[Advertisements⬇️]

DAWUUD CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

DAWUUD

CHAPTER 1


NUR D.S specialist hsptl first floor acade building anyerinxs strt porthcrt 23 December… +

Da wani irin speed motar ambulance ‘din specialist ‘din tashigo harabar building ‘din asibitin manyan Mercedes Benz 3600mz2018 black biyu na bayan ambulance din ko kyakkyawan parking basuyiba sukai saurin fitowa Babu Wanda hankalinsa ke jikinsa sbd tsananin tashin hankalin dake cikin zukatansu na ganin Wanda kowannensu baya iya kwatanta rayuwa babushi..

Arikice suka qaraso jikin ambulance din daidai lokacinda nurses maza da mata tareda doctors kusan biyar sukayo kan motar aka fito dashi cikin gaggawa akayi ciki dashi tun a hanya ake ‘daura Masa ruwa da jini sbd tun acikin ambulance andaura Masa cannula tareda Fara basa injections na jinin daya zubar sosai ta bakinsa..,

Cikin tashin hankalin dayafi na likitoci da nurses ‘din asibitin ganin babban likitansu Kuma Mai asibitin cikin wannan mummunan yanayin suke bin bayansu har aka iso bakin private aminity emergency suka shige dashi aka rufo qofar Dr ayub ne yasamu damar ‘dan waiwayowa cikin gaggawa da son kwantar musu da hankali yace

Sorry ma’am you will have to wait hia and please calm your self insha Allah he’ll be fine we’ll do our all best just pray for him,,

Ya juya ya shige tareda wasu nurses biyu dasuka zo shigewa da gudu ‘daukeda wasu kayan theatre..

Baya tayi cikin tsananin tashin hankali tareda fashewa da wani irin kuka sufyaan dake gefenta yayi saurin tarota cikin qarfin Hali ya bude bakinsa daqyar yasamu ya iya furta, 2


Wani sabon kukan tasaki tareda rintse ido tana cewa,

Ya Allah ka kawowa ‘dana sauqi da sassaucin wannan masifa,
Wannan wace irin qaddarace Mai wuyar cinyewa…..

Rufe Mata Baki sufyaan ‘din yayi da sauri Yana kallonta da idanuwansa dasuka ka’da sukai jajir tsabar tashin hankali…

Juyawa yayi ahankali ya kalli gefensa daidai isowar jass arikice ko gani sosai bayayi tsabar tashin hankali Yana isowa ya tsaya cak ganin irin tashin hankali dake tattareda kowannensu

Fuskar sufyaan ya kalla yaga hawaye sun cika jajayen idanuwansa Nan take yaji gwiwowinsa sun Gaza ‘daukarsa ya zube kan kujerar dake kusadashi tareda rufe fuskarsa da tafukan hannayensa hawaye na tsinke Masa Masu zafi da ciwo.

Sunkuyar dakai sufyaan ‘din yayi ganin halinda jass yashiga zuciyarsa na qara nauyi.,

Hawayen dayake dannewane suka gangaro Masa lokacinda ya ‘dago kansa ya ‘dora idanuwansa kanta tana zaune Nana na zaune gefenta ta riqo dukkanin hannuwanta biyu tanata qoqarin ganin ta kwantar Mata da hankali cikin hawaye da tsananin tashin hankali ganin kamar zarewa ‘yar uwar Tata zatayi sbd tunda abin yafaru ko motsin kirki batayiba bare hawaye saidai jajir da idanuwanta sukai Sam ita tafiso taganta tayi kuka yafi sauqi akan wannan halin dataga tashiga..

Lumshe idanuwansa dasukai jajir yayi cikin tsananin tausayin ALEEYA tabbas dukkaninsu suna cikin wani Hali Amma tafisu Dan kuwa ita qunci da Sauyin rayuwa tuni ya Dade da wargaza komai nata,
Ta Dade dayin bankwana da farin ciki,
Babu wani ‘digon farin ciki dayayi saura arayuwarta,
Qunci,damuwa,kuka,ciwo,zafi dakuma baqin ciki sune kadai sukeda cikakken mulkin mallaka arayuwarta yanxu kokuma yace arayuwar dukkaninsu dankuwa dukkaninsu sun Jima da manta yanda yanayin farin ciki ko annashuwa suke,A dah daza’ace akwai ranarda zasuji wata damuwa bare baqin ciki da bazai tsaya sauraroba Dan bazai yarda ba sbd dukiya, kyau,ilimi, wayewa,gata,dakuma ingantacciyar rayuwar holewa dusukeda ita a hannunsu Ashe komai na juyawa,,
Har ayanxu Basu rasa komaiba Amma komai yazama kamar babushi sbd babu farin ciki ko kwanciyar hankalin Jin dadin kenan dukiyar da kyawun,da ilimin da gatan da wayewar basuda wani amfani ayanxu arayuwarsu,
DAWOOD wani 6angare ne arayuwarsu dazasu iya kwatanta rayuwa babusaba,.. 1

Hannu yakai ahankali ya dafa kafadun jass tareda jinjina Masa Kai alamar rarrashi ‘dayan hannun nasa na riqedana mum sbd har lokacin wani irin kuka take Mai tattareda danasani,nadama da uwa uba fargabar rasa tilon ‘danta,farin cikinta.

Zaman jigum jigum sukayi cikin matsuwa da fargaba har tsawon awa ‘daya kafin doctors suka Fara fitowa har lokacin mum hawayenta Basu tsayaba idanuwanta sun kumbura matuqa ko gani sosai batayi fuskarta tayi jajir kasancewarta Fara sosai

Sam Batada qarfin motsawa lokacinda doctor Jeremy da Dr Aqeel suka qaraso gabansu
Ganin tana neman shiga wani sabon halin ne sufyaan yasake riqeta Yana rarrashinta
Saidai jass ne ya miqe tsaye jikinsa na’dan rawa sbd sam Shima tamkar mace yake baida irin dauriyar Nan sosai a irin haka.

Kallonsu yayi da jajayen idanuwansa murya na rawa yace,

How is h,,,kasa qarasawa yayi sbd kukan dayaso kubce Masa yayi shiru Yana goge fuskarsa da handkachief..

Dafasa Dr Aqeel yayi cikin damuwar Shima yace,

Kuci gaba da addua shine kadai abinda zamu iya cewa,
Kaida sufyaan are doctors kunsan irin yanda abubuwan ke juyawa so please just keep on praying for him sbd he really needs it…

Kallon mum sukayi cikin sanyin murya sukace,

We’re really sorry Mrs assiddeeq addua shine the best thing now… Allah yakawo sauqi muna fata.

Juyawa sukayi suka wuce jiki sanyaye cikeda tausayin familys din.

Zuru dukkaninsu sukayi kamar Babu Mai Rai suna kallo aka fito dashi aka Kai wani special room sukayi rubuce rubuce da sauran formalities ‘din kafin dukkaninsu suka fice.

Itace tafara miqewa Nana na riqeda ita sbd Bata iya tsayawa da kanta sbd jiri da ciwon dayake damunta for some years now sukaga room din.

Bakin gadon ta qarasa zuciyarta na wani irin bugawa,zafi da ciwon zuciyarta na shekaru na ninkuwa,
Kuka takeso tayi Amma takasa Wanda hakan yasa idanuwan sukai wata irin jemewa Babu kyawun ganin sbd komawar dasukai kamar na tsufa.

Qura Masa idanuwa tayi zuciyarta na nauyi sbd ganin yanda ciwo ya mayardashi,
Kyakkyawane ajin qarshe kasancewarsa halfcas Amma gabaki ‘daya kamaninsa sun canza
Fuskarsa ta rame tareda wani irin duhu musamman gurin gurbin idanuwansa sai bakinsa dayayi baqi ya bushe kamar yayi shekara goma baisha ruwaba..

Ahankali ta furta,
DAWOOD..

Jitayi zuciyarta ta amsa Amon sunansa data Kira
Nan take jikinta yafara karkarwa zuciyarta na neman rasa Jan numashi.

Da sauri Nana dake gefe tana kuka ahankali kamar ranta zai fita sbd tausayi abubuwan dake faruwa tsawon shekaru,,,,
Kowa na rayuwar farin ciki da Jin Dadi Amma cikin shekaru biyar kacal komai ya lalace,
Farin ciki yazamo tarihi arayuwarsu kuka da ciwo sune kawai ke qara wanxuwa a tsakaninsu

Ahankali mum tashigo ‘dakin jass na riqeda ita sbd sufyaan na bayansu..

Kallo ‘daya zakayiwa mum tabaka tsananin tausayi sbd yanda ta jeme cikin qanqanin lokaci tsufa yafara taso Mata duk kuwa da tsufan ne tayba
Gabaki ‘daya itama tayi duhu ga wata irin rama..bazaka kalleta kace itace Madame faraah ba the famous Mrs assiddeeq Damien da kullum ake bugawa a cover din fashion magazine ba sbd kasancewarta CEO na all the fashion empire na Miami,
Kyau,hutu,gayu,burgewa tareda ‘dinbin dukiya uwa uba bazakai Mata kallon babbar macenda ta aje babban the youngest multibillonaire doctor DAWOOD ASSIDDEEQ DAUDA ba dasukaci lokacinsu Wanda haryanxu ba’asamu madadinsa ba shida friends dinsa Amma yau duk Babu wannan sbd tun farko basusan qaddarar da Allah ya tanadar musu agaba.
Tsit dukkaninsu sukayi kowa da ka’dadden idanuwansa yake kallon dawood din dake tsakanin Rai ko mutuwa sbd baimasan waye akansaba. +

Sunjima ahaka kafin nurses biyu suka shigo tareda Dr shuan Lee Chinese ne cikin girmawa yace suyi excusing nasu.

Jiki a mace suka fito sufyaan da jass mota suka koma sbd ganin yanda jass ke buqatar air dinda zaiyi kuka son ransa Shima sufyaan kukan yakeson yi Amma nauyin dayake ji zuciyarsa yaqi Bari yayi kukan.

Cikin sheshekar kuka jass yace,

Yaan bansan yazan kwantanta rayuwa Babu ku ba acikinta,
Banda kowa saiku,kaima bakada kowa saimu,
Munajin dadin rayuwarmu and then everythings change,,,mun rasa maska Wanda rashinsa ya jijjiga duniyarmu da haryau Bata dawo daidaiba and now dawood… 1

Rintse ido sufyaan yayi da sauri tareda rungume jass ‘din sbd kukan daya saki har cikin ransa yakejinsa sbd qaunace ta junansu da Allah yasaka musu ajininsu su hudu DAWOOD, SUFYAAN, JASSPER,HAYDAR MASKA…

Jass yakasance Mai raunin cikinsu shiyasa koyaushe sukafi tausayinsa..

Kuka yake sosai Wanda duk dauriyar sufyaan saidayayi kukan Shima suka rungume juna suna kuka zuciyoyinsu ka karye.

Tana fitowa room din ahankali ta nufi gurin receiption ta lalubi kujera ta zauna…

‘dago idanuwa tayi ahankali ta ‘dora kan babban farin glass dake ‘daukeda sunan asibitin tana qanqame jikinta dakeson Fara karkarwa aduk lokacinda taga wani Abu daya danganci…..

Dafata taji anyi ta sake cusa canta cikin qafafunta sbd yanda taji hannun daya dafata Yana rawa yasa tasan kowaye…

Zama kusada ita mum ‘din tayi tareda qura Mata idanuwa…

Kyakkyawar fuskarta dake ‘dauke da kyawawan fararen idanuwanta ta tuno data kalleta yanzu taga yanda komai nata ya zabge,

ALEEYA kyakkyawar budurwar datai tashen hutu, dukiya dakuma kyau uwa uba aji da burgewa da barkwanci Amma qaddara da azabar SO sun juya rayuwarta harma sa kamanninta takoma kamar wata goggo yakumbo wadda ayanxu take iya wata batareda tayi magana biyu zuwa ukuba. 1

Hawayen tausayin aleeyar ne yanxu suka gangaro mata,
Idan ‘danta nacikin wannan azavar ciwon tabbas aleeya nacikin makamancinsa Yana cinta cikin Rai da ruhinta Wanda ciwon ciki tabbas yafi na bayyane duk da tasan dawood Kam sai wani ikon Rabb,
To idan duk suna cikin wannan halin tasan akwai wadda tafisu Jin ra’dadi da azaba fiyeda komai KINA INA NUR… shine kalmar data furta ahankali sabbin hawaye da 6alle Mata.

Jin furucin na mum yasa aleeya ‘dagowa ahankali tasake qurawa sunan asibitin ido akaro na farko bayan wasu shekaru da hawaye suka sauko idanuwanta

Jitayi nantake hawaye sun 6alle Mata ba qaqqautawa
Lumshe idanuwanta tayi batareda tadamu da gogesu dan tanada tabbacin Babu wani sauqi ko nauyi da kukan zai rage Mata na dangane da abinda takeji sbd wannan wani nauyine da Allah ya ‘dora Mata a zuciyarta Wanda sai ranar da numfashinta yabar jikinta zata samu sauqinsa.

A wahalce mum ta bude Baki tace,

Ina fatan samun sauqi da maslaha ga dukkanin damuwarmu,
Allah yabawa kowa ikon cinye jarabarsa domin kuwa dukkaninmu jarabarmu ‘dayace idan Allah ya ‘dauke ran dawood,,,,,ta qarasa fa’da tana goge idanuwanta dasukai luhu luhu ko ganinsu ba’ayi sosai sbd sun shige fuskar ta kumbura

Batareda tayi maganaba tasake ‘dagowa akaro na uku ta qurawa sunan specialist ‘din ido….
NUR D.S SPECIALIST.

Bazata manta yanda komai yasamo asaliba Wanda saidai takira hakan da mafari…..Sake lumshe idanuwanta tayi wasu hawayen suka sake gangaro Mata Masu zafi Wanda zafinsu tundaga tsakiyar zuciyarta ya fito…….


Layestrt adamawa 22 April

Buzaye ne irin wainda ake cewa sadaka yallah sbd talauci da baqar dau’dar data Kama jikinsu harta dafe su gashinsu da ‘dan sauran hasken daya rage musu kawai zaka gani kasan buzaye ne..

Zaune suke cikin wani kangon company dayayi shekaru ba’a qarasashi ba tsufa da alamu da zubewa duk sun bayyana a ginin duk da ginine da’akayi na cement zalla Mai qarko da kyau.
Sam girmansa baya Basu tsoro dan kusan Hawa biyarne na ginin sudai rayuwarsu suke aciki sbd basuda wani gurin zama idan ba Nan ‘dinba Wanda basusan yazasuyi da rayuwarsuba idan Mai companin ya nemi su tashiba., 1

Ahankali dattijon dake kwance tsawon shekaru biyu ba lafiya ya bude idanuwansa daqyar ya ‘dorasu akanta,,,

Zaune take kusadashi ta kwantarda kanta kan gwiwowinta ta qurawa qasa ido Wanda yasan idan zasukai wata safiyar ahaka bazatai maganarda ta wuce biyu zuwa uku ba…baabaa sannu,,,ya jikin,,,,kana buqatar wani Abu???? Wainnan sune kadai kalaman dayasan zata iya furtawa kokuma yace kullum sune iya maganarta saikuwa idan tana yiwa qaninta qwaya ‘daya tal aduniya magana ko wasa Wanda shi baima ta6a ganin wasa irin nataba da Babu wata dariya ko motsa jiki saidai murmushi kawai….

Tsawon rayuwarsa Bai ta6a ganin rayuwa irinta ‘yarsaba Dan kuwa ko acikin miskilan nata ya wuce tunaninsa Wanda tun yanada lafiya yayita nema Mata magani atunaninsa Batada cikakkiyar lapia ne sbd Sam arayuwarta Batada wani kuzari ko hayaniya,
Bata dariya sai murmushi Dan tunda ta diro duniya haryau data girma Bai ta6a ganin dariyartaba kowama Bai ta6a ganiba sai dai murmushi Wanda Shima dacene duk da bazaka kalli fuskarta kace a ‘daure takeba.,,
Bazaka ta6a cewa ta tsaya ta kalleka so biyuba kallo ‘daya takewa Abu ta sauke ‘dauke Kai wannan ‘dabiarta ne Wanda cikin jininta yake,
Ta fannin magana kuwa duk Wanda zai zauna da ita sai hakuri sbd Sam Bata magana saita Kama Dole Wanda ko dolen a gajarce zata baka amsa Wanda sanyin muryarma kawai ya Isa yasa kaji ranka ya 6aci Dan zakai tunanin bataso amsama bane..

Talakawane sosai ko Kuma ace mabarata duk da tsawon shekaru biyu kenan rabonsu da bara tunda ya kwanta ciwo rigis Wanda Sam basusan ciwon meneba sbd basuda kudin zuwa asibiti abinci madai sai idan qaninta BILAL yabi sauran buzayen dasuke zaune tare bara yake samo musu abinda zasuci wata Rana kuwa saisu yini su kwana Basu ciba sbd Sam ita tsoron mutane take Sam Bata iya fita ko ina tun kafin mahaifiyarsu ta rasu a gidan gurin haihuwar bilal Wanda itada baaban suka rainesa tun tanada shekaru takwas lokaacin harya girma yanxu yanada shekaru bakwai Amma yafita kuzarin Nemo musu abinda zasuci sbd kasancewarsa kyakkyawan yaro Mai shiga Rai Nanda Nan yasamo sadaka yakawo yakoma.

Sam shikansa wani lokacin yakan tambayeta ko Batada lpia sbd ganin kalar rayuwarta harya Saba yagane haka Allah yayita ita.Farace qal asalin buzuwar gske wadda ta ha’da da asalin kyakkyawar baqar fatar bahaushiyar mahaifiyarta sbd baabansu ne kawai buzu mahaifiyarsu bahausar Wanda kyawunta ya ha’dune na asalin buxu da mahaushe saidai tafi ‘debo komai na buzayen.,, +

Sam basuda wata suturar arziki Dan har gwara ita ta ha’da hardana mahaifiyarsu tana sawa,,,,

Kyawunta dayasa ake yawan kallonta yasa kullum jikinta a lullu6e yake har fuskarta da wata tsohuwar lafayar mahaifiyarsu data Bari baqa Wanda Bata saniba kalar baqin ke qara fiddo da asalin kyawunta duk da Rashi da yunwa sun 6oye fiyeda Rabin kyan.

Wata kyakkyawar sarqace ta asalin ‘danyen baqin azurfa aqafarta wadda tun asali itace sadakin mahaifiyarsu harta rasu tana qafarta bayan rasuwar ta ga’deta,
duk inda ta taka sai sautin sarqar ya fita Wanda hakan ke matuqar ‘daukar hankalin wasu mazan idan sunji
Sai wata sarqar a hannunta wainda Bata ta6a ciresu hakama Bata ta6a saka ranar ciresuba saidai idan ta mutu itama acire Mata
A duk lokacinda tayi tafiya babansu yaji sautin kukan sarqar mahaifiyarsu yake tunawa sbd komai Bata baroba na uwar tasu saima ninkawa datayi dankuwa uwarta harta rasu Bata ta6a zaunawa tayi Masa kallon ko minti ukuba kullum daga to sai aa idan yayi magana.

Ajiyar zuciya yasake ahankali cikeda tausayin ‘yayan nasa Dan yasan idan ya rasu basuda madafa wannan kullum shiyake ‘daga Masa hankali sbd itama haryanzu yarinyace shekara goma Sha biyar bazata iya fuskantar rayuwaba duk da baisan me rayuwa ta tanadar Mata agaba ba..

Cikin tsananin sanyin murya yace,

NUR…

ahankali ta ‘dago kanta ta kallesa da manyan fararen idanuwanta kafin ta ‘dauke Kai ahankali tace,

Baabaa kanason wani Abu ne?

Girgixa Kai yayi hawaye na taruwa cikin idanuwansa tana gani tasake lumshe ido tanajin wani ra’dadi cikin ranta Amma batasan yazatayi ta nunaba ahankali batareda ta kallesaba tace,

Yi hakuri baabaa..

Rintse ido yayi hawayen ciki suka zubo
Wani irin ‘daci da ra’dadin ciwo yakeji cikin ransa Amma Babu amfanin bayyanawa sbd babu abinda bayyanawar zai amfana.

Shiru sukayi idanuwanta sukai jajir ta miqe ahanakali ta fito daga kangon office dinda suke kirada ‘daki.

Ahankali takoma defen qofar ‘dakin ta zauna tana gani abokan zamansu suka dawo bara kusan su hu’du kowacce da ‘yayanta harma da mazajensu Amma mazan basanan ‘dayar Kuma mijinta ya rasu.

Tana ganinsu ta sunkuyar dakai ahankali tace,

Sannu da dawowa.

Ko kallonta basuyiba suka wuce suna bede abubuwan dasuka samo..

Lumshe idanuwanta tayi tanajin tausayin kanta na yanda Allah yayita Mara amfani kaman yanda take fada kafin cikin sanyi tace,

Astagfirulla..
Babban gidane dayaji komai najin dadin rayuwa musamman Masu gadi da securities da’aka zuba agidan,

Kwance take cikin lafiyayyan gadonta na cikin bedroom ‘dinta dakomai na cikinsa yake blue sbd shine kalar datafi so.,

Arazane ta tashi sbd mafarkin datayi Wanda inda sabo Yakamata ace tasaba sbd kusan kullum saitayisa tunda tafara sanin kanta.

Dafe goshinta tayi kafin ta miqa hannu ta jawo hular kanta data cire tana goge zufa da’ita….

Meyasa kullum saitayi mafarkin suna kuka na fitar hankali harsuna Aman jini itada wata wadda Bata ta6a ganin fuskartaba saidai yanda suke kukan atare yasa kullum takejin so ‘da tausayin koma wacece Yana shigarta….

ALEEYA….

Taji ankirata..
Da sauri ta juya ta kalli qofar ganin ammynta yasa tasaki ajiyar zuciya ahankali tareda saukowa gadon ta nufi ammyn ahankali ta shige jikinta ta rungumeta batareda tace kamaiba.

Shiru ammyn tayi sbd tafara sabawa da wannan sabuwar ‘dabiar ta aleeya duk da hakanan takasa fa’da Mata mafarkinta na kullum datakeyi.

Cirota tayi daga jikinta tana kallonta tace,

Aleeya kina wasa da addua yanxu ko?

Girgixa Kai tayi cikin ‘son yin Kuka tace,

Ammy wlh kullum inayi.

To naji duk da haka za’aiwa malam halilu magana ya qara dawowa baya a hisnulmuslim dinki..

Dariya tayi kafin tace,

Kai ammy baya Kuma inama laifin tsakiya.

Bayandai za’a dawo yanxu bama Shiba daddynki zai fice dubo tsohon building ‘di’dinsa daya kawosa garinnan inaso nima zan fita zanje gidan anty Nana da Kuma gidan hajiya zaarah tunda ina saka ran kowane lokaci daya gama abinda yakawosa zamu iya juyawa mu koma Dan haka ki shirya muje gidansu anty nanar. +

6ata fuska tayi cikin shagwaba tace,

Ammy Ni daddyna zanbi banason zuwa gidansu anty Nana sbd su siyama fa koyaushe firar maza sukeyi nidai banaso.

Zaro Ido ammyn tayi cikin mamaki da tsoron abinda aleeyar tafada sbd duka duka nawa suke dazasu Fara maganar samari lallai Kam bazataso aleeyar ta kusantu dasu siyamar Suma zatayiwa anty nanar magana ta tsawatar musu
Shekarar aleeya duka duka Sha biyar bazataso tafara sanin wani zance Mai Kama da wannanba.

Ajiyar zuciya tasaki kafin tace,

Yes inaga kibi daddynki zaifi tunda dama can kinfi son fita dashi.

Cikin tsananin murna ta miqe ta fada toilet tana cewa,

Inaji ajikina today issa special day..Blk 43 Dr d saddeeq apt camilleo street famenjs new Jersey 3rth January, +

‘daure da farin towel yafito daga bathroom ‘din dake cikin ha’dadden lafiyayyan room ‘dinsa farar fatarsa da mur’dadden jikinsa na cikakken qqaqqarfan namiji da hutu ya ratsa Sai qyalli takeyi.. 1

Tsayawa gaban mirror yayi yana goge gashin kansa da qaramin towel yaji anrungumosa ta baya ya lumshe manyan fararen oily eyes ‘dinsa tareda ‘dago Kai ya qura Matasu ta cikin mirror.. 1

Murmushi tasaki sonsa da qarin son sake samunsa Yana sake shigarta tareda dawowa gabansa tana shafa faffadan qirjinsa ahankali cikin sigar Jan hankali.,

‘dauke gira ‘daya yayi tareda bin hannun nata da kallo wani miskilin fitinannen murmushi na saukar masa.

Ba zato yaji hannunta cikin towel ‘dinsa ya ‘dago ya kalli cikin idanuwanta tareda Jan numfashi.

Zame towel ‘din tayi ta jefar tareda ha’de qirjinta da nasa wani malalacin murmushi yasaki tareda matseta jikinsa Yana shafo gefen fuskarta cikin nasa salon da qwarewa ta wannan fannin ya matso da fuskarta Yana shaqar numfashin dake fitowa hanci da bakinta kafin ya hade bakinsu.

Fincike towel din jikinta yayi tareda ‘dagata sama still bakinsa na cikin nata ya jefata gado yana cigaba da juyata son ransa.

Qanqameta tayi cikin wani irin Jin Dadi sbd qwarewarsa da baiwarsa ta iya gigita kowace irin mace a wannan fannin.

saidata murzu iya murzuwa agurinsa kafin suka fara maida numfashi cikin Jin Dadi da kwanciyar hankali duk da wannan shine round na kusan uku kafin safiyar.

Idonsa ne ya sauka kan agogon dake kan bedside drawer ya zabura ahankali a ‘dan rikice yace,

Oh God,,,tareda miqewa ya sauko gadon ya nufi toilet cikin sauri yayo wanka yafito a gaggauce ya shirya cikin dark blue suit ya nufi gurin takalmansa ya ‘dauko ‘daya yazauna bakin gado yasaka tareda ‘daukar wayoyinsa da car keys ya Ciro hundred hundred dollars cikin wallet dinsa dabaisan iyakarsu ba ya aje Mata a gefen gado ya nufi qofa da sauri Yana ‘daura agogon diamond na Yazole a hannunsa ya ‘dan juyo ya kalleta fuska a ‘daure kamar ba yanxu ya gama gurzartaba yace,

Make sure by ten kinbar gidannan before my crazy girlfriend or her stupid ilmannered maid su shigo su ganki coz ba ruwana you’ll be the one in hell.

Ficewa yayi da sauri a qaton palonsu ya ha’du da sufyaan daya fito kitchen sanyeda three quarter black da armless shirt riqeda mug, cikeda thick tea aciki Mai zafi sai turiri yake.

Kallonsa yayi cikeda mamakin ganin baiyi Shirin zuwa office ba gashi yasan yau sunada tiyatar dazasuyi atare a asibiti
Bu’de baki yayi zaiyi magana sufyaan ‘din ya katsesa da cewa,

I know, i know,,, so please just don’t say anything zanyi sauri na qaraso da wuri before time..

Kallon qofar bedroom ‘din sufyaan din yayi Dan ya tabbatarda macece aciki Amma ai yasan koma wacece she’s not special or different from sauran matan dazata saka sufyaan ‘din qin zuwa aiki in Time.

Juya tea ‘din da spoon sufyaan yayi Yana lumshe ido cikin wani salon nuna zallar garabasar daya kwasa a daren jiyan yace,

She’s virgin man.. and I didnt go easy coz I couldn’t control my self from the…….oh my am telling you man she’s damn hot sweet and….

Qaramin tsaki dawood din yasaki tareda juyawa ya nufi qofa Yana cewa,

Banza da kullum saiyayi santin mace,.’daga murya sufyaan ‘din yayi yace,

Eh naji kaima ai sbd haryau bakasan da’din virgin bane but trust me zaka ce nafada wata Rana.
Stupid””dawood yafada Yana ficewa daga palon daidai Nan Maid din saraah ta iso bakin qofar palon apartment nasu ‘dauke da qaton tray ta gaidasa idonta akan qofar daya fito kamar idon zai fado tace,

breakfast sir.

Ko kallo Bata ishesaba ya nufi mota cikin turanci Yana cewa,

Take it back.

Harya tada mota yaga tana qoqarin shigewa palon ya ‘danna horn da qarfi cikin takaici.

Waigowa tayi cikin ‘daure fuska
Ya nuna Mata hanyar komawa ta juya jikinta na rawa sbd yanda Sam baya sakin fuska ko ‘daukar iskancin kowa ko kadan Dan ko uwar ‘dakin tasu data ‘daukesu aiki tsoro da shakkarsa take baresu.
wucewa tayi tana ‘dan satar waiwayen qofar part din nasu dan tasan Sarai baza’a rasa mace cikin part ‘din ba Kuma har cikin ranta takaici takeji idan tagansa da Mata sbd Taya uwar ‘dakinta kishi datakeyi.

Saidayaga shigewarta qofar dazata sadata da apartment ‘din saraah kafin ya taka motar ya fice da gudu Dan dama tunda yafito security ya wangale Masa gate.

20 minutes tayi ahanya kafin ya Isa babbar asibitin dayake aiki a matsayin babban consultant likitan Mata wato gynecologist..

Yana Isa harabar asibitin yayi parking saidayayi kusan wasu mintuna hudu Yana waya da mum dinsa cikin kashe murya kafin ya fito ya nufi office dinsa Yana kashe dukkanin wayayinsa tunda yafito mota tundaga kan sauran doctors wainda basukai matsayinsaba da nurses harma da sauran ma’aikata ke qarasowa suna sharara Masa gaisuwa Yana amsa da hannu harya Isa office dinsa da’aka rubata DR DSD ( CONSULTANT DAWOOD SIDDEEQ DAUDA) ya shige….

Ko zama baiyiba ya duba diamond bylgari watch ‘dinda ke daure a hannunsa yaga 20 minutes to theater dazasu shiga sai kawai ya shige shirya cikin kayansa na theater ya fito nurses biyu na biye dashi rungume da files sai Dr sufyaan daya qaraso cikin nasa kayan tiyatar da sauri Yana kar6ar file ‘din da Dr Andre ke miqo Masa dukkaninsu fuskokinsu da hankalinsu na tattara ga aikinsu bazaka ta6a kallonsu kace gwanayen neman Mata bane kamar yanda suke gwanaye a aikinsu,, 1

Sun dauki aikinsu da mahimmanci matuqa sbd yanda a hospital suke tsananin Jan girma da class dinsu musamman Dr dawood ‘din da matuqar batare yakedasu sufyaan da Sameer ba bazaka ta6a ganin ko sakewar fuskarsaba bare kayi tunanin zai iya kallon mace harya nemeta.,

Sam ko nurses ‘dinsa baya sakewa sbd ‘daukar girma class uwa uba ego dayake dashi akan ganin matsayinsa kyawunsa da kudinsa Wanda yake ganin shidin Dole komai girma,kyau,class,gata,ilimi da dukiyar Mace Dole ta kallesa ta qara kallonsa duk da arayuwarsa baisa ranar dazai yiwa Mata kallon abin so ba ko burgewa bayan kawai abiya buqata dasu abiyasu sbd su ‘dinne basu ‘dauki kansu da darajaba,,,

So da dama idansu sufyaan na santin haryanxu akwai matanda suke virgin ma’ana Basu ta6a yin sex ba yakan kallesune kawai sbd a iya hange da iliminsa baya tunanin akwaisu Koda akwaisu Yana tunanin sai qasar dad ‘dinsa wato Nigeria Wanda Suma yanasa ran duhun Kaine da rashin ‘yancin Kai dasuke ba ‘yayansu sbd yayi zaman kusan shekara ‘daya acan Bai wani Jima da dasowaba sbd iyayensa dasuka koma can duk da bawai sun koma dindindin bane Amma a gigice yadawo sbd bazai iya rayuwaba a qasar Sam.,

Aryuwarsa baisan damuwa ko baqin ciki sbd ya taso tareda iyayensa duka biyu uwa da uba,
An haifesa cikin gata da daular dukiya yataso cikin tsananin gata da soyayyar iyayensa musamman mum ‘dinsa data ‘dauki so da kulawar duniya ta ‘dora akansa duk da yanada qani TAHEER Wanda suke kamar wasu abokai sbd rashin tserewarsu dakuma yanda taheer ‘din yafisa zama matured and responsible man Dan kuwa shi lawyer ne Mai zaman kansa Kuma Wanda ke tashe a fagen lashe kowane irin case sbd dagewarsa da dukkanin time ‘dinsa na rayuwarsa daya jingine a aikinsa yasa ko zama Bai cikayiba kullum meetings da clients ko sharia trip.,Yanayin aikinsa da ganin qwazonsa da Kuma sunan dayayi a iya aikinsa yasa gabaki ‘daya dukiyar gidan da takardun duka kadarorinsu Yana hannunsa sbd ataqaice dai kusan shine lawyern mahaifinsa,mahaifiyarsa da brothernsa dawood.

ASSIDDEEQ DAUDA tsohon chief judge ne daya zauna manyan kujeru na manyan muqaman alqalanci a qasar Malaysia tsawon lokaci kafin ya aje Dan girma da manyanci dayazo masa,

Ya taka muqaman ne bisa mahaifin matarsa faraah Wanda yake former minister of justice na qasar Kuma babban Mai fada aji..

Faraah da iyayenta ‘yan asalin qasar ne Wanda asalinsu are not Muslims saidai dayake basa rayuwar takura Kai tunda ta hadu da Assiddeeq ta gabatarwa da iyayenta dashi Basu takurata ba ganin Shima Yana sonta kamar yanda takesonsa sai kawai suka barsu suna soyayyarsu,

Saida suka kammala karatunsu dadynta ya Samar Masa aiki a babban guri Mai tsoka kafin sukai aure anan qasar daga baya ya taho da ita Nigeria gurin mahaifiyarsa sbd ita kadai ta rage masa akai musu nasa kalar auren amatsayinsa na musulmi.,

Bayan anyi komai Basu wani Jima Nigeria ba suka koma tareda ammynsa sbd kaita wani Muslims old age home data Dade tana fatan zuwa sbd samun damar bautawa ubangiji sbd anci mulki da iko lokacin mijinta na raye yanxu kuwa tsufa yazo ba miji ba ‘da sbd tana shekara koma fiye Batasa ‘dan nata a idoba shiyasa tace yakaita old age home inda tsofi sa’anninta suke musamman ma aminiyarta tun ta yarinta tana can.

Bayan aurensu da tsawon lokaci yasamu cigaba da dama tuni Shima yafara zama multibillonaire a qasar sbd tuni MR DAMIEN OLIVER ya aje aiki yabar Masa ragamar komai.

Faraah nada cikinta na farko ta musulinta Koda ta haihu ta haifi ‘da ammy datazo takanas dan ganin jikanta na farko aduniya da kanta tace asa Masa dawood wato sunan mijinta mahaifin siddeeq ‘din,

Tun bayan haihuwar dawood kowa ya ‘dauki tsaninin soda qauna suka ‘dora Masa sbd shikadai suke gani as the only little one dasuke dashi.

Dawood is 3years old mum ‘dinsa tasake haihuwar wani yaron still ammy tasa Masa suna taheer sbd har time din Bata koma old age home ba tun haihuwar dawood sbd tanason tabasa tarbiya da kishin qasarsu da addininsu.

Bayan haihuwar taheer da four years dad ‘din faraah ya rasu Wanda su duka sun girgixa matuqa
Bayan komai ya lafa suka tattara suka koma Miami inda dad yafara bude companies da dama..

Mum din faraah Mrs Damien ta musulinta tun bayan rasuwar mijinta sai ya zamanto itada ammy da Nanny’s ‘dinsu dawood suke kula da tarbiyar yaran sbd daga mum har dad din ba zama sukeba sbd aiki musamman ma ita da yanxune take matsayin justice.

Lokacinda su dawood suka girma suka Kai munzalin shiga high school lokacin Mrs Damien da ammy suka koma old age home tare sbd Sam gidan kullum bamai zama dagasu sai maids Masu aikin gidan.

Mum irin manyan high class madams ‘dinnanne da bazaka kalleta kace ta aje manyan handsomes samari ba sbd kyan jikinta da yanda take maintaining ‘dinsa kasancewarta tun farko Yar gayu,
Sam mum Bata yarda tasa Abu Mai sauqi ko arha ajikinta sbd takasance mace Mai tsananin izza da son komai nata ya zamto higher level tun kuwa daga kan mutanen dazatai muamala dasu har kan aikinta da komai nata,,

A aladarta ta tsananin tsaftarta da gayunta ko komai nata tafison tayi order nasa direct daga company
Sannan a rayuwa ba komai zakai Kai Mata daidaiba Wanda shiyasa Sam ko na qasa da ita Basu cika Jin da’dinta ba sauqinta ‘daya dasuke ji Sam Batada rowa Wanda ita idan tayi kyauta jitake wani sabon girma da iko na shigarta na ganin itace fa koyaushe asama saidai a risina mata.

Duk duniya ba abinda tafiso kamar baby boy ‘dinta dawood Wanda Sam rayuwarta takasa hada sonsa da komai Kuma shikadaine ya Isa yasata Abu tayi,
Taheer kasancewar yafi dawood din zama matured kamarma shine babba yasa Sam baidamuwa da yanda take fifita dawood din saima tausayi dasuke basa sbd ganin yanda gabaki ‘daya dawood ‘din yazama Mama’s boy Sam baison hayaniya da yawo Koda da friends ne kullum Yana jikin mum tana tarairayarsa Wanda Sam shi Wanda Sam shi dad ko ajikinsa sbd dukkaninsu rayuwar turaice ke yawo a jininsu. +

Kusanma dawood din ya biyo mum din harya zarceta gurin high level classy life sbd shi hatta shower cream nasa da duk abubuwan amfaninsa takanas yake bada ordernsu direct from the company shiyasa komai nasa is unique and classy
Sbd dawood mum tayi retire ta aje aiki sbd Sam bai yarda da kulawar kowaba sai ta mum ‘din ko breakfast Dole itace take Masa yanda ammy tasaba yi Masa sweet sweet Nigerian dishes, 1

Shekararda dad yayi retire ashekarar suka koma Nigeria zuwa time din tuni dawood ya kammala karatunsa Yama Fara aiki a new Jersey shida friends dinsu su uku 2 are from Nigeria one is an American Wanda tun primary sukai tare wato Jasper inda suke zaune cikin wani qaton apartment suna hole rayuwarsu sbd ba Wanda yakeda niyya ko tunanin wani Abu aure.
Dr dawood,Dr sufyaan,Dr jasper and dr maska sun kasance the hottest young billionaires doctors dake tashen class,kyau gata wayewa tareda kwarewa a fannin iya neman Mata sbd sun kasance irin mazanda kowace mace zataso tasamu.

Lokacinda su mum suka koma Nigeria Taredasu ammy suka koma gaba ‘daya harda taheer daya koma can Shima harya Fara aiki sbd shikam ba laifi qasar tamai Shima Saida yayi kusan 1 and half year kafin yadawo Wanda Sam jiyake he just can’t even think or imagine living in qasar….wheewww I’m damn tired man yafada Yana shiga office dinsa sufyaan na bayansa Shima a gajiye ya zauna bayan ya ‘dauko robar ruwa a fridge din office din yace,

Thank God it was a successful operation after doguwan wahala.

Lumshe manyan fararen oily eyes dinsa yayi Yana kwantarda kansa jikin couch ‘din office dinsa dayake zaune ahankali yace,

I need the hle night alone Dan na huta sosai yau…

Murmushi sufyaan yayi tareda miqewa sbd Kiran Jassper daya shigo wayarsa yace,

Let’s go Jass ya iso.

Miqewa yayi tareda daukar wayoyinsa da sauran kayansa a gajiye ya fito Yana lumshe ido suka nufi ha’daddiyar bughatti car din Jassper da shikadaine baiyi tiyata ba yau Bai tattareda gajiya kamarsu Dan dama sumtimes hakan sukeyi kowa zaizo cikin ha’daddun motarsa Amma idan sun tashi kusan duk Wanda Bai tareda gajiya shizaijasu sukoma gida amotarsa sauran motocinsu kuwa saidai drivers na asibitin su kaimusu gida.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]