[Advertisements⬇️]

GAMAYYAH CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GAMAYYAH


CHAPTER 5


Akan nuratu jakadiya ta tsayarda idanuwanta tana nazarinta sbd zama da rumanah yasa itama takeda nutsuwa daidai gwargwado……

Tsaya to idan zama da rumanah yasa takeda nutsuwa ba kamar mahaifiyarba me zai hana su dauki Mai nutsuwar gabaki daya.

RUMANAH”””shine sunan dayazo ranta atake tasaki murmushi cikin farin ciki sbd tasan sultana idan taji ta inda jikokinta zasu fito bazataji damuwaba

Sallamarsu tayi tareda juyawa kar tsaye ta nufi hanyar zuwa gurin sultan.

Tana zuwa akai mata iso cikeda girmamawa ta zube gabansa cikin bayyanarda farin cikinta tace,

Allah yataimakeka ansamu baiwa mafi nutsuwa da kyawu acikin bayin masarautar mineelik,
Baiwa ummu-rumanah ‘yar tsohon aminyaccen bawanka bulama.

Shima wani irin murmushi yasaki tareda kallon Jakadiya yace,

Allah yayi saina hada zuria da bawa mafi soyuwa agareni
Aje ashiryata yau za’a fara rakata turakar yarima
Bulama Allah yaji qanka da rahamarsa,

Jakadiya kije idan ta haifi namiji ina miki albishir da akwatin dalolin amurka. 10

Miqewa tayi tana zuba godia da farin ciki tareda adduar asamu biyan buqata.

Lokacinda ta isa gurin sultana ta zube gabanta ta zauna cikin farin ciki tace,

Allah yataimakeki Ansamu wadda nasan zakifi kowa farin cikin fitowar jikokinki ta tsatsonta.

Kallon rashin fahimta sultana tayi mata cikin qoqarin Kore damuwarta sbd jin ansamu mafita.

Baiwa ummu-rumanah ta wajenki itace nakega tafi cancanta da’a za6a sbd ganin nutsuwa dakuma shakuwar dake tsakani.

Wani irin kallo sultana ta jefi Jakadiya dashi cikin mamaki da takaici.

Datasan rainon datakewa rumanah na idan tasamu sanin asalintane daga mamani ta ‘yantata danta koma gida cikin yan uwanta ne.

Dauke kai tayi cikin bada umarni tace,

Kije kinema masa wata banda rumanah.

Kallonta Jakadiya tayi da sauri cikin mamaki tace,

Allah yataimaki sultana naga tafi kowace baiwa cancanta tazamo uwar jikinki koba komai tunda ‘danki ne ba wani akace akaiwaba

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


Girgiza kai tayi tareda juyawa takalli qofar bedroom dinta da rumanah ta fito cikin nutsuwa daukeda zanin gadon data cire ta fice tana mamakin kallonda suka biyota dashi kamar ta canza.

Laundry din masarauta ta nufa takai kayan ta karbo wasu sabbin zannuwan gado masu laushi farare qal tana fitowa mamani ta shigo part din laundry din daukeda kayan wankin adama itama takawo

Saurin matsawa tayi tana cewa,

Mamani sannu da aiki.

Tsayawa mamanin tayi tareda kasa danne baqin cikinta da takaicinta akan rumanah din sbd ko yauma dai ba’a zabi nuratu ba sbd ko wanka batayiba.

Cikin takaici tace,

Rumanah tunda kika zuga nuratu Dan karmu samu farin ciki kema bazaki ta6a farin cikiba arayuwa,
Keda iyayenki kunzamarmin muguwar qaddara sun mutu sunbarmana masifa gashinan kin shiga tsakanina da yata kin shiga tsakaninmu da farin cikinmu….

Rintse idanuwanta dasukai jajir tayi Cikin dannewa tace,

Kiyi hkr mamani bawa baya wuce qaddararsa ko…….

Shaqota tayi cikin tsananin baqin ciki jitakeyi kamar ta cire takaicin iyayenta na shekara da shekaru akanta ta huta.

Hawayen wahala rumanah ke fitarwa sosai batareda tayi yunqurin kwatar kantaba.

Motsi yasa mamani sakinta ta kwashi kayanta ta wuce zuciyarta na tafarfasa

Kukan datake riqewa tana shiga bedroom din sultana tasakesa zuciyarta na quna,

Sosai take kuka tana shesheka sbd yanxune take ‘dandana maraici da quncin dake cikinsa,
Wannan karon harcikin ranta takejin qunci da radadin abinda mamani ke mata shiyasa takasa danne kukanta duk yanda taso.

Sheshekar kukane yadauki hankalin sultana da jakadiya cikin sanyin jiki suka dubi qofar cikeda tausayawa Jakadiya tace,

Sultana amincewa kibada rumanah shine zai sanyaya mata qunci da damuwar datake ciki na uwar riqonta sbd natabbarda shine zai nesantata daga uquba da tsangwamarta.Koba komai wannan itace iya mafi girman soyayyar dazakiyi mata ta amince mata ta zama mai kawarwa da ‘danki sha’awarsa.,
Har abada rumanah bazata ta6a wulaqantaba idan ta hada shimfida da yarima koda kuwa bata haihuba,
Ki qara dubawa sultana. +

Shiru tayi tareda rintse idanuwanta cikin rashin madafa da shawara sbd bata fatar rumanah tazama baiwarda za’a riqa kwana da ita tana haihuwa ana kar6e ‘yayan daga qarshe kuma asallameta tayi nesa da qasar bazata qara kusanto ‘yayantaba.

Wani 6angaren kuma batada wata mafita ko ba6in daya wuce rumanah din Dan itace taga tafi cancanta da jikokinta su fito daga gareta koba namiji bane itadai gwara ace rumanah ‘dince ta haifar matasu ba wata baiwarba
Saidai zuciyarta na ganin kamar bata yiwa asma’unta adalcin zaman amincin dasukayiba
Hakama zuciyarta na hango mata wani irin rikici da tashin hankali agaba akan hakan.

Miqewa tayi cikeda damuwa da fargabar rashin madafa,

Masarautarsu has been cursed tun shekara da shekarun dasuka shude,
Duk wani abin alkhairi baya ‘dorewa a masarautar,
Sarakunansu hankalinsu da tausayinsu tareda imaninsu yana gushewa daga lokacinda suka hau kujerar mulkin basa da hukunci saina yankewa duk Wanda yayi laifi kisa,

Hannuwa da qafafun sarakunansu na jiqene da jinin mutane,
Sarakunansu are posses,
Duk Wanda ya alaqantu da kujerar mulkin mineelik sai cursed din yashafesa sbd mugun abin daga kujerar yake.,

Jakadiya kinsan me zamantowa uwa ga magajin masarautar nan yake nufi,

Maheer yaqi karbar sunan magajin sarkine sbd kubutardani daga zamtowa cikin makusanta kujerar mulkin,
Yaqi karbar sunan ne sbd kubutarda kansa daga jiqa likkafaninsa da kabarinsa da jinin bayin Allah, 5

Kinfi kowa sanin tarihin masarautar nan da abinda ke bibiyarta shine zamu ‘dauko yarinyar da batada hakkin komai musakata da abinda zata Haifa?

Rumanah kwaqwalwarta bazata iya daukar masifun dazasu biyo bayan zamtowarta mahaifiyar magajin masarautar nanba,

Idan muka sakata cikin wannan masifar muka jiqa hannuwanta da jinin mutane bamuyi mata adalciba,

‘Dana yakubatardani da kansa daga wannan masifar shine zamu saka yarinya aciki bayan batasan me hakan ke nufiba.,

Sultan alamarin yariga ya dade shigarsa ayanxu koda ‘Dan cikinsa baya tunani biyu kafin ya yanke musu hukuncin kisa,
Masifar tariga tashiga jikinsa bayaji baya gani rashin bin kowane irin umarninsa daidai yakeda fitar ranka….

Cikeda sanyin jiki Jakadiya tace,

Hakan zaki tuna kiyi hkr kibada rumanah idan ta haihu mu tseratarda ita ta hanyar turata nesa inda har abada bazata sake kawo kanta nanba wannan shixai mata Katanga daga zamowa MINEELIK-ASSULTANAH TA BIYU.

Shiru sultana tayi cikeda tsananin tsoro da fargabar abinda suke shirin yi,.

Fitowar rumanah daga bedroom dinta yasasu juyawa qofar.

Sunkuyar dakanta tayi sbd fuskarta datayi jajir sbd kukandatayi.

Wani irin mugun sabon tausayinta yashiga sultana batasan lokacinda tajawota jikinta ta rumgumeba cikin wata irin sanyin murya tace,

Asma’u ki yafemin.
Rumanah kema karki qullaceni.

Batamaji abinda ammyn kefadaba sbd kukanta daya dawo sabo tuntuni take Neman Wanda zai rarrasheta koda tsuntsune sbd mawuyacin halinda take ciki. 1

Jakadiya ma cikin tsananin tausayin rumanah din can qasan maqoshi tace,

Ki gafarceni rumanah amma rayuwarki ta birkice daga lokacinda kika haifi ‘da namiji sbd qaunar danake yimiki ina miki fatar samun ‘ya mace sbd kubuta daga muguwar tsinuwar dakebin makusanta kujerar masarautar mineelik.

Saida rumanah tayi kuka sosai Wanda hakanan yake zuwa takasa tsaidasa saidatayisa sosai kafin sultana ta ‘dagota tareda kallon fuskarta tana maida hawayenta takalli jakadiya tareda ‘daga mata kai ahankali.

Tasaki rumanah tayi bedroom dinta tanaji ajikinta haqqin rumanah bazai taba barinsuba.

Jiki amatuqar sanyaye ta juya ta fice Jakadiya tabita da kallon tausayi

Tana zuwa dakinsu ta zauna bakin katifarta tareda rafka tagumi ta fada tunani.

Nuratu ce tashigo dakin tayi saurin isa gurin rumanah din kawai ta rungumeta Tana cewa,

Rumanah karki karaya kisake jajircewa kina haquri da mamani zata daina wata rana ko ance tayi bazatayiba. 1

Murmushi mai ciwo tasaki tareda kallon nuratu tace,

Mamani uwace banta6a riqeta arainaba.

Zuciyarki nada kyau rumanah Allah yabarki ahaka.

Murmushi tayi tace,

Ummana,abbanah da ammy bayansu kece mutum ‘daya dana sani mai zuciya mai kyau Dan haka keda ammy Allah kuma yabarku ahaka.

Dariya sukayi suna qoqarin manta damuwar abinda yafaru.

Ahankali nuratu takalleta tace,

Rumanah kintuna lokacinda muke wasar riqe riqen gudu da ruwa a cup a dakin nan?

Murmushi tayi tareda kallon nuratu sbd wannan wasar itace abinda bazata ta6a mantawaba a quriciyarta,
Itace abinda nuratu ke tuna mata tasakata nishadi amma yau saitaji jikinta yayi sanyi tace

Meyasa kika tuna wannan yanxu?

Haka kawai na tuna sbd bansaniba kobazamu sake samun damar tunawaba irin haka cikin jindadi.

Qurawa nuratu ido tayi zatayi magana aka shigo dakin.

Kallon qofa sukayi sukaga bayi kusan biyar atsaye saiga Jakadiya tashigo fuskarta a tamke babu alamar wasa takalli rumanah ta ‘dauke kai ta juya Tana cewa,

Ku taho da ita zuwa part din gyara yanxunan.

Tana fada ta fice sbd kar tausayin rumanah yashigeta.

Kallon juna sukayi itada nuratu irin kallon da nuratu ke mata na tsananin tausayi yasa tayi saurin kallon qofar da jakadiya ta fita tayi kafin tasake kallon nuratu da tuni hawayen rabuwarsu ya gangaro mata.

Matsowa sukayi suka kama hannunta ko qwaqwaran motsi bata iyayi suka fice da ita.JAN HANKALI
‘Yan uwa masu zantuka akan wannan littafi masu dadi da marasa dadi tareda cin fuska duk inason Ku luradafa akowane lokaci mai rubutu idan zai isarda wani saqo na halin rayuwa tofa dolene saiya fara kawo 6atancinsa da 6arnarsa kafin yazo ga darasin ciki tareda gyaransa Dan haka please muriqa bari muna ganin inda aka dosa kafin muriqa fadar ea’ayoyinmu. 5

Komai bakinta baida kuzarin furtawa koda yanadashi ‘din baida ikon furtawa sbd hakan na nufin ruwan sama zai wanke jininta bayan anraba jijiyoyin dasuka riqe kanta da wuyanta
Saidai bazata iya hana zuciyarta qunci da radadin zuciya ba sbd sai ayaune ta sake tabbatarda ita baiwace Mara ‘yanci gaba da baya.

Kai tsaye part din gyara taga sun nufa nan shakkunta da wasi wasinta ya tabbata kenan itace zata zama…..

Kasa qarasawa tayi ta rufe idanuwanta da qarfi hawaye na 6alle mata.
Daganan kasa daga kafafunta tayi haka suka jata kamar makauniya suka shiga da ita.

Zaunarda ita sukayi tareda fara zame mata kayan jikinta har lokacin bata iya ‘daga koda Dan yatsanta bare ta iya ‘dago fuskarta.

Shigowa Jakadiya tayi kallo daya tayi mata tagano tsananin dukan da firgici yayiwa zuciyarta tayi saurin dauke kai cikin bada umarni tace,

Ku shiryata shirinda har abada yarima zai riqa tuna qamshi da kyawunta kuma Ku kwantarda hankali kuyishi anatse.

‘Dagowa tayi ahankali takalli jakadiya daidai lokacin hawayenta suka samu tsinkewa.

Cikin zafi da daure fuska jakadiya tace,

Karkiyi mana kuka sbd ke baiwace da akeda ikon kwana dake aduk lokacinda akaso kuma akeda ikon yin yanda akeso dake Dan haka ki saurara da kyau
Idan kikayi mana garaje anan wlh abincin kaji za’ayi da jininki. 2

Kalaman Jakadiya sundaki zuciyarta matuqa ta rufe idano ahankali ta budesu jajir sbd quncin zuciya amma tabbas babu yanda zatayi ita baiwace kuma yar bayi kamar yanda Jakadiya ta fada
Hannu tasa tashare hawayenta bata qara motsiba suka fara aikinsu ganin ta zame rigarta tashiga cikin ruwan madara da lalle dake cikeda bathtub suna zuba qamshi.

Jakadiya Juyawa tayi tafice takoma part dinda aka warewa baiwarda duk aka zaba akusadana suhailat yake Saidai baiyi girman nataba.

Duk wani abin jin dadi da hutawa da more rayuwa ansaka sbd so ake jikinta yariqa murmurewa fatarta tasamu isashen Hutu da kulawa ta yanda yarima zaiji dadin mu’amala da ita.

A cikin bedroom dinda ke part din wardrobe din dakin cike take tab da wasu irin kayan barci marasa kyawun gani basa qirguwa,
Hakama braziers masu daukar hankali dakuma panties,

6angaren turaruka kuwa duk wani turare mai tsada da qamshi ansiya har gaban mirror bai daukesuba aka zuba wasu a wardrobe.

Suhailat Jakadiya ta tambaya duk wani Abu da yarima yafiso ta 6angaren tayar masa da sha’awa zuwaga auratayya bisaga umarnin sultan,
Cikeda damuwa ta zayyanowa Jakadiya shinefa aka nemi turaruka masu matuqar tsada da kayan barci.

