WANI AURE
kyakkyawar yarinyar ce dai ta sake zuwan masa. deeni kuwa dake kwance warwars akan makeken royal bed dinshi ya zuba mata Idanunshi kawai , tundaga kan kwantaccen sumar gashinta kanta yake binta da wani irin mayataccen kallo mai cike da tsantsar sha,awa yayinda zuciyarsa ke wani irin harbawa da sauri da sauri ..ganin yarinyar ta miko masa zara zaran yatsun hannuta masu matukar kyau da daukar hankali ne yasa shi azamar fizgota jikinsa batare da wani bata lokaci ba ya rungumeta tsam tsam ajikinsa tare da cusa kanshi cikin sumar kanta yana shakar dadeden kamshin jikinta “take yarinyar itama ta narke masa ajiki tana taba wasu part na jikinsa cikin wani irin salo a haukace tamkar wani zaki DEENI yasoma romancing din every part of her “cikin zafi zafi ya hade bakinsu waje daya yasoma tsotsa tare da lumshe rikitattun idanu.. …….. sosai yake juya yarinyar yadda ya so batare da wani abu yamasa shamaki ba.
daidai komai yagama faruwa atsakaninsu ne ya farka afrigice zaune kmr jiya yana sauke numfashi sama sama..
tare da karanto addu’ar da duk tazo bakinsa na neman tsari daga sharin shedan ,ganinsa mafarkinsa nasaba da sharin shedan dan gabadaya yarasa dalilin dayasa yatsinci kanshi cikin irin wannan yanayin mai cike daban tsoro da alajabi .. hakika shi bazai ce Ga abinda ke damunsa acikin yan kwanakin nan dayasa yake tsintar kanshi cikin irin wannan birkitaccen yanayin ba . +
Tsawon lokaci ya dauka yana zaune Yayi shr kawai yana tunani.
” yayi yayi ya gane abinda ke damun rayuwarsa Amman Sam yakasa domin duk ta inda ya duba bai gano takamaiman abinda yasa yake irin wannan mafarkin ba ….. ‘ahankali yasa hannushi yajanwo hanky agefen bed dinsa ya goge gumin daya rufeshi . dan duk da AC dake aiki acikin dakin bai hana Gumi tsatsafo masa ta koina ajikinsa ba .. .. sannu ahankali yakai idanunshi kan agogon bangon dake manne a dakin.
karfe biyu yagani daidai ajiyar zuciya ya sauke tare da koma yayi kwanta lamo…. yana juyi kawai batare yasan abin yi ba dan kwata kwata idanunshi ya kyan kyashe bbu alamun bacci acikinsu tunani kawai yake yana juyi. …
Washegari
da safe byn ta idar sallar asuba bata koma bacci ba saboda tasan yanayinta domin tana komawa bacci me nauyi ne zai dauke ta.
” kowa Kuma yasan yadda baccin safe yake dan haka kishigida kawai Tayi kan pray mate .
karfe bakwai daidai ta fito daga dakin da’aka sauke ciki. shr koina babu motsen kowa ballanantana mutun ya saka ran ko akwai wani bil,adama acikin gidan kasancewar week end ce.
tafiya take ‘ahankali cikin tsanyi jiki , har ta iso part din ummi takutsa kai ta shiga da sallmarta … 1
nan ma shr ba motsin kowa ciki “can taji ” alamun motsen ruwa a bathroom dan Haka tabbatar da ummi tana.
” bata wani tsaya batawa kanta lokaci ba ta soma yin abinda yakaita, daidai nablah tagama gyara koina ummi tafito daga bathroom..
tana ganin nablah ta saki fuskarta sosai tare da yin murmushi . nablah ta gaishe da ummi cike da girmamawa .
Ummi ta amsa tana mai Bin nablah din da wani irin kallo mai hade da mutuntaka .
Jikinta nablah a sanyaye takarasa toilet din ummi tawanke koina tasss … sai da tabbatar data gyara duk inda aka nunamata tasss ..
Amman banda part din mai gida Dan so take sai ta gama da koina acikin gidan sannan tashiga part dinsa saboda tsaro ..
Tsaye take a bakin kofar da zata shigar daita cikin part din mai gida.. hannuta rike da handle din kofar .
“takasa murdawa tashiga a dalilin zuciyarta da tasoma wani irin harbawa da sauri .
ta dinga jin wani irin ajikinta wani irin yanayi ne na daban ta tsinci kanta ciki .
,yayinda wani part na zuciyarta ke bata umarni tashiga kawai batare da wani tsoro ko fargaban ba , a tunaninta may be ma yafita ,duk dai tasan week end ce bai zama lallai yazanmato yana ciki ba.
Amman kwata kwata fargaba datake ciki ta hanata yunkurin kusawa cikin dakin ..
,sai da ta runtse idanunta tare da tattaro jaruntar ta sanyawa gangar jikinta , sannan ta iya murda handle din a natse tashiga dakin ,da idanun take bin dakin da kallo Sha,awa.
koina tsab tsab tamkar an gyara bbu wata alamun da zai nuna mutun na rayuwa a cikin dakin , ahankali ta kamo gefen lip’s din bakinta ta Dan ciza kadan kana ta soma abinda ya kaita .
STORY CONTINUES BELOW
Daki daya ya rage a cikin part din da bata gyara ba Dan haka ta kutsa ciki ta soma da wanke toilet ta zo kan royar bed dinshi, ahankali tasa hannuta kan blanket din dake rufe da gado da niyyar cirewa ta nike Dan kwata kwata batayi tunanin zata samu bil ,adama kwance cikinsa ba” a tsorace Tayi sauri sakin blanket din
‘ tana zare idanu waje tare da furta wayyo Allah nah a kasan ranta , take jikinta ya dauki kirma ta gigice tama rasa hanyar fita dan neman tsira daga cikin dakin.
tsabar rikecewa batasan sanda ta kama handle din kofar bathroom ba ta afka ciki … Ai ko tana ganin ba kofar fita bace ta sake juyo da sauri ,bbu inda baya rawa ajikinta tare da tattara kayan moupystick dinta tabar dakin da saurin bala’i tana haki sama sama tare da fidda numfashi .
A can bakin corridor din dake tsakanin part din deeni da ummi taja ta tsaya ta sake fidda numfashi tare da addu’ar Allah yasota.. ..
shi kuwa deeni dake kwance ya sake lumshe rikitattun idanunshi kawai dan tun shigowarta dakin idanunshi ke bude ganin itace yasa shi sake lafewa jikin pillow , dan shi ko yaya akayi motse zai farka.
yadda yaga ta gigice ne ya fi tsaya masa arai .
Dan Haka a tsanake ya tmbyi kansa to me hakan yake nufi da wannan gigicewar dayaga tayi ?
tabe bakinsa yayi tare da jan tsaki sannan yacigaba da baccinsa .
Sai kusan azahar sannan yatashi ,yashiga bathroom yayi wanka hade da alwala yana fitowa ya goge jikinsa ya shafa lotion ya zira jallabiya long sleeve tare da fashe ilahirin jikinsa da turaruka masu mugun kamshi da daukar hankali….
ahankali yake saukowa daga step hannushi rike da gefen jallabiyarsa har ya iso babban falon gidan inda ya tarar da duk ahalin gidan zaune .
ya gaida ummi yayinda zeenat ta gaidashi .
nablah da tun
saukowarsa taji tana kiciniya da numfashinta dake namen barin gangar jikinta ta gaisheshi muryarta aciki.
Yana jinta Yayi banza daita tamkar bai jita ba Sai ma hankalinsa daya dauka kacokan yamayar kan ummi dake kallo, muryarsa a dake yace first lov ni zani masallaci ta juyo tana dubansa tare da ce wa To sai kadawo yarona , sa kai ya fice .
takasan idannu take kallon every step of him dab ..dab… kmr wani jinin sarauta yayinda duk takunsa daya ke daidai da bugun zuciyarta har ya bace wa ganinta idanunta nakansa km Sai lokacin tasamu natsuwar zuciyarta, dan gabadaya ilahirin jikinta bbu inda bayi sake ba .
Muryata Ummi ce tasa ta sake dawowa cikin natsuwarta . nablah ki dawo kan kujera man ki zauna kin wani je can kin rakube akasa… maza taso kidawo nan kusa dani kinji “ki saki jikinki damu nan ma tamkar gida ne , a sanyaye nablah ta Mike tayi kmr yadda ummi ta umarceta .
Ummi tacigaba da magana . kishirya zuwa anjima akwai doctor da zata zo ta miki test kinji nablah cikin sanyin muryarta tace to…..
Ummi tasa hannu ta dauki remut tana canza channel zuwa zeeword .
, zeenat ta dan juyo a wulakance tana kallon inda nablah ke zaune tare da watsa mata wata uwar harara .. bakinta ta tabe kawai cigaba da aikawa nablah da harara iri batare da tabari ummi taganta ba ita dai haka kawai take jin tsanar yarinyar har cikin ranta .
hirar ball ummi da Zeenat keyi jifa jifa har suka gangaro kan hirar duniya ummi ce ke kokarin saka nablah ciki hirartasu ” yayinda ita km nablah Ido ne kawai nata ko murmushi Dan kwata kwata ita batasan ma me zata dasu ba’ dan Haka tacigaba da sauraronsu har zuwa sanda mai gidan ya dawo daga masjid tare da wata mata suka shigo ..
byn sunyi shafta da wasa da dariya tare da mdm zeenat wanda hakan ya nuna alamun sun saba da junansu sosai ba tun yau ba ..
” ummi ta umarce doctor din data shiga da nablah ,hakan ce takasance domin bata tsaya wani tmbyr ummi ba Dan tasan abinda zatayi .
abinda yabawa nablah mamaki bai wuce ganin komai na aikin likitoci dake cikin dakin ba.
bbu abinda bbu har gadon kwanciyar marasa lafiya akwai shi a dakin. +
, Doctor din ta umarce nablah data zauna” ta zaro sirinji acikin hand bag dinta .
ta zuki jininta wanda hakan bai sa hankalin nablah tashi ko daya ba saboda daman hakan yana daga cikin budget dinta.
byn doctor din ta dibi jininta tashiga wani daki still dai acikin dakin da suke ciki tare da bawa nablah umarnin Wuce wa.
Ta Mike jikinta bbu kwari Sai dai bbu wata alamun damuwa ko fargaba atattare daita .
direct hanyar step tabi ” ta nufi dakinta” koda tashiga dakin ma rasa abinyi tayi domin kewar yan gidasu ne tattare da zuciyarta” tana ji kmr taje tasamu ummi ta roketa takirawo mata number auntyta su gaisa .
tunawa datayi Killa ma yanzu haka ummi na can tare da mutun da ko kafafunsa ta kalla zuciyata tamkar zata tarwatse takeji” yasa ta share kawai taki koma gurin ummi ..
Sannu ahankali Yau kusan kwanakin nablah goma kennan a gidan Amman bbu Wanda yayi mata bayanin komai dangane da jininta da a gwada.
duk da hakan bawai ya dameta bane illa rashin jin muryar daya daga cikin ah’linta ,tunanin hakan ne yasata .
Mikewa tsaye cikin hanzari da niyar zuwa tasamu ummi ta taimaka ta kiramata auntyta .
bude kofarta ke da wuya taga mutun tsaye abakin kofarsa yana kokarin yiwa kofar dakinsa da key .
Da sauri ta risinawa tana gaishe shi shiru yaki amsawa km bai da alamun zai amsa din sai ma dauke kansa dayayi yacigaba da abinda yake .
Jikinta yayi maseefar yin sanyi da abinda deeni yayi mata.
Dan haka ‘ahankali ta dinga daga kafafunta yayinda Rainta yake a dagule tana jin wani irin ciwo mai radadi , duk da kasancewarta mai matukar hakuri da rashin sauri fushi akan abu. Amman abinda mai gidan yayi ya taba ranta .
domin a rayuwarta idan akwai abinda ta tsana da Gani bai wuce tsagwaron raini hankali da cin fuska tare da isgilanci ba dan zata iya dauka komai Banda su .
ahankali ta dinga daga kafafunta dasuka gama sagewa ta nufi hanyar da zata sadata da ummi . dan gurinta kadai take samun sausauci acikin gidan. +
A tsanake yabita da Idanunshi tare da rike kungunsa da hannu daya yana bin bayata da wani irin matsiyacin kallo.
yayinda zuciyarsa ke harbawa ko kifta idanunsa bai da alamun yi ” so yake ya tabbatarwa idanunsa abinda yake Gani a cikin mafarkinsa , hajabi dake sanye ajikinta bai hanashi yimata kallon kurulla ba ” gabadaya idanunshi sun rufe ya shagaltu da kallon Surar jikinta a bayyane … domin ganinta yake murarta ba tare da wani hijabi ba .
Jin yadda idanunshi ke yawo a tsantsar jikinta ne ” yasa Kirjinta ke wani irin harbawa da sauri tamkar wacce ake bugawa guduma a kahon zuwa .
Yanayin sanyita da tafiyarta yasake shagaltar dashi ba dan deeni yagaji da kallonta ba ,ya dauke idanunsa akan ba Sai Dan gudun juyowarta cikin sautsayi.
What lokaci tana kan step Dan ko rabi batayi ba dan kallon da kafe dashi ne ya sayayar mata jiki tare da rage mata kuzarin jikinta .. ahankali km tasoma jin kmr takun mutun abaya daidai ta kai rabin step din cak…. taja ta tsaya tare da rabe jikinta gefe daya .
alamun tana son bawa duk wani mai son wuce dama ,duk da oready jikinta yabata alamun mutumin data baro tsaye ke saukowa sakamakon kamshin turarensa mai tada hankali da ta keji …
shr kusan two minutes sannan yazo ya wuce ta gefenta zuciyarsa na tacigaba da harbawa .duk da Bai bari jikinsu ya tabu da juna .
Tana nan tsaye har yazo ya wuceta tare da bude wata kofa ya shiga dan kusan har yanzu bata gama sanin kan dakun nan gidan ba.
,inda tasan zata samu ummi kai tsaye ta nufa zaune suke ita da Zeenat kmr koda yaushe suna kallo TV suna hira abunsu hankali kwance. Yayinda kayan fruit ke gabansu da sallmarta takarasa inda suke sannan tasamu guri kan Tia’s ta zauna tana wasa da Zara zaran yatsun hannuwanta. ummi ta juyo ahankali tana duban nablah byn ta amsa sallamarta kallonta kawai take Tare da nazarinta .
yayinda zeenat tunda ta juyo ta mata kallo daya ta dauke kanta tare da mai hankalinta kan film da,akeyi .
Sai da ummi tagama nazarinta tsab sannan ta takira sunan nablah ..
Nablah ya’akayi ne ?
Nablah tayi kasa da kanta tana cigaba da yamutsa yatsun hannuta a atsorace muryarta cike da sanyi da in…inna.. tace dan… Allah daman ina..Ina. son nayi magana ne da auntyna ta fadi hakan idanunta suna masu cikowa da hawaye. domin daukarta ko baza su kiramata auntyta bane shiyasa duk takoma wani iri .Ummi tayi murmushi kawai Tare da sake zubawa nablah ido ganin yadda duk ta dawo kalar tausayi ..
ummi ta girgiza kanta sannan tace yanzu akan zakiyi magana da auntynki ne duk kika dawo haka tamkar zakiyi da kuka?
.. gsky nablah akwai shagwaba atare dake tasa ummi takarasa fadar haka Tare da Mika hannu ta janyo wayarta dake gefe tasoma dealing number Salmah ta Miko mata wayar tare da nunawa nablah wani daki da hannuta . Kishi Ga nan kiyi wayarki kinji diyarta .. haushi da takaici ne gabadaya suka gama turnuke zuciyar Zeenat dake zaune gurin tamkar ta tashi ta shake wuyar nablah ta dinga a zuciyarta , tarasa yadda zatayi ne kawai yasa ta dinga ja tsaki tana aiyana yadda zatayi da yarinyar..
+
wayar manne da kunnenta har tashiga dakin da ummi ta nuna mata ,daidai nan murya aunty Salmah ta doki dodon kunneta tun kafin nablah tayi magana aunty Salmah tace assalamu alaikum hjy anyi lafiya .
murya nablah cike da doki da shagwaba aunty ba hjy ba ce nablah ce .
Aunty Salmah tayi murmushi A’a nablah.. yana ji muryarki haka kmr kina cikin damuwa ?
Sai da nablah ta sauke ajiyar zuciya sannan tace bazaki jini cikin damuwa ba , byn kewarku ta dameni duk sai aunty Salmah gigice.
tace ko dai akwai da matsala ne a gidan?
” nablah tace uhmmmm fa ba matsalar komai.. in ma akwai matsalar nan bai wuce kewarku ba .
Nablah tacigaba aunty baki bawa mama number wayar hjyr bane kmr yadda kika ce gsky zuwa yanzu na matsu da son jin muryarta, km kmr naganni agabanta haka nake ji ,aunty Salmah tace Eh ban bata number ba nafison zuwa nan da sati biyu tukun nasan zuwa wannan lokacin kingama da sanin halin mutane gidan , ni dai abinda nake so dake ki zauna lfy da kowa Amman da kinga akwai matsi da takura just give me a cul” furrrrr zaki ga aunty ki kmr flay.
nablah ta saki sanyayyayiyar murmurshin dayasa dimple dinta lotsawa sosai wanda hakan ke sake fito da ainihin bawar kyawun da Allah yayi mata . +
Ahankali ” tace Allah aunty bbu matsalar komai fa aunty Salmah tace to.to. shikenan ,ki kama kanki da kyau km ki dinga saka hijab dinki duk inda zaki shiga a gidan .
Nablah tace har baccima dashi nake aunty Salmah Tayi yauwa Yar gari nablah na murmushi tasake bude baki da niyar tambayar auntyta dip …maganar ta tsaya …… Tana zaro Idanu waje sakamakon hasken dataga ya gwaraye dakin gabadaya duk daman can akwai wuta a dakin dan koda tashigo fan na aiki ..
kwance yake akan kujera idanunshi a lumshe yana kallonta kmr ranar farko daya soma ganinta a rayuwasa .
murya aunty Salmah taji tana cigaba da cewa lfy na jiki shr kin dauke wuta kmr NEPA.
A daburce tasoma in in na , A’a…….uhmmmm ba komai to yanaga duk kin rikece kigayamin in wani abu nablah tace Allah bbu komai aunty to kigaida hjy zan Kuma bawa mama number hjy zuwa jibi inshallahu ki kwantar da hankaliki zata kiraki, itama ta matsu taji muryar autata ,da kyar nablah dake kokuwa da numfashinta ta iya bude baki tace to aunty sannan ta kashe wayar Tare da sauke wayar daga kunnena.
har lokacin bai dauke idanunshi akanta ba wanda shi kansa basan ma Yana kallon nata ba .
Itama shanyayun idanunta ta zuba masa kawai tana kallon kwakkywar fuskarsa dam …taji kirjinta da zuciyarta sun amsa a lokaci daya take ta soma jin tsoron yanayin irin kallon dayake mata.
,jikinta kuwa Banda kirma bbu abinda yake ,takoina gumi ya dinga tsatsafo mata ajikinta Jira kawai take taji yace arrrrrrr ta arce da gudun maseefa Amman Sai kawai taga sabanin haka, domin ko motsa bakinsa bai da alamun yi ballanantana akai gasamun fitowar kalma daya daga bakinsa Sai ma taga tabe bakinsa tare da dauke idanunshi akanta .
aransa kuwa cewa yayi munafuka kawai Tayi wani shr kmr ba yanzu tagama wage baki tana waya ba..???
Ni dai nace uhmmmm deeni Banda kin fad ar gaskiya…nooooo
komawa yayi sosai yayi kwanciyarsa normal ganin datayi ya kina ya kwanta ne yasa tayi saurin juyawa da jikinta na rawa ta bar dakin har hijab dinta na neman hardeta kafafuwanta . +
” afrigece ta dawo parlour inda ta bar su ummi .
Ummi kadai tagani zaune Banda mdm muzeenat ko Ina tashiga oho ita dai tunda tasamu ta mikawa ummi wayarta ta bawa karfa iska .
tayi shr sannan komai ta tuna ta dagamin kai …
Koda tashiga dakin ma bayi tashiga dan jin yadda cikinta ke murdawa ,tun sanda take tsaye gaban horo dan sunnan data bashi kennan take jin yadda cikinta ya cure guri daya .
toilet tayi sosai byn tagama tashiga cikin bathtub ta kunnawa kainta” shawa ta dade kwance tana jin dadin yadda ruwan ke rasa kowani part na jikinta .
sai data soma jin kiran sallar ne a masallaci dake cikin gidan sannan tayi alwala ta fito jikinta daure da towel zigidir tayi gaban mirrow tana goge sauran wuraren dake da ruwa ajikinta yayansa take bin koina ajikinta da kallon, yadda yanayinta ya canza gabadaya ‘ahankali tayi murmushi tana sake kallon kanta doguwar rigar mai dagon hannu ta zirawa jikinta tare da zira hijab dinta ta tada ikama…
Byn ta idar da sallah ne ta Mike ‘ahankali jikinta a tsanyaye takarasa jikin window dakinta .
” ta makale hade da dan zuge labule window kadan ,ta yadda zata ji dadin hango abinda ke wakana a compound din estate din. +
Tana nan tsaye tana kallon yadda motocin ke shige da fice a cikin estate din , ta zurawa waje Ido sosai kmr mai shirin hango wani abu na daban aciki estate din, yayinda take shakar wata iska ta musamman mai dadi da ratsa jiki.
wanda rabonta da jin irin haka ta dade , tun kafin shigowarta cikin gidan.
,har wani lumshe shanyayun idanunta take sakamakon farinciki data tsinci kainta ciki.
,Ta dauki tsawon lokacin makalle agurin tana shan iska “karar bude kofar dakin data ji anyi ne.
Yasa ta dan juyo da sauri hade da sakin labulen window.
ahankali nablah ta sauke idanunta fess. akan Zeenat dake tsaye kikam.. tana mazurai . take gaban nablah Yashiga faduwa da sauri a yatsine Zeenat ke watsawa nablah wani irin mugun kallon wanda ke hautsina kayan cikinta , ganin irin kallon rashin arzikin da Zeenat ke binta dashi ne . yasa nablah shan jinin jikinta.
tabe baki Zeenat tayi sannan tace Yar iskar baiwa… kawai abinda yakawo kennan , kin wani zo kin nemi waje a daki kin zauna kina tamkar boka dan tsabar munafurci , to kike so yayi miki sauran aiki da yayi saura uhm ?
Nablah tayi saurin girgiza kanta tare da cewa dan Allah aunty kiyi hakuri wlh na dauka ko mungama aikin ne.
Zeenat , ta sake watsamata wata uwar hararar hade da kallon banza.. wanda hakan ya suka sake frigita zuciyar nabla dake tsaye Amman ta dake batare da tabari Zeenat din ta gane yanayin data ciki ba .
Mtsssssss Zeenat taja tsaki tare da cewa dan Allah malam ni fito ki kije ki karasawa mutane aiki sannan km ki daura min abinci ,Yar isakar baiwa… nablah tayi shr tare da dago shanyayun idanunta tana kallon Zeenat dasu ,yayinda take jin zuciyarta tamkar zata kama da wuta tsabar takaicin sunan da Zeenat din kirata dashi .
Zeenat tace
Kin wani tsareni da idanunwa narai narai kina kallona ko baza kiyi bane ?
a tsanake batare da wata alamun tsoro ko fargaba ba nablah tace zanyi ..
Ok minti biyu kacal nabaki “naganki a kitchen “idan kika kuskura kika bata min lokaci zakiga yadda zan ci ubanki a gidan nan ” tana gama fadar haka
ta juya fuuuuuu tasoma tafiya tana kunfar baki. +
“Nablah tayi zuru kawai tare da bin bayan Zeenat da wani irin kallon mamaki da alajabi abinda tayi mata.
dan ko kusa batayi tsammani zata fuskanci irin wannan babbar wulakancin ba mai cike da al,mara .
Yau itace aka aiki tajawo aka zagin mahaifinta..abanza uban ta fa aka zaga ,ta furta akan akasan ranta, wato silar ainkinta ne jawo a dinga wulakanta mata uba Haka km ma har da kiranta da sunan baiwa…baiwa fa takirani dashi ta sake maimaita sunan a filli gabadaya abin yazo mata wani iri km abazata” tamkar ba gaske ba.
Anya kuwa rayuwar zata yuwu a Haka tun ba,aje koina ba an fara da zagar mata mahaifnta.
” Anya kuwa zan iya daukar wannan kalar kaskancin da iskanci kuwa ,abinda ta tmbyi kanta da kanta Keenan?
,’ahankali ta furzar da iska ta bakinta tana furta wlh da sake Dan zan iya daukar komai na kunci rayuwa Amman Banda zagar min iyaye .
,
, Mtssss taja tsaki itama tana harara kofar da Zeenat tabi .cikin sanyi jiki ta nufi kitchen .
Ko minti biyu batayi da daura ruwan abincin dare ba Zeenat takaraso ta tsaya a bakin kitchen din tana kiran.. ke….ke.. nablah dake tsaye tana jin Tayi banza daita duk da tasan daita take sannan km taki juyowa …
Sai ma cigaba da aikinta Tayi.
Sai da Zeenat ta sake maimaita kiranta sannan nablah da ke ..Kusan Sau uku sannan nablah ta juyo a danketa tana kallon cikin idanunta Zeenat .
Zeenat tace ,Yar iska yarinya kawai kina jin mutane suna kiranki Amman dan dakikanci irin naki kika yi shr..ko
nablah ta hadiye bacin ran dataji yana taso mata tun daga tsintsiyar kafafunta ,sannan tace kiyi hakuri basan dani kike ba” sbd ita kalmar ke.. din da kika ce bata daga cikinta sunan nablah….
. eyyyye Zeenat ta fadi Haka tare da ta ware ido tana kallon nablah da mamaki ni zaki kawa rainin hankali , nablah tace kiyi hakuri aunty barainin sense bane a zafafe Zeenat tace yi min shr stupid girl kawai ni zaki kalla kicewa ba sunanki ke ba…. Dan bakida mutunci , to kisani ni daga yau da sunan ke … zan dinga kiraki ,Dan Allah idan nakiraki dan ubanki karki amsa kiga yadda zanyi dake a cikin gidan nan .. .
nablah ta datse lip’s din bakinta na kasa da karfi gaske jin zafin abinda Zeenat tace mata , kusan minti biyu tsakani nablah ta sake duban inda Zeenat ke tsaye har lokaci gabadaya gabobin jikinta sun sage muryarta cike da rauni km Haka kawai ta tsinci kanta da cewa kiyi hakuri aunty .da hannu Zeenat ta katseta .. yimin shr Dan Allah dan bana son sake jin ko muryarki ne .. km ki sauke pot dinan ki daura min indomi yanzu yanzu taja tsaki tare barin kitchen din. +
cike da mamaki yarinyar Zeenat takarasa ta zauna ranta a abace wahake take fidda numfashi dan kwata kwata bata taba jin tsanar mai aikinta irin yadda take jin haushin nablah .
Gashin yarinyar kmr bata da wani alamun tsoro atare atare daita .
Cikin mintinan da basu wuce biyar ba ta sauke indomi ta yuye a plate sannan ta sake maida pot din abinci dare kan gas .
zaune ta sameta ta hankice a parlour sai faman cika take tana batsewa tare da hura hanci ‘tana kada kafa daya ..
ahankali nablah ta ajiye mata plate din indomi agabanta akan center table tare da kwalbar vitermilk kana ta juya ,tabar parlour .
,banda tunanin da mamaki Zeenat bbu abinda nablah keyi .
ko meyasa ita takasance irin haka ba kmr ummi ba ,mai matsananin son mutane da kyautata musu” km tana lura da irin yadda ummi din ke matukar bawa duk wasu mutane dake shigowa cikin gidan, kulawa ta musamman ” sabanin ita wannan bazanr matar mai kama da mutane China .
, ‘Ahankali nablah tacigaba da aikinta na zagin Zeenat din aranta sai data gyara koina tsab .
sannan taje tambaye Zeenat din ko akwai wani sauran aikin da zatayi Dan gujewa cin mutuncinta .
,a yatsine Zeenat din ta dago fuskarta tamkar hadari sannan tayi mata nuni da hannuta alamun zata iya wucewa kawai .
jikinta a mace tabar gurin , da kyar ta dinga daga kafafuwanta tsabar gajiya datayi , yayinda idanunta suka ciciko da Hawayen batayi kokarin hana hawayen idanunta zubowa ba,sbd tashin hankali take ciki da wutar dake ruruwa a zuciyarta tana tafe tana kukan zuci yayinda hawayen idanunta ke sake cigaba da bin fuskarta…
ahankali ta hau step daidai conar da zata kaita dakinta.
anan suka kusan cin karo da deeni da ba dan Allah yakiyaye da sai daita tajita a faffadan kirjinsa . sakamakon hannunta duka biyu datasa tana goge Hawayen idanunta ..
daddaden kamshin turarensa ne ya doki hancinta a frigice tayi sauri janye jikina..
Ta makale jikin bango batare da tasan Tayi hakan ba , jikinta ya dauki rawa kirrrrrrma hawaye km sharrrrrrr suna sake bin fuskarta ido cikin ido suke kallon juna ,itace ta soma janye idanunta ta ta runtse gam tana jinra kawai taji saukar mari ..
, tsayawa yayi cak Shima yana karemata kallo up and down . +
STORY CONTINUES BELOW
A tsorace tasa tafin hannunta duka ta rufe fuskarta dashi.. kijinta na sake daukar kirrrrrrma .
‘Ahankali ya ja wani irin mugun tsaki mtsssssss wanda hakan ya sake jefe zuciyar nabla shiga cikin rudani .
, yana tsananin jin haushi yadda yarinyar ke behaviors kmr wata dakiykiya ..
harara ya zabga mata kana ya sake jan tsaki sannan ya yasoma taka step . tana jin takunsa har sai da yakurewa step din Sosai sannan ta bude idanunta da sauri ta fada dakinta tare dannawa kofar key ..
.ta fada kan gado takarasa fashewa da wani sabon kuka…. Mai cin rai blaming kanta kawai take ta yadda tayi sanadin jefa kanta cikin meyakawoni matsala.
, meyakawoni cikin wannan gidan ?
meyasa na kawo kaina cikin halaka irin haka ?
anya kuwa nayiwa kaina adalci Dana zabarwa kaina irin wannan rayuwar ,mai cike da kaskancin da wahala ..
Anya kuwa zan iya cigaba da yin wannan aikin kuwa ? Haka ta dinga jerowa kanta tambayar iri iri batare da tasan abinda yakamata Tayi ba ..
yanzu irin rayuwar da zanyi kennan?
..Ta sake jeho kanta tmby.
agigice tatashi zaune ta jingina bayanta da jikin gadon dakin tare da zubawa celling dakin Ido tana tunanin abinda yakamata tayi “shr yabiyo baya na wani dan lokaci .
tuno auntynta datayi ne yasa tayi saurin sauke ajiyar zuciya, Dan tasan ita kadai ce zata iya fidda ita a wannan halin wulakancin datake ciki , batare wata matsala ba. ai aikin bai zama dole ba , da sauri ta hau goge Hawayen fuskarta tace zan kwantar da hankalina na zuwa wani lokaci “kafin nasamu yin waya da auntyna . ahankali ta Mike tashiga bayi ta dauro alwala sallar magrib koda ta idar ma bata tashi ba sai datayi isha’i a gurin .
, bata bi takan komai ba dan ko abinci bataji zata iya zuwa ta sakawa cikinta ba .
ballallantana ta hadu da hawan jini ,da ciwon ulcer wato deeni da Zeenat .
,Ta kwanta anan ta dunkule jikinta cikin hijab tare da lumshe idanunta kawai” duk da ba wani bacci takeji ba, ahankali tarinka jin yadda zuciyata tasoma beating dip….dip…. kafin daga baya tashigayi da sauri da sauri sakamakon tunowa da Mr horo datayi …
“Tarasa dalilin dayasa duk sanda tayi arba dashi ko ta tuno shi take shiga cikin tashin hankali, ba.
, addu’a tasoma aciki. zuciyarta ya Allah…ya Allah kamin tsari dashi da duk wani wani shirin dake tattare dashi . Allah idan zama acikin gidan nan alkhari ne a rayuwarta Allah kasamun natsuwa da hakuri zama da matar gidan .
,idan km bbu alkhari Allah ka fidda cikin kowace irin maseefa cikin sauki . haka tayi tayi yan addu’oita , har taji zuciyarta ta dan samu natsuwa daga tashin hankali data shiga na wuncin gadi ,daga karshe bacci mai nauyi yayi gabadaita.
Acan kasa kuwa DEENI ne kwance akan thrre sites hannunsa rike da remut yayinda zeenat ke zaune a gefenshi suna hira ,rashin ganin nablah yasa duk ummi ta damu har . takai ga tambayar zeenat ita , ummi tace ni kuwa ina yarinyar nablah take ne har yanzu banga saukowarta ba ko lafiya?deeni dake zaune yaji gabansa ya fadi zuciyarsa tashiga harbawa .
zeenat ta Dan yatsina fuska kana tace wa ummi . ai tun dazu kafin ki dawo ta sauko taci abincinta ta koma dakinta dayake fita ummi tayi ,yau . Ummi ok na jita shr ne .sannan tacigaba yabon nablah yarinya mai hankali wlh .
Zeenat taji magannun ummi na neman saka mata ciwon kai ,ta barta da karyar data ,sharara mata ta ba gaira ba dalili . +
Zeenat ta Mike tsaye tsam tare da yiwa ummi sai da safe Dan itama yau bacci take son yi da wuri sbd tana da lecture karfe goma daidai na safe .. .
ita data shiga dakinta da niyar samun natsuwa Amman zuciyar tashigo mata da tunani iri iri ciki kuwa har da maganar haihuwar da bata km samu ba har yanzu wanda shine jigon rayuwarta a gidan mijinta ..
‘Byn tafiyar Zeenat ummi dago Ahankali tana duban deeni tare da kiran sunanshi..
DEENI dake kwance ya amsa hade da dan mikewa zaune ya mai da hankalikasa kacokan a kan umminsa .
Ummi ta numfasa sannan tacigaba deeni naji kamin shr game da zance yarinyar nan mai aiki… , gabansa ya yanke ya fadi rasssssss …jin abinda ummi tace “ya zubawa ummi ido kawai yayi shr yarasa me zai ce mata ” saima shiga wani yanayi da yayi .’ahankali
ya runtse idanunshi yana Jin tamkar ummi ta watsa masa ruwan zafi yake ji da wannan maganar yarinyar datayi masa.
dan zuwa yanzu ya dauka ummi tabar zance ne kwata kwata ganin bata sake mishi maganarta ba .
“ummi tace kamin shr DEENI idan kasan baka shirya yin komai ba akai mezai hanna ni kabarni na aiwatar da komai domin nasan abinda zanyi ..
“ahankali deeni ya bude rikitattun idanunshi ya zubawa ummi su kawai yana kallonta ,kada masa kanta tayi alamun abinda ta fada din haka take nufi .
yace first lov kiyi hakuri Dan Allah zansan abin yi Amman dan Allah kidan karamin lokaci kadan kinji first lov .
Ummi tayi shr can Kuma tace shikenan Ni daita burina bai wuce nasamu abinda nake fatan samu daga yarinya ba .. tan Ga fadar Haka ta mike tana mishi sai da safe .
,Karfe shadaya daidai deeni Yashiga dakin Zeenat byn ya gama shirin bacci cikin wasu ratsasun kayan bacci.m masu matukar kyau.
batasan shigowarsa ba tana can duniyar tunani “ahankali DEENI yakaraso har inda take tare da ya kamo tafin hannuta cikin nasa Yana murzawa sannan ta juyo ‘ahankali tana sauke naunauyen ajiyar zuciya.
ya tsareta da idanunshi kawai sannan yace meke damunki Zeenat ?
Ke ke nan kullun bakya gajiya ,ki raba kanki da wannan tunani ,kisani tunani shine abu mafi sauki dake saurin nakasa rayuwar Dan Adama Amman ke kin maidashi abincin cinki kullun ..,kinsa Allah ba tunaninki ke damuna ba ,halin da first lov zata shiga sanadin wani abu ya sameki nake .idan akwai abinda kika san yana dumunki please tell me…
tayi shr kawai tana kallonsa sun dade a haka suna kallon junansu sannan , ko me ta tuna Kuma ta sakar masa murmushi karfin hali ta matse hannushi cikin nata gam tare da lumshe masa idanunta ta girgiza masa kai alamun bbu komai . +
Deeni yace I you sure bbu komai” ta dage masa girarta daya kmr yadda yake mata shima, har taso tabashi dariya yayi murmushi tare kwantowa jikinta ya rungumeta ajikinsa tsam tsam Yana aika mata da sakwanninsa masu matukar birkita mata kwalkwaluwa .. hannuwansa duka yasa ya zagaye kugunta dashi ,Haka kawai Yashiga aiyanata yarinyar, ‘ahankali ya sake narke mata ajiki yana duk inda hannushi yaci karo dashi itama cikin kwarewa tasoma romancing dinshi .
ranar dai kwana sukayi suna jiyar da kansu dadi deeni yayi Tayi batare gajiya ba .
Iya murzuwa Zeenat Tayi shi a hannun DEENI har kai saka masa kuka sannan yabarta ya Mike Yana mata korafin tacika ragunwaci.
ita batace masa komai ba . washegari gari ma da kyar tasoma tashi yayinda da kyar ta dinga kafafunta, bayi tashiga ta gasa jikinta da ruwan zafi .
baita tabar gidan ba Sai wuraren 9 AM .. ..
Tun byn fitar Zeenat nablah ke faman aikin gyaran gidan batare da samu damar zama ta huta ba.
,duk da matar gidan bata nan hakan bai hanata yin kokarin taga ta kammala da aikin ba .
+
Tana tsaye a kitchen din yayinda hannuta ke kai kawon gogen kayan kitchen din Wanda ya zame mata dole kullun garin Allah Ya waye sai tayi.
laraba ce tashigo kitchen din tana yimata sannu tare da sanya hannu tasoma kokarin taimakawa nabla da wasu ayyukan .
Nablah Tayi murmushi dama kinbarshi aunty yanzu zan gama ai”
Karki damu sis nima zaune nake bana aikin komai shiyasa kikaga naxo .
gashi km Naga kmr aikin Yayi miki yawa dan nasan yadda yanayin aikin gidan nan yake da cin rai km bai karewa.
” Dan ma Allah taimaka madam batanan da yanzu tasa jininki ya hau kilometers duhu.
,Dan har gara hjy da mai gidan akanta ” Dan shi maigidan kwata kwata baya shiga harkar mutune yayinda ita hjy wani lokacin takan tausayawa mutun.
nablah tace Haka ne .laraba tacigaba
amman ita madam Komai zata saka mutun Sai ta nuna maka iko da isa ” Ga zagin rashin mutunci , tamkar ta haifi mutane , km duk irin aikin da zakiyi mata idan bai gamsar daita a banza yake a gurinta .
nablah Tayi shr kawai tana sauraronta batare da tace mata ba , komai Sai ma maida hankalinta datayi kan aikinta.
laraba ta sake cigaba kinsa Allah ko abinci kika dafa wannan matar , muddin baiyi mata ba wlh dole ki sake yin wani .
Nablah dake tsaye ‘tana aikinta , tace nifa Ina ganin kmr mdm din nan taki , kwarkwar ce…….
“Haba aiko laraba ta kwashe da wata muguwar dariya , kai gsky nablah baki da kirki wlh madam din ce kwarkwar tana mai sake kwashewa da dariya .
nablah ta bar abinda take ta juyo Sosai tana duban inda laraba take .
Kinsa Allah wlh Ni kallon kwarkwar nakewa matar nan sbd wasu abubuwa dana Ga tana yi Na marasa hankali.
nan dai sukai ta hirarsu tare da zagin Zeenat din ,.
nablah har da cewa Allah Yasa ogon madam yakarowa mdm amarya labara Tayi saurin kai hannuta ta toshe wa nablah baki ,tare da leka parlour sakamakon jin kmr motsin mutun .
“ganin bbu alamun kowa ne yasa ta dawo ta tsaya kusa da nablah . +
“ai inaganin abinda mdm din tafi tsana kennan a rayuwarta .
“kishiya…. uhm zata iya yin komai akan mijinta. ba kya ganin ko inda mijinta yake bata son ana zuwa ,ke ko kananan kaya kika saka wlh Sai takawa mutun miki birki da guzirin Harare da zagin .
,kinji ba , ai abinda yasa kikaji nace miki , Ina mata kallon kwarkwar ,Dan some time sai inga kmr tana hararata byn ban mata komai ba inji cewar nablah.
Laraba ta numfasa sannan tace shiyasa lamarin zaman gidan Sai kin kara da hakuri. nabla ta sauke naunauyen ajiye zuciya sannan tace indai hakan kike fama da matar nan Na jinjina miki dan gsky kinyi kokari wlh.
, ai a Haka ma bakiga komai ba indai mdm ce inji cewar laraba , Dan naga kmr ke kina da wani matsayi a gidan” tunda har an barki kina ganin mai gidan ,gashi km har special room aka baki a sama.
” Mtssss nablah taja wata muguwar tsaki matsayi ko walaha byn bakada wata darajar a idanun masu gidan. “nabla ta sake yin kasa kasa da muryarta Dan kar wani yajiyo abinda zata ce sannan tacigaba abinda zan fada din nan Dan Allah bana son ki fadawa kowa” Amman Allah nayi mugun tsanar mdm Zeenat din nan byn Haka km Ina fatan Allah Yasa mijinta ya kara aure.
, Dan kawai nayi kallon irin kalar haukar da zatayi koda yake ma ,may be by the time din da zai kara auren ma ,na dade da barin gidan Dan bana jin zan dau wani lokaci a gidan nan .
, laraba tayi saurin marairaice fuska haba nabla Dan Allah kada kiyi Haka ,Karki tafi ki barni na rigada na saba dake banzan so ki tafi kibarni ba .hakuri kawai zakiyi da halinta ,kiyi abinda yakawo ki.
laraba da nabla suka cigaba da aikinsu suna hira sama sama laraba Na sake cigaba dabawa nablah labarin gidan dama estate din gabadaya ,Da yake ita tana fita sosai .
nabla sai murmushi take km tana kwadayin fita taga yanayin estate din Dan tun zuwanta gidan ko get bata sake lekawa ba .
+
Washegari gabadaya da gyre gyre aka tashi dashi a gidan.
koina ka kalla a hargitse yake saboda wani gyara da za’a a sama da km zuwan bakuwar daza suyi daga kasar India, kmr yadda nabla taji zeenat nafawa wata friend dinta datazo .
kai kawo nablah ta dinga yi tsakanin upstairs da downstairs , kallo daya zakamata ka gane tsansar yadda ta fita haiyacinta tsabar gajiyar dake tattare daita dole ma kaji ta baka tausayi .
tsaye take kusa da zeenat ta takure jikinta waje daya , byn ta gama waken kayan da Zeenat din tayi amfani dasu ,banda harara da kallon banza bbu abinda take jiho mata .
,A zafafe Zeenat din ta kallo inda nablah ke tsaye kinzo kin wani tsayamin a kai kmr zaki tsotsemin jinin jiki ki dauki plastic ki kawai my hrt.. takarasa fadar Haka tana watsawa nablah wanimugun harara .
Nablah tasa ‘hannu kennan zata dauka sai ga laraba tashigo kitchen wasu kayan wando jeans da Riga Tayi gurin frij .
zeenat ta kallite ta kalli kayan jikin laraba sannan ta watsa mata wata uwar harara ,har nablah ta ji hantar cikinta sun cure gurin daya .
Fuskarta a yatsine Tace meyye haka kuma laraba …kinsa bana son wannan iskanci a gidana .
bama na hanaki saka irin wayan nan kayan ba?
Nablah ta dago ta dubi aunty laraba jens ne a jikinta sai riga iya gwiwa .
ok karuwanci kika zo yimin a gida ko me?
, da sauri laraba tasoma bata hakuri .
dan Allah madam kiyi hakuri wlh bazan sake sanya su ba wannan mistake ne .
,da hannuta mdm Zeenat ta dakarta da ita ya isa bana son jin komai daga yanzu ma na kashe sa irin iriin wayandanan kaya muddin kina son zamanki ya daure dani. sannan ta kallo inda nablah tsaye har lokacin bataje inda ta aiketa ba ,tsawa ta buga mata ke kuma tsayuwar uban me kikewa mutane da bazaki wuce ba kin wani tsareni da shegun idanuki masu kama dana mayu.. bazaki wuce inda na aike ki ba.Duk da nablah taji maseefar tsoron yadda taga Zeenat Tayi Amman hakan bai sa ta nuna ta fito da tsoronta filli ba a dake sannan km fuskarta a hade ta bar kitchen din hade da tausayawa kai banta. +
Domin bata ganin laifi Zeenat sai nata domin ita takawo kanta da kanta cikin wannan maseefa.
Ta Dan tsaya kafin takarasa parlour mai gidan Tasa ‘hijab dinta tana goge hawayen daya yasoma bin kuncinta dan iri irin abinda zeenat takeyi musu yana taba mata zuciya sosai .
‘cikin sanyin jiki tasoma tafiya har ta iso parlour da mai gidan yake tare da bakinsa da sallamarta tashigo. muryata fal cike da tsoro da fargaba.
kallo daya DEENI yayi mata ya dauke idanunsa sai abokansa guda biyu ne suka amsa mata sallamar.
, ahankali cikin tafiyarta mai daukar hankalin ga duk wanda ya kalleta , ta karaso ciki sosai , ta tsugunna ta ajiye plastic din da cup’s .
Banda kallon kasa ido bbu abinda DEENI yake mata ,’ahankali tare da natsuwa ta soma tsiyaya musu coffee .
cikin wata kwasatsiyar murya taji ance ke zaman me kikeyiwa mutane anan …. oya live this place now…
Gabanta ya dukan uku uku ,cikin tsananin tsoro hade da tashin hankali ta Mike tsaye , jikinta ,har rawa rawa yake tasoma kokarin daga kafafunta yayinda idanunta suka ciciko da hawaye tafff, ta bar parlour, daidai bakin kofar main parlour ta kusan ci karo da zeenat da sauri taja da baya ta tsaya, tana mai sa bayan hannuta tana goge hawayen dake bin fuskarta.
Zeenat ta tsaya kawai tana kallonta tare da nazarinta da kyau sannan tace kukan munafurcin uban me kikeyiwa mutane ,kmr ba aikin kudi kikazo yi ba tasoma maseefa tana zaginta . +
, duk yadda nablah taso hadiya damuwar dake zuciyarta hakan yakasa samuwa , domin kuwa sabon Hawayen dake makale a idanunta ne suka samu nasarar zubowa .
, uhmmmm daman Sai Dana gaya ummi tabari a sallemiki Dan nasan bazaki iya tabukawa mutane komai Amman tace Sam…
Yanzu kukan iskanci me kikeyiwa mutane nablah ta girgirza kai tare da cewa bbu .
Zeenat ta tasoma kada kai cewa zama ayi komai din sannan ta Miko nablah wani karamin jug mai dauke suga tace ungo Ni ki kaiwa mijinta baiwar banza kawai.
,jikinta a sanyaye km badan ranta yaso ba ta sake koma parlour …
byn ta fito ne ma abokinsa manir yace DEENI ina kasamo wannan fine bby din mai tsabar kyau gaskiya tamin kyau sosai …..
Take DEENI ya hade rai tamkar Wanda yaji wani mugun abu .. meye matsalarka daita ?
Manir yace yarinyar ce tamun kyau kawai , a fusace deeni yace bakowa bace facce house girl dina.
dayan abokin nasa ne yace gaskiya yarinyar tana da kyau sosai ba karya gashi Tayi maseefar ta haduwa dayawa .
irin wayan nan Ai nashiga mota ne da kewaye kasashen duniya .
A zafafe DEENI yace bafa nason iskanci nan naku idan abinda yakawoku kennan natashi nakama gabana .
Manir yayi dariya tare da cewa kai fa matsalar kennan to laifi ne dan mutun yaga abu ya yaba sai km yazama abin damuwa.
Fahad dake zaune yana nazarin deeni ya amshe da cewa kai meyasa DEENI kike yin irin haka ne ? Kacika daukar komai da zafe.
DEENI ya hassala dan takaici Dan Allah ni kun dameni da zance wata banza yarinyar ni wlh duk na Raina da ajinku wlh .
” da har kuka tsaya karewa wannan banzar yarinyar kallo ” fahad yace idan kai makahone baka gani mu wlh muna Gani ,kuma dole mu yaba baiwar da Allah yayi .
, ‘Ahankali ya ture document din dake zube gabansa ,Coffeen da nablah tasoma siyaya a cup, din yasa ‘hannu ya dauka yasoma kurba ahankali ahankali tare da lumshe ritattun idanunshi .
Manir da fahad suka bishi da wani irin kallo ganin abinda yayi . yayinda manir ya cika da mamakin deeni .
Fahad yace mekake nufi yanzu da haka sai da hadeye wanda ke bakinshi sannan yace ga abinda nake nufi nan kuwa , kowa ya yakama gabansa.
Manir yayi murmushi sannan yace to munji amman zai siyayyamu coffee to , juyar da fuskasa yayi wani gefen sannan yace ai duk kuna da ‘hannu ,idan baku tashi Sha ba ,kubarshi .
murmushin fahad ya sake yi yace da alamun rashin mutunci kawai kake son yimana . +
DEENI ya daga kafadunsa, duka a alamun I don’t care .
nan dai suka mai da abun wasa atsakaninsu suka cigaba dayin abinda ya kawo su byn sungama ne DEENI ya Mike yace yana zuwa .
Zuwa yayi ya canza kayan jikinsa zuwa kanan kaya sai kamshi mat Hamilton 27 yake zubawa part din ummi yashiga yana kiran sunanta .. first lov.. were are you .
jin shiru bata amsa bane yasashi kutsa kansa cikin bedroom dinta kai tsaye batare da yayi tunanin wani abu .
Ita kuwa dake zaune tana jerawa ummi kayanta da mai wakin yakawo dazu a Waldrop ta zabura ta Mike tsaye da sauri, duk ilaihi jikinta bbu inda Bai dauki rawa ba saboda tsabar tsoron muryar data jiyo.
Sosai kamshin turarensa ke kusanto dakin alamun yana gab da shigowa . gashi bbu komai ajikinta daga ita sai daguwar riga mai ‘hannu harmless cikin sauri sauri ta soma neman hijab dinta .
data cire amman tarasa inda ta ,ajiye .
har yashigo dakin , cak ta tsaya ta kasa kwakwarar motse ,jin tsayuwarsa jingine da kofa yasa take kirjinta ya buga yayinda zuciyata tashiga ..
aikin da tasaba a duk sanda , ta kasance tare da DEENI.
shima tsaye cak yana Kare mata kallo tsab wanda in ba lura mutun yayi da kyau ba.
,ba za’ice ita yake bi da wannan mayataccen kallo ba .
shida kansa yasan in yace yarinyar batayi ba , tabbas karya yake km son ranshi ya fada .
ahankali yakaraso dakin sosai yana sake kiran sunna ummi . kainta a sunkuye a kasa yayinda zuciyata ke wani irin bugawa da sauri cikin siririyar muryata mai cike da in inna … tace ta.. tana.. bathroom …
Bai ma tsaya wani sararonta ba ballanantana ya nuna alamun yaji abinda tace ba , tunda shima yaji alamun haka.
juya kawai yayi yabar dakin cikin takunsa ,na tsanyaye namiji .
Numfashi ta sauke tana may sa dukka ‘hannuna ta dafe kirjinta dashi tare da sauke ajiye zuciya.
wayyo Allah wannan mutumin ba dai frigita mutane ba .
numfashi ta dinga fitarwa ‘ahankali ‘ahankali har ta dawo normal .km Sai a lokacin taga hijab din ta washe a gefen ‘tsabar rudewa ce tasa takasa Gani.
fitar shi bai fi da minti uku ba ummi tafito tanawa nablah sannu da aiki sannan tasamu waje ta zauna, tana dan Jan nabla da hira , itama dai ba laifi takan dan saki jikinta ummi dan tafi zeenat sau dubu har aka kira sallah suna tare da ummi dan dakin tadawo yanxun saboda aikin da za’a yi Wanda ya hada har da dakin nablah.
Mikewa tayi nablah Tayi tare cewa ummi Ina son naje nayi sallah .
murmushin ummi Tayi haba nablah yanzu sallah ma sai kin tambaya ,ummi girgiza kawai tare da cewa ,jeki kawai kiyi sallahrki kinji ..