[Advertisements⬇️]

ABBAS CHAPTER 4 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ABBAS


CHAPTER 4
A dinning ya same su gaba d’ayansu har daddy amma basu fara cin abincin ba har yanzu,da alamu jiransa suka tsaya yi.
Teemah na ganinsa tafara zare idanu tayi k’asa da kanta sarai tasan tayi masa laifi kuma bata kyauta ba,don babu wanda zai so a kushe masa muhallinsa ballantana ma ita na raini tayi.
Ko kallon inda take ma baiyi ba yaja kujera ya zauna tare da yiwa su daddy barka da gida

Amsawa sukayi daganan suka yi bismillah auka fara cin abincin su.

Teemah yau kam har mamaki ta bawa iyayenta ganin yanda ta ke cin abincin,ita kuwa cin k’arfin hali ta ke yi,don so take ta riga kowa barin kan table d’in tagudu d’akinta ta kulle kafin yah Abbas ya cafkota.

Kusan duk kaiwa spoon d’inta baki toh sai ta kalleshi,amma ko sau d’aya basu ta6a had’a idanu ba.

Taci abincin yakai rabin plate sannan ta tashi awurin tsam ko sallama bata musu ba.

Babu kuwa wanda yah tankata dan mamakin da ta cika su dashi,Abbas kuwa ko ajikinsa,cin abincinsa yake yi cikin kwanciyar hankali,yi yayi kamar bai san ma da ita awurin ba,koda ta mik’e d’in kuwa k’in d’aga kai yayi ya kalleta, amma tak’asan ido babu abinda ya wuce wa ganinsa,ta k’asan idanu yake ta kallon duk abinda takeyi harta gama ta tashi d’in

Tashin bata wani dad’e ba shima yaji ya k’oshi hakan yasa ya wa su mummy sai da safe ya wuce abinsa.

Ita kuwa Teemah ruwa ma sai data bi kitchen ta d’auka sannan tawuce d’akin ta da shi,tana shiga kuwa ta danna key tana Hamdala,murna fal cikinta dan tana ganin ai ta tsira.

Ruwan tasha ta ajiye ragowan agefen gadonta,sannan ta d’an rage kayan jikinta,school bag d’inta ta d’auko ta dawo ta hau tsakiyar gadon ta barbaza takardu wai nan karatun Test takeyi,batajima ba ta fara hamma,minute-minute kuwa hamman ke zuwa,tsaki tafar jerawa itama aduk sanda tayi hamman,haushin wannan cin abincin datayi yau sosai d’in nan takeji,
“ai duk wannan mutumin nan ne yasani”
tayi maganar azuciyar ta tare da biyoshi da wata doguwar tsuka.

Takai 1hr tana karatun sannan ta tattare shirgin takardun akan gadon,daga nan tayi addu’a adaddafe ta kwanta.

Washegari tana tashi kuwa sai da tayi sallah kafin taje ta yi wanka,zaman shafa mai tayi bayan ta fito daga bayin,sai da ta gama goge jikinta tukunna ta kai hannu ta d’auko man nata datake shafawa kullum.

“Awsh namanta ashe ban fad’a wa mummy ba”
tafad’i tare da dafe goshi

Da kyar tasamu tashafa man kasancewar babu ya k’are acikin robar,shiri tayi cikin uniform d’inta,tafito ta nufi d’akin daddynta,dayake daman idan daddy yana gari shi take fara zuwa gaisarwa kafin mummy,gani tayi baya nan,hakan yasa ta fito ta nufi d’akin mummy.

Daddy kuwa tafiyace tasame shi ta gaggawa,tafiyar bazata dan jiya kusan 10:15pm aka k’ira shi,Allah ma yasa yana da passport d’insa ,so tun adaren ya k’ira yayi booking flight,6:30am yabar gidan,kasancewar 10:00am zasu tashi.Gaishe da mummyn tayi sannan ta tambayeta “ina daddyn ta yake?
+

“Yayi tafiya ne”
Mummyn tabata amsa.

Sai cewa tayi “aida ya fad’a min ma da da tare zamu”

Kallonta mummyn tayi da mamaki sannan tace
“Toki bishi mana,ai baki makara ba”

Dariyah tayi kad’an
“Allah kuwa mummy da binsa zanyi da nasan zaiyi tafiyah,in bahaka inaji ina gani zaman gidannan sai ya gagare ni saboda wannan……..,…….sai kuma ta kasa k’arasawa

Mummyn ce takar6e zancen da fad’in ” ahh toh in juninki rashin kunya ne da tsokana aikuwa ba ruwana ni,dan ni nawa ido”

“Mummy hakama zakice”?

“Toh me zance Teemah?
“Bake rashin ji kika ce shine halinki ba?

Fushi tayi data gama jin abinda mummyn ta ce.

Tea kawai tasha shima sama-sama daga nan ta tashi tsaye.

“Mekenan” mummyn ta tambayeta tana kallonta.

“Ni na k’oshi mummy”

D’auke ido mummyn tayi daga kallonta kafin tace
“Ke kika sani ai”,kije jakata bak’an nan ki d’auki Kud’i aciki

fara tafiya Teemah tayi zuwa d’akin mummyn sai tajiyo muryar mummyn na sake fad’in

“Kuma yanda kika saba tafiyah dashi zaki d’auka, bance ad’auki harda na shan kayan zak’i ba,sai wata yayi ki takura min da fitina”

Karaf akunnen Abbas da shima ya zo dan ya gaida mummyn.

Kuma atake ya fahimci me mummyn take nufi,mamaki yafara yi ashe yarinyar nan har haka ta girma amma shine bata da wayo har yanzu?

Da wannan tunanin ya k’arasa inda mummyn take,tana ganinsa kuwa ta sake fuskarta dan mummy ba dai son jama’ah ba,sam bata da wannan al’adar ta k’in dangin mijinta.

gaida ta yayi shima,sannan yad’an zauna kamar mai jiran wani abu, nan kuwa zaman jiran fitowar Teemah yakeyi agurin.

Koda mummy ta masa maganar break fast d’inma cemata yayi a’a bayanzu ba sai zuwa anjima zai ci.

Teemah da batasan da shigowarsa ba,tafito kenan daga d’akin mummyn taganshi zaune,
Turus taja ta tsaya dan jitayi zuciyarta ta tsinke daganin nasa,dayake baya ya juya mata,so bai ga fitowar tata ba ,mummy ce dai ta lura da ita,kallonta tayi suka had’a idanu take sai tayi k’asa da kanta kamar mara gaskiya.

Dayake kuma daman da rashin gaskiyar,sai ta taho ahankali izuwa inda suke d’in.

“Ina kwana yayah “

Sai da ya d’an juya kansa sannan ya kalleta, dan bata gama k’arasowa daf dasu ba ta masa gaisuwar,

“Lafiya”ya amsa mata dashi,sannan ya dawo da kansa saiti suka ci gaba da maganar su da mummy.

Tana ganin haka ita kuwa tafice taje dakinta ta d’auko school bag d’inta sannan ta dawo zata wuce, gani tayi yanzun baya zaune awajen, mummy kad’ai ne azaune,

“Na tafi mummy”
Tafad’a sanda take gyara zaman jakarta akan kafad’arta.

“Adawo lafiyah” kawai mummyn tace mata.

Harta fita sai kuma tadawo tasake dawowa ta tsaya daga bakin k’ofa
tace Mummy mai na ya k’are fah” +

D’aga kai mummyn tayi ta kalleta batare da magana ba.

Teemah kuwa ta juya tafita abinta don tasan ai mummyn taji me tace d’in.

Tana isa wajen motar da za akaitan aciki taganshi a mazaunin driver.
kasancewar Habibu ne yakai daddy maiduguri inda zai hau jirgi, da kyar ma in sun isa yanzu ballantana ayi zancen dawowa.

Turus tayi taja ta tsaya tana k’are masa kallo.

kusan minti biyu shima dagangan yak’i yi mata magana,sai da yaga bata da niyyan shiga ne sannan yace mata

“U ar just wasting ur time,let me tell you,ni inada abinyi”

Bai kalli inda take ba yayi maganar hannunsa d’aya kuma na kan stairy.

Ahankali ta ta ko tazo jikin motar,tana k’ok’arin bud’ewa tashiga ta tsinkayo muryarsa yana fad’in
“Habibu kika gani ne acikin motar?

Sarai tasan me yake nufi amma sai tayi kamar bataji sa ba harta bud’e k’ofar tana k’ok’arin shiga sai taji wani uban tsawan da ysa take ta firgita ta,balle daman muryarsa razana ta take.

Dawani irin b’acin rai yayi maganar “bana son rainin hankali fateema,sa’ anki ne ni?

Ai tana jin muryar tasa jiki na rawa ta rufo k’ofar ta dawo gefensa tashiga ta zauna.

Wani guntun tsaki ya sake sannan yaja motar,wani uban horn yadan na tun kan su isa bakin get d’in,da gudu mai gadi yaje ya bud’e musu suka fice agidan.

Bai sarara da gudun ba har saida ya dangana da babban titi kafin nan,kasantuwar bai san inda makarantar ta ke ba,kallon ta kawai yayi sai yaji tace “NANA AISHA”

Aransa yayi murmushi dan yanda yaga tsoro kwance akan fuskarta”ga shegen tsoro ga rashin kunya,afili kuwa ko kad’an babu annuri akan fuskar tasa.

Daya ke yasan gurin sai bai k’ara ko kallon inda take ba ballantana magana har suka isa,yana yin parking ta fita da sauri tare da rufe k’ofar da iyah k’arfinta kai kace yau ta fara shiga mota,shigewa tayi ciki abinta batare da tasake ko waiwaye ba,bayanta yabi da kallo yana k’ara mamakin duk ina wannan yarinyar ta koyi rashin ji haka,komai na rashin ji salo-salo ta iya su,inbadan mummy tasani ba ma ke kinsa ne na kawo ki makaranta
(Kunji yamanta da shekarun baya😅)

Jan motar yayi ya shiga cikin gari,bai dawo ba har sai kusan 12na rana.

12:56pm
Mummy ce tsaye ajikin mota abakin makarantarsu Teemah tana jiran tashinsu,dayake cewa Abbas tayi ya kaita idan ta tashi zata bi ta ‘akota tunda ita zata yi,shiyasa bai koma d’auko tan ba,hakan ma mummy tana ganin kamar ta takurashi amma bata fad’a masa yaji ba aranta ne take jin hakan.

Abbas kuwa baisan dan hakane mummyn tace masa zata bi tad’auko tan ba,daya sani kuwa bazai barta ita taje d’in ba.

Bata wani dad’e agurin ba aka tashe su,tana ganin hakan sai ta koma cikin motar ta zauna saboda hayaniyar yara da kuma k’ura,kuma atunaninta ai Teemah tasan motar gidansu inta ganta ai zata ganeta.

Teemah ma bata san cewa mummy ce tazo tafiyah da ita da ba,bata fito da wuri ba sai da kusan rabin d’aliban suka wuce kafin ta fito, kuma koda ta fito data fito d’inma sai ta wani d’auke kanta daga ganin motar,dan ta zaci Abbas ne yazo yanzun
ma.

Bakin titi ta nufa da niyyan taran adaidaita amma cikin rashin sa’a sai bata samu ba,don gaba d’aya d’alibai sun tashi yanzu,kuma a irin wannan lokacin samun abin hawa wahala yakeyi,gashi ana zabga rana.

Wasu ne ‘yan mata su biyu suka zo inda take tsayen,’yan class d’insu ne,suma napep zasu hau,anan suka tsaya surutu,ranar ne yafara isanta,dan tun tana jurewa harta ji inaah bazata iyah ba,da gefen ido ta kallo motar,ga mamakinta sai ta hango mummyn ta zaune aciki.

Take taji wani farin ciki ya lullu6eta……..Da saurinta ta isa gurin motar,alokacin ma mummy hankalinta harya fara tashi da rashin ganin Teemahn,tana k’ok’arin fitowa kenan ta duba ta dakyau,sai taji muryarta ta k’ira ta

“Mummy”

Da sauri mummyn ta d’aga kanta ta kalleta kana tace

“Haba Teemah a ina kika tsaya fisabilillahi?

Karkata kai Teemahn tayi gefe tayi kalan tausayi,
Mummyn kuwa tacigaba da fad’in

“Wato dama haka kike wa Habibu idan yazo d’aukarki ko kisashi yayi ta jiranki ko?

“Ahh fah mummy ni na _d’auka_ wannan yayan ne shiyasa fah nak’i zuwa”

Haushi mummy taji dajin abin nan data fad’a d’in,gata gwanar fad’ar gaskiya bata fiye 6oye al’amarinta ba ita.

Cikin jin haushi mummy ta bata amsa da ” toh ai sai ki _ajiye_ da kika ga bashi d’in bane kuma”

“Sorry my mum”
cewar
Teemh ta fad’a tana zagawa d’ayan b’angaren ta inda zata shiga motar.

“Wato ke bazaki bar raini da mugun halinkin nan ba ko?

Mummyn ta ce bayan Teemah ta shiga motar

“Shiru tayi bata yi magana ba.

“Inda Abbas d’inne kenan haka zaki shanya shi?
Waini sa’anki ne shi d’in?
“Kalli time fa Teemah kusan 1:30 amma sai yanzu zaki taho,kinsan tun yaushe nake anan d’in inaji ranki?

“Allah mummy bansan ke bace kika zo da bazan dad’e ba.

“Hmm”Allah ya shiryeki “

Kawai mummyn tace tare da yiwa motar key,sun iso daf wad’ancan friends d’in Teemahn sai Teemah tace “mummy sabon pegi” tafad’a tare da nuno su.

Tsayawa mummyn tayi,Teemah kuma tayi musu magana suka shigo dan har yanzun basu samu abin hawa ba.

Gaida mummyn suka yi ta amsa musu cikin sakin fuska daganan ta d’auki hanyar sabon pegin,ba hanyarsu bace amma haka sai da ta kaisu har k’ofar gidan su da taimakon kwatancen da suke mata,har suka isa,godiya sukayi mata sannan suka shiga ciki dan dukkan su ‘yan gida d’aya ne.

Daga nan mummy ta juyo ta nufo hanyar gidansu dake Nyanya Quaters gujba road Damaturu.

“Allah mummy gwanda da kika zo,d’azu da wannan yayan yamin wani tsawa har sai da naji fitsari.

“Wataran ma ai har dukan ki zaiyi inde kika ce juninki rashin jine”

“nifah babu abinda namasa mummy”

Bata kulata ba,dan tasan koma me zata ce toh 6ata bakinta takeyi abanza kawai dan Teemah baji takeyi ba.Horn mummy tayi aka bud’e mata get d’in tashiga.
+

Da sallama suka shiga parlourn,babu kowa aciki dan haka kowa yanufi d’akinsa.

Teemah na shiga ta fara ciccire kayan jikinta,sai da taga tacire komai sannan tafad’a kan gado tare da fad’in

“wash wallahi nagaji”

takai tsawon mintina biyu akwancen kafin ta mik’e tsaye

Towel ta d’auka akan k’ofar bayinta ta d’aura sannan tayi unhooking bra d’in jikinta ta ajiyesa,ta nufi k’ofar fita,harta kusan fita daga d’akin sai ta tuna abinda ke jikinta dawowa tayi sai kuma ta tsaya ta fara kwalla k’iran Baabah Lami,bakinta uku taji shiru babu amsa sai ta d’auki hijab d’inta ta saka sannan ta fito,kitchen ta shiga ta d’auko ruwan goran c’est,garin fita daga kitchen d’in ne ta had’u da Baabah Lami ita kuma tana k’ok’arin shigowa kitchen d’in.

“Baabah Lami inata k’iranki kika k’i kulani”

“Yi hak’uri fatee,naje wurin hajiya ne,

“Owk dama ruwane kuma ma kinga na d’auko abuna”

“Babu wani abinda kuma kike buk’ata?
Baabah Lami d’inne ta tambayeta da dukkan kulawa.

“Ah ah bakomai “
Teemahn ta bata amsa.

Daganan tawuce d’akinta da ruwan ahannunta,tun kam ta k’arasa cikin d’akin sai ta cire hijab d’in ta rik’e a hannunta, zama tayi akan side drwaer d’inta ta d’aga goran ruwan takafa abakinta,dan ko kofi ma bata d’auko ba,sai data sha kusan rabi kafin ta rufe ta ajiye
“Gaskiya yau kam masha Allah akwai zafi”


Wanka ta tashi ta shiga kusan 20mins tana bayin sannan ta fito,wajen dressing mirror ta nufah tana goge jikinta,sai yanzu taji d’an dama dama,domin ruwan sanyi tahad’a tayi wankan dashi,shiyasa take so tad’an shafa mai koda ak’afarta da hannunta ne dan kar suyi mata wani iri.
Har taje ta tsaya gaban madubin sai kuma ta tuno ashe man nata ya k’are gaba d’aya,ai kawai sai ta fito ta nufi d’akin mummy ahakan datake,shaf ta manta da batun wani Abbas agidan shiyasa take al’amuranta cikin sake wa kamar yanda tasaba.

Sallah tasamu mummyn nayi take ta tuna ashe fah batayi azahar ba itama.

Zama tayi tajira mummyn harta idar sannan ta tambayeta batun man shafuwan.

Mummy cewa tayi “aini mantawa nayi ma gaba d’aya,ki bari da yamma zan aika asiyo miki”

“Toh”
tace sannan tamik’e da niyyar fita daga d’akin,

“Teemah”Mummy tak’irata tana daga zaune akan sallayar datayi sallahr.

“Na’am”ta amsa tare da juyowa

“Kindai san yanzu bamu kad’ai bane agidan nan ko?”Kai ta d’agawa mummyn alamar “ehh”

“Toh ki daina fita da irin wannan shigar dan Allah.”

“Toh mummy yan zunma mantawa nayi ne kuma dana fito ma ban had’u da kowaba”

“Ki dai kiyaye”

“Uhm”
Teemahn tace sannan ta fito daga d’akin.

Bata lura dashi ba har sai da tazo tsakiyar parlourn sannan taganshi,abu yake k’ok’arin d’auka a gefen TV,jitayi kamar tajuya tunda bai ganta ba,amma kafin tayi yunk’urin juyawan har ya d’ago daga inda yake tsayen.

Salati tafara acikin zuciyarta dataga yakafeta da idanunsa,ko kyaftawa bai yi,shikenan wannan mutumin yau kan nashiga uku ahannunsa,tun daga k’afarta yafara bi da kallo ahankali har zuwa cinyoyinta,dayake towel d’in k’arami ne sosai sai hakan yabashi damar kallon surar jikinta da kyau.

“Masha Allah” yace
azuciyarsa,yarinyace amma babu laifi take yaji wani sabon yanayi yana ratsa shi ta ko ina.

Ido yad’aga ya kalli fuskarta sai suka had’a idanu,kunyar ganin jikinta da yasan tasan yayi ne yasashi d’aga k’afafu ahankali ya tunkari inda take,itama kuma da tayi ya fara nufo inda take tsayen, sai ta rintse idanunta da k’arfin gaske jikinta har rawa yakeyi.”wayyo Allah nah” take ta nanatawa acikin ranta.
Daf da ita yazo ya tsaya ya wani k’ank’ance idanu kamar gaske bayan yagama morewa kallonta.

Har ya d’aga hannu zai kamo kunnanta sai kuma yafasa ya mai da hannun nasa k’asa,dan yana ganin kamar idan ya mata hakan zai iya sawa d’an guntun Towel d’in dake jikinta ya kunce saboda yanda yaga duk jikinta na rawa abin har yaso bashi dariyah,amma sai yayi murmushi kawai,”shegen tsoro da rashin kunyah duk ta tara”.

Jin shiru datayi bayan ta riga ta tabbatar da ya iso inda take tsayen,dan tanda tashi alamun mutun agaban,tsammanin sauk’ar mari tayi amma sai taji shiru 6ud’e ido tayi ahankali.

Sai taganshi tsaye agabanta yana sake kallon k’asan wuyanta.

Baya ta d’anyi da sauri tare da bud’e idanun gaba d’aya.

Matsawan datayi sai ya bada gaf mai d’an tsayi atsakaninsu.
Kuma sai hakan yasa taji wani k’warin gwiwa ya shigeta.

“Ba kijin magana ke ko?

“Nan d’in gidan iskanci ne aka gaya miki”
Ya fad’a da wani serious tune kamar gaske nan kuwa rasa abin fad’a ne yashi cewa hakan.

Batayi magana ba illah kallonsa data keyi itama kamar yadda ya k’ureta da idanu.

“Kunnan k’ashine da ke ko”

Hannunta ta d’aga ahankali ta sada shi da kunnanta, ta6a kunnan tayi,kamar wanda batasan da zamanshi ajikinta ba sai yau.
Jitayi kunnan da laushi.Sai ta sauk’e hannun nata.

“Tambayarki nake kin min shiru”
Ya sake daka mata tsawah.

“Kunnan k’ashi ne dake nace ko”?
Yafad’a awani hasale.

Jijjiga masa kai tayi tana kallonsa,

“Umhm”
ya sake fad’i.

“Kunnena bana k’ashi bane “!

“Toh menene?
Ya sake tambayarta shima.

“Na nama ne “
Ta bashi amsa.

Ji yayi dariya takamasa sosai,da kyar ya samu ya tsare,amma saida ya d’an kalli gefe da gefen sa sannan ya samu ya basar ,maida dariyar yayi tazama murmushin gefen baki.

“Zan kuwa koya miki hankali yau d’in nan”

Yafad’a yana me k’ara nufar inda take,
Ai da gudu tayi hanyar d’akinta,tana shiga ta tura k’ofar ta rufe ta jinginu tana maida numfashi.

Tsayawa yayi yabi bayanta da kallo,yanda mazaunanta ke juyawa lokacin datake cikin gudun har sai da ta 6acewa ganinsa.Jijjiga kai yayi tare da fad’in ” ~astagfirullah~ ” +

Mena keyi ne wai?.

Sai da ya isa d’akinsa sannan yaji dariyah ta k’wace masa,ya kuwa yi abinsa son ransa,zuwa yanzu duk lokacin day tuna Teemah jiyake kawai tana bashi dariyah,saboda irin ta’asar data iyah
“Yarinyan wallahi tafara bani tsoro”

Ficewa ya sakeyi daga gidan ya tafi yawonsa.

Teemah kuwa tashi tayi ta d’auro alwala sannan ta zira wata bak’ar abaya ta tada sallar azahar,

Bayan ta idar ne tacire abayar,kuma se alokacin tafara tunanin abinda ya faru,”mugu kawai dana tsaya k’ila da sai de mummy ta d’auki gawata,dan nasan jibgata zai yi,babu ruwansa.

(Kunjifah🤔 ita damuwarta lpyar jikinta ne bawai kallon bati da ya yiwa jikin nata ba).

shiryawa tayi cikin uniform d’in islamiyarta da zindimemen hijab ta fito.yanzun kam a parlour tasami mummy tana zaune,cewa tayi
“Ah yau har kin shirya dawuri haka,babu latti kenan”,murmushi tayi wa mummyn sannan tace
“hadda ta tarumin ne mummy inaso in rage”

“Abinci fah”

“Kai mummy,may be sai na dawo”

Daganan tafitah daga d’akin zuwa cikin gidan.

Bata fi 7mins da fita ba ta dawo ciki,sai da tayi sallamah,kafin tace “mummy gidan fah babu mota ko guda d’aya”

“Haka akayifah namanta ne,Habibu bai dawo ba har yanzu,Abbas kuma inaga ya fitane,zoki d’auki #200 ajakata inaga de kamar akwai,maza ki hau adaidaita ki tafi,kuma in antashi kar ki tsaya jiran driver ki dawo abinki dan ko Habibu ma yadawo zai hutane babu inda zashi sai dai zuwa gobe in Allah ya tashemu.

Da “toh ” ta amsawa mummyn tare da shiga d’akin.

Fitowa tayi sannan tace “toh na wuce mummy”

“Uhm Allah ya tsare”

“Ameen” tace sannan tafice daga parlourn.

Abbas ma bai dawo gidan ba sai da yamma,koda ya dawo d’inma kuma zamansa yayi a gaban gidan yana duba abu a system d’insa.

Dawo wanta kenan daga islamiyah ta ganshi zaune aharaban gidan.

Harara ta banka masa kasancewar baya kallonta,tana isowa inda yake kuwa dan dolenta tace masa “ina yini yayah”

“Lafiya “ya amsa mata dashi batare da ya d’ago ya kalleta ba,harta d’an gotashi sai kuma taji yace “ke kinga zonan!
dawowa tayi baya ta tsaya d’an nesa dashi.
“Waye ya kawoki gidan?
“Babu” tabashi amsa dan bata san inda tambayar ta dosa ba.

“i mean keda wa kika dawo, banji anbud’e get ba sai kawai na ganki”?

“Ehh ni kad’ai dawo”
tabashi amsa.

“Habibun fah ko har yanzu bai dawo bane?

“Nima bansani ba” tabashi amsa.

“Ok jeki”

Juyawa tayi tawuce ciki aranta tace
“Mutum sai mugun hali da bak’ar zuciyah”
(Toh fa,ni nakasa gane wanda keda mugun halin acikinsu)

Baijima ba awurin shima ya taso ya shigo ciki,zuwa yayi ya tambayi mummy akan batun rashin dawowar habibun har yanzu,anan takece masa itama abin na ranta wallahi,amma bari tak’irashi taji.

Koda ta k’irashin ma cemata yayi yana hanya yama shigo cikin gari.

Sai da taji haka sannan ta tsinke wayar tare da fad’in “toh Allah ya tsare.

Ba’a dad’e ba kuwa sai gashi ya iso.

Ashe accident yasamu bayan ya sauk’e daddyn ahanyar ta dawowa gida,daya ke ma bai bar cikin maidugurin dawuri ba,sai da yayi sallahr azahar acan,sannan yakamo hanya
cikin tsau tsayi kuma sai wani mai golf yamar karo daga bayan motar,toh shine ya tsaya aka d’an daidaita natsuwar motar kafin yasamu ya iso,jimami sukayi gaba d’ayansu,daga nan mummy tace toh yaje gida yad’an huta koda na sati d’aya ne,sannan tashiga ta kawo mar ‘yan kud’ad’e tabashi.

Godiyah yata zubawa mummyn.
“Nagode hajiyah Allah yayi albarka, Allah ya kare zuri’a……..Allah ya……… Allah yah…..

Hakade ba iyaka,mummy kuwa sai Ameen taketa fad’i dan acewarta ba’a raina addu’ah ko yaya take bakasan bakin wa yafi albarka ba.

Kafin yafita sai Abbas ya rigashi barin d’akin Habibu nafitowa sai suka had’u a hanya.

Hannu ya mik’awa habibun suka yi musabaha,raba hannun nasu keda wuya habibun yafara zuba wata sabuwar godiyar,shi kuwa bai tsaya ba ya wuce abinsa zuwa d’akinsa.

Ashe shima kud’i yabawa habibun,saboda yana tunanin Habibun da kud’in jikinsa yayi gyaran motar kuma karsu shiga hakkinsa arashin sani,amma dayake bai ba bai bari kowa yagani ba sai babu wanda yasan nawa ne.Amma de inaga bazai wuce 20k ba.
+

Ranar kam ko agun dinning ma basu had’u ba,dan Abbas bai nemi abinci ba ba ranar,
Kuma mummy bata aika ta k’iransa ba.

Tade neme shi a waya anan yace mata,bai jin ci ne yau d’in,tace anya lafiyarsa kuwa ?
“ehh lafiya mummy kawai de ak’oshe nake ne.

“Toshiken Allah ya k’ara lafiya”

“Ameen summah Ameen”yace mata daganan sukayi sallama.

Teemah ranar farin ciki kamar ya fasa mata k’irji haka taji.Washe gari kuwa Abbas da sassafe ya fice agidan,ko da Teemah tayi shirin makaranta ma sai dai kud’in adaidaita mummy tabata, ranta ma baya son hawan adaidaitan amma babu yanda zatayi tunda Habibu bayanan. +

Haka taje ta tari adaidaita ya kaita makarantar,koda aka tashima haka tadawo,amma sai bata dawo dawuri kamar yanda tasaba dawowa kullum ba,koda tadawo d’in kuwa zube wa mummy tayi ajiki da fitina wai kanta na ciwo saboda tsayuwan data yi abakin titi dan jiran adaidaita,gakuma gari akwai zafin rana sosai.

Haka mummy yau kam tayi ta biye mata,dan gaskiya ta d’an tausaya mata ganin yanda duk tayi sanyi.

Ranar ko islamiyah ma batajeba,sai da aka nema mata panadol tasha tayi bacci kafin nan ta warware.

Wasegari ma ba taje makarantar ba,k’in zuwa tayi,ganin haka yasa d following day
Mummy ta kaita ta kuma d’auko ta,next kuma ta tafi a napep Abbas ne yakawota gida.

Kwanan daddy biyar ya dawo,Abbas ne yaje har maiduguri ya d’auko sa zuwa gida,dayake daman tafiyar ba wata qasa bace yaje, lagos ya tafi batun kasuwancin su da suke yi kusan atare shi da yayan mummy,tare ma ake sauk’e musu kaya,yayan mummyn acan yake da zama shida iyalansa.

Dawowar daddyn Teemahn ne yake sanar musu cewa ai Mahmud (d’an yayan mummyn) anan zai zo yayi service d’insa kuma nan da two days zai iso,nextweek zasu shiga camp.

Mummy dataji wannan batun kawai sai ta fara hawayen farin cikin zata ga jinin d’an uwanta bayan tsawon wasu shekaru,babu wanda ya hana ta kukan dan daddy ne kad’ai yasan dalilin kukan nata,Abbas da Teemah kam babu abinda suka sani dan haka suka zuba mata idanu,Abbas mamaki yake yi akan dalilin kukan nata daga jin zasuyi bak’o…………..kodai…….kodai…….

Teemah kam dataga mummynta na kuka,da farko itama tsayawa tayi kallon mummyn amma daga baya itama sai ta fara kukan dan bata ta6a kallon mummy tana zubda ruwan hawaye ba tunda tayi wayo.

Mumm ganin da tayi y’arta na taya ta kukan sai ta yi k’ok’arin dakatar da nata hawayen,tana murmushi.

Janyo Teemah tayi ta rungume ta kiyi shiru,ki daina kuka kinji,kukan farin ciki nakeyi Teemah cikin ikon Allah bayan wasu tsawon shekaru zanga wani daga cikin danginah,Teemah jinin d’an uwana,maganar take tana murmushi amma still hawayenta bai daina zuba ba,kana ganin yanayinta zaka gane tana cikin wani irin yanayi ne marar misaltuwa.

Daddy ma ido ya zuba mata yana k’ara jin tausayinta acikin ransa.

Sallar la’asar ne ya tada su awurin,Daddy da Abbas suka wuce masallaci,Teemah kuma da mummy kowa ta nufi d’akinta.

Kafin isowar Mahmud d’in mummy akullum annurinta k’aruwa yake yi,komai tana yinsa cikin walwala da farin ciki,da ka ganta kasan annurin daya ke kwance asaman fusakrta har cikin zuciyarta yake,musamman yau daya kasance suna saka ran isowarshi agobe Musamman taje kasuwa tayi siyayyah sosai wai afad’arta duk na taran d’anta ne.

D’akin da zai zauna kuwa tun jiyah aka gama gyarasa tsaf,aka sa dukkan wani abin buk’ata aciki.

Washe gari asabar mummy dawuri ta tashi ta taso k’eyar Teemah ma,seda suka koma ta sake duba d’akin da zai sauk’a aciki ta tabbatar da babu wata matsala kafin suka fito,Teemah mamakin wannan al’amarin yabi ya cikata.

Kitchen sukaje da mummyn anan suka samu Baabah Lami,dukkansu mummy taraba musu ayyuka,yau da kanta tayi girkinta duk wanda take ganin zai burgeta shi tayi kusan kala uku,juice kuwa sun had’a d’aya already ansa afridge,gasu kuma suna kan had’a wani daban,inka ga yadda mummy ta dage agirkin,ka kuma dubi yawa da kalolin abincin zakayi tsammanin family guda ne zasu zo,abin ya d’aurewa Teemah kai,ita de jitayi ance mutun d’aya ne zaizo amma ga mamakinta sunyi girkin da kusan mutane goma ma zasu ci su kuma rage saura.

Kallon mummyn nata tayi sannan tace “mummy wai bak’i nawane zasu zo?

Mummy cikin murmushi tace “Mahmud ne zaizo Teemah.”

“Mahmud d’in shi nawa ne mummy?

“‘D’aya mana Teemah,wai miye matsalarki ne ke kam.?

Kauda kai tayi daga kallon mummyn ta cigaba da blending d’in data keyi,amma sai taji zuciyarta ta kasa hak’uri da wannan abin.

“mummy amma de kinfi sanshi akaina ko?

Dariya sosai tabawa mummyn hakama Baabah Lami,dariyarta sukayi san ransu,Teemah kuwa ta wani basar ko kallon inda suke batayi ba dan ita tambayarta har zuciyarta tayisa,so ta ke taji amsarta amma kuma sai suka maida maganar abin dariyah.

Saida suka tsagaita ne Baabah Lami tace “kai Fatu tun yanzu harkin fara kishi ne?

Fushi ta k’ara akan nada d’in datayi,dan maganar baabah Lami duk abin haushi ne awurinta.

Wai fatu……..
Kuma wai tana kishi……….ita aganinta ai gaskiyarta ne,dan yanda taga mummyn na zumud’in isowar Mahmud d’in dole ya sosa mata zuciyah amatsayinta na y’a k’walli d’aya tal agun mummyn,aiko zuwan Yah Abbas ma mummy batayi wannnan azar6a6in ba,koda yake shi zuwan bazata yai musu basu san da zuwan nashi ba,kawai sai de suka ganshi.

Turo baki ta k’ara yi gabamummy ce tace mata
“ki rabu da Baabah Lami d’innan kinji yayanki ne fah,ana kishi da yayah ne kuma ai ba’a yi,
kinga ni kuma ai dole nayi farin ciki da zuwansa shekaru nawa rabo na dasu Teemah.”

Lalla6anta mummyn ta cigaba dayi da kalaman kwantar da hankali,dan tasan halin Teemahn nata ba dai kishi ba,haka tayi ta binta a hankali har suka gama aikin gaba d’aya.Sai bayan la’asar kafin Mahmud ya iso gidan, lokacin Abbas da mummy ne kad’ai agida.

A babban parlourn gidan suka fara sauk’ar dashi, lokacin da mahmud ya iso daddy baya nan,Teemah ma tana islamiya,mummy tayi murna da farin cikin zuwansa sosai,Abbas kuwa sai dai ido,dan mummy murnar tata tanayi ne had’e da hawaye tana tambayarsa labarin iyayensa,shima d’in duk jikinsa yayi sanyi dan anjima ba’a had’u ba amma shi bai wani yi kuka ba,ganin mummy takasa daina hawayen ne yasa Abbas ya fara bata hakuri duk da bai san manufar kukan nata ba.

Koda teemah tadawo ma sannu da zuwa kad’ai tamasa,dan ba saninsa daman tayi ba,gara shima yasan da ita,kawai dai rashin zumunchi ne yasa babu shak’uwa atsakaninsu.

“Fatima zarah “

Ya k’ira sunanta lokacin data mar sannu da zuwa d’in,dayake sunzo sunanta kuma fatima zarah shine sunan da aka ambaceta dashi aranar.

Amsawa tayi daganan tawuce ciki abinta batare da ta zauna a inda ta tarar dasu d’inba.

Sallar maghrib ne ya tadasu a parlourn,Abbas masallaci suka tafi suna idarwa kuwa suka dawo gida sai a sannan suka tarar da daddy yadawo,gaisawa sukayi da daddyn daganan ya wa mahmud d’in Barka da isowa dan shi ya riga da yasanshi ,dayake suna yawan had’uwa idan yaje Lagos.
Ganin sun dawo d’inne sai mummy tafara kwallawa Teemah k’ira,bakinta d’aya ana biyu Teemah ta amsa.

Akan dinning tasame su,nufo wurin tayi tana fad’in mummy dawuri haka yau kuma?

“Uhmm”
Kawai mummyn tace mata.

Daddy ne yace “yau mummyn ki ta sauya mana tsarin mu angel saboda taga sabon d’anta yazo”

Yana murmushi yayi maganar.

Mahmud ne yace “a daddy harda kaima ko ?

“Ahh toh mahmud ai munga ana mana wariya ne,dole inyi k’orafi”

Sai asannan mummy tayi magana tana murmushi tace
“Bafah haka bane,ina gudun hucewar abincin ne kunsan dawuri aka gama shi kuma nasan idan ya huce bandaro zaiyi”

Dukkansu sai suka murmusa,sai asannan ne mummy tad’an sake ta rage damuwar data ke ciki,da kanta tayi serving d’insu abinci,kowa yayi bismillah ya fara cin abincinsa,amma banda Teemah da take ta kora ruwan juice tana binsu da kallo d’aya bayan d’aya.
Cikin haka suka had’a idanu da Abbas yawani sakar mata harara,murgud’a mai baki tayi sannan ta d’auke kanta gefe,Mahmud kuwa har yanzu haushi yake bata,dan ta lura mummyn ta tafi sonshi akanta,shiyasa shikam ko kallon arzik’i ma bai samu ba,gani yayi tana ta wasa da cokalin bata ci ba, baifi spoon biyu taci acikin abincin ba,
“Yah dai” yace mata

Bata san ma da ita yake ba amma sai ta d’ago idanu,had’a ido sukayi dashi,sai tawani d’ago baki sama,
“Me aka miki ne?
Ya sake tambayarta.

“Kyaleta mahmud daina 6ata bakinka indai wannan ce”

Daddy ne yafad’i hakan.murmushi kawai mahmud da mummy sukayi,Abbas kuwa sai ya kalleta.
caraf suka yi 4 eyes dashi sai tayi k’asa da kanta tana gunguni,minti biyu bata k’ara ba agurin sai ta mik’e tsaye,juice d’in tak’ara tsiyayah ta wuce d’akinta dashi kowa bayanta yabi da kallo,amma banda Abbas.

Sai da suka gama cin abincin kafin suka mik’e suka fice ad’akin,Mahmud da Abbas ne suka fita harabar gidan suna d’an taba hira atsakaninsu.

Sosai suka fahimci junansu dan Mahmud gwani ne a surutu shikam,bakamar Abbas d’in ba.

Tun daga lokacin wani shak’uwa ta shiga tsakaninsu sosai dayake kowa yaji d’an uwansa yamasa har aransa.

Abbas da mahmud kusan sa’anni ne,Mahmud yasamu delay d’in yin makaranta ne dalilin mahaifiyarsa,shiyasa sai yanzu zaiyi service d’insa.

Koda suka dawo daga sallar isha’i ma ad’akin Abbas suka yada zango,kuma sai alokacin mahmud yake d’an bawa Abbas labarin d’an abinda yasani,shima Abbas d’in sai yaji mummyn tabashi tausayi sosai.

Anan suka ci kusan 2hrs ,sai 10:15 Abbas ya koresa yace “kaje kai ka kwanta ka huta mana,kamanta nisan tafiyar dakayi ko”

Dariyah mahmud yayi kad’an tare da fad’in “kai de nagano ka so kake in baka wuri ka sake”

“Ehh naji ni dai jeka”

Tashi yayi yabar d’akin yana fad’in mu kwana lpy.

“Allah ya bamu alkairi”
Abbas d’in yabashi amsa.
Sannan ya mik’e yarage kayan jikinsa yayi shirin bacci bacci.

********
Dangantakar mummy da Mahmud tasamo asali ne daga iyayen su mummyn.

Iyayensu asalin ‘yan kano ne,dan tun tashinsu a kano suka tsinci kansu,Malam mamman sada shine sunan mahaifinsu,kayan miya yake siyarwa a kasuwa mahaifiyarsu kuma ummah fatsin kusan kowa haka yake k’iranta dashi, iyayensu su biyar suka haifah,amma duk sauran Allah ya kar6i abinsa,su biyu ne kawai suka saura agaban iyayensu har suka girma,suna rayuwarsu cikin rufin asiri da wadatar zuci,yayan mummy mai suna yusuf yana gama secondary mahaifinsa ya dage har seda yaga yasamu gurbin karatu a BUK kafin ya samu nutsuwa,cikin ikon Allah ya fara karatun da sa’a dan bai sami wata matsala ba,shigansu 200level ne suka had’u da kabiru shikuma yazo D.E ne,kuma shine yakasance abokinsa har suka k’are makarantar dan kusan halayyah d’aya garesu……

Tare suke komai a makarantar inka gansu zaka zaci y’an uwan juna ne ma su,dan basu fiyah rabuwa da juna ba.

Lpy lau suka gama makarantar su,

Cikin ikon ubangiji kuma kamar abinda babansu yake jira kenan yace ga garinku nan,dan kwanan yusuf hud’u da gama makaranta ranar da yamma Baban yana dawowa daga kasuwa mota takad’e shi,garin tsallaka titi hannunsa rik’e da ledar y’ar tsarabar daya saba kawo musu idan zai dawo daga kasuwar,abin ya faru ne akan titin unguwarsu ,hakan yasa ba’a sha wani wahalar ganeshi da gidansa ba.

Dawuri labari ya iso musu,duk kansu suka fice bakin titin da gudun gaske su ummah na kukan fitan rai,dasuka ganshi kuwa take mahaifiyarsu ta suma a wurin.

khadija kuwa kuka ta zube tanayi dan rasa kan wa zata fara zuwa tayi.

Da k’yar aka samu aka tattara su aka kai gida,shikanshi wanda ya kad’e mahaifin nasu kuka yakeyi da hawaye, ba’a wani d’au lokaci ba aka masa sutura, kanshi ne yafashe dan bazama kaso kaga yanda kan yayi ba hatta likkafanin ma sai da yayi ja,dukda an d’an ninka a wajen kai d’in amma sai da ya ratso,Yusuf ne kad’ai mai dauriyah addu’a kawai yakeyi azuciyarsa har suka sada baba da makwancinsa na gaskiyah.

Dayake wanda ya kad’e baban ma zuciyarsa mai kyau ne,dashi akayi komai har zuwa sadakan bakwai,kuma aranar ne ya bayyana abinda ke ransa game da batun diyyah

Yusuf ne yace su basu son wani diyyah akan mutuwar baban,koda akaso fahimtar dashi akan musulunci ne yazo da hakan ma cewa yayi ya sani,kawai bazai iya kar6ar komai akan dan babansa yarasu ba,mutuwa ai ta Allah ce

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]