[Advertisements⬇️]

AMININ MAHAIFINA CHAPTER 14 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

AMININ MAHAIFINACHAPTER 14Ranar Talata bamu yi exams ba sai ranar Laraba. Misalin karfe tara muna cikin exam hall muna jiran invigilators su shigo, sanye nake da doguwar riga dinkin Stella sai mayafi dana yafa mai yalwar fadi, fuskata daga hoda sai kwalli ko janbaki ban shafa ba saboda a sukwane na fita ranar don na kusa makara. Much to my surprise na tsinci Abbu cikin invigilators din, idanunshi suka zagaye ajin har sai da suka lalubo ni ya sakar min kyakkyawan murmushin shi da sai da yasa naji gwiwoyina sun sage, a dan kunyace na maida mishi martani tare da sadda kaina kasa ina tuno yadda muka rabu dashi a jiya da yamma da yazo wajena, yana insisting lallai sai munje ya nuna min gidan da zan zauna ni kuma nace mishi ba sai na gani ba, da yaga alamun ba zan bishi ba sai ya fara min abubuwan nashi da har lokacin kwakwalwata ta kasa daukar su ko sabawa dasu, da kyar na samu na zame na tsere
Lokacin dana sake kallon inda yake hararata yake yi kasa-kasa fuskar shi na nuna bacin rai, gabana ya fadi, crap! Me nayi? Ko dai tun laifin jiya ne har yanzu yake fushi dani don naga tun daga lokacin bamu sake waya ba kamar yadda bai turon text ba duk da cewa dai na tura mishi wani yau da safe amma bai turo min da reply ba. Aka fara raba mana answer booklet ya dauki wasu yayi row din dake gefenmu na dama, yadda na bishi da ido haka na tsinci idanun yawancin ‘yanmatan ajin suna bin shi da kallo, naji wani takaici da bacin rai yana lullube ni, meye nasu na Kalle min miji? Sai naji kamar in tashi in fidda shi daga cikin ajin, na dai daure ban yi anything silly ba har ya juyo ta bangarenmu. Yazo saitina ya tsaya yana kokarin ciro booklet din, kamshin turaren Armani Code ya mamaye wajen naja na shaka har da lumshe ido, a hankali nace mishi “Abbu good morning!” lokacin daya danyi leaningakan desk din da nake ya ajiye mun takardar, “me yasa kika fito da wadannan kayan a jikin ki?” ya fada muryar shi na nuna bacin rai da distaste, na kalleshi tare da kallon kayan jikina, saboda Allah meye aibun su? Gyalena mai fadi ne ya rufe duk inda ake bukatar ya rufe, kafin in samu ince wani abu ya kara gaba zuwa ga desk din bayana, na danyi shrugging slightly na fara rubuta sunana akan takardar.
Ana bamu question paper na fara rubutu, Abbu ya jingina da window din gefenmu na hagu saitina, duk da ban daga kai na kalleshi ba amma nasan da cewa idanuwanshi a kaina suke don kuwa naji su, don haka zan iya cewa jarabawar ranar cikin takatsantsan nayi ta, ko motsin kirki ban yi ba. Ranar ni na fara submitting, ban tsaya jiran komi ba na bar hall din a tunani na zan iya tsere mishi kafin ya fito, sai ganin shi nayi ya wuce ta gabana, “follow me!” kawai yace yayi wajen parking lot, na sadda kaina kasa in surrender, nabi bayan shi na bude motar daya riga ya mata key na shiga, ina zama ya juyo glaring at me, “na tambaye ki baki bani amsa ba, nace me yasa kike yawo da wadannan kayan?” na daga gyalen jikina ina kallonshi, “naga fa gyalen bashi da matsala babba ne, kuma ya rufe min jiki meye marabar su da hijabi?” yaja motar muka tafi, “it’s transparent for Goodness sake, ki duba kiga dazu da muka shigo, hannu da wuyanki duk a waje suke. Maza nawa na gani suna kallonki kina a matsayin mata ta?” juyawa nayi na kalleshi, ashe muna taya daya, “daga yau na hana ki saka gyale ko wani iri ne, be it mai kauri ko transparent I don’t care, wear hijab wadda zata dinga rufe miki dunduniya!” na zaro ido, “to ai ni hijabai na gabadayansu ma basu kai biyar ba kuma da guda biyu kadai nazo makaranta” ya daga baki cikin mamaki kamar zai yi magana sai kuma ya rufe bakin, ya sake budewa yace “akwai hijabai a cikin kayan lefenki, idan kin tare ma zan dinka miki wasu for now sai kiyi amfani da wadanda kike dasu kafin ki koma” nace “Abbu….?” ya juyo ya kalleni fuskarshi na nuna rashin jin dadi, “r u arguing with me Nafeesah?” nayi saurin girgiza kaina, “to meye?” sai kawai na sake girgiza mishi kai, muka cigaba da tafiya ba tare da munyi magana ba, wani tunani ya darsu a raina. Na hade fuska tare da turo baki nace “to in dai haka ne sai dai kaima ka daina sa irin kayan daka sa yau, Allah kadai yasan iya adadin matan da suka dinga kallonka yau, kai duka ‘yanmatan ajinmu were looking at you with interest in their eyes” daidai lokacin yayi pulling motar zuwa cikin lot din dake gaban hostel dinmu yayi parking, ya kwashe da dariya cikin farinciki da wani abu mai kama da humor, na kura mishi ido ina kallonshi relieved and amazed, at last! Yayi more than murmushi.
Sai da yayi dariyar ta ishe shi sannan ya kalleni, “ni kuma meye aibun tawa shigar?” Armani pants ne a jikinshi da open neck top, ire-iren kayan da suke boye shekaru da girman da yayi su fito da xallan yarinta da kyawun shi. Na turo baki ban amsa ba, hannuna ya kamo ya rike a cikin nashi yana caressing, “girl, Ashe kema kin iya kishi? Ni indai nine baki da matsala dani, ki fadi duk irin kayan da kike so in dinga sawa zan sanya babu musu, m all urs Amour” na sadda kaina kasa ina blushing, na duba naga duk cikin irin kayan da yake sawa babu wanda basu mishi kyau, sai na kauda hirar na fara kokarin janye hannuna daga nashi wanda ya fara sa min tashin tsigar jiki. Ya kalleni fuskar shi a dan hade, “na kula baki son ina rabar ki kwana biyun nan Nafeesah, mai yasa?” duk da maganar da yayi sai dana janye hannuna daga nashi na saka su cikin gyalena, shiru nayi kawai, to in ce masa me? Ina jin kaina kamar wata traitor ko mai laifi idan ya taba ni, I’m feeling awkward idan ya taba ni, feelings ne da ban saba jinsu a cikin rayuwata ba hakan yasa na fara having second thoughts, ko dai don yana abokin Dad ne na kasa sakewa da Al’amuran shi? Ya kuta kawai, “zaki gama kewaye-kewayen ki ne ma ki dawo hanya Nafeesah, ina so zan wuce gida yanzu, me kike so in kawo miki anjima?” nayi saurin girgiza kaina, “babu komi” frankly speaking zan fi so ace ba ma sai ya dawo ba, ya tabe baki “sai wani guduna kike yi fa, kin manta cewa komi wayon amarya sai an sha man ta?” na kalle shi, wani murmushin mugunta ne akan fuskar shi da yasa naji wani tsoron shi yana shiga ta, ya kamo hannuna duk nokewar da nake yi sai da ya kai bayan hannuna saitin bakin shi ya sumbata, nayi saurin bude motar na janye hannuna na fita, sai dana fitan sannan na leka ta tagar motar nace “Abbu a gaida su Hafsy, sai anjima” yayi murmushi kawai yana gyada kai, na juya da sauri na wuce.

A haka har muka gama exams dinmu, ina ta kauce-kauce yayin da Abbu bai fasa abin shi ba sai ma abubuwa da suke karuwa kullum. Kwana biyun nan ya dameni akan wai shi fa lallai sai ya kaini naga gidan mu, ni kuwa nasan muddin na taka kafa naje gidan to sunana sorry, kila warning din dasu Ni’imah da Firdausi suke yi mun na in daure kar in tare da ciki ya tabbata. Tun a ranar da nayi exams dina na karshe na fara hada kayana, na kira Daddy a waya yace washegari zai turo a zo a dauke ni saboda ranar sai da yamma muka gama exams din, nace mishi don Allah ya turo direban tun da safe mu tafi, a matukar kagauce nake da in tafi gida, I have to clear my thoughts and brain kuma nasan gidanmu ne kawai zai bani wannan natsuwar, ga kewar su Daddy da nake yi kamar me, hakika nayi kokari, watanni biyar rigis ba tare dana saka su a cikin idanuna ba. Na kira Ramlah da tace tace tare zamu wuce Kadunar da ita na sanar da ita, tace zata shirya sai mu biya ta gida mu dauketa nace to muka yi sallama.
Karfe tara na safe kayana sun kammala waje daya, nayi wanka na shirya cikin riga da siket na atamfa, hijabin data zame min mayafi na ajiye a gefen gado a linke, na dauki wayata na fara buga game don ya dan kashe min time kafin direba ya zo. Kiran Abbu ya shigo wayata, gabana ya fadi sosai gabadaya na manta bamu yi sallama dashi ba saboda doki, na dauki wayar na kara a kunnena, “meet me at my office” kadai yace ya kashe wayar, na bi wayar da kallo kamar ba zan tashi ba, can kuma na mike na saka hijabina, Firdausi bata dakin taje rubuta jarabawa don haka na rufe dakin na fita. Zaune na same shi akan kujera fara dake a tsakiyar ofishin da alamun jirana yake yi, na maida kofar na rufe na zauna akan kujera dake fuskantar shi na zauna, fuskar shi sam babu yabo babu fallasa hakan yasa naji sanyin jiki ya mamaye ni, Allah dai ya taimakeni muyi rabuwar aminci yau don na kula da cewa rigima yake ji yau. Murmushi nayi a sanyaye nace “Abbu ina kwana? Ka tashi lafiya?” yace “ke zan tambaya ai, amma ni kin tambayeni tashina lafiya bayan kina neman hana min abinda yake nawa ne?” na dan zamo daga kan kujerar da nake zaune nace “don Allah Abbu kayi hakuri, idan kayi hakuri ma duka kwanaki nawa suka rage kafin a kawo maka ni gabadaya kayi yadda kake so dani?” ya lumshe idanun shi tare da maida kanshi ya jinginar da kujerar da yake zaune, “I tried Nafeesah, I really do. But I can’t anymore, all I ask for u is just half an hour, please ki zo muje gidana, I so badly want you Nafeesah!!” na kura mishi idanu, idanun shi a lumshe suke har lokacin, Abbuna ne a gabana yake rokona, da ace zan iya da na mishi abinda yake so domin samun farin cikin rayuwar shi, sai dai ba zan iya din bane, I’m still not ready for it. Mikewa tsaye nayi a hankali, hanya mafi sauki in bar mishi ofishin kafin in kara bata mishi rai, nasan ba zai fasa tambayana ba, ni kuma in yaci gaba da tambaya it’s either inyi abu daya cikin biyu; ko dai in sallama mishi ko kuma inyi denying wanda duka cikin biyun babu wanda zai mun dadi, nace “Abbu don girman Allah kayi hakuri, kayi hakuri na wata da watanni ma balle na en kwanaki? I am very sorry, zamu wuce Kaduna yanzu don Allah kar kayi fushi dani Abbu…” na juya cike da sassarfa zan fita. Ban ji lokacin daya tashi tsaye ba sai maganar shi dana jiyo daga bayana, “Please Mana Nafeesahh!!” Ya fada cikin wata irin murya wadda ta narke cikin tsantsar qauna da soyayyah. Kaina na fara girgizawa a tsorace, “Bazan iya ba. Kai fa Abokin Babana ne please kayi hakuri, bazan iya ba wallahi!!” idanunshi ya zuba min wadanda suke a lumshe kamar na mashaya, dama a yawancin lokuta a haka suke, sai dai na yau sun banbanta dana sauran lokutan. Na yau cike suke da wata irin soyayyah, zallar qauna, pure lust, I can sense them radiating from his body. Muryarshi ta kara yin kasa sosai “ina tunanin mun riga da mun gama wannan maganar Nafeesah? saboda Allah mutane nawa kika san sun yi aure irin namu kuma suna zaune lafiya har ma da zuria a tsakaninsu, ko a cikin tarihi ki duba fa, Sayyadah Aisha RTA diyar Sayyidina Abubakar ce wanda ya kasance babban Amini makusanci a wajen manxon mu (S. A. W) nasan kin san da haka ba sai na sake gaya miki ba” maganganun shi haka suke sai dai na kasa convincing kaina da zuciyata” nace “yeah, I know.., I just need time please kayi hakuri” ya girgiza kai, “na gaya miki ba zan iya bane Nafeesah, it’s not as if wani sabo ne nake shirin aikatawa” Kai na ci gaba da girgizawa hawaye na sauka akan kumatuna, ya zanyi da raina da rayuwa ta ne ni kam? Ban san ya aka yi ba sai ganin shi nayi a gabana, kafin inyi wani yunkuri yayi pinning dina da bangon ofishin, “I love you Nafeesah….I want you n I know you do, u just don’t want to admit it!” “no…. No… I… I” na fara fada cikin in’ina kafin inji wasu tausasan lebba sun hana ni karasa maganar. Lebena na kasa ya kamo ya fara tsotsa cikin wani irin passionate kiss, a hankali na lumshe idanuna tare da kamo nashi leben na sama nima na fara tsotsa, ya saka hannu daya ya zagaya dashi ta kuguna ya kara matso dani zuwa gare shi tare da zura harshen shi cikin bakina muka fara hadamammen kiss, ihu ake a cikin kaina da kwalwata, “Ya Allah! What am I doing? He’s my father’s Friend for Heaven’s sake!! Cewar wani sashe na zuciyata, but hell! I couldn’t let him go, sai ma kara rike shi da nayi tsam…. 3

Karan da wayata ta dauka baby kakkautawa ne ya dawo da hankulanmu cikin ofishin, a matukar kunyace na janye jikina daga nashi yayi saurin janyo ni ya rungume a cikin kirjinshi, duk yadda naso in kwace abin yaci tura ina ji ina gani haka na Hakura har wayar ta gama burari ta katse, numfashi yake saukewa a hankali har ya dawo cikin natsuwar shi, ya hade goshina da nashi yana kallona ni kuwa naki hada idanu dashi, murmushi ya saki a hankali, “kin gani koh? We need each other Nafeesah, amma kina hana kan ki abinda zuciyar ki da gangar jikinki ke so, why?” a hankali na daga baki nace “kayi hakuri” ga mamakina sai naji yace “na hakura Nafeesah” na daga kai cikin mamaki na kalleshi, ya daga kafada, “to me zan yi idan ba hakurin ba? Kin san cewa ba zan taba tursasa ki ga yin abinda baki so ba, zan jira har a kawo ki din sai dai kada ma ki roke ni wani abu a wannan lokacin don ba zan ji ki ba…., muje in kaiki hostel din” ya zari makullin mota ya fita, na bishi da kallo ina murmushi, saukin kan Abbu yana burge ni sosai da sosai, Allah ya yaye min fargabar nan da wasi-wasi da nake ji ko na samu na faranta mishi rai kamar yadda yake kokarin faranta min. Na bi bayanshi na fita daga ofis din ya rufe muka tafi. Koda na duba miss call din da aka min direban da daddy ya turo min ne, na kira shi ya sanar dani ya iso nace mishi gani nan. Koda muka isa mun dauki lokaci muna hira da Abbu kafin muka yi sallama dashi akan cewa zamu yi waya, ya kama hannuna yayi kissing bayan hannun kamar yadda ya mayar dashi al’adar shi tun ina jin abun banbarakwai har nazo na saba da hakan yace “m gonna miss you baby” nace “me too” a kunyace, yayi murmushi, da haka yaja motar shi ya tafi. Firdausi ta taya ni dauko kayana muka lode su a bayan booth, daga nan muka yi sallama da ita ita sai nan da kwana biyu zata gama nata exams din, na shiga mota direba yaja muka wuce Kaduna bayan mun dauko Ramlah. Karfe biyu a Kaduna ta mana, da gudu na shiga gidan ina ihun kiran Mommy, ta fito daga kicin tana goge hannunta da kicin towel, na tafi da guduna na rungumeta ina murna, ta janye ni daga jikinta tace “ke tafi can ni, wannan yarinya ban san yaushe zaki girma ba ni kam” na kara shigewa jikinta ina tsalle abina, sai da Ramlah ta shigo sannan na sake ta. Suka gaisa da Mommy kafin muka shiga dakina muka yi wanka muka yi sallah, sai a lokacin na kira Abbu na sanar dashi mun sauka, nan muka danyi hira muka yi sallama sannan muka fita falo muka ci abinci. Da yamma Daddy ya dawo muka sha hira da murnar ganin juna, ko da dare ma dai hirar muka yi har sai da dare yayi sannan na musu sallama na wuce dakina. Washegari Anty Uwani tazo ta daukemu ni da Ramlatu muka tafi gidanta bayan ta sa mun dauki kayan sawar mu kala biyar, ban san me zamu yi ba na dai ji suna maganar Gyaran jiki ita da Mommy ni kam ban maida hankali wajen sanin lallai sai na san me zamu yi ba.Kwanan mu biyar a gidan Anty Uwani. Daki guda aka killace mana ni da wata mata, babu abinda take yi sai gyaran jiki dana fata, hatta da ruwan wankana ya koma na turare, man shafawa na turare, hodar da zan shafa, turare. A iya kwanakin nan ban taka ko kofar gida ba, kullum ina daki, daga matar nan ta fita da wannan abin daga dakina na ci sai ta shiga da wannan abin na sha. Aikin kenan. A kwana na shida ne ta min wani irin wankin gashi wanda yasa gashina yayi wani irin taushi mai ban mamaki, ya kara kyau, tsawo da baki. Washegari kuma aka min lalle, a ranar da yamma da muka yi video call da Abbu baki ya bude yana kallona kamar wata sabuwar halitta, koda yake kusan kamar an canza ni dinne, fatata ta kara haske da laushi da komi ma, ni kaina idan na kalli kaina a madubi sai nayi mamakin canzawar da nayi balle Abbu. Hirar ranar dai base on tambayoyin yadda aka yi na canza haka muka yi ta. Sai da Anty Yagana wadda take min gyaran jiki ta shigo tasa muka yi sallama, ina kashe wayar ta hau ni da fadan bata hana ni yin video call da kowa ba? Ni dai baki na turo gaba na kauda kaina gefe, kwanaki shida rigis ba tare dana saka Abbuna a ido ba ji nayi kamar numfashina zai dauke saboda kewar shi shi yasa na ture gargadinta gefe na danna mishi kira, murmushi nayi ina jin yadda naga ya rikice daya ganni. Ta dai gama fadanta ina sauraronta, sai data gama ne nace mata tayi hakuri, sannan ne ta fara gudanar da aikin daya kawo ta
Washegari da safe muka yi sallama da Yagana saboda ta gama aikin da zata yi, ta tafi cike da alkhairan da Mommy da Anty Uwani suka mata, ni kuma na sha shawarwari da koyarwar abubuwan gidan miji da rayuwar aure. Da yamma aka yi sitting a gidan Anty Uwani. Mata ne zalla a wajen yawanci kawayen su Mommy ne, sai kadan daga relatives da abokai na da muka gaiyata. Anty Shafa ce ta shirya ni, sai a lokacin nasan tazo ashe kwananta biyu a Naija. Ta shirya ni cikin wasu riga da zani da wani farin yadi mai holes a jikin shi, sai aka min nadi da blue din tie, blue din takalmi high heel, blue purse, blue mayafi karami data dora shi akan kafadata. Fadar irin kyawun da nayi ma bata bakine. Haka dai aka gabatar da bikin cikin salama komi ya tafi yadda aka tsara, anyi ciye-ciyen abinci, snacks da lemu kamar ba gobe, bayan nan su Ramlah suka fita suka kwashi rawa har da su Anty Shafa, koda aka nemi da in fita filin rawa ki nayi, na kara hakimcewa akan tuntu inda aka yi shirin kayan gargajiya kamar irin bikin nan na gidajen sarautun da, sai da Hajiya Amina kawar Mommy na tazo ta fiddo ni sannan na tashi naje filin nayi tsaye, dama can ni ba gwanar rawa bace balle kuma a gaban manyan mutane irin wannan kuma ace bikina ne? Taya ma zan iya rawa?? Nan mutane suka fara sauke ruwan naira a kaina sababbi kamar wasu takardu, ba shiri DJ ya maida sautin wakar dake tashi zuwa Ruwan Kudi, taro dai yayi lafiya lau Alhamdulillah, da yammaci likis aka watse taron.
Anty Shafa ta dauke mu a motar ta zuwa gidanmu, ai sai a lokacin take fada min cewa wai washegari za a kaini Kano. Na zuba mata idanu na a sanyaye cikin sanyin jiki kamar wadda aka zare mata laka, har muka isa gidanmu ban iya cewa komi ba. An sake fente gidan ya dawo kamar sabon gini, a farfajiyar gidan canopies ne an shirya su kashi-kashi ga kuma kujeru irin wadanda ake yi na tyres a shirye, hasken bulbs jajaye ya kawata wajen sosai da sosai, ina ji Ramlah tana tambayar Anty Shafa abinda za ayi tace wai shi kuma Dinner ce kawai su Mom da Dad suka hada min, a raina na girgiza kai ina jinjina bidi’a irin ta su Mom. Yan uwa suka wa motar da muke caa kamar kiyashi da kyar muka fito daga cikin motar, kai tsaye dakin Mom dina aka wuce dani, mutanen dake ciki basu wuce biyar ba duk abokanta ne sai Nene matar kawu Hassan da kuma Anty Asma’u matar Kawu Ali.
Mommy ta taso ta rungume ni, ina ji na a jikinta kawai naji na saki kuka, ta fara tapping bayana alamun lallashi ba tare da tayi magana ba nasan tana tsoron tayi magana ne kuka ya kufce mata. Anty Asma’u ce ta janye ni daga jikin Mom din ta kaini bandaki, nan ta cire min kwalliyar da aka min ta hada min ruwan wanka ta fita daga dakin, jiki a sanyaye na shiga cikin bath tub din nayi wankan tare da daura alwala na fita. Lokacin dakin daga Anty Shafa sai Mom da Anty Asma’u, suka umarce ni da inyi sallah, nayi. Ina gamawa suka fara caccaba min kwalliya, ana cikin yi aka kira Isha suka saki muka yi, Anty Shafa ta bar Anty Asma’u tana min kwalliyar ta koma wajen Mommy itama ta fara mata. Doguwar rigar shadda suka dauko mana maroon ta sha aiki tun daga sama har kasa, Mommy ma irin kayana ta saka sun mata kyau sosai ta fito kamar wata karamar yarinya. Muka jera muka fita falo da ita muna ta sheki, babu kowa a cikin falon sai Daddyna, ya sha babbar riga ta shadda irin ta jikinmu har ma da surfanin jikinmu, yana ganin fitowar mu ya tashi tsaye, hada mu yayi mu duka da Mommy ya rungume mu, na rirrike shi zan fara sana’ar hawaye yayi saurin daga fuskana yana girgiza min kai cikin murmushi, “umh umh Uwata, banda kuka ko so kike ki bata min kwalliyar ki?” na girgiza mishi kai, yace “good girl, muje koh?” suka saka ni a tsakiya shi da Mommy kowa ya rike hannuna muka fita. Wajen ya kara kawatuwa saboda dare da yayi, mutane duk suka mike tsaye suna tafi lokacin da muke wucewa ta gefen tables din da suke zaune har muka karasa wajen da aka tanadar mana muka zauna sannan suma suka zauna.
            Anty Uwani ce ta bude taron da addu’ah, bayan ta gama ne kuma Daddy da Mommy suka fita suka wa baki barka da zuwa, daga nan suka fara bayanin farin cikin da suke ciki na aurar da kwallin kwal din diyarsu, Daddy yace yanzu duk wasu burikan shi sun cika sai fatan gamawa da Duniya lafiya Mommy kuma tace buri daya ya rage mata shine taga Diya na jikoki a wajenta, aka yi dariya ni kuma na sadda kaina kasa. Bayan sun gama bayanan su suka dawo suka zauna, aka ci farfesun kifi sardines, chips, da lemuka, aka sake rufe taro da addu’ah sannan aka watse. Bamu tsaya yin komi ba kowa ya nemi makwanci. 
            Washegari Daddy ya ja mu sallahr Asubah a dakin shi, bayan mun gama sallar munyi karatu kamar yadda aka saba, Daddy ya fara min nasiha Mommy ma ta dora da nata, Daddy ya rungume ni yana lallashina daga kukan da nake yi babu kakkautawa, ya shiga lallashina har nayi shiru, yace “Allah ya miki Albarka Uwata, hakika ke ‘ya ce ta gari wadda ta zama sanyin idaniyar iyayenta, in Allah ya yarda sai kin samu wadanda zasu miki fiye da abinda kika mana, Allah ya albarkace ki da rayuwar aurenki gabadaya. Na hore ki da Biyayya ga mijin auren ki, ki bishi sau da kafa, ki mishi biyayya tsakanin ki da Allah, idan kika yi haka in shaa Allah ba zaki tabe ba Uwata!” kuka muke ni da Mommy, shi kan shi daddy sai daya share kwalla, bayan mun yi shiru muka koma dakin Mommy muka kwanta barci bamu tashi ba sai bayan karfe goma, break fast ya kammala amma na kasa cin abincinnan saboda tsabar fargabar rabuwa da iyayena, dama haka kowace ‘ya mace take ji ne?? Kwance nake shame-shame akan gado tunda na tashi daga kan dinning, yatsun hannuna ma da kyar nake iya daga su, Ramlah ce tazo ta dame ni da hira har na dan warware. Karfe daya motocin daukar amarya daga Kano sun dira, gabana ya shiga dukan uku-uku, kafin kace me! Na fara hawaye. Anty Shafa ta harare ni tace “wai ke tsabar iskanci ne ya miki yawa zaki saka mutane a gaba kina musu kuka, wa ya zage ki?” sai na kara kware mata baki, ta kama baki tace “to?! Ikon Allah, ni kam ba zan iya dake ba…” ta fita jim kadan ta dawo da Anty Uwani, da wuta-wuta Anty Uwani ta tura ni bandaki nayi wanka da wasu sabulai masu kyau da kamshi, ina fitowa nayi sallah. Anty Shafa ta min sharp kwalliya na fita muka gaisa da bakin da suka zo daukar amarya ciki har da Anty Ameenah, muna gaisawa na koma daki. Dama already duk wasu kayana an riga an kaisu Kano kwanaki biyu da suka wuce, bayan su Anty Ameenah sun huta sun ci abinci, nan aka fara min kwalliya data daukemu kyakkyawar awa guda, ana gamawa muka yi sallar La’asar aka bani riga da zani na na atamfa super ruwan ganye nasa, Anty Shafa ta dora min gyale akaina suka kama ni har dakin Daddy muka yi sallama ta karshe, ya jaddada min yin biyayya, juriya da hakuri a cikin rayuwar aurena, ana tashi dani na yi rau-rau da idanu, Anty Uwani tace “wallahi kika kuskura hawaye ya zuba a fuskar ki sai na mazge ki!” Daddy yace “a’ah Uwani, bi ta a hankali mana” ta kamo hannuwana ina turjewa ta jani tana mitar Daddy ya bata ni da yawa gashi za a kaini gidan aure, mutane suka biyo mu duu har gaban farar rantsamemiyar Land Cruiser ta daukar amarya, Daddy da kanshi ya bude motar ya kamo hannuna ya saka ni a ciki, zuwa lokacin kam kuka nake yi sosai har da ihu, da kyar suka tura ni aka rufe motar Anty Shafa da Ramlah suka shigo aka rufe motar, sauran masu rakiya da su Anty Ameenah suka shiga sauran motocin. Ina kallon su Mommy a tsaye, Mommy ta kwantar da kanta a kafadar Daddy tana kuka, motar tana fita daga gidanmu na yadda kaina a kafadar Anty Shafa na kara sakin wani kukan. Lalle gaskiyar bahaushe da yace ‘Aure yakin mata!’ in ba aure ba meye zai raba ni da masoyan Ruhina bayan mutuwa??Munyi nisa sosai kafin kukan da nake yi ya dauke, Anty Shafa ta miko min handkerchief na share fuska ta dashi, ta bude Jakarta ta ciro kayan kwalliya ta juyo da fuskata ta gyara min kwalliyar dana bata, na juya kaina ga window din motar na fuskanci waje zuciyata cike fal da tunanika iri-iri. Karfe shida muna cikin Kano, kai tsaye unguwar Galadanchi aka wuce damu gidan su Abbu. Can muka tarda mutane na jiran isowar mu, dakin Hajiya Siyama Mahaifiyar su Abbu surika a wajena muka sauka, aka damka musu Amana ita da Dattijan da muka samu a dakin nata, daga nan kuma aka kaini dakin Hajiya Fati nan ma dai gaisuwa da bada amanar ne, bayan an gama aka dauke ni zuwa wajen mahaifin su, ya mun nasiha sosai mai shiga jiki tare da addu’o’i, ya bada abin Sallah, Carbi da Turare aka bani a matsayin tsarabar gidan aure daga nan muka koma cikin mota sai gidan Aurena a Sharada phase 2.
      Gida ne flat mai kyau, dakuna uku manya duk an yi jere, akwai toilets a cikin kowane daki, kicin, sai toilet daya a cikin falo kila na baki ne. 
                   Su Ni’imah sune en jagora har zuwa dakina, sai da muka shiga daki Anty Ameenah ta yaye min gyalen kaina duk da haka kin daga kaina in kallesu nayi, Su Anty Shafa daya dakin aka kaisu ni kuma su Ramlah suka zauna a tare dani, nan dai muka dauro alwala muka yi sallah, kasancewar lokacin Sallar Isha’i yayi yasa muka yi har Isha’i din. Muna gamawa aka dire mana plates din abinci, Macaroni jollop da lemuka, tsakanina da Allah cikina a cike yake shi yasa na dinga tsakurar abincin, Sadiya data fara nauyi haihuwa ko yau ko gobe duk da ita aka yi jigilar gaisuwa da ita ko nauyin cikinta bata ji, tace “Amaryar Babban Yaya ya dai baki cin abinci ko dai kazar amarcin kike jira?” na harareta kasa-kasa ganin gasu Anty Ameenah a gefenmu suna zaune, Ni’imah tace “ta fa riga da taci kazar amarcinta tun ranar da aka daura aure, muma ba har muka ci saura ba?” na kuwa kai mata mintsini a cinya tayi tsalle gefe guda tana sosa wajen, Ramlah tace “ku kyale yarinyar nan, tun dazu take nuku-nuku kamar ba ita bace tace tana son auren, lokacin da yunwa zata taso mutum ya nemi abinci kuna ihu?” duk suka sa ihun, “Gida!!” tace “kun gani?!” ni kam sai na tashi na bar musu wajen kawai, na koma kan bencin dake gefen gado na zauna ina satar kallon kayan dakin, komi na ciki silver ne da black, gadon irin kananun Italian beds dinnan ne medium king size sai wardrobe data kusa cinye bangon dakin na gefen dama, dressing mirror, end of bed table, rug carpet, labulaye silver, sai sauran kananun tarkace da ba za a rasa ba amma kayan sunyi kyawu sosai, babu wata hayaniya irin ta kayan dakin zamanin nan.Su Anty Ameenah suka mana sai da safe suka tafi suka barmu da su Anty Shafa da Ramlah, er hirarraki muka yi kafin Anty Shafa tace yakamata mu kwanta haka, ni na fara shiga toilet nan ma kayan ciki har ba a magana, katoton Jacuzzi tub, sinks, akan canters kuma mayuka ne tun daga na gyaran fata har na gashi ne da turaruka abin ba a cewa komi, na tari ruwan dumi na dan yi relaxing saboda warware gajiya kafin na dauro babban towel na fito na danyi en shafe-shafe na fita, Ramlah ta shiga.
         Wardrobe na bude da niyar duba kayan barci, baki na bude a tsorace ina kallon cikin wardrobe din. Layi daya atamfofi ne wasu ma ko dinga su ba ayi ba, sai daya na laces, daya nasu jallabiya ne da dai dogayen riguna, daya nasu materials, saitin kayan barci kuwa sai da suka kwashe biyu, na zaro riga daya na daga ta sama, it looks more like a lingerie yawancin kayan barcin duk ire-iren su ne.
             Na juya da rigar a hannuna ina nunawa Anty Shafa, “meye haka Anty?” tace “kayan barci mana” na kara kallon kayan, “you didn’t mean… Ni zan saka su koh?” ta harareni, cikin gatse tace “a’ah ni zan sa…, ko kuma shi mijin naki!” na gumtse dariyata nace “amma Allah Anty kayan suna nuna jiki da yawa fa” tace “yi mun shiru malama, don suna nuna jiki sai me? Ina ce dai hakan ba Zunubi bane? Idan kin san ta yadda aka yi kayan nan suka zo nan ba zaki zauna kina ce mun wai suna nuna jiki ba, I specially went to Kamfanin da suke sarrafasu na bada oda, don haka tun kafin raina ya baci ki saka kayan nan, besides kayan nan na arziki ne idan kika yi comparing dinsu da wasu kayan, koda yake ke da kanki zaki san amfanin su kizo kina nema na” sai na gumtse baki na juya na maida rigar na fara laluben kayan sa wa, da kyar na lalubo riga da wando suma dai sai a hankali, wandon 3q, rigar mai hannun vest gasu silk, lokacin Ramlah ta fito nan muka bi lafiyar gado. Anty Shafa kuma ta ajiye katifa a tsakar dakin muka yi light off muka kwanta, kamar jira yake, sakon Abbu ya shigo. +

*“Sleep??”* nayi gaggawar tura mishi da, *“about to…. How was your day?”* ya turo *“dama nasan ba zaki iya barci ba baby na, tun yau fa baki ji murya ta ba balle kiga text dina, nima ina kewar ki baby na nasan da kyar barci ya dauke ni yau, amma kar ki damu, na yau ne kawai…, daga gobe babu wanda zai sake shiga tsakaninmu da yardar Allah”* lokacin dana karanta sai da er dariya ta kufce min, kai Abbu is full of self confidence. Na tura mishi *“says wanda yake da mata., plus ni fa barcin ne kawai bai zo ba amma babu wanda nake kewa sai Mommy da Daddy na!”* na tura ina dariyar tsokana, nasan kila har gari ya waye yau muna musayar sakonni ne, sai kuma har barci ya dauke ni bai dawo da reply ba.Sai da muka tashi sallar Asabar naga amsar daya maido mintuna kadan da fara barci na, *“zaki ce haka ai tunda har yanzu baki zo hannu ba, gobe war haka ki maimaita abinda kika fada yanzu please….” nayi murmushi kawai na maida wayar kasan filo na fada toilet. Muna gama Sallah muka koma wani barcin, sai karfe tara na safe muka tashi. Muka yi wanka muka kimtsa, an kawo mana abinci daga gidan su Abbu muka fita parlour muka karya. Falon madaidaici ne wanda ya dauki wasu rantsattsun beige couches guda biyu an jera su daya ta kalli gabas daya kuma ta kalli arewa, sai wasu Everette chairs navy blue guda biyu suna fuskantar couch daya, a tsakiya kuma an saka babban teburin gilashi kasan shi wasu woods ne suka tokare shi, a sama kuma an dora flower base mai kyau, sai lamp mai kama da bishiya, kasan parlor hardwood flooring aka yi, kai komi dai na falon ya fita very unique, muka hau kan dinning mai cin kujeru takwas muka karya. 
              Dakina muka koma Anty Shafa sai cafta take sauke min tana karawa duk da wasu abubuwan duk tuni ne take yi mun. Karfe daya munyi sallar Azzuhur sai ga Abbu shi da abokan shi biyu, nayi sauri na dauko hijabi na dora akan kayana, falo muka fita muka gaisa dasu, ban yi gigin daga ido na kalli kowa ba. Ramlah ce tayi jigilar entertaining dinsu, ni kam suna fara cin abubuwan data kai musu nayi wuf na fada daki. Gefen gado na samu na zauna, ban jima ba sai ga Abbu shima ya shigo. Kai tsaye inda nake zaune shima yazo ya zauna a gefena, hannuwana duka biyun ya kamo da daya hannunshi, dayan kuma yayi amfani dashi wajen dago kafadata, ya wani rausayar da kai, “me nayi ne yau kuma Babyn? Babu gaisuwa, babu murmushi, babu kallo?” na sadda idanuna kasa tunda ya rike fuskar, duk yadda naso in daga baki in gaida shi kasawa nayi, wani irin nauyi da kunyar shi da ban taba ji ba naji sun dabaibaye ni, ya nisa, “bari in maida su AbdulHameed gida in kuma dauko direban da zai maida Anty gida sai in dawo gare ki gabadaya koh?” ya kai hannuna bakin shi yayi kissing as usual kafin ya fita.
              Yana fita su Anty suka fara shirye-shiryen tafiya, nayi rau-rau da idanuna nan Anty ta samu abin fada, abin mamaki kuma bayan kamar awa daya da taji direba yazo sai kuma ta hau sharar kwallah, nan na rungumeta ina kuka, Ramlah ma tana gefe tana matsar kwallah, Abbu da kanshi ya leko ya sanar da ita zuwan direban. Ta mike tana share hawayenta tare da rataya jakarta, ta kamo hannuna ta rike cikin nata, “to Nafeesah, sai watarana, Allah ya baku zaman lafiya da maigidanki da abokiyar zaman ki, hakurin nan dai da kowa yake gaya miki kiyi da biyayya shi zan kara jaddada miki, sai kinyi exercising hakuri sannan ne zaki ci ribar rayuwar aure duk da nasan ki da hakuri amma dole sai kin kara kinji? Allah ya miki Albarka” na gyada mata kai ina hawaye.Ta sa kafa ta fara tafiya Ramlatu ta bita a baya nima na bisu, a bakin falo Abbu ya dora min hijabin dana saka lokacin da abokan shi suka zo, muka karasa fita har shi. Ina tsaye har Anty Shafa ta shige mota Ramlah ma ta shiga different mota tunda ita gidan Anty Haleemah ta nufa. Direba ya tashi motar suka tafi muna daga musu hannu har maigadi ya maida gate ya rufe, wasu hawaye suka kara gangaro min a kumatu, shikenan an tafi an barni ni kadai. Abbu daya tsaya a bayana ya sakalo da kanshi ta wuyana tare da zagaye ruwan cikina da hannuwanshi, duk da halin da nake ciki sai da naji wasu abubuwa na min yawo a jikina, a hankali yake magana, “m sorry Baby, In Shaa Allah ni zan maye miki gurbin su Daddy dinki kinji? Stop crying kinji? Yau ce rana ta farko fa da zamu rayu karkashin rufi daya a matsayin ma’aurata, rana ce mai matukar muhimmanci don haka babu kuka ok?” na gyada kaina a sanyaye, ya sake ni ya juyo dani ina fuskantar shi, hannu yasa ya goge hawayen fuska ta, ya kama hannu na yana min murmushin nan nasa mai kwantar min da hankali muka koma cikin falo. Muna shiga aka kira sallah, ya shiga dakina yayi alwala ya tafi masallaci ni kuma na tada kabbarar tawa a daki abina. 2

Bayan na gama sallar falo na koma na zauna ina kallace-kallace har Abbu ya dawo daga masallaci Maigadi ya biyo shi a baya da kuloli a hannunsa, na tashi na karbi kulolin na shiga kicin na fito na plates da cokula, Abbu yana kan dinning table a zaune naje ina wani sunke-sunken kai na zuba mishi abincin na tura gaban shi, nima na zuba nawa naja kujera da take fuskantar shi na zauna. Tsam naga ya mike dauke da plate dinshi a hannu, na bishi da ido cike da mamakin abinda zai yi naga yaja kujerar gefena ya zauna, abincin plate dina ya juye a cikin nashi plate din, yace “daga yanzu we share one plate, spoon, and if possible har kujerar zama kin gane?” ni kam dai nawa gyada kai ne, jina nake kamar wata sabuwar halitta. Cikin sanyin jiki muka fara cin abincin, idan yaci sai in karbi cokalin shi nima inci haka har muka gama cin abincin na tattara kayan na kai kicin na wanke kafin na koma falon, yana zaune yana waya ya miko min hannu, a kunyace naje na zauna a gefenshi, yaci gaba da amsar wayar shi ni kuma naci gaba da kallona, ya gama wayar ya janyo hannuna cikin tafukan hannayen shi duka, kunshin da aka sake min yake shafawa da alamun yana son kunshi sosai, ya fara ja na da hirarraki duk don in samu in sake dashi amma ina, na kasa. Yau dai gabadayan shi ya koma min kamar wani bako, irin awkwardness dinnan da ake ji when you were stuck up with a total stranger a waje daya shi nake ji, bai takura akan lallai sai na saki jiki dashi ba. 
              Sai da aka kira sallah sannan muka tashi, yace min sai bayan sallar Isha zai dawo nace toh. Daki na shiga nayi Alwala na fito nayi sallah, akan abin sallar na zauna ina tilawa har aka Isha na tashi nayi na hada da Shafa’i da Wutiri.
          Gefen gado na koma na zauna na dauko wayata, babu caji ma a ciki. Anty Shafa na kira na tambayeta ko ta sauka lafiya, nan muka gaisa da ita ta ba Mommy wayar muka gaisa kafin Anty Shafa ta sake amsar wayar, wata riga ta kwatanta min a cikin kayan barci na tace ita zan saka idan zan kwanta nace mata to, kafin muyi sallama ta kara jaddada min in saka rigar fa nace mata to dai. Bayan mun yi sallama da ita Ramlah na kira, ta daga da shakiyancin ta wai ina na baro angona nake danna mata kira da dare? Nan muka fara hira har Abbu ya dawo daga masallaci misalin karfe tara, na mata sai da safe na ajiye wayar ba tare dana kula da tsokanar da take jifana dashi ba.
             Dangin fruits ne ya dawo dasu sai gasasshiyar kaza, na dauko plates da wuka na kawo, muka zauna muka ci duk da dai tsakura kawai nayi fruits dinne ma dai na ci sosai, ya tsiyaya fresh milk mai sanyi a cikin cup ya miko min shima ya zubawa kanshi, na amsa na kafa kai na shanye ta ban bar ko digo ba. Ya kalleni “kin koshi?” na gyada kai, yayi hamdala shima ya karasa shanye nashi madarar. Na hada komi na kai kicin, na wanke na wankewa, sauran fruits da kazar kuma nasa a fruit. Ya leko kicin din ya tsaya a jikin kofa yana kallona, jin idanunshi a kaina yasa na juya, murmushi yayi yace “have you prayed?” na gyada kai, ya rausayar da kai gefe, “idan kin gama kije ki dauro alwala ki same ni a dakina” ya juya ya tafi ya bar ni ina zare idanu. 
            A sanyaye na gama shirya kayan na koma daki, wanka na fara yi na daura alwala ba shafa lotion mai kamshi na fito, cikin wardrobe na lalubo rigar da Anty Shafa tace in saka. Wata silk trim gown light purple wadda ta kai rabin cinyoyina, gabadaya saman rigar lace ne mai kama da net, na zura rigar ina karewa kaina kallo ta cikin mirror, gabadaya cinyoyina a waje suke kamar yadda ilahirin kirjina yake waje kai har ma cibiyata, ta yaya ma zan iya fita gaban Abbu a haka? Ni kaina kunyar kaina naji, nayi kamar in cire rigar sai na fasa, after dress na laluba na dora, na dauki hijabi na saka na fesa turare a jikina tun daga na jiki har na kaya. 
             Kafewa nayi a tsakiyar daki ina tunanin ta yadda zan karasa dakin Abbu, inje in ce me? Ni ba wawiya bace, nayi karatu daidai bakin gwargwado na kuma san muhimmancin sallar dana yiwa alwala yanzu kamar yadda nasan abinda zai biyo bayan hakan. Gabana yayi wani irin bugu just for the mere thought of it, me zai faru yau kam? A dan tsorace na kalli kofa jin ana taba ta, Abbu ya shigo dakin amma ba gabadayan shi ba, ganina a tsaye ya dan yi frowning, “me kike yi? I’ve been waiting for you fa” nace “ai.. Ehh dama yanzu zan zo ai!” ya kara bude kofar alamun in wuce, ba musu na bi ta gefenshi na wuce gabana na dukan tara-tara, ina jin lokacin da ya kashe wutar dakin tare da rufo kofar, gabana yaci gaba da luguden daka da yake yi har kafafuna na rawa. Yayi gaba na bishi a baya kamar wadda take jan kafar ta. Dakin shi shima ba wasu tarkace bane, daga gado wanda zai iya kwasar mutane uku, sofa, bedside table da lamps, walk-in closet sai toilet. Dakin zagaye yake da rug carpet mai zane baki da fari kamar jikin zebra. Ya shimfida mana abin sallah ya umarce ni da in bi bayan shi, Nafila ya fara jerawa sai da muka yi raka’ah takwas, ya fara jero mana addu’ah samun zaman lafiya mai dorewa da zuri’ah mai Albarka a rayuwar auren mu ina amsawa da ameen a cikin raina. 
            Ya tashi ya nade abin sallar, ban yi yunkurin mikewa ba ina zaune a inda ya barni ina satar kallon shi, dakin kayan shi ya shiga, ba a jima ba ya fito sanye da pyjamas na Marks and Spencer masu taushi ash color, ya latsa wani abu mai kama da remote hasken dakin ya dauke ya fara kawo wani jan haske an jima kadan sai blue ya kawo. A hankali naga ya daga kafafun shi ya fara takowa inda nake zaune, duk taku daya sai bugun zuciyata ya karu. Yasa hannuwanshi biyu ya daga kafaduna tare da mikar dani tsaye, hijabin jikina ya cire ya ajiye akan abin sallar, ya kai hannu yana kokarin balle maballan doguwar rigar jikina, da sauri nasa hannu na rike, daya hannun ya saka ya rike min hannun ya cigaba da balle buttons din rigar, ina jin lokacin da rigar ta sulale daga kafaduna ta sauka akan tafin kafata, da sauri na rufe idanu na don nasan ba zan taba iya hada idanu da Abbu ba.Hancin shi ya kai cikin gashin kaina ya shaki kamshin, a hankali kanshi ya fara gangarowa har ya kawo wuyana ya fara wani shinshinata, “Masha Allah baby! I like this scent…. Really!” ya fada cikin wata irin murya da ban taba jin shi da ita ba, faduwar gabana ta karu, rawar jikina ta linka ta da, a hankali naji wani abu mai sanyi da lema yana tracing din ilahirin wuyana da samar kirjina, a rikice naji kafafuna sun fara sulalewa kasa yayin da gangar jikina ta bisu zamu zube gabadaya, ji nayi an daga ni sama cak an dora akan gado, ba bata lokaci ya biyo bayana ya dora leben shi akan fuskata ya fara bin ilahirin fuskata da ruwan kisses har da lasa kamar wata alewa har ya gangaro wuyana, ai gabadaya wuta dauke min tayi, na manta a duniyar da nake, na kasa tuna a inda nake, babu abinda nake fahimta da ganewa sai lebuna, harshe da hannuwan Abbu da suke yawo a gabadayan sassan jikina. Haka kawai naji hawaye suna zubo min wanda ban san dalilin su ba duk da dai nasan cewa hakan baya rasa nasaba da sabuwar rayuwar da Abbu yake kokarin jefa ni ciki. Goshina ya hada da nashi yayin da hannun shi yake share min hawayen dake gangarawa suna shiga har cikin kunnuwana, “why baby??” ya rada min a kunne, tsikar jikina ta tashi a take rawar jikina ya karu, wasu hawayen suka kara zubo min, yace “nooo baby, don’t cry please. Please kar ki hana ni mallakar ki Nafeesah, I really want to do this please??” ni wacece da zan hana shi abinda yake mallakinshi ne, ni wacece da zan hana shi samun farin cikin shi?? A hankali nayi nodding kaina, yace “thanks baby… I won’t hurt you I promise, I’ll be gentle In shaa Allah! I love you” hannu nasa na rungumo shi kawai ina hawaye, and that is the invitation he needed, ya hade bakina da nashi yana tsotsa exploringly kamar zai hadiye ni
           Ba a dauki lokaci mai tsayi ba dakin ya cike da sautin shesshekar kukana, tun ina daurewa tsananin azabar da nake ji har na saddakar na bude baki na fara kuka da magiya har ina kokarin ture shi daga kaina, abin yafi kafin tunani na duk da cewa bai kai ma rabin zafin da nake hangowa ba irin wanda naji ana bada labari, amma azabar is still unbearable. Sai daya nutsu ne ya ankara da kukan da nake zubawa kamar wadda ake zarewa rai, ya fara jijjiga ni a hankali yana tafin bayana ba tare da yayi magana ba. Sai da numfashin shi ya dawo normal naji yayi magana, “I am sorry, did I hurt you?” a hankali na girgiza mishi kai, duk da akwai zafi amma nasan bai kai wanda za ace yaji min ciwo ba. Ya gyara min kwanciya a jikin shi tare da janyo bargo ya rufe mu, “ok, yi barci baby” muryar shi was soft, very soothing. Na lumshe idanuna ba bata lokaci barci yayi awon gaba dani. Cikin barci naji lokacin daya tashi ya shige toilet, na kara kudundunewa a cikin bargo. 
         Sai da asubahi sannan na farka shima wasu tausasan hannuwa ne naji suna shafa min kumatu, na bude idanuna inda naci karo da fuskar smiling Abbu, “Hii sleeping cutie pie, a tashi koh?” na dan motsa, slight pain din da naji ya ratsa ni yasa na maida kaina cikin bargo a sukwane, sai lokacin kwalwata ta tariyo min daren jiya. Yayi chuckling kafin naji an daga ni sama daga ni har bargon na fara wutsilniya amma bai dire ni ba sai cikin bath tub wanda aka tara ruwa mai dumi a ciki. Ya zare bargon jikina ya ajiye akan dressing table, ya dawo ya fara kokarin min wanka. Duk yadda naso ya fita ya kyaleni sai hakura nayi, ya taimaka min nayi wanka tare da dauro alwala, ya dauko towel mai fadi ya nade ni a ciki ya kara ciccibana muka koma daki. Rigar jiya ya dauko ya saka min kaina yana kasa na kasa hada idanu dashi duk da tsokanata da yake yi, nan ya tafi masallaci ya barni na lallaba na hau kan abin sallah na tada kabbara. Ina gama sallah na koma kan gado na sake nadewa saboda barci, ina jin sanda Abbu ya dawo ya hau kan gadon ya nado ni cikin jikinsa, na kuwa kara shigar da kaina cikin faffadan kirjin sa na lafe.
~Hahhh, If you were ask to say One Word for this night, what will you name it? ~Wa zai iya shiga kwalwar Abbu ya fada mana abinda yake cikin zuciya da Ruhin shi??

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]