Saidata tabbatarda gyaran komai yakammala takoma gurinda ake shirin rumanah din ta tarar sungama shiryata cikin wata irin doguwar riga maroon colour dataji wasu irin tsadaddun adon sequence stones sai rawa take tana qyalli

Mayarda kallonta tayi zuwaga fuskarta cikin tsananin mamaki da fargabar zallar kyawunda sultanace kawai take gani da kwatankwacinsa zuciyarta tayi mugun bugawa cikin zuciyarta tace,

Ya Allah kabar wannan fuskar mai tsananin kyawu da kwarjini ta dauwama ahaka karka wanke kyawun fuskarnan da jinin bayinka.Cikeda umarni tace, +

Ku rufeta mutafi daga yau rana bazata qara ta6a fatartaba harsai yarima yagama da ita idan ya gundura da ita,
Hakama daga yau idan tafara kwana barayar yarima duk bawa namiji yabari tsautsayi yasashi kallonta anyiwa zakunan fita yaqi alqawarin namansa.

Sam bata jinsu sbd damuwa da qunci dayayiwa zuciyarta yawa
Haka aka rufeta aka kamo hannunta suka jata.

Part din da’aka ware mata aka kaita har cikin bedroom Jakadiya ta kaita ta janye lullubinta tareda kallonta fuskar tamke da kakkausar murya tace,

Daga yanxu kinshigo kenan bazaki sake fitaba sai ranarda kika haihu,
Daga yanxu dokace mai tsanani babu Wanda yakeda ikon ganinki sai yarima kawai,
Akwai komai na buqata kullum dare zanxo narakaki barayar yarima harsai ranarda kika samu ciki saiki fara shiri daga yanxu
Zanje bayan sallar ishai zandawo nakaiki yarima baya jira Saidai ajirasa.

Ficewa tayi tabi bayanta da kallo idanuwanta na qoqarin cikowa,
Kukan datake dannewane tuntuni ya kufce mata ta zame qasa tafara wani irin kuka tana shidewa,

Kuka takeyi sosai tana qanqame jikinta cikeda tsoro,fargaba da baqin cikin rayuwardata tsinci kanta dakuma wadda zata fara daga yau bayan anfara kwanciya da ita duk lokacinda akeso.

Sbd kuka muryarta shaqewa tayi tashare hawayenta tareda miqewa ta nufi toilet din bedroom din tayo alwala daqyar take gani sbd kumburin idanuwanta da fuskart.

4 hours later.
Kasa kallon kanta tayi ta rintse ido jiki amatuqar sanyaye sbd kayanda ke jikinta,

Riqar baccice kalar black Wanda babu wani sashe na jikinta da rigar ta suturta,

Bra da pant dinda aka sata sakawa duka suma black ne aka daure dogon gashinta dashima aka gyara hatta turaren hayaqi mai wani irin qamshi anyiwa gashinta bare jikinta aka daure tsakiyar kai tareda ‘dora mata wata doguwar tiga mai hula data rufe koina ajikinta aka rufe fuskarta da hular tareda bata wasu takalmi masu laushi ta zufa anatse Jakadiya tace,

Mutafi,Allah yadatar dake da samun ciki acikin daren yau.

Jakadiya ce agaba sai ita abaya bayi kusan guda biyar sun zagayeta suna kama rigarta dake Jan qasa.

Duk takunta ‘daya kamar zuciyarta zata fadone ta buga sbd bugawa da tsananin tsoro da baqin cikin datake ciki,
Akaro na farko arayuwarta zata kwana da namiji ba mijintaba kuma duniya da kowa zasusan ana kwana da ita harta haihu,

Tabbas da ubangiji bai halastawa uwayen gijiyoyi bayinsuba da ayau tafison a raba kanta da wuyanta abawa dabbobi jininta data cika wannan umarnin amma sa6a musu da bijire musu tamkar ta bijirewa ma’aikintane sbd shine ya halasta hakan.

Wani irin tsaro ne na musamman a part din yarima ga wasu irin hasken fitilu masu kyau da burgewa haka duk fadin masarautar idan kacire uban gayya sultan part dinsane ne kawai mai palo hudu kafin akai master bedroom dinsa.

Cak suka tsaya bakin qofar shiga Jakadiya tajuyo ahankali tayiwa bayinda ke bayansu kallo daya
Suka ja baya suka tsaya tareda sunkuyar dakai kafin tajuyo takalli guards din bakin qofar cikin girmamawa suka wangale qofar ta saka qafa tashiga.

