi dane…

    ” cikin shagwaba tace fushi kuma! Nifa nifa…

     ” a hankali yakaiwa bakin nata sumbata kefa me?

     ” wane irin kallo tayi masa saida jikinsa yayi yar…

    ” ya kamata na duramana breakfast past 9 fa yanzu…

    ” murmushi yayi ya miki sannan ya hado tea da break da egg yazo ya ajiye a gabanta…

    ” cikin mamaki tace wanene ya kawo mana?

    ” Ne nakawo miki bariki ga naga bakyason ci a hankali yafara bata abaki sai yau ta tabbatar babu kamar soyayya…

      ” yaya na koshi fa…

            ” haba baby esha bafa kici da yawa ba…

     ” kada nayi Amai am okay wallahi u need to get ready for office fa…

     ” Wayan sa ya dakko yace hello sir ina kwana? ” lpylou harun, ” Inaso Na dauki hutun kwana uku ne..” okay babu problem u can..” thanky ” u always wlcm…

     ” hannun ta takai zata fizge wayar tana cewa gaskiya ne banji dadin…

      ” dan yatsanta yasa a lebanta u mean bakyason zamana agida?

    ” tace i don’t mean that fa, Naga aikin ka is so important shiyasa!!..

       ” but u are more important than my work! Ur are my life dear, in bake bazan iya aikin ba…

      ” Murmushi tayi…

Jigawa

    Oh abdul kaki kaine naga yartawa ko?

    ” mamee kenan bansamu time bani ba kinsan yanzu Nasiba takusa haihuwa gasu meenal skul that’s why fa…

    ” kai dai kafadi gaskiya yau matar taka tafara haihuwa? in bazaka kaine ba sai na tafi dakaina…

     ” a’a mamee baza’ayi haka ba, Amma fa tayi aure!…

     ” Aure fa kace?

           ” kusan 1year mafa kenan so kinga u don’t hv to go for her…

     ” abdul kenan har yanzu son humaira baibarka ba?

     ” shirya mu tafi dan mu dawo da wuri…

       ” a’a kada ka azazzala ne abdul sai na gama aiki ma kaje office in kadawo sai muje…

    ” shi dai duk ba’ason ransa ba ya tafi..

    ” mamee kuwa kankana da kwakwa ta dakko ta markada su sannan ta juye acikin roba, sannan ta markada zogale tare da kantu ta juye zuma aciki shima ta saka aroba, abarba ta markada da cocumber ta saka zuma shima ta saka aroba, Anan ta duba batada aya da dabino da cikwui da kanin fari da mazar kwaila ataki a lokacin ta bayar aka siyo mata ta dakasu sannan ta zuba kantu da dakakken zogale aciki ta zuba acikin wasu robobi, waya tayiwa matar mukhtar tace ta basa atsinko mata ganyen magarya…

    ” Sai kusan 2 abdul yazo tare da ganin mamee ashirye..

      ” Hanya suka dauka basu isa ba sai kusan 4.

      ” mamee wannan ledojin kuma fa?

      ” kai dai babu ruwanka shigo min dasu ciki…

     ” sadika ce ta rungume mamee ai nazata tsokanata kikeyi dan nasan bazuwa zakiyi ba…

    ” hahaha ke kullum meta gani ai yanzu nazo muje ciki muyi sallah tukunna…

    ” bayan abdul ya dawo daga masallaci ya shigo gidan…

     ” ina yini yaya abdul yasu anty nusaiba?

     ” suna nan lafiya, ki daina zumudi gurin yarta tazo ai…

     ” wai Aisha kuke nufi?

     ” mamee tace eh kinsan gidan Nata ne?

   ” Eh! Yaya abdul kusa da gidan yaya badaru fa wannan kirarren gidan…

      ” Ah haba ai nasan gidan mamee tashi muje dare yanayi fa!…

     ” suna isa gate din gidan mai gadi yace su shiga parking din motarsa abdul yayi sannan sukaga hanyar shiga gidan…

     ” Kande dake palour a zaune tana kallo sallama taje kamar ta mamee tashi tayi aguje ta rungumeta mameeta sai yau? Sannan ta saka hawaye i miss u mamee…

     ” itama mamee hawayen ne ya kusa wanke mata fuska, sai cewa tayi mee to ‘yata, kinga yadda kikaye kyau dubi less din riga da skirt kinyi kyau!…

     ” goge hawayenta tayi tace ina yayana?

     ” cikin karfin hali Abdul yace ganinan…

     ” Haba abban meenal yakayi shiru..

      ” Ai naga ta mami kike tayi…

     ” kaje ja’iri to kada tayi tane?

    ” To bari naje mota ina jiranki..

     ” Mashaa Allah humaira har ayi bikinki baki sanar dani ba?

     ” kiyi hakuri mameeta wallhi akasi akasamu Amma wallahi nayi niyyar nakai miki da kaina…

  ” humaira kinsan komai sai Allah yayi za’ayisa dubi yadda kikazama yar lukuta…

     ” Hahaha daman can da kibata mamee ya aiki?

    ” Aiki alhamdulihi, ina mijin naki yake?

     ” Nazata ma kun hadu Ahanya don yanzu yatafi gidan abokinsa…

      ” To agaida minshi, Akuma dinga hakuri kinje?

    ” Tohm mamee tashi ki zagaye gidan…

    ” To muje gida dai sai dai Allah yakara bude! 
   
    ” bayan sun gama ta zuba mata abinci lemo da snacks din datayi…

     ” mamee tanata tsokanar ta sai munzo suna…

      ” wai wannan ledar menene aciki?

     ” yauwa magunguna ne Na ni’ima kinga wannan jarkar mai kankana sha zaki dingayi, shima mai abarbar nan haka, dame zogale, wannan garin kuma acikin nono zakisaka in baki samu ba kisa madara ki shanye…

     ” Mamee ai sunyi yawa wayannan, ” ke maganin mata baya yawa domin shine yancin ki gurin mai gidanki ne dai abunda nakeso ki sane shine ki dinga gudun fushinsa kina kuma nunamai soyayya…

    ” Murmushi kande tayi tare da sunkuyar da fuskar ta tace kai mame…

      ” hmm humaira kenan in kinasha zakiga yadda lamari sai sauya…

    ” Tohm Nagode Allah yabar zumunci bare nakai daki sauran tasaka a frige…

     ” Tana shiga dak’in ta rasa me zata bawa mamee aikuwa ta tuna da wata shaddarta ta hada da takalmi da turaruka ta fito….

    ” To humaira ne zantafi…

      ” Haba mamee ba kwana zakiyi ba?

    ” A’a ‘yata sai kin haihuwa zanzo na kwana…

     ” haruna Dake waya a bakin gate yadda yaga kande ta fito tana murmushi ya bata masa rai…

      ” yayana wai me akayi maka kake faman bata rai? Cikin turo baki Tace ko fa Abinci bakace ba?

    ” bai hada ido da’ita ba yace ai azumi nakeyi da anso ince ai a bayar natafi dashi…lahh sorry abban meenal bari na zubo maka!…

     ” ke kyaleshi yaje sa fi’elinsa cewar mamee…

    ” haba mamee ne fa ya huce haka agurina!…

     ” dagowa yayi ya kalleta, haruna kuma ya karaso yana jefan kande da wasu mugayen harara, gaisawa sukayi dasu mamee sannan ya shiga ciki…

   ” Sallama sukayi sannan suka tafi…
  
      ” Haruna dake zaune ya b’ata fuska idon sa yayi ja…

        ” zama tayi tace sannu da zuwa!

     ” how many times zan gayamiki akan fita da hijjabi? Abdul ba tsohon saurayin ki baniba shine kika fita babu mayafi har kuna hira! To from today kada ki kara fita babu mayafi…

   ” Allah yabaka hakuri mijina mantawa nayi Amma bazan kara ba!

    ” kallonta yayi ciki da kauna sannan yace nasan halinki matatah…

     ” katashi kace abinci dear banson…

     ” rungumeta yayi yace I love u my wife…

*Abuja*

     Ummi ummi yanzu zamu tafi fah?

  ” abi ne yafito har yanzu baku gama rabon katin bane?

   ” abi mungama yanzu zamu huce gidan dady ne…

    ” haneef da muneef ne sukace we need to follow you cux tunda mukazo bamuga brother ba!…

     ” abi yace is better dai kuje ku gaishe su dan morethan 5years rabonku da nigeria..

    ” muneef ne yace Ai yanzu dai we are done sai kungaje da ganin mu…

     ” maryam tace kirawo sister fadila i think ta shirya..

       ” ummi ce tace u mean ni kadai zaku bare kenan…

      ” fadila ce tace cool down mumcy kinsan inason ganin amaryar brother ne…

      ” saddika ce tace ki dai bari da wata yarinya zai kwaso mana wai ita kande!

    ” hahaha bakuda m sister lets go…

        ” haneef u should drive them kuma becareful ku dauke key din babbar motar…

       ” tunda suka dauke hanya basu isaba sai after isha, dady ne yake faman murna yana yimusu sannu da zuwa…

    ” fadila muneef haneeg yaushe kuka dawo?

     ” almost 1mouth dady!

     ” Ga biki kuma yazo lallai dana ganku a waje ai bazan gani kuba…

     ” mumy ce tace kalle yadda muneef ya dawo balarabe…

       ” kai mumy dan fulani kike cewa fa!

       ” mama farida ce tace ina Ai yafi Dan fulani sai dai balaraben…

      ” abinci suka ci sannan maryam tace mumy muna fata ya Aliyu zai bar firdausi zuwa bikin namu?

     ” Yes zaibarta sai dai ma kande ban tunanin haruna ya barta…

    ” Taba baki sukayi suka cigaba da hira..

  Dady yace ga driver yazo sai ku tashi ku tafi…

   Sai ku fara zuwa gidan hamzan..tohm sukace sannan suka fita…

     ” fadila Nazaune tana shan grapes sai sallama taje..

     ” cikin isa ta amsa sannan tace ahh kuce yan dubai ne agidan namu…

    ” fadila ce tace tunda ku kunki zuwa mu sai muzo…

    ” hamza ne ya fito daga daki yace ahh ‘yaya ummi…

     ” muneef ne yace au kai babu kai…

    ” ai ne dan gidan mumy ne ko bahaka ba haneef…

     ” Nan maryam da saddika suka dinga yimush hira ana dariya..

    ” hamza ne yace  dakko musu drinks mana!

     ” haneef ne yace ai a koshi muke ma…

      ” yanzu ya zancen ai kin naku?

     ” brother ai mun samu har munfara! Saddika ma tafara!..

     ” hakan yayi kyau duk abunda kuke bukata ku sanar dani…

    ” okay brother bara muje gidan firdausi…

    ” suna zuwa gidan firdausi suka tarar tana ta bacci dakyar ya farka ta rungumesu tana murmushi…

    ” muneef ne yace lallai kinajen dadinki dear…

   ” lahh haneef harda ku? Lallai dubai ta karbe ku…

” fadila tace ai kema gashinan aure ya karbeki…

   ” card suka bata cikin murna tace Allah yasanya alheri…

   Sukace Ameen…Sukayi hanyar gidan kande…

     ” kande dake daki tayi niyar bacci ma, haruna na rungume da itah…

     ” hankali ta zame jikinta tace sallama nakeji fa?

    ” bakinta yake kokarin kaiwa nata! ” kabari yaya please….

     ” ki kyalesu please..” mikewa tayi ta saka hijjabinta tana fita tace sannu ku da zuwa…

    ” su maryam ne suka daki baki yadda sukaga takoma..

   ” ah kace har dasu ya muneef da haneef sassanun ku ina yinin ku…

   ” cikin mamaki duk suka amsa mikewa tayi ta ta hado musu lemo tare da meatpie!

   ” yasu abi da ummi?

      ” Suna nan lafiya lou” Amma dai kwanar min zakuyi?

    ” murmushi sukayi dukansu sannan sukace agidan dady zamu kwana…

    ” Ayyah banji dadi ba kwata kwata Nima yakamata kuzo ku kwanar ma!

    ” saddika ce tace ina mijin naki?

    ” Dakin ta shiga ta tarar dashi i danunsa arufe, hankali ta tabasa yaya?

    ” bude idanun sa da yayi ya jawota kirjinsa wato baki sunfine daraja ki? +

    ” Please yaya kadaina fadin haka domin…

    ” Janta yakara yi daf da shi sannan yace to muje…

     ” Suka gaisa dasu sannan suka bata kati suka tafi…

    ” fadila ce tace Amma kanden nan nada kirki…

    ” muneef yace tabbas…

   Bayan fitarsu kande ta kashe fitilo sannan ta huce zuwa dakinta tana kwanciya haruna ya jawota please karki hanani yanzu wallahi zan haukaci, ” tausayinsa ne ya lullbeta yadda taga ya gigice akanta sai sumbatar ta yakeyi, kukan da ta karayi yasa shi kara rungumeta..yau ma sai kusan 4 ya kyaleta..wane irin kuka takeyi masa shi kuma ya rungumeta a kirjensa my baby esha i love u so much please karki rabu dani, kici kwanciyar hankalina….

●●●●●

Yusra ce tace this early morning kin tasomu muneeba.

    ” Dariya mugunta tayi tace muje gurin likita i think yazo sun shiga ciki muneeba tace  inason kabani paison please…

   ” Yusra ce tace poison anya kinada hankali muny kinga allah karkisaka kanki cikin matsaslar…

    ” tsaki tayi sannan tace I can do more than this Akan haruna tabawa dr din kudi….

    ” murmushi yayi yace inada poison but wanda akwai makarensa duk wane babban likita zai iya maganinsa ..

    “Yauwa bani dr! suka fita directly suka huce zuwa gidan kande after sun shiga suka ajiye maltina akujerar da suka zauna…

     ” sallama tayi musu tace lafiya ku kazomin gida?

    ” yusrah ce tace we are really sorry akan abunda mukayi miki…

     ” cikin murmushi tace babu komai ai ….

     ” mikewa sukayi sannan suka fita zuwa motar su..muny tace  kema yusrah ai kin iya shiri kinga yanzu mun fitar da kanmu…

     ” Tunda suka fita kande taga maltina akan kujera! Ko yayane ya matan bari nasaka masa afrige…

     ” lokacin da haruna yadawo kiran kande ya dingayi…

      ” yes mijina gani nan…

     ” Dakko min drinks a frige..” nadakko maka mirinda kokuma maltina?

      ” ban mirinda, kokuma gwara maltinar…

     ” tana kwance jikinsa yana sha yakusa kaiwa rabi sai tare sai Amai, kande ke faman kuka tana jijjiga shi alokacin mukhtar ya shigo yatarar da haruna yana ambaton Allah ga wane abu kamar kumfa abakinsa..
Kin kashe shi kin… +

   ” ihu ta saka tace wallhi….
  

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]