[Advertisements⬇️]

ABBAS CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ABBAS


CHAPTER 5


Da malaman suka ji ya fad’i haka sai suka ce toh shikenan daman hakkin addini ne kuma dan gudun siga hakki ake son sauk’e shi,amma tunda yace haka shikenan,Allah ya k’ara musu hak’urin rashin dasu kayi,amma duk da haka sai sunji daga bakin manyansa tukunna,wasu daga cikin y’an uwan baban haushi sosai sukaji dan aganinsu Yusuf bak’aramin bak’in ciki yayi musu ba,amma da sukaji za’a tambayi manyansa sai suka d’an ji dama-dama dan sun zaci za’a samu sa6anin harshe ne.
+

Sai dai basu yi sa’a ba,dan da aka tambayi ummahn suma cewa tayi

” _a’a yanda idonta yaga jinin Baban ya zuban nan ko da sun kar6i kud’in gani zasuyi kamar jinin baban suka fansar,tsautsayi da k’addara ai abokan tafiyar dukkan wani halitta ne,babu wanda ya isa ya gujewa k’addararsa,Allah ya riga da ya rubuta inda ajalinsa yake kenan dan haka su basu da wani abin fad’a fatansu kawai Allah yah kyautata makwancin Baban
Ummah tana hawaye take wannan maganar,kusan kowa dake zaune agun sai da ya share hawaye,duk da zuwa yanzun abin yad’an bar zuk’atansu,sun riga da sun dangana tsakaninsu da Baban yamzu addu’a ce kawai.

“Allahu akbar”,

“Allahu akbar”

“Allahu akbar”

Babban malamin dake zaune agun ne yafad’i hakan tare da jijjiga kansa,d’ago wa yayi ya kalle su gaba d’aya sannan yaci gaba da cewa

“Hak’ika wannan kad’ai baiwa ce da Allah ya riga ya halicci ahalin wannan gidan dashi,kalamanku su suka bayyana hakan,ga dukkan alamu ba wani k’arfi ne daku ba amma wannan furucin naku yah tabbatar mana da cewa wadatar zuci abokiyar tafiyar ku ne,Allah kad’ai kuka dogara dashi,Hak’ik’a agurin Allah ku masu arzik’i ne da yardarsa,Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairi ya kyautata rayuwarku gaba d’aya daga yanzu har yaumul sa’a.

“Ameen-Ameen”!
sauran dake gurin suka amsa masa dashi,amma kowa jikinsa ya matuk’ar yin sanyi

Sake kallon Ummah yayi dake faman goge hawaye tun d’azu,sannan yace
“Kuyi hak’uri insha Allahu mutuwar malam hutu ce agare shi muna mishi fatan alkhairi insha Allahu,malam mutum ne da kowa yaji wannan mutuwar tashi ta matuk’ar ta6a zuk’ata da yawan gaske,amma dukkan mu yazama mana dolene muyi hak’uri,addu’a itace gatansa ayanzu”

Babban malamin ne yasake juyowa ga ragowar ahalin Baba yasake tambayarsu,suma da wuri suka amince sai bakinsu yazama d’aya dukkansu.

Da haka taron yawatse amma har aran Alhaji Muhammad ji yayi ya kasa hak’uri da wannan lamari ji yake bazai iyah kyalesu a haka ba
amma bai yi magana awurin ba yadai bar abinsa aransa ne kawai.

Dangin Baba kuwa haushinsu k’aruwa yayi akan nada, ji suka yi kamar su rufe ummah da duka lokacin da ta ke nata bayanin,koda aka zaga yo kansu da tambayar kuwa suma dan dolensu suka amince badan ransu yasoba,dan de kar aga zak’ewa da zilamar su ne,shiyasa basu canja baki ba,tunda bau wanda yasan meke acin ran su sai kowa ya yabawa wannan zu’ri’a ta mariga yi masu sanin ya kamata da girmama k’addarsu, inka d’auke mutune biyu dasuka kasance su d’in k’anne ne ga Baba,Mal.Hadi da mal.kallah sune kad’ai suka yi maganar datake har cikin zuciyarsu ne badan komai ba sai dan saboda Allah kawai, amma saura daga ciki duk bada son ransu suka amince ba,dansu aganinsu a irin yanayin talaucin da suke ciki kud’in ba k’aramin taimaka musu zaiyi ba,basu sani ba ashe irin kud’in nan baya kawar da buk’atar mutum dan tafiyah yake kamar ana hure shi,daga k’arshe ma karasa ya akayi ne ma yak’are gaba d’aya,inkayi wasa da tunani kawai zai barka,amma bansani ba kodan basuga yadda k’arshen d’an uwan nasu yakasance bane shiyasa tsoron rayuwar bata shigesu ba,domin kafin su iso har an sada baba da makwancinsa na har abada.Mal.kallah kanin marigayi Baba ne da suka kasance uwa d’aya su kad’ai mahaifiyar su ta haifah inda tarasu tun awajen haihuwar Mal.Hadi haka yataso baisan mahaifiyarsa ba da dad’i da wuyah haka de ya girma ahannun kishiyoyin uwa shida wansa,kuma sun kasance y’a’ya k’anana daga cikin y’ay’ayn da mahaifinsu ya haifa,dan mahifiyarsu itace ta k’arshe acikin matan mahaifin nasu while mal.Hadi kuma uba suke d’aya

Mahaifinsu ma masha Allah,dan ya mori duniya sosai,shekarar sa baifi uku da rasuwa ba yanzuh,tsufa yayi jigib cikin ikon _buwayi_ har baya gane mutane,kafin Allah ya kar6i abunsa.


*****
Alhaji Muh’d wanda yakad’e baban kenan kayan abinci yaci kasu dashi sosai iya iyawarshi,sannan yaci gaba da zuwa akai akai yana dubasu,kuma bai fasa yin azumin da shari’ah ta d’ora kansa ba.

Dangin mahaifin nasu kuwa tun daga ranar suka fita daga harkar su,basu k’ara waiwayarsu ba,kowa gudun d’awainiyah yake yi saboda yanzu sun zama marayu,mahaifiyarsu kuwa dama y’an cirani ne,ba’a san inda danginta suke ba tunda ta auri baba shikenan rabuwarsu da ahalinta.So basu san kowa daga 6angarenata ba.

Haka har Lokacin tafiyar Yusuf tayi,yatafi service d’insa,a Taraba state batare da wani fargaba ba,dan yanzu Alhamdulillah basu da matsalar abinci,domin sosai suke samun tallafi daga al’umma dan wani lokaci mutane basa tuna su taimaka maka koda sun san baka da k’arfi har sai sunga ka kwanta dama,alokacin ne zakaga zuciyar taimakon ta motsa, inkayi sa’a zuri’ar ka bazata wahala ba ko bayan baka,sannan ga Alhaji muhammad ma bai ta6a mantawa dasu ba,yanayin iyah k’ok’arinsa akansu wani lokaci har suna tausaya masa,na ganin kaddarar mutuwar baba tasa wani nauyi ya hau kansa batare da ya shiryawa hakan ba
sannan sunyi-sunyi dashi akan yad’an huta da d’awainiyar sam yak’i,sai dai yace musu shi saboda Allah yakeyi badan komai ba.
Kafin yah gama azuminsa rama yayi sosai kamar wanda yayi wata ka’aramar jinya,Addu’a kawai kawai suke binsa dashi dan itace kad’ai sakayyar da suke ganin zasu iyah masa,hak’kik’a yacika mutum managarci,ba kowa keda irin halinsa ba acikin mutanen mu na yanzu

Sau kusan biyar yusuf yazo ganin gida acikin shekara d’ayan da ya yi a taraban.

Yana dawowa kuwa Alhaji muhammad ya bashi jari,akan ya fara kasuwancin kansa da kansa,da kyar ya kar6i kud’in dan gani yake kamar sun d’orawa Alhajin wani nauyi ne na daban akan k’addarar da kowa bai isa ya tsallake ta ba,amma Alhajin yace sam dole sai ya kar6a,da yaga Alhajin yafisa baki sai yace toh yah rage yawan kud’in nan ma Alhajin yace shi abinda yayi niyyar bayarwa kenan so baze rage ko kada’n ba,haka dan dolensa ya kar6a,godiya kuwa shi kansa sai da ya rasa adadin daya ambace su,daga k’arshe ma Alhajin barin d’akin yayi ya barsa shi kad’ai aciki rik’e da kud’i,yana hawaye ya fito daga d’akin shima,karo suka ci. da y’ar Alhajin tana k’ok’arin shigowa itama,binsa tayi da kallo har ya fice agidan,dan take taji ya kwanta mata

Shikenan tun daga ranar ta nace masa mahaifiyar ta ma ta goye mata baya,har se da taga sun sami had’in kansa kafin nan ta sami salama.

Ga Alhaji muhammad kuwa bawai ba yason auren bane a’a shima yana matuk’ar farin ciki da kasancewar yusuf d’in sirkinsa dan ya yadda da tarbiyarsa sosai,
matsalar kawai maganan mutane yake gudu,kar wasu suce shi ya lik’a masa y’ar sa adole dan yaga basu da k’arfi,ko kuma dan basu da wani akansu yanzu

Amma da malamin daya wakilci auran ya fahimtar da shi cewa shi aure had’i ne na Allah,shiyake tsara abunsa aduk yanayin da yaso a kuma duk inda yaga dama,hakade malamin yata nusar dashi muhimmancin da hakan ke dashi, take kuwa shima yayi na’am da zancen,aka yi bikin lafiya aka kawo amaryar gidansu da suke zaune bayan gidan yasha kwaskwarima sosai.

Kuma Alhajin ne ya d’au nawin komai na bikin danma kar yusuf ya ta6a wani abu daga cikin dukiyar da ya bashin sai ya kar6e ya ajiye agunsa sai bayan bikin ya maida masa da abinsa.

Ganin yawan k’ud’in ne yasa yusuf yaje ga mahaifiyarsa neman shawarar sana’ar data dace yayi,cemasa tayi yayyayi kowanne ma inde yaga ta kwanta masa bata da matsala dashi matuk’ar yasan bazai sirka dukiyarsa data haramun ba toh yaje ya za6i duk sana’ar data mishi yayi.
+

Godiyah yayi mata tareda alkawarin insha Allahu zai tsaya akan iyaka halak d’insa ne bazai wuce hakan ba izinin Allahu.
Da addu’ar samun sa’a tabishi.

Rasa yanda zai yi da kud’in yai kwata kwata daga k’arshe sai ya k’ira abokinsa da suka yi makaranta tare mai suna kabiru dan yaga kamar su d’in ma harkar kasuwanci mahaifinsa yake yi,so aganinsa zai fi samun clue daga bakinsa.

Abokin nasa kuwa d’an albarka sai ya had’asa da mahaifinsa ya fara juya masa kud’in,watansu shida tare sai mahaifin kabirun ya ware ma yusuf iya tashi dukiyar tare kuma da ribar da suka samu akai,daganan ya k’ara ha d’asa da manyan y’an kasuwa da suke harka tare yace ya cigaba da harkokinsa shikad’ai dan sha’anin dukiyah wuyah ne da ita.

Yin hakan baifi da sati biyu ba Allah ya yiwa mahaifin kabirun rasuwa,Sosai mutuwar ta ta6a su gaba d’aya satin yusuf guda cif a Gombe wurin ta’a ziyar mahaifin kabirun sannan ya dawo gida cike da alhini,dan bazai ta6a manta karamcin mutumin ba,sai fatan Allah ya kai haske kabarinsa.

Ana raba musu gado kabiru ya taho kano yasamu yusuf suka yi shawarar yin kasuwanci atare,kabiru yanada k’anne biyu mace da namiji Sunan macen Zahra kuma itace ka’rama sai namijin mai suna Hassan ‘yan biyu ne shi amma d’ayan bai rayuba shekara ukune tsakaninsu da Hassan d’in,ko lokacin da aka raba musu gado ma kowa karbar nashi yayi danshi hassan tun shekarar data gabata yayi aurensa,auren gida Hassan d’in yayi shikuma kabiru ya tsaya yin karatu,Zahra ma tana gama secondary Mahaifinta ya aurar da ita rana d’aya da Hassan,alokacin da mahaifinta ya rasu ma ciki ne da ita

Sun fara kasuwanci lafiya lau kuma suna ganin haske aciki,Kwatsam sai suka wayi gari babu mahaifiyarsu Allah ya kar6i abinsa,tun daga lokacin kuma sai khadijan tashiga wani hali dan har alokacin ma bata k’are secondary ba,shekara kusan goma sha d’aya ne tsakaninta da yayanta Yusuf.

Matar Hassan kuwa ta haifi d’a namiji Hassan sai ya maida sunan mahaifinsu wa yaron wato _Muhammad_ ,sunyi matuk’ar farin ciki adangin gaba d’aya dan mahaifinsu mutumin kowane bade taimako ba,tun daga lokacin suka fara k’iransa da suna _Abbas_.


Zahra kuwa lokacin dazata haihu tarasu daga ita har y’ar data haifa babu wanda yayi rai acikinsu.

Hak’ik’a wad’an nan mutane sunga ikon Allah sai dai fatan Allah yajikan magabata .
“Ameen”

Yusuf shikada’ai wannan karon ma yaje ta’aziyar Zahra a Gombe,dan matarsa cikinta ya tsufah sosai.Bayan rasuwar Zahra baifi da 3 weeks ba matar Yusuf ta haihu,ta haifi d’a namiji mai kama da ubansa sak,yaro kyakykyawa dashi,tun da Khadija ta ga yaron nan ya shiga ranta sosai dan dama ita kad’ai ke rayuwarta bata abokin hira inde tana gida,
dan matar yayanta ba wani sake mata fuska take yi ba asalima shiyasa tun da aka haifi yaron nan farin ciki yacika ta,

Atunaninta zata samu abokin yin hira da wasa.

Ranar suna yaro yaci suna Mahmud,akayi shagalin suna aka watse,
Bayan anyi suna ne kabiru yazo ganin jariri,alokacin kuma yaron yana tare da Khadija ne so da yusuf yashigo da zummar kai wa abokinsa yaron sai ya gansa a hannun khadijan,
mahaifiyar yaron kuma tana bacci,kawai sai yace ta kaiwa Kabiru mahmud d’in yana can d’akin bak’i bari zai watsa ruwa yanzu,toh ta ce tare da d’aukan mayafinta tafita daga parlourn

Da sallamarta ta shiga d’akin ba’kin,daga ciki ya amsa mata

shiga tayi kanta a’kasa ta isa har inda yake zaune ta mi’ka masa yaron.

Kar6ansa yayi amma idonsa nakan fuskarta ganin ta’ki ko ha’da ido dashi.

Juyawa tayi da niyyan barin ‘dakin sai ya dakatar da ita yace tazo ta wuce da Mahmud d’in shi sauri yake y yanzu zai wuce,dawowa tayi kusa dashi ta tsaya,tsayuwar minti 3 zuwa hu’du tayi sai ya mik’a mata yaron bayan ya masa addu’a a kunnensa.

Leda ya sake mik’a mata a nan ne ta d’aga kanta ta kalle shi suka had’a idanu,da k’arfi ta gyara zaman yaron da ke ri’ke a hannunta,dan ji tayi kamar ze su6uce mata.

Dawuri tayi ‘kasa da idanunta ta maida kallonta ga mahmud da ke ‘dan motsawa saboda yanda ta matse shi a jikinta.

Sake mik’a mata ledar yayi tare da fad’in “kayan yaro na ne aciki naga kina wani tsorn kar6a”

Hannun ta d’aya ta mik’a ta kar6i ledar sannab tajuya,sai data fara tafiya kafin tace “angode”

Dan alokacin data kar6an idan akace dole sai tayi magana ma toh kuwa da sai de tasa kuka,dan ji tayi zuciyarta ta tsinke sosai da suka had’a idanun dashi,da zai lura ma da ya fahimci irin yanda jikinta ke rawa sosai.

koda ta koma d’aki kuwa rasa mai yake mata da’di tayi,shiru ta zauna tana tunani
tunanin da ita kanta bata san na menene ba.

Haka tasa Mahmud d’in da kayan agaba ta tsura musu idanu,kukan Mahmud ne ya fargar da ita,dawuri ta tashi ta ‘dauke sa tare da ledan da niyyan ta kaiwa Mahaifiyarsa shi.

Ha’duwa sukayi a kofar shiga parlournta,tana ganin su sai ta juya ta koma ta zauna,khadijan ma sai ta biyo bayanta

Saida ta zauna sannan tafara fad’in

“Daman zaman me kike min da yaro bayan kinajin irin kukan da yake yi tun ‘dazu dan salon rashin imani bazaki kawon shi ba”
Tana kar6ar shi ta ‘karasa maganar.
Karkata kanta tayi gefe sannan tace

“Ayyah Anty yanzu fah ya fara kukan shine na kawo shi”

“Dallah ni rufe min baki,wawuya kawai”

Antyn ne tayi wannan maganar tana ‘ko’karin sawa yaron mama abaki.

Ajiye ledar tayi tana shirin juyawa ta fice tajiyo muryar Antyn tana fad’in

“wannan fah malama zaki ajiye min abu batare kinmin wani bayani ba.”

Tsayawa tayi amma bata juyo ba tace “na Mahmud ne yah Kabiru ne ya kawo masa”

Tsaki Antyn taja batare data sake magana ba,domin ita asali jininta bai wani ha’du dana kabirun ba,kuma haka shima,shiyasa ko yau d’in ma dayazo bai nemeta dan su gaisa ba.

Yusuf dake shirinsa acikin ‘daki yanajin duk abinda suke fa’di amma bai kulasu ba.Ita ‘dinma bata san yafito daga wankan bane da bazata yi wa khadijan fa’da ba.

Sai da ya gama shiryawa sannan ya fito,kallon da ya mata ka’dai yasa tagane yaji abinda ta yiwa Khadijan.

Saboda a idonsa bata ta6a nuna wa khadijan tsana sai dai in abayan idonsa,saboda yanda yake nuna mata muhimmancin Khadijan a wurinsa.

Sosai tasha jinin jikinta,amma dayake ta riga ta yi nisa kuma tasan halin sa sai ta watsar da batun kawai.

Rakiya yayiwa abokinsa wani wuri kuma daga can ma yayi wucewarsa Gombe.

Yusuf sai da yamma lis yadawo gidan,dayake bashi da ri’ko sai bai dawo da wani 6acin rai ba,amma still abun yana ransa hakan yasa yamata maganar anutse,daman shi in abu yafaru adaidai lokacin yafi nuna 6acin ransa,amma in aka d’an ‘dauki lokaci toh shi kenan 6acin ran nasa ya kau.

Kamar de yanda ya kasance yau d’inma,atake kuwa ta nuna masa ai yau ‘dinma bada niyyah tayi ba kawai haushin kukan da taji yaron yanayi ne shiyasa tayi mata fad’an.

“Ni dai banaso pls ki kiyaye kinji”

Sai ta ‘daga masa kai alamar taji.

Kad’an daga cikin irin
rayuwar da Khadija takeyi kenan agidan yayanta tun bayan rasuwar mahaifiyarta,bata da sukuni ko ka’dan agidan dan ma tanada ha’kuri da kau da kai ga abubuwa.

Aikin gidan kaf ita ke yinsa,ga rainon Mahmud data riga ta saba da shi,ga masifah da hantara idan abayan idon yayanta ne.

Islamiyah kuwa tun haihuwar Mahmud bata ‘kara zuwa ba dan babu lokaci,bokon ma da ‘kyar take samu taje ahakn ma kusan kullum sai tayi latti.

Kuma a kullum sai ta dawo daga makarantar take d’aura abincin rana,dan babu mai yi Antyn bata yi,toshuwar da suke zama tare kuwa ba lafiyar idone da ita ba balle ta ringa yi musu girki,ga wankin kayan yaro duk tara mata akeyi idan ta dawo take wankewa,ga ‘daura ruwan zafi,ita zata ‘daura idan yayi ita zata ha’da ta kai ban’daki sannan ta dawo ta ha’da na jariri ma ta kai wa tsohuwa.

Alhaji muhammad hanata zuwa wankan gida yayi yace tayi zamanta a gidanta yafi,sai ya ‘dauko wata babarsa daga kauye yace su yi arba’in d’in tare.

Wankan jariri kawai tsohuwar keyi,dan ko wankan mai jegon ma Anty da kanta takeyi.

Alhaji muhammad ko mahaifiyar Antyn ma hanata zuwa gidan yayi,acewarsa baya son fitina.

Koda tace zata zo bayan da akayi suna ma sai ya ce sai dai zuzo tare da ita,haka ya sako ta agaban mota suka zo,basu wani jima bama ya ce su koma gida.

Haushin hakan yasa bata ‘kara maramarin cewa zatazo d’in ba.

Sosai zaka tausaya wa Khadijan agidan,idan ka ganta.
Amma ita hakan bai wani dameta ba dan tasan komai lokaci ne komai yanada ‘karshe.
Babu irin ha’kurin da batayi ba da matar yayan nata har suka gama kwana arba’in d’in,

Akwai ranar da zazza6i ya damu Khadijan harta je makaranta ma sai akace ta dawo ganin yanda jikin nata yayi zafi sai kakkarwa takeyi,Antyn ne da kanta ta ‘kira yayan khadijan tasanar dashi cewa Khadijan ta dawo gida da zazza6i,yanajin haka kuwa ya garzayo ya nufoh gida,asibiti ya kaita da gaggawa mafi kusa dasu aka duba ta aka rubuto musu magunguna da allurai,kafin suka dawo gida.

Fita yayi bayan ya dawo da ita gidan,yakoma ya siyo mata magani tare da kayan marmari,da kansa yazauna ya bata maganin tasha daganan yace maza ta kwanta tayi huta,tana kwanciyah sai bacci ya ‘auke ta,tun a baccin tafara gumi
cikin ikon Allah kuwa tana tashi a baccin tajita garau kamar ba ita ba,ganin hakan yasa Anty tace to ta goyi Mahmud tunda ta warke ita sai tayi girkin saboda yau ‘din rigima shima yakeji dashi.

Aikuwa tana goyashi yafara ihu yana zille-zille dan daman shi basan goyo yake ba.

Kamar an jeho yah Yusuf gidan sai gashi ya yi sallama,cikin mamaki ya sake ledar da ke ri’ke a hannunsa ta fad’I ak’asa
“Me nake gani haka ?
Yafad’a da fuskar mamaki tare da nufowa inda take tsayen.

“Sannu da zuwa yayah” tana murmushi tayi maganar.

Hannunsa ya ‘daga mata “ba wannan na tambayeki ba ni”

“Khadija yaushe jikin naki ya sau’ka dahar zakiyi goyo”
Baki da hankali ne?

Fusata ya sake yi ganin yanda yaron yake zizzille wa abayanta har yana ‘ko’karin kada itaina mamar tashin take ?

“Tana kitchen ne yayah tana girki shiyasa na goyeshi”

Ta fa’da tana me ‘kara jijjiga yaron,abinku da me zazza6i,kuma daman zazza6i ya iya yin lamo kamar ya sau’ka nan kuwa yana nan daram, take khadija tafara jin ‘karfin ta duk yayi low sai ta fara jin jirijiri,aikuwa caraf yah yusuf yah ri’keta dan ganin ta fara yin alamun fad’uwa,kunce goyon yayi daga bayanta ya zaunar da ita da kyau,tacigaba da maida numfashi.

Kitchen d’in ya nufa da yaron ahannu,ranshi duk ya gama 6aci,a ganinsa wannan ai rashin imani ne dazata ha’da yarinya da goyo bayan tasan ba lafiya ne da ita ba ga shi Mahmud ‘din ba laifi akwai auki dayake baruwa ake basa ba _baby_ _friendly_ suke masa shiyasa yazama wani 6ukeke dashi.

Ranshi a6ace ya isa kitchen d’in,suna ha’da idanu ya sake mata wata muguwar harara
take jikinta yayi sanyi

“baki da hankali ne Maryam “
taya zaki had’a yarinyar nan da goyo bayan kinsan ba lafiya ne da ita ba? idan goyon da dad’i ke ki goyi abinki mana ba d’anki bane,ko ita ta haifa miki shi”
“Yanzu badan Allah yasa nazo ba da kinsan me yake shirin faruwa ne,ke kina nan,wannan wani irin rashin imani ne dan Allah yake damunki?
Na bar yarinya rai ahannun Allah ina can na gagara sukuni hankalina na gida inata tunanin halin da take ciki ashe ma ke kina nan kin had’a ta da renon d’anki ga jaka ko?
“Okay shiyasa na yi ta ‘kiran wayarki kika ‘ki d’aukan wayar dagangan ko,missed calld nawa na miki amma kika ‘ki ‘dauka.”

Da masifah yake ta maganar idansa har ja yayi dan yanda yakejin ransa a6ace.

Kokad’an bai bata chance d’in yin magana ba,hakan yasa tayi shiru tana jinsa,zancen wayan da yayi d’inne ma yasa ta d’an d’ago idanu ta kalleshi dan bata san da wannan batun ba,asalima bata san inda wayar take ba ma tun ‘dazu data ‘kirasa bata sake bi takanta ba.

Daga lokacin be sake fita agidan ba har yamma masifah kuwa sai abinda ya ‘karu,dan wuni yayi abirkice sosai ya nuna mata kuskurenta,tun tana kar6ar laifin har tagaji ta fara jin haushi kuma,sai ta maida jin haushin akan Khadijan dan rainin wayo, a ganinta itace dalilin komai badan itan ba da haka bazai faruba.

Harta samu sauk’i bata ‘kara yin komai agidan ba dan sosai yayanta yatsaya mata,kwananta biyar ta warke rass harta koma makaranta
Ko abayan warkewarta ta kuwa sai ta’dan samu sauk’in aikin ka’dan dan yanzu Antyn tana ‘danyin girki wani lokacin,wankine dai sam batayi sai dai Khadijan tayi.

Ahaka har tagama secondary school ‘dinta gaba d’aya zuwa wannan lokacin kuwa Mahmud yayi wayo sosai har mamar shi ta yayeshi ma.

Ana cukucukun nema mata wata makarantar ne Kabiru ya 6ullo da batun san aurenta dan afad’ar sa wai shiru yayi kawai baiyi magana ba amma ya da’de da burin auranta aransa yayi shiru ne ganin bata kammala makarnatar ta ba.

“Yanzu kuwa Alhamdulillah tunda ta gama to yana neman izini”

Murmushi yah yusuf ‘din yayi sannan yace “lalle ka shammace ni Kabiru”

“Toh ya za’ayi ne babban yayah sharrin zuciya ne ba ni ba.”

Dariyah sukayi gaba d’ayansu.

Daga ‘karshe Yusuf d’in yace yabari yayi magana da ita tukunna sai su san yanda zasu 6ullowa lamarin”

Godiyah Kabirun yayi masa.

Yusuf bai wani 6ata lokaci ba da yaji maganar,yana komawa gida ya sami Khadija yafa’da mata cewa Abokinsa Kabiru na sonta da aure,itanma cewa tayi duk abinda yaga ya masa kawai yayi ita batada za6i.

Farin ciki yayi duk da yasan daman bazata fad’i wani abinda yake sa6anin hakan ba amma sai da ya nuna mata farin cikinsa afili dayasa ta gane cewa lallai yayi na’am da maganar tun farko.

Ba awani d’au lokaci ba,aka fara shirin biki bayan sunje k’auye dukkansu sun sanar dasu maganar,mal.Kallah yafi kowa farin ciki dajin maganar dan sauran kusan kowa bai bada wata muhimmanci a maganar ba,tsoronsu Allah da kuma batun kayan d’aki kar ace su zasuyi.Anty ne ma ta d’anso ta kawo musu wani mishkila kad’an dan fara cewa tayi wai +

“ai Kabirun ya girmewa Khadijan sosai ta yaya za’a ce shi zai aureta”

aganinta ai bai dace ba hakan.

Babu wanda ma yabi takanta a maganar tata duk dama basu san manufar maganar tata ba,Yah yusuf ne ma yad’an nuna mata cewa ai ba haramci aciki,tunda annabi ma yayi hakan kuma ba’a haramta mana ba,so bata da hujjar da zata ce hakan ba dacewa bane tunda bawai Kabirun ya shiga sahun dattawa bane,har yanzun sa amatsayin matashi yake”

Taji haushin k’in kar6ar maganar da akayi,amma dolenta ta hak’ura tayi shiru.

Ba awani d’au dogon lokaci ba aka yi bikin,sosai yah yusuf yayi k’ok’ari wajen ganin ya siya mata duk abubuwan buk’ata tare da sa hannun Alhaji muhammad amma bai yi da sanin ‘yar sa ba daga shine sai yusuf d’in suka sani,ahakan ma saida ya gargad’esa akan kar ya sake yaji labari koda abakin y’arsa ne,sosai yusuf yake yabawa da karamcin wannan bawan Allah,bashi da abin rama amsa illah yayi ta masa fatan alkhairi har karshen rayuwar
shi.

Bayan angama bikin ne kabiru ya d’auki matarsa yakai ta Gomben gefen iyayensa da ‘yan uwansa.

Anty kuwa sai bayan bikin Khadijan sannan ta san muhimmancinta da amfaninta agidan,dan sosai tafara shan wahala da aikin gidan,ga kuma yaronta da tun tashin sa Khadija ce ke kula dashi,yanzu kuwa abu ya dawo kanta,sai abin ya taru ya mata yawa ga rashin sabo,ga shi sam bata san k’azanta sai ta rasa yadda zatayi da rayuwarta,wuni take akan k’afarta amma still bata gane kan gidan,sai da aka samo mata mai aiki kafin gidan ya saitu mata.

Cikin hakan Allah ya d’aga kasuwancin Yah yusuf shima yazama tsayayye da kansa amma da taimakon Kabiru dansu sun san kan kasuwancin sosai,kan kace me sun zama manyan ‘yan kasuwa sosai kud’i ya zauna musu.

Tunda Anty taga Khadija na shirin kamota a komai sai tafara jin k’yashi aranta,sosai take jin Kishin khadijan,dama tun farko bata so Khadijan ta auri Kabiru ba aganinta ai ya fi k’arfin aurenta shiyasa takawo suka lokacin bikin amma b samu nasara ba.

Taso da wani daban aka samu aka aura mata dan ta samu damar takasu amma sai hakan bai yiwu ba.

Son zuciya sai ya kaita ga fara
Shige-shige,amma Allah bai bata ikon cutar su ba,taso ne tashiga tsakanin auran kKhadija da mijinta amma sai Allah ya karesu da karewarsa.

Shekarar Khadija uku da aure sannan ta haifi,’danta namiji sunyi farin ciki sosai musamman dayake tad’an d’au lokaci bata haihu ba sai wannan karan,amma dayake kana naka ne Allah kuma na nashi,tun kan ayi suna yaron yakoma ga mahallici,Khadija tasha ruwan hawaye dan tana da jarabar son ‘ya’ya tana murna tasamu nata kuma sai Allah ya kar6e abinsa,dakyar Kabiru ya taushe ta ta hak’ura ta dangana.

Ashekarar kuma Kabirun ya kafa cibiyar kasuwancinsa acikin garin damaturun jihar yobe,zama sai ya so ya gagare shi kullum yana cikin tafiye-tafiye.
Amma hakan bai ta6a damun Khadijan ba illah addu’ar sa’a datake binsa dashi akoda yaushe,yana kuwa jin da’din addu’ar tata kuma matuk’ar birgesa hakan yakeyi har baya iyah 6oyewa shima,sai ya bita da albarka mad’aukakiya.

Sai da aka shekara kafin khadija tak’ara samun wani cikin,murna kam kamar ance musu harta haihu ne ma kowa yana farin ciki da wannan abin musamman daya kasance Kabirun shine babba a familyn gidan,so kowa so yake yaga ya haihu shima.

_Allah buwayi gagara_ _misali_ shine yasan sirrin komai da kuma ma’anarta………… cikin rashin sa’a sai cikin ya 6are a wata shida bayan ciwon da tasha na azaba harta fita a hayyacinta ma.

Wannan karon kam cewa tayi zata dawo gida ta huta,dakyar mahaifiyar Kabiru ta barta a cewarta toh ta zauna da ita mana basai taje can kanon ba amma fir tak’i yadda.

Data je d’in kuwa sai datayi wata uku kafin tadawo,ran da zata dawo ma Mahmud kuka yayi tayi dan azaman datayi ba k’aramin sabo sukayi ba,ita ke tayashi komai,homework,da sauransu.

Kabirun da kanshi yazo yatafi da ita gida.Yana tsokanarta wai tazo gida tazama k’atuwa,kuma azahiri bawani jiki ta k’ara ba kawai de de tsokana ce irin tasa.
Wai ko dai tafison zaman kanon ne yabarta,cemasa tayi ehh” +

Duk da bawani jin dad’in zama da antyn takeyi ba amma dai tana jin dad’in ganin ahalin gidan nasu kuma zuwa yanzu ta yi wayon da komai Antyn zata mata ba damunta yake yi ba.tunda kallo ne kawai yanzu tsakanin su sai de ko habaici da Antyn ta tsiri yimata marar dalili.

Har k’auye duk taje ta kai musu ziyara kuma sunji dad’i musamman data je musu da tsarabar kayan amfanin yau da kullum, sosai sukayi mata tar6ar mutunci da karramawa.

Daworta da kusan shekara kafin tasamu wani cikin kafin nan kuwa har ta d’an fara shiga damuwa,mijnta ne ke tausar tare sake tunatar da ita cewa komai k’addar ne kuma ikon Allah ne.

Da tayi hak’uri ta dangana kuwa sai gashi Allah ya bata yanzu.

Cikin yaso ya bata wahala da farko amma data kai 3month sai ta ji garau,wannan karon ma kokad’an bata saka ran abinda zata haifa d’in zai zauna ba,sai dai tana addu’ar Allah yaraba su lafiya a kullum.

Da ikon Allah kuwa lokacin haihuwar da tayi sai ta gagara haihuwa da kanta,hankalin dangi yaso yafara tashi,amma sai likita yakawo shawarar cewa amata C.S,da wuri Kabiru ya amince dan yasan hakan shine kad’ai mafita agaresu.

Cikin sa’a kuwa akayi aikin aka ciro mata ‘yarta ‘yar mitsitsiya da ita.


Kowa ya ganta sai yayi mamakin girman nata dahar ya hana a haifeta sai dai da theatre,Khadija kuwa hamdala kawai take da Allah ya rabasu lafiya da babyn duk dama de theatre ce amma dole ta gode wa mahallici.

Mahaifinta ne yayi mata hud’uba da FATIMAH ZAHRA a madadin k’anwarsa data rasu ashekarun baya.

Kafin suna kuwa gida ya cika mak’il da jama’ah abin gwanin birgewa,dangi ta ko ina,Anty ma sunzo da ita da Mahmud,ga dangin Kabiru ma kaca-kaca.

Iyalan Hassan (mahaifin Abbas) kenan suma kusan kullum suna gidan dasu ake komai.

Abbas alokacin suma suna da jinjirar su mai suna Hannah,so bai wani damu da ko ganin jinjira ba harkar gabansa kawai yakeyi,shi kuwa Mahmud har yau bashi da kowa,shiyasa ya nace wa wajen da jinjirar take duk inda akayi da ita toh shima nan zai yi.

Anty ‘ki tayi ta sake haihuwa tun bayan data haifi mahmud,acewarta d’awainiyar yara wahala ne dasu,yah yusuf bai sani ba ma taje aka juya mata mahaifarta.

Koda taga yanda Mahmud yake ji da jinjiran nan kuwa haushi kamar ya kasheta,gashi daman zuwan dole tayi tace ma bazata zo ba da farko amma da yah Yusuf ya dage dolenta ta shirya ta taho.

Tunda tazo kuwa take ta shan k’anshi,ta na wani kallon raini a mutane,sukuwa babu wanda yabi ta kanta ma balle tankata suka ci gaba da sabgoginsu.

Ko kunya bata jiba ta tawo Mahmud ta jajja masa kunne akan nacin dayake wa yarinyar.

“Aranta khadija tak m
Sanin halinta da sukayi yasa babu wanda ya tankata,tunda d’anta ne ita ta haifi abinta,kuma ita keda iko da shi.

Khadija aranta take mamakin irin halin Antyn dan kwata-kwata batayi irin halin mahaifinta ba,shi ba haka yake ba sam.

Duk da haka bai fasa ba dan yaro idan yaso abu da wuya ake raba shi da abin,anjima kad’an ya faki idan mamar tasa ya dawo,lokacin Jinjira na hannun Khadija tana shan mama,hannun jinjirar ya kama,yace “Anty miye sunanta ?

Murmushi khadijan tayi sannan tabashi amsa da FATEEMAH sunanta”

“Lah Anty akwai wata ‘yar class d’inmu ma sunanta haka amma da TEEMAH kowa yake k’iranta,itama babyn Haka zanna ce mata “
“ko Anty?

Kai ta d’aga masa tana murmushi alamar “ehh”
wasu dake zaune acikin d’akin ma murmushin sukayi suna jinjina wayo irinta yaron.

Kamar wasa kuwa sunan yabita har girmanta.

Haka har taron suna ya watse suka koma kano,kuma tun daga lokacin Antyn bata k’ara waiwayar Gombe ba.

Sai ita mummyn Teemah da zuwan yazame mata dole,domin su kad’ai gareta sai kuma mijinta da ‘yarta.

Watanta hud’u da haihuwa taje Kano d’in, zuwa lokacin kuwa yarinya tayi 6ul6ul kamar ba ita ba.

Alokacin kuwa ba k’aramin wulak’anci tasha ba awurin Antyn danko y’ar ma bata ta6a d’auka ba,kuma ta hana d’anta zuwa inda Khadijan take,takaicin hakan na damunta,domin bata san dalilin da yake sa Antyn yin haka ba.Samun sauk’inta d’aya idan yayanta ya dawo gidan,danshi d’aukan y’ar yake yayi ta mata wasa shida Mahmud yarinya kuwa tayita dariyah.

Khadija tayi ta murmushi ganin yanda suke son y’arta ta.

Koba komai hakan kad’ai ma na sata nishad’i Anty kuwa sai dai ta kauda kai gefe tsabar mugun hali dan babu yadda ta iyah dashi sai dai ido.

Da lokacin komawar ta yayi kuwa yayanta yacikata da kayan amfani sosai yayi mata siyayyah,na kayan sawan jinjirar da kuma nata bayan wanda ya aika mata a suna.

Siyayyah tsakaninsa da Allah yayi mata bawai dan bata dashi ba a’a kawai sai dan yafaranta mata a matsayinta na y’ar uwarsa kwaya d’aya tal daya mallaka.

Hakan da yayi kuwa ba k’aramin cika haushi yayi ba azuciyar Anty,wutar tsanar suce tasake ruruwa azuciyar ta fiye da na baya.

Mahmud kuwa kuka yayi tayi kamar zai shid’e,

“Teemah na!

Teemah na!!

Teemah nah…….!!!

Haka yayita ambata,yana kuka babansa ne yayi ta rarrashinsa dan uwar kam ko kallo ma bai isheta ba da kyar ya hak’ura kuwa yayi shiru.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]