Wani irin numfashi rumanah tasake sbd kukama yanxu yagaji yagudu yabarta zuciyarta da idanuwanta sun bushe sauke numfashi kawai take yi akai akai sai jikinta dayake wata irin rawa ko Abu bazai iya tsayawa ahannuntaba.

Numfashi tasauke ahankali tareda ‘daga qafarta tashiga ahankali tareda rufe ido tabude sbd rayuwarta ta canxane daga yanxu data sako qafar palon yarima maheer ibn abdulshams abdallah.

Har lokacin fuskarta rufe takeda hular rigar dake jikinta ahankali take takawa faduwar gabanta da rawar jikinta na tsananta harsuka isa palon qarshe Wanda dagashi sai bedroom dinsa.

Abakin qofa Jakadiya ta tsaya tareda juyowa tayi mata kallon mintuna uku kafin tazagaya bayanta ahankali tasaka hannu ta zame doguwar rigar mai hula
Tasaka hannu ta zare ribbon dinda aka ‘daure gashinta
Gashin ya zubo kan kafadunta ta juya mata baya cikin sanyin murya tace,

Kishiga ki kwanta a gadon dake dakin kijira isowarsa.

Shiru tayi tareda Jan numfashi ahankali tasauke sbd barazanar barin qirjin qirjinta dayakeyi., +

Daqyar ta iya daga qafafunta dake rawa

Rawa hannunta keyi sosai takasa bude qofar bedroom din

Ganin haka Jakadiya ta matso tareda dafata cikin kulawa tace,

Karkiyi gardama da qaddara ki nutsu kibi umarni kiyi biyayya Allah ne kawai yasan dalilin komai dake faruwa.

Bude mata qofar tayi tareda juyawa sbd batada dama da iko tareda hurumin ganin makwancin yarima.

Akaro na farko da wani yayi mata magana da sigar lallashi tun bayan data zamto za6abbiya.

Ajiyar zuciya tasauke tareda saka qafarta cikin dakin Jakadiya ta jawo qofar ta rufe ahankali kafin ta juya ta fice da doguwar rigar ahannunta.

Komai na ‘dakin white and golden ne,
Sanyin AC da qamshin dakin da mai dakin tareda nata data shigo dashi suka taru suka sauyawa dakin yanayin qamshi mai dadi kasancewar turarukan arabian oud akayi mata amfani dasu sabanin nasa dasuke designers na turawa.

Daqyar qafafunta suka kaita bakin couch dake bedroom din ta sulale qasa ta jingina kanta jikin kejerar tareda rufe idanuwanta.

Qarfe goma da rabi yafito part din sultana ya nufi part dinsa guards biyu ba bayansa yana isa masu tsaron qofar sukai saurin budewa yashige.Gyara tsayuwa suhailat tayi daga bakin tafkeken windon bedroom dinta iska na daga curtains suna ta6o har fuskarta sbd sosai take buqatar iskar sanyin AC bazai mata ba she’s feeling suffocated already.

Gyara tsayuwarta tayi akaro na ba adadi tana tsananin buqatar Wanda zai bata kulawa ayanxu sbd wani irin kishin mijinta dakecin duk wani jini dake yawo acikin jijiyoyin jikinta,

Tana tsananin so da qaunar maheer,
Maheer na respecting relationship dinsu sbd ‘yaya dakuma zaman fahimta dasukeyi Saidai maheer na buqatar macen dazaiji dadin yin rayuwarda yakesonyi da ita Wanda bata fatar yasamu hakan daga wata macen bayan ita,

Yanda labari yazo mata baiwa rumanah ce aka za6a
Tsoronta na qaruwa aduk lokacinda ta tuno kamanni da tsarin rumanah din Saidai kuma bata tunanin tafi bata tausayi sbd sanin waye maheer bazai ta6a iya kwana da wata mace ba musamman wadda ba matarsaba.

Girgiza kai tayi tana mayarda dogon gashinta daya barbaje baya ta zauna bakin lafiyyan gadonta tana cewa,

Ya Allah ka yayamin wannan azabar danakeji cikin raina
Hawayen datake dannewa tun lokacinda zancen yazo mata suka 6alle ahankali tafara fitarda sautin kuka tana rufe fuskarta.

Kallo daya yayiwa gefenda take ya nufi bedroom yashiga ya tube yashiga cikin bathtub yakwanta tareda rufe ido yana qoqarin samun nutsuwa azuciyarsa har tsawon lokaci kafin yayi wanka yafito ‘daureda towel milk colour yanufi closet yadauki kaya yashirya cikin kayan bacci ya fesa turare mai sanyin qamshi ya nufi gadonsa ya kwanta hankali kwance cikin nutsuwa tareda shigewa lallausan duvet ya zira hannu yakashe wuta ya lumshe ido sbd shi baimasan ta yaya zai saka zancen sultan aransaba bare harya cika kwata kwata shi ba mutumne mai yawan maganaba idanuwansa da kallonsa suke bada magana ko umarnin abinda za’ayi kuma shima mutumne dazai iya 6ata lokacinsa gun abinda baima shafesaba kokuma abinda baidauka da mahimmanciba shiyasa ko kallo baiwar bata ishesaba idan sungaji da kawota zasu daina Dan Kansu ko yanxu yabartane aringa kawota sbd abinda sultan yafada akan ammynsa if not baisan yama za’ai yaringa kwana daki daya da wata macenba bayan ko matarsa basa kwana daki daya

Tunda yashigo ta lafe jikin kujerar tareda tsayarda duk wani motsinta ta sunkuyar dakai numfashinta na tsananta fita
Tana rabe kanta sunkuye yayi duk abinda yakeyi ya kwanta tana ji tana jiran taji ya tunkarota amma ko kallon inda take baiyiba harya kwanta.

Ajiyar zuciya tasauke ahankali hawaye masu sanyi suka gangaro fararen idanuwanta bada damu data sharesuba sbd duhune adakin ta kwantarda kanta kan gwiwoyinta hawayenta nacigaba da gangarowa.

Asubar farko Jakadiya tazo ta tsaya palon qarshe riqeda doguwar rigar dazata rufe kayan barcin dake jikinta.

Miqewa tsaye tayi jikinta ba qwari sbd kuka da rashin bacci ta nufi qofa.

Alarm din gefen gadonsa dake tadashi sallah sbd ba’a shigowa ko palonsa na biyu bare atadashi sallah yasa yakeda alarm na tadashi sallar asuba kawai.Ringing alarm din yasa ya cira hannunsa daqyar cikin bacci ya danna hasken wutar dakin
Tayi saurin juyowa afirgice sbd takai tsakiyar dakin takusa isa qofa daidai shikuma ya bude oily eyes dake cikeda bacci suka sauka akanta,

Dishi dishi yake ganinta ya lumshe idanun yabudesu itakuma hartayi saurin ficewa.

Tana ganin Jakadiya tsaye wani irin tsoro da mamakinta suka kamata amma saita sunkuyar dakai jakadiya ta miqa mata rigar ta sanya tareda janyo hular rigar ta rufe fuskarta suka fice.

Kallo daya Jakadiya tayi mata tasan babu abinda yafaru tsakaninsu tasaki numfashi tana cigaba da tafiya.

Suna fitowa qofar part din bayinda aka bari da Daren still sunan suka Mara musu baya suka kaita sabon gurinta suka wuce batareda Jakadiya tace da ita qalaba.

Zamewa tayi qasa bakin gado ta ta qurawa window ido ta fada dogon tunani fuskarta cikeda damuwarda tayiwa rayuwarta dabaibayi.

Tadauki lokaci kafin tamiqe tashiga makeken bathroom din dake dakin tayo alwala ta zame kayan jikinta tareda mayar musu da kayansu cikin wardrobe tasaka doguwar Riga tayi sallah.

Koda gari ya waye ankawo mata abinci bata iyacin komaiba hakama da rana ankawo amma takasa koda kallon abincin.

Arayuwa yanxu batada wani sauran buri ko mafarki sbd yanxu ta yarda mafarki baya zama gaskia,
Ita ayanxu tamkar wata dabbace da duk yanda akaso ayi da ita haka za’ayi ta yarda da qaddara tabarwa Allah alamuranta.

Sultana bawani doguwar nutsuwa bace acikin zuciyarta sbd har lokacin zuciyarta da gangar jikinta sunkasa nutsuwa da alamarin tsoro take ciki sosai sbd tana tsoron abinda zai iya juyewa gaba.

Koda gari ya waye Jakadiya tasanarda ita babu abinda yafaru tsakaninsu hakanan tasamu kanta da ajiyar zuciyarta tayi shuru tsawon lokaci kafin takalli jakadiya cikin wata irin murya tace,

Jakadiya zansa acirewa rumanah mahaifa sbd fargabata tana yawa Wanda hakan nabani cewar zata iya haihuwar namiji Wanda nibana mata fatar zamowa MINEELIK-ASSULTANAH kuma kinfi kowa sanin me hakan ke nufi,
Tayi yarinya da riqe wannan matsayin sbd bala’i da masifar dake ciki yafi qarfin shekarunta Dan haka abin zaifi ta6ata.

Shiru Jakadiya tayi kafin tagyara zama cikin son gyara zancen tace,

Allah yataimaki sultana cire mata mahaifa tamkar mun qarasa nakasta rayuwartane,
Ke tamkar uwa kike agareta muyi mata fatar samun ‘ya mace ta yanda idan tasamu yantawa akorata nesa da nan taje tayi aure tafara gina wata sabuwar rayuwar.

Ajiyar zuciya sultana tasaki tareda lumshe ido tana fatar Allah karya bawa rumanah cikinma kwata kwata ana dakatarda ita daga zuwa gurinsa ta ‘yantata ta turata nesa da nan.

Mamani duk wani baqin ciki da quncin duniya yataru axuciyarta tun lokacinda aka tafi da rumanah ko ruwa ta kasa sawa cikinta jitakeyi kamar zuciyar naci da wutane saidai tana addua da fatar Allah yasa ko cikin ‘ya mace karta samu bare na namiji. 1

Sarauniya adama kuwa komawa tayi tamkar zata mutu sbd baqin ciki acikin dakinta laifi qalilan zakayi tasa arabaka da lafiyarka sbd ta daura damarar yaqi da duk Wanda zaishiga tsakaninta da abinda take buri tun tana qanqanuwarta. 1

Kamar jiya qarfe goma aka zo tafiya da ita bayan anshiryata cikin rigar da gwara ta jiya da ita suka tafi.

Yauma a qofar shiga bedroom dinsa ta zame rigar sama da ribbon gashinta ya zubo dakanta yau ta bude tashiga batada kuzari ko kadan ta nufi inda ta ra6e jiya tazauna tareda kwantarda kanta kan gwiwoyinta ta rufe idanuwanta ahankali.

Kwance yake duk yau ko ina bai fitaba iyakacinsa palonsa na biyu inda nan yake cin abinci sbd nan ne dining room dinsa,

Ko suhailat ma so ‘daya takirasa awaya tana qoqarin boye damuwarta da kishinsa tagaidasa tabasa su amah sukayi masa ‘Dan surutunsu Wanda duk sukeyin abinsu iyakacinsa sauraransu suka gama.Ammynsa ma yau awaya yagaidata koina bai fitaba yayi kwanciyarsa.

Tun lokacinda tashigo yaganta ya rufe idanuwansa ahankali tareda gyara kwanciya sai alokacin ta fahimci yana ‘daki sbd duhu bata luraba amma ko motsawa batayiba tayi Shiru ko tunanin bata iyayi yanxu
Ahaka asuba tayi ta miqe jikinta amatuqar sake ta fice.

Ahankali kwanakin suka ja kusan sati biyu ana kaita amma baitaba ko kallon inda takeba. 1

Abu ‘dayane daya fara canzawa shine qamshinta daya kama koina acikin dakinsa har toilet dinsa Wanda hakan ne kesakashi 6acin rai wani lokacin

Itakuma ayanxu tarigada tasan bazai ta6a yin komai da itaba shiyasa kowane irin kaya aka bata bata damuwa sawa takeyi.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]