KANDALA CHAPTER 10

KANDALA


CHAPTER 10Tun daga lokacin ta daina bari ma su hadu, yau ana gama yimata kunshi haruna yazo ya huce yaga kunshin yayi mata kyau firdausi ya kirawo… +

” sister kije inji yaya haruna…

” kande ce tace me zanyi masa? Ke bazan zoba ba haba!
” haba k’ande! yaya ne yake kiran ki fa?

” To banjiki bani? Ai naji bakiga kunshi nake cirewa ba…

” To in kingama yana jiranki, ne bari nazo A farayi min Nawa…

   ” kinga firdausi u better go and tell him bazanzo ba karya dinga jiranki….

     ” Ne bazan iya zuwa ba! Amma ke in k’inga ma k’yaje ki sanar dashi…

     ” mtseww!!!

     ” farida ce tace lallai yarinyar nan! Mijinki ne fa!

     ” k’ande ce tace kekika daura mana auren? Bansan mijin nawa zai zama ba?

     ” firdausi ce ta dura musu ruwan girki,cike da tunanin nan da kwana uku tazama Amarya…

    ” A’a firdausi har kin dura abincin ne? Taimaka ki cewa kande taje inji haruna ya kirane yanzu…

    ” Nima nagaya mata tace bazata jiba kuma da Alamun abu zai tambayi ta!

     ” kande k’ande?
            
            “Naam Anty gani nan sallah zanyi…

       ” bakije haruna yana kiranki bani ba? Dan shashanci mikika tsaya yine…

    ” Yanzu zanje ai sallah kawai zanyi tashiga dak’inta wanka ta farayi wata doguwar rigarta ta saka wane kyau taga tayi can tace ne wannan hips din sunyi min yawa! Slimming zanyi Na huta haba! Amma fa nayi kyau tasaka dariya turare ta fesa ta daura dankwali ta tafi…

     ” haruna ke zaune akan gado yanata danne dannen laptop sallama tayi tace…

     ” Naji ance kana kirana gani…

     ” banza yayi mata sannan ya dauke numbersa number muneeba ya naima hello ykke? “Lafiya ta kalou  ya nigeria? Fine oo..” when zaku dawo?..” zan kiraki….

     ” ina jiranka fa ko na tafi ne?

     ” ohh ashe kinanan ai nazata kin tafi tunda bakisan darajata ba!

     ” i’danu wanta ta kada tace acewar ka ba?

     ” ai basai Nafada ba kekika nuna har yanzu baki fahimci irin soyayyar danake miki ba kenan?

     ” shiru tayi sannan tace to me nayi?

      ” au sai nafada miki, yakikeso nayi ne kinaso na zare kokuma nayi hulda dawasu matanne?

     ” kaga ba fahimtar wannan kalaman naka zanyi ba so sai anjima…

     ” Bakomai kice duk abunda kikeso Amma ki sane cewa ne mijin mace hudu ne so tunda haka kika zaba fitar min daga daki yanzun nan…

     ” har cikin harta sai dataji maganar sannan ta tsaya hawaye yana bin fuskar ta….

      ” cikin bacin rai yace walk out!!!….
   
Fita tayi jiki babu dadi dak’inta ta shiga Sai kuka mai cike da tausayi Ni daman Nasan baya sona kawai wulakanta ne zaiyi gwara yaya abdul tunda shi kaunata yakeyi…

    ” haruna tashi yayi yatafi office yana zaune duk abu ya damesa tsaki yaja sannan Mukhtar ya shigo….

    ” maza ankusa zama ango hehehe Aisha ta bano fa!…
  
     ” hmm kaidai bari mukhtar kwanan nan sai wane rigama take takalowa, ko magana nayi sai kaje ta kirane Dan iska…

     ” To kaima kabari adaura mana saura 3days fa!..

     ” yau ma azumi nakeyi wallahi! kaga gobe za’afara bikin ko nasa a daura gobe ko?

     ” Ai daman yanzu friday ake daura aure yayi daidai, to ya kayan nata ince dai angama dinkawa….

     ” gobe zai kawo ai, Nadai siya mata sarkoki da takalma gobe da safe zan bata!…

     ” ayi mata dai ahankali maza kaga yarinya ce…

●●●●

Bayan tayi sallar azahar sama ta hau, Nan ta tarar da farida tana ganin dinkinta Amma tana ganin ta shigo ta boye, wane diriss kande tayi sannan tace yauwa gobe less din zamu saka ko?

     ” A’a kowa nasa zaisa fa, lessi kowa yaje gidansa yasaka…

    ” farida tace sau nawa zangaya miki tun jiya fa nasanar daku a kitchen…

    ” ita dai kande kirjenta ne ya buga sannan tace toh, acikin ranta kowa babu abunda ta tanada ko dubu 5 bata dashi, ita dai tarasa wane irin miji zata aura uncare akan matarsa dubi duk mazajensu ne sukayi musu…firdausi ce tace ne dadaddare zanje gurin salon zan kuma shiga boutique Na dan karasa siyayya.. +

     ” farida ma tace nema dubu 50 yarage a hannuna da kayan dana kai dinki na lefena…

    ” kande ce tace nifa ban dinka komai ba lessin da baba yasiya na dinka!

     ” hahaha toh ai sai kisaka abunki…

    ” hamza ne yayi sallama sannan ya zauna kafin su gaisa yace my farida kinyi wane kyau fa!..

    ” murmushi tayi tace Allah ko? Yasu ummina da Abina??…

    ” Duk suna gaidaku, kande ya shirye shirye? 
   ” ai yana gurinku ya hamza!…

     ” farida bakida wata bukatar ko?

     ” acikin muryar iyayi tace babu, ka tashi muje kace abinci gashi can nagama…

     ” Tashi yayi yabita suka fita, firdausi ma angonta ne ya kirata tatashi ta fita..

    ” itama kande fita tayi ta huce dak’inta tagume tayi sannan ta dafe kanta yanzu wa zaimun dinki kafin gobe? Number nura takirawo tasanar dashi yace takawo zaiyi mata, lefenta ta bude ta dauke material guda biyu tatafi saka ajaka, gidan su nafeesa tafara biyawa …

    ” Nafisa tace yanzu naki shirin zuwa wallahi kinsan jiya muka sauka fa!

    ” gani ai ne nazo mutum lagos yakike?

    ” lafiya lou, Ashi kuma biki yazo Allah ya sanya Alheri da mutum naki za’ayi?

      ” A’a da ya haruna zaayi,…
    
      ” kai amma naje dadi kinsan Allah angon naki yayi sosai fa, kinga ga miski kidinga amfani dashi wannan kuma garin zogale ne zaki dinga sha da madara da zuma…

    ” ke nafisa harda hidima?

     ” Haba kawata bakomai ga kuma head din dakika tambayi ne Amma wannan pink ne ga kuma ash da blue…

     ” kai nagode wallahi natambaya rannan a hanya naje har yatafi 8k…

    ” Ai abunne sai addu’a gobe da sassafe zan tawo…

      ” Tohm ina jiranki..

●●●

  ” Tunda haruna yadawo kansa kiyi masa ciwo ga yunwa ga azumi anty yakirawo yace ina kande? ” tafita tun dazu nasan dai zata biya makaranta…

    ” kiranta yayi awaya hello kina ina?

      ” ina gurin mai dinki na, kayana zan bashi fa!

    ” kada kibashi kowanne dinki ya kashe wayar….

    ” mutum sai shigen fi’ilin tsiya, wai dinki wanene wannan nurah kabada hankalinka guda….

     ” Wanene ya kawomin gobe ne kuma bikin…

    ” Amma amaryar nan ta gwangwaje gaskiya yayi kyau, bari naje zan dawo…

Makaranta ta huce tana zuwa taga har sunfara jarabawar karba tayi takarasa, bayan sun gama malam hassan ya kirawo ta…

     ” Assalamu alaikum malam ina yini?

     ” lafiya lou Aisha to Alhamdulilahi Allah yakawo ko matak’i kin kusa zama matar aure, Akwai abubuwan daya kamata kigane ki kuma gyara abubuwan da kikasan bahali mai kyau bani ba, ki zama mai ladabi da tarbiya, ki dinga tsafta ki kuma zauna da mijinki da zuciya daya! Kikula dashi ki karemasa kanki da dukiyarsa ki kasance mai gaskiya da karamci, karki mai dagidanki kango kidinga karatun Alkur’ani ako da yaushe….

   ” Nagode Malam allah ya saka da Alheri…

      ” Amen…

     ” gida ta huce da ledoji Nike nike a’a baba ina yini?

     ” lafiya lou kande ashe biki yazo Allah yasanya Alheri…

     “Ameen tace sannan tahuce cikin gida su haruna hamza da su firdausi, mumy sai lissafin snacks takeyiwa dady…

    A’a uwata har kindawo?

    ” tsugunnawa tayi tace sannu da dawowa dady nadawo sun bani certificate da agogo…

     ” haruna kawai kallonta yakeyi yadda take magana cikin tsare da ladabi…

    ” toh mashaa Allah uwata gashinan dubu 20 ce kozaki bukaci wane abun…

    ” har cikin ranta taji dadi murmushi tayi sannan ta ansa tare da godiya ta mik’e….

    ” haruna ya zancen ginan ina fatan sun karasa yuntuni nake gaya maka afara da wuri…

    ” murmushi yayi yace kasan dady part biyu ne saboda k’arin kishiya agaba….Anty ce ta saka dariya sannan su mumy suma sukasaka… +

    ” kande kuwa uffan bataci ba ta shiga daki…

     ” hamza ne ya kalli farida kuje makeup din da wuri karku jirga mutane…

     ” murmushi tayi sannan tace inshaa Allahu..

     ” bayan sallar isha’i haruna yana zaune akan sallaya tun tea din daya sha…

     ” kande ce ta hau saman anty wai ina katin daurin auren ne?

     ” gasu can an buga gobe zaa daura fa karfe biyu…

     ” Anty gobe kikace fa?

    ” firdausi ce tace muma haka mukagani Allah yakaimu lafiya…

    ” kujera ta samu ta zauna tace oh ne bikin ma duk yafita raina wallhi…

    ” farida ce tayi dariya tace wai ke mumina hahaha zaima shiga ranki ne…

   ” mama farida ce ta dakko cup tace gashi ki shanyi nashi…

    ” menene aciki anty?

     ” Zogale ne da zuma da kantu sai madara…

      ” Ne bana sha, me zaiyi min innasha?

     ” menene haka kande duk yan uwanki sun shanyi nasu banda ke?

    ” Nifa Na koshi…

          ” firdausi ce tace DanAllah bani nashanyi yadda ango na yake Allah Allah nan ai sai kun karasa gyara…

    ” hahaha dadina dake wayyo inje farida…

    ” mamaki ne ya cika kande sannan ta huce dakin Anty ta zauna bakin gadonta sai hawaye…

     ” Haba kande menene na kuka?

     ” Anty kinje abunda yaya yake cimin kuwa? Daman nagaya miki bayasona kikalle su farida duk angwayensu sun basu kudi amma ne babu abunda yabani, Sai ya dinga cewa bani bace ai autar mata, ta kara fashewa da kuka harda…

    ” ya’isa Haka kande kema kinada taki matsalar kiduba kiga su firdausi kowa tararrayar nashi mijin yakeyi bandaki ki duba kiga abincin da tayiwa hamza, waya akai akai ga basu kulawa ke kinayi ne? Kiranki yayi sai kinga dama kike zuwa! Shi namiji a yadda kika dura masa ahaka zai tafi, kuma shi namiji kamar tirela ce a hankali ake janta, kinsan haruna aik’in sa a kwai mata sosai aciki idan baki ja mijinki ba wasu sa jashi…

     ” Goge hawayen ta tayi sannan ta karba kofin ta shanyi, Nagode bari naji Nadura indomie…

    ” Tana sakkowa ta huce kitchen indomie ta dafa sannan ta hada zobo directly wanka ta shiga tayi sannan tasaka hijjabin ta ta huce dak’in haruna sallama tayi amma yanata waya takusan 2mint sannan yace yes?

    ” haba yaya nakusa 3mint atsaye Amma kanata waya to wai dawa ma kake waya kusan awanku…

    ” murmushi yayi yace sorry banyi tunanin ke bace ba ….

      ” haka daman zakace ai ga abincin nadafa maka!…

    ” okay thank’s…

        ” gobe wane kaya zakasaka? Kuma kuma fa baka bani k’udin….

    ” it’s ok.. gobe mayi magana muneeba tana kirana okay…

     ” wai what are all this ne? Muneeban tafine ne?

    ” ko kallonta baiyiba ya kira muneeba, yace oya inajinki my dear me kike cewa?…

     ” kande ce ta bude kofa ta huce dak’inta kuka tasaka yanzu yazanyi da raina alwala tayi sannan tayi sallah nan tafara rokan Allah…●●
India.. +

   Muneeba this days bana gani kanki fa? What is going ne? I think kinfada so fa!…

     ” Yusra am in love with this handsome guy, kuma so nakeyi ya aurene…

    ” are u serious muneeba?

    ” i mean it yusrah yanzu ma u don’t see ta yarda yafara kulani, shi mutum ne mai son mace mai kwalliya da iya shiga kuma yanason hips da boobs but yaki sakewa dani…

     ” why not ki kaishi gurin boka?

     Yeah Na kaishi but still har yanzu yana kiramin matarsa gobe za’a daurah auren…

     ” kawai kishirya mube flight ai su dr zasuje bikin sai muma mu bisu muje tare kinga akwai wane boka anan garin nasu am serious fa ya isa aiki…

     ” that’s my friend, i love u dear let start prep…

   ●●●●

   K’ande kizo inje dady..

     ” okay ganinan firdausi, hijjabi tasaka sannan ta fita bayan sun gaisa tace gani dady…

    ” yauwa uwata ke kinje saloon din? Kokuma yanzu zakije kema?

     ” A’a kitso zanje yanzu gurin 2 zandawo..dady yaushe zanje kauye ne??

    ” haruna ne ya kalleta ya k’ada kai cikin zuciyar sa yace lallai kande bata tausayinsa jira kawai yakeyi a daura auren….

    ” yauwa dady bari naje,yaya ko zaka ajiyene?

    ” okay muje, yana shiga motar tace meke damunka todays ne?

     ” bakomai ina za’ayi miki kitson?

      ” Ga gidan can suna isa ya riko hannunta Aisha nawa kike bukata kudin dakikeso?

     ” k’allonsa tayi yadda yayi wane sanyi sannan ta janye hannun ta konawa ka bayar!

       ” Aljihunsa yasaka sannan yace ga dubu dare biyu nan duk abunda kikeso kisiya kinje!

     ” murmushi tayi tace ai sunyi yawa…

     
   ” A’a wallahi ne ga nima nakeyi sunyi kadan…

    ” Okay nagode dear!..

         ” Rik’i jakarta yayi yace I only want you to love me…

     ” murmushi tayi tashiga gidan shikuma yaja mota yatafi…

   ●●●●

        Mama farida tace mashaa Allah Amma momy masu decoration dinnan sun iyah fa!

      ” Nema haka dai nace, kande ta dawo ne?

     ” inaje tana hanya bari nakirata naje…

     ” so nakeyi sutafi gurin kwalliyar da wuri kinga har farida ta tafi…

   ●●●●●

Tunda kafara yimata kitson me kitson suke hira, ai yanzu kana zaune sai a asirce maka mijinka shiyasa sai ana addu’a duk yadda kakai da kyautatawa muje sai Addu’a…

     ” hmm ai ne abida me kitso bakisan Abunda yake damuna ba yanzu! Kwace miji akaiwa boka ya asirce shi…..

     ” K’ande ce tace kuma Da gaske wai anayi…

    ” eh Aisha anayi sosai sihiri babu abunda bayayi shiyasa yanzu akeso mata su dinga yawaita karatun Alkur’ani….

     ” Allah mudai yakaremu, hello nafisa kin karaso ne?

    ” ke gani agidanku harsu dady suna shirin tafiya dauren aure…

    ” Ankusa Agama min ganinan..

   ●●●●

   Mama farida ce ta dakko wasu fararen shadda ta bashi ya saka…

     ” Dady ne yace nayi kyau kuwa?

      ” Turare ta dakko ta karasa kusa dashi tace yadda kasan kaine angon, takai masa kiss kumatu…

     ” Allah koh, Kuma sai ku shirya ni in andawo office zan huce…

       ” Tohm Na bawa Haruna ya kawo maka abincin…

      ” Rungumeta yayi yace kina kula dani matatah…

       ” kara rungumeshi tayi tace ina mutukar kaunarka mijina..

     ●●●●
  Kauye ….

  Sadiya ce ta shigo iya habu yan dauren aure sun cika fa!

    ” ke dai kishirya idan angama zamu tafi, ki gayawa su anty zainab dukansu su shirya atafi….

     ” sunfi ashirin fa!

        ” Kinje shak’i yiyar yarinya to da anan zasu zauna? Su delo ma suna hanya…

    ” Anan angwayen suka karasu motoce dayawa kowa da tasu tawagar…

    ” haruna yasa farar  shadda, hamza kuma coffee colour, Aliyu kuma yasa milk… sunyi kyau sosai Nan aka fara addua ba adadi ba Aka daura auren haruna da Aisha kan sadaki dubu 70, hamza fa farida kan sadaki dubu 70, Aliyu da firdausi akan dubu saba’in… Nan aka bada goro da Alawowi cikin gida suka shiga sunata hotona abi dasu dady sunata karbar bak’i…haruna ne yashiga dak’in da iyah take gani iya habu…
    
     ” hannun ta ta saka ta shafa kansa Allah yayi maka Albarka, kasani yakai dana wannan yarinya marainiya ce ka kula da’ita, Duk abunda tayi maka ka dinga duba kuruciya ka kuma dinga hakuri Kasan zaman auren sai ana hakuri… +

     ” Inshaa Allahu…

          ” Nan aka dinga gaisawa Ana addu’a…

      ” Abi ne ya shiga gurin goggo yace aishe kina ciki…

      ” eh ina ciki sannunku da zuwa..
   
      ” yauwa ga gudun mawartawa dubu dare biyar ce sai gado da kujeru da zansa asaka mata….

      ” haba dan uwa sunyi yawa ai kudin nan, Ga Aliyu ma anyi masa hidima…

     ” ki kadaice dani fa idan banyi miki ba wanene zaiyi miki!

     ” Nan aka gaisa tayi godiya sannan suka dauke hanya zuwa gidan dady….

    
●●●●●

    Su haruna sun isa gida tun 12 dak’i ya shiga yayi wanka sannan ya saka doguwar rigarsar…

      ” kande ce ta fito daga toilet rik’i da towel, A’a ina Nafisa tatafi? Sallama taje sauri tayi tana neman hijjabi Amma har ya shigo ledar hannun sa ya ajeyi ga dinkunan kinan…

      ” To nagode please kafita, Ai banbaka izini ba!

     ” A lok’acin ma yak’ula towel ne ajikin Nan da nan ya matso kusa da’ita…

     ” sauri tayi ta bude wardrobe dinta zata dakko hijjabi ya ruketa…

     ” Au guduna kikeyi? Ai yanzu an daura you are mine, ko…

      ” kokari takeyi zata kwace hannun ta, taga towel din yana kokarin cerewa kuka tasaka…

     ” au kuka kikeyi haba my matatah ki tausaya min mana!

        ” Ne kasakene sai kuka…

      ” bak’insa yasaka Anata sai kokarin kwatar kanta takeyi ina haruna hankalin sa yafara tafiya…

     ” Data lurah, zai zarce gona da ire sai takara fashewa da kuka…

      ” Shafata ya farayi…

    ” Gani tayi yana kokarin cire mata towel…

      ” Takalmi ta kwala masa tayi sauri tafita saman anty ta shiga bedroom dinta ta wada…

      ” lafiya? Kande..

               ” shiru tayi sannan tace kadangare ne adak’in….

     ” dariya anty tayi tace Ai kadangaren katone kikadai zaki iya fita dashi….

     ” murmushi kande tayi tace mutum sai shigen jarabar tsiya mtseww ta dau hijjabi…

     ” Haruna kuwa yana fita wanka yakaraye sannan ya huce office…

     ” Kande tana sakkowa taga su Nafeesa, iya habu ta rungume, aa anty zee ina yinin ku…

  ” suka amsa dacewa mashaaAllah kin zama yar sukuta gakenan…

       “Murmushi tayi tace taso sadiya nafeesa kutawo mutafi…

    ” tana bude kayan mashaa Allah yayi kyau sosai kayan suka dauka suka tafi gurin Nanerh mai kwalliya…

Suna isa kande takira mai dinkin ta tayi masa kwatancen gurin kwalliyar ya kawo musu kayan.. tana budewa tace Nafeesa ga naki ke kuma sadiya ga naki nagobe da jibi wannan kuma kakaiwa iya habu….

     ” Nafeesa ce tace har ne kika dinga fatima?

      ” lahh har na dinner na dinka dake ai kin huce haka agurina..

    “Sadiya ce Ta gwada Nata woow gaskiya i love u ta rungumeta..

    ” A farayi miki kwalliyar sai ayimana sai kiyi gaba…

      ” Amma fa kinyi kyau Aisha dubi yadda kikayi fresh…

     ” Nagode tayi dariya…

  ●●●●
Yan’uwa da kawayen mumy sun cika acikin agida… hajiya sa’a ce ta shigo A’a gaskiya decoration dinnan yayi kyau, amma har 5 basu karaso ba…

     ” Anty tace kowa gurin kwalliyar sa yatafi banda suje guri daya…

     ” bari na kirasu, farida kin tawo ne?

     ” ina gate ma shigowa zamuyi yanzu..

     ” fitowa sukayi ita da hamza sun saka light kofi sunyi kyau kamar ba farida ba, masu hoto da videos sai dauk’arsu sukeyi kan chair dinsu suka tafi suka zauna..

      Ba’a jima ba su Firdausi sukazo sai murmushi sukeyi sun saka light orange sunyi kyau sosai masu hotuna da videos suka karasu suka huce gurin zamansu haka Kafara taro….

    ” Hankalin Anty ya tashi yadda taga Anata gulmar kande babu ma mutum abuja ummi sai cewa takeyi Ai Allah yarufan Asiri ga daidai da dansa….

     ” hello haruna wai ina kuka tsayane?

     ” itace bata karasa ba bari nakirawo ta…

      ” please kuyi sauri nidai Allah yasa kande tayi kyau!

     ” sadiya ce tace mamafarida Ai maganar fadar kyan da kande tayi bata baki ne…

     ” Alhamdulilahi kema gashi nan kinyi kyau…

    ” dariya sadiya tayi sannan tace thank you.. gurin mc tatafi yauwa ga wannan wakar zaka saka musu…

     Okay…

    Anata rawa ko’ina ya cika…

   ●●●●

   Wai ba’a gama miki baniba? Muka dai fa ake jira..

    ” Katawo to saura daure kawai..

    ” Nanerh ce tace woww fantastic kinyi kyau fa sosai, kun iya daukar colour fa!

     ” Najef Ne yayi driving dinsa sukazo daidai gurin mai makeup din suna zuwa kande tafito tayi shigar lemon garin da ratsen milk head dinta ma milk ne, haruna ma yasa shaddarsa green anyi masa aikin milk…Amma kinyi kyau wallahi..

    ” Murmushi tayi tace kaima kayi kyau ai..

    ” yadda dink’in sukabi jikinta dukiyar fulanin ta sunyi cak sai kallonta haruna yakeyi…

   ” Nafeesa ce tashiga gaba sannan suka huce…..

     ” Nan sadiya ta cewa fatima sun isu…, yauwa fatima ta samu friends  dinsu su hudu duk sunyi ank’on atampha milk tana shigowa za’asaka wakar mukuma sai muyi rawar wakar kungani ko?

     Tana fito kowa yasaki baki yadda sukayi kyau haruna hushiryarsa tafito ga hakurin maka dake walwali a bak’insa ya rike hannunta ita kuma ta sun kuyar dakai…

     ” Anty murna ba’acewa komai…

      ■ Su fatima ne suka fito waka Naja’tu ta Annabi aka kunna musu tafara tashi…

Rawar hannun suka farayi…

    _Din, din, din, he,he,he,he, ayir yir yir eheeee… mata Adon gari gamu a dandali kowa da gudun mawar kawalliya zai ambata.._

    Fatima ce tafito tace…

     _Nice ta fari sai kuce mine kirjin biki nayo ta kudi da nakiya fura da tsaki, Dankiyi farau farau idan daya sha ya yabamiki…._

    Asiya ce tafito tace…

        _Nima bara infirta   tawa bajintar kuji, ‘yar kwankwashe langa mai ado ga kuma bangaji Na baiwa kawalli kallabe sai muyi rangaje…_

      Halima ya fito tace..

        _Ne nashiga sansani kawaye da farin gani, dukka amarsu zatayi tayi farin jini zan bada gudumar fantika har da turaren huta…_

      Duk’ansu su kace..

   _koda yanzu kin zama Amaryar haruna_

    _Mu.. sauya.. baza zamu mu dau amarya…sai hakuri rayuwar aure yar uwata….Amarsu ki share duk hawayen ki..yau wanda kike yabon sa an baki…biyayya ta rage taki..Dan k’in bar gidan iyayenk’i zak’iyi nisa da k’awayen ki..yayye naki.. harda k’annen k’i.. Aisha ayau ki bada mamaki kiyi biyayya ga mijin naki!!!…_

     Suka karasa gaban su sannan suka shigo dasu sai fara’a sukeyi har su firdausi sai da suka je haushin su…

     ” sai hotona sukeyi har suka kara gurin zama!!…

     ” aka kirasu dik’ansu suka fito sai lek’i akeyi musu su mumy andage sai rawa ita da mukarrabanta..

     ” inna ma tasha liki sannan yan uwa ma sukayi nasu…

    ” Turare aka dakko sannan Aka fesa musu dukansu akayi musu kamu..

      ” Anan kabada takeaway da robobi da calender…

    ” Duk’ansu sunyi kyau sosai Amma kande ta cinye su ita da’akewa kallon yar kauye…

    ●●●●
Ba’agama bikin ba sai kusan 8 sannan akashi…

     ” kandey ce tace Fatima amma u mean so much to me nagode muku fa, wannan tsare naku yayi sosai wallahi Allah yabar zumunci…

    ” Sukace babu komai kande bakomai wallahi….

    ” jak’arta ta bude to ga katin dinner dinku….

     ” tashiga cikina gida ta rungume mumy tace nagode mumy, ta rungume dady tabaya father like no other…

     ” Uwata kinyi kyau fa! ” nagode dadyw bari naje gurin Anty…

    ” Tana shiga cikin dikin ta rungumeta takai mata pk naki special ne antyta da bamu shirya ba bansan yaya zanyi ba…

    ” Amma fa naji dadi dakikaye kyau haka…

     ” kinsan da lessin nan zan saka ashe yaya haruna ya dinka wannan…

  ” To kije kiyi sallah ko dauki kbbasa kiyi turaren nan…

     ” wai har kanun farin zan turara?

     ” Eh mana…

       Tana sakkowa daga binne tayi hanyar kitchen nan taji anjata…

    ” murmushi yayi kin tsorata ko?

     ” dariya tayi tace lafiya dai?

    ” kinyi kyau matatah hannunsa yakai kan kirjenta…

    ” Nifa ka takurawa jikina!..

   ” Ince dai sun zana nawa?
  
     ” murmushi tayi sannan ta bar gurin dak’i taje ciki da yan uwa tayi alwala tayi sallah sannan taci abinci….wane magani da antyzee ta hada mata tabata ajiyeshi tayi tace shigen magani sai saka mutum cikin tunani…..

    ” Hahaha nafeesa tace kyama shanyi…

   
●●●●

   Ke kika jawo ai ta cinye mu.. ince sai danaci kowa yasaka iri daya Amma kikace kowa ya saka nashi…

    ” ke dai bari firdausi ai akwai gobe sai na cinyeta…

    ” hmm ne dai bari naje Na kwanta sai da safe…

Washe gari gidan cike da mutane ko ina abi ne ya tarasu yace toh Allah yakawo ku wane mataki da zaku bar gaban iyayen ku ne tafiya zanyi Ina yimuku waazi da kuje tsoron Allah a duk inda kuke, kada kuyi tunanin ai aure jindadi ne gaba dayansa a’a shi aure zama ne ya zomu saba zo mu gyara, komai hakurin ki wataran sai an sabamiki kuma komai farin cikin ki wataran sai an bata miki dan haka! Komai zakuyi kudinga tunani kuna shawara da mazajenku, ku kasance masu ladabi da biyayya kuma ku guje abunda mazajen ku basaso… Allah yabaku zaman lafiya…

    ” Nan suka tashi suka tafi basu isa ko’ina ba sai gurin ummi itama tayi musu sannan suka fara shirin tafiya gurin kwalliya basu bar gida ba sai 6…

    ” zelmes event center mutane duk antaro, gurin zaman Amare, firdausi decoration dinsu white da ruwan toka, farida kuma Nasu pink da milk, sai kande blue…

   Yauma mc sai kwodasu yakeyi dukanin su sunzo sai hotona akeyi, sai daga baya kande tashigo tasaka gown dinta tayi kyau tariqe jakarta sai wasu yara agefen su Nafeesa da friends din haruna abayan su….

     ” sunyi masifar kyau haka suka dinga hotona yan uwa sunata yi musu lik’i…

     ” Haruna sai rada yakeyi mata abun ban sha’awa..

     ” An cashe ankuma rausaya kudi sunyi kuka basu dawo gida ba sai 11:30….

   ” Tunda kande ta dawo take faman kuka lokacin da taga dare yaraba shine ta tashi tana rokon Allah Akan zaman aurenta da haruna Ya Allah kabani hakuri da juriya tanata kuka….

  ●●●●
India..
      Heee this serious ooo look at haruna da matar tashi…

     ” Ai tafiki kyau muneeba fari kawai zaki nuna mata fa…

     ” ki shirya sai nigeria…

    ” Gwara dai muje abuge kansa! Amma da antsaya ana abun wasa…

    ” Kusan 5 to 6 hours sukayi sannan suka isa garin..bayan sun huta muneeba tace bazan iya zama ba ki tashi mutafi gurin bokan naki…

    ” okay let go… tafiya sukayi bata wasa ba kusan tafiyar 2hours sannan suka isa,manyan mutane suka tarar agurin sannan suka tsaya…

  ●●●●

      Nan kowaccen su ta shirya aka raba mutane sai gidanta sai da aka kai firdausi sannan aka kai kande sai kuma aka kai farida, Dukkan ninsu gida yayi kyau ba’acewa komai…

     ” Nan duk’an aka watse aka barsu yadda hamza yasa farida tayi alwala tare da sallah haka Aliyu yasa firdausi daga Nan saloo ya chanja….

    ” kande ta lulube kan gado abokanan ango sukayi mata Addu’a sannan suka tafi Nan mukhtar yace Adaiyi a hankali maza….

     ” haruna yayi dariya yace sai yadda hali yayi…

     ” Alhamdlhi yau Allah yakawo mu yau gani gaki daga ni sai ke.. sai kiyi alwala muyi sallah cikin kunya ta tashi tayi Alwala daga Nan suka yi sallah ya dakko nama sai daya tabbatar tace sannan ya kyaleta kwanciya tayi ko addua batayi ba….

    ●●● 
Yusrah tace azaba ta tabbata agareka boka…

     ” yace tare damasu biyemin…

    ” Na kawo maka kawata ce tanada matsala ne kuma nasan kai kadai zaka share mata hawaye…..

     ” hahaha koba haruna ba? Keeee kin sameshi kingama..

    ” Akasheta ko a haukata ta kokuma a batar da’ita?

     ” so nakeyi ya tsaneta Amma kada akasheta kuma kada ya kusance ta inaso yasone kuma ya aurene….

      ” Angama, kinsamu yanzuma ta kwanta babu addua zamusa aljani belmus ya shiga jikinta yanzu….

    ” yusrah tace hahaha yauwa boka!…

       ” bur bur bur bazai yihu yashiga jikinta ba yace tayi azkar da safe kuma acikin magaginta tayi addua amma zai dunga rabarta za kuma mutura dan celle jikin mijinta dan haka karku damu…

     ” muneeba tayi dariya tare dacewa great! Nawa zan bayar boka?

    ” kibada dubu 100 dakuma bak’in kare…

      ” muneeba tace ga dubu dare 300 ma in zamu dawo zamu tawo da kare….

      ” mungode dan wuta….

      ” wata kara yayi wewewewe…” yusrah kinga har 12 muna gurin nan… ” ke dai ba kikasance da haruna ba? ” yeap that’s my wishe’s…

    ●●●●

   Wanka haruna yayi fuskarsa cike da Annashuwa da murna yana zuwa ko bismillah baiyiba yafada kan gado rungume ta yayi sannan yafara shafata, ita dai a cik’in layi tak’e Amma k’uma tanajen sa yana kokarin rabata da rigarta….

     ” Ta tashe tace enough ya’isa ya’isa kadaina kadaina….

      ” My love for you is my only treasure, which on earth cannot be measured rungumeta yayi Yana kissing dinta, Fusace ta miki tabar dak’in…..

    *HML FIDDAUSI SANI Ali…. Barakallahu fiykum Wishing you the joy and happiness that you both deserve… May the blessings of Allah fill your life with happiness and open all the doors of success now and always…* Wank’a haruna yayi fusk’ar sa cik’e da Annashuwa da murna, yana zuwa k’o bismillah baiyi ba ya fada k’an gado rungume ta yayi sannan yafara shafata, ita dai a cik’in layi tak’e Amma k’uma tanajen sa yana k’okarin rabata da rigarta…. +

     ” Ta tashe tace enough ya’isa ya’isa ka daina ka daina….

      ” My love for you is my only treasure, which on earth cannot be measured rungumeta yayi Yana kissing dinta, Fusace ta miki tabar dak’in…..

  Kalaman innalillahi kawai yake fada da tunanin me kuma yasame kande!

      ” Wane daki ta wada wanda shima akwai gado aciki cigaba da bacin ta tayi…

     ” shikuwa haruna tunda tafita hawaye ya wanke fuskarsa wannan wacce irin kaddara ce? Why kande why?

      ” hakan yabashi damar komawa dak’insa yana kokarin kashe wayarsa tunda yanzu 2 tayi yaji kiran muneeba…

     ” Amincin Allah yatabbata agareka!

      ” bai san lokacin daya saki wane murmushi ba sai kayi tunanin tana gabansa, wanake ji kamar muryar muneeba…

    ” yes nice, ai ina garin ma naku gaba daya, Na bugo nayi maka Allah sanya Alherine!…

     ” Gobe ina zamu hadu?

    ” kazo beherj hotel mana daki mai number 07, ina Amaryar taka?

     ” Tsaki yayi yace bacci takeyi…

     ” cikin narkakiyar murya tace Nifa Banason Na dinga ganin ka cikin damuwa fa!

     ” Murmushi yayi yace tunda naji muryar ki ai Naji dadi bakin cikina ya gushe…

    ” That’s my love! Bari na barka ka kwanta zai kazo…

      ” jiyaye kamar kada ta katse wayar!..

    ” Da asuba D’ukan su babu wanda yatashi, sai gurin karfe 6 kande ta tashi cikin bacin rai!

     ” fitowa tayi tana mik’a.. toilet ta shiga alwala tayi sannan tazo tayi sallah tana kokarin yin azkar gaba daya sai hamma bacci ya kwasheta….

     ” shima haruna bai tashi da wuri ba sai almost rana ta kusa wanka yayi sannan yayi sallah ya shirya cikin shaddar sa blue yayi kyau….

    ” K’ande tana tashi tayi wanka tasaka duguwar riga tayi kwallliya da dauren ta maikyau, tunani ta dingayi anya tayi azkar kuwa? Anan ta dinga sak’i saki daga karshe tace Namayi, palour ta huce taje ta zauna tana….

       ” haruna ne yafito zai fita har yakai kofa tace yaya ina zakaje?

       ” tsaki yayi yace kin haife ne da zaki dinga yimun tambaya bansaniba….

     ” Amma dai hakkina ne kasanar dani inda zakaje…

     ” Bude kofa yayi sannan yafita zuwa gate, motar sa ya shiga sannan ya huce hotel din…

   Kuka ta fashe dashi Innalillahi ya Allah meke faru da haruna? Wannan wane irin aure ne? .. fita tayi tana zaga gidan tsaren gidan yayi kyau palour biyu dakuna 4 sai toilet 6 ga kitchen dinta kato yayi kyau sosai….

    ●●●●

   Dady ne yace wa mumy zai ishesu kajin kokuma akaro…

     ” Dady kusan guda 30 ne fa kace kowa goma goma ko?

    ” eh ai nayi tunanin sunyi musu kadan ne shiyasa!

      ” yaya ya’ishe su.

” mamafarida tace Allah ya tsare ka dady yakara bude…..

     ” Ameen…

   Mota guda sukayi sannan suka huce gidan firdausi gidanta yayi kyau tana cikin dak’i tana rufe da bargo taje sallama har ta tashi Aliyu ya rikota au barina zakiye?

    ” cikin shagwaba tace su iyane fa dasu anty please kabarni naji nadawo! ….

     ” shima mik’ewa yayi ya saka jallabiya sannan suka fito tare gaisawa su kayi sannan suka tsaya suna hira sak’onta suka bata sannan suka mik’i…

     ” Aliyu ne yace har zaku tafi?

     ” wallahi zamu biya gidansu farida ne kuma yau zamu tafi…

      ” Dubu goma ya dakko ya basu, su kayi godiya suka tafi….. 

  Suna isa gidan farida suna palour suna san tea, gaisawa sukayi farida tace sadiya badai yau zaku tafi ba?

     ” anjima kadan zamu tafi anty farida…

     ” ‘yar hira suka taba Nan ma suka mike zasu tafi hamza yabasu 30 thousand…Suna isa gidan kande tana cikin dak’in ta sadiya ce ta huce daki yaya yaya…. +

     ” rungumeta tayi sister dama ku nake jira? Muje anty zee tazo  dai ko?

     ” eh, tsugun nawa tayi ta gaishesu suka amsa Nan suka dinga hira har zasu tafi sukace ina harunan….

     ” Diriss kande tayi sannan tace ummhm dama suna da meeting a office shine yaje yanzu zai dawo ai…

    ” A’a tafiya zamuyi, daki tahuce sadiya ta bita, yauwa Wannan kibawa goggo dubu ashirin ne kuma ga 50 kuraba…

    ” Tohm Angode, Ai zanzo in anyi mana hutu…

     ” yauwa dan Allah kizo Nagode muje , sadiyace ta mika musu kudin wannan mai yawa din?

     ” lahh bakomai hajiya ku gaida gida kuyiwa dady godiya…

       ” suna tafiya tahuce dak’in ta takwanta…

   ●●●●●●●

  Lok’acin Da haruna ya isa hotel din fuskarsa ciki da murmushi da Annashuwa…

      ” sannu da zuwa dear! Hope katashi lafiya?Nasan baka karya ba? ga wannan ta mika masa milk da bread bayan ya shanyi yace kyaufa kikeyi min kullum fa….

     ” rike hannun sa tayi tace really?

       ” yes manah, Nan ta dinga jansa da kalaman soyayya…..

     ” gurin 3 yace anyi sallafa bari natafi see u tomorrow….

    ” see you dear..yana fita tace yusrah fito kije…

     ” muneeba kina huta fa irin wayannan kalamai…

    ” ke dan ma yanayi mun kwarjini amma tuni zan rungumeshi…

    ” Amma fa kitashi muje gurin bokan nan domin ya saki wane aikin mai zafi!

     ” To ina zamu samu karen? ” Nasa akawo bari muyi wanka…

    ” karfe hudu tana dak’inta azaune kan sallaya abubuwa sunyi mata caaa akai, mik’ewa tayi tahuce kitchen ta zuba Naman da bread sai pepsi ta zauna adinning gaba daya gidan ya cika da kida…

    ” kallonta haruna yayi yakara ware murya..

    ” ita dai uffab bataci ba sai data gama tace anya lafiyarka yaya wannan kidan shaidanun kake sawa…

    ” gidan ki ne? Kukuma kikeka siya cd?

     ” Bani nasiya ba Amma kuma hakkina ne in gayamaka gaskiya!

     ” wayarsa ya dakko ya kirawo muneeba sunata hira…. 

” kuk’ane ya wanke Mata fuska muneeba yaya yau kwana biyu fa da auren mu!

     ” so what?? Malama matsa daga kaina zanyi waya…

     ” batasan lokacin da ta fashi da kuka ba ta shige dak’inta wayan ta ta dakko tana lalubar number nafeesa Amma kuma tajeta akashi…

     ●●●●

    Su muneeba ne suke driving sai faman dariya sukeyi kana ganinsu kaga kwararrun yan duniya…

     ” muneeba dazu naga kamar dad naki ya kirawo ki?

    ” ke matsalar kudi yakeyi nayi masa sending, kisan dad indai zansamo kudi Na bashi bashida wani promblem, mum keda matsala cux tuntuni tace bani ba’ita…

    ” let me tell you! Tuntuni nasha tsinanne ya mallaki minsu, yanzu sai yarda nayi dasu, ke nasamu Wane Alhaji 1day 50million zai bani fa….

      ” Nema kwanaki mun hadu dawane mutum but ba easy fa!…

     ” dariya tayi sannan tayi parking din car din suna jan karen suka shige cikin dajin wasu suka tarar sannan suka hayi kan dutsen….

    ” keeee keee keee ku dakata akwai matsala fa yarinyar da muka turawa Aljani tafara kona kafarshi domin komai nata da Am baton Allah, kuma zata lalata aikin mu ko mukashi ta?….

   ” yusra ce ta mika masa k’aren ya karba yana dariya wannan shine aikin ku zamu gaba miki da shi harunan…..

    ” muneeba tace inason duk abinda nasa shi yayi kuma inaso yatsane matar sa,kafin nashiga ya koreta tabar gidan….

     ” hehuhehahehuuuu angama ki kwantar da hankalinki kin samo booo ku tafi ku tafi…

     ” mik’ewa sukayi sannan suka huce zuwa motar su ware waka sukayi suna tafe suna binta duniya tayi musu dadi….

    ●●●●●

     Barka da dare dady yagida ya kokari????

       ” banson sha shanci? Haruna ina kake zuwa office sai kaga dama kake zuwa? Me ke faruwa ne?

     ” murmushi yayi yace dady ban dan jindadi ne, Amma zan shigo in anjima Inshaa Allahu…

    ” Toh dai ak’i yayi ita sana’a ba’ayi mata haka adinga kiyayewa …

    ” toh, bari nashiga Mugaisa dasu mumy karasawa yayi suka gaisa, Anty tana sama ya karasa ya gaidata…A’a su kande an iya kiyo dubi yadda kayi wane fresh! +

    ” sauya fara’ar fuskar shi yayi yace wacce kande kuma muneeba dai….

     ” Anty dai cikin rashin fahimta tace koma me kake kiranta ga wannan sakon kakai mata….

     ” karba yayi batare da amsa ba ya huce…

    ” Tana zaune tana gyara wasu takardun ta haruna ya shigo watsa mata ledar yayi…

    ” Subhnlhi menene haka yaya? Ko sallama fa bakayi ba?

     ” Ke nefa Na tsaneki bama nason kallonki so from today karna kara ganin ki A palour na! in ba haka ba duk abunda  Nayi miki ke kika siya…

    ” Mik’ewa tayi ta shige dak’inta Sallah tayi sannan ta d’an k’i shingida Nan tafara mugayen mafarki farkawa tayi sannan ta mik’i zuwa bandaki Alwala tayi sannan tayi sallar isha’i Nan ta tsaya tanata Addu’a har bacci yayi awan gaba da’ita…

     ” my muny ina kika shiga ne nakasa sukuni tun dazu muryarki kawai nakeson ji…

      ” ohh love Nabar phone ne a daki ina palour! But Am srry love 30missed call not be easy oooohhh…

     ” ina fatan kina cikin koshin lafiya gobe zanzo hotel din mekike bukata natawo miki da?

    ” kai Nake bukata nagani please kazo da wuri…

     ” okay madam bari na kwanta!…..

●●●●●●

    Hamza ne ki zaune apalour yanata danne danne acikin laptop, farida ce tafito dauke da tray a hannunta…

    ” ajiye tray din tayi sannan ta zauna kusa dashi sai data sakankanci sannan ta dauke system din!.

     ” menene haka dear??

          ” haba husby tun dazu kake faman aiki fa Amma kwata kwata bakaci Abinci ba! Hankali na ba akwanci yake ba!

        ” hannun ta yarike oky dear kawo nasha!…

       ” murmushi tayi tace menene Amfanina ta fara bashi abaki….

    ●●●●●

      Muneeba ce ke faman sintiri, haruna tana shigowa ta fada jikinsa Nan ya dan zame what wrong dear?

     ” Don’t you see how i look! Wife naka takirane ta cimin mutunci harda cewa zata kasheni…

     ” what! What!!…u mean aisha?

      ” yes..kasan dai inasonka so banason abunda zai bata maka rai please kadaina damuwa da’ita…
     
    ” riki hannunta yayi yace zaki aure ne?

      ” murmushi tayi ta cije lebe soonest haka?

      ” Hakan zaifi kwantarmin da hankali dear please ki amince mana!.
    
    ” okay kaban 2mouth zanyi thinkn….

    ” murmushi yayi sannan ya fita yana karasawa gida directly dakin kande ya huce…

     ” lafiya kashigo min dak’i? Ko har tozarcin naka yakai haka?

      ” wanka mata maro yayi sannan yakara wanka mata mari….

   ” yaya marina kayi fa? Bazance maka komai ba, zan cigaba da zama dakai har lokacin da Allah zai bayyana mai gaskiya….

   ” bakar munafika daga yau inason kisane muneeba ita zan aura ko kinaso ko bakya so….

    ” Anya lafiyarka yaya..fita yayi yabarta ta fashi da kuka..Ahaka tafara kuka har Nafeesa ta shigo lafiya lafiya???

    ” Neman mata yakeyi takara fashewa da kuka wai aure zai kara!

     ” wa kike magana wai…

       ” haruna mana! ” haruna kuma innalillahi mekikaye masa?

    ” cikin kuka ta bata labari…

      ” Innalilahi Aisha Anya ba da asiri ba anya??? Any way ma yakamata afara bincikar abokansa da Wanda yake hulda dasu…

    ” cikin kuka tace yanzu ya zanyi Nafeesa wallahi ina son yaya…wallahi ina kaunar mijina…Innalilahi Aisha Anya ba da asiri ba anya??? Any way ma yakamata afara bincikar abokansa da Wanda yake hulda dasu… +

    ” cikin kuka tace yanzu ya zanyi Nafeesa wallahi ina son yaya…wallahi ina kaunar mijina…

     ” Nafisa ce taje tausayin yadda k’ande ke kuka, idon ta ta kallah cike da son mijinta, can kuma ta dafata ki daina kuka yar uwa Allah yana tare dake, abunda nakeso kisani kowa da irin kaddarar sa, Da kuma nashi kuncin rayuwa, kowacce kaddara batada Dadi Amma inkana Addua kana hakuri Allah yana saukaka maka!!!

      ” Nafisa kin kasa gane halin danaki ciki wallahi ko kusa dashi bayaso nazo, babban tashin hankalina wayar da kullum yakeyi da wata wai baby muneeba, i don’t know her? Bansan aina take ba taraba ni da mijina wallahi baya tane ina tsoron kada tajashi yayi….

        ” Daina Aisha karki karasa…Tabbas Namiji da bin mata babu dadi Amma Allah zai kareki inshaa Allahu kuma shima bazai auka wannan mummunar aikin ba…..

      ” Ina da hujjata dana gayamiki haka! Tun kafin nayi aure yake cikin muguwar sha’awa hakan yakan tsorata a yayin danaga baya shiga har kata ko abinci na baya ci fa!!!….

     ” bakomai komai zai huce kiyi hakuri amma kima danaki laifin dubi cd na wakoki apalourn ki sai kace kabila karfa ki manta yar’uwa tsoron Allah shine gaba da komai, ki yawaita karatun Al’kur’ani ba jin wayannan wakokin ba!

    ” Kinfi kowa sanina banfiye jin waka ba maigidan ne yasiyo abubuwan sa kullum ina masa magana Amma ina kullum cigaba yakeyi, kuma wallahi cikin kwanakin nan kamar an hanani ibadar sai nayita jin kasala ina jin bacci….

     ” duk aikin shaidan ne ke dai kitashi ki dage da Addu’a wallahi tun abu baiyi karfi ba!

     ” inshaa Allahu yar’uwa wacce shawara kike ganin zanbi?

     ” yauwa ina fatan kinsan abokanan sa?

     ” wane Amininsa nasani mukhtar dan da har gaisawa mukeyi…

     ” Toh kinemi number sa kije mike damun haruna sai asan ta inda za’a bullowa matsalar…

     ” wai abu mai kamar wuya, Amma zan gwada ki dubi yadda narame DanAllah?

       ” hmm bakomai ne bari Natafi sai munyi waya karki dinga sakace da addu’a dai nagaya miki…

     ” inshaa Allahu Nafeesa karki sanar da kowa danAllah ya kasance sirri a tsakanin mu….

     ” Tohm babu komai sai munyi waya Allah ya karya duk wane mugun Abu…

     ” Ameen..

           Bayan fitar nafisa Alwala tayi sannan tayi sallah kitchen ta shiga ta dura shinkafa da miya tana gamawa tayi wanka sannan ta dauki kur’ani tafara tilawa cikin babbar murya can kuma taje an ware murya waka sai tashi takeyi duba agogo da zatayi taga karfe 9 hawaye ne ya zubo a cikin idonta, A hankali ta mik’e tana fita taga ya miki tsayi yana waya har yafita, ita dai bataci dashi kala ba, a hankali ta bude dak’insa karamar wayarsa tagane tana dauka tafara kwafar number taje shigowar sa sauri tayi tashige bandaki…

      ” haruna ne ya bude dak’in yace baby muneeba Ai Nazata wannan jakar yarinyar ce ta shigo min daki da kuwa saina karya ta…

     ” cikin murya ta kwararru tace haba babyna i have tell you kadaina damuwa da’ita ka dauketa a matsayin shara!…

     ” okay my baby bari Nazo Nakawo miki ice cream, Bari na Dan watsa ruwa….

    ” cikin kande har ya kada sai kuma taga yafasa yafita, wasu sababbin hawaye ne suka karasa zubowa a fuskarta, wayar sa ta ajiye masa tayi saurin shiga Dak’inta ta saka key……

   
  ●●●●

      Mumy ce ke faman murmushi tana fara’a can tace kinga mama farida yaran nan lafiya lou suke da mazajen su…

  ” Dady yace gashi kusan 4 mouth Lafiya kalou babu wane matsala ai sai dai mugode Allah…

      ” Ita dai mama farida binsu take da kallo domin kande tun washe garin da aka kaita bata kirawo su ba hakan yasa ta shiga daki tafara neman number ta….

     ” Cikin sarkakiyar muryar dakasan kukatayi tace ina kwana Anty?

     ” haba kande ace tunda kikaye aure yau kusan wata hudu Amma bakizo ba duk’a ‘yan uwanki sunzo?

        ” cikin toshe baki tace yaki yabarni Shiyasa yaki yabarni….

      ” Anty tace to me nakeji? Kamar kina kokarin yin kuka dan yahanaki fita karfa kizama sokuwa namiji ya rainaki!… +

    ” Amma dai ya kamata ace Nazo ai!…

  ” Bakomai ai darajar ‘ya mace gidan mijinta ke dai kiyita hakuri..

      ” Toh tace takashe wayar ciki da hawaye acikin idonta tace da kinsan halin da nake ciki da baki kirani ba…

     ” Dady ne ya rungumeta ta baya ina Alfahari dake Matatah…

    ” Jiyowa tayi tana fuskantar fuskarsa tace ina Alfahari da kai mijina, kasan yanzu yaranne sai ana musu fada..

    ” hakane ne bari Na fita me kikeso Atawo dashi?

   ” Tace duk abunda kaga yadace damu..

     ” Tohm yace sannan yayi sallama..

●●●●

    Wai haruna kana cikin hankalin ka kuwa?

     ” menayi kuma mukhtar Ne fa Aure nakeso ma Nakara!

    ” Ai dama nace kana bukatar mental checkup, kullum Azumi abun fa yafara bani tsoro…

    ” To zina kakeso nayi? Tana daga cikin Abinda kullum nayi sallah sai nayi Addu’a Akan Allah yatsare ni but muneeba tana yimun abubuwan da basuda kyau hatsareni agareni wallahi…

     ” mukhtar ne yayi galala da baki yana kallon sa…

      ” kasam Allah maza babu abunda nake tsoro irin Azabar Allah gareni shiyasa kullum nake azumi…

     ” Mtseww kai dai wallahi kanada problem akanka, ni jinakeyi kamar ba kaikaki magana ba, ina matar taka?

    ” muneeba dai zan Aura soon, Amma ne natsane kande banason ganinta kai ne ko kallonta banson nayi….

      ” shiru mukhtar yayi sannan yakara watso masa wata tambayar yace wacece kuma muneeba…

     ” murmushi yayi yace har naji dadin sunanta daka Ambata matata ce nan da yan kwanaki, inasonta itace rayuwata…

    ” shi dai muktar shiru yayi yace wannan abu kamar rudani…

   ” Toh maza bari naje gida Inada inda zanje..

     ” Shidai mukhtar yana cikin hargetse mikewa yayi yasamu khalifa yace kai wacece muneeba?

