ABBAS CHAPTER 6

Advertisements

_____

ABBAS


CHAPTER 6
Zuwansu kano na k’arshe shine lokacin da Fatima take da shekaru hud’u da haihuwa.
+

sunje da farin cikin su kuma sun samu tarba agun yah Yusuf da Mahmud kamar yanda yake musu aduk lokacin da suka ziyarce su

Alokacin Mahmud ya yi girma sosai ya ‘kara wayo,shine ya kama hannun Teemah ya rink’a kaita neighbours ‘dinsu yana nuna ta wai suga ‘kanwarsa shima

Daya ke surutacce ne shi hakan yasa itama Teemahn ta sake jikinta dashi aikuwa sunsha yawo babu ruwansa

idan yazo yasa su Khadija agaba da surutu har baya gajiya da yi

“Anty kudawo nan mana muzauna tare!

“Anty kibar min Teemah anan kinji mun zuwa makaranta da ita”!!

“Anty in zaku tafi zan biku nima indai bazaki barmin Teemah ba” !!!

Khadija murmushi take binsa dashi kawai dan tasan acikin maganganunsa faruwar d’aya daga ciki zai yi matuk’ar wahalan gaske.

Tunda tasan tafiyah da Mahmud bazai ta6a yiwu ba dan Anty bazata bari ba kamar yanda ita kanta bazata iya barin ‘yarta a gun Antyn ba,itama daya ta tsira balle ‘yar cikinta.

Tana iyah hango irin hararar da Anty take binsa dashi idan yana irin wannan maganar,
Afili zaka fahimci manufar Antyn dan k’iri-k’iri take nuna bata k’aunar alak’ar Mahmud d’in dasu
abinda kuma zaiyi mata wahalar gaske wato yanke alak’ar dake tsakaninsu.

Dan Mahmud jininta ne,kamar d’anta yake,ba kama bama Mahmud ‘danta ne,me rabata da Mahmud kuwa sai dai Allah.

Sau tari takanyi mamakin halin Antyn ace k’arfi da yaji ka nuna baka son jinin mijinka,ada ta d’auka ko abin Antyn da yarinta ne idan tayi girma zata daina,amma sai taga sam bahaka bane,don zuwa yanzun ai Antyn ta manyanta,
ya kamata ace tasan dacewa da rashin sa basai an karantar da ita ba.

Satinsu d’aya tal suka koma Gombe abinsu,da d’umbin tsaraba daga Yah Yusuf harma da Alhaji muhammad.

Dawowar su kuwa baifi da 7months ba Yah yusuf ya tattara iyalansa gaba ‘daya suka koma Lagos da zama.

Kafin su tafin ma Khadija (mummyn Teemah) taso ta koma suyi sallama amma yah Yusuf ya hanata zuwa yace tayi zamanta kawai babu komai.

Bazata kawai tagansu a Gombe shida Mahmud,cikin sa’a kuwa alokacin Daddy yana gari,ranar kam tayi murna sosai dan wannan ne ziyarar farko daya ta6a kawo mata musamman dan ita batare da wani dalili ba.

Amma washegari da yamma suka koma Kano dan k’arasa shirye-shiryen tafiyar tasu bayan ya cika mummy da d’umbin alkhairai.

The next day sukayi sallama da Kano suka d’aga garin ikko.
Toh tun komawarsu Lagos mummy bata k’ara zuwa inda suke ba saboda nisan wuri,haka suma shiru,
sai dai suyi gaisuwa awaya ko kuma idan Daddy ya kawo musu labarin su dayake suna d’an had’uwa da Yah yusuf d’in wani lokaci saboda kasuwancinsu.

Anty kuwa komawa Lagos ‘din sai yazame mata abun farin ciki,dan ji tayi kamar dan ita akayi.

Da farko tana d’an d’agun kai da fad’i ma kowa,saboda tanajin kanta cewa ita d’in wata abace daban hakan yasa ta dad’e bata samu ko da wacce zasuyi maganar arziki ba ma balle huld’a.

Sai daga baya Allah ya had’a ta da wata jibgegiyar ‘kabilar mata.
Awajen saloon suka had’u acikin unguwan tasu,dayake Allah ya riga da ya tsara had’uwarsu sai bata yiwa matar irin halinta ba,tun a shagon saloon ‘din suka saba har da aka gama musu ma suka fito tare.

Ahanya ne suka fahimci cewa ashe ma a kusa suke da juna,shikenan tun daga ranar suka d’inke suka zama aminai na bugawa a jarida.

Anty chideh ake ‘kiran matar dashi haifaffiyar garin Lagos ce,sosai tasan Lagos fiye da zaton mai karatu,kuma zata d’an girmi Antyn da kusan shekaru hud’u zuwa biyar ahaife.

Zakuyi mamakin rayuwarta idan kuka gani bata da matsala da komai,sannan bata da ‘da ko guda d’aya rayuwarta take yi daga ita sai mijinta _na zo mu_ _zauna_ wanda ya kasance shine abokin rayuwarta alokacin.

Ba aure sukayi ba zamane kawai suke yi najin dad’i idan kaga yadda take ikonta shi abin har zai baka mamaki duk da yake ba ‘karamin mutum bane shi amma sharrin mace yasa yazama sokon cikin gida.

Anty ne ta shiga gidan ranar wata asabar domin haka suka saba ajunansu kowa yanada ikon zuwa gun d’an uwan sa aduk sanda yake da lokaci basa ta6a wuni basuga juna ba tunda suka san junansu.
+

Aduk lokutan da Anty take zuwa gidan bata ta6a had’uwa da mijin Anty chideh ba sai yau.

Mamaki ta tsaya yi bayan tashigo harabar cikin gidan,ganin yanda Anty chidehn tasaka babban mutun agaba yana wanke mata inners d’inta,ita kuma ta kame akujera sai taunan chewing gum takeyi tana bashi orders shikuma jikinsa na rawa yana bin umarni.

Duk da masu aikin da ke gidan da kuma loundary machine amma hakan bai hanata sashi yimata aiki ba dan kawai ta muzanta shi.

Abin haushi abin dariyah,da sassarfa Anty ta k’araso gareta Anty chidehn na ganinta kuwa ta washe hak’ora tareda mik’ewa tsaye.


Hannunta ta kama sukayi ciki,aparlourn Anty chidehn suka yada zango.

Gaisawa sukayi sama-sama da Antyn,gama gaisawan nasu keda wuya Anty Chidehn ta fara kwalla k’iran maid d’inta jin datayi bata amsa ba alamar maid bata kusa sai ta mik’e da kanta dan kawo wa Antyn ruwa.

Dakatar da ita tayi akan cewa tabari kawai bata jin ‘kishi ita.

“Why nah, ah’ ah”

Mum Mamud u don’t want to eat anything in this house why nah”
da fad’a da d’an 6acin rai.

Murmushi Antyn ta mata sannan ta bata amsa da harshen da zata fi fahimtar ta akan cewa bata buk’ata ne kawai shiyasa bazata sha ba.

Nan kuwa in kabar Antyn wai tana kyankyami ne ba zata iyah cin abincin daya fito daga hannun su ba.

Anty batayi k’auran baki ba kuwa tambayarta tayi ya akayi taga oga yana wankin inners bayan ga maid in ita bazata yi da kanta ba.

Nan Anty chidehn tayi dariya sannan tace mata kawai haka ta ga dama dama.

Antyn nuna mata tahau yi akan hakan ai bai kamata ba,tana rage masa darajar sa ne agidan kuma ma ai yafi k’arfin yin agareta.

Jin hakan yasa Anty chidenhn ta hau bata labari dan ita sosai ta yadda da Anty.
Dalilin da yasa ta ke mar hakan wai da farko aure suka so suyi amma danginsa musamman mahaifiyarta suka k’i ta wai bade ita ba sai de ya canja wata.

Alokacin kuwa suna son junansu hakan yasa suka gagara rabuwa har suka fara zaman su ba tare da kowa yasani ba.

Watarana Maman san sai takawo masa ziyara kawai sai ta ganta agidan,itama tayi mamaki dan atunaninta sun rabu da jimawa amma sai ta ganta agidan.

Atake kuwa ta tada musu bori da kyar yajata ya kaita gidanta yanata bata hak’uri harda alk’awarin zai sallameta aranar ma ba sai an kwana ba,don ko kad’an baya son 6acin ran mahaifiyarsa.

Itama Anty chideh taji haushin abin sosai zama tayi tafara tunanain mafita na yanda zata 6ullo ma al’amarin.

Shikuwa yana dawowa ya hau rarrashinta da bata baki akan tayi hak’uri akan abinda mahaifiyarsa tayi ma ya ciro kud’i masu yawa ya bata yace ta koma gida zuwa wani lokacin kafin yayi settling da ‘yan uwansa.

Bata yi musu ba ta kar6i kud’in daganan taje ta tattara kayanta ta tafi danbata so ya ga nacewarta.

Amma ga mamakinta tunda suka rabu bai sake neman inda take ba har kusan wata biyu sai abin yafara damunta.

Sai ta yanke shawarar dawowa taji inda maganar su ta kwana,amma cikin rashin sa’a data zo bata same shi ba wai yana Cotonou,haka takoma gida cikin jin haushin rashin samun nasa da batayi ba.

Wata guda ta k’ara kafin ta sake nemansa wannan karon kam ta sameshi agida,mamaki yayi daya ganta danshi har ya fara mantawa ma da al’amarinta.

Kusa tasa masa tazo da gudu ta rungume shi tana fad’a masa yanda tayi missing d’insa,shikuwa sai bubbuga bayan ta yake alamar rarrashi.

Daga k’arshe sai yasake bata hak’uri tare da jaddada mata haryanzu mum d’insa tak’i yadda kawai su hak’ura da juna yafi.

Tana jin hakan ta tashi afirgice tana kallonsa shi d’inma tashin yayi yana k’ok’arin yin magana kawai ta suri jakarta tafice da sauri tana me share hawaye.”Chiddy! +

“Chiddy!!
yafara kwalla mata k’ira amma tak’i waiwayowa tayi tafiyarta.

Tun daga lokacin ta fara neman hanyarda zatayi maganinsu gaba d’aya cikin sa’a kuwa ta samu.

Domin dakansa yaje har gidansu ya d’aukota ya dawo da ita gidansa.

Tace yanzu ko cewa tayi ya mari maman nasa toh kuwa marinta zaiyi da rawar jiki ma,rabonsa kuwa da zuwa inda mamar take har ita kanta ta manta,uwar cema ta ke d’an zuwa da kanta,idan kuwa tazo sai tace masa ya kulata kafin zaiyi mata magana,inkuwa bahaka ba harta tafi bazai kulata ba.

Tace yanzu maman ta daina zuwa musu dan kusan kullum idan tazo da kuka take komawa shiyasa ta hak’ura ta daina zuwa inda suke.

Anan Anty ta tambayeta “toh shi miye nashi laifin da har zata dinga bautar dashi haka.”

Anty chidehn cewa tayi wai haka ta ga dama.”

Har suka rabu mamaki bai bar Anty ba,sosai abin yatsaya mata arai har yasa tafara jin sha’awar aikata irin na Anty chidehn itama saboda guntuwar tunani.

Tun daga lokacin kuwa suka k’ara d’inkewa da Antyn sosai kamar wasa tafara bayyana ra’ayinta ga Anty chidehn.

Da Antyn chidehn taji tasamu passenger kuwa sai ta tayata k’iyayyar itama,nan tajata sukaje gurin mai mata aikin suka fad’i abinda suke so ayi musu.

Takuwa ci nasara don ba k’aramar katanga ta gina atsakanin iyalan gidanta da kuma mummy Khadija ba.

Tun daga lokacin zumuncinsu ya yanke kat.danshi yah yusuf har mantawa yakeyi da batun yana da wata ‘yar uwa aduniyah.


Sau tari zasu had’u da daddy har su rabu amma baya tuna tambayarta ma balle ya bada sak’on gaisuwa akawo mata.

