[Advertisements⬇️]

WANI AURE CHAPTER 18 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WANI AURE

CHAPTER 18
Cikin wani irin yanayi wanda kwata kwata ummi bata taba ganinsa ciki ba ya mike tsaye
tamkar may koyan magana ya bude bakinsa yanawa ummi sallama.
“firt lov ni zan wuce gida yasoma taku cikin isa da kasaita don barin dakin.
,cikin sanyi murya ummi takira sunanshi DEENI… Dan tsayawa yayi Tare da juyowa suna
fuskarta juna da ummi idanunta ta xuba mishi kawai Tana kallonsa tare nazarinsa ganin
yadda gabadaya yanayinsa ya sake sauyawa cikin Dan kankanin lokaci.
Yasa tace Ka tsaya kaci abinci Dan da alamun kana tattare da wunya,inyaso zuwa anjima
Sai ka wuce gida ko..shr kawai yayi yana kallon umminsa.
hakika umminsa tafi kowa sanin koshi waye Ta fannin halayyarsa da abinda ke tattare
dashi.
Sai dai ,shi sam baiji zai iya sawa cikinsa komai a halin dayake ciki damuwarsa dayake
tattare dashi , kadai ya ishe sa” ba Sai yaci wani abu , yafison yaje gida kawai domin yana
bukatar sake nazari akan maganarsa da ummi.
Dan haka ya Dan narkar da fuskarsa alamun baya da bukatar cin wani abu .
“bata rai ummi tayi ganin yadda yayi ,sannan ta Mike tsaye ta nufi hanyar kitchen .
kabani nan da minti goma yanzu, zan gama hada maka abinda zakaci kaji sojana ta fadi
haka tana karasa shiga kitchen.
yasan halin ummi sarai tamkar wuyan cikinsa muddin tace Ga abinda take so ,to kuwa
bata muradin mutsu ko wani jayyaya ” Dan haka jikinsa a sanyaye ya juya zuwa ga hanyar
step
‘Ahankali yashiga dakinsa” tsit ko Ina ba motsin komai “inda sabo ya rigada yasaba da
rashin son hayaniya. daman shi mutun ne .
“ba mai san hayani ba ballanantana kma part dinsa” komai yana nan tsab kmryadda Ya
bari tamkar yana rayuwa a cikin dakin “wanda yasan wannan duk cikin kulawar
umminsa ne sbd macce mai tsananin tsafta da kyankyami.
“kai tsaye bedroom dinsa ya wuce yasoma cire kayan jikinsa yaja towel ya daura Tare da
shigewa bathroom ya sakarwa jikinsa shower yana fitowa Bai wani tsaya shafa mai ba.
ya bude wordrob dinsa.
nan ma komai tsabtsab iske komai Sai kamshi turarensa dake tashi a gurin , wani irin
sanyi da dadi yaji a ransa.
” take kadan daga cikin damuwar dake tattare dashi ta ragu .
‘ahankali yasa hannu ya zaro jallabiya coffee colour ya zira a jikinsa ba karamin kyau ta
maisa ba.
fitowa yayi daga dakin nasa ya wuce kai tsaye ainihin main parlour din gidan ,ummi ya iske
zaune ita da Zeenat suna magana kasa kasa.
“duk da Bai san abinda suke Tautaunawa ba,amman jikinsa yabashi maganar shi suke
yi
Dan haka “kallo daya yayi musu ya dauke idanushin akansu’ batare da yace komai ba
direct to dinning area ya wuce , yana jin yadda kamshi abinci ke tashi ta koina a gurin da
dukkanin alamun umminsa tagama shirya masa abinci kmr yadda tace.
ya zauna ba dan yana bukace da son cin wani abu ba Sai Dan faranta ran umminsa.
shr yayi Tare da runtse idanushin yayinda zuciyarsa ke bugawa da sauri da sauri ‘ahankali
ya kamo lip’s dinshi na kasa yana dan cizawa sannu sannu.
Maganar da Ummi keyi da Zeenat kuwa, bawata magana bace, illa fada da take sake yi
mata akan abinda tayi Tare da bata shawarar hanyoyin da zatabi gurin shawo kan mijinta
cikin sauki.
,sosai jikin Zeenat din yayi sanyi likis..
ita kanta tasan” inda ummi bata kasance er,uwa,ce Ga mahaifiyarta ba ,hakika yaci ace
yadda Ta zubar da cikin jikinta ummi tasa danta yakarasa tsinke igiyoyi aurensa akanta.
amman Sai gashi hakan bata faru ba.
Sai ma nusar daita da take akan yadda zata sake mallakarsa a tafin hannuta.
Ummi dabance acikin mutane km zuciyarta may kyau ce ba kmr ta irin sauran mutane ba
km Allah yayi ta may tsananin zumunci ce.
ummi takarasa zanceta ” da maza tashi kije ki kula da mijinki.
“km cire wannan tsoron nasa danake hangowa acikin kwayar idanuki.
Da kyar Zeenat tasamu ta mike Tana may dagawa Ummi kai alamun taji.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Kusan minti goma yayi zaune a dinning table batare da yasan takamaimai akan abinda
suke zantawa akai ba.
Ganin yadda umminsa tabar shi gurin zaune tamkar wanda bashida aikin yi ,yasa ransa
yasoma sosowa.
yana ji a ransa da zai iya zubawa kanshi abincin, dayayi yaci yakama gabansa Dan kwata
kwata baya kaunar abinda zai sashi zama inuwa daya da Zeenat.
cikin haka ya jiyo takun alamun ana tahowa dinning wanda ya tabbatar kansa ba
umminsa bace.
Zeenat ke tahowa garesa Dan yasan takun kowanne daga cikinsu cikin sanyi jiki takaraso
har inda yake gabanta na wani irin mugun faduwa. tarasa dalilin wannan maseefar da duk
sanda zataga wannan yanayin na DEENI zuciyarta ke tsinkewa ,jarumta ta arowa ta
mannawajikinta cikin dakiya tasoma kokarin xuba masa abincin.
shinkafa ce da miyar parpeso na cat frish datasha kayan hadi take kamshin abincin ya
sake tasiri a hancinsa.
Sai data hada masa Komai yadda yakamata sannan tayi rolling din table din , plate din
abinci ya tsaya a gabansa ,har zatabar gurin sbd bazata iya jurar tsayuwa kusa dashi ba
tsabar tsoronsa datake ji karaf suka hada ido da ummi” ta harareta tare da yi mata alamun
ta zauna ,Dan haka ta samu guri ta zauna cikin kujerun dake zagaye da dinning table din.
ganin haka yasa deeni sake tamke fuska tamau tare da jin wani irin matsanancin
haushita ‘ahankali yasoma bude rikitattun idanushin suka kan abinci dake gabansa.
Cike da mazantaka ya soma cin abincin da Bai yi niyar ci ba, loma biyu yayi zuwa uku ya
Ture plate din, Dan kwata kwata baya jin zai iya cin wani abinci may yawa. Dan baya jin
dadinjikinsa gabadaya ma wani irin beting zuciyarsa ke masa wanda yarasa dalilin jin
haka, damuwar dake tattare dashi daban ce yayinda wannan yanayin bugun zuciyarsa
yake daban.
Bangaren Ummi kuwa addu’ar take tayiwa yaran nata ,akan Allah ya daidaita tsakaninsu.
jiki babu kwari ya mike, still Bai kalli inda Zeenat din take zaune ba.
ita kuwa Zeenat kanta na sunkuye a kasa takasa kwakwaran motsi gurin da ummi ke zaune
yakaraso ,fuskar nan tasa tamke kmr hadari bbu walwala acikinta.
muryarsa a dake yace first love ni zan wuce yanzu kam ,ummi ta dago Tana kallon yadda
yaron nata ya hade rai Ga wata uwar rama da yayi. sosai take nazarinsa sai ma taga
alamun knr zazzabi ne a tare dashi.
,deeni byn damuwar dake damunka akwai wani abu ne dake damunka ?
DEENI Yace, bbu komai first love.
amman sai naga kmr baka da lfy ?
Sai daya dan yatsina fuska tukun ya amsa da uhm kaina ke dan min ciwo, amman karki
damu dazarar na koma gida zan dawo normal,I won’t rest,
Ummi ta girgiza masa kanta Tare da Dan murmusawa.
bata bukatar yatafi gidansa cikin wannan yanayin dayake ciki.
“tafin son yadawo da farinkinsa kmr yadda yake a da.
, duk da, ada din ma Ba wai ya kasance may yawan fara’a bane, amman yafi wannan
lokacin.
Tace ” kaje part dinka ganin zuwa yanzu ya shagwabe fuska kmr wani karamin yaro Yace
uhmmmm first love ni gida nake son zuwa ina bukatar na huta.
km akwai aikin dazanyi .
,ummi ta sake murmusawa tare da cewa NO… my Son bbu inda zaka yau muna nan Tare.
‘Sai naga wannan kyakkyawan fuskar wannan zakin ta koma tamkar ta cikakken mutun,
murmurshi ne ya Dan bayyana a saman fuskasa ,har dimple dinsa ya lotsa “hakan ko yayi
wa ummi dadi Sosai har ta sake yin murmurshi ,haba ko kai kaifa kayi fuska kmr kana filin
daga ,haba sadaukina ka kara Dan sakin fuskar nan taka ma ,nafi son ganinta kunshe da
farinciki ta fadi haka Tana dariya ,duk abinda ke faruwa a tsakanin deeni da ummi Zeenat
na zaune a dinning area Tana jinsu, wani irin filling ne na dabam ta dinga jishin a zuciyarta
Ta zuba musu ldanu kawai Tana kallonsu” ba tun yanzu suke birgeta ba, hakika soyayyar
dake tsakanin uwa da “danta”daban ce km akawai banbanci da Sosai da sauran soyayya.
Deeni ya Dan langwabar da kansa Tare da cewa ni yanxu first love wani farinciki zanyi km
byn angama ruguzamin rayuwa.
kayi farinciki yarona duniyar nan tamu, Tana da fadi dayawa.
km zaka iya samu farinciki, acikinta fiyye da wanda kayi missing, kai dai kaje dakinka gani
nan zuwa bazan taba barinka ka tafi da wannan , zazzabin danake Gani acikin kwayar
idanunka ba.
nasanka sarai da rashin kula da son shan maganin.
Tana gama fadar ta wuce tabar shi nan tsaye yana kallonta.
, agaskiya baya son abinda umminsa ke kokarin son yi masa ,amman baya da zabin da
wuce dole yayin abinda tace domin baya son damuwar farincikinta shine nashi.
Dan haka ya juya ya km koma part dinsa yana may jin wani irin matsanancin bugun
zuciya kirjinsa dake masa zafi ya dafe tare da zama kan bed ya dan jingin bayansa da
bayan gado.
Bai fi minti biyar da shigowa dakin ba Sai Ga ummi tashigo da sallamar ita da Zeenat
hannuta rike da ruwa da magani ganinta Tare da Zeenat din ne yasa ya amsa sallamar da
Ummi tayi a ciki.
Tare da kauda kansa gefe yana kallon wani gefe ,ummi tasamu guri kusa dashi ta zauna ita
km Zeenat ta zauna daga gefe akan bedside.
, Zeenat na kallon ummi Tana gutsitsira maganin hannuta tamkar dai yadda akeyi wa yara
kanana wanda ba tun yau tasaba ganin hakan a gurin ummi ba, a Duk lokacin da deeni
bashi da Ify haka Ummi take masa kasancewarsa baya son shan magani.
ummi ta Mika masa maganin byn tagama gutsitsira wa sannan ta bashi ruwa ‘Sai datayi da
gaske da rarrashinsa sannan tasamu yasha maganin har abun yakusan bawa Zeenat
dariya yadda Ya dinga yi amman bbu dama yi.
Muryata A sanyaye tace sannu my hrt..ya jiki naka.
DEENI yayi mata banza tamkar bada shi take ba Sai ma
Zamo da yayi kadan ya dora kansa akan cinyar umminsa Tare da sake tamke fuskar .
Zeenat ta mike ta dauko blanket ta rufe mishi Rabin jikinsa dashi ,a ranshi yaja tsaki Tare
da cewa aiki banza kawai to bangode ba.
A hankali ummi ke mishi hirarraki masu dadi dasaka mutun cikin nishadi da walwala.
, ahankali ya dingajin yanayinsa na sauyawa daga damuwa zuwa birbishin farinciki
yayinda sanyi ke rasa kowace gaba ta jikinsa da ilahirin jikinsa har zuwa sanda yaji
ummi take cewa, acikin gidan nan aliyu da fadeela sukayi rayuwarsu may tattare da tarihi
da jin dadi wanda bazaso taba goguwa ba.
Tare da wani kyakkyawan terribby may matukar kyawun gaske da daukar hankali wanda
ke sakasu tsantsar farinciki da walwala a Duk sanda suka daura idanunsu akan wannan
kyakkyawan bby. farincikinsu baya misaltuwa.
,deeni najin haka ya sauke ajiyar zuciya domin ya rigada ya gane shine wannan
kyakkyawan terribby din da umminsa ke nufi.
“nasurudeen… Ummi takira sunanshi cike da tsantsar kulawa ya dago rikitattun
idanunshi yana kallon mahaifiyarsa, Tare da dage mata girarsa daya batare da Yace komai
,ummi tayi murmurshi sannan tacigaba’ kai kadai Allah ya azurtani ni da samu a rayuwa
byn tarin shekarun danayi da aure batare da nasamu haihuwa da wuri ba.
, dukkan wata soyayya da uwa kadai ce takewa , danta Ina may tabbatar maka ni uminka
ina maka fiyye dashi ,Ina maka sonka fiyye da komai dake cikin duniyar nan.
kai ne duniyata kai kadai da Allah ya barmu ,ka ishe rayuwar duniya, alhamdulilahi
kana min abubuwa dayawa fiyye da abinda ya’ya dubu zasuyiwa iyayensu.
, wani farinciki ya ne ziyarce zuciyar DEENI” har ya sake gyra kansa kan cinyar umminsa
yana dubanta da kyau shi kansa ya tabbatar da irin kaunar umminsa garesa.
,ummi ta kai hannuta ta shafi sumar kansa.
, Tana may jin kaunar tilon Dan nata sosai a ranta.
, deeni kaga Zeenat Sai lokacin, ma ya wani tuna da wata aba wai Zeenat Dan shi gabadaya
ya manta da Tana dakin ma.
, Ummi tace karo na karshe da zan km baka hakuri akanta.
a matsayin na uwa a gareka Ina son ka manta da Duk wani abu dayashiga tsakaninku
daita , ku koma shirya tamkar da ,ku runkugume junanku ku , zauna Ify shine farinciki na .
kuudin mafi kusancin yan, uwan juna ne ,banason sake jin komai atsakaninku baya Ga
alkhari, abinda ya faru ya rigada ya faru kum Ina bukatar wucewarsa har duniya ta nade.
idan har kana son farincikina da kwanciyar hankalina kmr yadda kasha fada to kabar zance
,sabanin haka tashin hankali kawai zaka jefani aciki .
domin nasan sanka nasan halinka da taurin kai tsiya da zuciya.
ummi takarasa maganata Tana may zubda kwalla a afrigice DEENI ya mike zaune daga
kwanciyar da yayi tare tari hanwayen da hannuwanshi duka hankalinsa a tashe yace haba
firt lov meyyyyyyy kuma kuka… Dan girman Allah kiyi hakuri ki rufamin asiri zubda
hawayenki maseefa ce a tare dani ,da hannushi ya dinga goge mata hawayen idanunta.
muryarsa a sarke ya sake cewa first love kiyi hakuri Dan abinda ya faru ya wuce amman
may tsayawa ne rai manta da wahala km shi Sai ‘ahankali komai zai goge a memory dina
amman inshallahu zanyi kokarin naga komai wuce.
amman itama kiyi mata magana Dan wlh bazan dauki kalar iskanci zubda ciki ba, Dan
bazai yiwu Ina shan walaha ana zubar min da cikina ba.
,ummi tayi murmurshi Tana may dungure masa kai.
yanzu ni kake gayama haka DEENI..
sbd baka kunya ko.. ya kashewa ummi idonsa daya.. Allah first love ba rashin kunya bane
gsky ce kawai nafada.
aiko ummi ta dinga dariya Tana wlh DEENI karaina ni dayawa ko..idan baji kunyata ta
matsayina na umminka ba.
Ai kaji kunyata ta matsayina na surukarka shi ma murmurshi yayi tamkar bashi ba hankali
ummi takamo tafin hannun DEENI da Zeenat ta hadesu guri daya ta mayar rufe
hannuwansa sannan ta mike tsaye ta fice daga dakin gabadaya Tare da rufo masu kofa.
Byn fitar ummi DEENI zaune rike da hannun yakasa cire hannunshi daga gareta sannan
yakasa cewa komai tunani yake kawai ta yadda zai cigaba da zama da zeenat zuciyarsa ke
bashi shawarar hakura Zeenat kawai ya zauna daita dai dai ya auri kaskantacciya km
maragalihu kmr yadda ummi tace yayinda wani bangare na zucitarsa ke bashi karfin
gwiwar gara kawai yayi aure koma wace iri ce jin saukar hawayenta a hannushi ne yasashi
saurin dawo daga duniyar tunani daya Lula.
‘ahankali yaja numfashi yana fesarwa tare sakin aijiye sannan ‘ahankali ya zare hannushi
daga cikin nata, yasoma yunkurin mikewa, yaji ta sake riko hannu gam cikin nata Tana
murzawa dole tasa shi ya koma ya zauna yana dubanta.
Sai lokacin ya lura da muguwar ramar datayi.
Ya tsareta da idanunshi ganin yadda take son cika masa kunne da kuka .
Duk ke kika jawo matsalar nan km inshallahu akanki zata Kare ya fadi haka, a kasan rashi.
Sautin muryata yajiyo kasa kasa Tana bashi hakuri my hrt Dan Allah kayi hakuri da abinda
ya faru wlh bazan sake ba.
hannushi ya sake zare ,tare da katseta da hannunshi “shi.. ki rike hakuriki ko zai miki
amfani a wani guri Dan bashi da wani amfani agareni
maganar zaki sake ko bazaki sake ba Shima ba matsalata bane haka km wannan bazan
,my hrt ko me..me… Da kike kirana dashi ,Shima bana son jinsa Dan bana bukata sbd ni ba
zuciyar ki bane.
,inda kin bani matsayina haka a zuciyarki kmr yadda kike fada.
,dabaki min muguntar da kike min ba yamike tsaye cikin sanyi jiki yashige bathroom ya
dauro alwala sallah magariba sbd yasoma kin kiraye kirayen sallah a masallaci dake cikin
gidan baifi minti 3 ba ya sake fitowa yazo ya tadda sallah.
Tana nan zaune tamkar wacce aka dasa,har ya idar da sallah ya zare jallabiyar jikinsa ya
saura daga shi Sai short niker ya kwanta a kan bed dinshi.
yaja blanket ya lullube rabbi jikinsa ,tare da juya mata baya.
tsawon lokacin Tana zaune a gurin batare tasan yadda zatayi ba har sanda tasoma jiyo
Kira sallahr ishai ” sannan ta samu ta yunkura ta mike tashiga bathroom itama tayo alwala
tazo ta hada magariba da isha’i Dan tuni jininta ya tsaya ,Shima ‘ahankali ya km. mikewa ya
gabatar da sallah ya km koma yayi kwanciyasa ‘ahankali yasoma runtse idanushin
sakamakon baccin daya dayasoma kawo masa xiyara yaji motsin mutun kwance abayansa
******
Kwanciya Tayi a bayansa… byn ta cire ilahirin kayan jikinta lamo tayi Tana shakar
dadeden kamshin jikinsa.
Lafewa tayi Sosai ajikinsa tamkar wata bby’ Tare da goga masa kirjinta a bayansa wani
irin shork… yaji a jikinsa tamkar an jona masa wutar electric yayinda sha”awarsa tasoma
motsawa ‘ahankali ‘ahankali shr yayi kmr yana bacci batare da yayi wani kwakwaran
motsi ba balanantana tagane ko yaji wani abu dangane daita ,ikin kwarewa da yadda
ya sabarmata wasannisa tasoma shafa kwantaccen gashin kirjinsa may matukar taushi,
zuwa kan nipply dinsa” still shr ne ya sake biyowa baya .zuwa yanzu koina aijikinsa kirma
yake yayinda zuciyarsa take dokawa da sauri da sauri. “gabadaya gabobin jikinsa sun
sauya sun fara amsar sakonninta har wani shake jikinsa yasoma.
“ganin haka yasa zeenat tayo kasa da hannu daidai kasan mararsa, nan ne fa yaji bazai iya
barinta taci galaba akansa ba” caraf ya cafke hannuta hade da zabura ya Mike zaune
tamkar wani zaki.
itama mikewa Tayi ta zauna ,kmr yadda yayi. tsareta yayi da rikitattun idanunshi masu
matukar kyau da tsoratawa.
take tsoron yanayin yadda yake kallonta ya mamaye zuciyarta. wanda tasan wannan
kallon da yake mata na gargadi ne.
Amman tabarsa Tayi tamkar batasan abinda hakan yake nufi ba.
dan haka ta soma kokarin sake matsowa zuwa gareshi.
a tsawace ya dakatar daita ,da hannunshi tare da daka mata wata irin razananniyar tsawa
,data frigita zuciyar zeenat har ta sata , mannewa da jikin gadon dakin batare da san Tayi
hakan ba.
“kallonshi take da bayyananen tsoro a saman fuskarta,take ya hadiye duk wani emotion
din dayake ji a gangar jikinsa.
Fuskashi bbu walwala Ya sauke idanunshi cikin nata Yana may nunata da dan yatsansa
ke…banaso iskanci da rainin wayo,ko ance miki ni Dan iskane da bansan ciwon kaina ba
da abinda nakeyi wato Gani jarabbabe ko?
kin wani kwaso jiki kina manne min” to jarabar tawa bata may dani Dan iska da bansan
abinda nakeyi ba.
Kin ma rainawa kanki hankali wlh Gani stupid na dinga miki ciki ke km kina yawon
zubarwa ko.
,to wlh baki isa ba ,bari ma kiji wannan shine zai zama last warning din da zan miki.. kar
ki sake na km ganin kafarki a ,inda nake matsawar bani ne da kaina na bukaci hakan ba.
Bansan meyasa mu tunani ba da har na amince na zabeki
Amatsayin abokiyar rayuwata ba.
da ko zuciyata kin isa ki hango ballanantana har ki samu waje a cikinta da damar zubar min
jinina
da
Ke.. koda kuwa mun koma gida ne bance kizo gareni ba ,kije ki rike mahaifarki. ni km
na rike joystick dina da Spam dina yakarasa maganar….. oya out from this room before
now Ifinished you..Ya nuna mata hanyar fita da yatsanshi daya.
Hannu zeenat ta daura aka Tare da sabon tashin hankali ,inna lillahi wa inna ilaihi rajiun
kawai take ambata akasan ranta wanna wacce irin maseefa ce tajefa kanta da mijinta ciki.
Gabadaya tashin hankali datake ciki ya hanata Ko gezau ballanantana Tayi yunkurin
mikewa daga inda take zaune.
magana take son yi Amman Sam takasa furta kodaidai da kalma daya ce, numfashi kawai
take ja ta bakinta Tana fitar dashi da kyar. al’amarin nasa yasoma girman tunaninta. Sai
da taji ya sake buga mata wata razananniyar tsawa.sannan ta mike tsaye da sauri jikinta
na kirma ta rarumo hijab dinta dake yashe a gefen gado tasoma kokarin zirawa ajikinta
sannan ta kwashi sauran kayanta a hannu taja ta tsaya tana kallon yadda gabadaya
yanayinsa ya sake canzawa ,ganin taki tafi ne yasa DEENI tattaro sauran kuzariinsa da yayi
saura ya mike yakamo hannuta yana janta. mamaki da tsoro suka taru suka hanata cewa
komai ,Sai ma binshi datake,har yakai bakin kofa ya bude Tare da hankata waje ya maida
kofarsa ya rufe da karfi…,Banda bangon data dafe da hannunta bbu abinda zai hanata
buguwa da bango.
wasu Hawaye ne masu dumi da ciwo suka zubo mata tasa bayan hannuta Tana gogewa
yayinda wasu ke sake bin kuncinta.
A galabaice ya fada kan bed dinshi ya kwanta Tare da’ runtse idanushin gam. ‘Ahankali
yaja laulausar bargo ya lullube jikinsa. wani irin tsuma jikinsa keyi tamkar zaki Ga sandar
girma sai Mikewa take alamun Tana bukatar abincin ta tsaki yaja mtssss tare dasa duka
hannunshi ya dafe saman joystick dinsa yana may sake jan tsaki akasan ranshi mt..
Daidai tsakanin bakin kofar dakinsa ta tsaya tana maida kayan jikinta Sai data tabbatar da
natsuwarta ta dawo gangar jikinta sannan ta nufi hanyar dakin ummi sbd kwata kwata
bata son ummi tadago wani abu a tattare daita
Koda tashiga dakin ma ummi “zaune ta ummi ta idar da sallah isha’i Tana lazimi.
,ummi ta dubeta Tana mata kallon tsab ,batare da Tayi magana ba,cike da natsuwa
tacigaba’da abinda take yayinda zeenat ta haye saman gadon ummi Tayi kwanciyarta
lamo tare kamkame jikinta wani irin kewar mijinta ce ke damunta, kuka take son yi
Amman bbu dama,damuwarta zata iya shafar ummi.
a dalilinta ummi zata iya muzgunawa DEENI, ita km abinda bazata so ba kennan, batasan
abinda zai sake hassalashi akanta wani irin matsanancin son take masa wanda batasan
tun lokacin data fara ba.
” yanzu ita Yaya zatayi da rayuwarta mayye rudeta da sha,awa cikin zubda ciki ,take
zuciyarta Ta bata amsa da rashin hakuri da godiyar Allah ne yasa kika aikata kuskure may
muni kin zubar da ya’ ya da bakisa ba ko iya rabon ki kennan a duniya .a boye take goge
Hawayen dake bin kuncinta ,har ummi tagama laziminta da sauran addu’o,inta.
bacci baiyi nasarar daukarta ba.
“Tana jin motsin mikewar ummi ta shanye kukanta Tare da goge Hawayen idanunta
Amman hakan Bai hana ummi gane wani abu ,daidai inda take kwance ummi tazo ta
zauna tare da kamo hannuta ,me kike tunanin km mamana ?
Kafin zeenat tace wani abu ummi ta km jiho mata wata tmbyr
Sai ma naga kmr kuka kika yi ko?
Zeenat ta Mike zaune suna fuskartan juna da ummi ,yayinda hawayen dake makalea
idanunta suka yi nasarar zubowa sharr..mayye km abin kuka tmbyrki kawai nayi
Sai km ki kama min kuka.
menene yake damunki ko wani abu shi DEENI din yayi miki ,ahankali take girgirwa ummi
kanta da kyar ta iya bude bakinta…Ummi na cuci kaina da kaina na ruguza rayuwar gidana
da kaina bansan yadda zanyi abubuwa su dawo min daidai tamkar da ba. basani ba a she
rayuwa bata da tabbas bansa abinda na aikata zai sa na tsinci kaina cikin ,kaka nakanyi ba.
inda abubuwa dake faruwa suka cigaba bana tunanin zuciyata dake kirjina zata cigaba da
bugawa ,ummi kiyi hakuri ban miki adalci ba arayuwa, duk tarin laifin dana aikata gareki
baki gujeni ba ko canza min takarasa fadar haka tana zubda kwalla.
Ummi ta rungumeta ajikinta tana may tausaya mata, kukan ta, isa haka abinda ya faru ya
wuce ki daina dawo da hannun agogo baya matsawar Ina raye ba zaki taba kasance cikin
bakin ba, ke din diyata ce, Ina kallonki tamkar fareeda Yar, uwata, ganinki tamkar
madadince a gurina abinda kika aikata kuskure ne ,km ya wuce tunda kinyi nadama
,Shima son zai sauko ,kinsa halin bakar zuciya irin tasa ,dan haka ki samu nutsuwa km kiyi
hakuri da duk wani abinda zai nuna miki kinji diyarta Sosai ummi ta dinga rararshinta.
tana anan jikin ummi har tasoma gyangyadi sannan ummi ta dan bubuga bayanta kwanta
kiyi bacci ,kinji , ummi ta Mike itama samu guri nan kusa da zeenat ta kwanta…
Abu kmr wasa Sai dasu zeenat suka share
Kwana biyu agidan ummi baTare da sun koma gidansu ba.
,kullun dare sai zeenat ta shirya takai kanta Ga DEENI Dan kar ummi tagane basu shirya ba
Amman yadda take zuwa” haka take dawo da full gargadinsa may karfi.
ummi tasa a soma nemo mata masu aiki kafin zeenat ta koma gidanta .
A cikin kwana,n a ukun ne suka tattara suka koma gidansu har ummin kmr yadda Ta fada
Kwana uku kennan da dawowar zeenat gidan DEENI. bbu laifi al’amura sun Dan canja
kadan kasancewar ummi dake tsakaninsu.
addu’a dai ummi take sake yi kan Allah daidaita tsakaninsu yasa zaman Ify yaci gaba da
wanzuwa fiyye da hakan har karshen rayuwarsu.
Kmr yau zeenat tun safe take aikace aikace gyaran cikin gidan, aiki kawai take kmr wacce
Tasha kwaya domin koina yayi kura tunda tadawo kullum Sai tayi gyara ,shr,n da ummi
taji yayi yawa ne yasa ta fitowa zuwa kitchen din a lokacin kuwa zeenat Tayi busy gurin
aiki.
Ummi tace wai har yanzu baki gama aikin bane?
Tun asuba dakika sauko ban sake jin duriyarki ba ki bar aikin nan haka man zeenat ki huta
tunda muka dawo kike fama da aiki ki bar shi haka,gobe ne za’a kawo miki masu aiki
nayiwa hajiya turai magana km ta tabbatar min da gobe goben nan za’tasa akawo.
,hajiya turai aminyace Ga ummi, sun dade Tare tun farkon zuwan Ummi Nigeria suka
sanadin mazajensu.
zeenat ta girgiza kai kawai ummi gara dai nasoma rage aikin nan kafin akawo masu aikin.
kinsa bbu abinda ya ya yafi tsana a rayuwa shi sama da kazanta,ummi Tayi murmushi
jin dadi to ai shikennan Allah yabada sa’a Amman kibari ki dan hutu haka. naga ko karya
bakiyi ba,ai yanzu nan zankarasa nama, Kusan gamawa.
,mamaki yacika ummi ganin irin aikin da zeenat din Tayi parlour ta koma abunta ta
zauna tare da kunna TV tana kallo zeeyword daga nan inda take zaune suke hira da
zeenat din ,kafin wani lokaci zeenat taci Rabin aikin gidan
Koda dare yayi ma zagewa Tayi, tashiga kitchen tashiryawa ogo DEENI lafiyayen abinci da
Miya kala biyu, farar shikafa ce da miyar pepesoup din kayan ciki ,sannan da miyar
pepesoup din freshe fish dataji kayan gadi sai kamshin ke tashi.
sannan Taje ta shirya komai tsaf tsaf a dinning ita km taje ta sheka wanka ta hade cikin
daguwar rigar material datasha stone work Sai kalli take zuwa Ga wani kamshi na
musamman dake tashi ajikinta karku manta zeenat akwai son kwalliya km taiya
musamman kit gareta na kayan kwalliya , ahankali take saukowa zuwa parlour kasa tayi
maseefar kyau dauu..sai kyali take kusa da Ummi samu guri ta zauna Sai dai idanunta na
kallon tsaitin kofar shigowa ne ummi ta kalleta tana murmushi kai Kai manana kinyi kyau
yau DEENI bazai ganeki ba zeenat tayi murmushi kai ummi har wani kyau nayi.
sallamarshi suka jiyo ciki ciki yashigo cikin parlour, kunnenshi makale da waya yana
magana, da saurinta ta Mike ta tarbeshi Tare da karbar briefcase din hannunsa Bai
hanata ba sakamakon idanun umminsa dake kansu Amman suna hawa upstairs daidai
bakin kofar dakinsa taja ta tsaya cak dan gudun tashiga dakinsa yayi mata maseefarsa.
Ahankali yasa hannushi ya amshi jakarsa dake rike a hannuta ya shige dakinsa yabarta
nan tsaye.
Byn kmr minti talatin ya sauko jikinsa sanye da Riga blue shirt da wando jeans
threeecutter Sai kamshin turaren Hamilton Ontario ne yake tashi ajikinsa, kai tsaye
dinning area ya nufa inda ya hangi umminsa zaune da alamun zaman jiran fitowarsa suke
ahankali yakaraso gurin tare da samu guri ya zauna yana gaishe da umminsa ta amsa
cikin sakin fuskar da kulawa ya aikin alhamdulillahi ya cire wayarsa yana operating
ahankali zeenat tayi wani irin Mikewa wanda yasa gabadaya santsar jikinta girgizawa
most especial kirjinta dayake suna kusa da juna ,dagowa yayi da niyar sauke mata ruwan
bala’i idanunshi yaci karo da kirjinta .. kallo daya yayiwa Rabin nonuwanta Ta saman
rigarta ya dauke idanunshi Amman duk da haka say da yanayinsa yasoma sauyawa notice
dinsa suka nemi kwacewa, kwalkwaluwarsa tashiga circulating ya dinga jin wani iri
aijikinsa, cikin natsuwa Tayi serving dinsa.
bawani wani abinci yaci sosai ba ya Ture plate din gefe kasancewarsa Bai fiyye son cin
abinci may nauyi ba
‘ahankali ya maida bayansa ya jingina da kujerar da yake zaune akai Tare da Dan
zamowa kadan yana duban umminsa itama ,ummi shi take kallo tana tabe baki ba dai har
ka koshi ba?
ya dage mata girarsa daya alamun haka ne ,kai dai bansan irinka ba wlh kwata kwata
baka kaunar son cin abinci, DEENI yayi murmushi kawai batare da Yacewa umminsa komai
a
murya a sanyaye zeenat tace to ko na hado maka coffee ne?
parlour ya dauki shr har kusan tsawon minti goma batare da ko Tari yayi ba, Sai da zeenat
din ta km maimaitawa tmbyrta tukun muryarsa a dake Yace.
please…banason damuwa dan Allah aikinsa Ina bukata km mayye na takurani da
questions.
jin haka yasa zeenat din Mikewa “ahankali tana jujuya mazaunanta har tashiga kitchen
idanunshi kam a kanta abinda ya tsaya masa a makwashi ne ya samu ya hadiye da kyar.
yana hango tahowarta da yadda take motsa kirjinta yasashi sake dimauce take ya
wurgawa kansa tmby what’s wrong with me ?’ahankali yakamo lip’s dinshi na kasa yana
cizawa da karfi har takaraso ta,aje masa coffee a gabansa baidana cizan lip’s dinshi ba
cikin dakiya da mazantaka yasoma sha , sosai yasha coffee din ,ummin ta zuba masa idanu
kawai Tana kallonsa sak mahaifinsa kusan har ya so zarta muhd aliyu da komai. , Ya dubi
yana murmushi ya,akayi first love ta hararesa ai nan kafi kauri Ga abinci baka, zauna kaci
ba sai ruwa .tsam ya Mike, ya soma taku first love ni zanje na kwanta bacci bacci..nake ji
tare da sakar mata murmushi ,to Allah ya tashemu Ify.
Daren ranar sam DEENI kasa runtsawa yayi kwana yayi yana watsa jikinsa ruwa da kyar
DEENI yasamu Ya runtsa sakamakon wani irin feeling da ya dinga tasoma masa hannunshi
yasa duka ya dafe joystick dinsa dashi yana juyi , sai wuraren asuba bacci may nauyi yayi
nasarar daukeshi.
Washegari da sassafe yabar gidan ya wuce office.
zaune yakea office dinshi aiki yayi masa yawa sakamakon matsowar karshen wata
Kanshi Duke yake yana fama da aiki rubuce rubuce dake gabansa yaji nocking din kofa
kansa na Duke ‘ yabada izinin shigowa batare daya dago kansa ba.
Manir abokinsa ne yashigo cikin office din da sallamarsa DEENI ya amsa batare da ya dago
kansa ba yacigaba da abinda yake” ganin haka Yasa manirya tsayawa abakin taga, yana
kallon shukokin flowers din dake zagaye da surrounder din gurin
dan yasan tunda ya iske DEENI kan aiki bazai taba sauraransa ba matsawar bagama yayi
sanin da yayi masa na may matukar son aikinsa.
Kusan minti shabiyar yayi tsaye, sannan yasoma takowa ‘ahankali izuwa bakin makeken
tablet din da DEENI ke zaune ,yaja kujera daya ya zauna yana duban DEENI, Sai lokacin
DEENI ya dago rikitattun idanunsa ya dubeshi manir dasu.
har kagaji da tsayuwar kennan inji cewar DEENI?
Ba dole nagaji ba,dan naga alamun sai nakai Ga zama tukun zakiyi lokacina.
manir ya mikowa DEENI hannu suka gaisha ,yaushe kashigo garin ? Dariya manir yayi
shekaranjiya wlh na dawo yau km nace nazo naganka ,ko baiyi bane ?
wani irin farinciki ya lullube zuciyar DEENI ya danyi murmushi har dimple dinsa ya lotsa
tsantsar kyawun sa ya sake bayyana ,yana son a dinga nuna masa kulawa, manir Yace
aboki Ify kuwa irin wannan farinciki haka?
Bbu komai nima haka na tsinci kaina.
,DEENI ya jingina bayansa da kujerar dayake zaune kai yana jujuyawa dashi ,manir Yace
ya ummi da zeenat iya rigima ,sai DEENI ya yamutsa fuska sannan Yace ummi tana Ify ita
dayar ce dai bansani ba .
manirya sake yin dariya,badai kaki ka dauki shawarata ba.
da yanzu an wuce gurin, DEENI Yace kai..bana jin zan iya bin wannan shawarartaka,
dominta yana dayawa kai kace nasamu Yar talaka na aura ,yayinda ita km first love ke son
na aure kaskantacciya km maragalihu domin faranta ran zeenat,ni km banajin zaniya,dan
haka nake jin zan hakura da zeenat kawai ,ok ummi ta kawo maka shawarar haka kennan
DEENI ya daga masa kai kawai ,to why not ,kiyi abinda tace kai ni Dan Allah rabani da
wannan shirmen nan dai suka maganar suka shiga wata hirar duniya .
Wayarsa ce ta dauki karar sauti may dadi ‘ahankali Yasa hannunsa ya janyota daga jikin
charge yana dubawa. sunan umminsa yaga yana yawo akan screen din wayar ,ahankali ya
zareta daga jikin charge ya manna wayar a kunnenshi tare da yin sallama.
Muryarsa a shagwabe Yace Oh! No.. First love don’t do this to me please. dan Allah kibari
har nazo tukun naga kalarsu kada bad dinsu yayi min yawa..
abangaren ummi kuwa murmushi kawai Tayi tare da cewa shikennan badamuwa sai
kadawo din ok first love Nagode lov you so much, love too my son.
Manir na zaune yana kallonsa har yagama wayarsa, yana shawarar yadda umminsa ke
kulawa dashi ,da yadda Shima DEENI din ke kulawa da mahaifiyarsa. al’amarin nasu mai
matukar girma ne ,hira suka cigaba dayi kafin daga bisani manir yayi masa sallama ya
Wuce
Karfe tara daidai na daren ranar yana kishingide akan kujerar three siter yayinda ummi ke
zaune a gefensa tasa zeenat Tayi kiran masu aikin da akawo dazu ,shigowarsu yayi daidai
da runtse idanunshi dayayi..
Karfe tara daidai na daren ranar yana kishingide a parlour akan kujerar three siter yayind a
ummi ke zaune a gefensa byn tasa zeenat Tayi kiran masu aikin da akawo dazu,shigowarsu
yayi daidai da runtse idanunshi da yayi.
Baiyi tunani da gaske umminsa zata iya masa irin wannan auren wulakancin ba. ,shi ko a
tarihi Bai taba jin inda akayi irin haka ba, har suka karasa shigowa cikin parlour Bai bude
idanunshi ba ballanantana yakarewa yanayinsu kallo ,zeena tasamu guri nan kusa dashi ta
zauna
Yayinda masu aikin suka sake gaida ummi tare da oga DEENI.. wanda shi kwata kwata Bai
ma san ta inda zai amsa musu ba,dan haka yashare kawai abinsa batare da yace komai ba
sai ummi ce ta amsa musu tare da musu nuni dasu tsaya can nisa kadan. Numfashinsa ne
ya nemi tsayawa sakamakon ji da yayi yanayin sent din parlour yana neman canza salo km
har lokacin idanunshi a runtse suke gam… bai da alamun budesu
‘Ahankali ummi takira sunanshi DEENI.Ya amsa batare daya bude idanunshi ba Na’am
first love.
ka bude idanunka man ka gansu, gasu nan, ‘ahankali muryarsa a sanyaye yace gaskiya
bazan iya kallonsu ba first love sbd basuyi ba ,acanza wasu masu aikin idan akwai ..iya
abinda ya iya cewa kennan .yayi shr tare da gyara kwanciyasa ya juya musu baya,shi
kadai yasan yadda ranshi yake a bace har wani sama sama numfashinsa ke yi.
Ummi ta maida idanunta kan Yan mata guda hudu dake tsaye a gabanta tana musu kallon
tsab, guda uku daga cikinsu hausa fulani ne.
“yayainda daya daga cikinsu takasance yare sai dai tana jin hausa sosai kasancewarta Yar
asalin adamawa ce ,basu da wata makusa ajikinsu in aka dauke wacce takasance yare”
itama rashin addani ne kawai makusanta.
Km daman ita bata sakata cikin wayanda zata hada da tilon danta ba sai ta zauna matsayin
may aiki ahankali ummi ta sauke ajiyar zuciya tare da basu umarnin dasu koma dakin
da’aka saukesu a ciki kafin zuwa gobe.
Ita dai zeenat Yar kallo ce batada tacewa domin bbu damar yin magana suna wucewa ya
sauke naunauyen ajiye zuciya tare sakin numfashi sannan ‘ahankali ya soma bude
idanunshi ‘ahan kali ya sauke su fes akan ummisa” harara ta watsa masa shi km ya kashe
mata idonsa daya yana may cizan lip’s dinshi kmr an sikareshi ya Mike yayi hanyar step.
Washegari ummi ta sallami masu akin sai dai tabar laraba wacce ba Muslim ba domin
aikace aikace gidan.
Tun daga lokacin ake kawo masu aiki iri iri gidan Amman Sam DEENI yakasa tantance
wacce zai dauka matsayin wacce zaiyi AUREN SIRRI daita idan ummi tayi magana sai yace
shi Bai samu wacce Tayi masa ba.
Km ,hakan dayake yi Bai wani damu zeenat din ba kasancewar tasan halinsa da
kyankyamin tsiya.
Cikin haka DEENI ya siyawa zeenat form din jamb km a sannu ‘ahankali lokacin rubutawa
yayi ,taje ta rubuta bbu laifi tasamu abinda ake so a course din da za ta yi .
Abu fa kmr wasa duk wacce akawo sai DEENI yace A’a bata mishi ba
cikin haka wani dare DEENI yakasa rike kasan domin sha,awarsa mai shegen karfi ce tun
yana azumi da shan magungunan har magani yazo ya daina aiki ajikinsa.
Dan haka ya yanke shawarar kawai garaje zuwa Ga matarsa ,yana zuwa kuwa yasamu
kyakkyawan tarba daga zeenat din ,ranar tamkar sallah ce a gurin zeenat daman itama
Tayi mugun kewar mijin nata sambatu bbu irin wanda batayi ba har da kuka ,shi km yana
gama savice ya Mike tare da sake tamke fuska tamau tamkar wani zaki.
Amman kwata kwata hakan Bai dameta ba ballanantana yabata mata rai tunda tasan ta
wannan bangaren ba haka halinsa yake ba ita tadagula komai tama gode da yadda
yakawo kansa gareta km hakan shi yafi komai yi mata dadi .
, tun daga lokacin abubuwa suka sake yin sauki.
Jifa jifa idan takurewa oga DEENI dole alallaba aje gurin zeenat ita km duk lokacin dayazo
ashirye take data bashi hadin kai duk tana jigatawa a hannushi kasancewarta may saurin
yin relex a wajen sex .
Bayan wata uku zeenat tasamu shiga Lagos state university tare da dalleliyar motarta 4mat
sabuwa dal. al’amura sunyi mata sauki rayuwa Tana gara mata yadda take so tare sabbin
kawayen datayi a school karku manta zeenat akwai son kawaye da daukar wanka shiyasa
duk inda taje batasamun matsala gurin tara jama’a.
Byn shekara uku
Haniyace kawai kake ji acikin babban Holl din dake cikin PLASNUW ROWS family estate
wanda ya tara manya da kanana na cikin dangi kasancewar lahadi karshen wata ne, km
shine lokacin sada zumunci a tsakanin wannan family byn komai ya lafa. gaishe gaishe da
shawarace sharawarce ne yabiyo baya akan cigaba family anyi taro Ify yayinda kowa
yakama gabansa.
Hiy Mariya wace aka fi sani da mama ta abuja ,Yaya ce Ga mahaifin DEENI uwa daya uba,
zaune take a parlour gidan DEENI ita da Ummi suna zantawa.
fadeela ki cire son zuciya sannan kikawar da zarge da’ake miki acikin dangi da mutane
gari “dan ganin zeenat diyarkice shi Yasa kika ki daukar mataki akan zamansu da DEENI
yau aurensu tsawon shekara bakwa kennan babu wani cigaba ko karuwa ta haihuwa.
km kin zuba ido kina kallo batare da kin dauki wani mataki akai ba.
kibari yaron nan yakara aure fadeela ko acikin dagin ne ko km yaje daga waje tunda
yarigada yayi na farko acikin family ,bbu lallai ko dale ya km yi acikin gidan nan.
ummi Tayi murmushi dan itama rashin haihuvwarsu yasoma damunta amman bbu yadda
taiya.
ummi tace karki Ga laifina Yaya ,Gani nake rashin haihuwarsu da wuri watakilla ni suka
biyu amman munan muna ta addu’a.
,to kunje asibiti ne and dubanta inji cewar mama ,ummi tace muje km an tabbatar mana
da mahaifarta lfy lau take km zata iya samun ciki at any time ,daga nan ummi Tayi shr bata
sake cewa komai ba.
ita kadai tasan shirinta dan bazata iya fitowa tagaya duniya abinda tashirya akan
yaranta ba.
wanda har zeenat bazata bari tasani ba sai lokacin yin haka yayi,
Duk maganar da suke acikin kunne zeenat sukayi shi ” saukowa take zuwa akasa darn
daukar wayarta taji maganar da mama takewa Ummi akan kara auren DEENI shine fa
tsaya tana gama jinsu kuwa takaraso da sauri tamkar anjihota tayi zaman dirshan a gaban
maman ta abuja tana rusa kuka dan girman mama kada kimin haka kada ki bada
shawarar akaro min kishiya domin bana sonta kwata kwata bana kaunar zama daita.
sannan ta juyo gurin ummi,ummi kada ki dauki shawarar mama dan Allah nima zan
haihuwa kinji ummi duk tabi ta rude ta gigice tafi haiyacinta sai kuka take .mama ta daga
matsa ni Dan Allah rufe min baki kin wani cikawa mutane kunne.
Karar hon ne yacikawa securities din bakin get din kunne da sauri daya daga cikin
securities din yazo ya wangale babban get din gidan yana dagawa DEENI dake zaune
abayan mota hannu.
Ahankali direbansa yasanyo hancin matarsa rang,rover cikin farfajiyar gidan.
Kai tsaye rumfar da’ake parka motaci dake kofar gidansa direbansa ya nufa yayi parking
din motar.
Sannan ya fito da hanzarisa ya bude masa murfin motar tare da kamewa guri daya yana
Sara masa.
Ahankali ya fito daga cikin motar cikin takun nan nasa kasaita idan bakasan shi ba zaka
dauka ko tsabar iyaye yayi masa yawa nan haka Allah yayi sa da tafiyarsa ta musamman
kai tsaye yashigo cikin babban parlour gidan yayinda gabansa ke wani irin faduwa.
inda dai kunnuwanshi ba karya suke masa ba sautin kukan matarsa yake jiyowa da murya
aunty, n sa gabanshi ne yacigaba da dokawa ai da sauri sanyo kansa cikin parlour,ganin
umminsa zaune Yasa shi sauke ajiyar zuciya tare da yin hamdala a zuciyarsa.
Domin tunaninsa ya dauka ko wani abu ne yasamu umminsa.
Zeenat naganinsa ta zabura ta Mike tsaye takaraso gareshi gabadaya ta gigice sai kuka take
my hrt dan Allah kazo kagayawa mama bazaka kara aure ba ni kadai na isheka rayuwar
duniya dan Allah km zan haihu Wlh nima Ina son na haihuwa dakai .
Dan Allah ka fahimtar daita ,zan iya haihuwa nima kmr kowace macce .ka fada mata Bana
son kishiya wlh muddin aka min kishiya wlh zaku rasani gabadaya dan zaniya kashe kaina,
jin haka Yasa DEENI jan mugun tsaki Tare buge mata hannuta data rike shi dashi abin
haushi abin dariya ‘ahankali ummi ta Mike tsaye tare da kamo hannuta ta zauna daita kusa
daita haba zeenat ki natsu man meyasa kike irin haka ince, magana ce kawai akeyi ko
kinga anyi miki kishiyar ne duk kinbi ki rude kin tadda hankalinki nima kina neman tada
nawa.
Wasu Hawaye ne masu zafi suka zubo mata Dan Allah ummi kibar ma ambato min sunan
kishiyar ji nake kmr mutuwa zanyi numfashin har neman daukewa take duk hankali ummi
yatashi da ganin yadda yarinyata ta dawo cikin kankanin lokaci rarashinta kawai ummi
take.,
Mama dake zaune ta ta zuba musu ido kawai ‘ahankali ta numfasa sannan tace lallai yau
naganewa idanuna abinda ake fada acikin gidan ,ashe dai gaske ne fadeela kece kike
daurewa zeenat gidin take yin wulakancin data gama.
,Dan wulakanci ma har wani lallaba yarinya kike kan za’a mata kishiya kanta aka fara yi
mutun kishiya ?
Mama ta dubin inda zeenat take zaune tana rizgar kuka…ince ciki naji ace ki zubar har
Sau biyu shine yanzu dan tsabar iskanci,zaki cewa mutane kina son haihuwa.
,da can kinsan kina so meyasa kika zubar da shi ,ummi zatayi magana mama ta dakatar
daita abinda nake son kusani shine wlh wlh nasuru..zai yi aure matsawar baki haihu ba
nan da wata tara kinji na rantse sam fadeela Banga alamun kina da tausayi ba ,ubansa ya
haife shi kadai ,ya mutu ya bartshi amman shi yakare a bbu ko daya sam hakan bazai yiwu
ba ,ummi ta sautata murya tasoma bawa mama hakuri ,yayinda zeenat ita km ke kuruwa
tana rizgar kukan har da shesheka.
DEENI rike da wayarsa yana daddannawa bame da niyar cewa komai amman jin abinda
mama tayiwa umminsa ya so-so ranshi km ya tsaya masa arai dan haka cike da haushi da
takaicin yace haba mama..meyasa zakice haka naga itama zeenat din diyarki bata
ummi kadai bace.
Dan haka bai ka mata kice wai ummi ce ke daure mata gidin yin iskanci ba.
“yakamata kiyiwa ummina uzirin km aure ai nine mayin shi idan naso zanyiwa mamata
kishiya Bai sai ansani ba idan bangadama ba kuwa bbu ub…Ai tun Bai kai Ga karasawa ba
ummi tayi tsalle ta dire a gabansa Tare da rufe masa baki dan tasan aika aika yake shirin yi.
mama dake zaune har lokacin ta dinga girgiza kai kawai.
meyasa meyasa kika rufe masa baki eh ..Ai da kin barshi yakarasa abinda yayi Niya ince
irin kalar taki tarbiyar kennan ,amman kusani wata tara kawai na baku tana cika ko
haihuwa ko amarya acikin gidan.
ta Mike tsaye tana kokarin barin parlour ummi tabi bayanta tana bata hakuri dan ita bata
son tashin hankali km koda tana so bazata iya da family muhd bello khaliyal ba…AA
A hassle DEENI yasoma hawa step yana takawa biyu biyu yayinda zeenat ke biyi dashi a
baya tana kuka tana bashi hakuri dan Allah my hrt kayi hakuri karka min kishiya wlh bazan
iya zama daita ba … am ready to give any type of bby you wont nima Ina son bby Allah ne
Bai km bani ba. Ta ya Allah zai km baki haihuwa zeenat byn bakya so kyautarsa .kin
butulcewa ni’ima ubangiji nki.
idanunshi a rufe yakarasa shiga cikin dakinsa ,warwas ya zube akan gado yana fidda
numfashi sama sama kuka take har lokacin fuskarta tayi jazir abinka Ga farar macce
ahankali tasoma cire masa takalminsa taje ta ajiye a inda yake ajiye takalmansa.
ta dawo ganin yana kokarin son balle maballi gaban rigarsa Yasa takarasa da sauri tashiga
balle masa ya Mike tsaye tare da zare rigar da wando ya saura daga shi sai dan karamin
boxes, kukuan ya isheni haka bana bukatar hayaniya yana gama fadar haka ya shige
bathroom har ya fito kuka take tana masa magiya tsausayi ne taba zuciyarsa duk da
tsananin haushinta dayake ji aranshi hakan bazaisa yaga ana wulakantata ya kyale ba Dan
ko bbu komai ita din wata abace may daraja a gurin umminsa.
dan haka cikin sanyin nan nasa yasa hannuwansa duka ya jawota jikinsa ya rungumeta tsam tsam
Uhmmmm uhmmmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]