[Advertisements⬇️]

WANI AURE CHAPTER 32 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WANI AURE 

CHAPTER 32

A matukar haukace ummi tayi kan zeeent Tana jijjigata tana kuka tana kiran sunanta zeenat …..zeenat ki tashi dan girman Allah ki tashi kar ki min hk kar ki mutu kibarni ….idan wani Abu yasameki bazan taba yafewa kaina ba nice sanadin komai ni najawo miki duk wannan wahalar da maseefar please zeenat…. 

shima deeni a zabura ya mike tsaye yayo kanta yana girgizata da wani irin sauri yaje ya dauko ruwa yashiga tsiyaya mata Amman still ko motsi batayi ba hankalinsa yayi mugu mugun tashi fiyye da tunani me karatu. sunanta kawai yake Kira yana girgiza kumatunta hatta haidar da Anan kuka suke sosai banda junior dake zaune yana kallonsu yana sheshekar kukan dayaci. 
hannuta haidar da Anan suka rike suna kiran sunanta aunci aunci ki ta chaci ki chaci aunty dady yace ki chaci deeni ya tallabota agigice ya rungumeta jikinshi yana kiran sunanta gabadaya ya rikice yarasa yadda zaiyi .
da inda zai nufa daita kawai ya cicibeta ya nufi dakinsa daita ummi da yaran na biye dashi abaya suna faman kuka Yana shiga dakin ya kwantar daita akan gadonsa.
” ummi wacce gabadaya tagama rudewa da gigicewa ta fita haiyacinta tarasa takamaimain abinda yakamata tayi .
ta saka wani irin Kara tare da cewa Dan ubanka nan yakamata kayo min daita ko hospital? Uhmmmmm wato kana son kashe min ita ne ko ? 
Deeni da alamun kana bukatar ganin bayana kanason ganin karshena wallahi muddin wani Abu ya samu zeenat wlh wlh bazan yarda ba .
bazan barka ba sai nayi kararka zuwa court… azubure ummi ta sake frigita ganin yadda kwata kwata zeenat bata motsi bata numfashi sai surutai kawai take zuwa tana zagin deeni. 3

A matukar hassale deeni ya juyo yana kallon ummi muryarsa a kausashe yace haba ummi ya kike son nayi da rayuwata? 

Ni kaina bazan so wani mummunar Abu yasameta ba first love.
ko babu komai zeenat Matata ce km yar uwata ce front &back babu ta inda zan yakiceta ajikina da zaki dinga cewa idan wani Abu yasameta bazaki yarda ba bazaki barni ba …….
ince duk kece kika jawo mata wannnan matsalar da tashin hankalin kece da kanki zaki kasheta da hannunki bani ba kece kika sakata cikin wannan damuwar da tashin hankalin bani ba da tun farko kin barni nayi aurena abayyane tasani kowa yasani da duk hk bata faru ba .
Amman gabadaya first love kin hana komai kin bata komai kin ruguza komai Amman kina neman daura min laifin da banawa ba. 
wlh first love koni idan wani abu yasamu zeenat ni da kaina zan fara kai kararki court kafin ki kaini .
Dan ni aka fi cuta kisani yin *AUREN SIRRN* da yarinyar mutane batare da saninta ba sbd kawai naki farincki keda yarki kina neman kaini wuta first love bisa ga zunubin zeenat yarinya tana aikata kuskure Amman Kiri Kiri baki son laifinta baki tsawata mata bakison wani yayi Mata hukunci bisa ga kuskurenta yanzu WA gari yawaya? 2

Ummi ta fashe da wani irin mahaukacin kuka batasan sanda ta cire Hannuta ta daukeshi da gigitaccen Mari tana kuka tace yanzu deeni har mu kawo wannnan stage din?

Yanzu ni Kake gaggayawa mgn hk? 
ina fada kana fada?Nice nazama abar sakace hakoranka.
ni kake fadawa duk abinda yazo bakinka dan kawai soyayyar wata ya Rufe maka ido .Amman wlh bazakasan bakada hankali ba sai kabari wani Abu yasamu zeenat dina a sanadinka lokacin zakasan ko waceceni.
km lokacin zakayi dakasanni kasancewata uwa gareka ta juya fuuuuuuuuuu ta nufi dakinta da sauri har tana hadawa da gudu gudu ta dauki waya tana kiran family doctor dinsu hawaye na Bin kuncinta.

Jiki a matukar sanyaye deeni ya dauko ruwa a fridge yashiga kwara mata still shr Kake jin zeenat ko gezo batayi ba wayarsa ya zero yashiga neman layin doctor yana zariya adakin yaran suka haye gado suna jijjigata da kiran sunanta idanusa ya zuba masu Yana mamakin yadda yaran datake jin haushin akan sunki sabawa daita suka damu daita..

duk da basanin halin datake ciki suka Yi ba .
ya runtse idanunshi daidai lokacin da’akayi pik din call.
a hanzarce ya bada Umarni kawai tare da cigaba da kaikawo acikin dakin ….hankalinsa atashe.

Yayinda nablah dake tsaye a parlour junior rabe ajikinta .

sbd tsabar rudewa da frigicewa da tashin hankali ganin abinda take gani sandarewa tayi agurin tazamo tmkr mutun mutumin tabbas babu karya cikin zancen deeni .
fuskar mahaifinta take gani har lokacin yana murmushi wanda tarasa na mene yana cigaba da daura aurenta da mutumin dake ganin jegoni ne arayuwarta .
babu abinda take gani sai hoton mahaifinta yana mikawa wasu daga cikin makwatansu hannu suna gaisawa alamun angama daurin aure yana musu godiya.

Nocking din kofar parlour gidan ake da Danna bell da karfi. 

koina agidan ya karade da sautin Kara deeni yA fito da sauri ya wuce nablah tsaye wiki wiki da idanu still tana kallon TV wanda ke sake rewaning din kanshi.
ya nufi kofa yana budewa yaga Ammar tsaye aiko take ya hade rai dan tunani shi ya dauka doctor ne yakaraso. muryasa a dan kausashe yace ya’akayi ne? 
Amar yace daman Big dady ne yace kazo yanzu yanzu yana son ganinka gabansa ya buga yashiga dukan uku uku nazo fa? 
Amar yace uhmmmmm hk yace. 
OK kace masa gani nan zuwa bai tsaya bi takan amar ba ya juya yakoma ciki tare da kule kofar. Ya 
Janyo hannu nablah gabansa na tsananta faduwa ya zaunar daita please nabeelah ki dawo cikin haiyacinki kisanyawa jikinki natsuwa kinsan bake kadai bace kurka sa zuciyata ta buga… shr kawai tayi takasa cewa dashi komai still imagine din abinda ke faruwa take acikin memory dinta .
yaja hannuta cike da sanyi jiki muje ki sauya kayan jikinki kin mikewa tayi sai ma alamun da tayi masa da kanta daya barta kawai.dan hk yabarta ya Mike yaje dakinta ya dauko mata doguwar riga ya zira mata daga zaune a in datake ..

Byn kmr mitin 15 sai ga doctor yazo .

da hanzari deeni ya shigar dashi inda zeenatb take kwance tmkr matacciya.
batare da bata lokaci ba yasoma AIkinsa cikin iya da kwarewa ummi takasa tsaye takasa xaune ta fice daga dakin tana adduar Allah yadawo mata da numfashin diyarta kuka take sosai tana furta duk adduar datazo bakinta da adduar da mutun zai Yi idan yana cikin kunci da damuwa *allahumma lasa’alah illa maja’altahu sahla WA’anta taja ‘alul huzna iza shita sah’alah*
Shi take ta maimaitawa da Inna lillahi wa Inna ilahi rajiun…

Shiru shr Big dady zaune zaman jiran zuwa deeni shr har awa daya ta wuce bai ganshi ba .

ya yunkura ya mike tsaye tare da sandarsa yasoma takowa ahankali yana saukowa daga balcony dinsa dan duk dramar da akayi akofar gidan deeni akan idonsa komai ya Faru kasancewar babu wani nisa tsakaninsu tundaga lokacin da zeenat ta hankado nablah harabar gidan ta fada kirjin deeni har zuwa sanda deeni ya rungumo yarinyar da bai san kowacece ba zuwa cikin gidan.
tun lokacin hankalinsa ke tashe yakasa samun natsuwa. Ahankalin dattijon yacigaba da takowa har ya sauko zuwa harabar gidansa tare da kwallawa amar Kira …
amar yataso da sauri yana amsawa Big dady yace muje ka kaini gidan deeni .
amar yacewa big dady yaface yana zuwa.. Nidai kaini kawai hankalina yaki kwanciya da alamun akwai wata Matsalar dake faruwa agidan. 
Hk suka shiga mota amar yaja sai gidan deeni amar yayi parking ya fito da sauri ya budewa big dady kofar motor .
big dady ya fito ya nufin door din gidan da kanshi yashiga dannan bell deeni ne still yazo ya bude masa yana ganina ya hau shafa keya yana masa sannu da zuwa kana yace big dady ai dakayi zamanka zanzo koda baka zo ba yakarasa fadar hk yana me bawa dattijon hanyar shigowa wanda daidai wannan lokaci numfashin zeenat yasoma dawowa tana farkawa ta saki wani ihu me karfi gaske deeni ya bar big dady zaune ya hanzarta da sauri.
” shi da ummi suka shiga rigerigen shiga dakin tana ganin ummi ta sake rushewa da wani sabon kuka ummi ta rungumeta ajikinta tana kuka zeenat na kuka shi dai deeni godiya yashiga yiwa Allah dayasa numafshin ya dawo jikinta .
yakarasa inda take rungume da ummi yakamo hannuta yana mata sannu tayi saurin zame hannuta cikin nashi tare da rutse idanunta alamun batason ganinsa. 
ya mike jikinsa a matukar sanyaye yana yiwa doctor godiya suka fito daga dakin suka nufo parlour inda big dady ke zaune .
suna fita numfashin zeenat yasoma sezing da kyar take jawo shi tana fitawar .
ummi ta saketa ta rugo da gudu tana kiran deeni da doctor turussss tayi ganin big dady zaune yana rike da junior yayinda idanunshi kyam Akan nablah wace har lokacin bata cikin haiyacinta .
take ummi tawayance tare da nuna wa doctor hanyar dakin da zeenat take. 
Doctor ya juya ya da wani irin mahaukacin sauri ya koma .
bayan doctor ummi tabi batare ta tsaya bi takan big dady ba.
tayi cikin dakin da sauri byn komai ya daidaita numfashinta ya dawo normal wanda zuwa lokacin kukanta ya Dan Tsaya sai numfashi datake janyowa.
da kyar ta bude bakinta kmr batason yin mgn tace ummi fitar Dani daga dakin nan zuciyata ummi zata buga idan nacigaba da zama cikinsa .
babu mutsu jiki na rawa ummi ta kamota jikinta suka fito .
kiyi hkr manana kiyi addua mamana zaki ji saukin radadin abinda ke damunki.ta nufi hanyar up stairs daita da niyyar kaita dakinta zeenat ta girgiza mata Kai ummi karki kaini… Kifitar Dani daga gidan nan gabadaya banason zama cikinsa take ummi tayo Hanyar main parlour din gidan batare da taso ba.

Yayinda big dady still yana zaune suna zantawa da deeni ya bude bakinsa Kennan da niyar tmbyrsa abinda ke faruwa ya hango tahowarsu ummi zeenat makale agefenta suna takawo ahankali yayi shr kawai yana dubansu.

ganin hk yasa ummi kasa wucewa ta gabansa ta zaunar da zeenat akan kujera itama ta zauna hannuta rike da yatsun zeenat sai lokacin ta gaida Big dady .ita ko zeenat kasa mgn tayi ta runtse idanunta gam tana jijjiga jikinta… Big dady ya amsa gaisuwa yana dubansu daya byn daya gabadayansu har nablah fuskarshi dauke da tambayoyi irir iri.
sai daya gama nazarinsa akansu tsab sannan ya numfasa yace ya duk naganku wani iri hk kmr akwai damuwa meke faruwa daku ?

Deeni yayi Shiru yayi kasa da kanshi yana yashafa keyarsa gabansa na cigaba bugawa jira kawai yake yaji abinda ummi zatace.

ahankali yaji sautin muryar ummi tace babu komai big dady. 
deeni ya dago kanshi da sauri yana duban ummi afrigece take suka hada ido ta tawatsa masa wani irin kallo tare da wata uwar harara sbd atunaninta shine yakira big dady .
big dady yace ya ina kallon tsantsar damuwa da tashin hankali afuskokinku har wannan baiwar Allah da bansa kowacece ba Amman fadeela kice min babu komai .
ummi ta daure fuskasta sosai ta sake cewa babu komai big dady .
ganin da deeni yayi kmr ummi batason asan abinda dake faruwa agidnsa ballantana asamu matsalaha Da daidaituwar lamari. 
gashi shi yanzu yagaji Da boye boye gara ayita takare kowa ma yasan komai shi badamuwarsa bane. 
dan haka gabansa na bugawa da karfi. muryasa a dake yace big dady akwai damuwar nan fa da tashin hnkali wanda km duk first love ce silar komai .ya sauke numfashi da ajiyar zuciya kana yacigaba 
big dady wannnan yarinyar da kake gani zaune yana nablah da yatsansa *MATATA CE* ta Susan wacce ummi ce da kanta takawo min ita gidan tace na aureta batare da duniya tasan da hk ba .
Big dady yayi Jim yana kallon deeni da ummi da da alamun yana bukatar Karin bayyani daga gunta. 
ummi ta tsunkuyar da kanta kasa Take wani gumi me zafi ya rufeta.zeenat ta dinga kallon ummi zuciyata na bugawa tason taji ummi takarya ta abinda deeni yace Amman taji ummi tayi shr .muryar na rawa tace karkawa ummi karya yaya ummina bazata taba min hk ba wlh, deeni ya watsmata wani kallo kana
Ya gyara zama yashiga zaiyanewa Big dady komai daki daki daya fair tun daga farko shirya lamarin har karshe .big dady dake zaune yana sauraron deeni har sanda ya dasa aya ya numfasa yana duban ummi sannan yakira sunanta fadeela kina jin abinda deeni ya fada meye gskyr lamari…..?  Ummi Tayi shr tana kallon big dady… Kennan gaskiya ne abinda deeni ya fada ta fashe da kuka tana jijjiga kai alamun hk ne… Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kawai big dady yashiga furtawa yana maimaitawa yana kallon ummi jikinsa a matukar sanyaye..Wani irin razananiyar Ihu May karfi gaske zeenat ta saka tayi zumbur ta Mike tsaye jikinta na kirrrrma ta jingina jikinta da bangon gurin tana duban ummi afrigice sannnan ta fashe da wani marayan kuka me taba zuciya da cin rai tace Wayyyyyyyyyyyyyo allahnah ummi kin kasheni na mutu na lalace wayyo ni muZeenat shikenan tawa ta kare atsorace deeni ke kallon zeenat yadda ta birkice ta fita haiyacinta ta zama tmkr wata sabuwar mahaukaciya sabon kamun hauka .
ta haukace ta Dinga kuka tana ihu tana kiran ummi kin cuceni ummi kin rabani da farincikina ummi ta dafe kirjinta azuciyarta narawa aranta tace tabbas na cuceki manana Amman bansa hk abun zai juye bisa kaina ba. 
kinci amana ummi kin yaudareni kin ci amanata kin cuceni .
da mahaifiyata na Raye nasan dabazaki min hk ba yanzu ummi ke da kanki kika yiwa zeenat dinki kishiya…..
Keda kanki zakiwa zeenat dinki kishiya..kishiyar ki rasa wace zakimin sai  yar aikina…. gsky baki kyauta .
Baki kyauta min ba ummi sbd bana haihuwa .
laifin danayi  ban cancanci wannan hukuncinba yar aikina fa ummi .
Ummi wani cikin ne fa daita har na tsawon wata shida nan da wata uku zata sake haifar masa wasu ya’ya nashiga uku ni muzeenat wannan wace irin bakar rana ce gareni .
ta sake zabura tayi wani irin ihu tayi kan nablah ummi tayi saurin rungumeta ajikinta tana kuka ummi nayi .
kiyi hakuri diyata bawai nayi hk Dan na  cutar dake bane diyata .
nayi dan nema maki farinciki acikin rayuwar aurenki ne. 
bansan gadar zare nashiryawa diyata mafi soyuwa araina ba tun ba yau nake kukan nadamar abinda nayi  ban km san rashe zai juye da mujiya ba  kiyi hkr tabbas kuskurena ne ya jefaki cikin bakinciki dakike ciki.
Amman duk rintse duk wuya bazan taba Barin ki wulakanta a duniya ba matukar ina raye ina sonki zeenat fiyye da komai dake cikin duniyar nan  adalilin sonki yasa na aikata hk.. 
kuka suke sosai gwanin ban tausayi. Kuka zeenat tacigaba da Yi Don yanzu wani irin haushin ummi takeji matuka acikin ranta ganintake duk abinda ya sameta ummi ce silar komai ahankali ta dinga zame jikinta daga jikin ummi tana girgiza kai tana kukan ummi kin cuceni kingama da rayuwata kin kassara zuciyar zeenat dinki tunda Arasa wace zaa min kishiya daita sai wannan ….. Diyar talakawar Mara galihu wacce sanadin babu taxo aikato ina zaune da kishiya guri daya batare da….big da ya katseta yana girgiza Kai batare ya iya furta komai ba dan gabadaya abin ya girmama tunaninsA bai Taba jin inda akayi aure irin wannan ba.

Wani irin kallon nablah kewa zeenat ME tattare da tsansar takaici 

Take  tana gama jin komai tazama mahaukaciya tuburan tafita daga hankalinta tafita cikin natsuwarta tasoma surutai bake kadai aka cuta ba aunty har Dani .

ni aka cuta wallahi ni aka cuta ..hankalin amatukar tashe takarasa inda deeni yake tsaye yana dubanta tashiga nunashi da yatsanta deeni ka cuceni na tsanaka bana sonka bana kaunarka deeni na tsaneka har abada bazan taba sonka ba kai ne Ashe kasaka rayuwata Cikin kangin rayuwa da bakinciki da ukuba da tsananin kunci rayuwa .

kai ne ka ruguza min farincikina ka lallaba ka dirka min ciki yanzu ga wani ciki .

Meyasa baka zo min a siffarka ta mijina ba ?

Meyasa baka Aureni ta hanyar da Allah ya halallata aure  ba ?

Meyasa baka inganta rayuwata ba ?

kasa na haifi  ya’yana a wulakance ankirasu da shegu alhalin  halallatattu ne ankirasu da yayan zina Kasa ankirani da Mazinaciya karuwa deeni …..kasa ni kaina ina zargin kaina .

Kasa ni kaina nakasa yarda da kaina takarasa mgnr tana zubda hawayen tausayin Kanta ahankali ta juya tsaitin da ummi ke durkushe Gaban zeenat har lokacin suna kuka me taba zuciya muryarta cike da matsanancin kuka tace  ummi yanzu  inda yarki ce ni ta cikinki zaki yarda Amata irin wannan auren wulakancin da kaskancin kodayake ma diyar da kike ikirarin kina sonta itama kincin amanatar duk da yake mu talakawa ne ta maida idanunta cikin na zeenat sosai sannan tacigaba da mgn cike da tashin hankali.ba kaskantattu bane mu ba Km wulakantattu bane ko aikatau da kikaga nazo Yi .
tawa kaddarar ce tazo hk bawai talauci ko rashin abincin dazamu ci bane yasa haka .
mahaifina bai da matacciyar zuciya sbd har yau yana neman na kanshi km yana rufa mana asiri tunda bai bar mu da yunwa ba ko kishin ruwa tunda ba tsirara muke yawo ba. 
Da zakice yar talakawa yar aiki naji ni yar talakawa ce Amman na mishi ranar da ke baki mishi ba .
Sosai ta dinga sakin magannu batare da wata fargaba ko shakka ba hakika ummi ke da danki kun cuce rayuwata.
ummi  na rikeki  bisa amana tmkr mahaifiyata  Amman sai gashi yazamanto da saka hannuki cikin jefa rayuwata cikin matsanamcin kangi me wuyar fita .
wlh wlh yau ko numfashina zai Kare sai nabar muku gidanku  ta sake Maida shanyayyun idanuta masu cike da ruwan hawaye kan deeni  sosai tana kallonsa wasu ruwan hawayen na tsiyaya, tasa hannuta ta goge hawayen kana tace ya’ya km naka ne na dade ina kwankwanto hk acikin zuciyata deeni na dade ina zargin wani alamari game da Kai. 
Na Dade ina tunanin cewa kaine kake zuwanmu acikin mafarkina ashe bamafarki bane gaske ne ummi na  dauke uwa nabi ki har daki nagaya miki matsalar dake damuna game da aljanu suna ku santata Amman kikace min wai babu wani aljanu  nayita addua kin mata Ashe dake aka hadu ake son tsaida yancina zuwa bauta…. +

Meyasa ummi ?

Meyasa kikayi hk wlh ban taba tunamin hk dagareki ba ummi ..ko numfashina zai dauke koda zan rasa komai da kowa arayuwata zan tafi zanbar  gidan nan yau km a yanzu km wallahi bazaka taba mallakata ba deeni sbd hanyar da biyo gurin mallakata. kabiyo ta hanyar da bata dace ba sannan km ya’ya  nakane gasu nan sannan km wannan cikin ko Zan mutu bazan haifeshi ba  .deeni ya zabura ya matso gareta jikinsa na rawa zai tabata tayi karka taba mugu ME cin amanar ya’yan mutane ta juya da sauri tayi hanyar dakinta..

Wani irin kuka xeenat ke Yi nafitar hankali da taba zuciya ahankali big dady da kanshi ya mike ya dagota ya runguneta ajikinshi yana shafa bayanta sun kusan miti goma ahaka sannan ya Dakota ya kura mata idonsa dake cike da ruwan hawayen tausayinta .. Girgiza Kai tafara cikin kuka tace big dady karkamin kuka kada kada zubda hawayenka akaina duk abinda ya faru Dani ,ni njawowa kaina. Da kaina da nayi hkr lokacin da Allah yabani nawa arxiki ya’ya da yanzu ban tsinci kaina cikin wannan damuwar da tashin hankalin ba. Gabadaya tausayinta yakama mutane gurin. Kuka take sosai tana nadamar abinda ta aikatawa rayuwa ta rarrafa zuwa inda ummi ke zaune tana goge hawaye.

ta daura kanta bisa cinyoyin ummi.. Ummi kiyi hkr kiyi hkr ummina ki yafemin ki min aikin gafara bisa furuncina gareki bazan taba yin fushi dake ba ummina nasan ni na cuci kaina bakece kika cuceni ba nasan kinyi hk ne sbd daurewar faruncikina a gidan yaya bazan taba butulce miki ba ummi duk duniya banida wacce tafiki …Tana kuka take mgn ummi ina neman alfarma agurinki ki taimakamin kisa deeni ya   sauwakemin aurenshi dake kaina na hutawa rayuwata da ganin bakin ciki.
ummi tashiga girgiza mata kai tana kuka..  ummi bazan iya ganin da jurar kallon yaya tare da wata ba .
zuciyata ummi zata tarwatse zan mutu…. Mutuwa zanyi ummi muryata cike da kuka takarasa mgnr…haidar da anan har junior da suke zagaye da ummi suka shiga goge mata hawayen dake tsiyaya da hannusu….

Yaran kamar wasu manya suka rungume ta, suna kuka, itako Nablah da gudu kamar zararriya ta sauko daga sama tayi hanyar fita, kota kan yaran bata bi ba balle kayan ta, cikin zafin nama Deeni yayi kanta ya manta da jama’ar dake falon, rik’o ta yayi gam a jikin sa, yace ” pls Nablah karkiyi min haka, karki guje ni, kar ki hukuntani da laifin da ba nawa ba, wallahi kece rayuwata idan kika barni mutuwa zanyi, matuk’ar bakya kusa dani Nablah rayuwa ta bata da wani amfani, ke haske ce a gare ni, pls karki min haka, ya k’arasa maganar hawaye nabin fuskarsa, da k’arfi ta hankad’e shi ta kalleshi  ido cikin ido ta nuna masa yatsa tace ” don’t, don’t ever touch me again, I hate you Deeni, you are monster, you are cheater,you are liar, deceiver,  I don’t want to see you again in my future life.

, ka yaudare ni, na yarda dakai, na d’auka kafi kowa so na, da tausayi na, ashe kai mugu ne, I can believe it, Deeni kaine kayi man haka. Duk   yaran suka taso suka bar jikin zeenat suka rungumeta a fusace ta cire su daga jikinta. Tana cigaba da mgn. +

Yara gasu nan, dama sune burinka, to Allah ya cika maka, ka rik’e kayanka, Deeni yace ” pls Nablah you are my life, don’t live me, murmushi tayi cikin kuka tace ” ur life, kanka kawai ka sani, ta juya zata fita, da sauri yace ” a matsayi na mijinki ban baki izinin fita ba, juyowa tayi ta tako gaf dashi tace ” miji!!! , ta nuna shi tace ” wai kai kana tak’amar miji, gaya man meye miji meye aure?

“Sannan ka sanar dani hakki na d’aya dakataba  sauke min, bayan biyan buk’atar kanka, kai yanzu baka ji kunyar kiran kanka mijin Nablah ba, yanzu .

Deeni shi kanshi mahaifina  kaji kunyar sa, bai sanka ba, bai san daga inda ka fito ba ya d’auki ‘yarsa ya baka, ya baka yarda da amana, nasan mahaifina ba dan matsayinka ya bakani.
  dan nasan baima san waye kai ba, balle yasan abinda ka mallaka, Deeni daga ni har mahaifi na ka cuce mu, ka yaudare mu, amma ba komai Allah na nan, ta juya saitin zuciyar sa ya dafe, yana kuka sosai kamar k’aramin yaro ya matso inda take, yace ” wallahi Nablah ina sanki fiye da komai da kowa a duniya you  are my first love, I love you so much, wallahi Nablah idan kika barni zuciya ta bugawa zata yi, mutuwa zanyi Nablah, rayuwata bata da wani amfani matuk’ar bakya tare dani.

Wani irin mahaucin kuka Zeenat ta saka tabar jikin Ummi tace ” Ummi kinga abinda kika jawo min ko?  Ina zaman lafiya da miji na kin d’auko min bala’i tunda nake da Deeni bai taba’a furta  kallar koda yana so na ba , balle yace he love me so much, Deeni bai tab’a gaya min kalaman soyayya ba, Ummi alhakin Nablah ne zai kamaki, shiyasa Allah ya jarrabi Deeni da sonta fiye dani, koma ince fiye da kowa harke tunda kema da kunnanki kinji abinda yake cewa akan ta, Ummi kinga yadda tunaninki ya cutarda mu, ta k’ara fashewa da wani mahaukacin kuka.

Shidai Big Dady kallan su kawai yake ya rasa abinyi, nablah tasoma daga kafafunta Deeni yace” pls ku taimka kuyi mata magana kusa baki karta tafi ta barni, wallahi ita ce rayuwa ta, kafin kowa yayi magana Nablah tace” wallahi ko mutuwa zakayi deeni sai na barka, kai koda gawarka kace a gaba na zan saka k’afa na tsallake ta, tasa hannu ta share hawayen dake zubo mata tace ” akan me zakayi *AUREN SIRRI* dani,.

shi ban kai maccen da za’ayi Auren bainar nasi dani bane komai?

Kai ya girgiza mata yana kuka kamar wani k’aramin yaro, tace” san kai ne yasa kayi min haka, ka aure ni, ban sani ba, ka rink’a kusantata ba tare dana sani ba , harka yi min ciki, ka k’ara lallab’owa ka d’irka min wani ciki, yanzu ma in banda Allah ya toni asirinka da sai dai kayi tayi man haka, ina haihuwa ka yanke min jin dadi kanannaye komai na rayuwata ta fashe da wani sabon kuka tace ” Allah ya isa Deeni, Ubangiji ya saka min, & I will never for gv u, ta jiya zata fice sosai Deeni ke kuka ya durk’usa gwiwa bibbiyu a gaban Nablah yana kuka wiwi yana rok’onta karta barshi.

Zeenat ma kukan bak’in ciki take, a gabanta mijinta yake durk’usawa agaban macen da bata kaita komai ba yake rok’onta ta so shi, zuciyar Ummi kuwa kamar zata tsage don bak’in ciki da takaici, ji take kamar ta d’ora hannu  aka ta fasa ihu, ta gwammaci mutuwarta da ganin wannan rana, Deeninta …tilon danta mai kyau,da tarin ilimi,da  aji, gata, ga naira, yau shine yake rusa kuka durkushe a gaban mace yana rok’on soyayyarta, a gabanta kuma ba Zeenat d’inta ba.

Deeni na dafe da zuciyar sa, yana kuka a gaban Nablah, ganin zata fita ne, kuma babu wanda ke da niyyar yi mata magana kan ta tsaya.

ya sashi cewa ” idan kika fita nabeelah ban yafe miki ba, Allah ya isa, ci gaba tayi da tafiyar ta,batare data juyo ba yaran ma suka bayanta suna kuka. 
murmushi irin na manya Big Dady yayi sannan ya kira sunanta NABEELAH!,  cak ta tsaya ba tare data jiyo ba, yace ” zo nan, diyata  a hankali ta jiyo ahankali tazo gabansa ta durk’usa, sai kuma ta fashe da kuka, da rarrafe Deeni ya rarrafo zuwa inda take yazo gabanta yace ” please  my heart kice kin fasa bari na, yayi maganar kamar wani zararre, Big Dady ne ya daka masa tsawa yace “deeni ka shiga hankalinka, sannan ya juya ya dauki waya yakira Ammar yace ” kasanar da Family gabadaya cewar akwai meeting, nan da 1hr maza da mata har wad’anda ke gidan miji ka kira su ka sanar dasu, Big Dady ya kalli Nablah yace ” jeki d’auko hijab d’inki, ba musu ta shiga d’aki ta kintsa kanta sosai sannan ta fito, Big Dady ya kalli su Ummi da Deeni yace ” nan da 1hrs ku hallara,r ya kalli Nablah yace ” muje, da sauri Deeni ya mik’e yace ” nima zan bita, wani wulak’antaccen kallon Big Dady ya watsa mai wanda yasa shi ya shiga hankalinsa dole, Anan, Haidar, Junior gaba d’aya suka rik’e Nablah suka saki kuka mai ban tausayi, Big Dady ya kalli Ummi yace ” jebi yara abin tausayi dan Allah, wallahi hakkin yaran nan kad’ai ya isheki, kodan gashi nan ma kin fara gani, Big Dady ya rik’e hannun Anan, ya kalli Ammar yace ” rik’e Babanka, Ammar yayi murmushi ya d’auki Haidar, da junior big dady ya d’auki Anan, suka tafi gidan Big Dady. Har nablah. 
+

Meeting room

A babban falon Big Dady kowa ya hallara manya da yara, maza da mata, ciki kuwa harda FK, gefe ga Deeni sai Zeenat dake ta faman kuka, kusa da Ummi, Nablah ma har lokacin kukan take, yaranta na nanik’e da ita, Big Dady yayi gyaran murya, ya kalli Fk yace ” bud’e mana taro da addu’a, bayan an kammala ne Big Dady ya kalli Deeni yace ” maimaita abinda ya faru, ba tare da tsoro ko wani fargaba ba Deeni yashiga  zayyana duk abinda ya faru tun daga farko har k’arshe, kmr yadda ya sanawar da big dady kowa a wajen ya hau kallon Ummi yana mamaki, had’i da yin sallallami, gyaran murya Big Dady ya kuma yi sannan ya kalli Ummi yace “

Yanzu ke fisabilillahi kinyiwa yarinyar nan Nablah adalci, idan ‘yarki aka yiwa haka ya zaki ji, wanne irin mataki zaki d’auki, ki duba yadda kika tauyewa yaran nan hakki akan farin cikin ki keda ‘yarki, a ganinki kinyi dai-dai, ke yanzu ko tausayinsu baki ji bA. 

, baki kunyar mahaliccinki, haba fadeela gaskiya baki kyauta ba, shiyasa Allah ya nuna miki baki isa komai ba, ya fifita yarinyar a zuciyar Deeni fiyye da taki ‘yar, mai gatan, shiyasa Allah ya nuna miki ikonsa yasawa Deeni matsananciyar soyayyar Nablah, ta yadda bazai iya daurewa ko yi miki biyayya ba, a gabanki, akan idonki ya durk’usa a gaban ta yana kuka akan ta so shi, wannan kad’ai ya isheki izzina, da kuma darasi ga masu halin san kai irin naki, ki dubi yaran nan ya nuna su Haidar yace ” idan suka girma suka ji abinda kikayi musu, da mahaifiyarsu kina ganin zasu k’aunace ki, ke ko tausayinsu baki ji, baki tausayin yarinyar nan k’arama yarinya kmr wannan dan nasan batafi 18yrs ba, kinga yadda Ubangiji ya nuna buyawarsa akanta ya hana ‘yarta ki haihuwa da Deenin.

“Ni nasan bazaki tab’a yarda ayiwa ‘yarki haka ba, idan ko akayi mata sai inda k’arfin ki ya k’are, gaskiya kina da san kanki, baki da adalci, wallahi ki nutsu ki koma ga Allah, ki nami yafiyar yaran nan, kinga dai yadda Allah ya saukar da aya a kanki wannan kad’ai ya isa ki gane kuskuren ki. 

1

Kinga dai yadda ke da kanki kika had’a muku GADAR ZARE, keda ‘yar taki, kika yiwa ‘yarki kishiya abinda tafi tsana arayuwarta, kuma bata tashi sani ba sai da kishiyar ta zama dole k’anwar nak’i, dan ko ba’a zauna da ita ba dole a zauna da ‘ya’yanta tunda ga tanan nan ma wani tsohon cikin, kinga keda kanki kinyi mata illar da harta mutu bazata manta ba, wannan kad’ai ya isa kusan komai na Allah ne,  shike yin abinda yaso akan wanda yaso, a kuma inda yaso, dan haka mutane mudaina gaggawa a rayuwar mu.

Sosai Big Dady yayi musu fad’a gaba d’ayansu ya had’a dayi musu nasiha mai ratsa jiki, sannan ya sallami kowa, duk wainar nan nan da ake toyawa inna bata sani ba, dan idan ta sani ba zaman lafiya shiyasa Big daddy ya hana a fad’a mata,  yace ” Deeni ya tsaya,Byn kowa ya watse. parloun’n ya dauki shr na tsawon wani lokaci big dady ya dinga kallon deeni yana mamakin reaction dinsa na dazu daya dinga Yi akan yarinyar. 

“ahankali Big dady ya cigaba da kallonsa tmkr wani sabon Halitta agabansa.
sakamakon  yadda cikin kankanin lokaci gabadaya kamaninsa suka sauya ya dawo wani irin mutun Abin tausayi. 
Ahankali big dady yake  kalleshi tare da nazarinsa Kana ya numfasa muryarsa a matukar raunane irin ta Manya ya kira sunan shi….. deeni ya dago rikitattun idanunshi da suka gama canza kala tsabar rudani da tashin hankalin da yake ciki .
ya zubawa big dady su yana kallonsa batare da yace uffan ba.
” sai ma hadiye abinda ya tsaya masa amakoshi yayi yana maida hankalinsa sosai gurin sauraron abinda  big dady zai ce .

Big dady ya sake fuskantarshi da kyau sannan yace nasuruldeeni na fuskacin kana matsanancin son yarinyar nan nabeelah kana mata mahaukacin so fiyye da tunanin me tunani wannan kalubali ne agareka sannan km babban yakine akanka daka San yadda zaka shawo hankalin yarinyar nan cikin sauki.

sbd daganin yarinyar tana da kafiya da taurin Kai da taurin zuciya sai kayi mugu mugun aiki da km yaki sannan Zaka samu ka shawo kanta da hankalinta.
” musamma sbd abinda akayiwa yarinyar wanda kowace Mace akayiwa hk zata iya yin hauka fiyye danata .
na Lura sosai kafi son yarinyar  akan zeenat duba da yadda ka dinga yi wasu abubuwa agabanmu gabadaya idanunka sun Rufe deeni akanta. 
so nidai abinda zance anan bai wuce nace kayiwa Allah kayi aldalci atsakaninsu deeni.

kayi adalci atsakanin matanka kada ka taba fifita daya akan daya karka sake kabari daya tagane kafin son daya akanta .

duk wacce Kake so axuciyarka kabarwa ranka yazama sirrin zuciyarka .
daman dole ne sai kasamu wacce zakaji kafi so atsakanin matanka .
Amman karkar kuskura ka bayyanawa kowace daga cikinsu. 
kabarwa zuciyarka kayi adalci kaji tsoron Allah karike matanka amana dan karkaga nabeelah ce me haihuwa uwar ya’yanka kace zaka wulakanta zeenat sannan kada kaga zeenat yar’uwarka ce ka biyewa mahaifiyarka.
ku taru  ku wulakanta nabeelah..
sosai big dady ya dinga masa Nasiha me ratsa jiki da huda zuciya dasa zuciya nadamar abinda ta aikata. Sannan zance ita yarinyar nan nabeelah kabarta anan tukun kafi asan abin Yi. ya daga kanshi alamun yaji. 
byn big dady yagama dashi yace idan ya fita ya turo masa zeenat. Jikinsa a matukar sanyaye ya mike tsaye da kyar yana yiwa big dady sallama hade da godiya…

Byn ya fito ya iske zeenat zaune a karamin parlour’n gidan ya zauna kusa Daita sosai yana jin wani irin matsanancin tausayinta yayinda sound din kukanta ke taba zuciyarsa.   “gabadaya nadamar abinda ya aikata agabanta yakeyi.

hakika bata cancanci hk daga gareshi ba kodan duba da yadda take  matukar kaunarshi fiyye da komai arayuwata . cikin sayin jiki ya kamo tafin hannuta cikin nashi yasoma murzawa ahankali ahankali kafin yace wani Abu.
Da sauri ta zame hannuta cikin nashi tare da juyar da kanta alamun bata son ganinsa .
yaja numfashi da karfi ya fetsar yana tsura mata rikitattun idanunshi yana kallonta cike da tausayawa. 
sannan ya bude bakinsa da kyar ya kira sunanta complete Name dinta muzeenat, …………..
zeenat taki juyowa ta kalli inda yake ballanta yasa rai da samun amasart.
sai ma jijjiga kafar daya da take tana cizan lips dinta. 
Miryarsa a raunane ya sake kiran sunanta My Zeenat am sorry…. am very  sorry  for  what I did…nasan ban kyauta miki ba .
sannan baki cancanci hk agurina  ba.
  ” tabbas naso na kuntatawa rayuwarki alokacin da kikayita zubar min da cikina arariya ….Amman bata wannan hanyar ba. 
Ko auren sirrin dana Yi da nablah ba’a son Raina nayi ba. 
Umarnin first love nabi wanda alokacin gabadaya daurewar farincikinki take nema agidana .amman kiyi please ki yafemin bisa biyyewa first love danayi gurin boye miki..
duk wannan bayanani dayake mata bata juyo ta kalleshi ba har yagaji ya Mike da niyar wucewa  tare da Sanar mata da sakon Big dady.zeenat wacce taci kuka tkmr zata bar duniya idanun nan nata suka sake kankancewa sukayi sumtuma sumtuma sukayi jawur dasu . tashiga dakin  da big dady yake zaune zaman jiranta.
wasu hawayen bakin ciki da takaicin abinda mijinta yayi dazu yashiga silalo  mata bisa kuncinta.
ahankalin tasamu gurin nesa kadan ta zauna tana fuskantar big dady sosai .
wani irin tausayinta gyaraye da tsantsar kaunarta ke  ratsashi. hakika yasan anyi mata laifi me girma…Wanda ta cancanci atausayawa rayuwarta da komanta. an tauye mata hakinta… anci zarafinta da mutuncinta.
an hukuntata da hukunci me radadi da ciwo da wuyar mantawa.
ya  ja numfashi da kyar ya fetsar  idanunshi kyam akanta yana nazarinta sannan ahankali yasoma da  yimata nasiha akan yarda da kaddara …..
muzeenat kiyi hakuri da yadda kika tsinci kanki. ki yarda da yadda kaddaraki tazo miki.
wannan Abu ba daga umminki bane ba daga nasuruldeeni bane ba daga ita yarinyar bane daga Allah ne .
wannan hukuncin Allah ne ,ya zarta akanki.
” kada kiyi jayayya da ikon Allah.
kada kiyi fushi da abinda mahalinciki Allah ya zarta akanki .
  “sannan rabon yayan nan ya rigada ya rantse muzeenat sai Sun xo duniya.
in ma ba haifesu ta hanyar sunnan aure ba sai sun zo duniya ,tunda Allah yarigada ya Kaddara akwai rabon ya’ya atsakain nabeelah da nasuruldeeni sai an haifesu kota hanyar   shegu ne, musamm ma idan kikayi duba da yadda Allah ya nuna ikonsa acikin shekara daya Allah yabashi yaya har uku sannan ga wani cikin wanda Allah Kadai yasan abinda zata haifa.. wasu zafafan hawaye masu ciwo da taba xuciyar ma,aboci tausayi suka shiga gangaro mata a fuska ..
zeenat ta dafe kanta  datake jin yana mata wani irin sara da mugu mugun ciwo. 
cikin wani irin matsanancin kuka tashiga girgiza kanta yayinda aranta ta dinga furta kalmar Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un …yaushe ni muzeenat zan samu sauyin rayuwa me dadi irin na kowace mace agidan aurenta? 
.. Big dady ya numfasa kana yacigaba muzeenat ki natsu ki sanyawa zuciyarki salama akan lamarin nan sbd idan kin matsa dayawa rabo zai iya kasheki, ki mutu kibarsu, su cigaba da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali .
Dan hk ina son kiyi hakuri ki Karbi wannan kaddarar data zo miki da hannu biyu biyu.
  ” ki rungume kaddarki muzeenat km da alamun yarinyar zata biki yadda ya dace .
zata miki biyayya kada ki zubda girmanki a idanunta itama Sosai yayi mata nasiha me ratsa jiki da sanyaya zuciya tunda big dady yasoma mgn bata dago kanta ta dubeshi ba .
Sai kuka datake kawai tana sake nadama abinda ta shuka arayuwarta.
wanda shi yajefa rayuwarta takasance hk.take wasu wurare suka dinga budewa jikinta suna karbar kaddarar tada fada mata. wani irin  tsoron Allah ne ya sake shigarta..

+

Kafin kace me tunin zance ummi yakarade ilahirin estate din .

“masu zaginta nayi masu side dinta nayi kowa da yadda yake fadan albarkacin bakinsa akanta .
wayanda basa side dinta kuwa suka dinga Yi daita suna zaginta. 
Tare da  tsananin mamakin sonkai irin nata da butulci da cin amana da yaudara da haincin irin nata.
Sosai suke  mamakinta . wannan wani irin sonkai ne daita? 
kwata kwata batayi adalci ba.Daga gidan big dady kai tsaye zeenat gidan babanta wasu daga cikin yan’uwaa suka nufa daita.
yayinda nablah ke gidan big dady Dan koda big dady ya gwada Yi mata Zance takoma gidan mijinta kafin asan abinyi. 
kin yarda tayi, ta koma gidan deeni… +

Daren Rana banda kuka babu abinda zeenat keyi wanda daga karshe ta yanke shawarar  kaiwa Allah kukanta.

,ta Mike taje tayo alwala tashiga jero nafilloli tana kuka tana neman sausauci agurin Allah, ya kawo mata sauki cikin lamarinta .
byn ta idar ta Dade zaune hannuta rike da carbi tana lazimi .
kwata kwata takasa runtsawa sakamakon tuno ummi datayi tasan duk inda ummi take tana can cikin tashin hankali da kuncin zuciya .
tasan ummi bazata taba iya runtsawa ba.
Tasan yadda ummi ke matsanacin sonta da kaunarta fiyye da komai aduniyarta .
wasu zafafan hawaye masu ciwo  suka shiga silalomata.
tana nan zaune tana ambaton Sunan Allah  har sanda aka Kira asalatu bata runtsa ba addua Kawai take…

Sosai ummi tashiga tashin hankalin rashin zeenat tashiga uku tarasa abinda ke mata dadi ta rame acikin kwana daya kacal .

abun Duniya duk yabi ya dameta gabadaya yanzu kunyar dangin take ji. 
da gudun shiga tsakaninsu sbd duk magangun da suke fada yana dawo wa kunneta hankalinta yayi mugu mugun tashi tarasa inda zata saka ranta taji dadin arayuwarta.
bata da kowa akasar Nigeria  sama da zeenat da deeni suka gareta. 
idan har zasu iya gujemata  zamanta bashida amfani akasar.

Ahankali ta mike tsaye jikinta kasalance ta shiga tsintiri adakinta na ainihin gidanta. 

Kafin daga baya ta nufi inda ta,ajiye wayarta takira Wanda ke mata biza zuwa kasar haihuwarta.
byn tagama wayar ta dauko yar karamar jakar matafiya tasoma shirya kayanta ciki tana hawaye tana jin wani irin radadi da kewar tilon danta deeni da zeenat aranta .
Tsab tagama shirya komai..
Itama tunda rigimar nan ya faru bata samu ta runtsa ba har zuwa yau din nan .

Washegari tana idar da sallah asuba ta dauki Jakarta da niyar barin kasar gabadaya.

ahankali take saukowa daga matattakalan gidan xuwa parlour’n kasa taji motsen alamun bude kofar cak ta tsaya da tafiyar datake jikinta ya dauki kirrrrrma…abinka ga jikin girma kadan ya rage batayi kasa ba. 
Km har lokacin danunta na kallon kofar shigowa.
tilon danta  deeni taga Yana kokarin sanyo Kai cikin gidan. Ahankali karasa  yashigowa  jikinsa sanye da farar jallabiya fara kal da alamun daga masjid yake.Take wani irin sanyin dadi ya zirayarci ilahirin jikinta da zuciyarta.ta dinga jinta wani Iri wani iri. 
Amman ta kauwar da kanta da abinda take ji tacigaba da saukowa ahankali jikinta naciga da rawa wanda har yar karamar Jakarta hannuta rawa yake.
gaban deeni ya buga da matsanancin karfi ganin umminsa rike da jakar matafiya .
Wanda duk sanda kaganta da ire iren jakunkunan Kasan tafiya zatayi.
har tazo ta gifta ta kusa dashi idanunshi akanta yana kallonta da mamaki a saman fuskarsa.
ganin tana shirin bude kofar yasa  da sauri ya riko jakar hannuta Jikinsa na wani irin rawa ..muryarsa cike da in… Inna… yace u’m…. ummi ina km zaki tafi hk ?
Meyasa ummi zaki mana hk ?
ummi please……. +

ummi kada kiyi hk Dan girman Allah kiyi hakuri ki yafemin ya zare Jakar hannuta ya ajiye agefe daya tare da tsungunawa agabanta gwaiwa biyu biyu ya daura tafin hannusa  duka bisa kafafunta please ummina kiyi min afuwa bisa ga laifin abinda na aikata miki bazan sake ba. 

na tuba ummi nabi Allah da manzonsa na biki. ummi karki kujemu.idan kika gujemu rayuwarmu zata tagyara zamu shiga wani hali dagani har zeenat dinki…… 
ahankali ta zare kafafunta zuciyar na wani irin bugawa jikinta yayi  sanyi. 
Take zuciyarta tashiga shawagin barin tilon danta da diyarta zeenat .. Taku daya tayi zuwa biyu taja ta tsaya hade da juya masa baya tana jin  wani irin matsanacin kunyar  deeni .har zeenat ahalin yanzu kunyar hada ido 
take dasu. 
Batason km hada idanunta danasu.
tarasa ina MA zataje ta saka ranta taji dadi da 
wa zatayi hirar ta rage zugin da zuciyar ke Yi akan abinda ya faru zeenat kadai gareta diya Mace gashi itama tagujeta ta juyawa rayuwarta baya akan  abinda ya faru…
Jikinsa na rawa da rarrafe ya samu ya matso inda take. 
yace  kiyi hkr ummina karki tafi ki barmu bamuda kowa a nan sai ke idan kikabarmu yaya kike son rayuwarmu takasance?
Ummi taja naunauyen ajiyar zuciya da numfashi  ta sauke da kyar.
Kana tayi dauriyar juyowa tana kallonsa  duk  da har lokacin zuciyarta cike take tab da jin kunyarsa  da kunyar abinda yayi mata gaban big dady da gaban  dandazon daginsa sbd common Mace…. Mace ma wace itace da kanta ta tsaya tsayin daka ta aura masa ita ,yana kukan bai sonta….
“muryarta a dake tace Ai wannaN bakomai bane idan na barka deeni.. karka manta yanzu kana da madadina wacce tafi agurinka .
har kake kokarin yimin tawaye akanta you give me double surprise deeni akan Macen da nice na tirsasaka ka aureta ba dan kana sonta ba..
ni… ni deeni ta nuna kirjinta da dan yatsanta Amman babu komai karku damu duniya ce.
sai dai kasani  ayau din nan zanbar muku kasarku da danginku gabadaya na koma tawa kasar .
dama dan wa Nike zaune?
Dan kai da zeenat ne Amman ayau kun nuna min ni din bakowa bace agareku km nasan ko babu ni arayuwarku zaku cigaba da rayuwarku yadda kuke so…. Takarasa fadar hk tana kuku .
deeni ya rude ya gigice hankalinsa yayi mugu mugun tashi ya sake rungumo kafafunta please ummi karki ce hk kice komai mu kice rayuwarmu kece farincikinmu kece jigon komai agurinmu karkiyi mana hk ummi yana mgn yana kuka yana rokonta tayi hakuri tayi masa aikin gafara ko a’lamura zasu daidaita gareshi.

gabadaya jikin ummi yayi tsanyi zuciyarta tayi rauni tausanyi dan  nata ya huda kirjinta. 

take komai ya kwance mata ita kanta bata kaunar abinda zai nisantata dashi shi kadai gareta  sai marainiyar Allah zeenat .
Tana tsananin son deeni Amman soyayyar zeenat dinta daban ce kasancewar kaunar dake tsakaninta da mahaifiyarta .
tsawon lokaci suka dauka ahaka deeni nacigaba da kuka yana bata hakuri.
da kyar yasamu ya shawo kanta hannuta na rawa ta daura bisa kanshi ta shafa sumar kanshi Kana ta zauna ya daura kanshi bisa cinyarta yana kuka yana bata hkr .
yayinda ita km ta cigaba da shafa sumar kanshi muryarta a  matuKar sanyaye tace is OK son kukan ya isa hk komai ya wuce Allah yayi maka albarka Allah sanya albarka arayuwarka data iyalinka gabadaya.
bai samun damar amsa mata ba sbd kukan dayake.
shi kanshi yayi muguwar nadamar abinda yayiwa yayinda ita km ta cigaba da shafa sumar kanshi muryarta a  matuKar sanyaye tace is OK son kukan ya isa hk komai ya wuce Allah yayi maka albarka Allah sanya albarka arayuwarka data iyalinka gabadaya.
bai samun damar amsa mata ba sbd kukan dayake.
shi kanshi yayi muguwar nadamar abinda yayiwa mahaifiyarsa mafi soyuwa azuciyarsa… Ka tashi ka zauna akan kujera  deeni ya tsinci muryar mahaifiyarsa.. 
ya dago kanshi yana dubanta yana girgiza mata Kai first love barni anan .
ya sake gyara  zamansa agabanta suna fuskanta juna.
ummi ta numfasa tana dubansa gabadaya duk ya rame yayi dogon wuya     data tuno dalilin abinda yasakashi dawowa hk tayi saurin runtse idanunta gam tana kukan zuci da blaming din Kanta.
itace silar fadawarsa cikin Matsala yana zaman zamansa da matarsa.. Da kyar ta bude idanunta tace ina zeenat dina take yanzu tana gidanka ne? 
Ya girgiza mata kanshi sannan yace dukansu basa gidana. 
Gabanta ya buga yashiga dukan uku uku bakinta na rawa tace ina zeenat Dina take ? 
Tana gidan  babanta……. ummi tayi dif kirjinta na wani irin lugude wasu sabbin hawaye suka zubo mata tasoma magana cikin harshen indiyanci , akan zeenat ta gujeta ta daina sonta sbd kuskurenta nason ganin rayuwarta ta inganta agidan danta. kuka take sosai tana daura laifin komai akanta. 
deeni na rarrashinta da goge mata hawayen idanunta first love  ki daina kuka yanzu zanje na dauko miki zeenat dinki bake kadai kika tsinci kanki cikin damuwar da tashin hankalin rashinta ba.
ni kaina nayi nadamar ramuwar gyayar da nayi niyyar mata yacigaba da gogewa ummi hawayenta .
ita km sai  girgiza masa Kai take muryata na rawa tace kaje deeni ka… Kawo min zeenat a duk inda take ko zuciyata da ruhina za samu salama. sai da ya sake goge mata hawayen idanunta sannan ya Mike jikinsa a sanyaye ya juya yasoma tafiya hard ya kawo bakin kofa yana daura hannushi kan handle yaji an murda kofar.
ya dan dakata .. ahankali aka bude kofar…. Zeenat yagani tsaye sanye da doguwar riga da hijab lulube har kasa .
ido cikin ido suke kallon junansu kowace da abinda zuciyasa ke sakawa akan dan uwansa. 
ahankali ta raba ta gefenshi ta wuce shi batare da tace masa uffan ba .
ya meida kofar ya Rufe ya biyo bayanta ummi na arba da zeenat ta Mike zumbur jikinta na rawa bakinta na rawa gurin fadar ma..ma… na tana me ware mata hannunta duka alamun tazo gareta zeenat ta fashe da kuka takasara tare da shigewa  jikin ummi.. Ummi ta rungumeta ajikinta tana kuka. 
a she tunani bai zama gaskiya a she zaki kawo kanki gareni byn duk abinda na miki? Gabadaya na ji  kunyarki zeenat .
naji kunya akan yadda fasaha ta dauke min na kulla miki  gadar zare da hannuna akamiki  kishiya batare da saninki ba. …
ummi ki daina kuka bazan iya barinki ba ummi dake kadai nasaba arayuwa bansan dadi uwa ba sai ke ummi. 
ban rayu da mahaifiya ba sake ummina Kin nuna min gata fiyye “dan” cikinki ummi duk inda zanje nayi rayuwa aikin banza ne idan bana tare da ke.. dan bazan iya jurar rashinki ba ummi. ina sonki duk duniya nan banida kmr ki hakika kin raya zumuncin dake tsakaninki da mahaifiyata. 
kin duba byn mahaifiyata domin nasan ko tana Raye da wuya tamin abinda kika min kin nuna min gata kinsa ban Yi kukan maraici ba.. takarasa mgnr tana kuka ummi ta yafito deeni da hannuta yakaraso ya zauna kusa daita tayi saurin goge hawayenta kana ta kamo Tafin hannushi ka bata hkr deeni….Ka Tausayawa rayuwarta har yanzu ina jin xeenat araina tmkr fareeda.. Ita kadai ke mayemin kurbin fareeda arayuwa. 
ita kadai ke dabemin kewar fareeda a duk sanda hkn yataso min …..takarasa mgnr idanunta na fidda wasu ruwan hawaye.. jikin deeni a sanyaye yace first love  tun jiya nake bata hakuri kwana nayi ina kiran wayarki danata Amman akashe .fisrt love nima abin atausayamin ne .ina bukatar tausayawarku ke da zeenat….Nasani… Nasani deeni Amman Kasan mace tafi bukatar tausayawa akan namiji. 
ummi ta hade hannusu  gurin daya ta damke cikin Nata sosai . 
atake zuciyoyinsu ya buga sbd tuno da rana da  suka mallaki junansu amatsayin ma’aurata ranar da ummi tabasu amanar junansu tare da tabbatar musu da su din yan’uwan juna ne  mafi kusanci da juna .
atare suka dago suna kallon juna kowanensu zuciyarsa cike da tausayawa…
muryarsa a raunane yace am very  sorry zeenat.. I Din mean to hot you .
ummi ta saka baki kiyi hkr diyata… Duk nice silar cutuwarki denni bashida laifi komai. Ki daura laifi gareni zeenst nice na miki laifi bashi ba. 
zeenat tashiga girgiza kanta tasa hannuta daya tana gogewa ummi hawaye muryarta raunane tace ummina na yafe miki …nasan duk abinda kikayi kiyi ne sbd ni… Nasan ko diyar da kika haifa acikin ki irin kulawar dazaki bata Kennan .
ummi ki manta da wani abu makamancin wannan ya taba faruwa arayuwarmu wallahi wallahi ummi na yafe komai .
shima yaya na yafe mishi duniya da lahira Amman  ummi akwai wani hanzari ba gudu ba. 
Dan Allah kicewa  yaya ya sawake min aurensa dake kaina tunda ni baya sona baya son farincikina.
bansan wani irin kiyayya yaya yake min ba wanda ya manta kowa da komai ya manta da irin rayuwar da muka gudanar a farkon aurenmu ya tsugunawa wata Mace agabana yana rokon taso shi ummi…. 
Idan har nacigaba da rayuwa aure dashi wlh ban kyautawa kaina ba …
amman dan hakuri na Hakura da komai na dauki kaddarata nima zanje gaba nacigaba da rayuwata….. 
Deeni yayi sororo tare da tsura mata rikitattun idanunshi yana kallonta cike da mamaki abinda tace. 
ummi tayi gyaran murya tace mamana bazan takuraki ba sbd tun farko aurnku ma ban takuraki ba ballananta yanzu Amman da zakiyi hkr ki rungumi kaddararki dana nafi kowa dake cikin duniyar jin dadi.
burina ba wuce naganku kuna rayuwa tare ba . abinda bakusani ba batun yanzu nake son ganinku cikin inuwa daya ba. 
Amman sbd sanin halin deeni danayi yasa naki hadaku tun farko ko lokacin dayazo min da zance aurenki naji matukar dadi Amman ganin ba sonki yake ba alokacin kawai yana son yin auren ne dan na matsa masa yasa naki amincewa .
Amman kikace kinji kin gani zaki iya… 
Ahankali ummi ta meda idanunta kan deeni bazan takurata mata ba idan kaji kana bukatar matarka Kanason cigaba da zama daita.
kasan  yadda zaka Shawo kanta idan km kasan bakada bukatarta arayuwarka sakar min  abata.
domin  abinda wani yagaji dashi yaga yayi masa tsufa shi wani yake so da dauki ganin ya mallaka.
deeni ya runtse idanunshi da sauri sbd jin haushi da takaicin zance ummi.
Ummi na mgn fadar hk ta Mike tsaye tabar gurin ta nufi dakinta tana goge hawaye .
bathroom tashiga ta zauna kawai tarasa abinda ke mata dadi.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

zeenat ma zame hannuta tayi cikin nashi yana kallonta Tabi byn ummi. 

a sikwane Yabi bayanta da wani irin  kallo .tana shiga dakin ummi ta fashe da wani sabon kukan sbd har lokacin tana jin mugun kaunar mijinta.
sonshi acikin jinin jikinta yake .rabuwa dashi babban tashin hankali ne gareta Amman zata dakewa zuciyarta ko zata samawar ruhinta salama sosai take kuka tana tuna rayuwarta acikin dakin datake yanzu. 
da yadda abubuwa suka dinga gudana daya byn daya suna wucewa da yadda ta rayu da matsanancin kaunarsa batare daya Sani ba. 
da yadda ya dinga jiyar daita dadin aure   ta dinga jin dama lokacin zai dawo mata da ta sake sabuwar rayuwar me inganci.
ashe daman zai kara aure arayuwarsa shi yasa lokacin datace yayi mata alkwarin bazai mata kishiya ba yace a’a zeenat bani ne da rayuwata ba. 
ban isa Na tsarawa kaina rayuwa ba. 
Aure nufi ne na Allah idan Allah ya kaddaromin sai nayi.
kedai ki tabbatar da kin tsare min hakina .
babu mamaki idan kika  tsaremin hakkina dake kanki ta yuwu gaba naki kara aure .
duk da babu yadda Allah baya juya lamarinsa.
tuno wannan zance nasa ya sake haukatata ta dinga kuka tana datasani arayuwarta…….
ahankali ta mike tsaye tana safa da marwa  …motsin turo kofar dakin taji anyi tayi saurin goge hawayen dake tsiyayowa daga idanunta batare data juyo ba.
ahankali taji an meda kofar an  rufe  alamun an shigo dakin.
jingina bayansa yayi da jikin kofor tare da rungume dukka hannuwasa akirjinsa.
ya tsurawa  bayanta   idanu kawai yana kallonta yayinda ahankali ya dinga jin wani irin tausayinta yana ratsa kowani shashi na gangar jikinsa hakika bata cancanci wulakaci ko sabanin hk daga gareshi ba a kullun yana yabawa da tarin kaunarsa gareshi. 
cikin wani irin sayin Jiki yakaraso gareta ya rungumeta ajikinsa ta baya yana me juyo daita suna fuskatar junansu. 
atare suka sauke ajiyar zuciya .
ya tallabo fuskarta da hannuwashi yana Kare mata kallo ya bakinsa ya tsotse bakinta muryarsa a matukar raunane yace ki bini mu koma gida zeenat mukarashe rayuwar aurenmu tare.

nifa bazan koma ba domin bazan iya cigaba da rayuwa dakai  ba…… Daga yanzu kasawa ranka mata daya kacal gareka..no… no.. don’t do this to me zeenat . kiyi hakuri please  kishirya yanzu mu wuce tare.

  ta girgiza masa Kai alamun bata komawa gidansa yin duniya yayi daita Amman taki amincewa ta bisa..

hk yagaji ya Hakura yabar gadan.  Kai tsaye gidan big dady ya nufa ya duba yaransa ita kam nablah bai samu damar ganinta ba sbd taki yarda  sukaga juna.

Hk ya koma gida ya shirya zuwa office.

koda ya dawo daga office gidan ummi ya nufa rarrashin duniya yayiwa zeenat amman tace Sam ya barta lokacin data  aureshi bai matsawa rayuwarta ta aureshi ba Dan hk yanzu bata Yin auren ya sallameta kawai ta aure  wani .
kmr ya mutu hk ya dinga ji alokacin datake fada masa hk.. 
a matukar fasace ya fito tmkr zai tashi sama .
ko gidan Big dady bai je  dubo nablah ba. Ya wuce gidansa 
dan yasan haukanta ya zarta na zeenat.
sai dai gabadaya bai da salamar zuciya .
Daren ranar da kyar yasamu bacci barawo ya samu nasarar daukarsa cike da matsanancin damuwa.

washegari zeenat gabadaya akwance take  ta zube tayi wata muguwar Rama sallah kadai ke tadata koda ko abinci ta manta rabon data sakawa cikinta ummi tayi ta matsa akan ta saki ranta taci abinci Amman furrrrrrr taki. 

Gabadaya komai ya cukudewa deeni guri daya takowani bangare babu sauki da sausauci gida da office baida natsuwa tafiya kawai yake Amman zuciyarsa tap take da damuwa da tsantsar tashin hankali da tunani mara misaltuwa.

daga office kai tsaye gidan ummi ya nufa yashigo gidan bakinsa dauke da sallama ummi kadai ya tarar tana zaune ta amsa masa tana kallonsa.
dan  ramar tasa ta yau tafi ta kullun nunawa ahankali ya zauna tare da ajiye jakar system dinshi yace first love mun yini lfy. 
lfy lau son ya aiki .
yayi dan jim sannan yace alhamdullahi kusan minti goma yayi zaune baiji motsin zeenat ba wanda abinda yasani ne matsawar ummi na guri dole ka isketa kusa daita.
jikinsa a sanyaye  ya fito da system dinsa cikin wata karamar bakar jaka yasoma dudubawa yana son karasa tura sakwanni .muryarsa akasalance yace first love ina zeenat?
Ya fadi hk batare da dago ba.
Ta mike tsaye tare da bashi amsa tana sama yanzu ta tashi .
OK turo min ita first love . 
koda ummi tasanar mata da sakonshi bata mutsa ba taxo  a parlour ta sameshi zaune kan daya daga cikin kayatattun kujerun parlour’n ummi na alfarma system dinsa akan center tablet agabanshi yana latse latse jikinsa sanye cikin wani farin yadin volya fari kal me shegen kyau hasken yadin da kyawunsa, su suka tona asirin tsadarta kashim turaren nan nasa na yau da kullun yana nan. yacika gurin batare daya dago ya dubeta ba ya nuna mata kujerar zama da hannusa cikin harshen turanci yace have a sit.
ba mutsu jikinta a matukar sanyaye ta zauna kusan minti goma bai ce daita komai ba yanata danne dannesa ta dago idanunta tana duban agogon dake manne a  parlour muryarta a sarke cike da matsanacin tsoro tace nifa gsky ina son komawa daki dan ina da abin Yi.
ya dago rikitattun idanunshi ya  dubeta..ya lashin lips dinsa na kasa kana yace Kibani minti biyar local in kammala muhinman aikina. 
Taja numfashi hade da kawar da kanta gefe .

ahankali ta sake kallon agogon minti biyar din tacika tana shirin sake yin mgn taga ya ture system din dake gabansa ya mike ahankali ya zagayo gefen datake zaune kafafunsa babu takalmi ya janyo wata yar karamar akujerar stood dake daf daita ya zauna ya rusuno sosai kusa daita har suna jiyo numfashin junansu. 

Muzeenat…….. ya Kira sunanta cikin laulausar muryarsa .
ta tsuke fuskasta sosai batare data amsa masa ba . 
bai wani damu da yanayin yadda tayi ba yacigaba da mgnrsa. 
muzeenat meyasa kika Xabi rabuwa Dani  ki auri wani?

alhali nasan kina mugu mugun sona?

da sauri ta dago idanunta ta sauke cikin nasa gabanta ya buga da karfi take ta kawar da idanunta tace daba lokacin ban san ciwon kaina ba Amman yanzu gsky bana wani sonka. 

Uhmmmmm ya sauke numfashi tare da yin murmushin yake.
nasan kin fada ne kawai sbd girman laifi da kike tunanin miki Amman in da gaske kin daina sona ki dubi kwayar idanuna ki tabbatar min da ba kya Sona ……
cike da rashin tsoro wanda duk daurace kawai ta aro tasanyawa jikinta ta Kalli cikin idanunshi tace yaya deeni na daina sonka.
bana kau… Yayi saurin katseta ta hanyar daga mata hannu tare da runtse idanunshi gam zuciyarsa na wani irin harbawa da suya muryasa a raunane tamkar zaiyi kuka yace naji na yarda kin daina sona Amman ki duba wasu abubuwa kafin kiyi tunanin barina na farko Ki duba rayuwar  ummi bazata taba jin dadin rabuwarmu dake.
sannan  mutane zasu zagene idan nabarki wasu ma sai Sun tsnemin akanki. 
kiyi hkr ki dawo mukarasa rayuwarmu tare mu ingantata tare gidana bazai Yi hasken da nake bukata ba matsawar ba kya cikinsa .

zaman gidaka din me zanyi yaya?

ni ba da “da” ba  ba samun kulawa daga gareka ba.
Ince ana hakurin zaman auren ne idan har ya’ya sunshiga tsakani.
, to ni banida ko daya atare da Kai gara kawai kowa ya Hakura .
na Kara gaba ko nima zan samu farincikin dana rasa agurinka takarasa fadar hk tana meda kukan dayaso kufce mata.

Zeenat zaki haihuwa Dani Jikina nabani zaki haihu Dani…

Zan haihuwa man nima na San da hk Amman bada Kai ba. 

yanzu kinfi son kije ki aure wani ki haihu dashi bani ba..

Kina son kibarni kiyi rayuwa da wani na alhalin ina Raye?

OK kai kai ka iya aurenka a boye har da haihuwa ina Raye.

OK a she fa  nice bazan iya yin hk ba  Ko?

tabbas bazan iya aikata hkn ba alhalin da aurenka a  kaina .

Amman ai zan iya rabuwa da Kai matsawar bana sonka?

ya sake runtse idanunshi gam sbd radadin furucinta dan ya tsani jin kalmar bata sonshi daga bakinta .

sai daya furzar da iska me gyaraye da zafi zafi kishi sannan yace  dake zan gama rayuwata zeenat kece uwargidana anan Duniya km ina fatan ko alahira ki zama shugaban matana a aljanna .

ina bukatar mucigaba da rayuwa tare ke kadai kika  kasan halina kika San yadda kike bi Dani .
duk wata Mace da zan kasance Daita abayanki take ki rigada kin sha gabanta takowani bangareni ta tabe baki wannan km matsalarkace.
matsalata ni yanzu nabarka nayi nisa dakai nayi maka Nisan da bazaka taba Kamoni ba.
ya kamo tafin hannuta cikin nashi yana murzawa cike tasasawa yace muzeenat dan Allah  ki taimake ni.. wlh bazan iya rabuwa dake ba sbd ina sonki…………… haka zaki tafi ki aure wani ki barni? 
karka soma furtamin wannan kalmar yaya naso ka furta min ita tun ba yau ba  Amman sai tsintarshi nayi abakinka durkushe gaban wata kana rokonta tasoka kana furta mata wannan kalmar dana fi son ji daga gareka ,batare da kayi alakari da ina gurin ba…
kiyi hkr ki dawo dakinki mucigaba da rayuwarmu  Wlh bazan iya barinki ba sbd ina sonki. 
Kabar soyayyarka zeenat tace batayi.
ka kara akan wanda kakewa na..blah wlh na yafe mata Kai  dan wlh yanzu banasonka tuni ka Gama fice min arai  gabadaya ya marairaice mata yana mammtsa tafin hannuta taga yana neman zube mata tun kafin yakarasa kasa tayi saurin tareshi tana juya masa Kai. kibarni zeenat sbd naga durkusawa nablah danayi agabanki shi yafi tsaya miki arai kibari kema namiki ko zuciyarki zata rage radadin datake miki akaina.
Wasu hawaye masu ciwo da radadi suka shiga zubo mata .
Kanta Kawai take girgiza Masa uhmmmmm uhmmmmm  bazan taba lamuncewa da hkn ba yaya…. Bazan lamunci ganinka durkushe agabana ba…….. Ni ni dai kawai aurenka yarigada ya fice min rai yayi wata irin zabura ya Mike tsaye wanda hakan yasa hantar cikinta kadawa.yashiga zariya adakin gumi na tsaftsafo masa ya dumkule hannushi guri daya ya cure sannan ya naushi iska.
  yajuya ahankali jikinsa na wani irin kirrma ya dauki naurarsa me kwalkwaluwa bai sake cewa daita komai ba ya fice daga gidan..

nan ta zube kasa tana rusa wani irin kuka Amman bataji zata km zama dashi matsayin mijinta… Da daddare suna zaune ita da ummi .

ummi ke tmbyarta yadda sukayi da deeni bata boye mata komai ba tasanar Mata  yadda sukayi dashi ummi tace mamana kiyi hakuri ki koma dakinki Allah ummi bazan iya cigaba da zama dashi bane .
Allah ya hada kowa da rabonsa ummi agabaki agabana agaban big dady yaya ya tsugunna gaban karamar yarinya yana kuka tasoshi… Alhalin nida muka dauki sama shekaru  takwas da aure bai taba mafarkin furtamin ba….

niko me zai saka nacigaba da zaman aure dashi yaje can Allah yabasu zaman lfy da matarsa nima Allah yabani nawa mijin ummi ta goge hawayen dasuka zubomata a boye….

Duk wannan gurmin da ake nablah na gidan big dady batasan komai ba .  kwana  biyu nablah takoma gidan deeni wanda da kyar big dady yasamu ya Shawo kanta ta amince ta koma gidan da Zumar taje tashirya ranar lahadi zasuje gidansu gurin mahaifinta har shi. 

Amman tana komawa gidan tana ganinsa ta tada balli ta sake tuburewa  ta haukace masa agida tana kuka tace ko sama da kasa zata hade ko duniya zata nade koda zan rasa raina baxan taba zama agidan nan ba  wallah kaji na rantse sai na barmaka gidanka km na fasa bar maka daya daga cikin ya’yana domin nawa  ne ni kadai.
km da ya’yana zan tafi tunda ban yayesu ba .
ta tubure masa sosai deeni ya riko hannuta. tayi wani irin ihu  hade da fixge hannuta cikin nasa ta kwasa aguje ta nufi hanyar get……… Zeenat dake cikin dakinta wanda zuwan Kennan kwasar abubuwanta na bukata ta fito sbd hayaniyar da tasoma cika gidan .

Deeni Wanda ranshi Yayi mugu mugun baci a matukar harzuke ya bi bayanta abinka ga dogon mutun tattaki yayi cikin sauri zaraf ya damkota xuwa gareshi tun bata karasa zuwa bakin get ba.

tirtirjewa tasoma Yi tana ya saketa Amman yaki sakinta sai daya shigo daita cikin gidan .
xeenat wace takarasa saukowa tabisu da kallo zuciyarta na tsananta bugawa .

ranshi a bace yasoma yaryarfa mata maruka masu rai da lafiya  zuciyarsa na wani irin zafi da tafarfasa ya zaunar daita ta Mike tsaye zumbur tana watsa  masa wani mugun kallo ka mareni an mareki .

ko zaki rama ne?

ahankali zeenat  ta Juya ta tabar gurin ta nufi dakinta .

Dan yanayin yadda tagansu .
Ya taba zuciyarta har yasa ta dinga jin zuciyarta na wani irin suya kirjinta ya dinga bugawa da sauri da sauri ahankali tasoma karanto duk wata adduar datazo bakinta domin samun sausauci dan har lokacin babu abinda ya ragu a zuciyarta a game da kishin mijinta.

Nace zaki ramane ya sake ta dauketa da wani gigitaccen Marin dayasa har “dan” dake cikinta yayi wani irin juyawa da sauri ahaukace take saki wani ihun tana dubansa da mamaki deeni kasake Marina ta fadi hk tana nuna kanta. 

Suna nan  tsaye zeenat ta sauko ta raba ta gefensu ta wuce abinta.

Wlh sai Allah ya saka min .

Bai sanda haushin kalmarta da ganin zeenat ta fice yasake yarfa mata wani Marin ba yana nunata da yatsansa Muryasa a matukar harzuke ya bude bakinsa  ya Kira sunanta nabeelah….

wace  irin halitar mutun ce ke da baki da tausayi ?

wacce irin zuciya gareki da babu imani cikinta ?

wace irin zuciya gareki  da baki yafiya?

kina son ki kasheni ne ….? 

sai ga kwalla yasoma saukowa daga idanunshi da sauri ya juya mata baya yasoma mgn cike da sanyi murya matsayina da mukamina da shekaruna wanda akalla da nasamu haihuwa arayuwata da wuri da yanzu kusan ina da kamarki… 
Amman duk na karyar da matsayina da girmana na durkusa miki gaban mahaifiyata   gaban Matata sbd kawai nasan a miki ba daidai ba arayuwarki .
Amman duk kika kunyarta dasu. 
muryata a hassale tace ai duk kaine kaja ya Ciro hanky acikin aljihun gaban rigarsa ya goge hawayensa ya juyo ahankali idanunsu suka sarke cikin juna kowanesu sai da zuciyarsa ta buga da mugun karfi gaske kawai taji ya rungumeta ajikinshi nabeeah ki taimakeni  a sanda na durkusa miki ban damu da yanayin da kowa yagani ba nablah idan kin cire soyayyar Allah da manxonsa da mahaifiyata kece kike bayanta Dan Allah nablah ki taimakeni zan rike ki amana zan rikeki da kyau ki bani dama nayi miki alkwarin zan zama tmkr bawanki ta fixge jikinta daga nashi ni kabarni please nifa gsky bana jin zan cigaba da rayuwata da kai wani irin duba yake mata yana jin yadda kaunarta ke sake huda masa zuciya da bawa kowani shashi na gangar jikinsa.. Shr yayi kawai yana kallonta kafin daga bisani ya daga waya yakira sule direbansa byn yazo yace Kaita gidansu .
wani duba tayi masa kana tace ka bani ya’yana Dan wlh bazan barsu ba. Ai kinsa inda suke kije ki daukesu. Ka dai je ka dauko min su 
banza yayi mata yayi tmkr bai ji abinda  tace ba yana aika mata da kallon bata isa ba . ganin bashi da niyar bata yaranta yasa ta Mike ta fice abunta. 
Sam bata ji wani tausayinsa ko kadan acikin ranta ba…….. 

shi kuwa tana fita yashiga sintiri acikin parlour’n tsananin damuwa tayi masa yawa yarasa yadda zaiyi duk yadda yazaci zai shawo kan nablah da zeenat . abin yaci tura sai dai baya jin zai iya Hakura dasu.

  hanyar dakinsa ya nufa. Cikin sauri ya kira wani direbansa yasa takalmi da hula ya dibi kudi masu yawa ya zuba cikin aljihun ya fita………..Kai tsaye gidan big dady deeni ya nufa jikinsa har tsuma yake tsabar tashin hankalin daya tsinci kanshi ciki. 
gabadaya komai na duniya ya rigada ya tsaya masa cak , sai km taimakon Allah yake nema da zuba ido yaga ta inda sauki zai zo masa. 
    “murya a marairaice yakewa big dady bayanin abinda ya faru atsakaninsa da nablah byn komawarta .
da halin dayake ciki da zeenat .
” big dady ya numfasa yana sauke ajiyar zuciya sannan yace shikenan Bari na tashi mutafi yanzu gurin mahaifin nata daman naso abari mu hadu da sauran kawun nan ka domin muhada karfi da karfi  muje , sbd rashin kyautatawar da akayiwa mahaifin yarinyar.
Ita kuwa zeenat kabarni daita Nata me sauki ne Inji Cewar Big dady. wanda oready yarigada yagama  mikewa  tsaye suka fito tare da deeni yace su biya su dauki mahaifin fk dana zeenat da ita  ummin karankata ..
Hkn ce kuwa takasance big dady da kanshi ya sanar mata data shirya maza maza daita za’a je gidansu nablah. +

Ummi tace zeenat ma ta taho suje tare motor ummi daban ita da yar gaban goshinta Direbanta adekule Najansu.

yayinda deeni da big dady da yaran duka uku suna cikin mota daya , mahaifin zeenat dana fk cikin mota daya 
sai motocin escort dinsa dake biye dasu agaba da baya .
  Deeni zaune akan kujera me zaman bazan agaban motarsa renge Rober ya dan kara karfin AC motor sbd wani irin gumin dake tsaftsafo masa ta koina ajinkisa.
anan rungume ajikinsa. ciro wayarsa yayi  agaban aljihun gaban rigarsa yashiga dieling number sule .

Kira daya Sule direbansa ya  dauka yana ambaton sunan boss cike da girmamawa .

deeni yace sule kuna daidai ina yanzu?

Bangaren sule kuwa  cewa yayi muna daidai underbrige din oshodi express. 

OK idan kun kai daidai ladipo kasan yadda Zaka Yi kujerani agurin ganinan zuwa yanzu OK boss .
deeni ya katse kiran Tare da ajiye wayar kusa da giyar motor .
gabadaya hankalinsa yayi mugu mugun tashi yarasa yadda zai Yi da rayuwarsa da yadda zai fuskancin mahaifin  nablah da zance dayen aikin da yayiwa diyarsa.. 
Ya juyowa ahankali yana sauke naunaiyen ajiyar zuciya tare da bawa direbansa umarnin ya taka Motar sosai ……
big dady yace dan me zai taka mota sosai kmr ya dibo dabbobi.
sannan ya maida hankalinsa kan direba yace yayi tuki ahankali ..

nablah dake zaune a byn mota taga sule direba yana rage gudun motar  da yake hade da gangarawa gefen titi ya Tsaya yana jujjuya kai alamun motor ta samu  Matsala, ta dan gyara zamanta kana tace lfy baba sule naga ka tsaya? 

Wani abu zan dan duba a motar yabata amsa da hkn .
taja bakinta ta tsuke batare da ta sake cewa dashi komai ba.
dan ita kanta hankalinta a matukar tashe yake da wannan ranar dazatakoma gidansu dauke da wani cikin wata shida da wani abu …

Lokacin da su deeni suka kusan kawowa ladipo oshodi  ya sake kiran sule direbansa yace yashirya gashi nan karasowa .

Suna wuce ladipo oshodi deeni ya sake kira sule yace ya biyosu abaya OK boss ai naga wucewar motocinku yanzu .

nablah tayi shr tarasa gane kan inda zance sule direba ya nufa kawai ta kawar da kanta gefen titi da kawar da zance dan gabadaya burinta bai wuce taganta acikin gidansu km gaban mamanta da babanta da yan’uwanta zaune ba.. Sunkai daidai iyana paja ta gane kmr tare suke da motocin deeni ranta abace ta juya bayanta aiko taga Motar escort dinsa abayanta tsaki taja kawai tare da hada uban tagumi…Cikin minti talatin motatocin su deeni suka shigo unguwarsu nablah yayinda Jama’ar dake zaune akan layin unguwar  kowa ya maida hankalinsa akan hadaddun motacin dake kokarin shigowa cikin geto area din tasu da kokarin son yin parking a akofar gidan  mlm salisu me wanki hula ……. 
Cikin ikon Allah suka ci sa’ar samun mlm salisu me wanki hula akofar agidansa. Wanda yake ta faman kokarin yin alwala ba dan lokacin sallah yayi ba sai dan yin alwala akoda yaushe ya zamemai jiki.. .

Ahankali su deeni da Big Dady tare da sauran jama’a da suka zo tare ke kokarin fitowa daga cikin motor daya byn har suka gama fitowa gabadaya har nablah wace ta dan yi jimmmmmm kafin ta sanyo zara zaran yatsun kafafunta zuwa waje. Kana ta fito da jikinta. 

aiko junior nayin arba daita ya nufi gurin yana murmushi sauran yan’uwansa ma suka marasa baya.
  ” yayinda mlm Salisu wanda ya kammala da alwalarsa dayake ya dago kanshi ahankali da zumar mikewa tsaye idanunshi karaf suka  sauka akan deeni dake tsaye tare da wasu mutane wayanda  bai san ko su waye ba .
Gefe daya km diyarsa ce nablah tsaye jikin mota yake kallonta zagaye da wasu kyawawan yara masu mugu mugun kyau da daukar hankali sak masu tsananin kama da deeni. Idanun mlm salisu kyam akanta yana kallonta a matukar tsoroce domin idan ba gitso idanunshi ke masa ba diyarsa yake kallo tsaye km kmr ciki ne ajikinta……. Ga km yara 
ahankali mlm salisu yake kallon deeni da nablah da sauran mutanen dake tsaye cirko cirko da ya’yan dake jingine jikin nablah suna manne daita Ya sake kai dubansa ga Anan…… take yaji wata irin mummunar muguwar faduwar gaba from no where ………
tayi masa ruf da dubu aka .
Hankalinsa yayi maseefa maseefar tashi .
tunani kawai yake to meye yahaddin nasuruldeeni da nablah guri daya .
Dayaga ta fito daga cikin jerin motocin da suka fito.
shi dai asaninsa da yayi deeni gurinsa yazo ya nemi auren nablah batare daya tafi daita ba .
to ina nablah taje tasamo ciki km har da ya’ya har guda uku…. Wani irin tsoro ne me cike da tsansar frigici da fargaba yayi mugu mugun shigarshi ya dinga jin Wani Abu na taso masa yana hawa kanshi. 
take yashiga addua acikin zuciyarsa hade da Kane abinda yaji yana tasomasa gabadaya mahaifin nablah ya kasa motsi daga inda yake itama nablah wacce sai yanzu hankalinta ya kai ga mahafinta gabanta ya shiga faduwa at the same time zuciyarta tashiga tsinkewa da harbawa.
deeni yayi saurin karasawa inda mlm salisu yake tsaye ya mika masa hannu.
jikin mlm salisu a matukar sanyaye ya bashi hannu suka gaisa sai dai har lokacin idanunshi nakan diyarsa nablah yana kallonta zuciyarsa cike da frigici. 
murya deeni a kasalance yace baba gurinka muka tare da dagina. 
Mlm salisu yayi saurin kawar da tarin damuwarsa .
sannan km take zuciyarsa tashiga Yi masa wasi wasi akan batare suke da nablah da nablah.
da dan hanzarinsa ya shiga cikin gida sannan ya dawo yayi musu iso ciki.

Byn sun shiga gidan aka gaisa zuciyar kowa cike da fargaba ..

mahaifin nablah ya boye tarin fargabansa hade da  nuna matukar  murnarsa da zuwan deeni big dady ya numfasa yace to deeni gamu a gaban mahaifin yarinya sai kayi masa bayani komai game da abinda yakawo mu Dan waka abakin meshi tafi me…? 
Sauran mutane  dake zaune agurin suka amsa da tafi dadi..

Jikin deeni yayi mugu mugun sanyi ya sake sunkuyar da kanshi kasa sosai wanda daman tun sanda yashigo parlour ‘n kanshi sunkuye yake kana muryarsa a sanyaye a raunane yasoma bayani tundaga kan farkon aurensa da zeenat da labarin zubar masa da ciki da zeenat take Yi masa har zuwa kan yadda akayi aurensa da nablah da yadda asiri ya tono kowa a daginsa yasani har zuwa yau din nan dayake bashi labari.Hankalin mahaifin nablah ya tashin kwarai da gaske zuciyarsa ta dugunzuma guri daya ta yunkuro abinka ga me zuciya.. 

ya Mike tsaye jikinsa na tsananta rawa tare da cewa Zance banza zance wofi.
“Zance banza inji mutane banza. 
Oh ! byn kungama cutar min da yar kun mata ciki ga ya’ya har uku ta haifa sannan ga wani ciki.
shine  kuka kwasota kuzo min daita.

to kuzo in muku me?

AI banida wani amfani yanzu ko ina dashi amfanina ya rigada yakare.

mlm Salisu ya meda idanunshi kyam akan deeni tunda da ina da amfani agurinka ko km kasan darajata da yadda kaxo ka aureta agurina kamata yayi ka dauketa ahannuna ba wai kaje ka rike min ita agidanka ba .
kayi mata ciki agidanka ta haihu ka sake dirka mata wani cikin ba.
Sam wannan ba adalci ne bane km wallahi azim nasuru baka min adalci ba yanzu yartawa ce tazama hk kmr a gidan magajiya nasamota ? 
Ranshi a bace ya dinga zazzaga masa tujara iri iri wallahi nasuru kaci amanata.
” Domin bansaka ba ban San asalinka ba na amince maka har nabaka auren diyata.
a fusace yashiga nuna deeni hannushi yana nuna masa kofar fita  ni maza maza ka tashi anan kabar min gidana bana ko son ganinka acikin idanuna na daukeka mutumin arziki mutumin kirki ban tsaya tmbyr ko kai waye ba.
na dauki yarta nabaka wacce ma acikin yayan nawa itace mafi soyuwa araina shine zaka min irin wannan sakayyar? 
Daman da niyyar dakazo auren nablah Kennan dan ta haifa maka ya’ya?
Amman babu komai kaje kawai Allah ya …….. Kafin yakarasa deeni yayi saurin mikewa tsaye ya katse shi ta hanyar cewa dan Allah dan annabi baba karka min Allah ya isa…….nasan matsawar kamin Allah ya isa zata bini…. Sbd nasan nablah yarkace .

STORY CONTINUES BELOW

Dan girman Allah ka taimakeni karka min Allah ya isa kar ka Kai karata gurin mahalicina..

A matukar fusace mahaifin nablah ya furzar da wata iska me zafi me cike da tsansar tashin hankali mara misaltuwa idanuwanshi suka rine suka jawur ya cire hular kanshi tare da goge gumin dake tsaftsafo masa sannan ahankali ya maida idanunshi kan nablah yace Kalli yadda kika maida rayuwarki……abin kwatance kanki kika cuta bani ba duk abinda yasameki ke kika jawowa kanki.. Muna zaman   zaman mu lfy bamu rasa ci ba bamu rasa sha ba bamu rasa gurin kwanciya ba .

duk da talaucina Allah ya rufawa min asirin da zan dubaku . 
km da talaucin nan nawa dakika raina na rufawa sauran yayyeki asiri har suka rayu suka zama abin alfahari agurina har namusu aure Amman ke kika daurawa kanki buri da son kwadayin  duniya wai ke a dole sai kinyi karatu me zarfi to yanzu wa gari ya waya. 
karshe ga kaddarar abinda son karatuna  nan ya fada miki nan..

GA kaddararki nan kin je a miki wulakaci abanza a wofi an wulakanta rayuwarki .

an dirka miki cikin da baki san ma kowaye ubansu ba.
” kika haifi ya’yan aka kara dirka miki wani cikin… Uhmmmmm kaddaraki Kennan da kika jawa kanki.
Amman  bada kowa zanyi bakiciki ko nayi Kuka ba.
dake zanyi kuka yanzu da badan Allah ya yanke miki wahala ba da yanzu ahaka zakiyi tayin ciki kina haihuwa batare da sanin kanki ba ballantana mu iyayenki da kikabar mu cikin fargaba da tashin hankali  dubi yadda mahaifiyarki ta dawo kalar tausayi kusan damuwarta har ta zarta nawa kullun zanceta akanki nabeelah kowa kika kalla agidan nan bashi da kwanciyar hankali..
Sosai ya dinga zazzzaga mata itama nata tujarar har ya kusan dukanta yayi mata gabadaya ranshi yagama baci idanunshi suka rufe wata irin  jawowa yayi mata da tshon ciki mahaiifin  zeenat ya kwaceta ahannushi. 
shi km deeni gani aika aikan da mahaifin nablah ke shirin masa yasa hankalinsa yayi kololuwar tashi da sauri sauri zuciyarsa ta dinga dokawa tana bugawa da karfi. 
mlm Salisu yace ku miko Mara jin mgn na sabautata na huta me zanyi daita…. Arayuwata.
yarinya  ta dinga janyowa mutane maseefa da ciwon zuciya  duk cikin ya’yana nafi son wannan shegiyar yarinyar da amincewa daita dabata yardata da amanata Amman Kalli abinda tajawo min tajawo kanta tuzarci banda a Gaban shedu da Jamar arziki na daurawa yarinyar nan aure da Jamar arziki na daurawa yarinyar nan aure da me mutane gari zasuce .
kinje an rike min ke har kika haifi yaya uku me kike son nacewa yan’uwa na da danging da abokan arxiki Dan wani ko ka rantse masa ba yarda zaiyi ba cewa zai Yi cikin shege tayi.
deeni yayi saurin runtse idanunshi dan shi kwata kwata ya tsanani jin wannan kalmar arayuwarsa.
idan kuwa akwai abinda yafi tsana nan duniya tana byn wanna kamal… Wallahi yau sai kin gane Taurin kai bai inda yake kai mutun sai nadama da danasani gara na kasheki na huta, daga ita har cikin dake jikinta….
Deeni fa yaga da gaske mlm salisu so yake yayi masa  hasarar cikinsa .
ga km tarin mugun son dayake WA nablah na sake fizgarsa take yashiga  bawa mlm salisu hkr yana karawa.
zuciyarsa kadan ta rage bata buga ba  
hade da yin wani irin tsalle .
cikin kirjinsa sai luguden tashin hankali da fargaban abinda mlm salisu ke shirin Yi masa yake. 
zuciyarsa ta dinga tafarfasa ranshi yayi maseefar maseefar tashin ya dinga jin jikinshi na wani irin tsuma tsabar tashin hankali yayinda nablah data fixge daga hannun mahaifin zeenat .
tayi byn deeni ta kamkameshi ajikinta tana wani irin kuka me ban tausayi tana kuka tana furta dan Allah ka taimakeni wallahi babanmu nada zuciya zai iya kasheni tunda yace zai kasheni zai iya kasheni ya huta.. Nasan halinsa zai iya kasheni tana kuka tana sake kamkame deeni ajikinta wannan ririkewar datayi masa ya sake jefa zuciyarsa cikin rudani da mawuyacin damuwa shi kansa afrigice yake da ganin yanayin mahaifin nata.
wanda tunda yake zuwa gurinsa bai taba ganin wannan sifar atare dashi ba .
Ahankali tausayinta da wutar sonta ke sake shigarsa da ingizashi .yayinda zuciyarsa ke cigaba da bugawa da karfi… Sbd yadda take gogar jikinsa da nata jikin…

Ahankali big dady ya mike yana duban ummi da wani irin yanayi yayinda deeni ke ta faman aikine bawa mahaifin nablah hakuri shi km yana furta sai ya kasheta.

da bata bijirewa maganarta ba .
da bata kai kanta gidanka har kaganta kaxo yin *AUREN SIRRI* daita ba… Zuciyar mahaifin nablah fa ya dugunzuma ya dinga kokarin ture deeni ya fixgo nablah ..
a zafaffe ya dinga cewa nasuru ka miko yarinyar nan idan ba hk ba wlh har kai zan hada  inyaso duk abinda za’a Yi ayi.. 
Big dady daya mike da kyar yace mlm salisu ka dubi girman Allah kadakata ka zauna miyi mgn.. 
Wannan mgnr da big dady yayi ita ta dakatar dashi daga abinda yake shirin aikatawa ko babu komai girman Allah da mutumin ya hadashi dashi da km ganin Girmansa wanda akalla  shekaru zai kusan daya da kwatan nashi.. Shiyasa hankalinsa ya Dan dawo jikinsa tare da kokarin son sanyawa jikinsa natsuwa daga  tsumar datake ba kaukautawa.. 
Sannan ahankali ya nemi guri ya zauna zuciyarsa na zafi da radadi yana huci zufa na sake karyo masa ta koina ajikinsa mahaifiyar nablah na kuka nuratu na kuka hatta yaran kuka suke ganin za’a dukar musu uwa .

Cikin sanyi murya big dady yace kayi hakuri mlm salisu ka yarda da kaddara datazo maka. 

ka dubi girman Allah da cikin dake jikinta da km wayan nan ya’ya dake kuka kayi hakuri ka godewa Allah da wannan Abu daya faru da ya’yan data haifa da cikin jikinta ba’a titi ne tasamoshi ba. 
aure tayi .
Aure km na Sunnan ma’aiki wanda kaine da hannuka ka daura shi.. Duk abinda Allah yakaddara bawa sai ya faru ..
km duk abinda Allah ya kaddara maka ka amsheshi da hannu biyu biyu.. Shine cikar imanin mutun. 
Ka sake godewa Allah da nablah ba cikin shege tayi ba wanda hakan shine abu mafi muni gareka damu gabadaya..

Da Allah bai Yi hikimarsa  ta zartar da aure tsakanin nasuru da nabeelah ba dafa tabbass sai an haifi yaran nan duka atiti wanda zuciyoyinmu bazai taba lamunta wannnan bakar maseefar ba .

amman  alhamdullahi tunda abin nan ya faru nake godewa Allah da ya’yan nan ya’yan sunan ne.
ba  shegu bane .

idan ya’yan gaba da fateeha ne idan km cikin shege tayi me zakayi?yaza’ayi dole dai hakurin nan zakayi har gara yanzu ma kana da hujjar Kare kanka da bakin mgn acikin jama’a. 

Kai kmr ba babba ba ina hankalinka da tunaninsa suka je ai idan rai ya baci hankali ke nemoshi ka tuna akwai yarda da kaddara acikin cika cikan muslinci mai Kyau ko mara Kyau.
soaai big dady shima ya dinga bashi baki har zuciyarsa ta dunga kasa tana lafawa da yin sanyi ahankali big dady ya dinga masa nasiha zuciyarsa tayi sanyi sosai Amman duk da wannan nasihar da big dady yayi masa bai hanashi mikewa tsaye yace naji km nagode sai dai bazan taba karbarta ba takoma can inda tafaro rayuwarta tayi cikin har ta haihuwa batare da sani ba. 
Ba munyi alkwari dake ba akan wata uku zakayi  ki dawo gareni ba ? 
Nablah ta girgiza masa kanta…mlm salisu yacigaba Kana ganin yarinyar nan sbd auren dana mata bada saninta ba yasa lokacin data rokeni akan nabata wata uku zata je gurin aikinta ta dawo nabata bisa ga kyautatawa Amman shine  tayi zamanta sai data haihu ta dawo min da wani cikin dayake makira ce ita.. 
Km tasan abinda tana son shuka.
nabeelah shi kanshi mijin daya zagayo gurina aureki km ya dinga zagayawa yana miki ciki kina haihuwa dame zai daukeni ?
tunani ma zai inda ace bashi ne yayi miki cikin ba hk zan km daukarki  da ciki na bashi .
nabeelah kin cuci kanki kin zubarwa da kanki da mutunci da kima ki bari azo gurin mahafinki aureki akai ki gidan mijinki kmr yadda akewa kowa ce budurwa me mutuncin da kimarki da daraja Amman kika cuci kanki .
sbd da baki bijirewa mgnta ba, kin zauna lokacin dana ce miki karki sake kije koina da bai ganki ya zagoye ya aureki agurina da wata manufa ba. 
nablah na wani irin kuka ta rarrafo zuwa gurin mahaifinta .
Tana kuka  mlm salisu yace wacce irin ya Mace ce me mutunci da daraja da kamun kai zata aikata irin abinda kika Yi domin cikar burinta ?
Tana kuka tana girgiza masa Kai alumun babu kana muryarta cike da kuka tace wlh baba bansan komai ba …ban San komai ba akan cikin jikina da ya’yan dana haifa ni kaina wayar kaina nake nagani dashi dan Allah babana kayi hkr ka yafe min bazan sake kinji mgnrka ba duk abinda kace nayi shi zanyi  bazan sake sabawa umarninka ba.. tana kuka tana rokonsa furzar da iska yayi yana girgiza Kai .

zeenat  tayi shr tayi zugun azaune tana kallon ikon Allah yau ga talaka me zuciya tagani .

Ashe daman talauci bayasa mutun ya kaskanta da wulakanta yazamo Mara galihu?

A she daman talauci bayasa mutun ya

tozarta kanshi?

A she daman talauci bayasa mutun ya daydayta yazamo abin tausayi ?

A she talauci bayasa mutun yazama kasasshe har zuciyarsa ta mutu. 

Tasashi jin bazai iya kwatarwa kansa yancinsa ba ?

A she talauci bayasa mutun yazama me matacciyar zuciya km Mara zuciyar kanshi.

Yau ga deeni me tarin arziki tsohon retaya soldier me tarin camfanoni da tarin dukiyar da shi kanshi bai san adadinsu ba .

tsaye GAban  wani wulakantaccin talaka me wakin hula  yana masa fada da maseefa har da rantsuwa..
Yau ga big dady shugaban   plant nuwaun rows family estate shugaban dagin gabadaya na nesa dana kusa ya zauna  a gidan talakan dako inda me gadinsa ke rayuwa yafishi daraja Amman ya zauna yana masa tujara yana rokonsa dan Girman Allah yayi hakuri ajiyar zuciya taja da karfi zuciyarta ta sake yin ladab akan rayuwar duniya sai lokacin km tasan lallai ba komai kudi ke wa mutun arayuwa ba.. 
Hk kazalika  ba komai kudi ke sai maka ba lallai akwai talakan dayafi me arziki  zuciya da tunani .. Atunaninta yadda motocinsu suka shigo unguwar da yadda arxiki ya nuna ajikinsu yaci ace ko tarin kirki mahaifinta bazai ba akan mgnr da suka zo masa daita Amman sai gashi ya dage iya karfinsa da gaskiyarsa yana surfa musu tujara..
Hk ma ummi tunanin datake Kennan Ashe tagudu bata tsira bane datace a auri yar talaka Mara gata da galihu kaskantacciya. Ashe baban nablah ba kaskantacce bane Mara galihun datake tunani mutun ne sak me zuciya ba wanda za’a iya cin galaba akanshi bane domin yadda take kallonsa a irin wannan zuciyar tashi ko shara’a zai iya Yi dasu duk kudinsu.
lallai yau tagamu dagamonta.
aranta ta dinga jin  idan baban nablah me arziki ne da basan me za Yi ba. tana cikin wannan tunanin nata na wuncin gadi mahaifin nablah ya gyara tsayuwarsa sosai yace yanzu sai ki Mike ki bisu ku koma inda kuka fito tare .
da son kokarin barin gurin mahaifin zeenat yayi saurin tararsa ta hanyar shan gabansa yace Dan Allah kayiwa iyayenka ka sauraremu. Mahaifin nablah yace ku daina hadani da Allah da iyayena akan cutar da’aka min kana ganin abinda nasuru danku yayi min kana ganin irin yaudara da cin amanar da nasuru danku yayi min wasu irin iyaye za,a yiwa irin hk a wanna duniyar da muke cike su lamunta ?
.Da kyar da Allah da big dady aka samu aka shawo kanshi har yazo ya km zama .
itama  ummi jikinta a sanyaye tashiga bashi hakuri tare da ce masa wlh duk wannan laifina ne sannan kuskurena ne ba laifin deeni da nablah bane .
asalima nabah batasan komai ba kmr yadda tagaya maka domin kuwa batasan deeni na kwamciyar aure daita ba sbd magani yake mata amfani dashi kafin komai ya wakana a tsakaninsu sosai ummi ta dinga vashi hkr akan Abunda daya faru.
sannan km tace yayi hkr ya yafewa nablah batada laifi komai idan ma akwai me laifi to itace babbar me laifi domin itace silar komai.
hatta zeenat ma da jikinta yagama yin sanyi da lamarin sai data saka bakinta gurin bawa mahaifin nanlah hkr Takara yarda da sanin Duniya da abinda ke cikinta ba komai bane ta dinga tunanin matsayi na big dady da deeni da sauran mutane dake zaune agurin Amman gabadaye kowa hkr yake bawa mahaifin nablah jikinta yayi mugu mugun sanyi ta bude baki tace Dan girman Allah baba kayi hkr ka yafemana gabadayanmu dukkaninmu masu laifi ne km masu kuskurene ko agurin Allah Amman kayafe mana Dan Allah.

Deeni ma ya matso sosai yace baba munayiwa Allah laifi ubangijin daya halicemu yabamu ci da sha yabamu lfy sannan km yabarmu da rayukanmu km muyi masa laifi km rokeshi yafiya ya yafemuna sosai deeni ya dinga bawa sirinkin nasa me kafiya da daurin zuciya hakuri yayinda nablah dake durkushe tana kuka .

ta rike kafafuwan mahaifinta tana fadar babana ka yafemin sau daya tak nasan nataba Saba umarninka aduk tsawon rayuwata Amman Kalli yadda rayuwata ta dawo  baba?
idan ka cigaba da fushi Dani bansan yadda rayuwata zata dawo ba. ta dinga risgar kuka tana rokonsa yafiya gabadaya jikin mlm salisu ya sake yin sanyi sosai .
nuratu da mama mahsifiyar nablah suma kuka suke suna nabashi hkr muryasa a raunane ya dubi gabadaya mutane gurin yace shikenan na Hakura na yafe mata….
take hankalin kowa dake gurin ya kwanta.
take Kuma  mlm Salisu ya bugawa Manyan ya’yansa waya da wasu daga cikin danginsa na nan kusa waya sannan yakira waliyan da suka daurawa nablah aure.
duk akazo aka hadu da dattawan unguwa har yayyenta da kannanta da aunty Salma .

Amman mlm salisu bai fito ya gaya masu gaskiyar lamarin ba sai yayi musu karyar cewa tun sanda aka daura auren.

deeni yazo daga baya ya dauki matarsa Amman sbd wani dalili yasa bai fitO ya sanar wa kowa ba sai yau din nan gashi nan har sun haihuwa ga MA wani cikin nan ajikinta ga danginsa nan….

To byn yan unguwa Sun fita .

sai yagawa daginsa da ya’yansa gskyr ainihin abinda ya faru nan dai aka sake neman yafiyar juna aka yafewa juna sosai .

byn komai ya natsa mahaifiyar nablah tace dan Allah abar mata nablah zuwa wani lokaci har ta haifi  cikinn jikinta zuwa lokacin hankalinta zai kara kwanciya.

da kyar deeni ya yarda ya amince da barin nablah agidan Amman banda yaransa .

bai samu damar kebewa da nablah ba Suka koma gida zuciyar kowane cike da farinciki Amman banda zeenat wace duk da abinda ta dinga Yi karfin hali kawai take Tana addur samun saukin abinda ke tasomata akan mijinta……….

Sannan ta wani bangaren km zuciyar cike take da jimami da tsantsar tausayin mijinta ta koma gida.Ko kadan xuciyarta ta kasa samun sukuni tunanin shi kawai take km tana matukar tausaya masa sbd ganin irin soyayyar da yakewa nablah acikin kwayar idanunshi..
Abun tausayi ita data taso marainiya ta rayu da tarin kaunarsa cikin zuciyarsa ita tafi cancanta yaso fiyye da komai baki kadai bazai iya furta adadin kaunarsa gareta ba hk xuciya bazata taba misalta yadda take jinsa cikin jini da jikinta na. 
ita tasan da tarin soyayyarsa zata mutu Amman ba komai zata tsaya daidai matsayinta da jajircewa akan rayuwarta wasu hawaye ne masu dumi suka sauka akan kyakyawar fuskasta.

Jin motsin shigowar ummi da muryar anan yasa tai Yi saurin goge hawayen fuskasta tashige bathroom wanka tayi hade da dauro alwala gabadaya ta fito tana goge gashin kanta da gudu anan tazo ta rungumeta tana mata mgn cikin gwarancin mgnrsu ta yara aunty ina kika Shiga tun dazu?

wanka nakeyi my ummi Bari na shirya sai muje muci abincin ko .

zaunar daita tayi kafin ta fara shirinta tasoma shafa mai a lallausar fatar jikinta kafin ta shafa powder ta km gyara gashin kanta tasa ribon ta kamasa atsakiyar kanta ta feshe ilahirin jikinta da sanyaya turare me dadin kamshi kana ta dauko doguwar riga meflay har kasa anan  na zaune tana kallonta.
suna hada IDo zeenat ta sakar mata murmushi ta cikin mirrorw tana me juyowa ahankali hannuta rike da kwalbar turaren tace ya’akayi ummina anan tayi murmushi siraren hakoranta wayanda suka fara fitowa suka bayyana. zeenat ta gyara mata jikinta da kanta itama tare fesheta da turare sannan ta dauke ta sabata akafa suka nufi parlour’n ummi Kai ta janyo haidar da junior  zuwa  dining area   tasoma da hadawa yaran tea tana basu daya byn daya ummi dake tsaye tana kallonsu ta lura tunda suka dawo daga gidansu nablah yanayinta ya sake sauyawa zuciyarya tayi rauni, da alamun zeenat dinta ta soma canzawa koma tace ta canza gabadaya sai faman jan yaran take jikinta ummi takaraso ahankali xuwa inda take zaune .
ta zauna kusa daita tana dubanta sosai ita da yaran gabadaya tausayinta yakamata ta dinga addur Allah daidaita tsakaninta deeni yasa takoma dakinta tasamu nata rabon ya’ya muryar ummi a raunane tace manana yakamata ace kiyawa kanki fada Ki koma gidan mijinki kizama tsohuwar gidan sai dai akwai Abu daya da nake son ki fahinta   a yanzu .
ki kiyaye sharin zuciya sannan ki rage wannan sakarcin naki ki tsaya ki kula da rayuwar mijinki fiyye da yadda kike Yi abaya .
zeenat ta hadiye abinda taji ya tsaya mata arai  tasoma cin abinci batare datacewa ummi komai ba Har tagama cin abinci fada da nasiha ummi ke mata byn tagama  ta mike tsaye tana shirin barin gurin ummi tace mamana bakice komai ba game da komawarki dakinki  ?

Muryar a matukar sanyaye tace ummi sai nayi tunani tukun bazan koma inda baa san mutuncina da kimata ba. Sannan ta saba anan akafadarta suka Koma kan kujeru suna kallo…..

Daren ranar zuciyar deeni fessss yayi bacci sai dai cike da tunanin matansa yayinda ya dinga ganin kima da mutuncin abinda zeenat tayi masa agaban mahaifin nablah tana kulawarta gareshi duk da yasan zuciyarta cike da jin haushinsa. Yasan irin maccen datakasance agurinsa ba kmr kowace Mace bace Tana sonshi tana sadaukar da farincikinta gareshi sosai ya dinga tunaninta yana bata matsayi me girma acikin tsokar dake makale da zuciyarsa.

Washegari da kuzari ya tashi byn yayi wanka  cikin shirinsa na zuwa office ya fito ya nufi gidan ummi escont dinsa na biye dashi abaya .

agidan ummi yayi breakfast Haidar da junior zagaye dashi suna zuba masa surutu tubda bai ga anan ba ya tabbatar tana gurin zeenat dan tun jiya ya lura da yadda take makale daita. 
har yagama break bai ga saukowar zeenat ba Dan hk yana kammalawa bai tsaya tmbyr ummi ba ya nufi dakinta kai tsaye ahankali ya tura kofar yashiga cak ya tsaya yana Kare musu kallo gabanshi na wani irin faduwa sannan yana jin wani bakon alamarin atare dashi dan ganin Anan rungume ajikin zeenat tana faman Yi mata murmush da alamun biyewa Shirman yarinyar take .yayinda jikinta sanye da doguwar rigar bacci me shara shara shara wanda bai boye komai na jikinta ba take ya dinga reaction dinsa na sauyawa duk kwanakin nan amatse yake Amman tashin hankalin dayake ciki ya girmame bukatarsa. 
ko kadan zeenat bata wani damu da tsayuwarsa ba agurin duk da taga shigowarsa km tun lokacin daya shigo hankalinta ke kansa kirjinta na wani irin bugawa Amman tasharesa tacigaba da biyewa Anan kawai.
ahankali yacigaba da kallonta yana takowa zuwa inda suke zuciyarsa cike da tsantsar soyayyarta gareshi  .
barin yadda yazo yaganta rungume da anan hkn bakaramin faranta ranshi yayi ba. 
yasan ta nuna masa tsantsar kauna da tausayi hade da sadaukarwa soyayya .
stood din dake ajiye agefenta ya janyo ya zauna idanunshi akanta yanaciga da kallonta. 
gabanta na wani irin dokawa ta dago idanunta tana kallonsa anan tayi saurin fadawa jikinsa tana kiran dadyna zan sha shuwet …ya rungumeta ajikinshi yace sweet km mamana da sanyin safiyar tace uhm yace OK let me  true with your aunty tare da sanyata atsakiyarsu .
shi km yana me fuskasta zeenat da wani irin sanyayen kallo gbadaya ya kashe mata jiki da kallonsa har takasa dago idanunta muryarta asanyaye ta bude bakinta tace yaya ina kwana… wani irin kallo ya jiho mata batare da ya amsa mata ba.
ta sake maimaitawa a tunaninta bai ji bane duk da tana da yakinin yaji Amman taji sai idanunshi dataji yana mata yawo a sansar jiki. 
ta dago idanunta asanyaye taga still ita din yake kallo .
idanunshi cike da mamakinta yadda yaga yanzu gabadaya ta canza biheviours dinta akanshi tana hira da kowa da sakewa da kowa acikin gidan shi kadai ta canzawa ..
batason kebewarsu tare sannan bata wani daukin son ganinsa ko nuna damuwarta dashi wanda da ba hk take masa ba.
cikin sanyin jikin nasa ya kamo tafin  hannuwanta duka cikin nashi yana murzawa ahankali yana kare mata kallo 
Kana muryas a kasalance ya Kira sunanta..  
zeenat meyasa kike son tarwatsa zuciyar masoyinki? +

Meyasa kike son tarwasa  rayuwarmu….? 

duk ma ba wanna ba na Lura atsakankanin wannan lokacin kin sauya Hali zeenat kin canza kwata kwata bansanki da taurin kai ba ballantana dagon fushi akan abu…. Meyasa kika kasa hakura da laifin dana miki. 
kinki  komawa Gidana alhalin km kince kin yafemin…..? 
Narasa gane kanki da gindinki zeenat  yanzu har takai ta kawo  har suna kin canza min na tashi daga zuciyarki na dawo zuwa yaya…. Wanda rabon danaji hk abakinki tun kafin muyi aure dake sai km cikin wannan hatsaniyar kika dawo da kirana da wanna sunan ……. Sbd kawai Yanzun kin daina sona ko..?

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]