[Advertisements⬇️]

GAMAYYAH CHAPTER 8 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GAMAYYAH


CHAPTER 8


Sanin batada ikon gardamawa yasa bata gardamaba ta rintse idanuwanta ahankali tareda Jan wani irin numfashi jin hannuwansa sun sauka a qirjinta
Sakin bakinta yayi ahankali ya dago lazy eyes dinsa yakalli idanuwanta dake rufe
Ya kai bakinsa saitin kunnenta ya furta mata wata kalma ahankali ta bude jajayen idanuwanta sai cikin nasa ta lumshe ido tasake budewa yakai bakinsa ahankali yayi kissing idonta na dama tareda cusa kansa cikin wuyanta yana giga mata dogon hancinsa nan tsigar jikinta duk ta miqe
Yasake dagowa ya kalleta hannuwansa na ‘dago masa kanta idonsa cikin nata ya Dora bakinsa anata ta rufe ido ahankali sbd jin inda hannunsa ya nufa. 2

Duk yanda takeda juriya saidata zubarda hawayen wahala sosai musamman data tabbarda ta fita daga cikin sahun ‘yan mata har abada. 1

Lumshe idanuwanta tayi hawaye suka gangaro tareda kallon qofar bathroom dinda yashiga.
Har lokacin jin hannunwansa da kisses dinsa takeyi ajikinta Wanda suke qoqarin ruda mata kwakwalwa saidai ko tashi bazata iyayiba sbd ba qaramar gajiya ya sauke akantaba ta rufe ido bacci yayi gaba da ita ahankali.

Qurawa kansa ido yayi ta cikin mirror tareda rufe ido yabude yasake kallon fuskarsa ya fitarda numfashi tareda mamakin kansa da yanayin dayakejin kansa.

Wanka yayi yafito daure da towel batareda yakalli gadon datake kwanceba ya nufi gaban mirror yayi amfani da hand dryer ya busarda gashinsa ya saka wasu kayan baccin ya nufi gadon.

Kwantawa yayi ya qurawa fuskarta datai jajir ido dagayen eyelashes dinta duk sun nannade da hawaye sbd kukan datayi duk da bamai sauti bane kukan,

Suhailat bata taba masa kuka ba idan suna making love ko a first time dinsu kuwa.
Rufe idanuwa yayi tareda shigewa dovet.
1

Qarfe takwas sultana ta fito palo cikeda mamakin rashin ganin rumanah din zuwa gaidata. 1

Zama tayi tareda kallon Carolina dake jera breakfast a dining tace takira mata rumanah.

Aje aikin tayi ta nufi dakin rumanah da sauri tana budewa bata gantaba tadawo cikin ladabi tace tana toilet.

Gyada kai sultana tayi tareda miqewa takoma bedroom dinta

Bayan mintuna tasake fitowa sbd ganin time din tafiyarsu yana matsowa tasake aikawa still tana toilet cikeda mamaki ta nufi dakin da kanta saidai har toilet taduba babu rumanah.

Duk inda ake saka ran ganin rumanah Carolina taduba batanan hakan yasa sultana zauna palo cikin fargaba tafara qoqarin kiran wayar maheer amma no answer.

Ahankali yabude idanuwansa cikin wata irin kasala yana kallon agogo ya dafe goshinsa cikin mamakin bacci mai nauyin daya hanasa tashi.

Gefensa ya kalla yaga har lokacin bacci take dunqule cikin duvet gashinta duk a barbaje kan pillow.

Fita duvet din yayi ya sauka gadon ya nufi toilet ganin yayi latti sosai yasa bai tsaya wanka ba yayo alwala yaxo yatayarda sallah.

Yana gamawa ya dauki wayarsa daketa fidda blinking alamar kira

11 missed call daga hospital yasan suhailat ce aka sallama
Sai 9 missed call daga ammy
Miqewa yayi yafada toilet.Yana shiga tailet ta farka ta bude idanuwanta ahankali sbd nauyin bacci dana kukan datayi tana ganin baya dakin tafara qoqarin miqewa ta sauko daqyar riqeda bargo tana rufe jikinta tajawo rigarta ta barci dake tsakiyar dakin yashe.

Tana daukar rigar yana bude qofar toilet yafito daure da towel,
Kasa dagowa tayi bare ta juyo saima rawa da jikinta keson dauka

Shareta yayi ya nufi gaban mirror yana goge gashinsa sbd Sam bayajin damuwar komai ko gajiya ras yakejin kansa. 7

Ganin kamar hankalinsa baya kanta yasa tayi saurin zura rigarta ta cikin bargon amma still kasa miqewa tayi.

Wayarsa tayi blinking yaga kiran ammy ne yayi saurin kallon agogo yaga har tara takusa Sam yamanta da tafiyarsu.

Shiryawa yayi cikin white shirt and blue jeansy trouser ya daure gashinsa ya dauki wayarsa ya nufi qofa,
Zai fita ya tsaya batareda yajuyo ba yace,

Saura 40min jirginku yatashi. 6

Yana gama fada yafice daga bedroom din.

Qofar ta kalla bayan ya wuce ta rintse idanuwanta ahankali tareda fitarda numfashi ahankali kafin ta miqe ta taka daqyar ta dauki doguwar rigarta ta zura kan rigar baccinta ta nufi qofa tana qoqarin daidaita tafiyarta duk da zafinda takeji.

Saukowa taringayi ahankali harta gama saukowa ta nufi dakinta
Tana kaiwa tsakiyar palon tayi ido hudu da sultana zaune ta zuba mata ido cikeda mamaki.

Sunkuyar dakai tayi idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin kunya da nauyin ammyn.

Juyowa sultana tayi ahankali cikeda mamaki takalli inda yake zaune yayi tamkar baimasan da isowar rumanah dinba ya danna kira asibiti.

Kasa maida kallonta tayi kan rumanah sai kawai ta miqe ta nufi dining.

Jiki sanyaye ta qarasa daki tafada toilet sai kawai tasaki siririn kukan kunya da ciwon da jikinta ke mata.

Wanka tayi da ruwan zafi sosai kafin ta lallaba ta fito tayi sallah ta shirya cikin sauri sauri ta fito kai sunkuye

Kallonta ammy tayi cikin sanyin murya tace,

Kizo kiyi breakfast mutafi munyi latti.

Kai ta daga ta nufi kicin a darare ammy tabita da sabon kallo harta shige tasake juyowa takalli maheer dako gefensu yaqi kallo,

Mamakin duniya ne ya taru akanta gashi Sam ko fuskarda zatai masa wata magana yaqi bata bare taji makomar rumanah daga garesa.

Daqyar ta iya shan tea da biscuit ta fito daidainan Carolina tagama fitar mata da kayanta zuwa mota.

Kodata fito ammy ta nufi waje sbd sunyi latti sosai dan haka ba kowa a palon saishi azaune yana waya
Qofa ta nufa riqeda qaramar jakarta tana qoqarin wucesa yakara mata qafa ta kwashi wani mugun tuntube ta fada masa ya aje wayar hannunsa tana qoqarin tashi ya matseta da hannunsa daya tareda kallon cikin idonta ya dauke gira daya cikin izza yace,

Ance kitafi ne? 6

Kallonsa tayi da sauri kafin ta Girgiza kai.

Hannunta yakamo yasaka mata wata Leda tareda sakinta ya miqe yafita batareda ya waiwayo ba.

Bayansa tabi da kallo kafin ta dawo da idonta kan ledar daya saka ahannunta taga magungunane

Sake dagowa tayi takalli qofar fuskarta da mamaki.

Qofa ta nufa ta fito tana sake damqe ledar maganin a hannunta ta nufi motar da tagansu.

Driver ne zai kaisu dan haka dukkaninsu baya suka shiga yana tsaye yana kallonsu aka tayarda motar
Dagowa tayi ahankali ta saci kallon gefensa idonsu yashiga cikin na juna tayi saurin sauke kai tareda sake damqe ledar maganin daya bata.

Suna fita yafidda key ya nufi hospital sbd tuni suhailat ta damu dayazo daukarta
Shikuma ji yake da bayada aiki sosai ammynsa xaibi Libya sbd damuwar sultan yasan haryanxu tana ranta
Yana isa asibitin yahadu da doctor dinda ke kula da suhailat sukayi magana da sauran rubuce rubuce suka nufo gida.Tun ahanya takeson tambayarsa maganar rumanah saidai zuciyarta na gargadin bakinta da furtawa sbd sanin bazaiso maganarba karma ta bata masa rai da kiran sunan an aura masa baiwa.

Suna isa gida ta tararda komai fes tashiga dakinta tayi wanka ta shirya cikin simple kaya marasa nauyi ta nufi bedroom dinsa.

Cikeda mamaki ta tsaya tsakiyar dakin tana sake bude hancinta sbd dakin wani qamshi yakeyi na dabam Wanda ta tabbar bana maheer bane.

Zama tayi bakin gado ta rafka taguma tana wasi wasin tunani
Ganin qamshin zai iya buga zuciyarta yasa ta miqe tabar dakin sbd dama bayanan yana ajeta ya koma asibiti.

Sun isa Libya da qarfe shida na yamma motocin masarautar mahaifanta sukazo daukarsu cikin qanqanin lokaci suka isa babbar masarautar mai tarin dukiya da adalci
Masarautar mineelik saidai ta nuna musu girma da iko tareda dukiya wadda ta hada data mulkin mutanen da ba’a gani sbd dukiyarsu nada alaqa data mutanen daba nasuba amma a fagen adalci da qaunar talakawa da basu yanci basu kamosu ba ko kadan.

Saida suka sauka fadar sultan jalaluddeen suka gaidashi tareda gabatarda rumanah amatsayin matar yarima maheer yasawa aure albarka kafin suka isa babban sashen sarauniya salma matar sultan jalaluddeen mahaifiyar sultana zaarah.

Sosai aka hau hidimarsu duk da manyanci daya kama sarauniya salma tayi farin ciki da murna sosai ganin rumanah amatsayin matar yarima maheer sbd lurada nutsuwarta.

Sashe guda aka ware musu acikin part din sarauniya salma mai daukeda palo da bedrooms guda biyu dasukaji gyaran tsadaddun decor.

A babban palon s salma sukaci abincin dare tareda ita kafin kowannensu ya nufi dakinsa.

Tubewa tayi tashiga wanka ta jima tana dumama jikinta kafin tafito ta shirya cikin kayan bacci tayi sallolinta harzata kwanta taje ta dauko ruwa tazauna bakin gado tareda fiddo maganin daya bata tasha takwanta cikin qanqanin lokaci bacci yayi gaba da ita.

Bacci tayi sosai mai dadi sbd gajiyardake jikinta bata farkaba sai bayan sallar asuba ta tashi tayo alwala tayi sallah tasake komawa ta kwanta.

Qarfe tara ta tashi tayi wanka tashirya tafito cikin doguwar riga black mai adon red sequence stones.

Dakin sultana ta nufa ta tararda ita tana waya tajira harta gama ta gaidata cikin girmamawa.

Cikeda kulawa sultana ta amsa tareda cewa,

Ya jikinki?

Shiru tayi takasa bata amsa sbd nauyi.

Shikenan tashi kije zansa afara kulawa dake harkiji sauki sosai sbd haryanxu jikinki bai nuna kin warkeba.

Kamar munafuka ta fito sbd tsananin kunya da nauyin ammyn datake ji musamman data riga tasan tabbas ammy tasan meya faru tsakaninsu.

Kodataje gaida s salma acan tayi breakfast dinta har akazo kiranta ta tashi tabisu tanaji tana gani aka hau gyaranta da gashinta kullum cikin sakata cikin ruwan zafi da wasu irin magunguna ake kuma kullum sai anbata ‘danyar madara tasha cup daya da safe gashi aiki ko daya anan batayi saidai idan taji jikinta yayi tsami da yawa taje dakin sultana tahau aikin gyara mata kayan wardrobe da wankin toilet duk da akwai masuyi amma wani lokacin tafison tanayi

Satinsu biyu tasaba sosai da kowa,
Sultana mamakin rumanah takeyi bata taba tunanin zataga rumanah tasake hakaba shiyasa ba bata lokaci tasa aka dauko wani Mexican malamin wata collage yana zuwa koya mata karatu.Sosai tayi fresh abinta ta dire dakyau kyawunta tuni yaqarasa bayyana sbd Hutu da gyaran da ake mata kamar kullum. +

Wanka tafito ta shirya cikin kayan bacci riga da wando tazauna bakin gado tareda jawo bedside drawer taqurawa ledar da kullum saita kalla ido tareda lumshe fararen idanuwanta tanajin hannunsa ajikinta lokacinda zai saka mata ledar ahannu.

Sake lumshe ido tayi tareda zamewa ta kwanta ahankali tana jin wata irin kasala.Sosai ta warke takoma tamkar batai ciwoba sun cigaba da rayuwarsu kamar da tuni tafara zuwa aikinta hankalinta kwance sbd ganin maheer yamanta da wata maganar aure da aka daura masa,
Abinda yake damunta yake hana mata bacci wani bi ‘dayane,
Maheer Sam bai cika nemantaba kamar da ataqaicema yarage sha’awa sosai sbd wasu lokutan tana lure da inda baya taba mata da yanxu yana tabawa saidai ita Sam bataso musamman nonuwanta Sam batason yana yawan tabasu sbd batason suyi laushi da wuri gashi dama shayarwa tafara lausar mata dasu.
Ada Sam basu damesaba shima amma yanxu yanason tabawa tarasa meyasa hakan. 3

Wannan karon sbd ganin uwar datasha dakuma tiyatar da akai mata yasa tayi allurar shekara biyu sbd tahuta mahaifarta tasake qwari.

Fitowarsa wanka kenan daureda towel wayarsa tayi ringin yakalli wayar kamar bazai daukaba saikuma ya daga.

OK kawai yace ya aje wayar ya shirya cikin kayan shan iska ya sauka.

A palo ya tararda baqon nasa yadauki remote yana canza tasha yace,

Uhumm.

Gyara zama mutumin yayi cikin girmamawa yace,

U wanted to see me sir.

Batareda yakallesaba ya karbi coffee dinda suhailat ke miqo masa murya a dake yace,

I need a first-class vip ticket…… 6

Kallonsa suhailat tayi da sauri cikin mamaki tace,

Zuwa ina? 1

Libya”””yafada kai tsaye yana sipping coffee dinsa idonsa nakan TV.Da sabon mamaki tasake kallonsa,

Libya?
Amma baby mezakajeyi a Libya yanxu? I mean is everything OK?……
Dakatawa yayi dashan coffee din ya ajiye tareda juyowa yakalli gefenta cikin izza yace, +

Ammy na Libya kike tambayan mezanje yi acan?unbelievable.

Miqewa yayi yabar palon sbd bayason damuwa da tambayar dazeta iya bata ransa.

Bayansa tabi da kallo cikeda mamaki saidai batajin dadin tambayar datai masaba itama sbd mahaifiyarsa nacan baikamata ta tambayi mezaije yiba.
Miqewa tayi tabisa dan basa hkr saidai koda taje waya yakeyi haka ta zauna jiran yagama.

Zaune suke a qaramin palon baqin s salma itada Mr aarib suna karatu harsuka kammala ya kalleta cikin sakin fuska yace gobe bazai samu damar zuwa ba qila sbd yanasaran zaiyi tafiya idan baiyiba zaizo.

Gyada masa kai tayi cikin sakewar fuska ita suka fito kusan atare yana sake maimaita mata wasu English words daya koya mata itakuwa sbd ta sake fahimta bakinsa ta qurawa ido tana daga kai ahankali fuskarta asake sbd ba laifi sunsaba da Mr aarib.

Tab dinda ake mata karatu da ita ya miqa mata ta amsa tana murmushi tace,
Thank you

Cikin jin dadi yace,

Ure welcm.

Juyawa yayi ya fice ta nufi qofar palon s salma na gaba tashiga har lokacin fuskarta daukeda murmushi tana shiga palon ta tsaya cak tareda juyawa da sauri sbd qamshin dataji yacika palon.

A fuskarsa idonta ya sauka yana zaune yana mgn da s salma gabanta yayi wani irin faduwa wani irin yanayi yashigeta na fargaba ko fuskar gaidasa bata ganiba ta hadiye wani yawun fargaba ta daga kafa daqyar ta isa gabansu kanta a sunkuye ta gaidasa batareda yakalletaba ya ‘dan daga hannu
Juyawa tayi ta wuce sbd yau babu batun fira a gurin s salma. 2

Tana isa palonsu ammy na zaune tana kallon wani English program
Zama tayi tareda aje tab dinta tana cewa,

Ammy yace qila gobe bazaizoba.

Ammy na kallon TV tace,

Eh ai gwara karyazo yanxu yajira bayan kwana biyu tukuna sbd maheer dake qasar baku hadu a palon ammee ba?

Eh yana can.

Murmushi tasaki tareda kallonta sbd jin amsar dan batai cikakkiyar kama da tambayar datai mata ba
Maida kallonta tayi kan TV tana cewa,

To yayi kyau.

Miqewa tayi ta nufi kicin jikinta duk ya mutu tasha ruwa ta tsaya jikin fridge tsawon mintuna tana sauraron bugun zuciyarta daya canza yaqi daidaituwa tun lokacinda idonta ya sauka akansa.

Fitowa tayi ta nufi dakinta ta zauna bakin gado tareda jawo bedside drawer ta kalli ledarta tsawon mintuna kafin ta rufe tareda sauke numfashi
Gabaki daya tarasa meya dagula mata nutsuwa ta miqe ta nufi toilet tayo alwalar sallar magrib datayi tazo ta tayarda sallah Tana gamawa palo ta fito ta nufi qofar fita dan zuwa gurin s salma saidai tana kaiwa qofa ta tsaya takasa shiga sai kawai ta juyo tadawo tana zama a palon sultana na fitowa ta zauna tana cewa, +

Yau bazaki gurin ammee bane?

Murmushi yaqe tayi cikin sanyi tace,

Karatu zanyi.

Satar kallonta ammyn tayi kafin tayi magana sukaji qamshinsa yashigo palon tareda sallamarda shikadai yaji abarsa.

Fuska ammy tasaki cikeda farin cikin ganinsa.

Itakam miqewa tayi riqeda tab dinta kanta asunkuye zata bar palon tana kawowa gurinsa kamar alamara sai tuntube
Tab din hannunta ta fadi
Sai kawai yatake ya wucewarsa batareda yanuna yasan da itaba bare tab dinta. 10

Cikeda mamaki ammy ke kallonsa tana kallon tab din da screen yayi mugun damage mamakinta meyasa ya taketa dan tanada tabbacin yaganta.

Rumanah kuwa tab din taqurawa ido sbd yanayin takawar ya nuna kamar yasan da ita to meyasa?
Kodai laifi tayi?

Sanin babu ikon tambaya ko sanin dalili yasata duqa ta dauka ta wuce dakinta.

Kallonsa ammy tayi ganin baimasan mesukeyiba yasa tace,

Maheer baka lura ka take tab din karatun rumanah ba?

‘Dagowa yayi ya zuba mata idanuwansa dasukai wani launi ko bude bakinsa yakasa sai kawai ya miqe yace, 2

Zan shige saida safe ammy. 6

Baki sake tasake kallonsa tace,

Maheer akwai abinda ke damunka?
You don’t seems alright,
Kodai sultan ne?
Ko abinci bazakaciba? 4

Juyowa yayi yakalleta daqyar ya iya cewa, 1

Gud night ammy.

Wucewa yayi yabar palon yanufi part din dayake nasa a masarautar tun kafin yayi aure.

Bayansa ammy tabi da kallo cikin fargabar abinda yake damunsa.

Zaune take gaban mirror ta qurawa tab din ido sbd ko kunnuwa batayiba alamudai sun nuna ta tashi daga aiki kwata kwata.

Hawaye ne taji sun ciko fararen idanuwanta sbd zuciyarta datake zargin laifi tai masa qila. 1

Aje tab din tayi ta rufe fuskarta da hannuwanta biyu tanajin damuwar hakan duk da tasan batai laifin komaiba saidai tana bawa kanta laifin koda acikin rashin sani tayisa. 5

Ammy ce tashigo dakin taganta ahaka
To itakuma wannan lafiya?

Cikin mamaki da kulawa tace,

Rumanah meya sameki?

Sunkuyar dakanta tayi tareda girgiza kai murya na rawa tace,

Bakomai.Bakomai kike kuka rumanah?
Dole akwai wani Abu kitashi kije kikaiwa maheer abinci ina jiranki idan kindawo mayi magana amma kam dole da wani abin. 10

Tashi tayi asanyaye tareda gyara zaman hular doguwar rigarta ta fito jiki asanyaye.

A babban tray ta jera masa komai ta fito ta wuce zuciyarta cikeda fargaba jikinta har wata rawar tsoro yakeyi amma haka ta nufi inda akace nan ne part dinsa.

Batai knocking qofar palo ba ta murda tashiga sbd sanin baya palo a wannan lokacin,

Kyawu da tsarin palon takalla koina qamshinsa yakeyi da sanyin AC ta nufi qofar bedroom tayi knocking ahankali tareda budewa sanin bazai taba maganaba ko bada ixnin shiga.

Baya dakin shiyasa ta nufi table din dakin kai tsaye ta ajiye tray din tareda bude fridge dindake dakin ta dauko ruwa tazo ta ajiye masa tana juyowa sukai ido hudu yana tsaye bayanta jikinsa ba kaya dagashi sai towel fari wannan karon dogon gashinsa asake ya zuba mata idanuwansa ya kafeta dasu yanda ko motsi zaiyi mata wuya.

Rudewa tayi tarasa yanda zatayi sbd hakanma yasake tabbarda akwai abinda tayi sai kawai hawaye suka ciko idanuwanta suka fara gangarowa ta durqusa qasa ta sunkuyar dakai cikin muryar kukan datake riqewa tace,

Yi hakuri ina neman afuwar laifina…….sai kawai kuka Mara sauri ya sake mata.

Sosai takeyin kukan yana tsaye yana kallonta kamar mai kallon wani show. 4

Matsota yafara yi tayi saurin rintse ido harya qaraso gabanta ya riqo hannunta na dama ya miqar da ita tareda kallon cikin idonta dahar lokacin ke tsiyayar hawaye yamaida kallonsa ga hannunta da dama dake cikin nasa yayi masa muguwar matsar da azaba tasata kallon cikin idonsa da sauri
Idonsa ras cikin nata yake kallonta batareda yasake mata hannunba.

Sabbin hawaye ne suka gangaro mata ahankali daqyar tasake furta,
kayi hakuri..

Sassauta riqon hannunta yayi tareda matsawa baya kadan yana kallon hawayenta dake tsiyaya

Da hannunsa daya ya shafosu yakalla ya matsota jikinsa sosai yakai bakinsa saitin kunnenta can qasan maqoshi yace,Kinyi kama da albinon malaminki da wannan hawayen. 14

Dagowa tayi takallesa ko qyaftawa batayi tana tsaida hawayenta kamar bashi yayi maganarba yaqara qasa da muryarsa yace,

Kallon fa?

Sauke idanuwanta tayi cikeda kunya tanason zamewa ta fice amma ba hanya sbd ya matseta jikin bango.

Cikeda mamaki da wani irin kallo dake nuna annurin fuskarsa yake kallon kunyarta data bayyana fili
Yasa hannu ya juyo da fuskarta tayi saurin rufe ido fuskarta dake fidda wani kyallin Hutu yaqurawa ido har zuwa qaramin bakinta dake qirjinta dake gugar nasa ya sake matseta yana zame band ‘din dake daureda dogon gashinta
Gashinta ya zubo har gefen fuskarta
Yasa hannu ahankali ya janye tareda yasake tura kansa cikin wuyanta murya a shaqe yace,

Bazaki zubamin abincin ba saiya huce and I don’t eat hutaccen abinci. 6

Saurin dagowa tayi takallesa saidai ko juyowa baiyiba ya qarasa kujera ya zauna

Akaro na farko da wani sahirtaccen murmushi ya kufce mata Wanda yasa kumatunta lotsawa akan idonsa ya dauke gira ‘daya tareda dauke kai.

Qarasowa tayi ta duqa ta bude masa tareda daukar ruwan data dauko ta mayar fridge din dakin ta canzo masu sanyi sbd wainnan sun huce.

Wayarsace ahannunsa yana duba wani saqo kamar bashine yasata aikinba.

Zuba masa ruwan tayi a glass cup ta aje masa ya miqa hannu yakarba ya kurba kadan ya dago yakalleta tayi saurin sauke kai.

Cikin nutsuwa yaci abincin kadan kafin yace,

I need a coffee.

Kwashe kayan tayi tafice dasu cikin sa’a ammy bata palo tashiga kicin ta aje ta hado masa coffee takoma.

Yana toilet kodata shiga yana waya ta ajiye tray din ta dauki cup din ta miqa masa yana karba ya hada da hannunta ya riqe yana cigaba da wayarsa kuma bai kalli fuskarta ba. 1

Kan jikinsa ya fixgota ta zauna tacigaba da wayarsa yana sipping coffee dinsa hankali kwance harya gama wayar ya aje coffee din tareda kallonta yace,

Me kike jira haryanxu? 2

Da sauri takallesa cikeda mamaki ganin har lokacin matse take ajikinsa ko hanyar tashi babu.

Sunkuyar dakai tayi cikin rawar murya kamar zatayi kuka tace,

Zantashi….. Sai hawaye.

Lumshe lazy eyes dinsa yayi yabude yana bin hawayenta da kallo a kasalance ya daga hannu ya shafo hawayen yana tattara gashin kanta daya barbaje.

Sakin kukan datake riqewa tayi batareda sanin dalilin yinsaba,

Zagaya hannuwansa bayanta yayi ya rungumeta tareda rufe idanuwansa.Lafewa tayi tana qoqarin goge hawayenta ya miqar da ita tareda zame mata doguwar rigar sama yabarta data ciki ya cirata sama ya suka nufi gadonsa yazura hannu ya kashe lamps din dakin tareda dora hannunsa akan siririyar rigarta ya zame.

Kallon agogo ammy tayi taga qarfe goma sha biyu harda rabi tasake fitowa amma Sam rumanah batanan ta aika gurin s salma batacan Sam hankalinta yaqi kwanciya sbd ganin kukanda rumanah din keyi dazu. 3

Hakanan ta hakura takwanta tareda mamakin maheer bama na rumanar ba.Qarfe hudu na asuba ya farka yabude idanuwansa daqyar sbd bacci da kasala,
Fuskarta dake kwance kan pillow daya datasa fuskar yakalla bayan ya kunna lamp yaga hawaye duk sun bushe mata a fuska sbd kukan da tasha adaren. +

Shafa fuskarta yayi kafin ya tashi zaune ahankali ya sauko gadon.
Toilet yaje ya kunna ruwan dumi a bathtub yadawo dakin,

Sanin koda ta tashi ba lallaine ta iya tafiya ba sosai yasa babu wani bata lokaci ya zura hannu cikin bargon ya dauketa ahankali ya nufi toilet. 3

Cikin ruwan yafara shiga tana hannunsa kafin ya kwanta tareda kallon fuskarta datake cusawa qirjinsa sbd tsananin kunya alamun ta tashi kenan tasan meke faruwa,

Tsananin kunya yasa takasa rabuwa da jikinsa saima sake shigewa datayi sbd babu abinda ke jikinta.

Shikuwa lumshe idanuwansa yayi ya rufe cikin wani irin kwanciyar hankali sbd ‘dumin ruwa dana jikinta dasuke ratsasa arayuwarsa bai ta6a samun body contact ba kamar wannan sbd ruwan dasuke ciki sun qarawa fatarta data hadu datasa laushi. 2

Gashinta da rabinsa yashige cikin ruwan ya kamo tareda dawo dashi kan kafadarta sbd duniya jiqaqqen gashi na burgesa sbd it’s so sexy and attracted. 19

Shower ya zura hannu ya kunna nan take gashinta yaqarsa jiqewa suna kwance cikin ruwa wata irin ajiyar zuciya ya sauke a 6oye kafin ya dago fuskarta yana kallon idanuwanta dasukai laushi yayi kissing dinsu ahankali yana shafa mata kumfa a wuya har zuwa qirjinta 1

Wani irin kasalallen numfashi taja tareda rufe ido tana qanqamesa sbd ba qaramin waiwayi hakan yamataba.

Yanayin yanda ta lumshe idanun kamar bazasu lumshe ba yasa yaji jikinsa na neman saki yasake kallon idanunta da nasa lazy eyes din itama shitake kallo amatuqar gajiye da baccin dabai ishetaba.

A lalace dai sukai wankan saidayaga lokacin sallah na wuce masa yayi wankan tsarki yafito itama daqyar ta iya wankan sbd kasala da bacci tana fitowa taga hand dryer dinsa dake maqale jikin socket a kunne 
6oyayyan murmushi tasaki sbd tagane me hakan ke nufi ta isa gaban mirror ta zauna tafara drying kanta tana gamawa tasaka kayanta tayi sallah tana idarwa anan ta kwanta sai bacci.

Koda yashigo dakin yaganta aqasa ya jima yana kallon gashinta dabata busar dashi sosaiba”””meyasa koyaushe takeda sa’ar yin abinda nafiso?? 3

Daukarta yayi ya kwantar a gadon bayan yazare mata doguwar rigarta yabarta da rigarta ta bacci.

Qarfe tara da rabi ta farka ta bude idanuwanta dasukai nauyi tasake lumshewa ta bude sai akan kyakkyawar fuskarsa dake daf da tata,Qura masa ido tayi tundaga kan idanuwansa har zuwa hancinsa 
Akan bakinsa ta tsayar da idanuwanta tana tuno laushinsu da qamshinsu…rufe idonta tayi cikeda kunyar tuno aikinda bakin yayi. +

Juyawa tayi zata sauka gadon can qasa taji yace,

Kingama kallon? 3

Zaro ido tayi cikeda mamaki kafin ta sauka gadon da sauri saidai tuni yadawo da ita ta fado masa ya riqe qugunta yana kallon fuskarta dake 6oye yanayin datake ciki.

Jin hannunsa cikin rigarta yasata kallonsa amma Sam kamarma bashine yasa mata hannunba.

Yanayin yanda yake wasa da cibiyartane zuwa qirjinta yasa numfashinta sauyawa tafara qoqarin zamewa amma tuni motsinta yasake basa damar jinta dakyau.

Zame rigar yayi ya juyar da ita takoma qasansa ya dora lips dinsa anata yana sake lalabeta tuni tafara kukan tuno wuyar datake sha. 2

Qarfe goma ta fito wanka daureda towel dinsa gashinta na tsiyayar ruwa farar fatarta sai wani irin sheqi takeyi,

Wani irin kallo yabita dashi yana latsa wayarsa da fararen idanuwansa.

A sukwane ta qaraso ta busarda gashinta ko ‘daurewa batayiba tasaka kayanta tajuyo a sukwane ta ‘dan saci kallonsa taga hankalinsa yana kan wayarsa.

Daidaita muryarta tayi cikin sanyi tace,

Ina kwana?

Dagowa yayi yakalleta yaga yanda tayi nar nar da ido ya ‘daga mata kai ahankali can qasan maqoshi yace,

Ina gaida ammy kafin nashigo.

Kallonsa tayi gabanta yayi mugun faduwa sai a lokacin ta tuno ammy tace taje tadawo tana jiranta. 1

Juyawa tayi ta fice jikinta na sakewa da wani irin nauyin ammy Dan batamasan mezatace mataba.

Gurin s salma tafara zuwa kamar mara gskia ta gaidata tana sunkuyar dakai 
Da mamaki ta amsa sbd sanin babu irin wannan gaisawar atsakininsu sbd sunyi sabo sosai suna sakewa da juna.

Miqewa tayi ta nufi qofar palonsu tanata kame kame hakadai tayi sallama ta shiga

Ammy dake zaune palon ta amsa tareda mata kallo ‘daya ta mayarda kanta kan abinda takeyi.

Ammy ina kwana'””ta furta muryarta na rawa.

Lafiya klau rumanah kintashi lfy?

Kai tadaga sbd babu bakin bada amsa 
Ammy tajuyo tadan kalleta taci gabada canxa channel.

Hanyar daki ta nufa tana tafiya a hankali ammy tabi bayanta da kallo tareda sakin murmushin tausayinta. 4

Kaya tacanxa zuwa doguwar riga mara nayi da hannu tafito taje dining ta hada tea kawai tasha takoma daki tana kwantawa sabon bacci yayi gaba da ita cikin nutsuwa.

Bai fito part dinsa ba sai lokacin sallar azahar daga masallaci ya nufo part dinsu yana shiga ammy na qoqarin zama kan dining suka zauna tare yana gaisheta cikin kulawa.Ita kunyarsama takeji yanda yayiwa yarinya son ransa amma ya fuske kamar bashiba +

Abinci suka faraci tana sake tambayarsa su amah saidai ya gyada kai kokuma gajeruwar amsa.

Fitowa tayi palon tana ganinsa taso juyawa ammy tace,

Rumanah bani sabuwar madara a fridge.

To tace ta nufi kicin tadauko tana kawowa ta zuba mata a glass cup ta miqa mata.

Daukar wani cup din tayi ta zuba shima ta miqa masa cikin ladabi.

Hadawa yayi da hannunta ya riqe tayi saurin kallonsa tana qoqarin zame hannunta ta saci kallon ammy 
Sultana tayi saurin ‘dauke kai tana kai cup bakinta. 3

Daure fuska yayi saidata fara tsiyayo hawayen kunyar ammy data tabbarda tagansu kafin yasaketa kamar baisanma meya riqeba. 2

Da gudu gudu ta isa daki sai kawai ta cusa kai cikin qafafunta tana share hawayenta.

Saidata tabbatarda yabar palon tafito ta tsakuri abinci sbd ko wata yunwar kirki bataji takoma daki ta zauna sbd 6oyo takeyiwa sultana sbd kunyar data hanata sukuni.

Da daddare saurin yin baccin tayi sbd karma tasamu dalilin zuwa dakinsa,
Washe garima da wuri tayi bacci
Amma baccinta rabi rabi tayisa qarfe tara ammy tace takai masa breakfast kansa na ciwo babu wani wasi wasi ta hada ta nufi part dinsa tana shiga tagansa dunqule cikin bargo ga AC daya qure duk sanyi yakama dakin haryayi yawa. 1

Aje tray din tayi tana kallonsa cikin tsananin sanyin jiki da damuwar ganinsa cikin wannan halin.

Qarasawa tayi bakin gadon ta leqa fuskarsa taga idanuwansa a lumshe alamar bacci yakeyi ta ‘daga hannunta ahankali ta dafa goshinsa taji babu zafi tasake leqa fuskarsa sai kawai sukayi ido biyu ta zaro ido tareda juyawa da sauri 
Taji yariqo hannunta cikin kasala ya tashi zaune yana zuba mata idanuwansa dasukai sauya sbd ciwon kan dake damunsa.

Sauka gadon yayi ya nufi toilet 
Tana ganin yashige takalli gadon daya tashi tafara janye bedsheet ‘din dake kai dan canxa masa wani duk da baiyi komaiba kamar ma yanxu aka shimfidasa
Cikin wardrobe taduba ta dauko wani ta shimfida tagyara gadon tafara gyaran dakin cikin qanqanin lokaci tagyara dakin ta rage AC ta duba taga turaren daki ta fesa nan take dakin yaqara daukar ni’imantaccen qamshi da sanyi mai dadi.

Ruwa ta dauko masa a fridge taba juyowa tajisa a bayanta takada juyowa saidai ajiyar zuciya datasaki sbd sanyin ruwan jikinsa dake tabata.

Juyowa tayi ahankali tareda kallonsa shima ita yake kallo ido ciki ciki.

Ruwan hannunta ya zare yasaka mata towel aciki batareda ya dauke idanuwansa ta cikin nataba 
Dauke idonta tayi ahankali ta dago hannunta takalli towel din dayasa mata a hannu ta dago takalleta ya dauke gira daya tareda nufar gaban mirror yazauna. 11

Matsawa tayi ta dora hannunta dake kyarma jikinsa tafara goge masa jiki harta gama babu wata magana atsakaninsu.

Tana gamawa ta sulale ta fita takoma dakin ammy tadan sake gyara mata duk da masu aiki sunyi gyaran.

Tana tsaye gaban wardrobe tana gyarawa ammy kaya yashigo dakin yana fidda wani sanyayan qamshin turarensa 
White gucci shirt da Blue jeans ne ajikinsa gashin kansa asake yana qyalli.

Kusada ammy ya zauna tareda riqo hannunta yayi kissing yana cewa,

Good morning ammy.

Kallonsa tayi tace,

Wuni dai sbd mu munjima da tashi.

Murmushin gefen baki yasaki kawai yace,

Yau zanyi tafiya zanje Mali mum din suhailat batada lafiya.Kallon rumanah da duk takasa sakewa sbd shigowarsa tace, +

Kuje tareda rumanah tadubota a maimakona.

Yi yayi kamar baijiba ya miqe yace,

Nanda 30min zan wuce kuma yau zan dawo.

Allah yakaiku lfy.

Ficewa yayi ta kalli rumanah tace,

Aje jeki ki shirya kinji yace nanda 30min.

Tariga tagama sai kawai ta fice tana zuwa ta canxa kaya sbd bata dade da wankaba.
Doguwar riga royal blue mai shegiyar tsada stones dinta sai wani qyalli sukeyi tayi rolling gyalen rigar sai wasu black wedges dake qafarta na lady dior dasukaiwa farar qafarta kyau sai handbag dinta da turarene kawai da powder aciki ta fito palo daidai lokacinda akace ta fito.

Cikin jin nauyi tayiwa ammy sallama ta fita.

A wata black mota tagani sai kyalli takeyi suka nufa aka bude mata baya tashiga yana zaune yana waya hankali kwance babu damuwar komai a fuskarsa.

Jan motar driver yayi suka nufi airport.

Abinda yafi bata mamaki shine ganin suna zuwa basu aka basu tickets dinsu 
Kenan the tickets are booked already.

Jerawa sukayi har cikin jirgi suka nufi gefen first class suka zauna yayi crossing legs yadauki jarida yafara karatu hankali kwance

Qarfe uku suka isa 
Miqewa tayi tana dan canxa fuska sbd qafafunta dasukai wani iri Sam yanxu bata iya dadewa zaune sai qafafunta su ‘dan kumbura.

‘Daga qafafunta tayi taji jiri ya ‘debeta 
Jikinsa tajita  ya riqo kafadarta yayi mata wani kallon ciki ciki. 1

Sunkuyar dakai tayi cikin laushin murya tace,

Yi hkr.

Riqo hannunta yayi cikin nasa dayan hannun kuwa cikin aljihun wandonsa fuskarsa sanyeda shades suka fito jirgin sbd ganin alamar kamar har lokacin jirin bai gama sakintaba.

Daga gidansu suhailat mota tazo daukarsu suna isa gidan nan aka fara hidima da farin cikin ganinsu.

Sosai iyayen suhailat suka tarbi rumanah babu wani damuwar komai.

Daqyar tasake sukaci abinci gaba daya a dining nan takejin su suhailat exam dinsu amah suke jira agama suzo dubiya suma.

Dakin mum din suhailat tayita janta ajiki danta sake jikinta saidai takasa sakewa sosai gashi yafita shida dadyn suhailat har magrib shiru baidawoba.

Ganin har anyi sallar ishai bai dawoba yasa tacire ran komawarsu ranar.

Qarfe tara da rabi yadawo ko shigowa baiyiba dad yabugowa mum din waya yace rumanah tafito sutafi.

Da mamaki tace,

Badai komawaba a Daren nan?

Aa masaukinsa zasu tafi dan gobe flight din qarfe takwas zasubi zuwa labanon akan wani  program damukai magana dashi yanxu.OK tace ahankali jikinta na sanyi sbd hakanan tausayin ‘yarta ya shigeta saidai tunda bai wulaqanta musu ‘yaba bazasuji zafi akan aurensa da matarsaba.

Cikin murmushi ta tashi ahankali ta nufi wardrobe ta dauko wasu dogayen rigunan Mali masu tsananin kyau guda biyu ta miqa mata daqyar ta karba tana godia suka fito

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]