[Advertisements⬇️]

WANI AURE CHAPTER 19 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WANI AURE.CHAPTER 19


Rungume take a faffadan kirjinsa har lokacin ” yayinda hawayen tausayin kanta ke cigaba da bin kuncinta” danasani tattare da nadamar abinda ta aikatawa kanta a can baya ne ke damun zuciya .
‘hakika rayuwa bata da tabbas gashi komai yana neman tsaya mata ” zuciyarta kemata wani irin zafi yau tazo mata tazo mata abu mafi muni ,kishiya …fa.
yau ita zeenat da kanta ake kokarin  son sanya  mijin yi karo mata kishiya… Kishirya.. ta sake  maimaita  hakan akasan ranta  abinda tafi mugun  tsana  a rayuwarta kennan ,wai aba kishiya .. +

  kirjinta ke mata radadi da nauyi  tamkar an dora mata dutse ita kadai tasan yadda take jin zuciyarta da gangar jikinta… wani irin maseefaffen kishin mijinta ne ke  sake tasomata fiyye da yadda take ji a da. 
  tsanar  sauran matan dake duniya zaune bbu aure ne ya dirar mata lokacin.

Kukanta yasoma damun tunani ,kasancewarsa mutun marason damuwa da yawan hayaniya. hakan yasa yasoma  sausauta rungumar da yayi mata daga qarshe ya ma  rabata da sansar jikinshi gabadaya.,
Tare da zuba mata rikitattun idanushi kawai  Dan shi sam kwata kwata bai iya wani abu wai  rarrashi ba   . ballanantana har ya tsaya wani bata lokacinsa gurin  rarrashinta . +

,a dake taji sautin muryasa   ‘,malama kiyiwa mutane shr duk  kinbi kin cika min kunne da wannan bazan kukan naki  mara ma’ana  ..

ko uban   wani ne ya  aikeki wulakanta cikin  da Allah yabaki tun farko .

  Wlh idan kikasa damuwarki  tashafi lafiyar  mahaifiyata   akan maganar kishiya ..nan zan baki mamaki ..
   kishiya …bama daya zanyi ba  har biyu idan nagama sai nayi .
   “inyaso  ki mutu sai ki kashe kanki kmr yadda kika ce  ,sha sha kawai  ya fadi hakan yana may  da jan mugun tsaki… mtssss  .

take jikinta ya dauki rawa kirrrrrrma jin maganar bama kishiya daya ba  har idan yaso zaiyi ..
  “ai …batasan sanda ta zube  kasa ba.
  Tana kuka Tana  girgiza masa kai dan  gabadaya  kasa magana tayi sai jujjuya  kai kawai  take tana zubda kwalla.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


Wata uwar  ,harara ya watsa  mata  hade da binta da wani irin bazan kallo wanda yasan hantar cikinta kadawa wayyo hrt karka min haka dan girman Allah karka min kishi….sai km Tayi shr Tana cigaba da kuka…. bakinsa Ya tabi tare da  cewa meyya haka oya Mike ..  Mike ni kibar  min dakin kinsa fa ni bana son damuwa .
Yana gama fadar haka ya haura saman gadonsa ya dau towel daman km abinda ya fito dauka kennan . +

bathroom ya sake koma   ya sakarwa kansa ruwa tare da dauro alwala sannan ya fito kugunsa daure da towel .

mamaki ganinta   yayi   har lokacin bata bar dakin ba Tana nan durkushe tamkar yadda yabarta  ,ganin yanayinsa da km yadda yake kallonta da rikitattun idanushi masu matukar  birkita mata kwalkwaluwa ,da hana zuciyarta sukuni .
yasa  ta mike tsaye da sauri jiki  har rawa rawa yake tsabar tashin hankali ,a sukwane ta  tabar masa dakinsa  Dan tasan halinsa maseefar sa, bakaramin aikinsa bane ya shuka  mata rashin mutunci idan ma taci sa’a Bai hada mata da mugun duka ba tunda daman ya mata  gargadi kar sake ganinta    bedroom ba  .

Fitarta daga dakin  yayi daidai da sauke  naunauyen ajiyar zuciyar da yayi..
, yayinda wani gefe na zucitarsa na Dan tausayawa mata  game da halin   rayuwar data jefe kanta ciki.

hakika shi yasan  tana   wahalar da zuciyarta ne kawai akan  batun   kishiya .
Dan kishiya ba fashi sai ta zauna daita.

‘ahankali ya sake  sauke  wani naunauyen ajiyar zuciya tare laso lip’s dinshi na kasa …
” cikin sauri ya shiga shirya  kansa cikin wasu hadaddun kananan kaya masu matukar kyau da daukar hankali shirt  ce  ashi  colour mai gajeren hannu  sanye a jikinsa sai  wando blue  jeans  wanda suka yi matukar karbar surar jikinsa.
‘ koda yake shi din may matukar kyau ne km kowani irin kaya ya sanyawa jikinsa    sai sun  amshi karbi shi.
cikin sanyin nan nasa da takunsa na kasaita  yakarasa gaban mirrow  ya dauki turarensa mai matukar  kamshi ya feshe ilahirin jikinsa dashi.
  ‘ sannan ya gabatar da sallah byn ya idar sallah ne ya sauko parlour kasa cike da isa .

Anan  ya  iske    ,Ummi tare da zeenat zaune sunyi jugun jugun abin duniya ya damesu.

  Ummi  ta rafka uban tagumi tana  tunani duk da yasan zance dai bazai wuce akan maganar aunty shi bane .

Yana tsaye yana kallonsu yaga  zeenat  ta   kwanta  akan  cinyar ummi tana kuka  ‘  tana goge Hawayen idanunta da bayan  hannuta kukan ya isa haka mamana kada wani ciwon yakamaki fa.. . Ummi bazan iya zama da kishiya ba wlh taba kirjina kiji ta fadi haka   tare da  janyo  hannun Ummi zuwa  saman  kirjinata .

Kallo daya yayi musu tare da   dauke idanunshi daga kansu..
ya tabe baki kai tsaye  dinning area ya nufa  yaci abincinsa hankali kwance   . Sannan yacigaba da zamansa yaciro wayarsa yana  operating ..
Km duk yana  jin abinda zeenat kecewa da yadda Ummi ke rarrashinta da kwantar mata da hankali akan bbu wata kishiya da za’a yo mata ita kadai ce bbu kari …
,  Jin haka Yasa Daga can inda yake zaune yayi gyaran murya.
  ,Ummi  ce ta  juyo  ‘ahankali Tana dubansa  ,yatsansa daya ,ya karkada mata alamun a,a harara Ummi   ta sakar masa yayinda  shi km ya girgiza mata   kai kawai yana tabe baki.

Ahankali Ya Mike tsaye ya dawo kusa da Ummi Ya zauna fuskarsa a hade yace  ke…..yi excuse dinmu please zata Mike kennan  ummin ta maidaita   Dan me zaka korar min yarinya tana cikin halin  damuwa ?
idan har baka shirya yin magana dani bane tana nan  kana iya barin maganar  har zuwa wani lokaci dan bbu inda zata ke koma kiyi kwanciyar kinji..
,koma kuwa  tayi  kwanciyarta  kmr yadda Ummi tace amman har lokacin Hawaye bai daina bin kuncinta ba  .

Kafadarsa ya sake  dagawa alamun bai damu ba da abinda Ummi tace ba ..
Wayarsa ce ta dauki kara sauti mai dadi  Mikewa tsaye tare da pic din call din ya manna a kunnenshi tana tafiya . +

Hello ..Yaya ganin nan zuwa yanzu   sannan yakashe wayar yabar musu gidan gabadaya .

Yana fita Ummi  ta dauki wayarta takira hajiya  turai bagun farko  hjy turai ta dauki wayar  da sallamarta ” bbu  abinda Ummi  tasoma tmbyrta sai  an km samu kuwa ?

  Ummi tayi hakan ne  Dan kada  zeenat din  tadago  wani abu dangane da shirinta.

bangaren hjy turai kuwa cewa Tayi eh ansamu amman  sai dai  guda daya ce  km Tanada dan shekara ,Ummi tace kmr shekara nawa gareta ?

eh zata kai kmr 23 haka inji cewar hjy turai ok ki  kawota naganta  hjy turai tace sai dai    kibari zuwa  gobe idan Allah Ya kai mu ‘ latifa zata zo gurina idan zata wuce gida  zan bari  takaraso miki da yarinya ,Ummi tace ok shikennan sai sun zo din takashe wayarta  tare yiwa hjy turai godiya .


Washegari da misalin karfe hudu daidai latifa takawowa Ummi shafa. kallo daya Ummi tayiwa yarinyar taji kwata kwata  bata kwanta mata arai ba a ranta tace  itama kennan Ina Ga oga DEENI.
   tasan ma bazai wank mu,ammultu  da yarinyar ba , girgiza kai kawai Tayi byn tasa an kawowa latifa abin motsa baki .

,’ahankali Ummi ta Mike tsaye ta nufi wani kofa  tayi warning  din glass  tare da cewa latifa ta biyo bayanta ,  latifa ta Mike ‘ahankali tabi bayan Ummi .

Wani madaidaici parlour Ummi takai latifa byn sun zauna ne Ummi tace Kira sunan lafita ta amsa kina jina latifa ..yarinyar nan bata min ba km nasan tunda bata min ba da wuya tawa mai gidan Shima  kinsa shi da kyankyami tsiya .

dan haka  asamo wata kota gurinki ne amman dai zan  bar Ita wannan din kafin asamu wata ,dan aikin gida sbd aikin nayiwa laraba yawa ,latifa tace ok babu damuwa ,daman kuwa  akwai wata yarinya dake neman aikin gida irin wannan  amman  kibari zan   miki kokari inshallahu .
Ummi tace shikennan latifa Nagode sosai suka yiwa juna  sallama sannan latifa ta wuce .
Byn fitar DEENI daga gida kai tsaye gidan  yayansa mahamud dake cikin estate din yayi . +

zaune suke shida  da Yaya Muhamud din  babban parlour baki na gidansa .
Shr yabiya baya kafin Yaya Muhamud ya numfasa tukun yasoma magana kmr haka  DEENI  abinda yasa nace kazo nan ina nemanka ,akwai  magana may mahimmanci da nake son muyi akan company,s dinmu.
,kaga dai yanayin danake ciki  halin yanzu nima girma ne yake zuwa min yayinda  abubuwa ke sake min yawa ni kadai raina nake kokari akan lamuran company,s dinmu na cikin gida da sauran kasashen duniya  shine naga  yakamata ace kaima , ka’ajiye wannan aikin naka kazo mutaru mu kula da komai Tare.

,kasan mutane wasu basu da amana , amman yaka Gani akan lamarin .. DEENI yayi shr kawai yana sauraransa har yakai karshen zance ,sannan ya dan yi murmushi karfin hali  har dimple dinsa ya lotsa ,rasa mezai cewa yayansa yayi dan haka yace  shikennan Yaya zan duba nagani  idan hakan zai yiwu dan gsky Ina matukar son aikina km banason abinda zai rabani dashi .

,DEENI..yaya Muhamud ya sake kiran sunanshi DEENI ya dago da idanushin yana dubansa dasu  , wannan aikin naka  yana mahimmanci a rayuwa  Shima   km talafawa company,s dinmu  haka ,amman abinda nake so dakai  kaduba din kmr yadda kace ,nan suka bar zance suka  shiga hirar duniya har DEENI yake sanar masa da abinda mama ta abuja, tayiwa Ummi akan zeenat , Shima Yaya Muhamud din baiji dadin abinda Tayi ba .


Bayan wata biyu
Al’amarin duniya fa yasoma damun  Zeenat  tayi mugun  tada hankali kan maganar aunty,n su Ita DEENI gabadaya afrigice take da komai , kawai burinta ahalin  yanzu bai wuce kawai ta ganta dauke da ciki ba . +

amman kwata kwata  hakan yaki samuwa gareta ga lokacin na tafiya   , gabadaya  hankalinta  a tashe yake matuka.

haka ma ta bangaren  Ummi itama  hankalinta  a tashe yake da  yadda take ganin yanayin diyar tata. 
,shi kuwa gogan sam  bbu ruwanshi da wani tashin hankali da suke cikin .
  ‘ hakar gabansa kawai yake domin  komai yana tafiyar masa yadda yake so  daga office har gida  .


Sakamakon damuwar da zeenat tasawa ranta ne har hakan yajawo   ta Dan rame kadan kallo daya mutun zai mata yagane tana cikin tension .
” Ko school ma sai da  wata friend dinta may suna halima  ta gane Tana cikin damuwa  dan haka tmbyeta ,zeenat bata wani boye mata komai dangane da halin datake  ciki ba .

,nan fa halima tace Ina ai baki Ga ta zama ba zeenat  kishiya fa ….Ai ni ko sunanta ban kaunar ji ballanantana tashigo min gida gaskiya kitashi tsaye tun wuri , zeenat marairaice murya hali bansa yadda zanyi ba ,bansan koina ba , hospital kawai nasa km muje ,hali tace ok kada ki damu akwai wani mutun danasan yana bada maganin haihuwa ,kibari zan rakaki gurinsa amman a sango ota dake hanyar abe okuta yake ,idai zaki zan rakaki  ,zeenat najin haka ta kamo hannunwan halima duka cikin hannuta Tana murna  dan Allah hali kitaima min koma Ina ne zani indai zan samu cikin haihuwa nidai banason mijina yayi min kishiya  dan bana kaunar zama daita a rayuwata  ta duniya  km nasan rashin haihuwar nan zai iya bawata shigo min gida .
gara mutuwata danaga zuwan wannan rana.
,hali tace haba kada ki damu zan taimakamiki ai murigada mun zama daya .
Nan fa suka bar zance da zumar gobe zasu tafi songo ota .
Washegari kuwa da wuri zeenat tashirya har Ummi tacewa yana Ga yau kinashiri cikin sauri haka.
Murmushi Tayi kawai Tayi wlh  , Ummi lecture gareni da wuri shiyasa kika ganni haka.
  Ummi tace ok ,  koke fa haka nake son ganinki cikin walwala da kazarkazar tattare  kwanciyar hankali .
,banason ganinki cikin damuwa zeenat ta sake yin  murmushi tare da  cewa  Ummi sai ta dawo Ummi tayi  mata addu’a .
+

Haka suka je gurin may bada maganin Ita da hali batare da sanin kowa ba .
Bawani abu mutumin  yabata ba, baya Ga  garin magani baki    yace ta da lemun tsami ta dinga da sha  da zarar sun gama sex da mijinta har sai maganin yakare har yana sake tabbatar mata maganin bazai kai Ga karewa ba zata samu ciki  . Uhmmmm

da murnarta dawo gida km Tayi  kmr yadda mutumin yace Tayi.
,tare da zaman jira tsammani , har zuwa  lokacin zuwan  period dinta, bata Ga  jini ba  , .

  Tacigaba da shan magani  ,murna kuwa  kmr ta Yaya ,dan duka  tunanin ciki gareta amman byn kmr sati daya da shanye maganin  sai Ga jini ..
ranar kuwa data Ga jinin zaman dirshan Tayi a bayi “tare da daura hannuta  duka bisa kai ta saka kuka a gurin .

,wunin ranar bbu inda  taje ko parlour kasa bata keko ba , ,  Ummi zaune ita da DEENI wanda Bai dade da dawo ba zaune yake  kusa da ummi suna hira ,ganin shr shr bata zeenat ba yasata  zuwa dakinta , da fari ta dauka ko bacci take ,ganinta kwance  tana sheshekar  kuka ne  yasa gaban  Ummi faduwa da sauri takaraso inda take kwance  Tana kiran sunanta ke zeenat.. lfy ki kuwa ,kukan me kike haka ? 

Aiko zeenat naganin Ummi ta sake rushewa da wani sabon  kuka km  tashiga gayawa Ummi abinda ya faru amman sai dai ta boye bata gayawa Ummi zance zuwa gurin amso magani ba .

Allah sarki Ummi baiwar Allah haka ta dinga rararshinta Tana kuka itama. jin shr yayi yawa ne yasa DEENI biyo bayan  Ummi yaga ko lfy  aiko  yaga abin mamaki dan zaune ya  tadda ummi yayinda zeenat din ke rungume ajikinta  suna aikin kuka tamkar wayan,da akayiwa mutuwa mai zafi.
Yana ganin haka yasan iskancin zeenat din ne ya motsa  ,dan haka bai wani damu ba ko tada hankalinsa.
dan yasan zance gizo baya wuce na koki ,sai ma tsawar  daya dakawa zeenat din ..Tare da nunata da yatsansa daya ke……. banson wulakancin da rainin hankali fa yazaki zo ki tasa min uwa gaba da  kuka?
Ke…duk matsalar ki sai sanya mutane ciki.

” kinsa Allah idan baki daidaita kanki da kyau ba zan iya  ra…..
Ummi ta katseshi   ta hanyar taga masa hannu ,ya isa haka  bana son jin komai .
km ni ai baita ce tasani kuka ba, Tayi missing din kwanakin period dinta ne so shine da shirmenta  ta dauka ko ciki ne  da Ita ,sai km Ga period din Ta yazo .
  ” kasanta da shririta shine ta zauna Tana kuka ,ni km tausayi tabani ,Ummi na kaiwa karshen maganarta , DEENI ya watsawa zeenat din harara ,yanzu ne kika damu da haihuwa ko da kika ji zance abinda kika fi tsana a rayuwarki ?
  Kinsa Allah zeenat ki fita daga idona  kada ki kashe min uwa da matsalarki .
,kikasa   wasa ma wlh me gabadaya zanyi in yaso ki mutu gabadaya na huta da matsalarki   , km bbu abinda zai faru Dan duniyata  zan cigaba da ci hankali kwance  byn baki raye .
kinga karshen kishi kennan…. zeenat najin haka  ta fashe da wanj sabon kukan Ummi kina jinsa ko …..so yake na mutu yakara aure  sbd ya daina sona …sai km  Hawaye sharrrrrr . +

Dakuwa Ummi Tayi masa da hannuta  ungo nan DEENI  wani  irin rashin imani ne haka ,kake nuna mata , rashin son nata har yakai ka dinga yi mata  fatar mutuwa km a gabana DEENI… ko kunya idanuna  bakaji ba .
To  inshallahu ta Allah bataka ba km  bbu wata  mutuwa a fuskar diyata km haihuwa zatayi shi da yarda Allah .

Zeenat fa  tashiga neman haihuwa zanga zabga tamkar zatayi hauka duk inda taji ana bada maganin  haihuwa sai karfa taje ba .

har gurin wata sabuwar malama datazo Lagos   wacce ake Kira da malama  shema,u taje neman magani haihuwa.

wanda mutune sukayi ittifaki akanta  muguwar Yar damfara ce daga Yola take  ,da farko Kano ta fara zuwa tana Dan farar mutane  mlm aminu Ibrahim daurawa ya fatattakota  ,shine tayo garin  Lagos . Nan ma dai zeenat taje  bbu wata nasara data samu sai kudinta data kashe  .

Cikin haka maganar da mama ta abuja Tayi akan kara auren DEENI taje Ga  kunne big Dady , musamman  yasa tazo daga abuja km  ya nuna mata sam Bai ji dadin abinda Tayi ba.

,inda ma shi DEENI din ne da kansa yaso kara aure wannan dadan bbu may hanashi  amman tace lallai sai ya kara aure akan wata lalura ta  matasa ko wani dalili na dabam , hakan baiyi ba dan haka bayason a km tadda zance .

Wannan batu da big Dady  yayi da km daurin gidin Ummi da take dashi yasa hankalin zeenat din kwanciya  .

Cikin dan kankani lokacin ta maida kibarta Tayi fes daita ta dawo da gayunta kmr da.

A cikin wannan lokacin ne latifa takira Ummi tasanar daita cewa  an samu mai aiki karama Yar shekara gamo shabakwai … yanzu haka jakar kayanta a gidanta ya kwana Amma ita bazata samu damar zuwa ba ,sai dai zata turo mata da number yayar yarinyar takira ta ,tabata address din estate din murna fall cike da zuciyar ummi tace badamuwa turo min yanzu yanzu ,kinji diyarta….ummi na sauke  wayar sako yashigo tana dubawa taga suna kmr salmah Tare da number .

Al’amarin gidan kuwa gabadaya ya sake canzawa  tun daga kan mutane dake rayuwa  a cikin gidan har zuwa Ga gidan  karan kansa  .
Dan gabadaya DEENI ya gyara kowa Ina a gidan inda ya sake fadada girman  dakunan dake kasa  tare da kawatasu da ado  .
Wanda  ,a halin yanzu  yakoma  amfani da dakin sama da kasa .kallo daya zakawa gidan ya birgeka km  kasan ya fita daban da sauran gidanjen dake cikin  estate din.

+

Ummi bata Kira number Salmah ba sai byn data sallami shafa da kwana biyu sannan takirata 

Ranar da shafa ta tarkata tabar gidan ranar  itama Zeenat   tashi da zumar dawowa dakinta na kasa wanda DEENI ya cire mata ,dan haka bata tsaya wani bata lokaci ba tasa laraba tayi mata komai ,tare da abubuwan ta masu mahimmanci sai abinda baza’a rasa ba tabari a dakin sama .itama takoma amfani da daki biyu a cikin gidan.

Matashiyar budurwa ce Tare da yayarta  tsaye  abakin titi .
suna jiran mota ‘ sun dauki sama da rabin awa tsaye  a haka suna jiran abin hawa amman kowace mota tazo wucewa”  cike take tap da mutane .
,sakamakon cunkoson  ababen hawa da aka tashi dashi a garin Lagos.

, aunty me zai hana muhau machine ne   , kinsa fa inda zamu da Nisa  sosai .
  , saboda ke da zaki dawo .
  Dan naga yanayin garin yau sai a slow inji  cewar  nablah…..

, aunty Salmah  ta dan juyo ta kalli gefen inda  sisinta  ke tsaye   tare da cewa  ‘shikenan nablah  muhau machine din kawai Dan nima bana son dadewa .

gaba  kadan suka  karasa  wajen yan machina, 
    malam dan Allah lawansi bustop zaka kai mu, inji cewar aunty Salmah.
mai okada ya  gyara tsayuwar machine dinsa ta yadda za su samu damar hawa ..

Kin hawa aunty salma tayi sai ma tmbyr mai okada take da  nawa zamu bayar tukun.

  , Atakaice dai  muna kai mutun daya  a naira dari mutun biyu dari da hamsi aunty Salma tace  Shikenan ke nablah  fara hawa.
” dayake kaidar Aunty salmah kennan.
muddin da kanneta zata hau machine bata yarda tafara zama a farko, sai dai tace su hau gaba ita km  ta zauna a  baya.
‘Ahankali Suka dane machine”
dai dai bakin  filling station din dake   lawansi, suka sauka aunty Salmah ta bude jakarta tabawa Dan okada kudinsa . +

tafiya   suka soma yi zuwa inda zasu shiga motar da zata kai su surelere .

Suna tafi suna hirarsu abin sha’awa   har suka isa wajen shiga motar Masha.

, daidai Bakin get din da zai kai ka ilori Street suka sauka , tafiya kadan sukayi suka isa inda zasu .

aunty Salma tasa hannu ta tura get din gidan wanda  koda yaushe  haka yake a bude, .

Da sallamarsu suka karasa bakin net din latifa  .  Aunty Salmah na kwalara mata Kira latifa latifa..  Amman shiru ba amsa yayinda   kofar ma take  a kulle .
Tsayuwar Minti goma sukayi  kafin daga  baya suka jiyo sautin  muryar latifa .
ku biyo  ta nan kofar  kitchen,an kulle nan ne sbd yara .
” zagayawa  sukayi ta kofar kitchen  suka  shiga.

Latifa   naganin su tasaki murmushi ,kai kai gsky dai Salmah kunyi latti wlh    kin kuwa san nisan unguwar da zaku kuwa ?

aunty Salma tayi dariya  wlh kinsa halin mutumin naki  hukuma ne sai da rarrashi .
duk shi ya bata mana lokaci , gashi Bai fita da wuri  ba.

, to shikenan sai kuxo Ku tafi   tun rana batayi ba .        “ai ma hajiyar takirani  tun sassafe tamin kwantance yadda zamuje can din ” da ,na so mu wuce ta mushi ne saboda akwai mota mai zuwa  can direct  sai dai kinsa jakar nablah na nan shiyasa dole sai  munbiyo tanan din .                      
  
Latifa tace ok  ina zuwa ku shiga daga ciki  bari na amso sako  dana aika  .
dan Allah kiyi sauri  ba sai munshiga  ba . +

ina  jakar take saboda kar  lokaci ya wuce ?latifa  ta kwallawa  mai aikinta  kira… ke uzaima … 
“uzaima ta amsa tare da karasowa ,Gani aunty jeki dauko  jakar nablah a karkashin step yanzu .

Sannan taje tasamu yaron mijinta da ta aika tun dazu ATM tace ibrahim ya’akayi ne ,ya tura hannu ciki aljihun wandonsa ya  ciro kudi masu yawa ya mikawa  latifa Tare da ATM a saman kudin  tace yauwa  na gode.

  har ya juya ta  kiransa  ya dawo ,  akwai wa’yanda nike son  ka    dan kai mun   su inda zasu samu motar zuwa  obalende .
, yace to badamuwa ,ta koma ciki inda ta tarar har an dauko jakar nablah  ,latifa  taciro dubu biyar ta mikawa Aunty  salmah gashi kikara kuyi kudin mota dashi ,saboda yanayin hanya .

aunty Salma ta amsa tayi  godiya, hade da yi mata sallama .
bakomai  sai kin dawo mayi waya duk abinda ake ciki Kya sanar min ni dai addu’ata Allah Yasa tayi musu ..
  
Kai tsaye   inda zusu samu motar da zata kai su  obalende  ya, ajiye su .

,  Suna tsaye  cikin mota BRT  dayake standing suka samu ,  Aunty  salmah tace  nablah ajiye jakar kayanki   ki zauna akai  .
Sannan kiciromin wayata a jaka ki duba dealing zakiga wata number MTN karshenta 12 kikiramin ,ki mikomin.

,haka kuwa nablah tayi tare da  Mikowa Aunty salmah wayar .

ta  manna wayar a kunneta tare dayin sallama. hello hjy gamu cikin motar obalende daga nan wace motar zamu shiga” daga can bangare  ummi kuwa  cewa tayi yauwa inkunzo ku hau motar mai zuwa aja sai ku sauka (a jakonde first get).
ai kinsa lekki ko?

”  aunty Salmah tace A,a bansan side din  ba , ina dai jin sunan waje.

Ok ..   inda kun sauka a first get din kiyi  flashing dina.
Aunty salam  ta, ajiye wayar..

Bayan kmr  awa daya da rabi   sai gasu     jakonde first get…

Kiran ummi suka sake yi kmr yadda  tace .
ok kuyi crossing main road  ta hannuku  na daman zakuga sambord an rubuta lekki road hanyar zaku biyo layi na uku .
daga hannun hagunku in kun kai kikirani

,nan dai suka sakeyin tafiya minti goma suka sake kiranta byn ta dauka ne tace kuna kan layin ne?
  Aunty salmah tace  Eh to zakuga cona ta hannun  hagunku  zakuga wani babban church ,dan suna tafiya ne  suna waya da ummi  tana basu direction .

Aunty tace ga church din nan  ma mungani  to ku tsaya a wajen zaki ga get  opposite din shi .aunty Salmah tayi saurin cewa  shine.

PLASNUW   ROWS FAMILY  ESTATE ?
Ummi tace yauwa shine  kin iya rubuto?
Sai da  Aunty salam tayi murmushi sannan tace  ba laifi .
ok  bani minti biyu   na kira securities din get din.
” za su tambayi sunanki aunty salam tace to ….
+

Nablah ta zubawa hadadden  get din gidan idanunta kawai  wanda basan yadda zata iya kwatanta  girman sa ba ballanantana tsawonsa .

sai dai zata iya kiran get din  da JAMA GET ..wato na gidan bursunan dake garin Lagos KIRIKIRI .

   daya daga cikin securities din get din ne ya dan leko ganinsu tsaye ne  yasa shi  cewa  madam can i help you?  
who are you, looking 4 duk  a tare ya  jehowa auty Salmah tamyr dayake itace kusa dashi.
,  
the person we are lokin 4 said we should Wait  4 her “inji cewar aunty Salmah mutumin yace or rigth  sannan yakoma mazauninsa “

can ya sake lekowa yace  are you salmah ?
  “auty  Salmah ta  daga masa  kai .
  ‘yace ok you can  come in.
tare da  bude musu Dan  karamin get suka shiga  ya nuna masu ,wani gurin yace inter and rigth ur ful name down
,Can  u  write ya sake tmbyr Aunty Salmah.
tace Eh.
byn sunyi komai har da sign sannan ya sake bude wata kofar   yayi gaba yace su biyo shi a baya.
‘Ahankali ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta wanda kusan rashin abinyi ne kesata yin haka. +

,haske taga ya garwaye parlour gabadaya ‘koina ya dauki haske tamkar rana ce ba dare ba.
wani irin kamshi ne mai azababen dadi  yake kusantota ,har inda take zaune ,yayinda mamallakin turaren ke tukarowa parlour zuwa indasuke haka shima kamshin ke kai kawo acikin hancin nablah .
har zuwa sanda mamallakin kamshin  ya karasa  yashigowa,  gabadaya parlour ya canza wani  irin cent na daban”,  take gabanta yashiga dukan uku uku  gashi tana san  dagowa ta kalli kowaye mamallakin wannan azababen kamshi Amman takasa dago idanunta,dan ko kwakkwaran motse kasawa tayi   ballanantana tasan kowaye mamallakin wannan turaren mace ko namiji ne sakamakon  kanta dake Duke   akasa har lokacin.
Ta kafe teas din parlour da  ido “.

Ta kasan idanunta ta hango wando jeans. wanda hakan ya tabbatar mata  da mammallakin kamshi turaren nan    namiji ne .
“duk da   bataga komai   nashi , baya ga Zara zaran yatsun kafafuwansa da kowani ke kwance da gargasan gashi.
  ‘ahankali  yake takowa zuwa inda ummi  take zaune  .

Muryar ummi  taji tana cewa ka fito son ?
tun da zu  muke Jira … matarka tace wanka kake yi  ,’ahankali ya  juyo ga  mahaifiyarsa  yana kallonta sannan yadanyi  murmushi gefen baki .
   hannunsa yasa  ya  dauki remut ya canza channel zuwa ta  kallon Ball  sannan ya   Mike kwance kan  three site hade da cewa gani  first lov  anything for you my beautiful mum…  
Ummi  ta saki murmushi sakamakon jin dadi abinda yace  sannan tace  kai ko Allah ya shirya min kai …tare da kai  hannuta  kai kan tilon dan nata ta shafa tautausar  sumar kansa  tana jin wani irin sanyi a ranta .
Muryata A dake  takira sunansa ‘ deeni…..
Ya dago rikitattun idanushi yana kallon ummi batare da yace komai ba …
  “maganar mai aiki da mukayi dakai za’a kawo   ,to orready ma  she’s here..  ta iso sauran muji meyye ra:ayinka   nidai na  amince daita hundred percent  .. +

kasa kasa yayi da muryasa wanda  daman can  haka  yanayin maganarsa take .. 
Kuma yadda yayi magana  ummi  ce kawai zata iya jin meyace ..

tana ina …….?

abinda kunne nablah  ya ji kennan.
gata can ummi ta fada tare da nuna inda nablah take zaune …

‘ahankali ya juyo tare da  kallon  inda ummi  tayi mishi  nuni da hannuta. idanunshi ya runtse  gam sannan cikin sanyayyayiyar muryasa mai kashi jikin duk wanda tsautsayi yasa ya fada kunne shi ” yace first lov…  kice ta Mike naganta ..

tsoro da fargaba tare da  frigice ne  suka taru suka kaiwa zuciyar nablah farmaki” tashi daya taji   jikinta yakama rawa  gabanta yashiga faduwa da sauri, tasoma  tunanin abinda   ya kawota  wannan gida mai cike da abun tsoro da abubuwan ban mamaki …

sai kawai ta tsinci kanta da ambato sunnan Allah a kasan ranta  da karanto  duk addu’ar datazo bakinta Dan rage jin tsoro ” take taji wata natsuwa tazota mata   aboye ta dinga sauke ajiyar zuciya .

‘Ahankali ummi  takira sunata  nablah  Mike tsaye  man ya ganki ,  batare da wata gardama ba,ko bata lokaci ta Mike tsaye kmr yadda ummi tace .Amman still jikinta Bai bar kirma ba haka ma  hannuwata suna sarkafe  da juna tana cigaba da wasa dasu  ” yayinda ta cikin hijab dinta  kuwa uhmmmm tashin hankali kennan ‘dan kuwa  jikinta sharkaf yake  da gumi tsabar frigici datake ciki  ,duk da tsanyi AC dake aiki a  parlour hakan bai hana  gumi tsassafowa ilahirin jikinta  ba .

idanunshi da Suke a runtse ya kafeta dasu yana kallonta ,jin shr,n da yayi yawa ne yasa nablah dago fararen idanunta dan satar   kallon  mutumin dataji an Kira da suna DEENI . take zuciyoyinsu suka buga a lokaci daya …….
Yayinda  jikin nablah  ya dauki  kirma… zuciyarta ta sake amsawa daf..daf..daf.. ‘da sauri tayi kasa da idanunta ahankali ta furta  wayyo Allah na.. a kasan ranta.. mutun ko aljani nake Gani yau .

, tsabar kyauwu halitta  da Allah yayi masa .tunda take  a rayuwarta bata taba ganin mai tsananin kyau halitta  da kwar jinin irin mutumin da take gabansa tsaye a halin  yanzu haka ba .

kusan   tsawon  minti  5 ya dauka yana kallonta batare daya bude Idanunshi ba” sannan ‘ahankali ya dauke idanunsa daga gareta  yakoma ya  kwanta sosai acikin kujerar dayake “ummi  tace ya’akayi ne DEENI  naji kayi shr…  ….

Tayi…..
abinda kawai nablah ta iya  ji  kennan daga bakinsa , Dan gabadaya ma jitayi kunneta ya daina jin magana tsabar tsoro da rikici   hakan  km  sai lokacin hankalinta ya dawo gangar jikinta daga mummunar damuwar data tsinci kai  ciki …
Amman fa duk da Haka  a tsorace take da mutumin dake kwance a gabanta . +

,ummi kuwa ta furta kalmar alhamdulilllahi yafi Sau dari kafin daga baya ta kalli nablah  a tsanake sannan tace jeki nabla ma hadu gobe  kinji ..

,muryarta nablah a sarke tace to … sai da safenku sannan   ta juya  cikin tsanyi jiki  ahankali take tafiya yayinda itama   ummi  ta juyo tana sake bin bayan nablah din da  kallo har tabar parlour  zuciyarta na karanto mata abubuwa dayawa game da yarinyar ga wani irin tausayin yarinyar daya mamaye zuciya …

Bangaren   deeni kuwa gabadaya ji yayi tamkar am masa wanka ne da ruwan sanyi  , jikinsa ya mutu murus tamkar mara lfy haka ya dinga ji ajikinsa tun sanda yabi hannu ummi  da ido .

kwarai  yaso ya bude idanunshi yakarewa  yanayinta kallo Amman sam  yakasa aitawatar da hakan , sai ma tsintar kansa da yayi da mummunar faduwar gaba a lokacin da yake kallonta .
, wanda har yanzu dayake kwance a wajen  bai daina jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri  ba ..

‘ahankali yasake runtse idanunshi gam ko zai daina jin abinda yake ji  ajikinsa ,amman kwata kwata sabanin haka  Ya dinga  ji .
Sai ma  zuciyarsa da tacigaba da  harbawa da sauri da sauri .

abinda bai taba ji atare dashi ba kennan tun iya tsawon rayuwarsa wai faduwar gaba akan mace  ….
Macce ma , mai matsayin mai aiki …

ahankali ya furta sunan  da yaji umminsa  takira yarinyar dashi nab….lah… Yadda ba mai jinsa ….

muryar matarsa yaji tana cewa ummi   ai wannan yarinyar bakaramin  daga tuta tayi ba ,  tunda har my hrt yace tayi.

ummi  tace al,amarin Allah kennan nima gsky  naji dadi matuka da tamasa saboda daganin  yanayin yarinyar ba tmby akwai natsuwa atare daita .
kema kiyi kokarin ki sota a ranki ” ba mamaki wata rana tayi miki amfani .
dagani   bazamu samu matsalar daita ba   “, zeenat tayi murmushin karfin hali tare da kwabe baki   Dan ita   kwata kwata bata ji son yarinyar aranta ba   . tanaji a zuciyarta tamkar ta sallameta daga gidan ne yanzu yanzu …. 
+

Muryata Cike da takaici tace wani   amfani km  ummi .Allah yakiyaye wannan yarinyar tayi min amfani .
ni wlh Dan  bani da iko  ne.
tunda kince ta kwanta miki a rai .
wlh da tuni  korarta zanyi. Dan  Haka kawai nake jin tsanar yarinyar har cikin raina .

deeni dake kwance ya ja tsaki mai tsawo..Dan takaicin maganar Zeenat din  sannan ya Dan  juyo ya tsareta  da rikitattun idanunshi masu sata natsuwa a duk lokacin daya watsa mata su.

take tayi shr ta hadiye maganar ta  ,sannan   yace I don’t want to hear anything stupid here.
A Zafafe yacigaba magana haba kin cikamin kunne da shirme banzan ki .

sannan ya dan sausauta murya tunowa da yayi ummi  natare dasu ,cikin sanyi jiki ya juyo suka hada Ido da  ummi . itama shi ta zubawa  idanunta kawai .
Cikin sanyi ya kamo hannun ummi  cikin nasa  yana mai karkada mata kai  ‘ahankali yace am sorry…my first lov  .

take ummi taji wani irin sanyi a ranta  , gashi bata iya fushi da  tilon dan nata, Kuma bata son damuwarsa ,gara ace duk abinda zai same shi  ya tsaya  a kanta.

”  hannuta tasa ta dungure masa kai dashi ” tace kai dai kacika maseefa wlh ai barewa batayi gudu ba danta yakasa rarrafe like father like son ai lokacin aliy ….. ganin ummi zata soma tabo labarin  dad dinsa yasa yakatseta da hanzari muryarsa  cike da shagwaba yace please first lov ya nuna mata yatsansa alamu tabashi 1 minti  sannan  ya juya inda zeenat ke zaune ta kasa kunne, kallo daya yayi mata wanda yasa ta gane abinda yake nufi tun kafin yayi magana ta Mike tsaye ‘ahankali tabar gun.

hade da cewa maseefafe banza  kawai akasan ranta in maseefarka  ta motso kowa yashiga uku acikin gida.

sai da ya tabbatar da Zeenat tabar part din gabadaya sannan yace ok continue first lov  ummi  ta tabe bakinta sannan tace anki ayi continue din.
dan saboda za’a yi maganar dad dinka  shine ka koranmu yarinya.
A shagwabe  yace haba first lov a gabanta zakirinka jistin din abinda dad dina yayi ya girgiza kai impossible…. Ai zaki sa ta raina ni .
Ummi Tasaki murmushi ganin yadda ya hade rai kmr mai shirin kai gumurzu sannun gyenbo sarkin son girma aiki DEENI ya yamutsa fuska jin abinda ummi tace murmushi tayi  nan dai suka cigaba da hira su ta tsakanin uwa da “da” …..
+

Koda nablah  ta koma dakin daaka sauketa ciki ,key tayiwa kofar saboda tsaro ,sannan  ta cire hijab din jikinta   ta tsaya tana bin jikinta da kallo yadda  take ajike  jagab da gumi tana tsiyaya  ,dariya ce  ta kufce mata, ai kuwa tashiga yiwa kanta dariya ,sosai tayi dariya har da rike ciki  saboda tuno yadda ta koma kallar tausayi dazu a parlour.
,a hankali  ta zare kayan jikinta dayake doguwar riga ce “ta daura zaninta data zo dashi tashiga bathroom..

Byn tayi  wanka hade da dauro alwala ta fito , duk wani abu da yazama na aladarta kafin tayi bacci  sai datayi , tare da yin addu’oi tsari ta shafe jikinta dashi ta nemi waje akan gado tayi kwanciyata cike da kewar iyayeta da yan’uwanta ‘ahankali ta runtse idanunta tayi lamo akan gado wani tunanin ne  yazomata take taji gabanta yashiga faduwa. anya kuwa … banyi kuskuren cewa bazan koma gida ba  kuwa?  duk da  lokacin dana fadi hakan ummamu  kin  amincewa tayi  da hakan.
  ‘ahankali” ta sauke naunauyen ajiyar zuciya a filli ta furta  kai bazai yiwa ba wlh na canza shawara gwara  narinka zuwa gida time to time ina ganin yangidamu .
jin wannan shawara data bawa kanta ne  yasa taji wata natsuwa nasake bin jikinta ta  kudindine jikinta  waje daya a haka har barci mai nauyi yayi awon gaba da ni….
Can kuwa  bangaren  uwa da “da” ummi ce ke kokarin  mikewa tsaye  tace kai ni tashi kaje gun matarka Lada ya isa haka bacci nake ji  .
DEENI ya karyar da wuya yana duban agogon dake manne a bangon parlour sannan yace look at the Time first lov.  fast ten fa yanzu  muna hirarmu mai dadi  shine zaki koreni ko…  Cike da tsokanarsa ummi tace .. ni na isa na kor i farincikin rayuwata hasken duniyata hade ta karasa fadar haka tana kama bakinta. +

DEENI  ya tabe baki kawai batare da yace komai.. ok baka yarda  Kaine duniya ta ba.. murmushi gafen baki yayi tare  da kashe mata idonsa   daya” ai na dade da sanin  wannan .
Kmr yadda  nima  kece duniya first lov ….. sannan suka  Mike atare yace muje naraki .
har dakinta  yakaita ,ta juyo tana sake kallon dan nata Allah ya maka albarka yadda kakemin biyayya  kaima Ina rokon  Allah yabaka  masuyi maka fiyye da abinda kamin ina addu’a Allah yabani aron rai da lafiya naga jikokina wato yayanka….

  jikin deeni  na maseefa daukar  sanyi ” a duk sanda mahaifiyarsa taimasa wannan  addu’ar yakan tsinci kansa cikin tashin hankali.
,da yanada yadda zaiyi yasamu yaran dazasu  yasamarwa mahaifiyarsa   farinciki da tuni an wuce wajen .
batare da ya bari tayi nasa auren datake kokarin yi masa ba.

yana son kullun yaganta cikin farinciki  fiyye da wanda take ciki  a yanzu tana  tagama fadar haka, ta juya masa baya dan bata san ganin damuwarsa.
, cikin sarkewar murya tace  kaje abunka  ai burina  ya kusan cika ”  Allah yatashe mu lfy da kyar  ya iya  amsawa da Ameen sannan, ahankali ya juya ya bar dakin direct dakinsa ya wuce   ya zauna  akan kujerar da yake zama idan zai yi aiki a system dinshi tare da sa hannushi duka ya dafe  goshinsa  dasu .

yana matukar jajantawa kansa ” hakika  Allah  yabashi komai tare da wadatashi da abubuwan more  rayuwar duniya sai dai yarage shi da abu daya Wanda yakasa daurewa wato zubar masa da ya’ya da Zeenat ta dinga yi arariya  …..
‘Ahankali yasoma lumshe  rikitattun idanunshi Yana budesu sunnu Ahankali har ya rufesu luf… Sosai yayi zurfi cikin wata duniya ta daban .yayinda zuciyarsa  ke bugawa ,da sauri Wanda yarasa dalilin jin hakan. 
yana cikin wannan tunani ne bacci mai nauyi  yayi awon gaba dashi .
+

Sapanin bangaren Zeenat da” tunda ta kwanta akan makeken gadonta bacci ya kaurace daga idanunta” bbu abinda take tunani Sai mijinta.wanda tun tahowarta da tunaninsa take bacci take tashi 
” taso a daidai wannan lokacin tana tare dashi rungume  a saman fadadden kirjinsa mai cike da yalwan gashi  amman kashiii… ..
son zuciyarta da km kaddara data gitto  tasanyata zama cikin kadaici da kewar  mijinta.

‘Ahankali tasa hannu    ta rarumo pillow dake kusa daita “ta  rungume tsam akirjinta,tare da fatan samun saukin abinda take ji ,a tunaninta ko hakan datayi  zai ragewa zuciyarta damuwa akan rashin mijinta kusa daita. amman sam hakan yaki samuwa gareta.
‘ domin pillow kadai bazai taba .  maye mata gurbin dumin  jikin mijinta datayi missing ba.

Dan  yarigada yayiwa jikinta  “mugun sabo da zazzafar soyayyarsa mai cike dadi da kashe tsansar  jiki.

Uhm DEENI kennan daban yake   acikin maza Haka ma soyayyarsa .
ganin bacci ya kauracewa idanunta ne yasa, ta Mike da kyar tashiga bathroom ta dauro alwala, nafilar dare ta fara ‘da zumar samun sausauci a gurin ubgj  tare da rokon Allah Ya sake mallaka mata mijinta a tafin hannuta. ,

Hankalisa kwance yake shakar baccinsa tamkar Yana sama jannati.
Kyakkyawar budurwar ce take kusantoshi har inda yake kwance flat akan bed dinshi tare da sa hannuta,ta shafo kyakkyawar fuskarsa mai cike da suma da annuri.

‘ahankali yasoma  bude Idanunshi tare sauke kwaryar idanushi acikin nata , tsaye take kyam . tana sakar masa kayataccen murmushin daya bayyana wushiryarta.
  ‘ahankali ta Miko masa zarara yatsun hannuta masu matukar kyau da daukar hankali. tamkar  jira yake ya damki hannunta tare da fizgota saman daddaden kirjinsa mai cike da yalwar gashi ya rungumeta tsam tsam ajikinsa yana sakin numfashi shima Ahankali yakai bakinsa tsaitin wuyanta  Yana shinshina kamshin jikinta  .

cikin wani irin salo yasoma cire mata kayan jikinta, bata hanashi ba har yagama cire mata kayan jikinta tsab .
ta saura daga ita sai pent da bra Shima ‘ahankali ya zaresu yayi flinging dasu gefe  , breast dinta   masu matukar kyau “da daukar hankali suka bayyana sai sheki suke tsabar baiwar da Allah yayi musu .
tamkar wani mayyunwacin zaki   a gigice yasa hannuwansa duka ya damki  dukiyar fulaninta yasoma murzawa Ahankali Yana lumlumshe idanu, itama  kmr Jira take ta dinga narke  masa ajiki tana cire masa kayan jikinsa, habawa Ai  gabadaya deeni ya susuce ya fara romancing dinta cikin zafi zafi tare da hade bakinsu waje daya Yana tsotsa tamkar yasamu loly pop +

Cike da shauki ya birkito daita takoma kasa tare da zare mata  pent din dayayi saura ajikinta , sannan   yahaye saman   ruwan cikinta ” yasoma kokarin ware kafafuwanta kana ya   tsaita kan joystick dinsa cikin kofarta, Ahankali cikin wani irin salo   ya zira jijiyarsa ciki.

hankali kwance yasoma saduwa  daita Yana cikin kokarin yin  realize ne sautin . allahu Akbar lahu akbar …. kiran sallah da’ake kwallarawa daga masallaci dake cikin estate din ne ya farkawa dashi  a , afrigice ya farka tare da wata mummunar faduwar gaba ya Mike zaune  hannushi dafe da kirjinsa Yana waige waige acikin dakinsa.

Numfashi sama sama kawai ya dinga saki ” Tare da kallon ilahirin  jikinsa dake kirma… duk abinda ya farkar dashi daga baccinsa bai bashi mamaki ba facce  ganin  jijiyarsa’ da yayi a mike sambal… da km  yadda take harbawa da sauri yasa hankalinsa mugun  tashi.
  Gabadaya gangar jikinsa rawa yake zuciyarsa ce ke harbawar da sauri ,take ya   Daura  hannuwanshi duka  kan joystick dinsa ya dafe  .
wani irin azababen  shock yaji ajikinsa Wanda yasa jikinsa sake cigaba da kirma…
  , ‘ahankali ya dinga furta kalmar inna lillahi wa inna lillahi rajiun   akasan ranshi, ya jima zaune  yana maimaitawa  sannan ya samu sauki da natsuwa zuciya iya tunaninsa Bai san meyasa yin irin wannan mafarkin ba” haka nan km Bai kwanta da Sha,awar wata diya macce  a ranshi  ba ,hasali ma zuciyarsa cunkushe take da abubuwa da yawa kafin ya kwanta ,Sai dai ko daga Allah ne .
   Mike yayi Ahankali  yashige bathroom domin tsarkake kansa.
Byn yayi wanka tsarki ne  ya fito  tare da  dauro alwala yazo ya gabatar da raka’a taini fajir sannan ya wuce masjid . +

koda ya idar da sallah ma ya dade zaune Yana jimami da  mamakin mafarkin da yayi har ya dawo gida ,ya kwanta rigingine akan royal bed dinshi Bai daina jin sa some how ba .

8:00 

Daidai   Ya tashi .
duk ilahirin jikinsa  a sanyaye yashiga bathroom “wanka yayi ya fito yasoma shirin zuwa aiki .
Yana   gama shirinsa tsam cikin uniform din su na soldier .
,  ya nufi  part din first lov  domin   yaga yadda ta tashi dan ka,ida ne muddin  gari ya waye sai yasanya mahaifiyasa a idanunshi sannan yake fita .

da sallmar sa yashiga dakin  zaune  yasameta akan gado, tana ganinsa ta fadada fuskarta da murmushi ”  tasoma masa kirari kmr yadda tasaba”  kaga namijin uban mazaje namijin  duniya yaro in bakayi bani guri” sannu zaki maza,km   jarumina    matashi magidanci son kowa kin wanda yarasa.

“da” daya tilo ” da” daya  .
kafi Yaya dubu agurina ,sadauki ranka yadade ta dunkuleta hannuta tare da  jinjina masa  “

DEENI ya karkace  kai kawai yana kallon mahaifiyasa “yana sake jin yadda soyayyarta ke sake  ratsa kowani part na  jikinsa.

duk duniya bashi  da sama daita. itace duniyarsa  ,shiyake daita ,ita take da shi cikin takunsa na kasaita  yakaraso har  inda take   ya zauna kusa daita yana murmushin ,duk  wannan kiraki nawa ne   ni kadai first lov sannan yace  mun tashi lafiya .

,tana murmushi tace lafiya lau  dana , yakata shi kaima ?

,ya shagwabe  fuska  kmr wani karamin yaro yace lafiya Amman ba lau ba .

Ummi ta zaro idanu  tunaninta ko wani abu ne yana shi yin bacci .
  ,meyasa Meka ya kai dana ummi ta fadi hakan tana mai nazarinsa ” Ahankali ya shagwabe fuska byn tunaninki ne ya saka gaba ya hanani yin  bacci   ummi ta sake  zaro idanu tare da sakin  murmushi  irin na manya.

Aiko  ” tunanina    bai kyauta min ba wlh . 
  ” Har daya hanawa tilon dana samun natsuwa”

Deeni  yasake narke fuska yana duban umminsa , Allah first lov ki nemo shi  tunanin ki hukunta shi da kanki .

ta sake yin murmushi kusan koda yaushe agaban mahaifiyasa haka yake zama  tamkar wani jinjiri   , ummi numfasa sannanAuntyna tace  maza tashi kaje  nasan yanzu haka ko breakfast bakiyi  ba  kike shirin fita ?
A sukwane ya Mike tsaye yana duban ummi .
“mkr kinsani wlh  amman  daga  wajen yin break zan wuce office , ganin yana tsaye bashi da alamun tafiya  ne  yasa tasan abinda yake  Jira ,dan haka  tashiga yimasa addu’a tare da sake nuna masa mahimmanci Zeenat a gurinsa .
sannan  ya fice daga dakin  hade yi  mata sallama  ..
+

Koda ya bar part din first lov part din zeenat yashiga kwance ya tadda ita Tayi zurfi cikin duniyar tunani sannan    idanunta na kallon celling dakin da dukkannin alamun ma bata samu runtsawa ba .

‘Ahankali Yasa hannunshi  ya ja yatsun kafarta dashi ‘ a sanyaye ta kallosa  da idanunta tana may sauke  naunauyen ajiye zuciya sannan ta zuba masa kwayar idanunta cikin nasa hk  shima yake  kallon tare da   dan matsowa kusa da ita sosai  yana son  sake karantar yanayin  da take ciki .

haka kawai wani lokacin  yake tsintar kanshi da tausayawa mata   ,sbd yadda take maseefar sonshi da kishinsa.

daidai kunneta yakai bakinsa,  kana yayi kasa kasa da muryarsa yace  meke  damunki haka Zeenat …….? ‘Ahankali ta girgiza masa kanta ,alamun bbu komai, ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa .
saannan yace ok..to   meyya hanaki bacci?

Ahankali ta  juyo ta zuba masa kananun idanunta tana kallonsa dasu sosai take jin yadda  kaunarsa ke sake  taso mata tamkar zata huda mata zuciya , tare da mamaye mata dukkan sansanr jiki .
Sai data kalleshi son ranta sannan ta sauke numfashi ‘ahankali muryata a shagwaba tace kai ne da tunaninka ya hanani runtsawa.
ya runtse Idanunshi sannan Ya bude su  Dan sake dubanta  suka hada Ido dashi  ta lumshe masa  idanunta  tana sake tabbatar masa da iya gskyrta ta fada . +

yes ….  tunaninka ke damuwana yayinda kewarka ke  hanani ke hanani sukuni ballanantana na samu sararin ishashen bacci .

, ajiye zuciya ya sauke tare da  zama  gefen bed side dinta ,yakamo tafin hannuta cikinsa yana murzawa ahankali ‘ahankali .
  tsareta yayi  da rikitattun idanunshi yana kallon cikin kwayar idanunta .
  ‘ itama shi take kallo still  take ta dinga  jin wani iri iri ajikinta  . gabadaya tsigar jikinta suka Mike tsaye   yrrrrrrrrrrrrr……

   Bazato ba tsammani taji sautin muryarsa  meyasa kike son halaka kanki da tunani na Zeenat ? 

cike da damuwa yake magana , alhalin duk maseefar da tasameki kece silar jefa kanki  ciki.

kau da kanta tayi gefe window   ta  zubawa wajen idanu kuri batare da tasan abinda yakama tace ba .
  ” ganin da yayi hawaye ne keson zubo mata ,  yasa hannusa Yana juyo da fuskarta garesa  suna sake fuskarta juna.

yace karki soma barin hawayen nan  su zubo daga idanunki sbd bana bukatar ganinsu km basu na tmyeki ba  .
D karfin tsiya ta ciza lip’s dinta   tasoma kokarin mai da kukanta.

   inason  kin manta komai dangane da abinda ya faru baya kicanza new life  banason ganinki cikin wannan moon din “ko kinason  first lov  ta fuskanci wani abu na damunki   byn damuwar rashin  haihuwa da tasan itace  matsalar mu ,  ta girgiza kai   yace kiyi fatan samun wasu  ya’ya masu albarka  .
maganar dayayi mata kadai Ya taba tsantsar jikinta tare kwantar mata da  hankali.
Hannuwata dake cikin nashi  tasa ta matse tafin hannushi cikin tare da danne hawayenta , muryata a sarke tace Ina sonka dayawa  my heart….. ,meyasa kaima bazaka  soni tamkar yadda nake maka ba Ina son kasancewa tare da kai bana son yin nisa daika .

Uhmmmm  Zeenat kennan Ina sonki man abinda kika aikata gareni ne yasa soyayyarki takasa yin tasiri a zuciyarta  sannan kece kika hana wannan soyayya samu gurbi may mahimmanci,Amman dai… Sai km yayi shr  tare da   mikar da ita  tsaye   ya   mannata da gafen jikinsa yana shafa bayanta ‘ahankali ,  .
  dan yasan   duk randa basu kwana tare ba “bata samun  ishashin bacci ga tarin  tunanin rashin  haihuwa da take kwana yi wanda   duk ita  tajefa kanta cikin .
Ahankali Ya juyo daita suna facing juna  tare dadago habarta   ya zubawa  fuskarta eyes dinshi sannan  ya kai bakinsa kan nata ya tsotsan lip’s dinta yace I still care about you. +

  murmushin tasakar masa  Wanda ta jima batayi irinsa ba ,cikin jin dadi ta kamo tafin hannushi  muje kayi breakfast  .

am orready late Zeenat anajirana a office nebazan iya tsayawa cikin komai ba . uhmmmm nidai  please muje kaban ko 5 minutes na hada maka  ko  tea ne kaji.
ya karyar da kai kawai yana dubanta , atare suka jiro hannunsu sarkafe da juna har darning wanda daman komai  a kammale yake  ta zaunar da shi cikin sauri sauri ta hada mishi tea kurba uku yayi ya Mike tsaye , tasan yanzu tana sake yin wani complain .
sunanta sorry  a gurinsa Dan wannan kulawar  dataga daga gareshi tasan darajar addu’ar data kwana tana yi ne da km ummi dake tsaye a tsakaninsu har Bakin  kofar main falon din su takai shi ta Mika masa briefcase dinsa Dan bayarda da hakan sannan ta koma dakinta  …

Direban sa wanda shima soldier ne yataso da sauri yakarbi briefcase din hannunsa hade da Sara masa sannan  ya bude masa murfin  kofar.
,tun kafin karosowarsa  Bakin get din gidan securities ke Sara masa har aka bude get suka bar gidan .. 

Tunda ta tashi tayi sallar asuba take kwance takasa fita ko nan dacan   tana jiran kira  daga masu gidan Amman shr ga yuwa tasoma kmr me .
  Mikewa tayi jiki a sabule tashiga bayi wanka  tazo ta canza kaya tare da  zubawa sarautar Allah Ido can taji ana nouking dakin ahankali ta Mike  ta bude kofar ummi tagani tsaye ta dan  matsa taba hanya   tashigo dakin  sannan ta  gasheta cikin sakin fuska ummi  ta amsa tace nablah ya kwanan bakunta ?

Ta Dan yi murmushi tare da cewa  alhmd  ummi tace Masha Allah yanzu dai muje kiyi breakfast daga nan sai mamana ta nuna miki aikin da zaki rinkayi ummi  nagama fadar haka ta juya itama nablah tabi bayanta …

Falo uku  sama uku kasa uku banda dakuna wanda sunkusan goma acikin gidan , madam kmr yadda taji laraba  nakiranta da shi ita ke nuna mata  komai.
A yatsine  tace ki dauki gyaran sama kibarwa laraba  kasa  nablah tace mata  to dan batada zabi sai abinda tace ..
har falon magidan da dakin sa komai dai ataikaice sai da aka nunamata  Kuma tun a rana tasoma aikita hade da tattaro kayanta tadawo sama  kmr yadda ummi  tabata umarni .

Misalin karfe takwas dai dai na dare nablah ta kammala da komai na aikin gidan  har part din abinci wanda tare da madam muzeenat sukayi komai wai  tana son ta kware fannin abinci mai gida dan haka gabadaya  agajiye take  likis.

Tana shiga dakinta  kwanciya  tayi  bata dade ba bacci yayi gaba daita.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]