     ” wata yarinya ce damuka hadu a india it seems like zaman kanta takeyi fa, cuz ta mutu akan haruna tana sonsa over dan lokacin dazamu dawo sai cewa tayi indai tana duniya sai tayi komene domin haruna ya sota…

    ” Toh Allah yasawake…

       ” Ameen aboki…

●●●●●
    *Kauye*

    ” sadiya tace goggo ina baki labarin gidan ‘yarki wato dai gidan nan ya gadu komai na zamani kinga wasu kofofi ma!…

     ” Toh sadiya Allah yabasu zaman lafiya, Naji bata kiramu kwana biyu ba,…

     ” Eh to inaje ko wayan tasamu matsala nidai abunda zance ki kasance cikin yiwa ya kande Addu’a domin ‘yarki tana bakin mutane…

     ” Allah ne ke karewa kuma zai kareta, dauki kikaiwa iya habu wannan kwan…

      ” salamu alaikum .

   ” wa’alaikis salamu, ja’era yanzu nake jiran zuwanki zoki lalubo min number haruna mugaisa…

       ” Tohm yauwa gashi yafara ringing hello hello haruna kaci gidanku…

    ” murmushi yayi yace iya ina yini?

     ” lafiya lou ina kande bani ita mu gaisa..

      ” Shiru yayi Nadan lokaci sannan yace to daga Nan ya mik’i ya shiga dak’in babu Abunda takeyi sai karatun Alkur’ani ke ya cillamata wayar…

    ” dauka tayi tace inayini lpya lou ‘ yata babu dai abunda yakeyi miki?

    ” cikin jin tausayin kanta tace lafiya lou babu komai…

    ” To kikwantar da hankalin ki zanzo kwananan kinje?

     ” Tohm sai kinzo..

  ” tana Gamawa yace karki mikomin ajiye akasa zan dauka domin banson kizo near me…

     ” Ita dai kala batace masa ba..

●●●●
muneeba ke faman sintiri a bakin hotel din can taga ya fakar da motarsa…

      ” baby muneeba Am sorry wallahi waccan yarinyar ta batan lokaci….

     ” awana daya ina jiranka, wato matarka tafine kenan?

     ” haba baby wacce magana kikeyi hakane ya za’ayi tafiki? Kinsan nafi sonki fa!…

      ” Anyway nafasa fitar katafi da daddare ko minti daya kakara wallahi bazanfita ba u understand?

    ” haba my dear kinsan dai i can’t go kuma kina fushi dani..

    ” hugging dinsa tayi tace how can i be angry with my husby..

      ” has u said it! Known am happy, cikin zuciyarsa kuwa fade yakeyi why not muneeba ta daina rungumeshi?

     ” Kanada magana ne? nop banda! But i will miss u dear!

      ” hotel din ta shiga a bakin kofa sukayi kicibus da yusra nan tace har kindawo …?

     ” yeap, ya mutumin nake? ” ke akwai matsala fa cuz shikansa haruna yanada addu’a komai sai ya ambaci Allah, kuma sai mafarki nakeyi da matarsa wai ta biyo ne da wuka tana addu’a….

     ” hahaha see you muneeba wayaki ta dreams ana relity? Malama kece da goganfa….

     ” hmm yusrah ko irin wannan hugging din nasa danakeyi baya so fa!…

    ” zai mafaraso ma ke me komana ledar mana!…

   ●●●●●

     Tsaki yaja ayayin daya isa bai tarar da kande ba? Wane haushin kansa yaje daya barta tatafi gida…

       ” guri yasamu ya zauna a setroom dinsa yanata kallon gari shi dai jinsa yakeyi wane iri baisan ainahin menene matsalar sa ba…

   ●●●●

      Tunda kande taje suka gaisa da dady yake tambayar ta lpyta kalou dai?

     ” lokaci daya hawaye yatawo sai tayi sauri ta goge lapya mu kalou dady..

    ” Anty ce taketa tsokanar ta ko ciki ne yasata rama?

    ” murmushi karfin hali tayi tace sai dai ko firdausi…

    ” firdausi tace ai ne da bazan kulaki ba ko ankira wayarki ba’a samu yaya haruna yawane kulleki acikin gida haba please kidinga shan iskar gari mana…

     ” To firdausi.. barina zauna ne nagaje ma tun karfi uku suke hira sai gurin 5 anty tace to kowaccen ku sai ta zo mu shiga kitchen Nan sukayi girki sai karfe 6 Aliyu yazo bayan sun gaisa kande tace nidai ku ajiye agida…

    ” Mumy ce tace toh idan Haruna yazo fa?

     ” shiru tayi sannan tace gwara na tafi Nagaji wallahi..

     ” A mota sunata hira har suka ajeyi ta firdausi tace my husby nayi mata alkawari zaka kawone fa?

   ” Kande tace ai yaya aliyu baya hanaki zuwa ba..

   ” Tana shiga taga haruna yana kallonta, Ta gefensa ta huce sannan takarasa ciki dauke da flask a hannunta…

    ” biyota yayi ne zaki mayar karamin mutum kinje kince musu bazan iya kaikeba kenan shine harda sa su firdausi su ajiyeki?

    ” Cikin bacin rai tace toh yakakeso nayi kanaso Natawo akafane? Naga lokacin dazan tafi hanani kudin mota kayi…

     ” shiru yayi sannan yace from today ban yarda kibiyo kowa ba in bahaka ba!!..

     ” In bakaso Na biyosu sai ka zo ka dakko ne?

     ” Ne zan daukike a motata? See this bulshit…

      ” Ai in muneeba ce  bakada matsalar kaita tashige cikin gida..

   ” Bayan sallar isha’i kande ta kira mukhtar awaya tana kuka taba cewa Dan Allah meke damun haruna?

     ” hmm Lamarin fa akwai hargitse acikin sa sai dai Allah yasawake, nikaina nakasa gani kansa Amma kuma akwai yarinyar danake zance wai ita muneeba…

     ” wallahi itace kullum nema zancen ta yakeyi min kullum nifa ina tsoro kada ta…

     ” babu abunda zai faru domin na tabbatar da asiri tayi masa…

     ” To wai ita wacece yarinyar?

     ” a binciken danayi muneeba yarinya ce yar shekara 28 takaranci art and business tayi kuma karatu a turkey mahaifinta haifafan can ne ita kuma mum nata yar nigeria ce, zaman kanta takeyi dayawo aduniya da bin maza…

     ” innalilahi To mukhtar tayaya za’a rabasu?

     ” karki damu addu’a zaki dage da ita idan yana bacci ki dinga ware masa karatun suratul bakara kamar yadda annabi (saw)yace gidan da ake karanta suratul bakara shedan baya zama ballantana ya haihu wannan itace kafa tafarko da zaki fara yi masa, tabiyu kuma komai rashin jituwarku idan ya kwanta bacci ki dinga yimasa addu’oin kwanciya bacci…

    ” Zanyi inshaa Allahu to tayaya za’a karya sihirin yanzu?

     ” sihiri dai gaskiya ne kamar yadda yagabata kuma akwai hanyoyin warwareshi zamuyi waya gobe kidai kifara wayannan din…

     ” Tohm inshaa Allahu zanyi nagode..

    ●●●●
Yau jumma’a tana zaune tana kuka akan kujera mama farida ce tayi sallama kukan da taga tanayi shi yatada mata hankali ….

      ” lafiya kande lafiya?

    ” A firgeci ta tashi au anty yaushe kikazo?

     ” kukan mekikeyi?

” Babana natuna shiyasa nake kuka…

     ” To Allah yayi masa rahama kina lpya? Duk kin rame ko cikin ne?

” kuka tasaka tace Anty please kicewa dady yaushe zan fara zuwa makarantar?

   ” wallahi wannan fuskar taki akwai damuwa..?

     ” kuka tasaka tace baya kaunata wallahi, Allah Anty baya son……

  

About Ismail

Check Also

KANDALA CHAPTER 6

KANDALA CHAPTER 6 To hamza nagaji da jiranka yau kusan sati biyu kana yimun wasa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *