QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 33

QADDARAR SUMAYYAHCHAPTER 33
Kyawawan idanuwanshi wanda suka wadatu da gashin idanu kamar yadda girarsa take masu kama da na wanda ke jin bacci suke kan ta,shi daya ne tak sanye cikin qananun kaya sabanin dukka sauran wadanda suke tsaye tare,baki dayansu shadda ce jikinsu dinkin tazarce kaloli daban daban,kusan tare suka janye idanuwansa,gabanta ya shiga faduwa,kasa zaman wajen tayi,batasan ana iya gajin mutum ba,gashi ko mayafi babu a jikinta,sai ta miqe jikinta na rawa gabanta na faduwa ta bar wajen,ta tura qofar ta kulle ta dawo cikin bedroom din anty dijen. +

Gefan gado ta kwanta rub da ciki tana sauke numfashi,maganganun baabaa suka soma dawo mata,har yau ta kasa gane me yake nufi,tana da buqatar qarin bayani,tana buqatar taimako wajen wanu ko zata fahimci me yake nufi,amma ta taimaka masa wajen gyara rayuwarsa kamar yaya kenan,wanu mummunan abu yake mara kyau yakeso ta saka baki?,amma ita a wa?,bata da wannaj power din,ganin qwaqwalwarta na neman daurewa yasa ta kada kai tare da yin watsi da maganar,maimakon ci gaba da tunani sai ta sake daukan wayarta ta lalubi zainab ta kirata,din jiya suna wajen dinner taga misscall dinta baya kuma samu ta bita ba.

Bayan sun gama gaisawa da mama ta musu Allah ya sanya alkhairi zainab ta karba,nan take gaya mata jiya aka kawo lefe sati uku kuma aka sanya,murmushu sumayya ta saki tana tsokanarta
“Kice mu fara shirin tahowa kano ko?”
“Wallahi yaya,kizo ayi tsare tsare masu kyau”
“Insha Allah,ina huce gajiyar wannan bikin zaki ganni,Allah ya nuna mana da rai da lafiya”
“Amin yaya,ina abdallah na”
“Uhmm,ni kaina bansan ina yake ba,yana gidan biki”
“Ki gaisheshi tunda ya manta da mu” dariya ta danyi
“Zaiji,ki gaidan halimaty,wayarta bata shiga”
“Zata ji” suka katse wayar. 1

 Tana sauke wayar ta jiyo muryar abdallah yana karadi daga qasa shi da sh hafiz,sauka tayi daga gadon ta sauko qasa,yayi masifar kyau cikin wata arniyar shadda ash wadda batasan inda ya samota ba,hulace kanshi zanna wanda sau faman zuba qyalli take,qafafunshi saye da takalmi sau ciki,abinka da uwa da da,yana ganinta ya tako da gudu ya daneta,murmushu tayi ta zube saman kujera yana faman zuba mata surutu da bata labari.

        Ganin sha daya tayi ga gidan babu kowa sai ita ya sanyata yin shahada ta yafa mayafinta ta fito,kamar zata nutse haka ta dinga ratsa mutane a darare tana wucewa har ta kai ga cikin gidan bayan ta kira humaida ta gaya mata inda suke,ko ina harabar gidan ‘yan uwa da abokan arziqi ke kai kawo,kowa ka ganshi cikin kwalliya da walwala,daga gefe guda ta hango mahmoud da tarin abokansu ciki har da alqasim,suma sun ganta saboda haka ta qara sauri don kada su rusketa.

       Batayi aune ba sukayi karo kanta ya daki qirjinsa,tayi taga taga ta komo ta fada qirjinsa,zuciyarta kamar zata fito saboda tsoro,tayi yunqurin janyewa,ta samu nasara saidai hannunta na cikin nashi hannun yana duban qwayar idanuwanta,sai yanzu ya samu amsar inda ya samu qamshin da ya buwayeshi tun shekaran jiya,wanda har kuka su’adah tayi sabida jin qamshin,don ta tabbatar hadin humra ce ta mata ta musamman ba turaren namiji bane,gaba ta tusashu tana tambayarsa ina ya samu turaren,baki daya zuciyarta ta gama zayyana mata yana neman wata ne,idan banda haka ina zai samo turaren mace a hannunshi?baya ga haka ta lura wannan karon sam baya marmarinta,baya nemanta idan ba ita ta buqata ba,bayan a baya ta sani cewa duk sanda suka hadu har sai ta gaji ta hada kayanta ta gudu yake qyaleta,amma wannan karon sam ba haka bane,yana jinta yayi mata banza ya gama shirin baccinsa ya kwanta tare sa juya mata baya,don bashi da amsar bata,shi kansa yana jin qamshin cikin hancinsa amma baisan inda ya sameshi ba,baijin zai iya bata lokacinsa ya mata wannan bayanin tunda har tana zarginsa,to ta dauki duj hukuncin da take gani zata iya dauka,hakan ya sake hassala zuciyarta,itama ta shiga fushi da shi gadan gadan miqe ta fice ta sauya dakin kwana,bata san cewa ba shi ta yiwa ba kanta ta yiwa,tunda ba yau farau ba da yake kwana shi daya tamkar gauro,idan da sabo ai ya saba. 
       So take ya sakar mata hannu ko don idanuwan mutane da ke kai kawo a wajen,uwa uba ga haramci na riqe mata hannu da yayi,tayi yunqurin zame hannun nata amma abu yaci tura yana tsaye qyam yana dubanta,babban goro sai magogin qarfe,ya kusa lullube tsahonta baki daya,dududun nata tsawon bata fi iya qirjinsa ba,ga wani kwarjini daya cika wajen,ganin masu wucewa sun soma ankara ya sanyata cewa
“Ka sakar min hannu” cikin izza da motsa labbansa
“Saikin gayan abinda ke baki tsoro,me ya koroki bayan kowa na kai kawo a nutse amma banda ke?” Daga fararen idanunta tayi ta watsa mishi su,duk da yadda qirjinta ke bugawa,lumshe idonsa yayi ya bude ya janye nashi idanun daga kallonta,bai taba ganin mace mai farin qwayar idanu ba kamar haka ya raya a ransa,tsaki yaja a fili sannan ya saki hannun nata
“Ki kula next time,ban son irin wannan shirmen” ya fada yana duban gefanta,ita ke shirmen ma?,abun ya bata haushi,sai ta banka masa harara ta gefan ido duk da yadda gabanta ke faduwa qasa qasa tace
“Kaima sai ka kula tunda kana da idanu ai ba ni kadai ke da idanuwa ba” batasan tayi kuskure ba saboda kaifin ji da Allah ya hore mishi,ko yaya magana take yana iya jiyota,yana daya daga cikin wadanda Allah ya yiwa baiwar ji,har wani lokaci ba’a iya gulmarsa matuqar yana cikin gidan,har yayi gaba ya juyo a mamakance yana dubanta,karo na farko kenan da wata ‘ya ta taba maida masa magana,bakinta ta murguda duk don ta sake bashi haushi tayi gaba abinta,wani abu ya tsaya mishi a rai,ranshi ya baci,yau shi akewa rashin kunya?,abinda yafi tsana kenan a rayuwarsa tun lokacin quruciya,abinda ya fara hadashi kenan da su’adah tun tana qaramarsa,lallai zaiyi maganinta,wace ita da har take jin karanta ya kai tsaiko,babu shakka sai ya hukuntata. 17

      A bangaren anty maamaa ta tadda su,tana zaune tsakiyar yayunta anty farida da anty huda da matan yayyen ta ni’imah da fahariyya,sai qawayenta da cousins dinta irinsu eesha humaida ummu salma da sauransu,a hankali ta qaraso saboda lasalar da take ji cikin jikinta tana karbar saqon harara daga amira,duk da haka murmushi ne kan fuskarta,ta riga da ta sani itace mai laifi,sauran da suka san mekw faruwa dariya suka dunga yi sunsan za’a kwashi daramer,amma sai sumayya ta kashe mata gwiwa da fadin
“Ta zama ta saifullahi,ayya yarinya zata bar gida” ai kuwa sai ta soma qwalla,tana dariya ciki ciki ta qaraso ta zauna gefanta ra mata rada a kunne ma tsawon minti biyu,sau gani sukayi ta saki dariya tana share hawayen,huda ce taja tsaki
Au qaryar banza,dama fa son aurenta take ‘yar banza bansani bane,saifullahin da ake ji da shi kamar a lashe mishi mazaunai” dariya ta kamasu baki daya,dqi dai da dai dai sumayya ta bi ta gaida kowa,batasan matan yaya adam ba sai lokacin ni’imah da fahariyya,fahariyya ita ta fara tahowa ni’imah ta jira maigidan sai jiya suka taho tare da daddare,bata ga fahariyyan ba saboda ‘yar jin kaice itama kamar yadda amira ke gaya mata,ni’imah din ce babu ruwanga,hakanan take haquri da halayyar fahariyya na goranta mata da take lokaci lokaci akan rashin haihuwa,saidai zaman nasu babu yabi ba fallasa,rashin mutuncin fahariyyar da sauqi sakamakon cewa adam din tsayayyen namiji ne,bai yarda a wulaqanta masa uwar gida ba,sam basa shiri da su’adah da fahariyya saboda kowacce na jin kanta da jin cewa ta isa saidai daya tabi daya,duk da a zahiri duk cikin yaran gidan babu wanda ke da dukiyat almustapha,wannan ya qara kishin su’ad cikin zuciyar fahariyya,itakam ni’imah ‘yar babu ruwa na ce,ta kama mutuncin kanta,don iyayenta ba wasu bane rufin asirin Allah ke garesu,sai a yanzu da tayi dace da miji na qwarai suke samun sauyin rayuwa sanadiyyarsa,duk da haka dama tana da managartan halaye wadanda su suka fusgi adam zuwa gareta,duk da tarin yaran masu kudi dake sonshi a lokacin,ta kasance ta daban a gunsa har a yanzun duk da bata taba haihuwa da shu ba,sakamakon haquri biyayya da tsantsar iya zamantakewa da miji mai tafiyar da hankali. +

        Da daidai suka miqe suka fice ya rage saga sumayyan sai anty ni’imah sai humaida,suma sun maqale ne saboda suna kwasar wasu sirrika da lacture da anty ni’iman ke bawa amira,wanda baga fara ba sai bayan da wadancan suka fita,ba amira ba hatta su sumayya sun qaru da ita sosai,a nan suka zauna suka ci gaba da hirarsu,ni’imah ba dai sauqin kai ba,kamar qannenta haka ta daukesu,aqalla zata girme musu da kusan shekaru goma,amma sam hakan bai wani nuna ba sosai sabida tsabar gayu.
      Qarfe bakwai na magariba aka tafi kai amarya,babu wani takura ko neman mota kasancewar kusan kowa ya mallaki motar hawanshi,wanda ya taho daga wani garin ne bai taho da abun hawanshi ba sukayi amfani da motocin gidan baabaa,ga kuma ta familyn saifullahi.

       Ba shakka wannan shi ake kira qwarya tabi qwarya,ba shakka amiran ta shiga gidan da yayi dai dai da ita,gidane na alfarma wanda ke tafiya da tunanin mai tunani,sanda aka fara tafiya amiran ta riqe sumayya gam kan sai ta jira anzo an sayi baki,sun riga da sun gama tsarawa babu batun siyan baki,ko akwai din ma ita batajin zata tsaya,saboda mutum biyu daga cikin abokan saifullahi da suka uzzurawa rayuwarta tun ranar kamu,ta musu qaryar a niger take,saboda haka bata son su hadu bare su takura ta,dabara tayi mata cewar bari taje tayi fitsari daga haka ta arto gida.

      Biki ya tashi lafiya,ummee da kanta ta yi ma sumayyan godiya tare da godiyar kayan humra data yi mata wanda su aka jerawa amiran ma,kunya ce ta kama sumayyan,duka duka me tayi,su basu duba tarin karamcinsu wanda ya kai ga cancantarsu kan yi musu komai.

       Tun a daren ta kashe wayarta kwata kwata,don ta tabbatar cewa gobe kamar da qasa sai amira ta nemeta,jikinta ya gaji tubus irin gajiyar da bata taba yin irinta ba,lallai biki ba wasa bane,tunda ta kwanta bata tashi ba sai da gari ya waye,ta makara sallar asuba,don sai shida da rabi ta yita,tana gamawa ta koma ta sake kwanciya,ba ita ta farka ba sai sha biyu saura na rana,yunwa ta sadakarta,a guje tayi kicin ta tadda anty dije na soya miya qamshinta ya cika gidan baki daya,ba magana ta mata nuni da kayan break dinta dake ajjiye gefe,tana kaiwa baki daya yiwa antyn sannu da aiki
“Ai ke zanwa sannu,yaran nan sunso tadaki badon ma hanasu ba,shi yasa da abbansu zai fita na hadasu da shi ya kaisu wajen inna(kakarshi)”
“Kai kina ji da ni anty na” ta fada tana jan kujera don ta ji dadin cin abincin sosai
Ba dole ba,kece fa babbar diya” suka sanya dariya baki daya sannan suka ci gaba da hira suna tattauna wasu daga lamuran da suka faru yayin bikin,antyn na juye miyar cikin warmer tace
“Ai ke kam bakiga hutu ba,saura sati uku a shiga wani bikin”
“Wallahi anty shi yasa nakeso nayi kamar kwana uku haka ina bacci,don so nake next week na wuce kano” hararata antyn tayi
“Dama na sani ai,ke kam garin nan kamar yana mintsininki,gidan fa baki daya baya dadi wallahi idan kika tafi,hatta da abbansu ya dinga mitar kin dade,amma wani lokaci sai na rayawa a raina dole fa mu saba tunda wataran zaki aure,idan kika tafi kuma ya zamuyi” shiru sumayyan tayi taci gaba da kurbar tea,saboda anty dijen ta kawo zancan da bata qauna cikin hirar tasu,sai data gama sha ta sure cup din tana goge hannunta sannan tace
“Anty,wata tambaya ce da ni”
“Uhmmm,Allah yasa na sani” shiru ya danyi tana tsara yadda zata jefa mata tambayar kafin tace
“Wai idan wata ko wani yazo ya cewa budurwa ki taimaka ki gyara rayuwar wane,wai me hakan yake nufi?” Waiwayowa tayi ta kalleta har sai da gaban sumayya ya fadi,Allah yasa ba wani mummunan abu bane,kamar antyn ta tambayeta wa ya fadawa wani hakan sai kuma ta fasa,taci gaba da aikinta tana bata amsa
“Maganar na da ma’ana bangare biyu,nq farko idan har aka fadi haka ga wani ko wata makusanciya ta mutum ana nufin ta dinga bashi shawara da hanashi aikata wasu abubuwa,ko kuma wani abu na son faruwa da shi ana son ka taimaka kada ya fada cikin wannan abun,sannan ma’anar na iya daukan AURE ko SOYAYYA,abun nufi…….shi wanda ya gaya miki maganar yana ganin kamar kina da wasu qualities da wani namiji ke buqata,wanda wannan qualities din zau taimaka masa wajen gyaruwa ko ingantuwar rayuwarsa,babu kuma hanyar da zaki gyara ko ki inganta rayuwar tasa sai ta hanyar AURENSA ko yin SOYAYYA da shi,to sai a baka maganar a dunqule” tunda ta dauko maganar gaban sumayyan ke faduwa
“Da gaske baba na nufin kenan ta auri almustapha?,abinda baabaa ke son fadi mata kenan” kai ta shiga girgizawa cikin zuciyarta ta soma furta
“La haula wala quwwata illa billah,Allah ka sani ina ganin qima da darajar wannan bawa naka,ya Allah ka fidda masa wannan tunanin daga zuciyarsa a kaina,ka jefa masa tunanin wata,Allah kada ka bashi iko ya tambayi abinda bazan iya masa ba”
“Ke sumayya meye haka?” Inji anty dije ganin yadda take kada kai tana mus mus da baki,murmushin yaqe na musamman ta qaqalo sannan tace
“Ba komai,kawai ina mamakin yadda muka kasa fassarar maganar,wani ne ya gayawa wata” ta fada tana miqewa tsaye sannan ta fice daga kitchen din,da kallo anty dije ta bita,cikin zuciyarta tana addu’a,Allah ubangiji ya sanya sumayyan tayi gamo da miji ne dan gaske,wanda zata huce takaicinta,babu shakka zata so za kuma tayi burin sumayyan tayi auren da zata huta ta sanadiyyarta,juyawa tayi taci gaba da aikinta tana addu’a cikin ranta.
A sanyaye ta zauna bakin gado maganar na sake y mata yawo,indai haka ne ba shakka dole ta qauracewa haduwar ta da baabaa,kai ya zame mata jazaman tafiya kano,kuma bata jin zata dawo nan kusa idan ta tafi din,zata yita qirqiro dalilai ne wadanda zasu zaunar da ita a can. 1

       A daddafe ta haqura ta kai ranar alhamis kamar yadda ta gayawa anty dije,sannan ta shirya tafiya,wanda ya rage sauran kwanaki goma sha hudu bikin,anty dije ta bata saqonni gun mama sannan tace suma nan da kwana bakwai suna tafe,wannan karon saboda tsabar zaquwa ta tafi bata iya jira abban laila ya dawo daga kaduna da yaje ba ya hadata da driver,motar haya ta hawo ta tafi,ba yadda anty dije bata yi ba amma ta kasa daurewa ta jira.

        Tana hanya taji kira,lambar amira ce,tun kafin ta daga ta saki murmushi
“Amaryar saifullahi bada kanki a sare” kamar wadda ke shirin sakin kuka ta soma mata qorafin kota nemeta ko?,sun hada baki da saifullahi sun sace mata wayarta,shi din ma ya rufe gidan ba shiga ba fita wai sai sun huta,ya kuma hanata wayarshi sai yau ya bata wayan,dariya ta dinga mata din yasan da wannan plan din,sai da ta gama qorafinta sannan suka gaisa tace yaushe zata zo don Allah
“Kin ganni hanyar kano,wani bikin ya sake kira na,bikin zainab dita”
“Wayyo,dama a kusa da namu ne,naci burin zuwa fa namecy” dariya tayi
“saidai ki tara ana halima idan Allah ya kawo”haka nan suka gama hirarsu ta baiwa saifullahin suka gaisa sannan sukayi sallama.

   Kamar ko yaushe sunyi murna da zuwanta,mama nata tsokanar abdallah wai ya qara qiba
“Amma dai zaka koma ko?” Wuya ya maqale a kafadarsa
“Nan yafi dadi,can kullum kuna rufe a gida” dariya suka saki don abdallahn badai son yawo da wasa ba,hararshi sumayya tayi
“Nima babu inda zaka bini,rigimammen kawai” ko a jikinsa dariyarsa ma ya sanya abinsa,washe gari yaya yahansu tazo ta daukeshi ma sukayi tafiyarsu,sai ranar kamun zainab tace zata dawo da shi.

       Tunda tazo babu zama suna ta shirye shirye ba kama hannun yaro,ita da anty salma qanwar mama da anty amina matan yaya abubakar,sunyi waya abdur rahman bai nan amma zai dawo da shi za’a yi daurin auren shi yasa take hidimarta hankali kwance ba wani damuwa ko takura,cikin ikon Allah da baiwarsa komai yana tafiya daidai,sumayya taga yadda ake komai cikin tsari saboda haka ta dage ta tsarawa ‘yar uwarta komai yadda zai qawatar ya kuma burge,kudi sosai tasa yaya abubakar ya bata bayan wanda anty dije da uncle farouq suka bata,dinkuna sosai ta yiwa mama,atamfofi masu tsada da kyau,harda mayafai da takalma duk da yaya abubakar yayi musu amma tace wannan nata ne,sannan ta siyawa malam gezna ta asalin wadda zai sanya ranar daurin aure,takalmi mai kyau harda agogo da turare da sabon rawani fari qal,kasancewar malam din ba baya bane wajen tsafta shi yasa kusan kayansa galibi farare ne,aka yi masa dinkin babbar riga ‘yar ciki da wando,ita kam dama bata da matsalar sutura sai anko kawai data yi,sai abdallah data masa shaddar daurin aure duk da dumbin kayan da yake da su,saura kwana tara biki kuwa saiga anty dije da iyalinta,nan aka shiga hidima sosai.Kan hanyarsa yake ta dawowa daga airphort bayan ya kai anty dije da yaranta sun tashi zuwa kano,tun daga nesa yaga kamar motar baabaa prof a tsaye,hakan ya sanya ya rage gudun motar ya qaraso a hankali ya faka tashi motar bayan tasu sannan ya bude ya fito. +

      Baabaan ne tsaye gaban motar,kana dubanta kasan matsala ta basu,qarfen nasara da bashi da tabbas,motar kwata kwata shekararta guda,ba yadda mustapha baiyi kan a canzata ba kamar yadda ya saba sauya masa motocin hawanshi amma yace a sauya sauran amma ita banda ita,yana jin dadin motar,da ita yake zuwa gidan gonan sulensa duk qarshen sati,duk randa zai tafin baya tafiya da wasu motocin face wadda ita kadai zai hau,kuma daga shi sai druvansa,yana jin dadin zama gidan gonar,ya zazzaga yaga gidan gonar sosai,yanajin nishadi da farincikin yadda dukiyar sulensa ke habaka,fatanshi Allah nuna masa ranar da zaiga sulenshi,a irin haka ne yau motar ta tsaya musu a hanya. 2

       A aladabce uncle farouq ya qaraso
“Subhanallah,baba kada dai ace qarfen nasara ya muku tsiya?” Cikin murmushi mai dauke da dattako yace
“Wallahi kuwa,to ya za’ayi,yau da gobe ai sai Allah,babu wani abu dake matabbaci”
“Gaskiya ne” inji uncle farouq yana fidda waya daga aljihunshi yana fadin
“Bari a kira gida to a turo wata ko baabaa,tamu motar ba lallai ka iya shiga irinta ba” murmushi ya kuma subucewa baban,har ya sanyashi ya juya ya sake kallon motar duk da ya santa,motace mai lafiya wadda bata da wani aibu ko makusa,ko kai waye zaka iya hawanta,amma ya sani cewa irin motocin da mustapha ke ajjiye masa yana hawa shi ya sanya farouq din tunanin yafi qarfin wannan
“Haba faruqu,saidai kawai idan rawar hawa motar take kake min,amma ni din waye da bazan hau wannan motar ba” ya fada yana dariya,bakinsa ya rufe shima yana dariya
“Afuwa baabaa” ya fada yana bude masa gaban motar,kafin ya shiga ya waiwaya ya dubi drivan nashi
“Kada ka tsawaita tsaiwa a nan,ka kira bakaniken nan,idan bakaniken ya iso ka bashi muqullan ka taho gida” a ladabce yace
“Yallabai man yace kada a sake barinka ka hau motar da baniken hanya ya tabata ranka ya dade” murmushi ya saki
“Qyale wannan,idan na biye masa ma a jirgin sama zan dinga yawo,ni waye da bakaniken hanya bazai taban mota ba,shi yasa na hana a kira gida agaya musu motarmu ta tsaya nasan zai iya jin zancan ya damu mutane da batub sauyan motoci,bayan ni din duka kwana nawa ya rage mana a duniya,kayi yadda nace kawai”
“To ranka ya dade” inji drivan,baban ya juya ya shiga motar faruqun ya rufe ya zagaya shima ya shiga ya tadata suka fara tafiya.

       “Asalina daga qauye na fito faruqu,kiwon dabbobi  na dinga yi ni da aminina,da can ko jaki bani da shi na hawa bare a kai ga mota,din me zan dinga manta asalina,ita duniya gaba dayanta yadda ka dauketa haka take zuwa maka,mafi daraja cikin mutane shine wanda a zahiri ya isan amma yake daukan kanshi ba’a bakin komai ba,girman kai rawanin tsiya ne,wanda ke zaton ya isa kuma sai Allah ya qasqantar da shi a duk inda baiyi zato ba” kai uncke farouq ke gayadawa cike da gamsuwa,tsohon dattijon qwarai ne,yana bala’in son zama da shi saboda dole ka dauki darasin rayuwa,idan ya shiga cikin wasu baka isa kace shine wannan professor din ba,kuma tsohon jakadan nijeria a qasar amurka. Danja ta tsaidasu uncle farouq yaci burki da sauri saboda yana dan gudu,wanda hakan ya sanya katinan dake zube gaban motarshi suka zubo,jiya ya karbosu shi yasa aka yiwa malam su na daurin auren zainab ya baiwa anty dije ta tafar mai da su ragowar ya ajjiye wajansa zai bawa kawunshi
“Bismillahi” malam ya fada yana cewa
“Kaima ashe kana dan taba irin tuqin almustapha kenan ko?” Ya fada yana murmushu tare da duqawa yana kwaso katinan sa sukw zube din. +

       Caraf idanunshi suka kai kan sunan dake jikin katin wanda ke qunahe sa sanarwar daurin auren SULAIMAN AMINU DAHIRU GOMBE,sake maimata sunan yayi,sunann da ya kasance sak irin na tsohon amininshi sule,tsohon aminin da kullum zuciya ke begen ganawarsu,maimaita sunan ya dinga yi tare da kallon rubutun da aka tsarashi kalar golden,tamkar zai gano masa da zargin da zuciyarshu ta fara yi,uncle farouq ya lura da hakan sai yace
“Bikin qanwar mai sunan mama ne,wato ‘yar yayar khadija” wawiyar ajiyar zuciya ya sauke ya maida dubanshi ga farouq
“A ina suke faruqu”
“A kano suke”
“Kano?,meys asalin mai gidan” kai ya girgiza cikin kokwanto
“Bamu taba zancan gaskiya da ita ba,amma dai a kano na sansu,wani abu ne baabaa?” Kai ya kada yana maida katinan mazaunansu
“Sunan ne kawai ya yimin kama da na wani tsohon aminina wanda har yau nake neman bayan ya bata tsahon shekaru”
“Ayyah,Allah ya bayyana shi”
“Amin amin faruqu”. Bai bar babaan ba sai daya dangana da shi har cikin gidan sannan baabaan ya sauka yaba masa godiya,kunya duk ta kama faruqun,a rayuwa babu wani abu da zaiwa baban da har zai masa godiya,bayan babu wani nau’in karamci da kyautatawa da baban bai masa ba tun daga sanda ya sanshi har zuwa yau. 5

      Tunda ya koma gidan baki daya ya kasa sukuni,katinan da sunan sun tsaye masa a rai,daren ranar kasa cikakken bacci yayi,yayi salloli sosai kafin ya samu bacci yayi awon gaba da shi,da asuba da ya tashi da abun ya tashi cikin ransa,har gari yayi haske,sai kawai ya tsinci kanshi da jawo kiran wayar uncke farouq ya buqaci adress din gidan mamallakin sunan da ya gani jikin katin,babu haufi ya tura masa don baya shakka cikin nagartan baabaan,yasan cewa koma mene alkhairi ne IN SHA ALLAH.

        Waya kawai ya sake dagawa,ya lalubi lambar mahmoud ya buqaci ganinsa,ba bata lokaci ya iso kasancewar yana cikin gidan,sanar masa yayi ya laluba idan akwai jirgin da zai tashi daga abuja zuwa kano ya yankar masa ticket guda hudu,shi daya mahmoud din daya mus’ab wanda yazo biki bai koma thailand ba,da kuma drivansu,bai wani mamaki ba saboda yasan lokaci zuwa lokaci baaban nasu nayin tafiya kota ziyara ko duba gidajen gonar wannan babban aminin nashi da tunda suka taso suke jin sunanshi suka kuma haddaceshi,tare da riqe girma da matsayinsa wajen babansu,lokaci lokaci sukan yi bita da tilawarsa,saidai har kawo yanzu idanuwa basu taba ganinshi ba,cikin sa’a aka samu jirgin azaman wanda zai tashi ne da la’asar qarfe hudu na yamma,ba haka baban yaso ba amma haka ya karba.

        Qarfe hudun jirgin ya lula da su sararin subhana zuwa kanon dabo,wanda cikin mintuna suka isa cikin yarjewa da ikon ubangiji tare da sahalewar ci gaban zamani irin na yanzu,kano tamkar gida take wajen baaban,saboda haka suna sauka suka tarar da motoci guda biyu suna jiran isowarshi,ba bata lokaci suka shiga suka fice daga airphort din.

       Wayarsa baban ya ciro,ya lalubo adress din ya soma karantowa drivan,kasancewarsa dan kano ne tuni ya fahimci wajen,sannu a hankali suka dinga keta unguwanni har suka qaraso unguwar da ya buqata,a bakin qofar gidan sukayi parking,drivan ya sake tambaya aka tabbatar masa nan ne gidan malam sulaiman,yaron ya aika ciki ya tambayo yana nan kamar yadda baabaa ya buqata,saidai yaron ya sanar musu baya nan amma bayan sallar isha’i yana gida,ya sake aika yaron yace idan ya dawo a gaya masa yayi baqo,amma zai dawo bayan sallar isha’in ya tsumayeshi don Allah,sai da ya isar da aiken sannan suka tada motocin suka bar layin yaron na bin motocin da kallo saboda yadda suka yi masa kyau. Baabaa prof ji yake kamar isha’in ba zata yi ba,fata yake cikin ransa Allah ubangiji ya sanya sulensa ne,Allah ya qaddara saduwarsu,haka kawai yake jin zumudin zuwan sallar isha’in yayi yaje yayi tozali da mai wannan suna. +

       Kai tsaye gidansa daya fara zama cikin garin kano tun zamanin quruciya can aka wuce da shi,gidan har yanzu yana nan da kyansa da daukar hankali,kasancewar bai bar gidan ya lalace ba,ko yaushe sake sabunta shi ake saboda ba’a rasa cikin iyalansa mash zuwa kanon,gida take kano a gun kowa,ko baka shigo ka zauna cikinta ba baqunta ko kasuwanci ya kawoka,ko ba haka ba ma hanya ta wuce da kai ta cikinta,wanka yayi ya sauya shiga sannan suka wuce masallaci shi da mus’ab da mahmoud baki daya kasancewar dab ake sa fara sallar magariba.

       Basu suka baro masallacin ba sai da akayi sallar isha’i,kai tsaye hassan driver ya koma gida ya fiddo motar ya kawota bakin masallaci suka shiga,tafiya ce da bata wuce minti talatin ba ta maidasu unguwar,guri suka samu sukayi parking sannan suka aika yaro yaje ya sanar da malam ana sallama,cikin sakanni ya dawo ya gaya masa yana fitowa.

      Tsaiwar mintuna biyar kacal ya hangoshi,idanuwa ya zuba masa baki daya ko qwaqwaqwaran motsi baya yi,tun kafin ya kai ga qarasowa inda suke ya shaidashi,girma ko tsufa baiyi isar da zaya sanya ya kasa gane sulenshi ba,dadi ko wuya babu abinda zai mantar da shi sule,shima takowa yake saidai sam bai kula da wanda ke gabansa,kasancewar yafi ganin mahmoud da musa’ab dake tsaye gaban baabaa prof din,a hankali ya qaraso ya dubi su mahmoud a nutse
“Yan samari kuke sallama da ni?”
“Basu bane,muntarinka ne,muntarinka ne sule,suken mai gado” da hanzari ya daga kai shima din gani waye?waye wannan dake ambatarsa da sunan nan qwaya daya jal da yasan duk gadin karkararsu shi kadai ke kiransa da shi,ya sanya masa sunan me tun daga lokacin da malam muhammadu(mahaifin baabaa prof) ya basu tarihin annabi sulaimanu da nana bilkisu,kutsawa yayi tsakiyar su mahmoud yana fatan kayalinsa ya zama gaskiya,ya tabbata kuwa,muntarinsa ne,muntarin da kullum matuqar rana zata fito ta fadi walau yana da cikakkiyar lafiya koko babu ita sai ya tunashi,sai yayi begen ganinsa,da sauri suka qarasa zuwa ga juna suka rungume juna kowa na ambatar sunan dan uwanshi,kowannansu jikinshi na rawa,lamarin ya yiwa su mahmoud nauyi ganin yadda dattawa ke fidda ruwan hawaye,yara masu wucewa suka soma tsayawa suna tunanin wani abu ne ya faru ga malam din,mus’ab ne yayi qarfin halin cewa
“Amm,baabaa yara fa sun fara tsayawa” abinda ya fargar da malam kenan ya saki muntari yana kallonshi,ji yake kamar zai sake bace masa bazai kuma ganinsa ba,ko kuma mafarkin da ya saba ne yake yi
“Ina zuwa” malam ya fada cikin sauri har yaja tuntube ya shiga gida a gaggauce ya karbi muqullin sitting room wajen mama yana shaida masa yau ga muntarinsa a gidansa,muqullin kawai ta bashi tana tantama,muntarin da tunda suka hadu take jin sunanshi daga bakinsa amma bata taba ji sun hadu ba shine tau aka ganshi?.
Jikinsa har rawa yakeyi ya bude sitting room din suka shiga,har yanzu kowannansu gani yake kamar almara
“Sule kaine?,ko almara ce?”
“Nima haka nake ji muntari,saidai lamarin ubangiji yafi gaban haka,shi sami’ud du’a ne”
“Qwarai kuwa ba shakka”doguwar gaisuwa sukayi bayan sun gama sumbatun ganin juna,sam sun mance ma da wani mus’ab da mahmoud a wajen,har sai da mahomud da mus’ab din suka matso suna gaida malam ya amsa fuskarshi na fitar da annuri,dukkan wani nauyi dake cikin zuciyarsa ya yaye,a yau ya tabbata farinciki bazai barshi yayi bacci ba
” wadan nan ‘ya’ya na ne sule,gasunan,akwai biyar a gida,baya ga jikoki da suka kusan tasamma guda goma matan aure biyu,kaifa sule?,ya rayuwa ta kasance?”ya fada yana dubansa,wani sashi na zuciyarsa na masa susa ganin alamun sulen bai kama koda kaso daya cikin goma na arziqin da shi yake da shi ba,bayan kusan tare suka sha wuyar tattala da tara dukiyar,saidai alhamdulillahi kana ganinsa kasan baya cikin wahala,yana cikin matuqar rufin asiri,miqewa mahmoud sukayi shida mus’ab suka koma qofar gida don bash waje suji dadin ganawa sosai,gyaran murya malam yayi sannan yace
“Bayan barina garinmu muntari na jima bansan inda hankalina yake ba,da na tashi kawai na tsinci kaina cikin makarantar allo ta almajirai,wani malami dake yawon rarraba almajirai ya tsintoni ya hada da yaran da zai kawo kano,sai na karbi rayuwar a yadda na ganni,na riqe karatuna da hannu bibbiyu,na zama daya daga cikin hamshaqan dalibai haziqai da malam ke ji da su,gefe daya kuma kasan tun asali bani da matacciyar zuciya,a duk lokutan da ba na karatu bane nakan fita neman na kaina,duk aikin da na samu zanyi kowanne iri indai na halal ne,batun gida kam baki daya na manta ma ni din dan wanne gari ne,tun malam na damuwa yana qoqarin tambayata har ya haqura ya watsar a haka rayuwa taci gaba da turawa,na samu cikakkiyar haddar alqur’ani mai girma,na zama daya daga cikin amintattun malam,’yan gaban goshinsa,muntari ban tashi tunawa da garinmu ba sai sanda Allah ya yiwa mahaifina rasuwa,naje na tadda rasuwarshi,na kuma samu labarin dukan abun arziqin da kake yi,na tambaya saidai kash ko daya ba wanda yasan inda kuka koma acikin gari,suce zuwa musu kake ka koma,da haka na isa ga dangin mahaifiyata wadamda suma mutuwa ta daddaukesu sai ‘yan ragiwa,muka gaisa na dawo cikin gari na hau cigiyarka,wasu suce min sun sanka amma basu san matsugunninku ba,wasu suce ma basu sanka ba,da haka na haqura da dawo kano bani qwarin gwiwa,bayan wasu shekaru ban haqura ba na sake komawa,sai naje na tadda ma baki daya kunyi qaura daga gombe kun dawo kano,naji dadin hakan saboda ina zaton zan sameka ta sauqi tunda muna gari daya,saidai na manta cewa kano nada girma da fadi yawan al’umma da yawan qabilu,akwai tarin qananan hukumomi qarqashinta,haka na qaraci nemana tsawon shekaru,tun inayi tuquru da qarfina har na haqura. Uwar ‘ya’yana a yanzu diyar malam ce,wanda saboda yadda da gamsuwa da yayi da kyakkyawar halayena da dabi’una ya bani aurenta,na samu tarin ilimi daga wajen malam har bayan rasywarshi sunan malam ya dawo kaina,duk da ban iya ci gaba da kula da almajiran ba kowa ya koma garinsu,amma ban fasa bada karatu ba wa dalibai masu zuwa su tafi,a yanzu haka muna da yara hudu da jikoki biyu,sannan cikin qarshen wannam satin zan sake aurar da yarinyata ta uku,kazo a daidai muntari,ko yaushe ina bege idan wani abu da ya shafi iyalina ya taso,inama ace muntarina na nan”cikin farinciki baabaa ke dubanshi
“Allah ya amsa addu’armu sule,Allah shine abun godiya” a hankali baabaan shima ya soma zayyane masa yadda yayi tashi rayuwar,gyada kai kawai malam yake yana kallon muntarinsa yana jin dadi,baabaa prof din ya qare da cewa
“A yanzu haka sule na kaima kana da taka dukiyar ta kanka,kyautar da nayi maka ban fasa ba sule,itace naci gaba da kula maka da ita har kawo yau,a yanzu haka duk wani gidan gona ko yoghourt ko fresh milk dake dauke da tambarin S.A.D mallakinka ne” mamaki ya kama malam,girma matsayi na muntarinshi ya sake ninkuwa cikin idanunshi,samun mutum mai amana irin haka a wannan zamani abu ne mai wuya,samun aboki irin muntarinsa a zamanin nan tashim hankali ne,bai manta wani waqe da wani balaraben mawaqi ya tabayi yana cewa’a yanzu zaka samu cewa,zukatan abokan gaba sune a jikkunan abokai’ma’ana a fili a bokai suke a idanun kowa,amma a badini kowannensu gagarumin abokin gaba ne ga dan uwansa,bai qaunarsa,bai son ganin ci gabanshi,burinsa kawai yaga faduwa hasara sa damuwa tattare da shi,kai malam ya kada
“Duka wannan ba shine abun damuwa ba,haduwata da kai kafin Allah ya zare numfashi daga jikina shine babban abu,kuma Allah ya cika mana wannan burin” shima kai baabaan ke kadawa
“Dukkan abunda muntari ya mallaka na sule ne,yana da iko da shi,bare wata qaramar kyauta da ya masa tun zamanin quruciya?,haqqinka ne sule dole ka karba,munyi haka tun a gaban idanuwan malam,A yanzu bayan qaaa ta rufe idanunshi sai mu sauya?,sam haka bazai faru ba” inji baabaa. +

        A daidai qofar gidan kai napep ta saukesh,ita ne da zainab da halima,a gajiye suke matuqa,don sunyi yawo sosai gidan ‘yan uwan mamanta rabon chewing gum,burin sumayya kawai ta samu inda zata jefa haqarqarinta ta kwanta,don ko ta abinci bata yi,Allah ya sota tayi sallolinta baki daya.

       Kamar ance dubi can ta hangi mahmoud zaune saman motarsu yana jajjefa qafa yana murmushi,bisa dukkan alamu yana jin dadin yanayin,haka sauyin waje zuwa unguwar da bai santa ba bai taba zuwanta ba hakan yayi masa dai dai,idanu ta zuba sosai wai ko idanuwanta ke mata gizo,ta sake matsawa wajen,tabbas shine,daidai sanda ya waiwayo shima,baki ya bude yana mamaki
“Wa nake gani haka?,me ya kawoki unguwarnan?” Ya fada yana murmushi tare da saukowa daga saman motar 
Da gaske kai ne?,to me kake yi a kano kuma a unguwarmu a qofar gidanmu?”
“Kina nufin nam shine gidanku?” Ya fada yana nuna gidansu da yatsa
“Qwarai kuwa,nan aka haifeni”
“Malam shine aminin baabaa dama,sulen muntari?” Wannan magana ce kawai ta kasa gane me yake nufi,sai ta dubeshi tana neman qarin bayani,baisan ta yadda zai fasaara maga zancan ba sai ya dora da cewa
“Tare da baabaa prof muke fa sumayya,babanku shine tsohom aminin nan masa da yake yawan ambata,wanda ba yadda zakuyi magana da shi ta awa daya bai sako zancansa ba” ya fada yana murmushi har cikin zuciyarsa yana jim dadin yadda a yau burin mahaifinsu na tsahon shekaru ya cika,mamaki ya kamata qwarai,tabbas babu shakka zata iya tunawa ko ita yana sako mata zancansa lokaci lokaci idan hira ta dan hadasu
“Malam dinmu?,baaba yanzu yana ciki?” Duka tayi tambayar a tare lokaci guda cike da dimbin mamaki,wai babanta shine tsohon aminin baabaa prof,bugu da qari kuma wai baban ne yau a gidansu
“Qwarai kuwa,mun fito mun nasu guri ne din kinsan tsaffin abokai idan aka hadu ba dama,kada a tuno wata quruciyar aji kunya a gabanmu” ya fada cikin irin salonshi na tsokana,dariya ya basu baki daya
“Allah mai iko” sumayyan ta fada har yanzu abun nata na bata mamaki
“Bari naje na gaida babanmu” ta fada tana yunqurin wucewa
“Wannan qani na ne,shike bi mini,mus’ab dake thailand,gashi nan ku gaisa” ya fada yana dukan kafadarsa,a mutunce suka gaisa sannan ta sanya kai zuwa cikin gidan cike da zumudi da mamaki. 
       Sai da tayi sallama biyu aka bata izini sannan suka sanya kai cikin dakin,suna zaune irin zaman da kama dubansu kasan muhimmiyar ganawa suke,ganawa kuma mai dauke da qauna da fahimtar juna,duk da ruwa dake lemukan gaban baabaa prof babu wanda ya taba,ganin sulenshi da sauraron labaranshi ya fiye masa komai,daga kai baaban yayi cikin mamaki yana dubanta
“A’ah,mama na,daga ina haka” kanta a qasa cikin murmushi ta qarasa gabanshi ta duqa
“Baabaa,yau kaine a gidanmu?” Sai ya maida dubanshi ga sule yana fadin
“Kada dai kace min sumayya diyarka ce?” Cikin murmushi ya daga kai
“Tabbas,ita ce diya ta tabiyu,ita ce kuma ta haifamin babban jika na” kai baabaan ke dagawa,wani madaukakin farinciki na mamayarsa,tabbas Allah na sonshi,Allah na duba ga zukatan bayinsa ya musu taimako cikin ayyukan alkhairin da suka sanya gaba,a ladabce sumayya ke gaidashi da su zainab ya amsa cikin farinciki yana sanya musu albarka. 2

       Sosai wani irin farin ciki ke shigar shi,ji yake tamkar babu wanda ya kaishi farinciki yau a duniya,mamanshi cikin zuriyyar sulenshi?,babu ko tantama Allah yana nufinsa da alkhairi,sosai yake jansu da hira abinshi,tun su zainab na dari dari na rashin sabo har suka saki jiki
“Ba don bikin da za’a yi ba shakka sai na daukeku baki daya,dama ita mama na ‘yar gida ce” baabaa ya fada yana murmushi,dariya suka sa baki daya suna sake jinjina girman qaunar dake tsakanin iyayensu,sumayya ce ta janyesu tace bari su shiga ciki suma don su sake basu waje sosai,murmushi ne dauke a fuskar baabaa prof har suka fice sannan ya maida idanunsa kan malam. Sule,dama sumayya diyarka ce?,wannan abu ya faranta min fiye da yadda kake zato,tun sanda naga yarinyar naji ta kwanta min,na yaba da halayyarta,haka naji ina qaunarta kwatankwacin yadda nake qaunar amira,ashe jininmu ce,jinin sulenmu ce” murmushi malam keyi sannan yace
“Mai sunan inna daban take muntari cikin ‘ya’yana,Allah ya yi mata baiwar ilimi hankali haquri da nutsuwa,zakayi mamaki odan na baka labarin irin rayuwar data fuskanta,da irin qaddarorin da suka fuskanceta,cikin ikon Allah ta cinye jarrabawarta,dubeta,yanzh waye zai ce ta taba fuskantar matsi da qunci makamancin haka,waye zai ce harda maraya gareta?” Dubanshi kawai baabaa keyi,don shi bai san sumayyan ta taba aure ba
“Kana nufin kace mama na ta taba aure?” Kai malam ke kadawa don tabbatar masa
“Qwarai kuwa,har da yaro” gaban baabaa na faduwa cike da faata yace
“Ina fata amma a yanzu bata da aure ko maganar wani kanta?” Cikin mamakin gambayar da muntarinsa ya masa ya amsa masa da eh,sauke ajiyar zuciya baabaa yayi yana furta
“Alhamdulillahi,sule,ko zaka iya taimakamin ka bani auren mama na?” Dubanshi yake alamun bai fahimta ba
“Ina nufin ka bani auren mama na na karbawa d’aana mustapha?” Murmushi ya subucewa malam din,amma sai ya gaza cewa komai,baaba ya dora da bayani
“Mustapha na cikin yara mafi soyuwa a wajena kamar yadda mamana take,tabbas da dan adam keda ikon tsarawa dan uwanshu rayuwa bazan zabawa almustapha rayuwan da yake yi ba a yanzu,taimako nake da buqata ka yiwa yaronka mustapha,don Allah kada a hanashi,bari na gaya maka wanne irin rayuwa mustapha keyi da iyalinshi” hankali kwance baabaan ya zayyanewa malam komai,kai kawai malam ke kadawa,shi kam bai ma tabajin rayuwar aure ta tsantsar nasaranci ba irin wannan,baiyi yawon duniya ba bare ya santa,wadda tazo cikin qur’ani da sunna da wadda akeyi cikin kowanne gida a society dinmu kawai ya sani,shi da ko karatun boko bai bari anyi a gidansa ba banda zamani daya tilastashi ya bar halima da zainab sukayi candy,
“tabbas wannan wani taimako da jihadi zakayi sule,saboda yau da gobe tafi qarfin wasa,almustapha lafiyayye ne,yana da tarin dukiya wadda tafi tawa,kai duka cikin zuriyata babu mai dukiyarshi,’yammata na qasashe daban daban na sonshi koda ba soyayyar aure ba,yana da iko da ‘yancin yin komai,WA YASAN GOBE?,wa yasan gobe mai zata haifar,gwara tunda ina da ikon kawo gyara na kawowa rayuwarsa gyara ta hanya halastacciya” mamaki ke ci gaba da ratsa malam wamda ya haddasa masa kasa magana,wannan wace iriyar mace?,ita zata iya daga hannu tayi tutiyar ita din matar aure ce?,murmushi ya saki ganin yadda muntarin ya zuba mishi idanu yana jiran amsarsa,irin kallon wanda ke tsoron jin fitowar amsa mara dadi daga bakin wani
“Ba qaramar kunya ka sanya naji ha muhtari,yanzu don Allah ka cancanci ka roqeni kan neman auren mai sunan inna?,ashe ma ba daya muke ba,ashe ma yadda ka daukeni ban kai nan ba,sannan baka amince da yadda matsayinka yake a guna ba,har kwanan gobe muntarim ban sake aboki ko amini wanda nake jinsa kamar ni da shi tagwaye muke ba tunda muka rabu da kai,muhtari,ba almustapha ba,ko kai keson sumayya na baka ita halak malak bare tsatsonka,kai,ko moqocin maqocinka kesom sumayya wlh yaci albarkacinka,kana iya aurar da ita ma ba tare da na sani ba,NA BAWA ALMUSTAPHA SUMAYYA HALAK MALAK,amma wani hanzari ba gudu ba,sumayyan tayi aure ba guda daya ba har biyu harda yaro,kana ganin hakan ba matsala bace?” Kai yake kadawa
“Naji dadi sule,na gode da wannan karamcin naka,sumayya ko aure dubu tayi matuqar nace wa mustapha ina so ya aureta babu musu sai ya aureta,baaga auren budurqar ba anyi meye ne a ciki?,bazawara nada tata baiwar ta musamman kuma ta daban matuqar ta tsare mutuncin kanta tasan ciwon kanta,hankalinta da na budurwa ma kadai akwai banbanci,nasan mustapha cikin ‘ya’yana,ni inda nake kokwanto mamana,kada muyi abinda zai sabawa ra’ayinta” dariya malam yayi
“Muhtari kenan,wacce maman namu?,yadda kake da tabbas kan danmu almustapha haka nake baka tabbas kan maman taka” cikin farinciki suka saki dariya dukansu,hannayensu damqe cikin juna farinciki na shawagi da su cikin duniyarshi,tamkar baabaa ya tashi ya taka rawa haka yake ji,yau Allah yayi mishi baiwa manya manya guda biyu,ko yau Allah ya dauki ranshi tabbas ya cika masa burikansa,a hankali malam ya warwarewa baabaa labarin sumayyan da irin gwagwarmayar da tasha,tausayi da qaunarta ta sake yawa a ranshi,qimarta ta dadu,tabbas wannan itace macen aure,ba shakka irin wannan matar ita ta dace da a nema,ya godewa Allah data kusa zama halak malak din familynsa,wannan shi ya sake motsa baabaa ya dubi malam
“Sule,idan zai yiwu ina son a hada auren nan da na ‘yar uwarta,idan yaso bayan an daura a nutse sai ta tare ko bayan kwanaki nawa ne,ji nake kamar wannan damar zata subucewa mustapha” dariya ta subucewa malam
“Haba muhtari,tunda na bada sumayya wa almustapha duk duniya banga wanda ya isa ya maida wannan alqawarin ba,kawai ina ganin shi kansa yaron bai sani ba tunda naji kace yana can dubai wajen aikinshi,amma tunda sai kafi nutsuwa da hakan hakan za’ayi,za’a hada da zainab din in sha Allah,ubangiji ya tabbatar mana da dukkan alkhairi yasa wannan hadin ya zamo abun alfahari da farinciki wa zuri’ar ta da taka”
“Amin ya rahmanud dunya wal’aakhira” cikin madaukakin farinciki baabaa ke amsawa,shigowar mus’ab sitting room din shi ya katse sauran maganar da sukeyi,ya dan rusuna yana fadin
“Afuwa,baabaa sha daya na dare,nace ko nan zaka kwana mu mu wuce?”ya fada cikin salon tsokana,daquwa baabaan ya watsa masa
” baka gama fahimtar waye sule a gurina bane,da da hali kwanan zanyi,amma na tabbatar idan na kwana din kwanan zaune zamuyi ni da shi,don hira tsakaminmu ba mai qarewa bace,ni sai naga ma kamar daren yana gudu”dariya ya basu don babu wani gudu da dare keyi,idanuwanshi ne kawai,har bakin motarsu malam ya takowa aminin nashi masoyinshi,gab da baabaa zai shiga motar ya dubeshi Gobe ya kama saura sati guda kenan daurin auren ko?”
“In sha Allahu”
“To madalla,ina zaton gobe zan koma gida na sanarwa da mutanen gida muma mu fara shiri,don wancan auren da yayi ba’a qasar nan aka daura ba,hakan yasanya daidaiku ne suka je masu ikon zuwa,amma wannan karon d’aana zai auri diyata sai inda kati ya qare” dariya sukayi a tare,malam ya rufe mishi murfin motar yana mausu fatan alkhairi da fatan wayewar gari lafiya. 
       Sai da suka fara tafiya a titi sannan mahmoud ya dan zunkuda kadan,tun dazun daya tsinci maganar ake mintsininshi,so yake yaji shin abunda yake zato ne?
“Am….baba daurin auren waye kuma nan da sati guda?” Waiwayawa baabaan yayi ya dubeshi sannan yace
“Yayanku almustapha in sha Allahu” idanu suka waro mahmoud yace
“Shi da wa?”
“Diyar sule aminina sumayya mai sunan mama na” ya basu amsa kai tsaye,duk sai kasa furta komai,babu abinda ke yawo kansu irin halaye da tsare tsaren yayan nasu almustapha wanda babu wanda baisan halayyarshi ba,shin baabaa na shirin daura masa aure kenan baida masaniya da yarinya ‘yar afrika?,
“Yarinyar tayi,tayi wlh bata da makusa,ga nutsuwa ga hankali,koni a lokacin da na soma ganinta don dai kawai akwai alqawari tsakanina da rahma da tuni na saka kai” ya fada yana dan kauda ido waishi kunyar baabaa,murmushi baban ya saki,idan da sabo ya saba da irin wannan barkwancin tsakanin mus’ab da mahmoud,yaso ace haka halayyar mustaphanshi take kan barkwanci,saidai kowa da yadda Allah ya tsara masa halittarsa,suna hira da raha sosai da shi,sun maida shi tamkar kakansu,yabon da ya sake yi kan sumayya ta sake faranta masa rai,kafin ya sake cewa komai mus’ab ya muskuta yace
“Hmmm,dan gaban goshi,auren gata wannan karon za’a masa,yana can yana harkokinshi an nema masa aure,mu kuwa gamu nan tamu maganar ma ko ya ake ciki ne mahmoud?” Ya maida tambayar kan mahmoud,dole dariya ta qwacewa baabaa saboda salon yadda mus’ab din yayi furucin,daquwa ya watsa masa sannan ya dafa kafadarshi
“Kai ka jawo tsaiko da karatunka bai gama kammala ba,amma ku din ma ba zaku wuce nan da wata biyar ba” sai suka saki dariya kuma suna jin kunya,su kamsu sunsan yayan nasu yana buqatar dauki,sunsha rayawa a ranau idan sune ba zasu iya wannan auratayyar ba,saidai da yake maza ne babu wanda ya gayawa dan uwanshi ko suka zauna suka tattauna batun,saidai kowa yayi shida zuciyarshi,da haka suka qarasa gida ko zuciyarshi fes. 1

   ******   ********    ******
Washe gari tun tara na safe suka gama shirin fita ci gaba da shirye shiryensu,sabida a yau sumayya keson su gama rabon i.v saboda ta gaji,gashi uwa uba kuma so take da anfarawa zainab din gyaran jiki kada ta sake fita,tuni anty dije wadda yau tare zasu fita ta iso,tana wajen malam suna hirarsu ita da shi da yaya abubakar wanda yau bazai fita kasuwa ba ya taho gidan hira,amina ma na nan zuwa anjima don kusan gidan take wuni tunda satin bikin ya kama,sai da suka kammala sumayyan ta leqa falon malam din tana fadin anty dijen ta taso su tafi sun gama shiryawa don ma nafisa ta tsaidata ta tsaya amsa kiranta wadda ta tabbatar mata zata halacci bikin zainab,don zata zo kano dama gaida iyayen mijinta mahaifan auwal
“Jeki ki kira min babarku ku taho tare ke da ita” inji malam,haka kawai taji qirjinga ya buga,tashin farko jikinta yayi sanyi,ta juya zuwa bakin fanfo inda maman ke daura alwalar sallar walha ta gaya mata,qafafunta kawai ta kammala wankewa ta bita suka nufi dakin. +

       Sai da suka samu gu suja zauna suka nutsu sannan malam din yace
“Haqiqa na tabbatar da cewa duk wanda ya kwana ya tashi cikin gidan nan yasan abun farincikin da muka kwana da shi na bayyanar aminina,to bayan mun gama farinciki na ganin juna muna hira bayan ke sumayya kun shigo kun fita ya bijiromin da wata buqata,na sani kun san cewa duk da baku taba ganin muhatari ba amma kunsan muhimmancinsa gareni da irin shaquwa da halaccin da yake tsakanina da shi,ya bijiromin da wata buqata wadda na tabbatar yagi qarfinta a wajen iyalina,duk da nasan cewa haqqin sumayya ne amma na amshi buqatar hannu bibbiyu saboda nasan cewa na isa da ita sannan ba zata taba watsan qasa a ido ba” tun kafin yaci gaba qirjinta ya fara wata iriyar sukuwa,kanta yayi nauyi ta kasa dagashi,maganar da sukayi da shi kafin tahowarta kano da fassarar da anty dije tayi mata suka fara dawo mata daki daki
“Ya nemi na bawa yaronshi auren sumayya bisa wasu hujjaoji daya zayyanamin wadanda sun isa sun kai baya ga matsayin muhtarin a gurina a bashi auren ita sumayya,saboda haka na bada auren sumayya ga yaron nashi wanda za’a daura auren ranar juma’a tare da na zainaba insha Allah” wani kuka ne ya qwace mata wanda sautinsa yaso fitowa tayi hanzarin sanya hannu ta rufe bakinta,
“Alhamdulillah” kawai anty dije ke jerowq,kamar ta tashi ta taka rawa haka ta dinga ji,ta kasa zama waje daya sabida farinciki,ba shakka tana mai tabbatarwa kanta sumayyan tayi kyakkyawan gamo mai dauke da dumbin alkhairai
“Kiyi jaquri sumayya,na miki shishshigi,saidai ina mai baki haquri tare da neman alfarma kan ki yimin wannan alfarmar kada ki watsan qasa a ido” maganar malam din ta hadu ta sake yi mata nauyi a ka,duk da halin ha’ula’in da take ciki amma haka ta tattara kalaman
“Don annabi ka daina fadan haka malam,ka daina bani haquri,ni bani da wani da na cancanci a nemi alfarmata a kansa,kaine silata kai ka haifeni,duk yadda kayi da ni malam daidai ne,na tabbatar ba zaka taba cutar da ni ba,na amince na miqa wuya a gareka,roqon da nake maka kadai shine malam ka bini da addu’a,ka sakani cikin kowacce addu’a taka,Allah ya qarfafeni,ya hanani gazawa bare na watsa maka qasa a ido,na samu juriya mai yawa da zata kaini ga cika burinka” tana kaiwa nan ta gaza dairewa,sai ta fashe baki daya da kuka zucuyarta na tuna mata abubuwa masu yawa,wadanda suka faru da wadanda kan iya samunta a gaba,fata take Allah yasa SHAFUKAN KUNDIN QADDARARTA sun qare ashe akwai wasu sabbin shafukan kar a gaba,sai yaushe ne zata kammala bitar wannan kundi mai dan karen wuya da sanya zuciya da gangar jiki yin rauni,rauni kuwa bana wasa ba,ya barwa zuciya da rayuwa tabbai masu wuyar warkewa,masu wahalar sha’ani da sarrafawa tare da tanqwara zuciya a kansu,duk wanda ke dakin jikinsa yayi sanyi,sunsan mai take tunawa
“Insha Allahu sumayya daga wannan karon ba zaki sake kuka ba,da yardar ma duka lokacin dariyarki ne yayi,na tabbatar da cewa ban kaiki imda zaki wulaqanta ba,na kaiki ne cikim ahalin da suka gaji karamci da mutunci tun daga tushe,ko bana raye ina da yaqinin muhtari ya isheki uwa da uba ma baki daya,addu’a kuwa kullum kina cikin addu’o’ina,zaki rabauta sumayya da yardar Allah,tashi kije,Allah ya albarkaceki da dukkan wani abu da ya shafeki”
“Amin” baki daya mazauna dakin suka amsa,sai ta kasa tashi saida anty dije ta kamata,kai tsaye dakinta ta kaita ya zaunar da ita sannan ta zauna gefanta tana kallon yadda take kuka kamar hawayenta zai qare,bata cemata ta tafas ba har sai data soma tsagaitawa don kanta,bawai don ta gaji bane ko ta samu sassaucin da take son samu,ta tsagaita ne saboda yadda idanunta suka soma radadi da kuma yadda ta fuskanci antyn nason tayi magana da ita
“Sumayya kuka kike saboda auren almustapha?” Ta jefa mata tambayar kamar wadda batasan batun ba
“Na tabbata bakisan waye almustapha ba,banda haka da sai nace kukan da kike kin yiwa Allah butulci” jajayen idanunta ta daga ta kalleta alamar tamabaya,ciki yaqini anty dijen ke kada kai
“Tabbas abinda na fada hakan yake,kinsan irinsu mustapha suke tsada a wannan lokaci?,kinsan yadda mustapha ya tara managartan halaye kuwa?,kin taba tambayar kanki me yasa su’ad ke tsananin kishinsa duk da kishin banza take tunda batasan yadda zata riqeshi ba?,kin manta waye baabaa da karamcinsu?,kina zaton idan kika qi aurensa zaki ci gaba da zama haka ba tare da kinyi aure ba?,kinwa kanki wadan nan tambayoyin?” Kai take girgizawa bayan ta gama sauraronta,cikin rawar murya ta soma furta
“Anty a fuskata almustapha bashi da kirki,bai taba kyautata min ba ko sau daya,anty…kin manta yadda auren soyayya ke kayawa a wannan zamanin ina ga irin wannan?,baki daya almustapha anty ba ajina bane kamar yadda nake nima ba ajinsa bace,babu dacewa tsakanina da shi anty,komai nawa da nashi ya sha banban,ra’ayi yanayi al’ada wayewa da dabi’u,ta yaya zamanmu zaiyi daidai,baya ga haka ma baki daya anty KISHIYA!,kishiyar ma irin su’adah,kin manta anty ina kika baro wannan?,kin manta kishiya duk inda na shiga itace babbar qalubalena,bayan bansan me na musu ba,ko don ni yarinyace?,ko din bani da qarfin qwatarwa kaina ‘yanci,ko don ban iya mugunta da baqin hali ba,wadan nan sune 
dalilan?” Ta fada wasu hawayen masu dumi na bin kuncinta,hannunta anty dije ta riqe tsam cikin nata,madadin taga tashin hankali bisa fuskarta sai taga murmushi ne ma kwance kan fuskarta
“Almustapha?,ko ba haka bane sunanshi?,kin manta shi namiji ne?,namiji kuwa ko wayeshi ta bangaren zamantakewar auratayya dole ya sakarwa mata,ki manta da wannan ki cire rashin soyayya a tsakaninku a matsayin matsala,kishiya ita kike tsoro?,ina zaton zuwa wannan lokacin kin horu sumayya,meye yayi saura meye bakiji baki gani ba,sai d’ai d’ai,wannan karo ki sama ranki cewa kishiya ga gama yin nasara a kanki da yardar Allah,waccan karon ma dan dai kawai yana cikin KUNDIN QADDARARKI ne,ke mai bawa wata labari ne,dame kishiya zata tsorataki sumayya,bayan kina da Allah,kina da tsarkakakkiyar zuciya,ke matuqar su’ad ma ta baki tsoro sumayya ke kika so,ki kwantar da hankalinki damuwa ba taki bace,bakisan sirrin da Allah ya boye ba har ya turo baabaa dai dai wannan lokaci,bana son qara ganinki hawayenki daga yau” Kai kawai ta gyada mata ba don tana tsammanin samun salama cikin ruhinta ba,komawa tayi kawai ta lafe kan gado kanta na sarawa,ita kadai tasan me take ji,kai kawai take mirginawa tana jin nauyi da girmam zancan a qirjinta,su halima da zainab ne suka shigo a sanyaye saboda ganin yanayin sumayyan,antyn tace suje kawai ba zata samu zuwa ba ita da sumayyan,bata son ta tafi ta barta a yanayin da take ciki,wayarta dake gefanta tayi ruri,kiran abdur rahman ne,idanuwanta ta runtse tana kiran sunayen Allah,sai a sannan ya fado mata,me zata da shi?,me zata gaya masa ya yarda da ita,tabbas bata da abinda zata ce masa,hakanne ya sanya ta qyale wayar taci gaba da rurinta har ta katse don karan kanta,qarar wayar kawai qara mata ciwon kai yake,wanda zuwa lokaci wani zazzafan zazzabi ya rufeta ta kwanta sosai,saidai bata bari kowa ya gane ba. 6

  ******  *******    ********

       Tunda ya isa gida kafatanin al’umar dake cikin gidan suka fuskanci akwai wani gagarumin al’amari na farinciki da ya faru da mai gidan,tun daga manyan ma’aikata na gidan har qananu,take ya yiwa kowa qarin albashi sabida tsananin farinciki da nuna tsantsar godiyarsa ga Allah.

      Bai samu ganawa da matan gidan ba sai bayan sallar magariba,ya warware musu komai,babu abinda ummee tace,ita kanta tasan yaron nata yana da buqatar sauyin rayuwa,kawaici kawai irin nata yasa basa tsomala baki cikin lamuransa,saidai sauyi wanne iri?,sauyin zai yiwu kuwa ta wannan bangaren,bayan kowa yasan ra’ayim almustapha wajen zabar matar aure?,kai hasalima kaf tarihin rayuwarshi bashi da muradi ra’ayi ko sha’awar yin mata biyu sam sam,bata manta yadda ya dinga qananun maganganu sanda yayansu adam zai sake aure na biyu,saidai a tarbiyyarsu sam babu musu ko jayayya kan duk hukuncin da jagoran gidan ya yanke,saidai su tayashi bin dokarsa ko hukuncinsa,bangaren anty maamaa ma tayi farinciki,don a dan zamanta da sumayya ta karanci halayenta,ta kuma san ta sha banban da halayyar su’ad,saidai itama tata fargabar ta yaua almustaphan baqin bature dan ra’ayin riqau mai doka da qa’idoji zai amshi wannan lamarin,gashi uwa uba baban yaja kunnen kowa da kada wanda ya sanarma almustapha maganar shi da kansa zai sanar masa,kome meye tasan na dan lokaci ne zai wuce,to baki dayansun masu biyayya ne gareshi,sannan babu wanda baida burin ganin farinciki cikin rayuwar mustaphan. Anty farida da huda kam da suka ji lamarin har wani ihun farinciki suka saki,kasa zama sukayi sai da suka dangana da baabaan suka yi masa godiya tamkar su ya yiwa,murmushi kawai yayi yasan lamarin na damun kowa,koma dai meye shi ya fisu farinciki da shigowar jinin sule cikin tashi zuriyar.Gaba daya ta koma ta zama wata irin cikin kwana biyu kacal,duk wani kuzari da buri data ci na bikim zainab yayi nashi wuri,tsantsar tashin hankali take shiga a duk sanda ta tuna lamarin dake tunkarota,ko ya zata qare?,ko meye zai faru da ita wannan karo?,shine tambayar da take yawaita yiwa kanga,uwa uba Abdallah da ya tsaye mata a rai,ana ya gobe kamu nafisa ta iso gidansu,wani kallo take binta da shi tana tabe baki
“Ke yanzu sai kace wadda zatayi auren fari kamar wadda yau zata fara zama da kishiya shine kika bi kika susuce haka?,a haka zaki qwaci kanki duk kin fafa zabgewa kina ramewa?,amma wallahi kin bani kunya” cewar nafisa,daga kai tayi tana kallonta tare da mamakin wanda ya gaya mata zancan
“Me kike kallo na,munyi waya da amira ta gayan komai,ta kuma ce tana kiran wayarki amma kullum switchoff,na gaya mata zan shigo kanon tace na duba mata ke don Allah” ta sake fadi tana duban sumayya,fada ta zarce da yi maga,kuka ya qwacewa sumayyam,wau su don Allah ita kadai take gano abinda take ganowa,su basu hangen komai,ta gama fadanta sannan ta koma lallashinta,inda daga qarashe ita ta tilastata ta miqe tayi wanka tace zata rakata siyayya,jiki babu qwari haka ta shirya,ga zazzabin dake sakadarta a hankali,bugu da qari ga wani ciwon mara da ya saukar mata,wanda bata sani ba ko tashin hankalin da take ciki ne ya jawo shi oho. +

       Wani katafaren shago wanda ke saida kayan jiki na zamani nafisa ta kaisu,da idanu sumayya ke kallonta sanda take loda kayan tana zaba,harda wanda sumayyan yanzu ke amfani da shi tun wanda ta taba siya mata a uk har yau da shibtake amfani da yake ya karbeta,suna cikin mota take shaida mata yadda zata yi amfani da sauran,haushi ya kama sumayyam,yamzun suna nufim wami namiji zata yiwa hidimawa jikinta saboda za’a daura mata aure da shi
“Wallahi da kin gayan ni kika  siyawa bazan barki ba,sabida asarar kudinki kawai kika yi babu abinda zanyi amfani da shi cikinsu” a fusace nafisan tace
“Wallahi baki isa ba kinyi kadan,amfani da su wallahi ya wajabta a kanki” ganin yadda nafisan ta hasala ya sanyata yin shiru,saboda ko qwaqwaqwarar magana bata sonyi yanzu kanta zau fara sara mata.

       A bangaren baabaa kuwa shirin daurin auren yake babu kama hannun yaro,kai kace wannan shine karon farko da za’a yi daurim aure cikin familyn baabaa prof din,ana ya gobe daurin aure suka baro abuja suka sauka gidanshi dake kano,saboda ya kasance kusa da abokinsa,duk wanda ya dace ya san da daurin auren babu wanda baabaa bai aikawa ba.

       Duk abinda ake idanu ne nata sai ta koma ‘yar kallo sabanin daa da itace amara,katunan daurin aure masu dan karen kyau tsari da tsada baabaa ya sanya aka buga ya baiwa malam wani shima ya raba wani,duk wanda yaji daurin auren ya zama na mutum biyu harda sumayya sai yayi mamaki,saboda kowa yasan babu ita a batun,da kansa baba ya sanya cikin kwanaki hudu aka yima sumayyan akwatu uku na suttura wadanda zata sanya kawai bawai lefe bane,lefanta yace sai almustaphan yayi kamar yadda ya yiwa su’ad,kaya ne masu kyau da tsada dinkakku,kama daga shadda laces atamfa material sa sauransu. +

        Da ido kawai take binsu lokacin da aka zo yima amarya zainab lalle,almara kawai take ganin komai,wai ita za’a daurawa aure nan da kwana uku?,abinda ko cikin mafarki bata taba hasashensa ba,qememe taqi bada hannunta ayi mata komai,anty dije tace a barta kada a matsa mata,tasan cewa akwai lokacin da ita anty dijen da kanta zata sanya ayi mata kuma dole ta bada hannunta.

        Ana ya jibi daurin aure kwana tayi tana kuka saboda nasihar da mama tayi mata,ta gaya mata duk wanii motsi da zata yi wanda bai dace ba tamkar ta watsawa mahaifinta qasa a ido ne,ga gidan ya fara amsar baqi,haka ta tashi washegari da zazzabi da ciwon kai amma haka ta dinga cijewa tana shiga jama’a,wanda hakan bai amfana mata komai ba face sake qaruwar ciwon kanta.
          Bayan sallar isha’i tana kwance cam uwar dakan maman kan abun sallah,hasbunallahu wa ni’imal wakil kawai take ambata babu qaqqautawa saboda yadda taji nugun zuciyarta na daduwa,sallama taji anayi tsakiyar gidansu wadda ta sanyata miqewa dungur gur ta zauna tanq raba idanu kamar wadda aka ritsa da wuqa a maqogaro,muryar abdur rahman ce,sai gabanta yaci gaba da faduwa ta fashe da kuka qasa qasa tana cusa kanta tsakanin cinyarta.

         Daga airphort direct gidan ya zarto ko gida bai nufa ba sakamakon mummunan labarin da ya sameshi ta bakin bahijja,kai tsaye aka yi masa iso falon malam wanda shigowarsa gidan kenan,a mutunce suka gaisa saidai kallo daya malam yayi masa yaga sauyi tattare da yanayinsa
“Ina fata lafiya malam abdur rahman” cewar malam din,kai ya girgiza cikin sanyin murya
“Malam,na jima ina neman yarda da amincewar sumayya tun kafin rasuwar yaya mukhtar har kawo yau din nan,na fara samun hadin kanta a kwanakin nan,saidai ta nemi alfarmar na bar maganar har ka kammala aurar da zainab,kwatsam sai jiya na samu labarin wai za’a aurar da sumayya malam haka ne?” Kai ya jinjina kafin yace
“Wannan haka yake abdur rahman,zan aurarwa dan aminina sumayya,sam banyi tunanin kana ci gaba da neman sumayya ba abdur rahman,ban kawo haka a raina ba” sosai ya girgiza da jin amsar malam din,idanunsa suka kada ya dubi malam din
“Malam ni nafi cancanta da sumayya,ka yimin alfarma ka aurar min da ita” cikin tausayawa malam din ke dubanshi Kayi haquri abdur rahman,wannan wanda zan baiwa sumayya wa familynsu sunfi qarfin na musu haka,idan da wani ne can daban babu abinda zai hana na maida auren kanka,amma zan gaya maka kadan daga labarin muntari,zan gaya maka kadan daga cikin waye muhtari a gurina” warware masa yayi DANGANTAKAR dake tsakaninsa da baabaa prof,dangantakar kuma da suke fata da burin ba zata sake katsewa ba har ABADAN,wanda hakan suna burin ya zama hanyar ci gaba da yado da qarfafa zumunci da dangantakarsu. 1

        Cikin gamsuwa abdur rahman yakw gyada kai,babu shakka irin wannan dangantaka dake tsakanin malam da muhtari ko shine idan yana da diya abinda zai iya faruwa kenan,ba zaiso ya zama silar datse wannan kakkaurar tsohuwar igiya ba da ka qullata tun duniya na kwance,tun basu gama sanin su waye su ba kawo yau,saidai rabuwa da sumayyan ba abu bane mai sauqi tattare da shi,wani mugun ciwo ne da zai ci gaba da illata shi
“Shikenan malam,ina muku fatan alheri,saidai mu a tayamu da addu’a,Allah ya bamu haqurin jurewa” ya fada cikin karyewar murya
“Allah ya yi maka albarka,ya sanya juriya a zuciyarka,ya musanya maka da wadda ga fita alkhairi a gareka”
“Amin malam,na barka lafiya” ya fada yana mai miqewa,cikin tausayawa malam din ya bishi da kallo,har ya kai qofa ya kirashi ya dawo ya tsugunna kansa a qasa
“Abdur rahman”
“Na’am malam”
“Idan har babu takura kuma ba zaka damu ba,mai zai hana ka nemi halimatu ‘yar uwar sumayyan,a tunani kamar zata iya maye maka gurbinta”
“Indai malam kana ganin hakan yayi daidai bazqi haifar da wata matsala ba na karba,ina kwadayim zuriyarka ne malam,na tabbatar akwai alkhairi ga dukkan wani d’aa da ya fito daga gidan nan” murmushi malam din ya saki cikin jin dadi
“Kayi tunani a nutse,kada kayi abinda kasan zaka takura,idan halima tayi maka ka dawo zan baka ita,idan bata yi maka ba babu komai zan biku da kyakkyawar addu’a”
“Ta yaya malam zanqi jininka,halima jininka ce jinin sumayya,na karba malam,kuma in sha Allahu a gobe zan bada sadakina nima kada itama na rasata”murmushi ya subucewa malam,sosai ya sanya musu albarka tare da jan doguwar addu’a ta fatan alkhairi a garesu baki daya,yace yaje sitting room a bude yake zai turo masa haliman,miqewa yayi kansa a qasa yana yiwa malam din godiya,abun mamaki cikin qanqanin lokaci tashin hankalin daya tsinci kamsa kaso dari sai yaji babu hamsin ciki,ya taka ya fice sitting room din gidan yana jiranta. 5

      Malam yana daga falon ya qwalawa haliman kira,gama cire lallenta kenan taji kiran malam din,ta goge hannum nata ta sanya hijabinta ta shiga dakin
“kije sittin ro abdur rahman na jiranki” jin maganar tayi banbarakwai sai ta daga kai ta dubi malam
“Ni ko yaya sumayya dai?” Daquwa ya mata
“Dan gidanku na kasa gane sumayyan sai ke zan kira?,ke nace ba sumayya ba” bata sake cewa komai ba ta miqe ta fito ta nufi sitting room din gabanta na faduwa. Tsaye yake tsakiyar sitting room din hannayensa goye a bayansa ya zubawa qofar shigowar idanu,tana sallama suka hada ido,karom farko taji wata faduwar gaban da bata taba jin irinta ba don ta kalleshi,idanu ya zuba mata yana amsa sallamar,sai yake hango yanayinta da sumayya muraran,ya taba kula da hakan shekarun baya amma ba kamar yanzu ba,ga mamakinsa murmushi sai ya subucewa lebansa,ya zuba mata ido yana ci gana da kallonta har ta qaraso gabanshi,cikim diriricewa tace
“Ya abdur rahman gani…..malam yace wai…..kana jira na”
“Bismillah zauna” babu musu ta taka ta zauna kan daya daga cikin kujerun,gabanta ya iso a hankali ya zube a gabanta wanda hakan ya sake haddasa mata faduwar gaba da,sai ta jita ta takura sabida basu taba zama gab da gab irin haka na,duk a qasa yake zaune a gabanta amma yana kusa da ita
“Halimatus sa’adiya,malam baice miki komai ba?” Kai ta gyada da sauri sabida ta gaji da yadda gabanta ke faduwa,murmushi ya dan saki,wato shi zai yiwa kansa yaqi kenan ko?,daga idonsa yayi ya zubesu a kanga,sai ta janye nata idanuwan
“Halimah kina sona zaki iya aure na?” Taji tambayar babu zato na tsammani,ido ta zaro tana dubanshi,kasa cewa komai tayi har sai da ya maimaita,bakinta na rawa tace
“Yaya abdur rahman…..yaya sumayya…..ita yaya sumayya fa?” Murmushi ya saki
“Bakya gidan ne?,bakisan malam ya bata wani ba?,ni kuma a yanzu malam ya bani ke zaki iya aure na?” Shiru tayi gabanta na faduwa,yayin da kunya ta kamata ta sadda kai qasa qwalla na taruwa a idonta,hakan taji tsoro ya kamata,malam zai aurar da ita kenan itama,jin shiru ya sanyashi sanya yatsunsa ya daga fuskarta,kallo daya tak yayi mata ya fuskanci ta karbi lamarin duk da bata bayyana ba muraran sabida kunya da tsoro
“Kice wani abu mana halimah,koda baki sona ki amince min zan saki ki soni kinji,kada nayi asarar zuriyar malam baki daya ace na rasa ko daya,da wallahi barin garin zanyi” dariya taso qwace mata saboda yadda ua shagwabe mata,kunya ta lullubeta saita qudundune kanta cikin hijabi,dariya ya saki
“Iyeeee,ko baki ban amsa ba ma na gano a bata,ashe dai har kunyar abdur rahman din akeji,lallai na samu karbuwa,koba haka bane?” Shiru tayi taqi amsa masa
“Shikenan tunda ba zaki ce komai ba bari na haqura na tafi,kuma ba zaki sake ganina ba,zan kuma gayawa malam baki amince ba sai na haqura” ya fada kamar mai tafiyar,da sauri ta daga kanta tana shirin cewa wani abu,sai ta ganshi tsaye a gabanta,kunya ta sake kamata tayi qasa da kai suna dariya baki daya. +

       Komai na Allah ne haka komai nufin Allah ne,sai gashi ya shantake har qarfe tara da rabi yana gidan,halima akwai kunya saidai alamu baki daya sun nuna ta karbeshi,sai goma saura sannan yayi mata sallama,ya zuba hannayensa a aljihu yana dubanta
“Ina wayarki” cirota tayi daga hijabinta,karba yayi yana qoqarim cire layin ciki ya zura a aljihunaa sannan ya ciro daya daga cikin layukansa ya saka mata yana cewa
“Gashinan,ni kadai zan dinga kiranki kafin na siya miki wani layin,ina da kishi bana son wani ya sake jimin muryar mata ta,sai da safe muje na rakaki” har bakin qofar shiga tsakar gida ya rakata sannan ya juya ya fice,zuciyarsa fes yana mamakin lamarin Allah,ya riga ya qaddara sumayya ba matarsa bace shine masanin GAIBU mai rubuta QADDARAR BAYINSA,Allah kenan mudabbirul amri mai jujjuya al’amura a lokaci da baka zata ba,ya shigo gidan cikin tashin hankali da jimami ya fita cikin farinciki da annushuwa,babu abinda zai cewa dattijon arziqi mai karamci sai godiya tare da yi masa fatan kyakkyawan qarshe.

        Tana shiga tsakar gidan taga shigar zainab dakin mama wadda ta fito daga kitchen ta dafawa sumayya tea,da sauri tabi bayanta don fatinciki ke cinta,bata da ‘yar uwar da take sharing sirrikanta da ita kamar zainab din,tsaye ta taddata tama fifitawa sumayya tea din,sam halima bata kula da sumayya dake dakin ba ta dane bayan zainab wanda hakan ua sanya tea din hannunta tangal tangal zai zube
“Wayyo zainab,yau Allah nima ya bani yaa abdur rahman,zainab mallam ya bawa abdur rahman ni,a gobe nima zanbi sahunku zan zama matarshi” sak sumayya tayi tana dubanta,tun dazun take jira taji wani abu daga wajen abdur rahman din ko malam amma taji shiru,gani tayi zainab tayi shiru kawai saita sake kallonta
“Baki ce komai ba ya kikayi shiru” da idanu tayi mata alama da wani na gun,ta wurga idonta saita hangi sumayya,da sauri cikin jin nauyinta ta juya zata fice,cikin kasalalliyar murya tace
“Zo yaki halima” cikin jin nauyinta ta iso inda take ta zauna,ta karbi tea din da zainab ke miqo mata ta aje gefanta
“Meye na jin kunyata halima kamar wadda ta aikata haramci,wallahi har ga Allah naji dadi da wannan hadin da malam yayi,sannan abdur rahman ya cika mai sonmu tsakani da Allah da son iyalan gidan nan,ki saki jikinki ni yayarku ce har abdur rahman din ba tun yau ba dama,ki manta da cewa abdur rahman ya raba sona,Allah shine dama yasan abinda ya boye shi yasa bai taba darsamin soyayyarsa ba ko qanqani,illa ganin girma da mutuncinsa da nake,babu wani abu da ya isa shiga tsakaninmu,dan uwa ba wasa bane,idan banda Allah babu wanda ya isa yayi maka kyautar dan uwa,Allah ya baku zaman lafiya ya tabbatar da alkhairi”
“Amin” suka amsa baki daya,taji dadin addu’ar sumayyan sosai,to tsakanin daren zuwa wayewar gari sun sake wata qwaryar
qwaryat shaquwa,kusan kwana sukayi suna waya sumayya na jinsu,wadda tuni ta goge duk wani abu da ya shafi abdur rahman daga wayarta,tayi lamo bisa gado,kewa ta kamata,ta dinga matse hawaye tana tuna mukhtar,mutuwa mai tonon silili,idan banda mutuwa ta dauke mata shi da tuni sun jima da shimfida sabuwar rayuwa,wataqila ma da tuni ta sake haifa masa ‘ya’ya,saidai tsarin Allah shine tsari,(Allah kasa mu dace ka cika mana burikanmu kasa mu cika da imani don alfarmar sayyadina rasulullahi S A W)amin. 
        Washe gari kawu da wansa da qaninsa mahaifin abdur rahman sai gashi da safe yazo nemawa abdur rahman din auren halima,wanda ya bawa malam dariya,yace ai da abdur rahman da halima duka nashi ne,ko basu zo ba sai ranar daurin auren ya riga ya bashi ita,a nan kawun yayi godiya qwarai suka tafi,a nan suka bar abdur rahman ya sake baje kolin soyayyarshi,sai da aka soma nemansa a asibiti sannan ya tafi,binsu sumayya take da kallo,wato bawa bai gujewa Qaddararsa.

     *KUNDIN QADDARA*

     Rana bata qarya saidai uwar diya taji kunya inji malam bahaushe,wannan haka yake,domin yau take juma’a wadda ta kasance rana ce mai girma da muhimmanci da kuma dumbin tarihi wajen malam sulaiman gombe,wanda zai aurar da duka diyoyinshi mata da Allah bashi cikin mutunci da rufin asirj,wanda abun farinciki ne da godewa mahalicci a irin wannan zamanin namu mai cike da rudi da abubuwan firgici ga ‘ya’ya mata Allah ya yi maka baiwar aurar da diyoyinka mata baki daya hannun nagartattun maza da kake saka musu ran zasu musu riqo na mutunci,ta hannu daya baabaa prof shima cike yake da farinciki,domin kuwa tun qarfe tara ya iso wajen a maimakon qarfe goma da za’a daura auren. Daga cikin gida kuwa tuni zainab ta yi wanka kwalliya irin ta amare,tana sanye da wani lace mai azabar kyau wanda sumayya ce ta siya musu,haka amarya halima na sanye cikin shadda wadda ready made ce abdur rahman ya aiko mata da ita,tayi mata kyau ainun,dukkaninsu idan ka dubi fuskokinsu qunshe take da fara’a sabanin sumayya dake kwance ko wankan ma bata kai ga yi ba,binsu take da idanu tana rayawa cikin ranta,kowa yana rayuwar farinciki banda ita,ita kadai ke fadawa halin jarrabawa cikin yaran gidan nasu?,nafisa ce ta sanyata a gaba wanda tilas ya sanyata tashi tayi wanka ganin tana son qara mata ciwon kai,ta fitar mata da wani dan banzan lace cikin kayan da aka kawo mata dinkin skert da riga mai dogon hannu,kamar yadda ya qawatu lace din haka ya qawatata ta,babu abinda ta shafa banda turare mai da hoda amma sai ta fito cas gwanin sha’awa,fuskar ta tayi fayau ta dashe tare da ramar da tayi,naji ance amarya daban take ko batayi kwalliya ba,to kusan hakanne ya tabbata ga sumayya,komawa tayi ta kwanta abinta,don hayaniyar data cika gidan kadai ma damunta take bare ta waje,wanda tuni layin ya soma dinkewa,tana iya jiyo kwaroroto da muryar maroqa iri daban daban,sun baje hajarsu kowanne yana kwasar rabonsa,basa wasa da bikin daya shafi gidan professor mukhtar muhammad adam,don idan kazo a sa’a wani daga ranar ya daina roqo sai ya samu jarin da zai isheshi sana’a,ballantana yau da sunan almustapha ya bayyana baro baro na cewa shi zai sake aure. +

       Cikin qanqanin lokaci layin ya cika ya tumbatsa da jama’ar baabaa prof,jiniya iri iri ke tashi wadda ta qusoshin gwamnati ne da jami’an tsaro,kowa yana iya jiyo yadda daurin auren ke kayawa sakamakon maroqan dake bayyana dukkan abinda ke faruwa a wajen,auren zainab sulaiman gombe aka fara daurawa da angonta abulkhairi muhammad bala kan sadaki dubu talatin,sannan aka daura na halimatus sa’adiya sulaiman gombe da angonta abdur rahman Ahmad yusuf kan sadaki naira dubu hamsin,daurin auren qarshe shine na doctor muhammad almustapha professor mukhtar adam gombe wanda aka daura kan sadaki naira dubu ashirin,sai kuma kyautar mota duka cikin sadakinta take,daidai kunnenta nafisa tazo ta rangada guda,jin gudar take kamar ana zaqular qwaqwalwarta,saita dunqule ta cure waje daya,ta saki wani marayan kuka wamda bai fidda sauti,ita kadai yasan me take ji cikim zuciyarta,shikenan yau din ta sake zama mallakim wani bayan mukhtar?,wanin ma da baisan daraja ko qimarta ba,ya zata kaya musu?,ya zata kasance?,bata da amsar wannan.

       Kusan ranar haka ta wuni,da daddare ta dauki kayan sawarta kala uku ta gudu gidan anty dije,a can ta barje kukan ta son ranta,saboda a can babu dama saboda idon mutane,itama antyn batasan tana nan ba,sai wayar mai gadinsu ta ara ta gayamata don kada su nemeta,washe gari aka sha yini sosai,duk abin nan da ake sumayyan na gidan anty dijen,haka ta wuni kwanciya don mai gidan baya nan,ita kuma antyn a can gidansu ta kwana,sai gobe zata dawo idan an kai amarya,halima itama sai next week za’a kaita,kafin nan an kammala yi mata tata siyayyar.
*******     ******   *******
       Zaune take a uwar dakan anty dije wadda jiya bayan kai amarya ta dawo gida,tana ta faman shirya kayansu cikin trolly abinta,sumayya na zaune daga bayanta,sanye take da doguwar riga ‘yar kanti mai qaramin hannu,kanta ba dankwali sai gashinta mai baqi da santsi data hade cikin ribbom,jingine take da kujerar dake dakin qafafunta amiqe,hannunta riqe da cup din tea wanda tun dazun aka hado mata shi har yana gab da hucewa bata yi masa kyakkyawan shaa ba,idanuwan nan a kode tamkar danyen nama kamar yadda fuskarta take a kode alamun ko yaushe cikin kuka take,sam anty dije taqi bata fuskan kawo wani qorafi ko wata magana kan auren,tunda dai an riga an daura ta riga data zama matar almustapha,abu guda ne kawai yanzu a gaban anty dijen yadda zata shirya diyar tata fes ta iya shiga kowanne bigire na rayuwa,abinda ke sake karya zuciyar sumayya yadda taga ita antyn ma murnarta take,hannunta
1take,hannunta tasa ta shafa gashinta hadi da lumshe ido tana kiran sunan Allah qasa qasa,ita kadai tasan meke yawo cikin kwanyarta,kamar ta cire qwaqwalwar ta huta haka take ji,waiwayowa antyn tayi tana cewa
“To zaki bimu abujan ne ko kuwa sai munzo daukar amarya?” Mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki,aisai kawai ta saki kukan ta sosai ta dire cup din tea din,baki anty dije ta kama dariya na subuce mata
“La’ilah,ku jimin yarinya,wai ita bilhaqqi da gaskiya bata son almustapha,mutumin da ake so ko kallon arziqi ya yiwa wasu,to wallahi saidai kiyita kukanki kada ki fasa bazan lallasheki ba,tunda kinqi jin lallashi ballantana shawara,da kinsam tun usilu ba zaki iya biyayya wa su malam ba ai da kin gaya musu tun sanda suka tasamma hada auren,sai yanzu saboda yankan baya zaki tasani gaba da kuka me zan miki,haka zakije ki yi gaban su’ad din,tabdi wallahi da kuwa kin jawa kanki,idan kin gama kukan kya tashi kiyi abinda ya dace,don tun jiya malam ke tambayarki bai gqnki ba zai damqa miki sadakinki” anty dijen ta juya tana ci gaba da aikace aikacenta har sanda laila ta shigo da wayar sumayyan hannunta tana fadin
“Anty amira ce a layi” ta miqawa sumayyan,harara ta danqara mata hakan ne ya sanya anty dije karbar wayar ta kara a kunnenta bayan ta sanyata a handsfree tana fadin
“Ai amira kema ta shafeki ba zata amsa wayarki ba,ke da jin muryarta sai bayan wani lokaci”dariya ta qyalqyale da ita
” don Allah anty matsa kusa da ita nayi kata waqar ta zama ta zama,nima haka ta yimin,ranki ya dade amaryar yayanmu ayi mana haquri,amma dai ya musty ne ya riga ya zama mijin sai haquri,anty barta ko bata yi magana ba yanzun zata yi idan muka zo sayan baki”dariya suka sanya baki daya,hakan ya sake qular da zuciyar sumayya,sai ta miqe ta fice tana kuka muraran kamar wata qaramar yarinyar,binta anty dije tayi da kallo tana dariya,har yau da sauran quruciya sosai tattare da sumayyan,gata nan a zahiri ta bayyana. +

         Tunda aka daura auren ranar juma’a baabaan bai bar kano ba har zuwa yau litinin,misalin qarfe takwas na dare bayan ya gama cin abincin dare ya dauki wayarsa ya soma lalubar musty man.

         Dawowarshi kenan daga asibiti,yau a gajiye yake saboda mutum uku ya yiwa c.s,kayan jikinsa kawai ya cire ya rataye suit dinshi a inda yake rataye kayan da za’a wanke masa,ya zaluqo daya daga cikin towel daga ma’ajiyar towel ya daura sannan ya shiga wanka,kwanciyarsa yayi luf cikin ruwan wankan mai azabar dumi da qamshi,duminsa na ratsa kowacce gaba ta jikinsa,idanunsa na alumshe sai ka rantse da Allah bacci yake saidai idanunshi biyu,tunani ne kala kala kan kwanyarsa yake yawo,ya soma gajiya da zaman wannan hotel din wanda kusan a ciki yake rayuwa,duk da yana da gida mallakinsa cikin qasar,saidai hakanan yafi sha’awar zamam hotel din yana ganin kamar ya fi masa sauqi,idan gidan ne dole sai ya nemi ma’aikata da zasu zauna cikin gidan su kula masa da tsaftarsa da komai da komai wanda shi ba kasafai yake son ma’aikata haka barkatai ba,musamman a qasar da ba taka ba,tun yana cikin bayin ya dinga jin rurin wayarshi,data katse wani kiran ke shigowa,sai ya saki tsaki ya sake gyara kwanciyarsa ba tare da koya bude idanunshi ba bare yayi haramar fitowa,ga 
tsammaninshi su’ad ce don kimanin sati guda rabon da ya nemeta,ta kirashi dazu zai shiga thiather ya dakatar da ita,saboda abu na farko data fara da shi shine mitan ya watsar da ita sabida ta koma zata qarasa karatunta,shikam a yanzun yana ganin matsalarta ce,shi ya gama da wannan issue din,sabgogin dake gabansa ma kawai sun shasa masa kai,sai da ya kammala wankansa a nutse sannan ya fito ya daura towel dinsa a qugu wanda hakan ya fito da dukkan suffa da zatinsa na cikakken namijin da ya amsa sunanshi,ya qarasa wani sashi daban ya daura alwala ya fito. +

        Zai gifta wayar kenan ta sake ruri,ya waiwaya kadan ya dubeta sai yaga sunan abbu na yawo saman screen din,sunan da ya sanyawa baabaa prof kenan,da hanzari ya fasa abinda yake ya isa ga inda wayar take ya daga cikin girmamawa tamkar yana gabanshi cikinnn nutsuwa da sanyin murya
“Barka da warhaka” ya fadi
“Barka kadai,ina ka shiga ne haka tun dazun ina kira ko kana asibiti ko company?”
“A’a wanka nake” ya fada a taqaice,don a tsarinsa bai fiya doguwar magana ba,kadan ce mai ma’ana
“To madalla”
“Lafiya kuke baabaa ya kowa da kowa?”
“Kowa lafiya qalau yake almustapha”
“Masha Allah”
“Ammm,almustapha kawai tsarin zuwanka gida ne nan kusa?” Dan jim yayi kafin ya amsa
“A’ah,saidai ko idan kana son ganina ne?” Yana mamakin yadda yake da kaifin qwaqwalwa da cimma abun tun kafin ka kammala bayaninka,sau tari suna fara magana da baabaan yake gane mai yake da buqata tun bai qarasa ba
“Tabbas,ina buqatar ganinka,wani muhimmin batu ne ya taso ma rayuwarka nake so mu gana a kai,yaushe kake da chance din zuwa?” Duk da maganan ta dan sanyashi a duhu amma bai da niyyar tambaya
“Yaushe kake son gani na?”
“Eh to,ko kamar nan da sati biyu haka”
“Sati biyu masu zuwa ina zuwa da yardar Allah”
“To masha Allah,Allah yayi maka albarka,sai kazo”
“Amin,na gode” a hankali ya ajjiye wayar yana binta da kallo,zuciyarsa na son sawwara masa muhimmin batun da baabaa yace ya taso wa rayuwarshi,duk iya hasashensa bai canka ba,hakan ya sanya ya dage kafadunsa biyu na rashin damuwa ya nufi inda ya ajjye kayan shafarshi a tsare kamar wata mace,komai nashi mai aji da tsada irin wanda maza ke amfani da shi,yana shiryawa yana tunanin yadda tafiyan zata kasance,dama yana son zuwa daya daga cikin asibitocinsa dake kano kwana biyu bai leqa yaga maike faruwa ba shu da gidan marayunsa,duk da yana da wakili dake gano duk abinda ke tafiya kuma a kai duk abinda ake da buqata wuraren,amma bai saki komai ba balle kowa yayi mishi yadda yaga dama,mutum ne shi mai doka da qa’ida baison kuma a saba masa ko a taka mishi kamar yadda bai taka dokar kowa.

       Yana shiryawa yana kiran lambobin da ya saba kiran idan yana buqatar abinci,duk da sun san kusan cimarsa ta dare,ba wani abu mai nauyi yake ciki ba,a ladabce suka amsa buqatarsa ya kashe wayar,wanda kamar jira ake ya kashe wancan kiran wani kiran ya shigo,su’ad ce da layinta na america,yana kallon kiran yayi banza da shi har sai daya gaji ya katse,haka ta dinga kira har ta hada masa wajen miscal biyar,wanda tuni ya maida wayar silent don baison hayaniya,daga qarshe saqon tex ya shigo yasan kuma daga ita ne,baibi ta kai ba ya share ya tada shafa’i da wuturi,da wuri yake son kwanciya yau ya huta sosai saboda gobe yana da meeting da ma’aikatan companynsa na saqar abaya.

To masu karatu yanzu fa kusan aka soma ko?,

About Ismail

Check Also

QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 29

QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 29 Shuru amiran tayi tana duban sumayya cike da qwarin gwiwa da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *