[Advertisements⬇️]

DAWUUD CHAPTER 6 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

DAWUUD 


CHAPTER 6Tana dawowa daga airport ta kwanta Nan danan zazza6i Mai qarfi ya sake kwantada ita kuka takeso tayi kota samu sauqin abunda takeso a qirji da zuciyarta Amma yaqi zuwa saima wani irin yaji da idanuwanta ke Mata na Jan dasukai. +

Hankalin ammy tashi yayi sosai nan tafara rarrashinta tana Bata Baki sbd kobata fadaba tasan ciwon na rafiyar dawood ne.

Ita gabaki ‘daya ma alamarin tsoro yafara Bata wannan wace irin soyayya ce tun ba’aje koinaba tafada cikin ranta cikeda tausayin laylar.

Cikin kwana biyu ta canxa sosai duk da tana qoqarin ganin ta sake sbd kullum sai sun raba dare suna waya hardar yanxu dabasa kusa narke Mata yake kamar zaiyi kuka itama wani lokacin da hawaye suke rabuwa ta wayar gashi tunda yaje suka daina video call sbd yace akwai wadda bayaso taganta Koda mistake ne datace waye Bai Mata qarya ba yace Mata ex-girlfriend dinsa sbd hakan na ‘daya daga cikin qualities dinsa shi baya qarya baya 6oyo.

Ranar daya fada Mata Saida yabawasu maska tausayi sbd shiru tayi taqi magana jiki na rawa yakashe ya danna Mata video call 
Hawaye yagani fuskarta suna tsiyaya Nan yahau kawo zance kala kala cikin tashin hankalin ganin hawayenta saidataga kamar zai sawa kansa ciwon Kai gurin qoqarin lallashin ta goge fuska tareda sakin siririn murmushi tace,

Ok Ya isa haka you need to rest ji hancinka yanda yayi ja alamar you’re having a headache..I’m ok.

Lalla6asa tayi suka gama wayar tana ajewa ya lumshe lazy eyes dinsa zuciyarsa na tunano Masa saraah sbd itace baya fatar Koda wasa tasan maganar Nur bare taganta sbd yasan hw stupid and crazy she is zata iyayin komai and that he can’t dare to take.

****
Duk wata shaquwa da aminci tashiga tsakanin taheer da aleeya sbd arayuwarsa baida friends ko ‘daya Bai ma ta6a yinsu ba yayansa shine abokinsa idan Yana gari sbd akwai soyayya da shaquwa sosai atsakaninsu sai yanzu daya samu aleeya yakejinta sosai cikin ransa amatsayin aminiya daya yarda da ita.

Mum kuwa duk da’din duniya ya isheta data gano irin soyayya Mai qarfi da aleeya kewa mi’amor ‘dinta sbd duk duniya ba abinda take tsananin so da qauna kamar ka nuna kanason mi’amor dinta.

Uwa uba data Kira CJ ta bugi cikinsa taji abban aleeyar ba laifi he’s very rich and famous Dan haka tasan mi’amor dinta his in-laws will be Rich and famous kamarsu just the way datakeson abubuwan sukasance Dan babban burinta shine yanda suka mallaki billions of dollars suke billionaires duk wainda zasu zama in-laws dinsuma su zamo.

Tuni ta qara sakewa aleeya tana qara nuna Mata qauna da kulawa na musamman tareda qara koya Mata abubuwan fashion sbd tanason matar ‘dan nata tazamo like no other.

Aikuwa tuni aleeya taqara tsundumawa cikin soyayyatar mi’amor ‘din mum din Dan tuni mum ta nuna goyan baya dari bisa dari Dan harma so take tafi aleeyar zaqewa Dan tuni tafara yiwa dawood ‘din maganar aure Dan taji ra’ayinsa aikuwa ga mamakinta Kai tsaye yace Mata ya shirya kowane lokaci zai iyayin aure sbd bayason adauki time yanama son zuwa dama yafada musu aure yakeson yi.

Wani irin dadine yaqara kama mum din cikin zumudi tace,

Ok my love saikazo sbd nima banason ka qara wani lokaci ba auren.

Kai tsaye tafadawa taheer da aleeya yanda tayi dashi cewar ya shirya yin aure.

Da daddare takira cj tafada Masa abinda ke faruwa nason juna da dawood da aleeya keyi sosai yayi mamaki sbd yasan Sam dawood baida niyar aure ayanzu sai zuwa gaba qila Amma Kuma daya Kira dawood ya tambayesa shiyace zaiyi aure yanxu Kai tsaye yace Masa eh qilama Nanda 3 months.
Aje waya dad din yayi cikeda mamaki Amma Kuma tuna yaji daga bakin dawood din ai shinkenan abin farin cikinsune.

Ba 6ata lokaci washe gari dasuka gama saka hannu akan partnership nasu dad yayiwa Abba bayanin abinda ke faruwa sosai abban yaji Dadi ranar dasuka dawo Miami da kansa ya tambayi aleeya ba kunya tace eh tanason dawood din.

Ranar murna da farin ciki gurin mum harda wata special dinner sukai having dukkaninsu Abba ma farin cikinsa baya 6oyuwa wannan tafiyar tasu tayi Masa Dadi sosai sbd komai anyisa cikin nasara ga zumunci zai qullu. +

Ranar kosu ammy da Layla da aka bugo aka sanar dasu angama komai dasun dawo za’a bawa itama saurayin Layla dama ya Aiko baza’a Bata lokaciba za’ai bikinsu sbd mum dake ganin idan aka tsaya jan time za’a iya samun matsala.

Farin ciki ranar gurin Layla da ammy kamar me ranar kusan raba dare sukayi suna waya da aleeya da zumudi da farin ciki yasa takasa sukuni gashi tun adaren mum tabawa wani babban fashion empire aikin dinko musu wasu irin dogayen rigunan dazasu saka agurin bikinsu har agama.

Tun tana waya da aleeya kiransa ke shigowa wayarta tana gani tasaki murmushi tun tana fahimtar Mai aleeya ke fada harta daina dukkanin hankalinta yakoma kansa Kuma takasa cewa aleeyar Yana kiranta tana kallo yaita Kira ba qaqqautawa aleeyar da kanta ta gano hankalin laylar baya tareda ita ta kashe wayar tana murmushin farin ciki jitake ta matso tahadu da dawood din Kota samu sassaucin sonsa dake neman rabata da nutsuwarta.

Aleeya na kashewa kiransa na sake shigowa tana ‘dauka taji lokacinda ya sauke wani irin kasalallen numfashi tareda cewa,

NUR ahankali kamar Mara lafiya.

Ajiyar zuciya itama ta sauke batareda ta amsaba sukayi shiru dukkansu.

Miskilancinsa ne ya motsa yau Dan haka haka sukai shiru Kati na tafiya abanza tsawon lokaci kafin taji Yana sauke numfashi ahankali alamar yayi bacci.

Murmushi tasaki tareda kashe wayar ta aje sbd ta saba da hakan idan Jan ajinsa ya motsa sai kawai yakira Yana sauraron numfashinta haryayi bacci.

Kwantawa itama tayi tareda lumshe Ido tana sake girmama abubuwan datakeji gameda dawood din.

Washe gari da sabon farin ciki suka tashi sbd ranar su aleeya zasu sauka da kanta tayiwa aleeya wani qaramin chocolate cake da samosas yan kadan.

Ita kadai taje daukarsu suna ganin juna suka rungume cikin farin ciki ba tsalle tsalle ba ihu ahankali tace,

I missed you so very much my love.

Cikin farin ciki aleeya tace,

I missed you more sweetheart.

Sakin aleeya tayi tareda kallon Abba tana murmushi tace,

Abba welcome.

Thank you layla,,hp mun sameku lafiya?

Lafiya qlau abba munyi kewarku sosai.

Hmmm kewa ai sai Bilal sbd kullum saiyi kaman zaiyi min kuka awaya wai munqi dawowa.

Murmushi tayi suka nufi mota bayan ansake booking flights din dazai wuce dasu Abba da ammy yau da yamma.

Rungume ammy aleeya tayi tana cewa,

Ammyna nayi kewarki.

Muma munyi kewar hayaniyarki.

Dariya sukayi dukkansu Nan suka shige bedroom dinsu sukabar ammy da Abba a palon.

Tubewa aleeya tayi tayo wani wanka tasaka jeans da white vest tayi sallah suka fito Palo Nan sukaci abinci gabaki ‘dayansu har zuwa qarfe biyar suka Kai su ammy airport suka wuce sukuma suka dawo.

Da daddare kusan kwana sukayi fira kafin suka kwanta sbd gobe Dole zasu Fara zuwa school danma anfara lectures tun last week.

Tunda sassafe kafin layla ta tashi sbd zumudin son ganin dawood din Layla aleeya ta tashi ta ‘dauki keys na flat ‘din dawood din da layla tace yabar Mata sbd bazai dadeba zai dawo.

Tana shiga babban palon tayi arba da makeken hoton maska daya qara qawata palon yayi kyau harya gaji sbd he is looking so hot a hoton Dan a beach yayi hoton da kayan Shan iska ajikinsa dasuka qara fitarda kyawu da hutun fatarsa.

Wow,,,he is damn hot and cute”””tafada tana dariyar taya laylarta farin ciki.

Saidata qare Masa kallo ta juya ta fice tareda rufe flat din tana komawa ta fada toilet tayi wanka tana fitowa Layla na tashi itama tashiga tayo wankan suka shirya coke da cake Layla taci itakuma Tasha golden morn suka wuce school.

Ahanyarsu ta zuwa aleeya ke driving layla kuwa massages din dawood take replying sai wani irin sahirtaccen murmushi takeyi sbd yanda duk ya ‘daga hankalinsa zai dawo tana lalla6atasa akan yabari yadawo Taredasu dad dinsa sbd koyazo shikadai su anan bazasu bashi aureba Saida iyayensa.

Kallonta aleeya tayi tace,

Naga hotonsa ‘dazu you two will make the best perfect couples.

Kallonta Layla tayi tace,

Kingansa da gske?

Yes dazu kina bacci naga hotonsa.

Murmushi layla tasaki tana sake kallon hotonsa dasukai tare dake wayarta aranta tace,

Dama I know my aleeya zatace kayi.

Suna Isa school suka shiga kowa yayi gurin lectures dinsa sbd Layla medicine takeyi aleeya Kuma law.

Ahankali suka Fara nisa akaratunsu sbd exams ma suke rubutawa kuma zuwa lokacin tuni aka yanke shawarar tsayarda ranar bikinsu danma antsaya jiran dawood din Layla yazo da iyayensa sukuma su dad ‘dinsa daya tuntubesu da maganar yaushe zasu koma Nigeria sukace sai next month sbd sukuma anasu tsarin so suke sai su aleeya sungama exams saisuxo ayi komai gabaki ‘daya.

Ranar dasuka gama exams washe gari suka wuce Lagos sukuma su mum aranar suka sauka Abuja dawood kuwa sai washe gari zai sauka daga baya su sufyaan zasu biyosa sbd kar saraah tayi zargin wani Abu.

Ranar dasuka dawo tun a airport suke mamaki da tsokanar Bilal ganin yanda lokaci ‘daya Yana Shirin zama saurayi Dan harma ya kusa kamosu a tsawo.

Ranar gidan cikin farin ciki da nishadi suke komai sbd gida ya kammale.

Ana saura biyu su mum zasuzo Lagos ammy tabugawa anty Nana tafada mata maganar neman aurensu aleeya daza’azo atsayar da date.

Siyama na zaune Koda ummanta ke waya da ammy taji duk abinda aka fada ta ta6e Baki tana cewa,

Duka dukafa Basu Dade dafara University ba shine za’ayi musu aure.

Numfashi umman tasake kafin tace,

Ba Dole suyi musu auren da wuriba kinaji tace bazaa dauki lokaciba za’ayi sbd aurene za’ayi na yayan billionaires sbd mazajen ko wacce ba’ama qasarnan suke zauneba.

Wani kallo siyama tayiwa umman tana juya zancen cikin ranta kafin tace,

Wai harda ita sadaka yallan ba’a qasarnan zatai aureba.?

Saikuma kiyi tunda ke kin kasa tsaida ruwan Ido ki tsayar gashi harkin gama degree saiki tsaya kiyita kallon anayi.

Wani ‘daci ta ha’diye a maqoshinta tareda aje nail polish ‘din datake shafawa a hannunta ta miqe tana cewa,

Lokacin komawata gidan yayi.

Harararta umman tayi tace,

Ki tsinci uwar me acan bayan duk buhun wulaqancinda sukai Miki Akan sadaka yallah.

Wani shu’umin murmushi tasaki tareda kallon umman tace,

Kika sani nima idan inacan abban yahadani da ‘daya daga cikin yaran rich mutanensa.

Baki umman ta washe tana cewa,

Hakane kumafa…wlh maza shirya gobe kitafi kafin kitafi kisayi ‘yan mayukan Nan Masu Dan tsada ki qara fito da kyawunki tunda ba finki akayi ba.Washe gari motar asuba tabi zuwa Lagos taso shiga jirgi Amma sbd karma ta tambayi ammy kudin ticket kamar yanda tasabab idan zata gudun kar ammy tace tayi zamanta yasa tashiga mota 
Tunda suka dau hanya ta kwantarda kanta tareda rufe ido cikin ranta tana kissima yanda zata Hana auren Layla auren mijin yadawo kanta.

2

Lokacinda ya sauka a Abuja taheer ne da kansa ya daukosa daga airport cikeda murna da farin cikin ganin ‘dan uwansa suka rungume juna sbd sun Dade Basu ha’du shi taheer baya zama sbd aiki shikuma Bai cika zuwaba tunda su mum suka tarki zama Nigeria.

Koda suka iso gidan anshirya Masa dishes na lunch kala kala cikeda farin ciki mum ta qarasa ta rungumesa atare itadashi sukace,

I missed you my love.

Itakuma tace,

I missed you more mi’amor.

Direct part ‘dinsa da aka gyara aka zuba komai yanda akasan yanaso da duk sauran abubuwan amfaninsa duka mum tasiyo tazo dazu tun daga can aka Kai luggages dinsa.

Saida yayi wanka ya kwanta ya huta Yana tashi Nur yafara Kira tana ganin numbers ta Nigeria tasaki wani lallausan murmushi sbd farin ciki da wani irin kwanciyar hankali dataji ya shigeta.

Tana ‘dauka taji lokacinda ya sake ajiyar zuciya ahankali tareda Kiran sunanta can qasan maqoshinsa Wanda dagashi har ita Saida tsigar jikinsu ta tashi.

Akasalance tace,

Do you really have to do this Everytime?

Lumshe Ido yayi tareda sake bu’de Baki daqyar yace,

you’re my life Nur,,I love you and know all I’m feeling is I can’t live a life without you in it,
Duk duniya yanxu Kece kawai abinda nake nake tsananin son samu so just tell su ammy su shirya I’m coming tomorrow.

Ajiyar zuciya tasake ahankali tanajin sabuwar qaunarsa da sonsa na qara shigarta murya qasa qasa itama tace,

Thank you.

Qasa qasan Shima daqyar yace,

Tell me how much you love me…

Words can’t describe it just keeps one thing in mind har lokacinda numfashina zai bar jikin Kaine ka’dai zaka zauna azuciyata wannan matsayinkane Kuma alqawarine bazai ta6a canxawaba.

Shiru yayi jikinsa na qara mutuwa sbd yazamo cikin jininsa jikinsa yake  duk lokacinda muryarta ta sauka cikin kunnuwansa sai dukkanin jikinsa ya mutu saidai dayake dama baida hayaniya ko kazar kazar baza’a ganeba saisu jass kawai dadukasan halin abinsu.

Shiru sukayi dukkaninsu tsawon lokaci can Kuma murya a kasalance yace,

Do you miss Nur.

Murmushi tasaki kafin tace,

No.

Wat”””yafada da sauri tareda tashi daga kwancen zaiyi magana ta rigasa cikin murmushi Mai sauti tace,

Silly”””tafada ahankali tareda kashe wayar ta aje fuskarta na qara wanxuwa da murmushin data kasa dainawa.

Aleeya data sata gaba da kallo harda tagumi sai dariya take tana ganin ta kashe ta tashi zaune a tsakiyar gadansu tana leqa fuskar laylar dake nuna tsananin sonda zuciyarta ke Masa tace,

Hmmm anya Layla dawood ‘dinnan Bai tafi da fiyeda rabinki ba yabar Mana saura.

Harara ta watsa mata still fuskarta ‘daukeda murmushi batareda ta Bata amsaba.

Sake matsowa tayi jikinta ta kwantarda kanta a cinyar Layla din tace,

Layla koda Ni bansamu soyayyar mi’amor ba zan dawwama cikin farin ciki ke kinsamu soyayyar Wanda kikeso tunda bamu taru mun rasaba.
Kallon fuskar aleeyar tayi cikin sanyi Jin yanayin muryarta,,
Shafa gashinta dake tsefe tayi itama cikin sanyi dason qarfafa Mata gwiwa tace,

Ina roqon Allah idan har Dole ‘dayanmu ne zai samu farin cikin samun soyayyar Wanda yakeso to yazamto Kece sbd Ni zanyi farin ciki naji Dadi idan Kece kike tareda abinda kikeso sbd Ni na ‘dandana naji ko haka na tuna zanji Dadi. 1

Nikuma ina roqo da dafatar dukkanin ‘yayana su samu soyayyar wainda suke so har abada. 1

‘dagowa sukai atare sukaga ammy tsaye hawayen da kowaccensu ke riqewa na tunanin halinda zasu shiga idan hakan dasuke tunani takasance suka gangaro musu da sauri ammyn ta qaraso ta rungumesu itama jikinta na mutuwa. 1

Washe gari Layla ta sanarda ammy zuwan dawood da iyayensa ammy tafadawa Abba shikuma ya bugawa cj ya fada Masa Dan suxo su ha’du da iyayen dawood din layla a tsayar da Rana tare.Threequarter yasaka black da black shir Mai hadeda hula ya fito ya nufi gurin mum dinsa sbd dad bayanan tunda ya iso Bai gansaba. +

Dama tunda yatafi takasa sukuni sbd baici abinciba Kuma gashi batason damuwarsa tanason yasamu isashen hutu kar ciwon Kai na stress yakama Mata shi.

Yana shigowa palon ta aje magazine din hannunta tareda miqa Masa hannu ya qaraso ya zauna kusada ita.

Kallonsa tayi Cikeda kulawa tace,

Bakaci komaiba haryanxu my love.

Kallonta yayi cikeda qaunarta aransa yace,

No mum nasha milkshake banajin yunwa yanxu I want to talk to you and dad abt sumthing serious..

Murmushi tasaki tana kallonsa tace,

Ok kabari sai dad dinka yadawo after dinner we’ll talk Amma right now I wanna tell you something,

Zuba Mata lazy eyes dinsa yayi sbd Yana iya hango zumudi da farin ciki akan face dinta da abinda takeson fada.

Well you see my love Akan maganar aurenka ne munason zuwa jibi idan mukaje a tsayar da ranar auren gashi haryanxu bakuga junaba shine nakega why not Kai gobe ka wuce kafin jibi muzo kun…ga ju..na…..

Rawa muryarta tafara da I ina sbd kallon daya tsareta dashi
Daqyar tasamu zancen yakai qarshe tace,

Meyasa kake kallona haka.

Lumshe Ido yayi tareda riqo hannunta daya yace,

Sorry I didn’t get wat you’re saying ne.

Ajiyar zuciya tasaki ta ‘dauka zaice yafasa ne tasaki sabon murmushi tace,

Yarinyarda muka za6ar maka nake nufin kaje kuga juna tunda kace kaima ka shirya aure kakeso….

Zame hannunsa yayi daga nata Yana sake kallon fuskarta yaga idan da gaske take.

Ganin Yana qoqarin miqewa yasa tayi saurin riqosa  zatai magana ya katseta da cewa,

Bansakaku Nemo min kowaba Koda nayi maganar zanyi aure nafada ne sbd nasamu wadda nakeso Dan haka tun wuri mum kidaina maganar nace zanyi aure Kun Nemo wata.

Murmushin qarfin Hali tasaki cikin sigar lallashi tace,

Come on sweetheart idan kaga yarinyar zaka sota, she’s very beautiful, classy,rich and…..

Zare hannunsa yayi tareda barin gurin yakoma part ‘dinsa gaba ‘daya.

Bayansa tabi da kallo tanajin wani irin zafi na taso Mata duk da split AC kusan guda uku dasuka sanyaya palon.

Komawa tayi ta zauna zuciyarta na tsalle sbd Sarai tunda yace bayaso bayi zaiyi ba itakuma tunda taso wannan auren bamai hanashi sai Allah duk yanda tasan zatayi ayi auren saitayi Amma Kuma batason takura ‘danta.

Taheer ne yashigo Ganinta cikin yanayin yasa yaqaraso ya zauna kusada ita tareda Kiran sunanta.

Kallonsa tayi da sauri tareda sakin ajiyar zuciya ta riqo hannunsa tace,

Darling kaga abinda mi’amor ke shirin yimana ko?
Wai yanada wadda yakeso baimada lokacin abinda mukeyi.

Numfashi yasauke Dan dama yasan za’ai haka tunda ba’ayiwa dawood ‘din gwari gwari ba tun farkon zancen.

Lallashin mum din kawai yayi yace ta kwantarda hankalinta dawood din zai amince idan ta lallashesa tai Masa magana.

Akan haka ta miqe tayi sashen dawood din sbd tunda yafara haka baxata ta6a Bari dad yajiba sai dawood din ya amince sbd dazarar yaji zai bawa dawood din wadda yakeso Koda kuwa basuda kudi sosai.

Tana zuwa a Palo ta tarar dashi zaune idanuwansa a lumshe.

My love””””takirasa ahanakali tareda zama kusadashi.

Tashi zaune yayi tareda zuba Mata idanuwansa Bai ce komaiba.

You see my love wannan yarinyar danake fada maka tafi duk wasu models da…

6acin ransa yayi qoqarin dannewa yace,

Mum tunda kin sawa ranki maganar yarinyar Bari na yanke zancennan,
Banasonta ko ‘yar gidan waye Kuma baxan auretaba wadda nakeso ita zan aura wai for godsake mum me can you go right now.

Kanada hankali kuwa Ni kake cewa na fita.,ita wannan da kake tada jijiyan wuya akanta ‘yar wacece dazata sa kana ‘dagamin murya.

Rufe idanuwansa dasuka kada sukai jajir yayi kafin ya bude yace,

Mum ko Yar waye,koba Yar wayeba ita nakeso ita zan aura and thats final idan kikace bazan auretaba then ki shirya tarar abinda zai biyo baya and one more thing kidainama sako maganar auren watacan sbd that will never happen sbd I rather die Dana auri wadda ba Nur ba so please mum mubar wannan maganar.

Baki tasake ta kallonsa zuciyarta na tafarfasa da maganganunsa.,
Nan take kishin Nur din daya fada ya rufe zuciyarta yanda duk duniya ba abinda ‘danta keso da qauna kamarta Amma yau son wata yasa Yana fada Mata mgn,
Wata irin tsanar Nur din daya fada ta cika zuciyarta tanaji aranta bazata ta6a barinsa ya auretaba sbd tun yanxu Yana Mata haka akanta idan ya aureta shikenan zai rage sonta koma ya daina sonta. 2

Girgixa Kai tayi tana cewa,
Inaaaa.

‘daure fuska tayi cikin ‘daga murya tace,

Bazaka auretaba yarinyar danake so ka aura ita zaka aura kodan ciwon sonka dake neman kasheta and thats final sannan duk kafadawa dad dinka wani Abu Akan haka daga lokacin kasa aranka bakada mahaifiya a duniya sbd na yafeka daga lakocin. 2

Qura Mata idanuwansa dasuka qara rinewa yayi zuciyarsa har wani tsallen 6acin Rai takeyi yace,

Bazan fada Masa ba Amma inanan kan ra’ayina bazan auri kowace bitch ba idanba Nur duk Wanda zai mutu ya da’de Bai mutuba anrufe.

Qarasowa taheer yayi tareda riqe mum cikin taushin murya yace,

Mum Please abar maganar aleeyan tunda yace bayaso kibarshi da wadda yace Yana so Mana.

Lafiyayyan Marin datakeson saukewa dawood tini ta sauke Masa tsantsar 6acin ranta na qara bayyana ta kallesu su duka cikin kausasa harshe tace,

Koyanaso ko bayaso saiya aureta kuma wlh cikinku duk Wanda yafadawa dad ‘dinku na ciresa acikin jerin ‘yayana and one more thing ka shirya gobema zamu je gidansu aleeya anfasa saka auren nesa kusa za”a sakashi.

A fusace ta juya tabar part din 
Wani zafi da 6acin Rai yakeji a zuciyarsa ga wata irin tsanar aleeyar dayake Kama kowane lungu da saqo na zuciyarsa sbd wannan shine karo na farko da wani yashiga tsakaninsa da abinda yakeso kuma ko so ‘daya mum Bata ta6a ‘daga Masa muryaba sai akan hakan harma da Marin taheer Wanda ga dukkanin alamu shitayi niyar saukewa da taheer din baizoba.

Taheer dake cikin takaici da mamakin Marin da’akai Masa yaga yanda Nan take fuskar dawood din tayi jajir abinka da farin mutum ya matso zaiyi Masa magana Amma tuni yayi hanyar bedroom ‘dinsa cikin tsananin fushi da 6acin Rai Abu ‘daya ya aje aransa shine bazai ta6a auren kawace mace idanba Nur ba.Da daddare Koda Abba yadawo babu Mai walwala acikinsu sai mum din dake qoqarin sakewa Dan kada yagano komai.

Washe gari rikici sosai aka sake tafkawa tsakaninsa da mum sbd ko qofar bedroom dinsa yaqi budewa bare tasamu damar sake maganar..

Yanda yaga dare haka yaga safiya idanuwansa har wani laushi da jemewa sukayi sbd rashin bacci da kwanciyar hankali adare ‘daya Tak kasancewar Bai Saba da rashin hutu da isashen bacci 
Babban abinda ya qara birkicesa gabaki ‘daya shine baisan yakai wata irin qololuwa ason Nur ‘din ba saiyanxu da mum tafara wannan maganar ta rabasu Wanda tuni yasan abune dazai faru bayan ransa sbd Babu ranar rabuwa da Nur agaresa saita mutuwarsa.

Aranar da daddare Koda yakirata kwanciya yayi tareda rufe idanu cikin sanyi yace,

My love kimini zancen dazaisani bacci inajin damuwa sosai kewarki nakeji please kiban dama gobe naxo naganki I seriously want to see you Angel.

Lumshe ido tayi sbd yanda jikinta yayi sanyi ya mace lokaci ‘daya sbd tsananin sanyin data jiyo a muryarsa.

Ka qara hkr har lokacinda su dad ‘dinka zasuzo,.

No Angel I can’t…inajin zan iya zama komai ne idan narasaki,
Meyasa nake sonki haka Nur???
zuciyana zafi yakeyi Sam banada nutsuwa ko sukuni yanxu I’m restless,
Haka son yake dama..?I love you Nur..I love you so very very much.,
Kece rayuwana yanxu I have to get you at any cost Nur.

Jitayi idanuwanta sun ciko da hawaye kalamansa sun sanyayata daqyar cikin tsananin sanyin murya tace,

Ka kwanta kayi bacci Saida safe.

Kashe wayar tayi ta aje tareda rufe idanuwanta.

Washe gari mum sabon tashin hankali akai sosai sbd tuni ya ha’da kayansa zai tafiyarsa Nan hankalin mum ‘din yaqara tashi gashi batason rarrashinsa Dan karya canxa mata ra’ayi Kuma tasan dazarar yatafi bazai sake dawowa kusaba qilama sai matarsa dayakeso sunyi aure.

Dafe goshi tayi cikin tsananin damuwa da neman mafita.
Wani tunani ne yafado Mata ta ‘dauki wayarta ta danna Kiran maska.

Cikeda kulawa ya ‘dauka asake yace,

Hello mum.

Cikin sauri sauri da tashin hankali tafara yimasa bayanin abinda ke faruwa ta ‘dora da cewa,

Son please do something, call him tell him koma meyene I don’t want him to go please my boy kayi wani.

Numfashi yasauke sbd jikinsa dayayi sanyi Jin wannan rikicin dakuma tsananin tausayin halinda dawood zai shiga idan mum tacigaba da dagewa akan rabasa da Nur..
Gyara murya yayi yace,

Mum meyasa kikeson Dole saiya rabu da Nur? they’re so much in love with each other mum.

Son please just call him now zamuyi sauran maganar but for now kasan yanda zakayi ka hanasa tafiya.

Ok…yace tareda kashe wayar Yana kallonsu jass dake sauraronsu.

Wayar dawood yakira Amma Bai ‘dagaba harsaida yayi Masa kusan Kira uku.

Yana ‘dauka yanayin muryarsa yasa jikinsa sanyi a tausashe yace,

Dawood mum called.

Numfashi Mai zafi ya sauke murya a shaqe yace,

I love her maska but I can’t do this,
Zanyi komai Dan ita Amma wannan karon ta ‘dauko babban al’amari sbd I can’t live without Nur.

Bazamu so ka rabu da farin cikinba ba but karkayiwa komai garaje kabi mum din ahankali I’m sure zata barka da farin cikinka tana sonka sosai bazata juri damuwarkaba so karkayi fushi.,Qaramin tsaki yaja cikin ‘dan zafi yace, +

Zantafi idan ta sauka zan dawo sbd ba yanda za’ayi naje gidan datake son naje.

Kar6an waya sufyaan yayi yace,

You’ll have to go dawood sbd idan wancan ‘din na sonka zatace ta hakura ka samu wadda kakeso kawai kaje kafada Mata gskia you don’t want to get married to her kanada wadda kakeso I think this will work.

Shiru dawood yayi ransa na qara quna sbd har cikin jininsa yakejin tsananin qiyayyar yarinyar ko ganinta bazaiso yayiba ace kamarsa harsaiya tsaya yiwa wata bitch bayani kafin yasamu wadda yakeso Amma it’s like he has no other option,
Akan Nur zai iya zuwa ko inane yayiwa duk mutanen duniya bayani.

Zubewa yayi bakin gado tareda dafe kansa dake Sara Masa sosai ga wani zafi da zuciyarsa keyi Amma bayason ya qara 6ata lokaci ayau zasu wuce gidansu yarinyar.

Su maska kuwa suna gama waya dashi dukkaninsu sukai tsit suna juya tsananin damuwar da abokinsu yake ciki ayanxu Dan kuwa sune shaidai tsananin son dayakewa Nur din,
Tun tasowarsu Basu ta6a ganinsa yaso Abu da tsanani hakaba kamar yanda yakewa Nur.

Ajiyar zuciya jass ya sauke cikin kulawa yace,

This is not good.

maska dake juya zancen aransa yace,

Dole zamuje da wuri yana buqatar wani akusadashi Dole.

Waya sufyaan ya ‘daga yafara Kira ayi musu booking tickets na zuwa Nigeria.

Wanka yasakeyi ya shirya cikin qananun Kaya dark blue da facing cap  tareda shades black yafito su mum kuwa tuni suka shirya sai washe Baki takeyi tana Nan Nan dashi suka fito gabaki ‘daya suka nufi airport.

Lokacinda aka bugo aka sanarda zuwansu tuni su ammy suka hau shirye shiryen tarbon baqi gashi itama Nur dawood yakira yasanar da ita yau zaizo da dad ‘dinsa zuwa dare ko gobe da safe idan sun baro gidan abokin dad dinsa.

Musamman mum tasake bugowa tafadawa aleeya suna hanya ba 6ata lokaci cikin farin ciki aleeya ta damu Layla Dole suka fita sukaje wani queens beauty pal&spa.

Gyara na musamman akayo Mata har wani irin qyalli take tayi tayi Layla tayi tace aa sbd dawood bayason hayaniyar kwalliya yafisonta a natural ‘dinta.

Koda suka dawo gida qarfe biyu ta ‘dan wuce Dan haka sallah kawai sukayi ta canxa kayanta zuwa doguwar Rigar wata Julius Holland dark brown ta ‘daure gashinta ta ‘daura qaramin vail akanta tareda zura bedroom slippers ta Taya aleeya shiryawa sai farin ciki suke suna fira Nan Bilal ya shigo aleeya ta kallesa da sauri tace,

Little qani sun iso?
Kaga brother inlaw ‘dinka?
He’s very handsome right?

Dariya ya bushe da ita kafin ya matso ya zauna kusada ita Yana kallon yanda tayi kyau kamar wata model yace,

Daina rawar jiki sunfasa sai gobe Kuma….

Zaro Ido tayi zatai magana layla tayi saurin Kai Masa duka a kafada tana cewa,

Mode spoiler.

Ajiyar zuciya tasake da qarfi tareda miqewa tabi bayansa da gudu tana cewa,

saidakasa zuciyana tsinkewa Allah saina ragewa coconut head ‘din Nan naka girma.

Dakin ammy yayi Yana dariya tabisa Nan ammy taraba rigimar Layla tace,

Allah ammy ya rainamu yaron Nan jifa yanda yatashi saka kwalliyar damuka tsara”””tafada tana gyarawa aleeya gyaran gashinta da sul6insa yasa yafara zarewa daga ribbon.

Sallamar siyama ce tasa dukkaninsu juyawa cikeda mamaki sbd ba Wanda yasakaran ganinta.

Fuska ‘daukeda murmushi da farin cikin da baikai zuciba ta qaraso tareda rungume aleeya tana cewa,Wow cousin you’re looking fabulous. +

Murmushin yaqe tasaki tace,

Thank you siyama saukar  bazata.

Eh wlh naso baku surprise ne,
Ammy ina wuni ya nasameku?

Lpia klau siyama,
Yasu anty Nana da babanki.

Duk suna gaisheku.
Kallon Layla tayi fuska asake tace,

Layla ya gida.

Lafiya qlau””tace tareda miqewa ta fice tana cewa,

Bari naje naqara duba cake ‘din da Nana keyi koyayi.

Tana fita aleeya da siyama suka biyo bayanta suna ‘dan fira.

Suna bedroom ‘dinsu sukaji isowar baqin kusan atare zuciyoyinsu suka buga lokacinda Bilal yashigo yafada musu baqin na Palon Abba.

Fira sukeyi Amma kowa kusan Rabin hankalinsa baya gurin.

Acan palon kuwa taheer ne yashigo taredasu dad dawood kuwa harabar gidan ya tsaya Kiran numbern Layla Amma yakasa samu jiyake kamar zai zauce idan baiji muryarta alokacinba.

Ammy ta gaisa dasu sosai cikin girmama takalli taheer dake gaidata ta amsa a mutumce sbd tunanin shine dawood din kafin sukai palonta da mum.

Nur ce agaba sai aleeya da siyama abayanta suka shigo palon ammy.

Zuciyar mum cikeda farin ciki ta amsa gaisuwarsu tana qara godewa Allah dazai cika Mata burinta.

Nur dake gefen ammy ta kafawa Ido ganin wani irin hutu da kwarjini dake fita a jikinta Nan take taji tana yiwa kanta sha’awar ace sirikarta ce,
Tabbas tafi dacewa da dawood ‘dinta saidai lokaci ya qure saidai taheer ‘dinta.

Ficewa sukai daga ‘dakin ammy tace,

Layla kije ki qarasa da dawood din guests palour zaifi sakewa sbd su abban Naga hirar business suke tukuna.

Ok ammy.

Aleeya da siyama bedroom suka koma ita Kuma ta nufi palon Abba Kai tsaye.

Da sallama ta shiga..

A cikin idanuwan taheer idanunta suka Fara sauka tayi saurin sunkuyar dakai numfashinta na fita da sauri.

Gaidasu abban tayi tasanarda abinda yakawota Nan taheer daya Dade da mutuwar zaune miqewa sbd baita6a tunanin Laylar ta zarce yanda take a hoto sosai.

Fitowa sukayi palon yace Mata dawood na harabar gidan.

Shigar dashi palon tayi suna qara gaisawa ta juya tana cewa,

Bari naje na shigo dashi.

Tundaga nesa ta hangosa ya bada baya Yana waya saidai kallo ‘daya tayiwa bayansa ta tsaya hakanan taji numfashinta na fita da sauri ta tsaya cak kamar wadda aka tsayar.

Wayarta yaqara Kira cikin sa’a tayi ringing.

Saurin kallon wayar hannunta tayi shikuwa Jin qaran waya bayansa yasashi juyowa.

Wani irin jirine ya ‘dibeta tayi saurin juyawa ta shige Palo batareda tabari yaqarasa juyowaba.

Rawa jikinta yakeyi sosai daqyar ta lalubi kujera ta zauna tana qoqarin Jan numfashinta daya tsaya.

Sake shigowa Kiran yayi tana gani ya katse zuwa lokacin ko wayar ta kasa riqewa rawa jikinta keyi sosai arikice ta miqe tayi dakin Nana sbd can ne kawai tasan ba Wanda zai ganta cikin wannan yanayin.Kasa zama tayi kodata shiga ‘dakin ta tsaya tsakiyar ‘dakin tana qoqarin samarwa kanta nutsuwar fahimtar abinda ke tabbatuwa arayuwarsu, +

Wasu irin hawayene suka gangaro Mata tana qoqarin danne kukan dakeson biyo bayansu.

Dawood ‘dinta shine dawood ‘din da aleeyarta keso meyasa takasa fahimta tuntuni daya sanarda ita garinda iyayensa suke.?

Meyasa dawood yaqi fada Mata cewar,

Iyayensa sun nemar Masa Mata…?

Wannen wane irin alamarine ya kusantosu.
Rufe Ido tayi tana tsananin Jin zafi azuciyarta,
Rawa qafafuwanta suka Fara yimata ta sulale tsakiyar ‘dakin hawayenta na tsananta gudu sabuwar doyayyar dawood takeji har cikin jininta,
Soyayyar dawood tariga tazamo wani 6ari na jikinta wani irin zafi da nauyi takeji ayanxu data gansa amatsayin na aleeyarts to Yaya aleeya zataji idan taji shine dawood ‘dinta.

Girgixa Kai tayi hawayenta na qara gudu cikin rawar murya ahankali tace,

Wlh zafi nakeji sosai cikin zuciyana aleeya bazanso kiji wannan zafinba  Bazaki iya juresaba. 1

Ahankali tafara kuka Mai qaramin sauti har lokacin jikinta Bai daina rawaba.

Tunowa da ammy yasa ta tsayarda kukanta tareda tattaro qarfin Hali tasawa zuciyarta ta share fuskarta tareda miqewa da sauri ta fice tana roqon Allah yasa ammy da dawood basuga junaba.

‘dakin ammy ta nufa tana qara qoqarin danne halinda take ciki.

Ammy ce kawai a ‘dakin itama wayarta tazo ‘dauka takoma palon gurinsu Abba.

Ahankali ta qaraso gaban ammy ta riqo hannunta tareda dawowa bakin gado suka zauna.

Sunkuyar dakai tayi hawayen datake qoqarin dannewa sunason fitowa Amma ta ‘daure ta mayar dasu Amma idanuwanta sun jajir.

Sanyi jikin ammy yayi ta qura Mata idanuwa ta lurada yanda jikinta ke ‘dan rawa ta riqo hannunta da sauri cikin tsananin fargaba tace,

Layla?

‘dagowa tayi takalli ammyn Nan take ammy ta qara shiga ru’dani ganin Jan idanuwanta tace,

Layla meke faruwa?

Ammy tunda na taso cikin quncin rayuwa da talauci na taso,
Babu Wanda ya ta6a yimin kallon mutum bare ya bani mutuntawa da darajar da Allah yabawa mutum,
Ni Almajirace ‘yar bola Mara asali da gata,
Ammy duk duniya bayan iyayena dasuka haifeni Babu Wanda nake tsananin so da qaunar farin cikinta irin aleeya sbd itace takalleni amatsayin mutum ta miqamin hannu ta cironi daga qanqantacciyar rayuwar titi da bolan danakeyi Wanda da yanxu na zama wata abar qyamar., 3

Ammy har abada ina roqon Allah daya nesantani da abinda zaisa nakawo damuwa a fuskar aleeya.,…..

Sosai jikin ammy yayi sanyi murya a sanyaye tace,

Layla meyasa kike tado da abinda yazamo tarihi?…..

Dr Dawood ne Wanda aleeya zata aura..

Yawu ammy ta ha’diye sbd gudun garajen fahimta tace,

Banganeba Layla sakemin bayani.

Ammy dr dawood shine ‘dan abokin Abba dasukazo yanxu.

Mummunan fa’duwa gaban ammy yayi ta lashi busasshen bakinta sai alokacin tasake qurawa layla Ido taqara hango mummunan halinda take ciki tana qoqarin dannewa.

Layla wannan ba abun damuwa bane tunda ba auren aka ‘dauraba zanyiwasu abbanku bayani yanxu..

Miqewa tayi laylar ta riqo hannunta tareda dawowa gabanta ta sunkuyar dakai cikeda qarfin Hali tace,Ammy ke uwace dabakyason kan ‘yayanki ya rabu,
Kin manta nayi Miki alqawarin toshe duk wata hanya dazata kawo 6araka atsakaninmu,
Ammy wannan shine alqawarina dazan cika bazan ta6a Bari hawaye yasauka kan fuskar aleeya ba ta hanyata,
Ammy kiyimin alqawarin har abada Bazaki ta6a fadawa kowa wannan maganarba… 2

Girgixa Kai ammy tayi cikin tsananin tashin hankali da damuwa tace,

Wannan shirme ne kikeyi layla sbd bazai ta6a yiyuwaba,
Idan har farin ciki kikesowa aleeya to Bazaki Bari ta auri Wanda baya sonta yanada wadda yakeso wace irin rayuwar aure zatayi da Wanda keson wata mace ba itaba…

Hawaye ta goge da bayan hannu tace,

Ammy shine farin cikinta,shitakeso bazata ta6a iyason waniba bayansa….

Kidaina fadamin haka sbd wannan ba sacrifice bane Layla rayuwarku ce ku uku zata lalace,
Kalli halinda kike ciki yanxu,
Ji yanda kike qowarin danne quncin dake ranki Amma ina iya ganinsa,

Dawood ke yakeso bazai ta6a son aleeya ba sbd tun farko ba ita yakesoba.

Tsananta hawayenta sukayi tace,

Ammy Koda Baki yardaba na yafe dawood har abada sbd bazan iya cigaba dason abinda aleeya kesoba,
Wannan alqawarina ne duk ranarda aleeya taji zancen Nan zan tafi tafiya ta har abada ammy sbd bazan iya hada Ido da itaba nayi tarayya da ita akan abinda takeso nakasa cirewa zuciyata cewa hakan ba laifina bane.

Tsananta tashin hankalin ammy yayi tace,

Layla meyasa zakiyi haka Dan kuwa hakan shine babban kuskuren dazaki tafka wannan ba mafita bace.

Kuka tasake ahankali ammyn tayi saurin rungumeta tana danne nata hawayen sbd Laylan tasakata a tsaka Mai wuya sbd rayuwarsu duka su biyun ne zata lalace garin toshe 6araka za’ayi gaba Mara da’di.

Jin motsin shigowa yasa laylar zamewa ta miqe ta shige toilet ‘din ammy.

Siyama dake jinsu tun farko ta gyara tsayuwarta tareda sakin wani shu’umin murmushi tace,

Hmmnn dagani abubuwa zasu zomin yanda suka Dace,
Dawood sukeso dukkaninsu hmmm,
I will make this my mission matuqar inada Rai da lafiya bazan ta6a Bari aleeya tasan da wannan zancenba sbd dataji kamar koyaushe Layla xata samesa hakan na nufin koyaushe itace a gabanta..
Duk Wanda yayi qoqarin ha’dasu kuwa saita ‘dorasa adaidai inda bazai qara kallon matsalar waniba tasama tafi qarfinsa.
Mission ‘dinta na biyu kuwa taheer,
Kallo ‘daya tayi Masa ya tafi da zuciyarta Dan haka kuwa duk duniya batasaran zata zauna ta huta batareda burinta na aurensa ya cikaba.

Daki takoma tana zuba murmushin farin cikin samun sauqin abunda yakawota.

Aleeya kuwa tunda sukaje palon taheer kawai suka tarar suka gaisa siyama kallo ‘daya tai Masa tasaki Baki tuni tafara tunanin yanda rayuwarta zata canza idan ta auresa.
Ganin zata zubarwa da kanta aji gurin kallonsa yasa tamiqe takoma ‘daki anan kunnuwanta sukayo Mata farin ji.

Fira suke hankalinsu kwance akai akai saiya Fadi sunan Layla saidai kawai tayi Masa dariya sbd tun acan tafada Masa akwai Wanda Laylar keso.

Daqyar taheer yaje yashigo dashi sbd lokaci ‘daya ya burkice sbd rashin Jin Nur gashi yanxu ta kashe wayar gabaki ‘daya ma.
Kodaya shigo Sam mantawa yayi da maganar inda yake daqyar taheer yayita basa Baki yadan sassauto ya nutsu.

Kallon inda take yayi fuska a ha’de..

Lumshe Ido yayi cikin tsananin takaici,
Mum Sam batamasan abinda zai iya soba,.

Fa’duwa gabanta yayi ganin irin kallon daya jefeta dashi amma duk da haka zuciyarta cike take fal da farin cikin ganinsa Wanda tuni sonsa yaci gaba da ninkuwa a zuciyarta.

Kasa magana yayi sbd yanda nutsuwarsa ke qara hautsinewa ya miqe tareda fiddo wayarsa ya fice Yana cigabada Kiran Nur.

Taheer ne yabiyosa da nufin fada Masa abinda yayi Bai daceba Amma ganin yanayinsa sai jikinsa yayi sanyi yace,

Dawood please relax kabari zuwa anjima saika sake Kira yanxu bakaga muna gidan kunya bane.

Wani mugun kallo ya watsa Masa tareda juyawa ya tada motar dasukazo da ita daga gidansu nanan yabar gidan gaba ‘daya.Jingina jikin qofar toilet ‘din ta jingina tareda zamewa ta durqusa tareda sakin kukan datake dannewa gaban ammy ahankali,
Shesheka takeyi sosai tasa hannu ta rufe bakinta kukan na tsananta. +

Rarrashin kanta tayi ta miqe ta tsaya gaban mirror tareda kallon fuskarta taga yanda lokaci ‘daya tayi jajir.

Wanke fuskar tayi jiki ba qwari ta goge fuskar da towel tareda qara tattaro juriya ta fito.

Har lokacin ammy na zaune bakin gadon ta rafka tagumi da hannuwa biyu takasa miqewa bare ta fita takoma Palo.

Fitowarta yasa ammy ‘dagowa ta qura Mata ido ta yanda fuskarta tayi jajir lokaci ‘daya har wani fa’dawa fuskarta tayi.

Qofa ta nufa zata fice ganin kallon da ammy ke Mata taji tace,

Layla matuqar Bazaki auri dawood ba aleeya ma bazata auresaba.

Da sauri ta juyo tana kallon ammyn.

Eh wannan nawa hukuncin ne sbd Babu dalilin dazaisa ta auri Wanda baya sonta ko ka’dan ‘yar uwarta yakeso.

Dawowa tayi ta zauna murya a karye tace,

Ammy kenan niba ‘yar uwar aleeya bace.

Me kike fada layla??har abada aleeya Yar uwarkice.

Idan har ‘yar uwatace Ni ‘yarkice to ammy bazaki hanata samun abinda takesoba sbd ni bansamu ba.,
Ammy mezamu fadawa su Abba idan kikace aleeya bazata auri dawood ba?
Kowa zaisan abinda yake faruwa daganan za’a iya samun rashin fahimta daga wasu Kinga qarshe dai abinda ake gujewar zai faru Kuma dukkanin ‘yayanki zasu rasa farin cikinsu hakan zai ta6a zuciyarki da kwanciyar hankalin gidannan,
Ina roqonki ammy daki Bari aleeya tasamu farin ciki da Wanda takeso…..

Katseta tayi cikin ‘dan ‘daga murya da cewa,

Layla kin kasa ganewa farin cikin ne bazata samuba har abada idan ta auresa.,Kuma me zai faru idan dawood ya ganki amatsayin ‘yar uwarta kina tunanin zaiyi shiru ne?

Numfashi Mai ciwo ta sauke murya a karye tace,

Bazai qara ganinaba ammy sbd na yanke duk wata alaqa dashi saita wadda zamu Fara yanxu bayan aurnsa da aleeya amatsayin ‘yar uwar matarsa.

Ammy kiyimin wannan alqawarin na bazaki fadawa aleeya ba.

Me kike cewane Layla?””sukaji anfada daga bakin qofa.

Itakadaice ta juya da sauri tana qoqarin danne halinda dake ciki ganin aleeya a tsaye bakin qofa.

Ammy kuwa miqewa tayi ta fice batareda takalli su duka biyunba sbd zuciyarta na ingizatane ga fadar gskia saidai Kuma fadar gskiar zai iya kawo rashin fahimta sbd shaidan zai iya saka musu kishin juna ko yayane sbd za’a iya cewa ya auresu duka Wanda kwata kwata har abada bazataso hakanba Dan Dole watarana za’a samu sa6ani.

Qarasowa tayi jikinta amatuqar sanyaye,
Da sanyin jikin abinda dawood yayi Mata ta shigo Amma Jin abinda Layla ke fada ya qara sanyaya jikinta.

Zama tayi kusada laylar tana kallonta cikeda mamaki da fargabar ganin sauyi sosai atareda ita,
Idanuwanta dasukai jajir da fuskartama gaba ‘daya takalla tuni kafin taji koma meyene idanuwanta suka cicciko Nan take damuwar datake ciki ta dawood ta 6ace asanyaye tace,

Dama Layla akwai abinda harzaki saka wani alqawarin kar afadamin??
Wane irin sirrine da Ni bazan iya 6oye mikiba har kike guduna dashi….

Jin muryar aleeyar tafara rawa yasa tayi saurin riqo hannunta tana qoqarin Hana hawayenta fitowa Amma Saida suka gangaro tace,

Har abada Babu wani sirri dazan 6oye Miki idanma akwai to kisaka aranki Dan ciganki da farin cikinki ne…

Inason sanin koma menene Layla kifadamin tun kafin zuciyata ta buga da fargaba.

Share hawayenta tayi ahankali tace,

Dawood iyayensa sun Masa Mata har antsayar da ranar aurensu bazai ta6a aurena……

Tun kafin laylar takai qarshe kukan datake riqewane ya kubce Mata tayi saurin rungume laylar cikeda wani irin tausayinta dama tanason yin Kuka Dan rage zugin zuciyarta na tsantsar qiyayyarta data hango a idanuwan dawood idan ba kuskuren gani tayiba.

Kuka take sosai na tausayin Layla da kanta saidai tafasa fadawa Layla damuwarta Akan qiyayyarta data gani a idon dawood sbd karta qara Mata damuwa ko ammy bazata fadawa ba zata bar maganar aranta ta Taya ‘yar uwarta jimamin abinda yasameta..

Sosai tayi qarfin Hali ta nunawa aleeya ta rumgumi hakan amatsayin da dama bashine mijinta ba. +

Girgixa Kai aleeya tayi tana fitarda sabbin hawaye tace,

Yanda kikesonsa har abada bazaki daina sonsaba,
Tun zamana dake akwai wasu farin ciki da annashuwa dashine kadai yake sakiyinsu koni bana sakaki duk kuwa danasan babbn matsayin danake dashi agunki,
Layla bazaki iya babushi ba Ni zanje har gurinsa na roqesa yadawo gareki zan qasqantar da kaina na roqesa qasqantarwa ta qarshe Dan yadawo gareki..

Share hawayenta tayi tana qaqalo murmushin qarfin Hali sbd so take arufe maganar dawood da ita gaba ‘daya ayau basai ankwanaba ga kanta dake tsananta ciwo zazza6i Mai zafi takeji sosai.

Aleeya na dangana nabarsa har abada Dan haka daki tayani nemosa gwara kitayani mantawa dashi.

Sake rungumeta aleeya tayi cikin tsananin tausayinta da Jin zafin dawood ‘din daya za6i wata yabar Layla Nan take taji ta tsanesa Koda zai dawo bazata ta6a barinsa ya auri Laylan ba sbd Bai cancancetaba 
Laylanta ta cancanci Wanda yasan darajarta fiyeda komai.

Jin jikin laylar da zafi yasa ta ja hannunta suka koma bedroom ‘dinsu ta kwantarda ita tareda ja Mata bargo cikeda kulawa tace,

Have some rest zakiji qarfi zuwa anjima.

Miqewa tayi ta zame kayanta tasa jeans da vest tadawo bakin gadon da laylar ke kwance ta rafka tagumi cikeda tunani da damuwar kanta data laylar.

Itama Layla rufe idanuwan kawai tayi.

Daqyar ammy ke sakin murmushin yaqe hardai Abba ya tambayeta maganar iyayen manemin Layla kawai suke jira su qaraso yanxu.

Rufe idanuwa tayi tareda ha’diye wani ‘daci a maqoshinta cikeda damuwar abinda zata fada tace,

Saidai ayi hkr akwai wadda iyayensa keso ya aura Dan haka sun fasa zuwa saidai zuwa gaba idan ansamu fahimta.

Fada Abba yahauyi Rai a6ace yace,

Dama dai bada gskia yakeyiba Dan da bazai Raina Mana hankaliba yace zasuzo.

Hakuqi CJ yabawa abban Yana cewa,

Agodewa Allah bama Saida akazo ‘daurin aure yace yafasaba.

Exactly fa ai gwara da tun yanxu akasan stand nasu””””mum ce tafada hakan tana nuna tausawarta ga ammy datayi nisa a tunani ko abinda suke fada bataji.

Zuciya ba da’di hakanan Abba da dad suka tsayar da bikin wata biyu Masu zuwa hakanan mum ta haqura badan tasoba sbd da wuri taso ayi.

Koda suka koma gida dawood bayanan Kota kansa batabiba tayita harkokinta cikin farin ciki.

Baidawo gidanba sai dare sosai kallo ‘daya zakai Masa yabaka tausayi sbd kwata kwata Bai saba da wahala ba Amma yau ko ruwa baisawa cikinsaba haukacewane kawai baiyiba gurin Kiran layinta yakira yakira,yayi yawo agarin harya 6ata saidaya Kira taheer yaje yadawo gida dashi.

Ganin yanda daqyar yake bude bakinsa daya bushe yasa mum da taheer hankalinsu Fara tashi Nan tahau lallashinsa akan yasha Koda juice ne Amma yaqi.

Wasa wasa saiga zazza6i Mai qarfi ya kwantar dashi adaren Babu Wanda ya rintsa cj cikin tashin hankali yasa sukabi jirgin safe suka dawo Abuja.

Koda suka dawo babu abinda yayi sauqi gashi yahanawa kansa sukuni da daina Kiran layinta.

Da daddare Dr dayazo tasashi yayi mixing alluransa Dana bacci yayi Masa Nan take bacci yayi gaba dashi. 1

Dr na fita ta ‘dauki wayarsa ta duba numbern datake nema ta goge tareda duk wasu massages daga gareta duk wani Abu daya danganceta saidata goge ta ‘daga wayar sama ta sakota qasa tareda ficewa daga bedroom ‘din.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]