[Advertisements⬇️]

ABBAS CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ABBAS 

CHAPTER 2


Shirye-shirye aka farayi na tafiyar abbas ‘din makaranta,dayake hankali bai gama isan Teemah ba shiyasa bata wani damu da batun tafiyar ba har se ranar da ze tafin kafinnan, wato ranar laraba. +

Dawuri yagama shirinsa don shima irin yaran nanne masu jarabar son makaranta.Baya wasa da harkar karatun shi tun asali,wannan halayyarsa ne tun yana yaro qarami.

Ballantana Yanzu da ya ‘kara wayo sai ya fi jin yin karatun sosai.

11:00am ne flight dinsu,ba sassafe zasu tafi ba,hakan yasa yau ‘din ma yace shi ne zai kaita makaranta.

Ahanya neh yake sanar da ita cewa shima fah zai tafi makarantarsu anjima,ko ajikinta bata damu ba illah cewa datayi “ai nima zan dinga raka ka kullum inzaka je”

Dariya ma tabashi shikam,dan shirman nata abin dariyah ne, wannan shi ne ana ce miki ga gabas kina ‘kara tambayar ina al’kibla.

Sai da yayi dariyar kuwa sannan yace mata

” ke bafa anan bane makarantar,tafiyata zanyi nima,yanzu sai de Habibu ya rin’ka kawoki a mota kullum.”

Kanta ta lan’kwasa gefe ‘dayan kafa’darta tare da fadin

“hum um-hum um”
harda bubbuga kafafunta a’kasa irin na shagwa6a66un yaran,sannan tace ni banaso.
Kallonta yayi sosai dan so yake ta fahimci maganar tasa sosai amma yarinta bazai barta ba sai kawai yace mata

“dolenki ai yarinya,inkuma bahaka ba sai de ki rin’ka zuwa ke ka’dai.”Kinga habibu ma huta da zirga- zirga.

Kuka tafara masa na rashin dalili,ehh mana rashin dalili,daga cewa habibu ne zaina kawota makaranta kuma sai kuka,toh danma bataga yatafi yabarta ba kenan daya zatayi. abin dariyah wa
cewa tayi .
“sai na fa’da ka da Daddy”

Batasan cewa daddyn shi ne jagoran tafiyan ba.kiyi ha’kuri karki fada ni da daddy ya fa’da da sigar yanda itama tayi magananta,ta ke kuwa yabata dariyah.”me zan siyo miki idan naje makarantar ya tambayeta.”ai nima binka zanyi inzaka tafin,irin yanda kake rakani,a’a nawa nikai zanje bawanda zai rakani kuma idan natafi zandade bandaqo ba.amma wannan karon bata kulashi ba don yafara bata haushi.sai kuma ta tuna fruits ‘dinta 

Kai ta ‘daga ta kalleshi,hannunta na ri’ke cikin hannunsa suna tafiyar.sai tace toh yayah idan katafi wazai dinga siyamin Apple da pineapple harda babana ma?
Habibu zaina siyamiki kinji? Yabata amsar tambayarta ta cikin sauri. Kuka tafara masa wai ita bata son na habibun nashi take so.

suna tafiyah tana kuka,tausayinta yakeji dan yasan dolene daman taji ba da’di,shikansa ma bada’din yakeji ba don sosai sukayi sabo fiye da zaton mai karatu.

Da ‘kyar ya lalla6eta tayi shiru sai da yace mata dawasa yake mata babu inda zaije.Kuma shine zai na siyamata apple ‘dinta kullum.

tana jin haka kiwa kuka ya ‘dauke cak.
Haka ya rakata makarantar dai dai zata shiga ya miqa mata lunchingbox ‘dinta yace ta shiga class dinsu banda wasa,harta fara tafiyah sai ya ‘dan ‘daga ‘kafa ka’dan ya iso gareta,dayake bata wani yi nisa da inda yake tsayen ba,hannunta yakamo sannan ya tsuguna dai dai tsayinta.

Sake daidaita mata ‘dan Hijab ‘din uniform ‘din dake kanta yayi,wanda dudu-dudu bai wuce iyah kafa’dunta ba.

Kallon cikin idonsa tasa keyi itama,sai yayi murmushi ya kamo kumatunta duka biyu ya ‘dan jijjiga mata fuskar

“Smile mana kin wani 6ata rai kamar an dokeki”

Dariyan kuwa tayi masa.Tana sa ke kallonsa.

“Silly girl”

Yace ahankali
yana murmushi

Hannunta ta ‘dago ta danna saitin dimple ‘dinsa.

Bawani zafi amma dan kawai ya ‘dauke mata hankali yasa shi cewa

” kai kai,Allah yarinyan nan kin iyah mugunta”

Sai yayi kamar zaiyi kuka tare da kama gurin data danna ‘din.

“Sorry yayah”

Tafada tana turo baki gaba

Sake 6ata rai yayi sannan ya ce.

“Zan ha’kura amma sai naje anmin allura idan ya daina zafi toh shikenan zan han’kura amma idan bai daina ba toh shikenan bazanma dawo ki ganni ba.Kin yadda?

Ya tambayeta.

Kai ta ‘daga masa alamar ehh tayadda.

Tashi yayi tsaye sannan yace toh ki je class,”

“barinje amin allauran ko?

Sa ke ‘daga masa kai tayi

“ko zaki rakani?ya sake tambayarta

yanzunma kai ta kuma jijjigawa alamar a’a.

“To kije class anjima habibu zaizo ya ‘dauke ki kinji.

Duk da kai take bashi amsa.

Sannan tajuya tanufi cikin makarantar shima bai tafiba tsaya wa yayi yana kallon bayanta harta isa bakin class din su sai ta juyo kamar tasan bai tafinba.

Hannu ta ‘dago ta mai bye-bye.

Shima ‘daga mata hannun yayi.

sai da yaga ta shiga class kafin shima yajuya ya kamo hanyar gida.awurin mai kayan fruits ya tsaya,alokacin ma mai kayan bai gama kintsa wurinba,haka Abbas yajirashi tsaye agefe har ya kammala gyara wurin ya kik-kintsa fruits ‘din kowanne a muhallinsu kafin abbas ya matso yasiyah matah,wanda tafi ra’ayinsu daganan ya isa gidan.
Yana shiga yasamu mummy zaune aparlour tana kallon wani series,binsa tayi da kallo dan ganinsan datayi ri’ke da leda a hannu.

Dariya yayi yana kallon mummyn shima saboda irin kallon tuhumar datake binsa dashi.

“Mummy kayan Teemah ne na siyo mata don zata dawo yau bana nan”

Murmushi mummyn tayi tare da fa’din “lalle Abbas da ‘ko’karinka.Kai da zak tafi har se ka biyeta kasiya mata bayan ma kawi agida.a’a mummy cewa tayi nawan tafiso.” Ku kuka sani ai mummyn ta qarasa zancen nata tare da komawa ta jinginu da kujerar da take zaune akai.

“Toh kaiwa fanni tasaka mata a fridge kafin tadawo

karsu lalace dan yauma naga garin adafe yake,ragowar mafa inaga yawa ne dasu a fridge din”

Ce mata yayi

” a’a mummy wannan yafi da’di.haka yafadawa mummyn yana qoqarin barin parlourn .

“Zan gani ai idan ka tafi wa zai rin’ka siya mata mai da’din tunda namun ba da’di.

Dariya kawai yayi sannan ya ‘karasa 
Fita daga ‘dakin,wurin Fannin ya nufa a inda yasan zai fi samunta cikin sau’ki, daga nan yawuce ‘dakin Teemahn,bayan yabata ledar.

Guri yasamu ya zauna abakin gadonta ya yi tagumi.

Ha’ki’ka sabo ba da’di don yanda Abbas yakeji,jiyake kamar kar yatafi yabarta,amma bazai yiwu ba.

Sosai ya 6ata lokaci a’dakin nata amma shikanshi baisan dalili ba,illah kawai kewarta dayake ji tun kan ya tafin.

10:30 suka fita shi da daddy da mummy,Habibu ne ya kaisu airport ‘din daganan ya dawo da mummy gida su kuma suka wuche Abuja.

Koda lokacin tashin su Teema yayi Habibun ne yaje ya ‘dauko ta yadawo da ita gida.

Sai data gansu a ‘kofar get ‘din gidan habibu na danna horn kafin ta turo baki Sannan tace

“Nifah bahaka yayah yake min ba”

Juyowa yayi ya kalleta daidai anbu’de get ‘din gidan.

Cewa yayi Bayan yaja motar ciki

” me yayan yakeyi wanda ni banyi ba,?

ni dama na kawoki a mota”

“shi ai yayan kullum se ya siya min fruits ahanya”

Kai kuma baka siyamin ba,ai inya dawo daga alluran sai na fa’da masa”
kuma ‘dazu yace wai zaka dinga siyamin kafin yadawo”

Tafa’da masa da turarren baki irin ita adole tayi fishi ‘dinnan.

“Fishi yana gaba yarinya “

habibu yafa’da azuciyarsa don yagane cewa wayo Abbas ‘din yamata da sunan allura zashi.

Afili kuwa yace mata yayi ” ii ha’kuri ‘yar Daddy yanzu zanje insiyo miki.”

“a a ni banaso na yayah nakeso ni,idan ya dawo zai siyo min ai. tafa’di hakanne bayan sun fiffito daga motan.

Aransa yace “ashe zaki jima yarinya” afili kuma ya ce mata”kinga ai kin hutar dani”

Ciki tashiga da sallamarta ‘yar siririyah,bataga kowa a parlourn ba hakan yasa ta wuce ‘dakin mummy.

Zuwa tayi da gudu ta rungume mummyn nata tabaya dayake atsaye take agaban ma’ajiyan kayan sawanta wata ‘kila wani abun zata ‘dauka ko ajiyewa dan ba kaya ta ke nema ba.

“Oyoyo mummy”

Teeman tafa’da

Itama mummyn cewa tayi “oyoyo yarinyar mummy”

Sannan ta kama hannunta tazauna akan side drawer daga gefen gado tace mata”wato yau yayah bayanan harda oyoyo na samu ko?

“Ai mummy allura yaje zai dawo yace min “

Hmm ” kawai

mummyn ta ce

Rage mata kayan jikinta tayi sannan tace mata taje fanni ta watsa mata ruwa,sai ta dawo.

Fita tayi hannunta ri’ke da kayannata tashiga ‘dakin ta watsa su aakan gado tayi wajen fannin akitchen tasameta tana wanke wanken kayanda aka gama anfani dasu yanzu.

+

‘Dakin suka koma fanni tamata wanka kafin su gama kuwa tasha surutu kuma duk hirar yayah ake tayi mata.

Itama fannin ta biyeta,suka tayi tare.

‘Dakin mummyn suka dawo bayan fanni ta shiryata.

Mummy naganin sun dawo ta mi’ke tace suje suci lunch dan tana so ne ta’dan fita.

Harsun zauna anfara zuba abinci teemah tace ita kam a’a bazataci abinci ba pineapple ta keso.

Jin haka yasa mummyn ta fara mata masifa da ‘dagun murya akan rashin son cin abincin data koya.fanni ce ta tuna da fruits ‘din da Abbas ya kawo ‘dazu kafin ya tafi.

Bata yiwa mummyn magana ba illah zuwa datayi ta duba,cikin sa’a kuwa tasamu pine apple ‘din aciki.shikadai tadauka ta feresa mai kyau sannan ta dauko takawo wa Teemahn.

Sai da taka wo sannan mummy ta tuno dashi,Ashe fah Abbas yasiya mata kafin yatafi kamar yasan ma zata musu rigima akai.

Haka ta wuni tana shan abinta taqi cin abinci.

Da lokacin islamiya yayi habibu ne yakaita ya dawo da ita kuma.

Har washe gari bata wani damu da rashin Abbas ‘dinba,don ita duk atunaninta alluran yatafi dagaske kamar yanda ya sanar da ita.kuma ai yace mata sai ya warke sannan zai dawo……….

Dataga lokaci yafara jah ne sai tafara takurawa mummyn akan ina yayan yaje?,mai yasa ya’ki dawowa?

Tun mummy na ce mata yatafi alluran itama kamar yanda Teemahn ta ‘dauka harta gaji ta tafara ce mata ya tafi makaranta ne bazai dawo yanzu ba.Tun lokacin da Abbas ya tafi kuwa Teemah bata ta6a mantawa dashi ba,don mafi yawancin lokuta idan ka ta6a ta ko kamata wani abin takance “sai nagaya ka/ki da yayah,koda kuwa amakaranta ne ko gida,harta mummy da Daddy basu tsira ba,suma abu kad’an sai tace sai ta fad’awa yayah dan ita azatonta har yanzu watarana zai dawo. +

Mummy bata ta6a kuskuren had’a su awaya ba don acewarta daga ta gwada k’ira mata shi sau d’aya tasan Teemah ta ringa damunta kenan kullum,shiyasa bata ma fara ba,duk da basu fasa waya da ummahn Abbas d’in ba suna wayarsu kusan kullum, haka sometimes mummy kan bata labarin irin rigimar da Teemahn keyi akan rashin ji daga Abbas d’in da batayi ba har yanzu,dariyah kawai kowaccen su keyi daga haka su shashantar da zancen.

Akwai ranar da ta ta6a saka mummy agaba da kuka wai dole suje gurin yayanta,mummy tarasa yazatayi da ita ta ce mata ai alluran nasa bai k’are ba”kuma in yak’are zai dawo da kansa,amma sam ta’ki yadda.ita wai dan dole suje su kawo shi gida,

Haka data dage sai da mummy tayi wayar k’arya ta tambaya awayar ta ce “abbas nake nema?

“Aw baya kusa?

Alluran haryanxu?

Owk toh shikenan inya dawo ace masa Teemahn shi ce ta ke nemansa.

Da mummyn tacire wayar akunnenta sai tace mata

” ai wai bayanan amma alluran ma yakusa ya k’are kuma idan ya k’are zai dawo.

Ai Teemah najin haka tafara dariyah ta fad’a kan cinyar mummyn.

Salati mummy tafara kamar gaske ,

Kai abbas d’in nan bayajin magana ,ashe yawo yatafi abinsa ya kyale angel d’ina agida.

D’ago kai Teemah tayi ta kalli mummyn

“Mummy ke ba yayanki bane?

“A’a Teemah” mummyn tafad’a sannan ta sa hannu ta d’ago Teemah ta tsayar da ita agabanta.

“Mummy yah abbas fah sunansa ke kuma kina ce mishi “Abbas”

Kumatunta mummyn takama duka 6angare biyun tana mata murmushi.

Teemah “Abbas d’ana ne ba yaya na ba.ke kuma kinga ai ke k’arama ce.K’anwarshi ko?

Kai TEEMAH tad’aga wa mummyn tana d’an smiling itama.

“Yauwa my angel 

“maza jekiyi home work d’inki ko”
mummy is sleepy”

Da haka mummy tasamu ta kora ta daga wurinta dan tasan inba hakan tayi ba to hirar bazai ta6a k’arewa ba.

Teemah da fara’arta ta fita daga d’akin mummyn ta nufi nata.Yau farin ciki ta keji har aranta don yayah yace zai dawo in allurarsa suka k’are.

Ai kuwa daga ranar tafara lissafin ranar da abbas d’in zai dawo.ita kadai tayi ta ware rana amma kullum shiru ba labarinsa.

“Mummy gobe yayah zai dawo ko”?

Kullun sai tambayi mummyn,amsar mummyn kuwa baya wuce “bansani ba nima Teemah”dan bata so tafiye yi mata k’arya.Inkuwa daddyn ta ne zai fita ce mas take yi idan yaje yadawo mata da yayah! +

Shima cemata yake toh,inya dawo ta kuma tambayarsa kuma sai yace ai basu had’u bama da Abbas d’in.

Itama Teemah tun tana damuwa harta zo tadaina damun kanta akansa,takance “ai ba ruwana da yayah yanzu tunda ya manta dani yah daina sona” haka ahankali harta ha’kura ta manta dashi ma gaba ‘daya,abinku da yarinta.

Hakan da yafaru kuwa ya matu’kar samawa mummy lafiya,dan acewarta itama ta huta da fitina.

Har ta gama primary tashiga Js class amma Abbas bai ‘kara dawowa gidan su ba itama kuma ba’a ta’ba zuwa abuja da ita ba.Kuma zuwa wannan lokacin kwata kwata ta manta da tarihin rayuwarta tare Abbas d’in,tadai san tana da ‘dan uwa amma ko da a photo taganshi bagane shi zatayi ba.

Tana Ss1 wata ranar jumma’ah tadawo gida dayake dawuri ake tashinsu. In ranar Friday neh,motar su na shigowa ta hango wata sabuwar mota a wajen parking bata san me motar ba,dan haka ta shiga parlourn da sallamarta,Daddyn Abuja tagani azaune shi kad’ai a parlourn yana waya.da fara’arta ta k’arasa inda yake zaunen ta zauna kusa da shi,daga inda ta ke zaunan tana iyah jiyo muryar wanda suke magana da daddyn,tana jin irin yanda yake yiwa daddyn nata.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Kauda kai tayi tare da ta6e baki.

Daya gama da wayar ne ya kalleta ya ce “uwata kin dawo ne”

Dariyah tayi kad’an tace “nadawo daddy ya hanya yah ‘yan Abuja?

“‘Y’an abuja gaba d’aya “dadyn ya tambayeta.sannan yacigaba da fad’in mamana fah ashe an girma”

Kunya taji da sai tad’an rufe fuskarta da hannunta.

Daidai nan kuma daddynta ya fito cikin shirin sa na fararan kaya.

Sai da ya iso ya zauna akujerar da take fuskantarsu kafin yace mata “ya akayi ne baga kin dawo da wuri?”

“Daddy yau fa friday kamanta ne,”

Ohh sorry haka ne fah,ashe dawuei kuke tashi,”

Na zaci ai ganin daddynki kika dawo kiyi dan kinji yazo” ya fad’a mata da sigar zolaya.

Toh aini bansan ma yadawo ba daddy waye zai fad’amin nida nake makaranta.

Nasani ne angel “

Ko daddyn naki ne yasanar da ke.

Dariya sukayi gaba d’aya daga nan ta tashi ta d’auki jakarta “daddy ina zuwa “

Tafad’a tare da barin d’akin.

Parlourn mummy tafara zuwa tana yin sallama taga ummah azaune au da mummy,yada jakar tayi ta tafi da gudu tafad’a kan cinyar ummahn tana dariyah,

“ummah na ashe harda ke akazo shine daddy bai gayamin ba?

Ai gani kinganni”

Ummahn tafad’a tana maijin dad’I har cikin ranta yanda Teemahr take sonta.

Gaida ummahn tayi tare da yimata ya hanya amma still bata bar jikinta ba.

Mummy ce tace mata 

“Ai se ki d’aga ko tunda hankalinki ua kwanta,da wanne zataji da gajiyar hanya ko kuma da nauyinki”

“Katuwa da ke sai son jikin tsiyah”Ummah wai ni k’atuwa ce inji mummy”! +

“Kyaleta mamana bawani k’atuwar da kike”Kawai dai tana fad’a ne.

“Hakama fah d’azu

naji wani ma babba dashi yana yiwa daddyn Abuja shagwa6a awaya”amma ni sai mummy tahana ni tace min wai ni k’atuwa? 
Tak’arashe da turo baki gaba.Dariya ne yaso kama ummah dan tasan wannan sai aikin Abbas.

Amma afili bata cewa Teemahn komai ba illah

cigaba datayi da lalla6ata harta hak’ura.

mummy kuwa kauda kai tayi sannan tace “rashin aiki dai”

“Ai in kika biye ta wannan zaki sha fama”
mummyn tafad’a tana mai nuna Teemahr da baki.

Murmushi sukayi ummah da Teemah dajin abinda mummy tace, mummyn kuwa ta ta6e baki.

Tashi tayi daga kan cinyar ummahn ta zauna sannan tasa hannu ta d’auki d’aya daga cikin abin ta6awan da aka ajiye wa ummahn.

“Ummah bari na watsa ruwa in dawo”

Da toh ummahn ta amsa mata,ita kuwa tuni ma takusa barin parlourn.

Sai da ta cire kaf d’in kayan uniform d’in dake jikinta sannan tafara k’ok’arin neman abinda zata d’aura ajikin nata amma bata samu ba,

tana daga tsayen tafara kwalla k’iran Baabah lami mai aikin gidansu na yanzu,bakinta biyu kafin tayi na ukun baabah lami ta amsa mata tare da tahowa d’akin,bata tuna ba kaya ajikin ta ba harse da taji motsin tafiyar Baabah Lami d’in kusa da d’akinta kafin ta tuna,hijab d’in makarantarta ta d’auka tasaka akanta ko gwiwa ma bai rufe mata ba,amma dai yafi babu.
Da sallama Baabah Lami ta shigo d’akin 
Tun kan ma ta gama shigowa Teemah ta jefa mata tambayar

“Baabah Lami banga Towel d’ina ko d’aya ba.”?

“Aw suna baya bakince a wanke miki su ba”.

“Owk toh anwanke d’in ne ?

“Ehh anwanke”

Baabah Lami d’in ta amsa mata dashi. Sannan ta k’ara da fad’in barin je inkawo miki.Daga nan tajuya tafita daga d’akin.

Dayake fanni tajima dayin aure hakan yasa tabar aiki agidan nasu sai aka samo musu wannan Baabah Lami d’in.Baahbah Lami bawata babba bace don bazata wuce 27/28yrs ba amma dayake bazawara ce,yaranta hud’u kuma sune suke k’iranta da wannan sunan wato Baabah Lami hakan yasa sunan yabita kowa ma haka yake k’iranta da shi yanzu. +

Koda Baahbah Lami ta kawo towel d’in azaune tasame ta abakin gado tana kallon fuskarta acikin d’an madaidaicin mirrorn dake rik’e a hannunta.Daganin Baaba Lami d’in kuwa ta tashi ta kar6i kayan ta,tsayuwa tayi har sai da taga baabah Lami tafita taja mata k’ofar kafin ta cire hijab d’in kanta ta d’auki towel d’aya ta d’aura ajikinta, sauran kuma ta ajiye su a inda tasaba ajiyewa sannan ta d’auki wani fari k’arami daga ciki ta rik’e ahannunta kafin nan tashiga bayin.

Ta 6ata ak’alla kusan 40mins a wanka da yin shirinta kad’ai.

Tana fitowa kuwa wajensu daddy tafara zuwa ganin basanan sai ta nufi wajen su mummy,tana shiga da sallamarta tafara tambayar mummy “ina su daddy suka je kuma,?

harararta mummy tayi, da me zaki musu? Mummyn ta tambayeta.

sai ummah ce ta bawa Teemahn amsa da fad’in “sun tafi masallaci ne zasu sallaci jumma’ah”

“Ohh na manta ne ummah ashe fah yau Friday”

Daya taga reaction d’in mummy data shigo,mummy da harara tabita kuma tasan ma’anar hararan haka yasa yanzun bata zauna ba ta kuma ficewa daga d’akin,don tasan in bata fitan ba mai zai biyo baya anjima ko gobe,kunnan ta ne zasuji ajikinsu.

Mummy bata son wai taringa zama a inda ta ke matuk’ar tana tare da bak’i.Dan yana rushe tsarin tarbiyar yaro.Itama dayake tasan abinta sai kawai tafice can bayan gidan tayi zamanta a inda taga yafi mata da’din zama.

Da lokacin sallah yayi ne ta koma ciki dan ta yi sallahr itama.

Bayan su daddy sun dawo ne aka had’u agun cin abinci,kowa yana ci amma banda teemah da bai fi spoon biyu taci ba kawai,Daddyn abuja ne ya hankalta da ita hakan yasa ya tambayeta ko bata jin dad’in abincin ne?

Murmushi tayi masa batare datayi masa magana ba.

Daddynta ne ya bawa daddyn abuja amsa da fad’in

“da de kayan itatuwa ne da ba sai ka 6ata bakinka wurin sata ciba ,amma abinci kam ni har na gaji da yi mata magana akai ma”

Da kyar ta dage tad’an ci abincin dan yadda taga daddyn abuja yadamu da rashin cin abincin nata, bai san cewa wannan d’in ma daure wa tayi tafara ci ba dan ganin suna nan,amma in su kad’ai ne ita da iyayenta ma ko kula dining d’in batayi musamman in abincin rana neh,su har sun riga da sun saba da wannan halayyar tata.

Kwanan su Daddyn Abuja d’aya washegari suka koma Abuja,dayake daman wani abu ne yakawo su garin,shine har suka kwana.

Teemah jitayi kamar ta bisu da zasu tafin don ita akwai son mutane sosai.

Baifi wata biyu da tafiyarsu ba Daddynta ya shirya wai zasu je passing out d’in Abbas a katsina shida su daddyn Abuja,Allah ya kiyaye kawai Teemah tayi mar tare da fad’in ya gaida mata da su ummah da daddy.

Har gun mota suka rakashi

“shiga yayi bayan ya amsata driver yaja suka tafi airport.

Haka suka je lapiya qalau cikin ikon Allah.acan suka had’u da su daddyn Abujan har sun rigashi isa ma.

Abbas yayi murna da zuwan Iyayen nasa,inda suka gama abinda yakawo su cikin sa’a har zasu tafi ma sai kuma Daddn yace su jira Abbas d’in kawai inyaso su taho tare tunda shima washe gari zai tafi.

Kud’i sosai su daddy suka kashe kafin Abbas yasamu wannan matsayin,don da farko har daddyn Abuja ma yace wai sai dai Abbas d’in ya hak’ura ya bari ya nemi wani aikin,amma daddyn Teemah yace sam baza’ayi haka ba, don sanin daya yiwa Abbas tun yana k’arami burinsa kenan,Burinsa yazama sojan Nigeria,dan haka ya dage sai da yaga burin Abbas ya cika,don acewarsa rashin bada muhimmanci akan al’amarin yara yana matuk’ar affecting d’in cigaban yaran.don haka ya tsaya tsayin daka ya shiga ya fita har sai da yaga burin abbas d’in ya cika kafin ya samu salama.Dayake daddy yana da manya kuma yabi masa ta sama ne,kuma short service yaje, shima Abbas d’in ya shak’i karatu sosai shiyasa cikin sa’a yafito da babban matsayi, amma kafinnan fa aljihun daddy sai da yayi kuka.A can katsinan aka barshi ba aka kaishi ko’ina ba amma kafinnan sai yayi hutu tukunna zai koma gaba d’aya…..Da zasu dawo su baro katsinan Abbas bai bi su ummahn sa zuwa Abuja ba sai yabiyo daddyn Teemah suka taho tare. +

Yanda yatarar da gidan ya matuk’ar birgesa,musamman yanda aka canja tsarin gida ya koma na zamani,hakan ya k’ayatar dashi.Aransa yakejin ai hakan yafi da ace ana ta canje canjen muhalli ana bin zamani ai gara ka renovating wanda kake dashi in hakan zai yiwu.

Sosai yaji daddyn ya burgesa da irin yadda ya maida gidan “so take away😘

Bakamar daddynsa da kullum cikin canja muhalli suke ba.

Lokacin da suka dawo Teemah na school,bayan ta dawo ne ta tarar da daddyn ta ya dawo,murnar kamar tacinye sa d’anye.Inka ganta sanda ta ke murnar zaka zaci tafiyar shekara guda yayi,nan kuwa kwanansa uku kacal da barin gidan.Sai data gama murnar sannan daddy yace toh taje ta gaida yayanta,shima yazo yana d’akinsa,Zaro ido tayi waje sannan tace “daddy wani yayannawa?”

“Abbas neh angel ,Abbas na Abuja.”

Daddy ya bata amsar tambayar data yi.

“Owk”

Tacewa daddyn
Sannan ta k’ara da “amma daddy barinje incire uniform d’innan tukunna”
Tafad’a tana kallon fuskar daddyn nata.

“Uhm,jeki cire abinki”

Daddyn ya bata amsa da haka.

Tashi tayi ta sannu ta d’auki school bag d’inta,harta fara tafiya sai kuma tace ”daddy ina mummy fah”

“sai yanzu kika ga daman tambayar inda nake ko?

“Wato dan kinga daddynki ko?

Muryar mummy tajiyo tana fad’in hakan,yayinda daddy yafara dariya k’asa ‘kasa.

Waigowa Teemah tayi nan ta hango mummyn awajen dinning tana k’ok’arin daukan abu.

Karakata kai tayi gefe .

Mummyn ko kulata ma batayi ba,data d’auki abinda zata d’auka ficewarta tayi tabarta a inda ta ke tsaye.

Daddy ma kauda kai yayi kamar bai san meke faruwa ba.

Ganin haka yasa ta fice kawai daga parlourn, d’akin ta ta nufa,kamar yanda tasaba sai da tacire uniform d’in kaf,kafin nan tanemi towel ta d’aura ajikinta.

Toilet tashiga ta watso ruwa tare da d’auro alwala,Shiryawa tayi cikin wata gown na material marar nauyi,d’inkin ya mata kyau yayi cifcif dajikinta wani k’ara min gyale ta d’auko wanda bai ma fi ak’ira shi da d’ankwali ba,ta yafa akanta.

Parlourn ta koma ,dan ita kwata-kwata tama manta da batun wani yayah,amma haka sai tana jin ranta wani iri sai taji bata da nutsuwa.

Daddy tasamu still azaune yana kallon news d’in rana,aranta tace

“daddy da news badama.”

Shiganta keda wuya tun ma kafin ta zauna kamar had’in baki sai ga mummy ta 6ullo ta itama har tayi wanka tacanja 

muryar Mummyn tajiyo tana fad’in “yauwa Teemah yiwa yayanki magana kinji,lunch is ready”.

Dum taji zuciyarta ta amsa,bata san dalili ba,amma tafi kyautata zaton k’ila dan ta jima bata had’u dashi bane shiyasa.

Dayake daman bata kaiga zama ba,sai kawai tajuya ahankali ta fara tafiya dan zuwa aiken mummyn.

“Ni kinma je kin gaidashi kuwa?”

Tasake jin muryar mummyn tafad’I.

Kai ta jijjigawa mummyn batare data waigo ba dan duk jitayi jikinta yasaki.

“baki san yazo bane?

Mummyn tasake tambayarta.Ynzun kam saida ta waigo kafin tace “nasani mummy,d’azu daddy ya fad’amin,daman inada niyyar zuwa”
Kai alanga6e tayi maganar kamar zatayi kuka.
+

“Hmm”

kawai mummyn tace,daganan bat qara kallon inda Teemahn ta ke ba.

Daddy kam k’ala bai ce musu ba.

Juyawa tayi taci gana da tafiya,koda taje k’ofar d’akin nasa ma jitayi kamar karta shiga,amma data tuna cewa mummy ce ta aiketa aikawai sai tayi shahada ta tura k’ofar ahankali tashiga sannan ta maida k’ofar ta rufe,gani tayi d’akin duhu bak’i k’irin ba haske,neman inda switch yake tayi ta danna,amma still ba haske.

Hakan ya tabbatar mata da cewa bulb d’inne suka lalace,kuma dayake ba’a cika amfani da d’akin ba shiyasa babu wanda yabi takansu,ballantana a canza su.

Ahankali ta k’ara cikin tsakiyar d’akin jitayi shiru ba alamar motsi,sai de uban k’anshin turaren da yau ne farkon fara jinta dashi,da kyar ta tattara la66anta ta harhad’a sunansa.

“Yah….yah Abbas”!

Shiru taji

“Yah Abbas”!!

Ta sa ke maimaitawa amma still no answer.Juyawa tayi tafita daga d’akin,taje tasanar da mummy akan bayanan Yah Abbas d’in.

“Babu inda Abbas yaje Teemah,k’ila ko zuwa bakiyi ba”

Cewar mummy

Teemahn ne ta kar6e da fad’in…..

“Allah naje mummy,kuma fah d’akin duhu ba haske”.

D’auki wayata ki haska,maza kije ki dubo minshi, inaga ma bacci yake saboda gajiya”

Tana d’aukan wayar tace “mummy harfa k’ira nayi amma babu wanda ya kulani”

“Shine ai nace ki duboshi in bacci yake karki tasheshi,ki dawo kawai”k’ila ma dakika ga duhun k’in shiga kika yi ko?

Kwa6a fuska tayi 

“Nashiga mana mummy “

“Naji toh ni sauri ki dawo”

Mummyn tafad’a sannan takawar da kanta gefe.

Fita Teemah tayi ta nufi d’akin Abbas d’in,data isa bakin k’ofa zai ta tsaya ta kunna hasken wayar kafin ta tura k’ofa tashiga.

Ko sallama batayi ba don ita azatonta babu kowa ad’akin kamar yanda ta tarar dashi d’azu.

Saida ta maida k’ofar ta rufe kafin ta d’aga hasken hannunta haska,Hasken ya gama haska ilahirin d’akin ,don wayar mummyn badai haske ba.

Mutum ta hango a tsaye dogo mai d’an hasken fata,k’ugunsa d’aure da towel,wuyansa ma wani towel d’inne rataye kuma duka farare,hannunsa d’aya riqe da man shafawan daya d’auko da niyar shafawa, jin an6ud’e masa k’ofah batare da neman izini bane yasa ya tsaya,dan yaga wani gwani ne wannan.

Ko tsoro bataji ba tasake daidaita hasken asaitinsa a k’ok’arinta naganin wannan mutumin da akace wai shine yayanta.

Hannunsa d’ayan ya d’aga ya kare hasken dashi,dan ta saita masa ne afuska,sannan ya mik’a d’ayan hannun ya ajiye man shafar.

Kallon mai haskashin yake da mamaki,so yake yaga waye wannan d’in,amma dayake hasken ahannunta yake sai hakan ya hanashi ganinta dakyau.

Takowa yafarayi zuwa inda ta ke tsayen,amma still bai sauk’e hannun daya d’aga dan kare hasken dashi ba.

Bata motsa ba,kamar yanda bata kawar da hasken daga saitinsa ba,sai da taga yakusan cimmata kafin tajuya bayan ta yada wayar agurin,ta nufi k’ofa da gudunta.

Tsayawa yayi cak,daga inda yake tsayen, sai ya kama kunkumi da dukka hannayensa biyu gefe da gefe,yabi bayanta da kallo,harta k’arasa bakin k’ofar. +

Jijjiga kansa kawai yayi jin yanda ta ja k’ofar da k’arfin gaske.

Idonsa ne yakaiga wayar data jefar d’in garin gudun rashin gaskiya.

“Hmm”

afili,sannan ya k’arasa ya d’auki wayar ya kashe hasken.Daganan ya koma ya d’auki mansa ya shafa ya shirya ya fito da wayar a hannunsa.

Ahankali yake takawa danko k’arar takalmansa ma ba’aji.

Abakin k’ofar shiga parlourn yayi sallama,daga ciki daddy ya amsa masa,jin amsawan da akayi ne yasa shi d’aga labilen yashiga fuskarsa cike annuri……..

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]