Daddy kansa yana mamakin abin,shiyasa idan ya dawo in dai yasan mummy tasan da had’uwar tasu sai yace mata yah yusuf na gaisuwa.

Amsawa takeyi ita d’inma kawai bawai danta yarda shid’inne ya bada gaisuwar ba.

Dan ko awaya ta k’irashi ma bai fiyah tsaya wa ya saurareta ba,balle ya kaiga gaisuwa.

Uzuri ya fiya bata da alk’awarin sake k’iranta daga baya idan yasamu lokaci,ki’randa bazata ta6a gani ba kenan yawuce ta.

Sau tari kuka take yawan yi idan hakan yafaru daddy ne mai lallashinta ya kuma bata hak’uri akan abin.

Da k’yar ta zo tasaba da hakan dan da kanta ta ta fahimci ehh lallai Yah yusuf dagaske yakeyi yanzu yamanta da ita.

Daga baya sai abin yabi jikinta itama ta daina neman nasu koda awayar ma,amma bata ta6a mantawa dasu ba azuciyarta.

Watan su Yah yusuf hud’u da komawa Lagos Hassan (baban Abbas) shima ya k’aura yakoma Abuja da iyalansa.

Ganin hakan yasa daddyn Teemah yace suma su koma damaturun gaba d’aya tunda harkokinsa sunfi yawa acan.

Dasuka koma damaturun kuwa sau biyu Abbas yakawo musu ziyara alokacin daya samu hutu sosai sukaji dad’in zuwan nasa dan Abbas sam baida rigima irinta yaran nan,kuma mummy nason shi dan nutsuwar shi jininsu ya had’u da shi sosai.
Mummy taso Mahmud ma ya dinga kawo musu ziyara kamar yanda Abbas yayi sai dai inah haka bazai yiwu ba bata san dalili ba amma abin sosai ya ke damunta naganin har zuwa yanzu babu wata shak’uwa tsakanin ‘yarta da jinin yayanta.

Zuwan Abbas na ‘karshe a damaturun kuma sai alokacin suka fi sabawa da Teemah dan zuwa lokacin tafi da wayo sai dai kuma tunda ya tafi bai sake dawowa ba sai da ya girma yayi passing out d’insa.Wannan dalilin ne yasa da daddy ya kawo mata maganar cewa Mahmud zai zo yayi service d’insa a damaturu kawai sai tafara hawaye dan tunowa datayi da yayan nata da kuma barinta da ya yi k’arfi da yaji batare da wani ‘kwa’kw’kwaran dalili ba.Da daren ranar da Mahmud ya iso ne mummy takewa daddy k’orafin rashin kammala makarantar Mahmud d’in dawuri tace Mahmud d’in fah sa’an Abbas ne amma dubi yanda Abbas ya jima da kammala karatun degree d’insa amma shi Mahmud sai yanzu”
+

Daddyn cema ta yayi shima abin ya bashi mamaki da Yah yusuf d’in ya ce masa wai Mahmud zai zo dan yin service a damaturu har hakan yasa shi tambayar dalilin dayasa har ya makara haka!

Yah yusuf d’in ne ya bashi amsa da cewa “wallahi matsalar daga mahaifiyar sa ne.

“Hmm Allah ya kyauta”kawai mummyn tace daga nan tayi kwanciyarta tana mai k’ara godewa mahallici.


*****
Mahmud ma ranar kwana yayi batare da ya runtsa ba tunani kawai yakeyi akan halin mahaifiyarsa.

Tun lokacin daya kammala secondary school ta dage wai sai dai an kaishi k’asar waje yaci gaba da karatun acan shi kuma Abbansa yace sam d’ansa bazashi wata k’asa dan yin karatu ba tunda ga makarantu nan a Naija sai wanda ya za6a shi ba zai kashe kud’insa dan zuwa wata k’asa karatu ba, shi bai ma amince wa Mahmud d’in yaje ko’ina ba in dai har ba cikin Nigeria bane toh bada yawunsa ba”

Wannan dalilin ne yasa Mahmud d’in yajima bai cigaba da karatu ba,domin Mahmud d’in kansa da farko ya yi na’am da batun fita abroad d’in amma daga baya daya ga abin kanshi yake shirin cuta sai ya hak’ura kawai,
dan ganin Abbansa bashi da niyyan canja ra’ayinsa kamar yanda Anty ma ta nace akan nata ra’ayin.

Ganin hakan yasa ya yanke shawarar cewa shifa zaiyi karatunsa koma a ina ne yafi mishi da wannan zaman banzan daya keyi.

Akan wannan maganar Anty har fushi tayi dashi wai dan yak’i amincewa da batun data zo dashi,kuma aganinta wai taimakonsa takeyi.

Da kyar ya sha kanta ta hak’ura sai da ya bata baki sosai akan hakan kafin ta hak’ura ta barshi.

Cemata yayi ta bari yayi wannan d’in inyaso idan yagama inzai cigaba sai ya nema awajen ai duk d’aya ne.

Ran Anty baiso ba ta hak’ura duk da irin aikin datasa akayi mata akan al’amarin amma wannan karan batayi nasara ba.

Koda Mahmud yajewa Abbansa da batun zaiyi karatunsa a Naija ba k’aramin dad’i Abban nasa yaji ba har hakan yasa ya bud’i baki yayi ta sanbad’o masa albarkatai gwanin birgewa.

UNILAG mahmud ya nema ya fara karatunsa kamar wasa sai gashi kuwa ya kammala lafiya k’alau.

Toh gurin cika service ne yayi abinsa batare da shawaran kowa ba,dan abin Antyn shima yafara damunsa gani yayi kokad’an bata son yayi ma zancen Antynsa Khadija balle yayi zancen zuwa wurinta.

Hakan yasa ya cika service d’insa da Yobe dan yana da labarin Anty Khadijan nasa a Damaturu jihar Yobe take da zama kuma abakin Antyn yaji hakan.Itace da kanta ta fad’a masa watarana daya tambayeta,da fad’a-fad’a ma tabashi amsar amma shi ko ajikinsa bai damu ba tunda dai yaji.

Dama niyyansa ya sand’i jiki watarana ya taho Yoben batare da sanin kowa ba amma kafin hakan ya yiwu sai Allah ya dubi niyyarsa ya aiko masa da batun service alokacin da baiyi zaton hakan ba.

Dan har ya isa wurin cikawan ma tunanin cika yobe bai zo kansa ba,wani yaji daga gefensa ya ambato yoben a maganarsa
sai kuwa yaji.

Take shima sai ya tuno da batun Anty Khadijansa.

Murmushi yayi daya tuna wannan ma babban chance ne Allah ya aiko masa tunda iyayensa basu san zumunchi ba,shikam zai yi ne ko ta karfi ma sai yaje yoben nan ko nawa zai kashe kuwa bashi da matsala da hakan matuk’ar zaiga kansa acikin jihar yobe toh he can do anything just to see himself there.

Iyayen nasa dukkansu babu wanda yayi tunanin zai cika da nisa shiyasa ma babu wanda yasa al’amarin akansa.

Cikin sa’a kuwa list na fara fitowa sunanshi ya fito acikin sunayem y’an tafiya yobe state.

Farin ciki yaji kamar yayi fiffike ya tashi sama amma haka ya 6oye murnar tasa acikinsa adole ya sakawa fuskarsa 6acin rai lokacin daya shigo gida.

Koda yazo da slip d’in gida ma mik’awa Abbansa yayi tare da fad’awa kan kujera batare da yayi magana ba.

“Me nake gani ne haka Mahmud?
Abban ya tambaya yana mai sake kallon papern da kyau.

“Abbah yobe aka turani fah”

Zaro ido Abban yayi waje tare da fad’in yobe kayi mai kuma?

“Bautar k’asa Abbah” Mahmud ne yabashi amsa da wani tsarewa alamar shima bayason gurin.

“Haba Mahmud shine har can saboda Allah!

“Abbah toh ya zanyi an riga an cire list d’in bansan yanda zanyi ba,nima yamin nisa gaskiya,
amma dai zan gwada sa’a ta nagani ko za’a dawo dani kusa”

“gaskiya kam ka gwada amma ai yobe yayi nisa sosai.”

Mahmud bai k’ara magana ba illah tsayawa da yayi yana kallon Abban nasa da mamaki,ganin dayayi kokad’an bai kawo batun y’ar uwarsa dake zaune acan d’inba ko kuma irin yayi farin ciki da hakan yaru ba kamar yadda ya saba.

Aganin Mahmud ai murna ya kamata Abban nasa yayi dayaji batun zuwansa yoben bawai yayi againsing ba,amma ga mamakinsa sai yaga ko ya nuna alamun irin da wani nashi ma acan d’in baiyi ba balle ace zai k’arfafa tafiyar kodan dalilin Anty khadijan.

Lokuta da dama yana mamakin irin
girman laifin da Anty khadija tayiwa Abban nasa da har yasa yake kaucewa duk wani al’amari dazai shafeta.


Gagara hak’uri yayi har baisan lokacin da ya bud’i baki ya tambayi Abban nasa ba.

“Abbah meyasa kamanta da Anty khadija ne?

Yah yusuf najin abinda Mahmud d’in yafad’i sai ya d’ago fuskarsa da sauri ya tsurawa fuskar Mahmud d’in ido kamar wanda akace zai ga wani abu akan fuskar Mahmud d’in idanuwansa har tara ruwa suka yi.

Gani hakan yasa Mahmud lumshe idanunsa tare da d’auke fuskarsa daga saitin daddyn yamaida shi inda yaji takun tafiyah anan ya k’arasa bud’e idanun nasa ya sauk’e su akan K’afar Anty dake tahowa da takunta na k’asaita.

“Ha- ah
“yah na ganku jigum-jigum haka?
“Meke faruwa ne?

Tana maganar ne tare da hanzarto wa izuwa garesu.

Abban ma sai da yaji muryarta kafin ya d’auke idanunsa daga kan Mahmud d’in ya maida shi kanta.

‘Zuwa tayi ta zauna a gaf d’in dake tsakaninsu,sannan ta maimaita tambayar tata.Mahmud bai kalli inda take ba ya bata amsa da fad’in Anty service d’ina Yobe state yafito”
+

Hannunsa yana yawo akan fuskarsa yayi maganar.

Karkuso kuga yanda Anty ta firgita daga jin an ambaci yobe har taso k’ara saka Mahmud cikin tunani amma sai ya waske.

“Haba no wonder naganku jigum-jigum ai dole”

“Su rasa inda zasu kaika sai wancan garin?

Dukkansu kallonta sukeyi yanzu kam,kowa da abinda ke ransa.

Abbah so yake yayi maganar ‘yar uwarsa Khadija amma azahiri yakasa furtawa,aransa kuwa harhad’a maganar yakeyi tsaf
“Yauwa Alhamdulillah fad’uwa tazo dai-dai da zama tunda Khadija nacan ma na tabbata baka da matsala da komai”

Maganar dake ran Abbah kenan amma afili ya gagara furtawa,nawi yakejin harshensa yakeyi akullum indai akan Khadija ne.

Mahmud kuwa mamaki yakeyi aransa shima naganin ko Anty ma bata kawo batun sauk’in da hakan keda shiba ganin Anty Khadija nacan ko kuma irin yaga ta nuna farin cikinta akan faruwar hakan.

Alwashi yaci aransa nasa cewa sai ya tambayi Anty yaji ko me Anty Khadija ta musu suka tsaneta haka,kowa baya son abu agidan indai al’amarin yashafeta ne.

Ahakanma gara Anty dan ita idan ya tambayeta abu tana d’an bashi amsa koda kuwa da fad’a-fad’a ne sa6anin Abbansa da ko magana baya masa indai ya had’a da batun Khadija ne toh sai dai kallo da idanu
babu magana ko kad’an.

Abbansa bai ta6a bashi amsar tambayoyin dayake masa ba akan Anty khadija ko da kuwa sau d’aya.

Washe gari kuwa yaje yasamu Anty da tambayar laifin da Anty Khadijan ta musu da har suka d’auki irin zafi haka da ita!

Masifa Antyn ta fara masa kamar ta ari baki garin masifar ne ta d’an kuskure ta ce masa
“Bana son fitina Mahmud kai komai sai ka bishi da tambaya ne?
Meyasa bazaka bar komai ayanda kaganshi ba?
Ina zaman zamana kar ka kuskura kaja min fitinar dana kwantar da ita da kyar”

“Fitina kuma Anty wace iri?

Ya tambayeta da mamaki kwance akan fuskar sa.

“Irinta uwarka”?

Tabashi amsa kai tsaye.

“Ah ah naji ne kince kin kwantar da ita da kyar toh kuma ni bansan fitinar ba Anty laifine dan na tambaya?

“Katashi kaban wuri ni banason hauka”

Ta fad’i da matukar 6acin rai dan zuwa yanzun sosai ranta ya fara 6aci dan ganin Mahmud d’in nason ya k’ureta.

Bud’an baki yayi zai sake magana ta mik’e tsaye kamar andannna mata remote hanyar fita ta nuna masa

“I said get out from this room now”

Da wata uwar tsawa tayi maganar hakan yasa ya mik’e tsaye yana k’ara gyara zaman rigar dake jikinsa har ya fara tafiyah sai kuma ya juyo ya kalleta sannan yace

“Hakan da kuke yi ne yake k’ara samin sha’awar tafiya wancan garin dan na san meke faruwa na tabbata zanji koma menene acan d’in ba kamar yanda kuka barni acikin duhu b………

Bai k’arasa ba ta kar6e maganar

“Mahmud kar ka ce min da kanka kacika wannan garin dan ka muzanta ni……..tak’ara sa maganar tana nuna kanta da yatsanta.

Murmushi yayi sannan ya lumshe mata idanu.
ga dukkan mai wayo yasan hakan dayai alamar tabbatarwa yayi mata.

Haushi sosai taji sai kuwa tace
“Za ko kaci ub……..?Juyawa yayi ya fara tafiyah ahankali yana jijjiga kansa
yana fad’in “yau kad’ai Anty kin koyi zagi narasa ma’anar hakan fah”
+

cewa tayi
“Eh zaka ce haka mana dake ka maidani sa’ar ka,zanga kuwa ubanda zai barka kaje can d’in ai, idiot”

Bai kulata ba yanzun kawai ya
cigaba da tafiyarsa har yabar cikin d’akin,yana k’ara jin mamakin Antyn yanda ta wani d’au zafi akan wannan simple abun.

Ai dole ma naje kodan na
tambayi Anty Khadija abinda ta musu suka tsaneta haka.


Kwanaki na k’ara ja lokacin tafiyar Mahmud na sake k’aratowa,kamar yanda hankalin Anty ke k’ara tashi akan batun tafiyar,ita aganinta tasamu ta d’an sake babu batun dangin miji ya zai je ya jaji 6o mata jaraba tana ji tana tana gani.
_Kuji fah ikon Allah_

Babu irin k’ok’arin da batayi ba akan tafiyar amma abun yaci tura gani take kamar ma himma take k’arawa Mahmud d’in akan tafiyar.

Shikuwa dagangan yake komai akan batun tafiyar duk dama har yau Abbansa baice komai akai ba amma yanda Antyn tayi reacting so yake yaji dalilinta nayin hakan kuma tak’i sanar dashi asalin dalilinta dan haka yake abinsa da gangan dan yata tunzura ta ko zata yi zuciya tafad’a masa dalilin amma shiru.

Sai dai tayi ta hantarar sa kamar wani yaro d’an goye ga wani zafin rai data d’auka ta d’orawa kanta da ya rasa manufarsa kwata-kwata.


Tafiyar saura baifi sati ba ne Daddyn Teemah yazo Lagos anan Abbansa yake fad’a masa cewa ai mahmud d’in zai zo Yoben Bautar k’asa.

Daddy dayaji hakan bak’aramin farin ciki yayi ba musamman kodan matarsa Khadija yasan zatafi kowa farin ciki da wannan batun,amma bai nuna zak’ewarsa ba tunda yaga yanayin Yah yusuf d’in asanda yake maganar shima bawani farin ciki ya nuna da faruwar hakan ba.

Sai dai duk da haka sai da yatambayi meyasa kuma sai yanzu Mahmud d’in zaiyi service?…… me yasa baiyi karatun da wuri ba?………

Amsa Abbah ya bashi atakaice.

Haka suka rabu da Yah Yusuf d’in Daddy nacewa Allah ya kawo shi lafiya ina nan ina jiran isowarsa.

Shima dagangan ya daina sako zancen Khadija a tsakaninsu dan ganin kamar yah yusuf d’in baiso.

Dan idan ya matsa masa da tambayar ya sanar dashi laifinta kodan ta nemi yafiyarsa ma sai yaga yatsaya jim kamar an dasa shi wani lokaci har k’walla yake sharewa amma still bazai bada amsa ba.

Ana washe gari Mahmud zai tafi ma Antyn kamar ba d’anta ne zaiyi tafiya ba,ita adole fushi takeyi dashi har wani lokaci ji yake kamar yafasa tafiyan amma inah sai yaga bazai iya ba yazama dole ne ma yaje shi d’in.

Zuwa yayi ya zauna akusa da ita sai tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da kallon television d’in data keyi.

Shima sai ya maida kallonsa zuwa inda take kallan sannan ya fara magana

“Yanzu Anty fisabilillahi kin kyauta min?
ace zanyi tafiya amma ko kulani ma sai ki dai nayi bayan kinsan dole ina buk’atar sa hannunki ashirin da zanyi?
Ni ne fah Anty ki ganni dakyau fah idan na tafi ba dawuri fa zan dawo ba”

Amsa shi tayi da

“Sai mai toh Mahmud,idan katafi dan Allah karka dawo Har abada kaga ko zan damu”

Ido ya zaro waje tare da fad’in “har abada dai Anty”

“Uhm,ka gwada mana kagani”
ta bashi amsa.

“Niii d’in “ya kara tambayarta

Harara tabisa dashi kawai

“Toh aini Anty bazan iyaba,ina zan iya rayuwa babu ke akusa dani!”

“okay sai yanzu kasan amfani na kenan,daka maida ni tamkar abokiyar wasan kan kamanta ko?

“Bahaka bane fah Allah,haba Anty kefah uwace ,kar kifiya son kanki dayawa mana,ki tuna abaya dalilin bin umarninki nayi shekaru ina zaman banza agida batare da na k’ara sa makaranta ta ba,alokacin fah dakin bari nayi na tabbata da yanzu na wuce wannan level d’in da jimawa,amma haka na biyeki daga k’arshe kuma bagashi ba ahakan dole nayi batare da burin naki yacika ba.
Toh wannan d’in ma haka kike so na kuma yineh?
Bayan inada right d’in yin hakan Anty?bama wannan ba
Nidai dan Allah ki daina fushin nan kisamin albarka awannan tafiyar tawa.” +

Kinji”.

Haka yayi ta lalla6a ta harta sauk’o daga fushin amma dai har yanzu ranta bai d’auki tafiyar ba.

Haka dai ta hak’ura tanaji tana gani washe gari ya kama hanya yayi tafiyarsa dolenta tayi masa fatan Alkhairi badon taso ba sai dan son da take masa a matsayinsa na d’anta k’wallin k’wal a duk fad’in duniya.

Juyi mahmud yayi zuwa d’ayan gefen sannan yace wannan tambayar ta dawo kanki mummy dole in tambayeki dan so nakeyi in sami amsa ta kafin nabar garin nan.
_Back to labari_ ……..


Sam Mahmud baiyi wani baccin kirki ba adaren,sai kusan 3:00 o’clock kafin baccin ya d’auke sa bayan yayi sallahr nafila sannan yayi baccin.

Sallar asubah ma da kyar ya yi ta acikin d’akinsa,saboda baccin dake fisgar idansa,yayin da su Abbas suka wuce masallaci dan sunta mar knock amma bai bud’e k’ofar ba a tunaninsu baccin gajiya ce ta d’ebesa basu san cewa kwanan zaune yayi ba shikam.

*****
Washe gari ma Mahmud bai fito ba sai kusan 10:16am
kafin suka ganshi.

Ad’aki ya samu Abbas yashiga da sallamah abakinsa amma bai tsaya jiran umarnin shiga ba ya shiga abinsa.

Abbas na zaune akan cough da system a gabansa sai kawai yaga mutum yashigo,danshi sam baiji sallamar da mahmud d’in yayi ba dan gaba d’aya hankalinsa yatafi ga abinda yake kalla.

Juyawa yayi suka had’a ido da Mahmud take sai mahmud d’in ya mik’o masa hannu.

Shima hannun ya mik’a suka tafa

“Ya ne guy u look bored,meke faruwa ne”?
Abbas d’in ya tambayeshi.

Tsaki kad’an Mahmud d’in yaja sannan yace “kabari kawai gajiya ce wlh”

“Hmm jiya danake koranka kaje kayi baccin ai iskanci kaso yimin sai gashi kuma tun ma ba’ayi nisa ba kana complain”

Abbas ne yafad’i hakan yana d’age gira sama.

Mahmud baiyi magana ba illah tashi da yayi tsaye sannan ya d’anyi mik’a,Abbas d’in sai ya sake binsa da kallo yana murmushi yace “sai wani abu kake fah kamar mace yanzu akan baccin ne kaketa wannan abin”?

“Allah baccin bai isheni ba ne”

“Sai ka koma ai ka cigaba dayi tunda bai isheka ba”
inji Abbas

“Mummy nakeso ingani ne shiyasa in badan haka ba ai ko tasowa ma bazanyi yanzu ba.”

Abbas d’in ma mik’ewan yayi jin Mahmud ya ambaci mummy.

Yace “muje toh nima ban shiga ba har yanzu”
Atare suka fito suka isa babban parlour,koda suka isa babu kowa acikin d’akin hakan yasa suka zauna akujera suna d’an hira.

Zaman sun baifi da 7minutss ba saiga mummy tafito,murmushi ta sake data gansu,sai kuwa ta nufosu fuskarta cike da annuri.

Haka tazo ta zauna suka gaisa ta tambayi Abbas ya yanayin garin yace “Alhamdulillah mummy” +
“Masha Allah” tace
Sannan ta juyo ga Mahmud shima tamai ya gajiyan hanya da kuma bak’unta,
cewa yayi “wlh mummy jinayi ma kamar yanzu ne nayi tafiyar tsabar gajiya”hmm” kawai Abbas yace
Mummy kuwa murmushi tayi sannan tace “sai a hankali ai”, gacan break fast d’inku a dinning Daddynku ma shikam yafita tun d’azu,bari na k’ira Teemah dan itama bataci ba ni tun safe ma banganta ba” +

Tana fad’a tamik’e tsaye.

Amma sai Abbas yadakatar da ita da fad’in “haba mummy dakanki?
yi zamanki bari na mata magana.”

“Toh shikenan tunda ka hutar dani ai.”

Tayi maganar tana komawa a inda ta tashin.

Abbas kuwa wucewa yayi kamar da gaske,ya nufi d’akin Teemah,daya isa bakin k’ofar sai kuma ya tsaya,sai ya rasa ya zaiyi ma,to k’ira zai kwalla mata ne ko kuma sallama zai mata idan tafito sai ya hankad’a keyarta zuwa parlourn.

Rasa wanda zaiyi acikinsu yayi,sai kawai yasa hannu ya tura k’ofar ahankali ya shiga ciki.

Gani yayi d’akin bakowa,sai ya hau rarraba idanunsa,yaune farkon shigarsa d’akin nata tunda yazo gidan.

D’akin tsab ba wani datti sai dai tabar windown baya a bud’e.

Takawa yayi a hankali ya isa wurin windown,labilen ya d’aga sai ya hango yanayin wurin ya matuk’ar k’ayatar dashi.

Daga inda yake tsayen yana iya hango cikin lambun dake gidan nasu,sai yaji hakan ya matuk’ar k’ayatar dashi hakan yasa ya 6ata lokaci agun yana kallon wajen har ma baisan lokacin data fito ba.

Itama bata lura da shi ba dan yunwa na cinta sosai sauri ta ke ta shirya dan taje ta samu abinda zata ci,kuma kokad’an bata zaci wani zai shigo mata d’akin ta ba.

Allah sai ya taimaketa bata cire towel yau ba kamar yanda tasaba.

Gaban mirror ta wuce tazauna tana k’ok’ari d’auko man shafawan ta ne ta hango sa tacikin mirrorn,firgita tayi sosai take saita mik’e tsaye daidai shikuma ya juyo.

Kallonsa ta tsaya yi kamar yanda shima yake kallonta.
Tsawon mintina biyu kafin ya kauda kansa gefe.

“Astagfirullah”
Yace azuciyar sa sannan ya dawo da kallonsa kan fuskarta.

“Ya akayi ne kin wani tsaya kallona”

Batayi magana ba still illah k’asa da tayi da idanunta.

Ganin hakan yasa ya juya ya koma wurin windown.

“Meyasa kike bari abu’de?yajeho mata tambayar.

“Mantawa nayi”
Itama ta fad’a atakaice.

Barin wajen yayi yasake dawowa inda taken “kidinga kulawa idan zaki kwanta kinji”

kai ta d’aga masa alamar taji

Daga nan sai ya nufi hanyar fita harya kusan isa ga k’ofar kafin yace “kiyi sauri ki shirya ki fito mummy na k’iranki”

“Uhmn” ta masa masa dashi daga nan sai ya fice abinsa.

Sharp-sharp ta shirya tafito tasame su a palourn.

Zuwa tayi gefen mummy ta zauna sannan ta gaisheta daga nan tagaida su Abbas ma.

Mummy ce tafara mik’ewa tana fad’in “bismillanku”

Teeamh ce tafara biyo bayanta sannan su Abbas ma.

Bayan sun isa sun zauna ne mummy tace toh teemah tayi serving d’insu.

Tashi tayi ta had’awa kowa nasa sannan tahad’a nata ma daga nana ta zauna.

Mahmud ne ya lura da yanda take shan tea d’in yau ba bu yanga sai yace
“cin abincin daman zuwa-zuwa ne”Mummy ce takar6e zancen dafad’in “ai in kaga haka toh yunwa ne yaci k’aniyarta”
+

“Ai kuwa naga alama”yana
murmushi yayi maganar.

Abbas kama bai kulasu ba illah kallonta dayayi sun kuwa had’a idanu sai tayi saurin kawar da kanta gefe.

Itace tafara tashi a table d’in ta koma d’akinta.

Su kuwa suna gamawa Mahmud yace su fita yawo cikin gari.

Haka suka fice yayinda Mahmud kejan motar sikuma Abbas na gefensa azaune.

Yobe state university(YSU) suka je dan Mahmud yace akwai wani friend d’insa dake lecturing acan.

Basu suka dawo gidan ba har saida suka yi sallar azahar.

15minutes to 2 suka shigo gidan,direct kuwa suka nufo parlour dana tun d’azu Mahmud ke mitan yunwa yakeji kuma yayi-yayi da Abbas akan su tsaya wani wuri su d’an ta6a abu sam Abbas yak’i shi wai sai abincin gida zaici.

Zubewa sukayi aparlourn yayinda suna d’an ta6a hira.


Muryarsu ne yasa mummy fitowa anan ta samesu sun yi d’ad’d’aya akukera,Abbas sai mita yake yi wai Mahmud bashida dauriya ya fiya ragwanci.

“Mahmud kuma yace angaya ma yunwa ta tana yi da wasa ne?

“Toh cinye ni mana kafin abincin ya iso”inji Abbas

kafin Mahmud yayi magana sai sukaji muryar mummy tanace musu duk su taso abincin ai tun d’azu yake jiransu.

Sai alokacin suka lura da fitowarta,gaida ta sukayi ta amsa tana zolayarsu
daganan suka mik’e suka wuce kan dinning d’in gaba d’aya.

Tun kafin su isa mummy taketa kwalla k’iran Teemah, jin Teeman ta amsa ne yasa
mummyn yin shiru suka zazzauna.

Mahmud ne yace “wai ita mummy kullun wannan yarinyar sai an gayyatota cin abinci ne kafin takeci”

Mummyn amsa masa tayi da fad’in “ai inka barta kace sai ta nema da kanta toh kuwa zaka dade baka ganta ba,shiyasa nake sata ci acikin jama’an wai ko zata saba”

Mummy nagama fad’in hakan sai ga Teemah ta 6ullo,binta sukayi da kallo harta k’araso.

Abbas aransa yace “masha Allah” dan sai yanzu ya lura da kyaun datayi dukda bawai ta canza kaya bane tun na safen ne data saka ajikinta amma kuma sai yanzu ya lura da kyaun datayi dan d’azun bai kula da hakan ba.

Jiyayi yana jin zafin kallon da suke mata d’in gaba d’aya.

Zuwa tayi itama ta zauna akusa da mummy sai ya kasance tana tsakanin Mahmud ne da mummyn.

Mummy ce tace Teeman ta tashi tayi serving d’insu abincin.

Zaro ido Teemah tayi waje tare da fad’in”mummy nikuma?

Da “ehh mana Teemah” mummyn ta amsa mata.

Sai tace “amma mummy idan na saka kowa sai ya cinye nasa gaba d’aya”

“Naji ni dai tashi kisa mana abinci yarana duk yunwa suke ji”

Tana jin haka sai ta turo baki gaba sannan tace “wlh mummy kullun wareni kikeyi agidan nan tunda kika gansu,nima indai hakane gidan daddyn Abuja zan koma abuna”


Dariya tabasu gaba d’aya,amma sai dai mummy da Mahmud ne suka dara Abbas kam murmushi kawai yayi.

mahmud ne yana d’an dariya yace
“kai mummy ki barmin lil sis d’ina pls adaina 6ata mata rai”

“Hmm ni wlh dariya ma kike bani Teemah toh har ina abin fishin yake anan,kede Allah ya rabaki da mugun halin nan Teemah”

“Kauda kanta tayi gefe haushi kamar zatayi kuka.Mahmud kuwa ganin bazata saka musu abincin bane yasa shi fad’in “banace zan kaiki da kaina ba maza tashi kisa mana abinci kinji baby sis rabu da mummy” +

“Ai cemin tayi mai mugun hali”

“Sorry ‘yanmata wasa take miki fah”
ya fad’a yana kallonta.

Zata sake magana yace” haba mana Teemah yunwa fah nakeji”

Abbas kam sai rarraba idanu yake akansu ya kalli wannan ya kuma kallon wannan.

Dayaji mahmud yace yunwa yake ji ne shima yace “Allah dai ya shiryaka mahmud”

“Ehh naji haka kurun ai da gaskiyata ko so kake nayi shiru yunwan ta illatani ne”

“Kai kasani ai”
Abbas d’in ya fad’a dajin haushi

Daganan Teemah ta tashi tana turo bakin ta zuba musu abincin harda na mugunta sannan tasaka nata kad’an ta zauna.

“Hmm mummyn tace tana k’ara yin murmushi ahankali tace “Teemah ko rigima in ance mugun hali kuma tace ita ba ita ba,inbanda haka ina zasu kai wannan abincin.”

Bata kula magananar mummyn ba
Zama tayi suka fara cin abincin.

Wurin shiru bakajin k’aran komai sai na cokula.

Kowa yayi nisa dacin abincinsa yayinda Teemah kwata-kwata spoon d’inta uku sai juya cokalin takeyi a hannunta kamar mai k’rga abincin.

Mahmud ne ya lura da ita ganin bata cid’in ne yace
“Yadai kici mana keda kika ce kowa sai ya cinye nasa gaba d’aya,ahakn ne zaki cinye?”

Sarai tasan da ita yakeyi amma sai tak’i kulasa ko d’aga kai ma takalle sa k’inyi tayi.

“Barta mana wai ita sarkin wayo ba” cewar mummy

Mahmud kuwa barinta yayi
ya sake d’iban wani abincin yakai bakinsa,daganan ya d’ebi wani ya nufo ta dashi.

“hun haahh”
yace yana kallonta,itama da mamaki tabi abincin da kallo sannan ta kallesa.

“Open your mouth mana”
Yafad’a da seriuos tune

Sai da ta kalli mummy tukun sannan ta kalli Abbas sai ta ga dukkansu babu wanda hankalinsa yake wurinsu.

Bud’e bakin tayi yasaka mata abincin.Abbas kuwa duk abinda ya faru yana lure da shi,sai da yaga zata kalleahi ne kafin ya maida kansa k’asa tamkar tun zamansa awurin bai kalleta ba……..bata san tun d’azu yake lura dasu ba, jiyayi tamkar ransa zai fita ajikinsa data kar6i abincin,jiyayi ya gagara natsuwa sam,”innalillahi yake ta fad’i azuciyarshi bai san dalili ba amma sai yaji ya tsani wannan scene d’in.

Take tunanin baya ya fad’o masa arai,irin yadda yake kula da ita shima yake bata abinci abaki,yau ga wani daban ya fanshe shi……….

Haka yaci gaba da bata abincin ita kuwa kamar jira takeyi daman abata sai kar6a takeyi
mummyn kam cewa tayi “aikuwa aiki ya sameka Mahmud indai wannan ce”

Maganar tata ce ta dawo da Abbas cikin hayyacinsa sai alokacin ya lura ashe Mahmud cigaba da bata abincin yayi ko kunyarsu bayaji.

Shikuwa Mahmud zuciyarsa d’aya yake bata,dan yasan is not a crime tunda sistern shi ce.

Spoon kusan biyar takar6a a hannun Mahmud sannan tace ya isheta.

Wani uban tsakin da Abbas yaja harni ma na tsorata da ita,sai dai sa’an shi d’aya azuciyarsa yayi shiyasa babu wanda yaji.

Cak ya mik’e tsaye ransa amatuk’ar jagule amma babu wanda zai fahimci hakan sai wanda ya sanshi sosai,saboda yanayin yariga yazame masa jiki,shiyasa babu wanda yagane halin dayake ciki.

Ummansa kad’ai ke fahimtarsa aduk halin dayake ciki sai ko Daddynsa.

D’akinsa yawuce direct yana shiga ya hau fincike riga kamar ita ce tamai laifin.

Bayi ya shiga ya watso ruwa ya fito dayake yana ta fad’in “la haula wala kuwwata illah billah”acikin zuciyarsa tunda abin yafaru sai hakan yasa yad’anji sassauci.Kwanciya kawai yayi agadon dake d’akin sa cikin sa’a kuwa sai bacci ya d’auke sa.
+

Yayin da Mahmud yake can zaune da mummy Teemah kuma tashiga dan shirin zuwa islamiya.

Fitowa tayi da hijab d’inta ahannu tace “toh mummy na shirya yau wazai kaini”?

“Je ki d’auko kud’in adaidai ta ajakata”cewar mummyn.

Har Teemah ta juya da nufin zuwa d’akin mummy sai Mahmud yace ta dawo zai kaita.

“Dauko wanda zaki dawo dashi toh”mummyn tasake fad’i

Mahmud d’in ma sake cewa yayi “bari zan d’auko ta mummy idan sun tashi”

“Karfa a takura ka Babana”mummyn tafad’a tana kallon sa

“Haba mummy akan d’an wannan d’in”
Shima yabata amsar maganar tatta yana murmushi

Teemah hijab d’inta tasaka ranta fari k’al dan dama ta tsani hawan adaidaitan dan bata samu ma da wuri gashi ana zabga rana.

Koda suka fito kuwa Mahmud sai da ya lek’a d’akin Abbas da niyan sanar masa da fitar tasu amma sai yaga ma yana bacci.

Hakan yasa ya fito suka tafi abinsu.

Kamar yanda yafad’a d’in kuwa ana tashi yawuce ya dawoda da ita gida.

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

ABBAS CHAPTER 19

Advertisements _____ ABBAS CHAPTER 19 Haka a gida ma da yawan mutane na farin ciki …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *