ABBAS CHAPTER 7

ABBAS

CHAPTER 7

Mahmud shegen surutu ne dashi, gashi baya da bak’unta sam gashi da iya jan mutun da hira hakan yasa awannan fitar da sukayi da Teemah har sabo ya shiga tsakaninsu na ban mamaki.
+

Tun daga ranar shiyake ajiyeta a school ya kuma d’auko ya dawo da ita gida da yamma ya ajiyeta a islamiya kuma.

Tare suke zama suyi hira haka abinci ma bai fasa bata ba kamar yanda ya fara tun farko sai ya mik’e kawai da haka, dan suna zama a kan table zai fara bata sai yaga tace mar tak’oshi kafin yaci shima, wani lokaci har d’akin sa take zuwa dan kawai suyi hira idan taga Mahmud d’in bai zo nemanta ba,idan akayi rashin sa’a kuma ranar yana d’akin Abbas sai fatattako ta tmdawo tana ture-turen baki tana mita,mummy najinta kuwa aja bakin har sai tayi kuka.


Koda lokacin shiga CAMP d’in Mahmud yayi ma Abbas ne da Teemah suka rakashi,Teemah harda d’an guntun hawayenta tana ta mar shagwa6an wai zai tafi ya barta shikuwa Mahmud yanata mata dariya.


Abbas haushin hakan yaji, sosai abun ya sosa ransa har ya gagara juran ganin abinda Teeman takeyi dan Mahmud zai shiga CAMP ai baisan lokacin daya sa hannu ya finciko ta da k’arfi ba, bai tsaya ko’ina ba sai daya danganta ta da cikin motar ya tura marfin ya rufe sannan ya zagaya ya shiga shima ko takan Mahmud d’in ma bai k’ara bi ba.

Idan kagan shi zaka yi zaton ko gajiya yayi da abinda Teeman keyi shiyasa yayi hakan, kamar dai yanda Mahmud ma tunaninsa ya tsaya iya nan.Hakan yasa yabi bayansu da murmushi yana k’ara jinjina hali irin na Abbas d’in sam baisan wargi.

Abbas kuwa takaici ne yagama cika mas kwakwalwa, suna shiga cikin motar kuwa ya d’aga hannu ya sake mata wani rankwashii mai azabar zafi dan ya yishi ne a zuciye, amma sai ya waske da fad’in cewa bata da kunya ita kokad’an, wai ‘yar k’arama da ita sai fitinan tsiya.


Bata fahimci mai yake nufi ba, amma zafin abinda yamatan sai yasata kuka,kukan tafara da d’an sauti dan abin biyu yazame mata ga missing d’in yah Mahmud ga kuma zalinta da akaci abanza.


Takuwa k’iyin shiru da gangan ma taketa yin kukan da sauti aranta take cewa aikuwa zaka ga fitina yau d’in nan ganin idonka.

Bai k’ara kallon inda takeba balle ya kulata sai da yaga kukan bana k’are bane kafin yayi parking agefen hanya da k’arfinsa sannan ya kalleta yace
“Zan 6a66allaki anan wallahi idan bakimin shiru ba idiot”
yafad’a yana wani zaro idanu

Shiru tayi cak kamar anyi offing switch dayake daman kukan na isaknci shiyasa tayi tsit da wuri dan sosai ta tsorata da yanayinsa na yau d’in acikin ranta tasake fad’in “ashe dai ni zanga fitinar bashi ba.”

” _Banza jarababbiya_ “
Yafad’a lokacin da yake k’ok’arin tada motar aranta ta amsa da “wallahi badai ni ba kam sai dai kai”

Tana fad’a tawani kau da kai gefe kamat wata jaruma.

Dayake bajinta yayi ba shima sai bai kulata ba.

Tuk’in ya cigaba dayi batare da ya d’auki hanyar da zata sada su da gida ba.

_Waziri ibrahim_ ya nufa ita kuwa sai ware ido takeyi da mamakin yaushe yasan unguwar kuma mai ya kawo su hanyan nan d’in, kodan ma ai bai san gari ba ba mamaki 6atan kai yayi”duk aranta tayi wannan tunanin.Hakan yasa da gwanintan ta tace “yayah nan fah ba hanyar gida bane”
+

Hannunsa ya d’ago da niyar gwa6eta a baki sai tayi saurin yin k’asa da kanta ta 6oye fuskar atsakanin cinyoyinta.

Hakan datayi ne ya kwaceta sai shima ya maida hannun nasa kan stairy tare da fad’in “nonsence”.

Tafiya kad’an ya k’ara sai ya sa hannu ya d’ago wayarsa yayi dialling wata no.


Baiyi magana ba sai kawai “uhm” dayace yana fad’in hakan kuwa ya cire wayar akunnan sa tare da ending call d’in sannan ya ajiye wayar a gefensa.


Parking taga yayi a k’ofar wani gida,minti biyar mai kyau basu k’ara ba sai ga wata y’ar kyakykyawar budurwa tafito daga cikin gidan tana zuba murmushi.

Shikuwa yana ganinta ta fito sai shima ya bud’e motar ya fita ya tareta suka had’u a tsakiya.Yarinyar kam masha Allah ba dai kyau ba,Teemah k’ura mata ido tayi tana ta kallonta har Abbas d’in ya isa gareta.Sai alokacin nr ta d’auke idonta daga kan yarinyar.


Saitin yarinyar Abbas ya tsaya sai ya zamana Teemah bata hangota kok’ad’an dan duk tsawon Abbas ya kare ta,sai dai bakin gyalen yarinyar da iska yake ta kad’awa shi kad’ai Teemah ke iya hangowa game da yarinyar.

Amma tun fitowar yarinyar Teemah ta lura yarinyar “A” ce afagen kyau, hak’ik’a kyau kam Allah ya bata ba laifi,taso tayita ganin yarinyar har tasamo abin kushewa amma sai Abbas yayi mata yaawah yayi babakere ya rufe ta gaba d’aya sai bayanshi kad’ai Teemah ke iya hangowa bata san meke gudana a tsakaninsu ba, ba kuma tajin akan abinda suke tattaunawa.

Rasa abinda zatayi tayi aranta takejin kamar tafita taje inda suke tsayen taji mai suke fad’a amma tsoro ya hanata dan tsan inta kuskura tamasa badaidai ba tilabta zaiyi shikam baruwansa balle ma yanda taga yau d’in yake 90% tasan babu abinda zai hanasa dukanta.

Kalle kalle tafara acikin motar kamar wanda yau ne tafara shiga cikinsa,ita kanta batasan mai take nema ba cikin haka kuwa idanta ya sauk’a akan wayarsa dake ajiye agefen inda ya tashi.

Karambani yasata ta d’auko wayar, cikin sa’a kuwa wayar bata shiga security ba tana bud’ewa taga akan k’iran da yayi d’inne wayar take haryanzu

“Muhibbat” tagani arubuce, karantawa rasake yi kusan sau uku, jitayi sunan ya tsaya mata aranta, amma daga ganin sunan tagane itace wacce yayi waya da ita d’azu dan tunda sukayi wayar bai kuma yin wata waya ba, kenan wato sunan wannan yarinyar ne Muhibbat d’in tunda da ita kad’ai yayi waya kafin ya fita a motar , ta6e baki tayi sannan tafita daga wurin k’ira ta nemi gallery ta shiga,images tagani sai kawai ta danna kansa ta shiga pictures d’insa ne zallah aciki, sai wanda taga sun d’auka su uku acikin parlour zaune akan kujera da wata yarinya bazama ta wuce sa’arta ba da kuma Ummahn Daddyn Abuja.

Yarinyar ma dashi take kama aranta tace k’ila itace wacce ake gulamata akanta d’in kwananki.

Canja folder tayi ta shiga camera, anan taci karo da zallan hotunansa masu d’aukar hankali, wasun sanye yake da kayan sojoji wani ma harda bindiga rik’e a hannunsa.

Cigaba da dubawa tayi takuwa dinga cin karo da hotunsa wani kuma bashi kad’ai bane,wani suna training ma akayi,cigaba da bi tai tayi harta iso wanda akayi da daddynta da daddyn Abuja da Ummah da kuma wasu daban da bata ma sansu ba,tana k’ara turawa taga wanda yayi shi kad’ai ya d’aga bindiga kamar zaiyi harbi.


Jitayi photon ya birgeta sosai,sai ta tsaya akan wannan d’in tana ta kallon shi,gani tayi yayi kyau sosai har bata son wuce wurin dan inta d’anyi gaba sai ta kuma dawowa baya.Afili tace ” ai dole kayi mugunta, mtun kullum cikin mugun hali, ashe har bindiga ne dashi shima wannan yanda yake da muguntan nan ai inkayi wasa wataran harbeka ma zaiyi”

Tana cikin maganar sai ta d’ago kanta ta kalli inda suke tsayen,ai kuwa sai taga yana k’ok’arin dawowa,da wuri ta mik’a hannu ta ajiye wayar a inda ta d’auka garin sauri ma ko fita a galleryn mantawa dashi tayi, jikinta har rawa yakeyi tsabar tsoro.


Sa’anta d’aya bai kalli inda ma wayar take ba, kamar yanda ita kanta bata samu kyakykywan kallo daga wurinsa ba.

Tada motar yayi ya nufi hanyar gida, tak’asan ido Teemah take kallonsa, sai yanzu take mamakin yaushe ma yazo garin harda zaiyi budurwa lalle wannan kam akwai aiki agabansa indai hakane, ta6e baki tayi tare da maida idanta ga titi,babu wanda yayiwa d’an uwansa magana har suka iso gida.

Cikin sanyi ta shigo d’akin dan sai da suka shigo harabar gidan kafin Mahmud ya fad’o mata arai.

Sai yanzu taji sabon missing d’in Mahmud d’in aranta,” Allah sarki yayah”

Tace afili gurin mummy taje ta zube ajikinta ta kwanta shiru batare da magana ba, sai mummyn ce ta tambayeta ya akayi ?

Amsa ta bawa mummyn cikin sanyi ” mummy yah Mahmud ya tafi ya barni”

“Abinda yakawo shi garin kenan ai Teemah”Mummyn tabata amsa.

D’ago kanta tayi sama tana kallon mummyn

“Toh kenan bazai sake dawowa ba mummy”
Ta sake tambayar mummyn nata.

“a a zai dawo mana nan da 3weeks insha Allah”

“Allah ya nuna mana” kawai Teemahn tace sannan ta maida kanta kan cinyar mummyn ta kwantar.

Mummy har ranta sai taji tana tausaya wa ‘yar ta ta, domin tasan illar shak’uwa ba dad’i musamman in aka had’a da kalmar rabuwa toh sai a hankali.

Abbas kuwa yana shiga d’aki ya d’aga wayarsa da zummar k’iran daddynsa dan yau basu gaisa ba kwata-kwata yana bud’e wayar sai yaga hotonsa afiskar wayar
mamaki ne yacika shi dan shi dai yasan bai san picturensa a wallpaper ba,amma ga mamakinsa daya shiga sai yaga ashe akan gallery ne wayar take

“TEEMAH”
Ya anbata dan ita tafara fad’o masa kuma yasan inba ita ba babu maiyi masa hakan.

Murmushi ne yaji ya kwace masa da ganin hakan sai zuciyarsa ta tabbatar masa da cewa ai photonsa ta tsaya kallo shiyasa har tamanta ta bari akai abinka da marar gaskiya.


Sai hakan yad’an sanyayah masa zuciyah.


*****
Koda da dare da akaje cin abinci ma cakula ta dingayi M har aka k’are cin abincin ita bata ci komai ba.

Duk Abbas na lure da ita, sarai yasan matsalarta, dan shima dauriya kawai yayi yaci abincin, wannan abin nan da Teemah keui jiyake kamar azabtar da zuciyarsa takeyi,ita kuma bata san hakan ba, dan kar aga kamar abu na damunsa ne shiyasa kawai ya daure yaci saboda sanin halin mummy da yayi dan tana ganinsa wani iri zata saka sa agaba da tambaya ne shikuwa bai san amsar da zai bata ba.


Kwanan Mahmud biyar kacal agidan kai agarinma gaba d’aya amma zakayi mamakin shakuwar su da Teemah, acikin kwana biyar d’in kwana d’aya ce da wuni d’aya rak ta waru wanda yakasance Mahmud bashine ya ciyar da ita ba amma sauran kwana kin duk shike bata abincin abaki hakan sai yana tuno masa da rayuwar su tabaya.Washegari Habibu ne ya kaita makaranta da yake ya dawo tun last 3days, koda akaxo cin abinci ma da daren ranar haka tayita rarraba idanu,dan rana kam ma bata cikin lissafi ita ba’a maganarta danko waiwayo gun abincin batayi.
+

Har suka gama bata ciba ita, mummy ce tafara mata surutu akan tunjiya ta lura bata wani ci abinci agidanba, amma daddy yace “tabarta ai ita tayi ra’ayi ba wani ne yace karta ci ba, kuma ai intana jin yunwa dakanta zata nema basai ansata ba”.

Jin haka yasa ta cewa ” nama fah ci amakaranta daddy”

“Toh ai kinji” daddyn yafad’a yana kallon mummy

Tsaki kad’an mummy taja daga nan bata k’ara kallon inda suke ba ma dan takaici.

Tun daga ranar Abbas yarage ganinta ma gaba d’aya, dan yanzu mummy ma ta daina damun kanta tunda ta lura daddynta ke goye mata baya.

Bak’aramin jin haushin abin nan datake yi d’in yake ba, amma bai ta6a kulata ba, sai dai yana ganin kamar ta raina su ne gaba d’aya.


Kuma abin mamaki rainin datake masa na rashin kunyan bata ta6a yiwa Mahmud ba koda sau d’aya a lokacin da yake gidan.

Idan ya tuno yanda take sake jikinta suyi ta hira da Mahmud d’in suna wasa da dariya,in baka sani bama sai kace agida d’aya suka taso sa shi.

Lokuta da dama idan yana ganinsu a hakan bak’aramin jin haushi da takaici yakeji ba, amma bai ta6a nuna musu hakan ba,nuna musu yakeyi sam bai damu da al’amuransu da shirginsu ba ma.

Koda korarta da ya keyi wasu lokuta idan tazo yana yi ne irirn kamar tazo ne zata damesu da surutu bawai dan wani abu ba kuma ko Mahmud d’in ma haka ya d’auka.

Sai shima Abbas d’in ya tafi a hakan dukda manufarsa daban shi kam, dan azahiri takaicin ganinsu taren ne yake sashi koranta.

Sarai yasan rashin sakin fuskan da baya yi matane ya sa ta ke k’insa da kuma hana tayi sabo da shi, dan shi da Mahmud they are 2 different people halayyarsu ta d’an banbanta kad’an amma tsabar zafin kai sai ya take wannan ya d’au laifin gaba d’aya ya d’ora mata.

Kawai sai yasa aransa cewa ai raini ne yake damunta……….Koda awurin cin abinci lokacin da Mahmud yake nan sosai suke bashi haushi, dan tunda Mahmud ya fahimci bata kula abinci sai an gayyato ta ko kuma an tilasatata, tundaga lokacin sai Mahmud ya d’auki d’amarar sata taci dan dolenta koda bata da ra’ayi.

Ko kunyar su mummy baya ji haka zai ta lalla6ata akan ta ci abincin ita kuwa tayi ta yanga da shagwa6a, haushi kamar yakashe Abbas amma adole yake mazgewa.


******
Gani yayi abin nata sai k’ara gaba yakeyi gashi indai aka zauna sai ta sako hirar Mahmud,abinci kuwa sai abinda yayi gaba.

Abbas ma daga baya daina zuwa kan dinning d’in yayi gaba d’aya, da farko mummy ta tura Teemah akan tak’ira sa sai yace mata he is full,the following day ma haka sai dai wannan karon da taje ki’ran nasa cemata yayi taje ta kawo masa abincin ad’aki zaici.


Zuwa tayi ta had’o takawo masa,tana shirin fita ya tsaida ta kamar wanda zaice ta mik’a masa wani abu amma sai jitayi ya tambayeta wai ” taci abincin ne ita”
kai ta jijjiga masa alamar a a, ai kuwa ya tsareta yace wai dole sai taci abincin data kawo masa d’in inbata ciba kuwa shida ita ne dan harbeta zaiyi da bindigan sa wai kanta zai fasa babu abinda ya damesa.Aikuwa tazauna ta hau cin abincin adole duk da ranta bayaso amma haka ta ta turawa, shikuwa yana kwance abinsa da wayarsa a hannu yana ta aikin dad-dannawa, data ga ta k’oshi sai kawai tafara hawaye.
+

Allah ya taimake ta adaidai lokacin sai ya d’ago kai ya kalleta da niyar ganin ko tana ci d’in ne ko kuma a a, sai yaga taci ma kusan rabi amma tana kuka, suna had’a idanu kuwa ta sake kukan nata mai sautin sa ya bayyana.

Dariya tabashi shikam amma sai ya tsare bai dara ba.

Tashi yayi ya zauna kafin ya zubo da k’afafun sa k’asa sannan ya sake kallonta.

“Miye kuma na kukan?
Ya tambayeta.

Batayi magana ba kawai sai ta cigaba da kukan ta abinta.

Kyaleta yayi kawai yatsaya kallonta tana kukan kusan mintina biyu sannan yasake magana “idan bazaki fad’a min ba kimin shiru inba haka ba Allah makeki zanyi”

Cikin shash-shek’a tabashi amsa da
“nah………nah……k’oshine……….daga k’arshe taja dogon ajiyar zuciya.

Sosai maganar ta d’in ya k’aramar dariya amma sai ya jijjiga kansa kawai”yarinyan na bazaki ta6a girma ba”
ya fad’a acikin ransa sai yayi murmushi agefen bakinsa.

“Tashi kije”

Yafad’a yana komawa kwanciyar daya tashin.

Ai tana jin haka tayi saurin mik’ewa tsaye ta tattare plates d’in ta fice da sauri, shima bayan ta yabi da kallo aransa yace

“mara kunyan banza kawai, nida kene ai a gidannan”.

Tana fita ta wuce kitchen ta ajiye plate d’in sai ta wuce d’akinta,tana shiga kuwa tafad’a kan gadonta taringa kuka mara dalili amma deep down tana tunawa da Mahmud ne dan tasan da yana nan da hakan bai faru ba, da shikam tayata ci zaiyi ya,a bata abaki amma wannan shi sai bala’in mugunta.

Washe gari ma da aka zo cin abincin haka mummy tayi ta kwalla mata k’ira dolenta ta fito tazo tasami mummyn.


Mummyn cewa tayi

“yiwa yayanki magana maza yazo yaci abinci”

Baki ta tura gaba tayi kamar zatayi kuka, mummy kanta ak’asa yake bata ma lura da abinda TEEMAH tayi ba.

Ganin haka yasa Teemah juyawa tanufi d’akin nasa ranta amatuk’ar 6ace.Knocking tai tayi daga waje shikuwa yana zaune agaban d’an k’aramin madubin d’akin yana jinta ya k’i kulata dan yasan itace inba ita ba babu mai mar irin wannan iskancin.
Ganin ank’i kulata ne yasa ta tura k’ofar ta shiga a hankali, take taja ta tsaya dan ganinsa datayi zaune akan kujera yana gyaran fuskarsa, sai jin haushin ta ya k’aru fiye dana d’azu, a tunanainta barci yakeyi aai kuma taganshi a zaune.

Azuciyarta take ayyana “dama yana jina yak’i kulani dan salon wulak’anci kenan, dayake gani k’aramar danga amma daya je wurin waccen yarinyar ai tana fitowa shima ya fice ya tareta ahanya irin ma kar ya 6ata lokaci ranta ya 6aci d’innan”

Haushi ne ya k’ara kamata sai ta kalleshi dayake bayansa take iya kallo sai kawai ta banka mar harara.

Karaso wa tayi kusa da shi,ta tsaya

“Yayah ina yini”
tafad’a tana wani kauda kai.

“Banganshi ba” yabata batare da ya kalleta ba.

Juyowa tayi da mamaki ta kalleahi dan ita tasan ba wani abu ta tambaya ba, giransa d’aya ya d’aga mata sama sai taga ya bala’in yi mata kyau take abinda ke ranta d’in ya kau ta hau wassafa kyaun sa aranta, dan d’an zaman da yayi agidan har fuskarsa tafara tara gashi, kuma ya mar kyau dan sanda yazo gidan babu komai akansa da fuskarsa amma yanzu kam duk sun fara fitowa kuma sosai suka masa kyau.l suka kar6esa.Sosai taji ya birgeta musamman data ga shima hankalinsa nakai alamar shima yanason abin.

+

Ta6e baki tayi ta maida idonta gefen madubin sannan tace

“mummy na k’iranka”

Juyowa yayi kamar baisan da tsayuwarta agurin ba tun farko.

“Baki iya sallama bane?

Ya tambayeta idonsa k’ur akanta.

Kasa tayi da kanta da wuri batare da ta k’ara yin wata magana ba.

Bayyanan niyar murmushi yayi wanda azahiri sautin ya bada
“hmm”

sannan ya juya yaci gaba da abinda yakeyi “kije in abinci ne ki had’o ki kawo min nan d’aki”

Tana jin haka ta juya ta nufi hanyar fita aranta ta ce

“Nikam na shiga uku na, yau kam Allah yasa bani zai sa cin abincin ba”

Haka taje ta had’o tana ta farga ba jikinta har rawa yakeyi tsabar tsoron kar yasata cinyewa sai tasaka abincin d’an dai-dai.

Yaukam cikin sa’a sai yace mata ta zauan tajirasa idan yaci sai ta wuce da plates d’in.

Tasabar farin ciki har sai da tayi murmushi duka yana lura da ita.

Tun da ya fara ci bai d’ago ya kalleta ba, kansa da hankalinsa ya tattara gaba d’aya ya bayarwa abincin.

Kamar wasa ya fara ci sai gashi kuwa yacinye tas.

Kuma sai daya cinye d’in kafin ya d’aga daidai ta kalleshi sai suka had’a idanu sai abun yabasu dariya gaba d’aya amma murmushi suka yiwa juna.

Yana murmushi yace ” kinga ai yau d’in na rowa kika sako min gashi yamin kad’an”

Sai kuma yafara yunk’urin mik’ewa
yana fad’in
“jeki k’aro min”

Ai kuwa da rawar jiki tatafi k’aro wan takuwa d’ibo yanzun harda na mugunta ganin d’azu bai sata taci ba shine ta k’aro da farin cikinta.


Koda ta dawo sai ta sameshi atsaye yana 6alla botton d’in rigar jikinsa.

Shigowa tayi ta ajiye masa tana shirin shirin juyawa ya dakatar da ita akan cewa ta tsaya ta daman wannan nata ne shi ya riga da yaci nasa.

So wannan nata ne kuma tayi da wuri dan fita zaiyi yana da gurin zuwa,irin najiya yace maza tacinye tas.

Sai ta d’ago da sauri ta kalleshi,da alamar mamaki “uhhhm” yace mata da alamar shima amsar mamakin nata yabata.

Sai itama tace
“Abincin fah yawane dashi yaya”

“Ahakan nan kuma zaki ci ‘yan mata”

Fuskar tausayi tayi zata fara magana ya dakatar da ita da fad’in “hurry up pls nace miki zan fita ko”

Sai tace
“Toh kaje abinka yayah Allah zanci”

“Gani yaro ko Teemah”
Yafad’i yana kallonta

Jijjiga masa kai tayi da sauri sannan tafara chin abincin dan taga kamar tafara k’ureshi.

Haka tafara tura abincin da kyar data k’oshi sai ta karkata kanta gefe tana kallonsa da ido ruwa-ruwa.

Ji yayi ta bashi tausayi gashi kuma shima yana da uzurin fita sai kawai yace
“tashi kije”

Yauma da sauri ta tattare ta fice daga d’akin nasa amma koda taje kitchen d’in sai ta samu wuri ta zauna tana maida numfashi dan gaba d’aya taji ta wani iri kamar ba ita ba abincin data ta turawa ne suke sata jin numfashinta yana sama-sama.

Baabah Lami ce ta tambayeta ” wai lafiya kuwa Fatu”?

Kallon Baabah Lami d’in tayi batare da tayi magana ba.
Illah kauda kanta gefe datayi sannan tace
” Baabah Lami keda Yah Abbas ne kad’ai bakwa k’aunata agidannan”

Zaro ido Baabah Lami d’in tayi tare da fad’in “haba ke kuwa k’auna gaba d’aya?

“Ehh mana kullun sai kin k’irani da sunan da bana so shi kuma duk abinda banso shi yake sani yi kullun”

“Toh kiyi hak’uri an daina insha Allahu”

Baabah Lami d’in tafad’a tare da ficewa ta k’ofar baya.

Da kyar taji ta tayi d’an daidai sai ta tashi ta lalla6a tawuce d’akinta taso taje wurin mummy tace mata tayi masa magana ya daina sakata cin abincin dolennan amma sai ta tuna mummy ma ba goya mata baya zatayi ba.

Sai kawai ta wuce d’akinta tana rage kayan jikinta sai taji kawai tana son shiga bayi.

Da sauri ta wuce ta shiga bayin aikuwa bayan gida mai taurin tsiya ne ya matsa ta.

Da kyar tasamu yafito har sai da idonta ya cicciko da hawayen azaba.

Koda tafito sai ta kwanta agado tana maida numfashi.

Afili tace Gab ake da kashe miki y’arki mummy amma nasan kona gaya miki bayansa zaki bi bani ba”

Sai data huta kafin taje tawatsa ruwa tazo ta kwanta take kuwa bacci yayi awon gaba da ita.

Washe gari ma data tashi sai da tayi kashi kafin anan tayi wanka ” nikam Allah zai saka min wallahi, mutun wai in baiga yayi mugunta ba bai jin dad’i”


Haka ta shirya tafito dan har ta d’anyi latti ma.

About Ismail

Check Also

ABBAS CHAPTER 19

ABBAS CHAPTER 19 Haka a gida ma da yawan mutane na farin ciki da wannan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *