[Advertisements⬇️]

QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 28 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

QADDARAR SUMAYYAHCHAPTER 28

Kwanaki nata tafiya,tun tana a takure da zaman garin har tazo ta fara sakin jiki,abu daya ke damunta kewar abdallah,tausayinsa take hakanam tausayinsa ya ninku a zuciyarta tun daga randa ya rasa mahaifinsa,kullum takan kira a bata shi su gaisa susha hirarsu,abinda ya sake kwantar mata da hankali a nan ba inda take zuwa bare ta gamu da wani yace mata yana sonta,hakanan kiran waya ma da ake ana nemanta tun ranar da anty dije tayi magana aka samu sauqim kiran,sai jifa jifa shi din ma ba dagawa take ba,abdur rahman ne kadai ke kiranta su sha hirarsu har ta riga da ta saba,babu wata rana da zata fito ta fadi bai kirata ba,ta sake sosai don bai qara yi mata wata magana daban ba banda ta zumunci,anty dije tayi ta mata tsiyar batasan muguwar kifin rijiya bace ita sai yanzu,bata son zuwa ko ina,ko gidan baabaa prof shigarta biyu kwata kwata shima da dalili na farkon kiran laila da taje,na biyu kuma da sumayyan tayi dambu gidan ba yara ta sata ta kaiwa anty maamaa da yake ita mai son dambu ce,kota shiga din ma bata wuce minti biyar ko goma ta fito,hakan ya sanya anty dije ta bada sautun kayan turare da humra aka kawowa sumayyan ta soma yi a nan,cikin designers kwalabe take zubawa,nan take kuwa ta soma ciniki,duk da wani gu ake kaiwa,’yan unguwar ne kawai ki zuwa siya cikin gida. +

Yau ma kamar kullum babu yara a gidan suna makaranta,gab suke da fara jarabawa ayi musu hutu saboda gabatowar wata mai alfarma na azumin watan ramadan,suna zaune da anty dije a kitchen tana anty dijen ke girki yau sumayya na ganin yadda take yi din don bata iya irinsa ba,iya zamanta da anty dijen ta qaru da abubuwa da dama ta fannin zamantakewar gida,girki iri iri,gyaran jiki da kuma uwa uba iya gayu,wayarta anty dijen ta daga wadda ta fara ruri ta kara a kunne,ganin haka sumayya ta karbi yankan cabbage din da takeyi taci gaba,sai data gama sannan ta dubi sumayyan
Sumayya,inaga fa ke zaki miqawa anty maamaa humrar nan,kaya take hadawa kuma kinga yaran basu dawo ba” kasaqe tayi,sarai anty dijen ta gane bata son zuwa ne,bata san me yasa bata qaunar shiga gidan ba amma sai ta shareta,ta gane mai anty dijen ke nufi tilas ta miqe tace to,dakinta ta shiga ta sanya dogon hijabinta har qasa sannan ta jawo ledar data jera humrorin wadda anty maamaa ta bata tayi mata,saboda umrar azumi da zasu tafi ita da maigidan da kuma ummee,sai babban yaron gidan shi da matansa biyu sai qaninsa da tashi matar,sai manyan jikokin gidan su biyar duk da basu wuce shekara sha hudu zuwa qasa ba,duk laila aku(sunan da idan taso take kiranta da shi kenan kusamman idan tayi hali ) ke bata wannan labarin tunda ita ba shiga take ba ballantana ta sani. 2

Kamar kullum a hankali ta dinga ratsa gidan bayan sun gaisa da mai gadin dake gadin wannan qofar sa suke shigowa da yake akwai wata qofar ta baya,mutumin ya haifeta shi yasa take ganin girmansa,mutum me mai faran faran da son jama’a,duk da ganinsa da sumayyan baifi uku ba amma yana yabawa hankalinta yadda take rusunawa ta gaidashi,duk da yasan iyalan gidan alhj umar farouq ba baya bane wajen tarbiyya.

Kanta a qasa qirjinta na bugawa ta dinga kutsawa cikin gidan,batasan me yasa take yawan faduwar gaba ba idan ta shigo gidan,ko don tana ganin kamar akwai banbancin matsayi tsakaninsu bai kamaci ta dinga shiga musu gida ba. 2

Tazo mararrabar sashin anty maamaa data ummee sai taso ta manta wane waje ne na anty maaman don bata rarrabewa da sunayensu,a hankali ta juya idanuwanta tana canki canki,karaf idanuwanta suka sauka a kansu,zaratan samari ne ke tsaye su biyu suna magana da junansu,dukkaninsu dogaye ne saidai daya yafi daya masu matsakaicin jiki,kowannensu na sanye da t.shirt da trouser masu mabanbantan kaloli kowa da kalar nasa,farare tas da su kamar yadda ta dan fahimci haka kalar fatar masu gidan take,fuskar daya kawai taje gani bata ganin ta dayan kasancewar ya juya baya ne yana magana da dayan,da alamu kuma duk hankalinsa na kanshi,shima ya ganta,idanu ya sanya yana kallonta har waccan ya kammala fadin abinda zaice yayi gaba ya shige daya sashen.
Rudewa tayi kamar mara gaskiya,jikinta ya soma rawa ta fara qoqarin juyawa ta koma inda ta fito ganin kamar yana takowa inda take
“Wa kike nema?” Ya tambayeta fuskarsa ba yabo ba fallasa,cikin qoqarin daidaita nutsuwarta ta hada kalmar
“Sashen anty maamaa nake nema”
“Ko gun amira kika zo?” Ya sake tambayarta yana kallon ledar hannunta,bata ma gane wace amirar ba,sai tave masa
“A’ah,saqo na kawowa anty maamaa” sai taga ya saki murmushi
“Yauwa,muje ma na rakaki,Allah yasa wannan turaren mai dadi aka kawo mata wanda tamin alqawari” ya fada yana yin gaba cikin mishadi,ta bishi a baya tana cike da mamakin sauqin kai irin nasa,batayi tsammanin haka ba. +

    Falon suka shiga yana sallama cikin daga murya,wannan budurwar da take zaton ita ce amirar ta fito da sauri daga kitchen tana dariya,bata lura da sumayya dake bayansa ba,ganinsa ya sanyata tsaya tana dubansa tana qyalqyala dariya,da alama wani abu da ya faru dazun tsakaninsu taje tunawa
“Ya akayi yaya mahmoud?” Ta fada tana sake tuntsira dariya
“Zaki zo hannu ai kin sani…..yanzu ba wannan ba ga baquwa nan tazo wajen anty maamaa” dan leqowa amiran tayi inda sumayya ke tsaye,sai tayi murmushi
“Ba baquwa bace a gidansu umman khlipha take,duk da dai baquwa ce a gidan nan saboda na fuskanci bata son mutane” ta fada tana murmushi
“Ke kuma gaki da shegen kwashe kwashe ko,ki bata guri parrot tukunna,ki gayawa anty zan dawo anjima,yanzun yaa man ya aikeni ne” ya fada yana juyawa zai fice,ganin haka yasa amira daga murya
“Don Allah ya mahmoud ka siyo min na tuba” ta fada a shagwabe tana kama kunnuwanta guda biyun,harara ya watsa mata yayi ficewarsa,sai ta narke fuska kamar zata yi kuka har ya bace a falon kafin ta maida kanta wajen sumayya.
Murmushi tayi mata sannan tace
“Ga waje zauna,amma sai kin dan jira antyn don tana wajen dan tsohon mijinta,kinsan ba’a kiranta idan ya shigo sai mutum ya jirata” ta fada cikin salon tsokana tana dariya,itama sumayyan sai ta saki murmushi,kusan haka halayyar anty dije take,take mukhtar ya fado mata,a hankali sai murmushin nata ya soma gushewa damuwa ta fara bijiro mata,take ta fada kogin tunani tana tuna wasu lokuta masu dadi daga cikin rayuwar da sukayi tare da shi. +

       “Ga lemo bismillah” amiran ta fada tana ajjiye tray data dora lemo da kofuna a kai,kai sumayya ta kada cikin murmushin yaqe tace
“Alhamdulillah,a qoshe nake”
“Al’adar gidan anty maamaa ne,dole kisha wani abu kafin ta fito” ta fada tana tsiyaya mata a cup,kallonta sumayya tayi tana yaba karamcin hakan,sai a sannan taga kamanni da wanda ta kira mahmoud a dazu,da alama kwai dangantaka ta jini mai qarfi tsakaninsu,hannu ta saka ta karba tana fadin
“Na gode”
“Ba komai,bari na duba girki kada ya kama”
“To” sumayyan tace,kurbe daya tayi masa ta ajjiye damuwa ke sakadarta,a haka taji an bude wata qofa dake can wani sashe daban na falon,anty maaman ce ta fito tana cewa Ayyah tun yaushe kika zo” murmushi tayi
“Ban jima ba,ina yini” ta gaidata amsawa tayi tana zama tare da amsar ledar humrorin,budewa tayi tana shanshanawa tare da yaba yadda sukayi bala’in qamshi,godiya tayi mata sosai tamkar ba biyanta tayi ba,miqewa tayi tana shirin tafiya
“Umhmmm,za’a gudun ne?” Amira take baro kitchen ta fada tana dan murmushi,waiwayawa tayi tana dubanta itama fuskarta qunshe da murmimushin,sam batayi zaton zata yi sauqin kai haka ba
“Na baro aiki ne a gida shi ya sa”
“Ayyah to sai yaushe?,ko sai na shigo?”
“Allah ya kawoki lafiya”
“Amin,ni sunana sumayya na gaskiya,sunan mamar babanmu ce ake kirana amira,kefa?” Murmushi ta saki
“Nima suna na kenan?” Idanu amiran ta zaro gami da rufe baki
“Kai kai,dama baabaa na kusa ya ganki,yaga mai sunan mamarshi,yana son mai sunan mamarsa wallahi,me ake ce miki to?”
“Shi ake gayan” kai ta kada sannan tace
“Gaskiya ni bazan fadi haka ba,zan dinga kiranki kema da amira,amiran umman khalipha” dariya sosai sumayya tayi 
“Shikenan to” ta amsa mata sannan sukayi sallama ta juya da niyyar fita tana dariya amiran,kusan zasuyi shekaru daya da ita,saidai yanayin inda ta taso da gata sai take ganin kanta kamar qaramar yarinya,duk da aqalla zasuyi shekaru ashirin da daya. +

      A bakin qofar shigowa falon taji tayi karo da abu har yana bangazar kafadarta,da sauri ta ja baya tana fadin
“Subhanallah”
“Mtsweeeeww” taji an tsaki,baya ta sake ja tare da daga kanta tana kallonta wanda ita dinma kallonta take,saidai nata kallon yasha bamban da wanda sumayyan ke mata,kallon farko ta fahimci macace mai izza da jin kanta,haka yake don sumayya bata yi qarya ba,matashiya ce dake jin duniyarta dai dai,wadda a qalla ta doshi shekara ashirin da takwas a duniya,doguwa ce sosai hakanan siririya ce,fara ce itama sosai kamar yadda sauran suke,sanye take da wani baqin hight rise slim leg jeans da v neck t.shirt mai gajeran hannu,hakan shi ya fiddo surar ta da shape dinta baki 
daya,kanta yane da wani dan kwali mai santsi don ba za’a kirashi mayafi ba,idanunta saye da sun glases da ya kusa cinye rabin fuskarta,wani kallo take wa sumayyan na sama da qasa cikin izgilanci kafin ta zare gilashin nata,tsaki ta ja kafin ta wuce tana taku dai dai tana duban amira
“Maamaa fa?” Ta tambayi amira kamar bata son yin magana
“Ta haura sama” ta fada tana nufo sumayya dake gab da ficewa daga falon,da sauri ta daga murya
“Kiyi haquri sumayya” amiran ta fada cikin damuwa,sai ta waiwayo tana sake mata murmushi tare da fadin
“Kada ki damu”, sai da sumayyan ta fice sannan ta dawo da kallonta cikin falon ta saukesu kan wadda ta shigo din,sai ta kada kai kawai ta shige kitchen ganin ta zauna saman kujera tana jiran saukowar maamaan,ta sani sarai ba zata iya haurawa saman ba dama idan ba da wani qwaqqwaran dalili ba,shi ya sanya tayi saurin komawa kitchen don kada ma tace zata aikata. 1

      Tana hanya tana tuna irin kallon da ta yi mata,a qa’ida ita ta bigeta,ranta yaao baci amma sai ta dorama kanta laifin,ko ba komai ita tazo musu gida,tana isa gidan ta bawa anty dije labarin amiran,
“Amira kam akwai son mutane ai haka take ita da mahmoud ai mutane na ne”
“Eh kam na ganshi shine ma ya rakani wajen anty maamaa,yana da kirki sosai”
“Shine d’a na uku a wajen ummee”
“To ita amiran ‘yar waye ne anty,yau tana can gobe tana nan”
“Itama d’iyar ummee din ce”
“Ita ummin bata da yara ne?” Hararta tayi tana cewa
“Yau kin zama ‘yar jarida,to ban sani ba,ai baki son jama’a ne,banda haka watanki nawa a gidan nan yaci ace kin gama saninsu,tunda alhamdulillah mutane ne masu kirki karamci da son jama’a” dariya sumayyan tayi tana kame bakinta da yatsunta Ni dama amiran nake son na san ‘yar ina ce kuma an gayan” sai suka yi dariya anty dije na qorafin qib sakin jiki na sumayyan. +

       Da daddare dukkansu suna zaune a qasa suna cin abincin dare har da mai gidan,sumayya ce kawai ke zaune can gefe tana cin nata,babu yadda anty dije da uncle farouq baiyi ta dinga cin abinci cikinsu ba amma ta kasa,kunya gareta,bata da sabo sosai idan ba wajen yara qananu ko mutanen gidansu da suka taso tare ba,tun suna qorafi har suka suka haqura suka zuba ido a haka suka saba saboda sun lura halittarta ce ba zata sauya ba.

         Sai da suka kammala baki dayansu sannan hafiz yace cikin doki
“Abba,wanne albishir ne da kace sai mun gama cin abinci zaka yi mana?”idanu ya zaro yana murmushi yana duban hafiz din
” ummm,wannan zumudi haka?”
“Eh wallahi abba nima na qagu ya rigani fada ne kawai a baki” juyawa yayi yana kallon lailan,wannan karon dariya ce ta subuce masa
“Au kema?”
“Eh abba” ta fada itama tana dariyar,sai ya dubi anty dije
“Kefa madam?” Murmushi tayi tana gyara zama
“Ai yara sun gama magana,nima na zaqu inji wanne albishir ne?” Dariya ya sake yi
“Uhmmm,shine kenan to tunda bakinku yazo daya” ya fada yana gyara zamanshi,sumayya na gefe tana satar kallonsu,yanayin rayuwarsu tana burgeta,soyayya dake tsakanin uncle farouq da anty dije kullum kamar wasu sabbin aure,waiwayawa yayi ya fito sumayyan da hannu
“Taso kema ya shafeki” sai tayi qasa da kanta sannan ta miqe ta qaraso tana murmushi,gefan laila ta samu ta zauna,duk sukayi shiru suna sauraronsa.

     “Alhamdulillah,Alhamdulillah” ya fara cewa
“Wato a yau labari ya iskemu gwamnatin tarayya ta aiko da takarda ma’aikatarmu,ta zabemu mu goma zamu tafi london bayan sallahn nan mai zuwa da sati daya,zamu qaro karatu don samun qwarewa kan aikinmu na tsawon shekara guda” ya fada yana sauke numfashi,duk sai fuskokinsu suka sauya,kowa da abinda ya fara yawo cikin zuciyarsa,suna wassafa yadda zai tafi ya barsu da yadda zasuyi kewarsa,dariyan da ya saki ita ta maido hankalinsu kanshi
Jibi fuskansu,to gwamnati ta bamu daman tafiya da iyalanmu amma kada su wuce mutum hudu,shine babbar matsalar,gashi mu mun kai mu shida,tunani daya wa za’a bari da wa za’a tafi?” Shuru dakin ya dauka,murna ta soma komawa ciki,kowa na zulumin kada ace shi za’a cire,banda sumayya da farinciki ya mamayeta zata koma kano kenan har tsawon shekara daya,don dama ko a mafarki bata zaci ma zata bar state dinta ba balantana akai ga qasarta,ganin ba wanda yace komai sai sumayyan tayi gyaran murya don fidda abinda ke cikinta,dubanta uncle farouq yayi yace
“Ummm,me zaki ce?” A ladabce tace
“Dama uncle…..cewa nayi…..ni mai zai hana a cireni a lissafi sai na koma kano kafin dawowar taku?”
“Shawara bata karbu ba” anty dije ta fada kanta tsaye,sai ya saki dariya yana kallon sumayya
“To kinji abinda antynki tace” yana maganar tare da mai da hankalinsa kan anty dije
“To ke hajjaju mai zai hana cikin taskarki din nan da ake boyo ki dauki nauyinmu baki daya?” Ya fada cikin zolaya wanda hakan ya sanyasu dariya baki dayansu,sai da suka nutsa sannan yace
“Ni a binda nake gani,hafiz,kai zakayi haquri saboda karatunka a yanzu yake buqatar nutsuwa da dagewa,kai zamu bari a nan garin,sumayya kuma kema ‘yar mu ce,kinga kuwa mai ‘ya mace bazai dinga barinta wani gu ba,ni zan yi mata passport da visa a kudina,shikenan madam?”murmushi ta saki
” yayi yallabai,mun gode Allah ya saka da alkhairi ya qara arziqi”hafiz wanda sam baiji dadi ba har cikin ranshi,amma da yake yarone mai hankali da haquri,da wuya ka gane bacin ranshi sai yace
“A wanne gida abba Zan zauna?”
“Duk inda ka zaba,ko gidan inna(kakarsu da yake nan ya dawo da ita,ba wata tazara bace mai nisa tsakaninsu),ko gidan baabaa prof,kayi haquri kaji hafiz,girman kenan kaji?”
“Ba komai abba” ya fada,sai ya baiwa antu dije tausayi
“Ni har ka tunan ma abban laila,ina zuci zuci sukai sumayya ta gaidata,innan tace wai ba zata iya gane sumayyan yanzu ba”
Yana miqewa yace Kinsan tsufa sai a hankali,ai babu damuwa ko zuwa gobe ko jibi sai suje”
“Allah ya kaimu” injita,miqewa hafiz din yayi yabi bayan abban nasa da ya kirashi yace yazo ya karbi wani abu,take falon ya sarqe da murna,laila anata wassafa kai a jirgi,sumayya na dubanta tana dan murmushi duk da hankalinta ya kasu kashi biyu,ran qwashi anty dije ta zuba mata tace kota nutsu ko ta saka a cire sunanta a saka na hafiz take ta kame bakinta duk da bata fasa mutsu mutsun murna ba.
Falon anty dije ta basu tana fita laila ta dora daga inda ta tsaya,har gwada irin shigar da zata dinga yi take idan suka tafi,sumayya na gefe tana kallonta tana dariya,can qasan ranta kuwa tana ta jujjuya maganar,wai itace zata wata qasa wata uwa duniya a jirgi har london?. 2

       Suna haka hafiz ya fito daga wajen uncle farouq,fuskarsa qunshe da murmushi hannunsa dauke da laptop sabuwar qar,idanun laila suka fara kaiwa kai
“Laaah,ya hafiz sabuwar laptop abba yayi ne?”
“Wannan ba ta abba bace,tawa ce wanda ba za’a london da shi ba” ya fada yana zama tare da budeta ya kunna,tuni laila aka fara raba ido,ta matso kusa da shi
“Da gaske kake ya hafiz” hararta yayi
“Da da wasa nake miki” shiru tayi sannan daga bisani tace
“Allah ko nima na fasa zuwan ne a siya min,kada muje mu dawo dadi ya qare kai kuma ga abarka nan kama mora?” Dariya ta qwacewa sumayya,tana niyyar cewa wani abu anty dije itama ta fito daga dakin hannunta dauke da wata laptop dim,gefansu sumayyan ta zauna tana kallon hafiz

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

“Tofa,an samu nayi ko?” Murmushi yayi kawai yana danne dannensa dadi ya cikashi,sumayya ta miqawa laptop din tana cewa
“Ungo wannan” amsa tayi tana duban antyn
“Daki zan kai miki?”
“A’ah taki ce,abba laila ya siya miki yace zai miki bayani,akwai abinda ya shirya miki kan bunqasar karatunki yana so kiyi karatu ne da ita,idan mun tafi ina tsammanin akwai makaranta da zai sama miki da zaki koyi karatu ma shekara gudan,nasan baki da matsala ta karatu da rubutu duka kin iya,hakanan turancinki ba laifi zaki iya karantawa ki fahimci wasu abubuwan,fahimtar sosai da maidawa yadda ya kamata ne kawai matsalarki” qamewa tai a gun tana mamaki,to ita ya zata iya da wannan aba da uncle din ya mallaka mata,kasa magana tayi har sai da laila ta saki dan ihu tana karbarta daga hannunta
“Wayyo!,muma munyi computer,ya hafiz ka daina mana kallon banza” cikin sanyin murya da sake gasgata qaunarta da anty dije tace
“Anty na rasa wacce iriyan godiya zan muku,na gode na gode Allah ya saka muku da alkhairi,ya biya muku dukkan buqata ya jiqan magabatanku,ya hada kan zuriyyarku baki daya”
“Amin” anty dijen ta amsa tana shigewa ciki.
4

        Da sauri laila ta miqe ta jona mata chargy hadu da kunnata,tana da rawar kai hakan ya sanya ta iya laptop din kamar wadda ako koyawa,don suna game sosai a cikin ta muhsina daya daga cikin qawayenta jikokin gidan baabaa prof,nan ta fara duba games din ta ta tarar a ciki,ta zabi daya ta fara bugawa minal ta matso tana kallo.

        Daga bakin qofa akayi sallama,dukkansu hankalinsu na kan laptop din sai sumayua wadda ta amsa yana waiwayowa,amira ce ke shigowa fuskarta qunshe da murmushi,sanye take da black gown brided tube midi mai adon zane orange a jiki mai dogon hannu,kanta yane da mayafi medium orange haka plate shoes dinta,hannunta riqe da wayarta,fuskarta ba makeup saidai akwai alamun hoda da lipstic,bayanta wata matashiya ce,sanye da baqin skert da t.shirt ruwan omo dukkansu na yadi,sai dan madaidaicin hijab dake wuyanta,kallon farko zaka gane ‘yar aiki ce,eh tana daya daga cikin ma’aikatan gidan baabaa prof,qarasowa tayi cikin falon wanda hakan ya ankarar da su laila
“Anty amira ina wuni” suka gaisheta baki dayansu ta amsa tana zama gefan sumayya
“Kin ganni da daddare ko?” Murmushi kawai tayi tana janyo lemo da ruwa nata wanda tun dazun bata sha ba da suka gama cin abinci ta ajjiye gaban amiran tana cewa
“Bismillah”
“Um_um,a qoshe nake,shopping naje nayo sai nace bari na shigo,ina so dama na baki haquri ne kan abunda ya faru dazu” kusan ta mance ma ma ya farun
“Mefa?” Sumayyan ta tambayeta
“Bigeki da antynmu tayi dazu,kiyi haquri don Allah,antynmu ce saidai bata da kirki sam,kiyi haquri” murmushi ta kuma yi har fararen haqoranta na bayyana
Babu komai,ai karo mukayi”kai amira ta girgiza
” duk da haka,nasan halinta ai,kiyi haquri”
“Bafa komai” ta sake maimaitawa,maida dubanta tayi ga wadda suka shigo din tare,tana tsaye har yanzu
“Ki zauna mana” sumayya tace mata,murmushi tayi tace
“No madam,na gode”. Kan ta sake cewa komai wayarsu ta tafi da gidanka dake  kitchen ta fara burari,laila ta subi khalipha
” jeka duba khalipha”kanta na ga laptop don bata son a mata game over,da sauri ya miqe ya shige kitchen din minti daya tsakani ya fito
“Anty sumayya ke ake nema” yana fada alqasim ya fado mata,fuska ta tsuke
“Kace bana nan”
“Yace don annabi ki daure ki daga” khaliphan dake tsaye bakin qofar kitchen din ya fada,goshinta ta dafe da tafin hannunta,bata so a hadata da ma’aiki taqi yin abu,amira ta miqe tana dubanta
“Kije ki amsa mana namecy,zan tafi sai da safe ki gaida umman khalipha” ta fadi tana murmushi
“Sai da safe ki gaida gida” sumayyan ta fadi itama tana miqewa,ita tayi kitchen su suka fice ita da mai aikinta.
Murya a sanyaye ya mata sallama,a dake ta amsa
“Bakisan halin da zuciyata ta fada sanadinki ba sumayya,please don Allah ki daure ki dinga daga wayata ko ba zaki ce min komai ba”shiru ta danyi ta rasa me zata ce da shi,zuwa yanzu yaci ace yayi zuciya ya bar nemanta
“me kake so nace mai kake buqata?”
“Yauwa beauty,a qalla ko gaisuwa ma ta wadatar” kusan wannan ne abinda abdur rahman ya gaya mata,gashi yana neman jefata cikin tarkon sabo da jin muryarsa,wannan wanne irin wayo ne,ba zata yarda ba kam
“Sai anjima” tace masa tana kife kan wayar ta fito daga kitchen din tana sauke numfashi,inda ta tashi nan ta koma ya zauna ta janyo wayarta tana laluban lambar mamanta tana son jin muryar abdallah.
+

******    ********    ********

       Ramadan ya rage saura kwanaki uku,nan sumayya taga tsari,yadda anty dije ke tsara gidan nata tare da sauya abubuwa sabida shigar watan,baki ta sake tana mamaki don su duk basu irin wannan,dariya anty dije tayi
“Da kike mamakin nawa gyaran kice idan kika ga na gidan baaba prof saikin yada idonki?”ido ta qwalalo
“duk kyau da tsaruwar wannan gidan sai an sake masa wani tsarin?”
“Duk shekara iwar haka sai dukka gidan sun sake komai nasu,sai su rabar da tsofaffin ga ‘yan aikinsu,wasunsu har kayan sawa da yayi shekarar nan ake canza wardrobe baki dayanta” baki sumayya ta sake tana duban anty dije kamar ita ce ke sanya su
“Gaskiya mutanen nan mabarnata ne,yanzu wannan gidan ba ya isheka har qarshen rayuwarka ba,wani ma idan yana wani gu baisan da wani ba,har meye ne zai tsufa a shekara a sauya shi?”dariya sosai anty dije tayi
” lallai har yau bakisan wannan familyn ba,kowa da irin matsayinsa fa,ita rayuwa kowa da inda Allah ya ajiyeahi,idan kaga rayuwar wasu kai a gunka barna ce da almubazzaranci,ko kaga tsabar warya ce ko bazata yiwu ba,amma kaima da Allah zai kaika irin wannan matsayin babu shakka sai kayi kamar ko fiye da abinda yakeyi,yanzu kamar ni din nan,da wasu zasu ga abinda nake cewa zasuyi nima almubazzaranci bane,amma ba haka 
bane,idan Allah ya wadataka kana da shi ka sauya to ka bawa na qasa da kai wancan su amfana suma,ba ka qanqame ba ka qanqame jama’a ba,amma…..zauna na gaya miki su waye wadan nan family din kinji”ba musu sumayyan ta zauna tana baza kunne,itama anty dijen zama tayi,kafin tace komai laila ta shigo tana sanar mata tayi baquwa tilas suka katse hirar ta fita wajensu,sumayya ta tashi ta kama mata aikin da ta tafi ta bari. +

  *********  ******  ********

      Baki daya a yanzu rayuwar gidan bata yiwa karima dadi,bata da buri a yanzu da ya wuce taga yaranta da mijinta kusa da ita amma abu ya gagara,kowa tsoro da haushin zama kusa da ita yake,hatta da lukman din ma kwanciyar bacci kadai ke kawoshi bangaren,ya sauya mata irin sauyin da bata taba zata ba,bai shiga shirginta indai ba haqqinta na aure zai sauke mata ba,wanda shima yasan idan ya take mata sai Allah ya tuhumeshi,a nan takan so jan ra’ayinsa amma abu yaci tura,da ya gama yake wanka idan an kusa asuba ya zauna karatun qur’ani da addu’o’i har sai an kirayi asuba ya fita yayi sallah,idan ya dawo ya zarce wajen hajiya su hafu da yara suyi karatu sannan su shirya ya miqa su makaranta,idan ya dawo shine zai shigo mata yayi wanka ya fice ko sauraron abincinta baiyi gun hajiya shima yake ci,hakan shi ya sake taka muhimmiyar rawa wajen rugujewar duk wani aiki da zata masa,walau na abinci ko na jinnu,ya tsayawa addu’a abincinta kuwa baici bare ya dameshi,bata gane bata da wayo ba sai sanda taso ta gwada yi masa tawaye kan yadda yake maganar sumayya da daukar yaranta ya kaiwa mama su,ranar taga tijarar da tunda Allah ya hadata da shi bai taba yi mata ba,tayi kuka na fitar rai,a hankali kuma sai ta soma tunanin me yafi zaman lafiya dadi?,me zaisa ba zata haqura da komai ba ta kawo qarshen wannan zaman fagen yaqin da sukeyi,abinda bata sani ba tanqwara busashen itace abune mai wahala,ta riga da ra yiwa kanta mummunar lamba wajensa.
Duk sanda yaje yakanyi yunqurin karbar adreas din sumayya wajen zainab ko halima,saidai duk sanda yaso yin hakan sai ya taras basa nan suna tahfiz,ita kuwa mama ba wani riqe adress din tayi ba,yaciji yatsa yaji ciwon abun da tun lokacin aurensu da tace zata gidan anty dijen lokacin da shima zaije abujan bai bita ba yaga gidan,da tuni yanzu bakinsa alekum sai ya kama hanya,wayarta kuwa idan ya kira sau biyar idan yaci sa’a zata daga sau daya su gaisa ta tambayi yara,daga haka zata katse kiran sai kuma wani lokacin.
1

STORY CONTINUES BELOW

******   ********   ********

       Ranar lahadi da daddare watan azumi ya bayyana,hakan ya sanya litinin daukacin al’umar musulmin duniya suka tashi da azumi a bakinsu,duk gidan kowa na azumi banda minal saboda shekarunta basu qarasa ba,ta fara gwadawa zuwa sha biyu anty dije ta bata abinci,kafin azahar su laila anyi laqwas saman kujera,khalipha an fara mutstsuka idanuwa,dariya sosai sumayya ta dinga sheqa musu yayin da anty dije tayi kicin kicin da fuska don kada ma wani yaga fuskar da zaice zai karya,hafiz ne kadai da qwarinsa da yake shine babba.

       Biyu da rabi bayan sumayya ta kammala sallar azahar tana tilawar qur’ani anty dije ta taddata da hijabi jikinta itama da alama bata jima da gama sallarta ba,gefe ta zauna hakan ya nunawa sumayya magana tazo yi da ita saboda haka tana kaiwa qarshen shafin ta rufe tayi addu’a ta shafa ta waiwayo ga anty dijen
“Ya ibada,ke kam azumi nasaj gwaninki ne,tunda kina na litinin da alhamis dama” murmushi tayi
“Wallahi kam anty”
“Allah ya kawo min sauqi wannan karon shi yasa nace bari nazo na sameki,kinsan duk watan azumi nike wa baabaa prof abinci har a kammala azumin,abban laila ne yasa a dinga yi saboda karamcin dattijon,yana son abinciccikan gargajiya duk da kasancewarsa dan boko,to su mutan gidan sun fishi boko,da azumi basa wani abincin azo a gani sai abinciccikan zamani,ummee ce ke masa lokaci lokaci don itama tana so,to wannan karon ummee sun tafi umra mazan ne kawai suka rage a gidan,duk da kowa na da mai aikinsa amma shima baabaan baison girkin ma’aikata shi danshi ya gado” ta fada tana dariya data tuno shi
“nasa gwanar girkin gargajiya ce ke,ni ki barni da girkin gida ki dinga na baabaa” murmushi tayi
“To ai zan iya ma anty duka,haba,sai kace ba mace ba”
“Nasan zaki iya,ai ranon mama ce,amma kya dai tayani na gidan”
Tom anty” miqewa anty dijen tayi
“Naga yau garin kam masha Allah akwai hadari,ko yau zamu samu ruwan farko a ranar farko?”
“Allah yasa anty,dama tun muna kano naga irin garuruwan nan kunfi ko ina samun ruwa,ga damunarku itace qarshe wajen tafiya”
“Wallahi masha Allah,muna shan ruwa kam,saidai zafi”
“A hakan anty,duk wannan ac da kuke kwankwada”
“Saikin fita ai sumayya zakiji a jikinki”
“Saidai haka” ta miqe itama tana nannade abun sallahr ta don shiga kitchen saboda su kammala komai kan lokaci.
1

      Ana la’asar kuwa ruwan farko ya soma sauka zuwa qasa,tana kitchen din a lokacin,sai ta zuge glass tana kallon yadda ruwan ke juqa shukoki yana tayar da qamshin qasa,a rayuwarta tana son damina,murmushi ya subuce mata data tuna sanda suna tare da mukhtar,duk sanda baya gida takan fito ita da yaranta dake tayata zama susha wankansu a ruwan sama,kafin ya dawo ta share gidan ya sauya kayanta kamar bata shiga ruwa ba,amma kallon farko idan ya mata yake gane ta shiga ruwa,musamman gashinta dake saurin fallasata saboda cikarsa da tsahonsa bai bushewa da wuri,abinka da quruciya a lokacin yaron da bai saba qarya ba idan yayi ma sai an ganeshi,sai ta fitittike tace masa wankan tsarki tayi
“Wanne wankan tsarkin,me ya sameki bayan fitata da zakiyi wankan tsarki?” Narai narai take da ido tace itadai wankan tsarki tayi a tunaninta shi kadai ne mafitar da zai yadda ba wasan ruwa tayi ba tunda wankan tsarki ne kadai ake jiqa kai idan za’ayi,idan yaga ta dage sai kawai ya qyalqyale da dariya ita kuwa ta sake hade rai don kada ya gano,tilas yake sakin murmushi yace ya yadda,tana kawowa nan a tunaninta ta saki itama murmushin qwalla na bin kuncinta
“Allah ya gafarta maka ya mukhtar,ya kyauta makwancinka” tayi furucin tana goge hawayen da tafin hannunta,baki daya sai walwalarta ta tafi kamar yadda hakan ke faruwa yawancin lokuta idan ta tunashi,girkin take amma zuciyarta babu dadi,duk da haka hakan bai hanata hanzari ha,kafin kace me wannan ta gama girkin baabaa prof,dashishi ta masa da miyar ganye,wanda kallonta kadai ya isa ya tsinkar maka da yawu,tun ba yau ba tun tana qaramarta haka hannunta yake da iya sanwa,ballantana a shekaru takwas zuwa tara da tayi gidan aure ya sake maida ta gwana fagen iya girki.
Ko da anty dije tazo tayi mamakin saurin girkinta,don tuni suma ta musu miya,miyar qwaice da alayyahu tayi shar tayi kyau sosao,gun any dijen ta koya amma sai take ganin kamar ta fita ma iyawa,kasancewar sumayya bai bala’in qwaqwalwa da saurin dauke abu,cewa tayi ta bar mata sauran ta qarasa tunda tayi kusan rabin aikin gidan bayan na baabaan.
+

      Daki ta shiga tayi wanka,saura kusan awa guda kafin a sha ruwa,ta fito ta shirya kanta cikin atamfa riga da zani,kanta ta daure da dan kwali ta dauki carbinta ta fito falo,dariya ta zo mata ganin yadda laila ta sake bajewa saman kujera,khalipha kuwa tuni bacci yayi awan gaba da shi,bata ce musu komai ba ta sauya tasha zuwa sunna t.v wanda suka sako tafsirij shehun malaminta sheik Ali ibrahim isah fantami,sosai take jin dadin tafsir din har zuwa wani lokaci data koma kitchen din ta tadda anty dije ta kammala komai,ita ta dinga kwaso kayan tana shiryawa saman dining anty dije kuma ta shiga wanka ganin saura mintuna akira sallah.

     Lokaci qalilan gidan ya kacame,kowa na kaiwa baki,daga nan uncle farouq ya kada kansu zuwa masallaci sukayi sallar magariba.

     Babu kowa gidan duka sun fita sallar asham tarawih,ta sanya hijabinta zata tada tata kenan cikin gidan anty dije ta shigo itama sanye da hijabi
“Sumayya,yanzu abban laila ya kirani,yace ki miqa abincin baabaa prof,ga driver nan yana waje zai amshi nashi abinci sai ya riqe miki wasu kwanukan” babu musu yau kam sai faduwar gaba jin an ambacin gidan tace to,dirvan nasu shi ya dauki kwandon ita kuma ta dauki flask daya da ya rage.

     Tana gaba yana binta a baya har suka isa bakin qofar,a mutunce suka gaisa da baba harunaya bude mata qaramar qofar suka shiga,harabar gidan tarwai take da haske da fararen qwai,ko ina a haskake tamkar rana,grass carfet da shukokin dake jere a tsare sun samu ruwan sama sunyi kyau gwanin sha’awa,kamar yadda garin yayi dadi,iska mai dadi mai cakude da qamshin qasa na kadawa,sai ta dinga jin wani mishadi na shigarta,tana shaqar iskar tana mata dadi har cikin qirjinta,ta dinga takawa a hankali har zuwa tsakiyar harabar gidan,su biyu ta fara hangowa tsaye da alama magana suke kamar rannan,mahmoud din kawai ta iya ganewa saboda shike fuskantar qofar shigowar,kamar wancan karon dai dayan na fuskantar mahmoud sai bayansa kawai ta iya hangowa,yana sanye da jallabiya ta maza fara sol da silifas farare a qafarsa,hannunshi riqe da dadduma,tana gab da isa garesu ya juya ya shige ta wata qofa da zata iya sadashi da waje,yayin da mahmoud har ya juya sai ya hangeta,tsayawa yayi yana murmushi har ta qaraso,hanmunsa ya miqa zai amshi flask din hannunta yana fadin
Bisa alamu abincin baabaa ne” murmushin itama tayi tana miqa masa
“Eh shine”
“Masha Allah,a gaida umman khalipha” sai ya dubi drivan yana miqa masa hannunshi alamar ya bashi ,rusunawa yayi cikin girmamawa ya miqa masan sannan ya juya zuwa qofar fitan,dubanta yayi
“Muje nayi sauri na rakaki kada liman ya tada salla na rasa wata raka’ar,don na tabbata ya isa masallaci saura minti biyar a tayar” dan baya ta ja kadan
“Ai ba sai na shiga ba ma,ina cewa ma duka masu gidan basa nan,ka kaima baaban kawai kace ina gaidashi” murmushi yayi
“Kamar ya sanki,na tabbata baki taba zuwa kin gaidashi ba,sannan ko ba kowa a gidan su anty farida da sauran yara na nan” murmushi ta sake yi
“Zanzo na gida baabaa in sha Allah,su anty farida kuwa ka gaishesu na tabbata suma basu sanni ba,amma kace ina gaishesu,nima sallah zanje nayi”
“Is ok,ki yiwa umman khaliphan sannu”
“Zata ji” ta fada tana juyawa a hankali ta fice daga gidan.
1

      Tana shiga ta isarwa anty dije saqon,sannan ta shige dakinta,da hanzari ta tada isha jin an fara kiran sallar tarawih don sun gama isharsu,cak ta tsaya lokacin da limamin ya fara karanta fatiha,daina aiki qwaqwalwarta tayi na wucin gadi,babu abinda kunnuwanta ke ji sai karatun dake fitowa daga lasifiqar yana karade unguwar kasancewar masallacin na daura sa su ne,muryar da bazata iya mancewa da ita ba komai tsawon zamani,komai sauyawar yanayi,komai dadi komai wuya,muryar MUKHTAR dinta take ji tana karade kunnuwanta,wani irin faduwa gabanta ya dinga yi har ya haifarwa da gabban jikinta yin sanyi,tana so ta zauna amma ta kasa,jin kunnuwanta take kamar zasu zaunce,hannunta ta sanya ta toshe kunnen nata ko zata daina jin amsa kuwwar karatun amma hakan ya gagara,kanta ta shiga girgizawa
“A’ah,ba mukhtar bane,wanda ya mutu baya dawowa” ta fada tana ci gaba da girgiza kanta hawaye na shirin soma sauko mata,a sukwane ta juya ta fito zuwa falon gidan ba tare da tasan me zata aiwatar ba.
Birki ta ja a falon zuciyarta na wata iriyar bugawa,idanu ta shiga rarrabawa qwaqwalwarta ta daure tamau,muryar na ci gaba da ratsa kunnuwanta cikin daddadan sautin karatun mai qunshe da muryar mukhtar,me zata aikata?,abinda ta kasa baiwa kanta amsa kenan
“Ya mukhtar,ya mukhtar” ta soma fada hawaye na zubo mata,shigowar laila a guje wadda fitsari ya korota daga wajen sallar ya dawo da ita hayyacinta,bata jirayi qarasowar lailan ba ta isa gareta ta riqe kafadarta
“Laila,wake karatun sallah a masallaci?,mukhtar ne?”dariya ta saki tana kallonta tare da yin tsalle alamar fitsarin ya matseta
“A’ah,yaya ne fa,duk azumi shi yake jan sallah” ta fada tana zillewa ta ruga bandaki,sam bata fuskanci bayanin laila ban ta ji anty dije na cewa
“Shike limanci fa,nan da goman qarshe zai tafi a saudiyya yake sallah sai dai malam usman ya qarasa” firgigit tayi tana duban anty dije,sai ta kada kai kawai ta juya jiki a sanyaye zuwa cikin dakin nata ba tare da ta furta komai ba,zama tayi bakin gado tana jingina da jikin gadon,tamkar wadda aka zarewa laka,ta kasa kowanne irin tunani,muryar ce kawai ke ratsa dodon kunnenta tana mata shawagi,runtse idanunta tayi ta koma ta kwanta a gefan hannun damanta,wani abu take ji yana yana zagaya kanta kamar ana yamutsa qwaqwalwarta,haka hawaye yaci gaba da tsiyaya ta gefan idanuwanta.
Sallar da bata iya yiba kenan har aka kammala sallar laila ta shigo kiranta tazo suci abinci,can qasa ta amsa mata data qoshi sai anjima zata ci,haka taci gaba da kwanciya,tana ganin tarin misscalled din abdur rahman amma ta kasa dagawa har ya gaji ya bar kiran ya turo mata texs,baccin dole ne ya dauketa,bata wani jima ba ta farka,har a lokacin tana jin wata iriyar damuwa na ratsata,sallar isha’in da bata yiba tayi,sannan tayi tarawih din raka’a bakwai har da wutiri. +

  *******   ******   *******

       Daga ranar karatun shi ya zame mata abun sauraronta daga sallar isha’i har a kammala,sosai karatun da muryar ke debe mata kewa ya sanyata nutsuwa,wani lokaci tana ji tana hawaye don ba qaramin tuna mata mukhtar yake yi ba,babu wanda yasan halin da take ciki sai ita kadaj,kawai dai anty dije taga ta rage walwala,bata kawo komai ba ta dauka ibadar da ake ciki ne.

       A haka aka kammala azumi ashirin cif,ranar ashirin da daya sai taji ba waccan muryar bace,duk sai taji ta damu,ji take kamar ta fita ta gano me ya kawo wannan sauyin,daga bisani ta tuna anty dije ta gaya mata goman farko da na tsakiya kawai yake jan sallah,to wannan wane ne?,babu shakka ba don anty dije ta sanshi ba babu abinda zai hana tace mukhtar dinta ne,baki daya sai ta jita sukuku,ba qaramin dadin jin muryar take ba,a ranar uncle farouq ya shigo musu da kayan sallarsu,kowannensu kala shuda shida a dinke,sumayya laila da anty dije kam harda mayafai takalma da jakankuna,daga mayafin kawai sumayyan tayi ta ajjiye gefe,tun mutuwar mukhtar ta sake qanqame hijabi duk da cewa dama al’adarta ne sanyashi,sai dai a baya tana sanya mayafan lokaci lokaci,anty dije ta lura sai ta bada sautun yadin hijabai masu kyau aka yi mata irin wadanda take so,anty dijen ita ta sanya kudinsu ta saya musu dan kunnaye da awarwaro da sarqa fashion designers masu kyau kala uku uku.

         Washe gari akayo aike daga gidan baabaa prof,duk da cewa a jiya ya daga saudiyya shima zasu dawo tare da iyalansa a ranar sallah,a qasarsa yake nashi bikin sallah saboda ziyara da ake kawo masa tako ina,abokai ‘ya’ya jikoki ‘yan uwa da abokan arziqi,daya daga cikin ma’aikatan gidan ne,sanye da unifoarm dinsu,a mutunce ta gaida anty dijen sannan ta miqa mata wata qatuwar baqar leda dake dauke da tambarin wani company dake dubai,company ne da yaje mallakin daya daga cikin iyalin baabaa prof din,shahara da daukakar company din ya sanya wasu suma saka jarinsu a ciki
“Kiyi haquri umman khalipha,tun jiya baabaa ya bada saqon,sai yau na samu sauqin aiki,munata ayyuka ne”
“Babu komai shema’u,baabaa dai kam bai gajiya,Allah yasa a gama lafiya” murmushi tayi
“Baabaa badai alkhairi ba,ko mu bai mana mu kadai har ‘yan uwa na kusa alherinsa bai barsu ba,ina zaton wannan karon har baquwarki da nata kayan,naji kamar ita taiwa baabaan abincin kwana ashirin ko?” Dariya anty dije tayi
“Sumayya,eh itace”
Ai baabaa na jin dadin abincin nan kam qwarai,rannan har yasa a kira ta su gaisa sai yayi baqi kuma ya sha’afa”
“Allah sarki,ai idan suka dawo da kaina zan tura ta ta gaidashi,Allah ya saka masa da alheri,yaci gaba da shirya masa zuria”
“Amin ya Allah”
Shema’u ta fada tana ficewa. +

       Juya ledar anty dije tayi tana murushi,tambarin kamfanin kadai data gani tasan ba kaya bane masu qananun kudi,bude ledar tayi ta fara zarosu,diguwar riga ce irinta mata mai bala’in kyau da tsari wadda aka zauna aka yiwa aikin duwatsu daga sama har qasa,iya dutsen kadai idan ka kalla kasan ba qaramin kudi zaka sanya ba kafin ka mallakesu,yadin kansa abin kallo ne bare dutsen,guda daya baqa ce,sai dayar fara ce qal da aka yiwa aikin baqaqen duwatsu,dayar kuma ruwan jinin kare ja ba dau ba ya dan rusuna amma baikai duhun maroon ba,tana duba size din rigar ta gane sune na sumayya,kowacce akwai vail da ya dace da ita,murmushi tayi don tasan aikin amira ne wannan,wani shegen fashion mai zubin gwal guda daya da banguls dinsa,haka na lailaa suke saidai banbancin tsaho da kala,tasan laila kam za’a sha murna,duk shekara ya saba haka yake musu,duk cikin kayan sallarta tafi ji da kayan gidan baabaa prof,mazan ma baki dayansu jallabiua ce irinta maza mai tsada,sai gezna wadda kana mata kallon farko itama kasan ansha kudi kala bibbiyu duka kalolin iri daya,sanda aka kawo su sumayya basanan sun tafi wankin kai,da suka dawo baki sumayya ta saki,zata iya cewa banda lace din da aka bata taba kaya masu tsada haka ba,ko lace din ta tabbata baikai kudin wadan nan ba,yana ajjiye ma bata dinkashi ba,godiya tayi sosai kamar suna wajen tare da yaba dimbin karamcin ahalin gidan.

      Cikin ranakun goman qarashen so kadan bata yi sanya wajen zabga addu’a gareta da d’anta da sauran yaran musulmi ba da al’umma ba,musamman ranakun da suke mara,wato ranakun da ake tsammacin dare lailatul qadr,tayi addu’ar samun kyakkyawar rayuwa da kuma kyakkyawar QADDARA,sai ta dinga jin nutsuwa da kwanciyar hankali,tsoro da damuwarta suka dinga raguwa a hankali.
Ran ashirin da tara ga wata aka tabbatar da ganin watan sallah waahegari idin qaramar sallah kenan,a gajiye ranar suke don wuni sukayi gidan qunshi,da cewa sumayyan tayi ma bata yi,anty dije ce ta matsanta mata tilas ta bisu,ga wainar shinkafa da ta tsara zata yi musu a ranar sallah,Allah ya taimaka kafin ta kwanta tayi miyarta,zumudin zuwan sallar take sosai wannan karon,saboda uncle farouq yace sallah da kwana biyar zasu tafi kano,a qalla zasuyi sati guda sannan su dawo su fara shirin tafiya london. +

*******   ******    *********

        Qarfe goma na safe tuni an sakko daga sallah,zuwa lokacim sumayya ta kammala aikinta,wankanta tayi ta shirya cikin daya daga cikin dinkin da abban laila ya musu,ba wani makeup tayi ba amma kayan sun mata kyau,rabon abincin sallah anty dijen tayi kamar yadda ta saba.

       Da yammaci su laila da khalipha nata hada barka da sallah sabbin kudi baki yaqi rufuwa,sai shigowa suke suna bawa sumayya labari su wance sunzo gidan baabaa su wane sunzo,itakam kusan bata sansu ba saidai tace musu to,dariya anty dije tayi
“Abokansu ne jikokin baabaa prof, ‘ya’yan babban dansa da me bi masa,kinsan duk wani da nashi da jika dake nesa a gida yake sallah”. Abban lailan nata baqi,wasu na zuwa wasu na tafiya kusan haka suka wuni.

        Wajen biyar tana sama dakin anty dije tana gyara mata,saboda yau baki daya ta kasa zama saboda baqi,hayaniya ta dinga jiyowa da qarar motoci,sau ta miqe a hankali,ta yaye labule tare da bude qofar da zata sadaka da balcony din anty dije dake saman,bata fiya budeshi ba sai lokacin zafi ko kuma idan ta kama saboda idan ka fita kana iya hango jama’an waje suma suna iya ganinka musamman da yake yana center din tafkeken get din shiga gidan su amira,duk da cewa waccar babbar qofar da akafi shiga  wadda jami’an tsaro ke gadinta tana daya daya layin nasu,wannan a nan suka fi harkokinsu.

      Motocine na alfarma qirar zamani,wanda ke dauke da lamba mai tambarin sunan baabaa prof,wanda hakan ke alamta mallaki ne na ahalinsa,kimanin mota shida kowacce na qoqarin shiga gidan ba tare da wata ta gogi wata ba,sai da suka kammala shiga baki daya sannan wadanda suka wangame get din suka rufe shi,ajiyar zuciya ta saki sannan ta juya ta koma cikin dakin wanda hakan yayi dai dai da shigowar anty dije
“Kai,har kin gama?” Tana duba yadda ta gyara kayan
Na gama anty” inji sumayya tana dan kashingidewa
“Kinga yanzun abban laila ke gayan su baabaa sun dawo,amma dai wannan karon zaki ki masa sannu da zuwa ko ku gaisa”dan murmushi ta saki yana yamutsa fuska
“Eh anty,amma dai ba yanzu ba ko?”
“Nima ai bance yanzu ba,kinji an ambaci maqiyinki shiga gidan baabaa ko?” Dariya ta tuntsire da ita har tana kwanciya ganin irin yadda antyn tayi maganar. +

  *****  ********    ******

    Washe gari da yammaci hudu da ashirin bayan ta gama yima anty dijen komai,sai ta shirya cikin wasu kayan nata,swiss ne mai asalin tsadar wanda aka tsara mata dinki na riga da skert,babu kwalliya a fuskarta kamar ko yaushe tun bayan rashin mukhtar cikin rayuwarta illa hoda jagira da liptsic,sabon hijabinta mai hannu wannan karon iya gwiwarta ta zura wanda yayi marching da lace din jikinta,tayi kyau sosai kayan sun haska ta,tun dazun take laqai laqai na zuwa gaida baaban,hakan ne yasa ma ta tsiri yi masa dambun zallar tsokar kaza. 1

       Anty dijen ita ta sake turo qofar dakin karo na biyu tun bayan shigarta wanka
“Baki gama bane har yanzu?”
“Na gama anty” ta fada tana fesa turare
“To,saidai fa ki shiga ke daya kya tadda lailan acan,don duka suna can gidan,ta kasa jiranki,don naji tana kamar zasu park ne”
“To” ta fada badon ranta ya so ba,takalmi ta zura mara tsahon dunduniya sannan ta fito.

        Daga qofar gidan baka gane gidan na qunshe da baqi ba sai ka kai ga shiga harabar gidan,yara ne da ‘yammata kala kala,wadanda kana duban yanayin shigarsu zaka tabbatar da cewa lallai boko ya ratsasu,wayewa da kuma sanin kam duniya,kamar yadda group group ya rabu haka kowacce da irin tata shigar,ta wannan tana wace wance,nan da can zaka ga mutum biyu uku har hudu ma a tsaitsaye,kowa na sabgar gabansa saboda wadatar guri da kujerun zama a ko ina,wanda suke nuna lokaci irin wannan ake fiddo su ayi amfani da su.
Sai taso ta rude baki daya,ta dinga takawa a hankali tana tunanin inda zata shiga
“Muje na rakaki,naga alamar ko yaushe tsoron shigowa gidan nan kike,ko wani ne zaya kamaki?” Taji an ambata daga gefanta,waiwayawa tayi a hankali,mahmoud ne,yayi adonshi cikin shadda ruwan sea blue,ta masa kyau sosai ta fidda ainihin surarsa,murmushi ya subuce mata,sai ta girgiza kai kawai tana gaidashi,ya amsa mata suka fara takawa zuwa ciki
“Naga kowa tun daga ranar sallah da muka dawo zuwa yau,amma ke kam ban ganki ba,su laila tun dazu suna gidan nan,zaman gida bai damunki ne?” Murmushi ta sake saki tana kada kai
“To ina zanje,ba wanda na sani”
“Nan fa,nan ma gidanku ne,ko bakiga yadda su laila suka maidashi gidansu ba?”
“Haka ne” ta amsa masa don batasan me zata ce ba,shima shirun yayi suka ci gaba da takawa,suna gab da shiga bangaren anty maamaa yace
“Dama dai wani abun dadi kika kawowa baba,yau a gunsa zan maqale,kinsan ni da yaa man bamu cin abinci idan akayi buda baki har sai an kawo na gidan umman khalipha,yace shikam bai gane mana wannan wayon namu ba da muke maqale masa a kwanon,har gwara ni gauro ne shifa yaayaa fa” dariya ya bata har sai data murmusa,ta fuskanci mahmoud irin mutanen nan me masu barkwanci faran faran da saurin sabo da mutane. +

        A falon anty maamaan suka ci burki,wasu ‘yammata ne zaune a falon biyu na saman kujera biyu na qasa,kowacce ta baje kayan kwalliya suna makeup,baki daya sun cika falon da hira da karadi,kayan sawarsu na aje gefe da alamu fita zasuyi wata unguwa,kana dubansu zakasan suna daga cikin baqin da gidan ke karba a irin wannan lokaci,sallamar mahmoud ita ta janyo hankalinsu
“Anty maamaa” kawai ya fadi,daya daga cikinsu wadda ke qoqarin daura dankwalinta tace
“Tana G-kitchen” juyawa yayi ya dubi sumayya
“Idan baki gaji ba muje bata cikin nan” bata ce komai ba tabi bayansa yayin da ‘yammatan suka bishi da kallo,wadda ke daura dankwalince ta tabe baki,kishi ne fal bayya ne a fuskarta,ta kusa da ita ce ta zungurota ganin yadda take binsu da kallo
“Uhmmm,yadai?” Qaramin tsaki ta ja
“Nikam baisan me yasa Allah ya zubawa mazan gidan nan girman kai ba,suna jin kamar su kadai ne halittar maza da Allah ya qirqira a ban qasa,jibi,kamar baisan wace ni ba” dariya wadda ke shafa powder ta qyalqyale da ita sannan ta tsaya da abinda take yi
Kema kinsan su isa sun kai suyi girmankan,karfa ki manta su su waye?,kina zaton samunsu a bagas ne,nikam banga laifi ba don sunyi girman kai sun kai suyi ne,kibi a sannu idan da rabonki zaki shiga familyn prof,nikam tuni na sallama” ta fadi tana ci gaba da murza hodarta,shiru tayi bata sake cewa komai ba sai taci gaba da gyara daurin dankwalin nata cikin sanyin jiki. +

      Bayan suka zagaya sai gasu cikin wani qaton kitchen wanda idan ba wajajen kayi ba ba lallai kasan da zamansa,kitchen ne babba mai dauke da electrics kala daban daban da manyan tukwane,kayan girki nau’i daban daban,kitchen ne da ma’aikatan gidan ke haduwa suyi amfani da shi duk lokacin bikin sallah irin wannan,biki ko suna na gidan idan ya tashi,gaidasu sumayyan tayi tare da yi musu sannu da aiki,antyn na tsaye sanye da jar shadda wadda keta maiqo da qyalli dinkin bubu da aka yiwa adon baqin zare,duk da ta tasamma shekara arba’in da kusan biyar amma sai ka zaci ‘yar talatin ce,anty mama kam badai ado ba,tana sabe da wata kyakkyawar yarinya wadda aqalla zatayi shekara daya,an mata kwalliya cikin riga da wando,gashin kanta kuwa adin ribbom ne kala kala,ma’aikatan take sanarwa mai za’a dafa a mazaunin abincin dare a gidan baki daya
“Ah mahmoud yadai?,kun fasa tafiyar ne?” Ta fada bayan sun gama gaisawa da sumayya,shi kuma yana jan yarinyar dake kafadarta din da wasa wadda da alama itama jikar gidan ce,sumayyan na tsaye gefanta antyn riqe da hannunta daya
“A’ah,wannan mai tsoron shigowa gidan nan din na rako zata gaida baabaa” murmushi tayi ta juya tana kallon sumayya,haka nan sumayyan take burgeta tun ganin farko,da alamu zatayi nutsuwa,bata da rawar kai da fi’ili irin na ‘yammatan zamani,shigarta kadai ta tabbatar mata da cewa daga babban gida ta fito,koda ba gidan da suke da kudi da ababen more rayuwa ba,a’ah,babban gida na nufin gidan mutunci da karamci,gidan da aka san dattako,gidan da usuli ilimi tarbiyya da wadatar zuci,gidan dake cike da tarbiyya da daraja
“Ba tsoro bane,baqunta ce” inji antyn tana murmushi,kusa da antyn ya matso bayan ya ajjye mata kwanon
“Nidai anty gashi nan,a tuna da ni idan baabaa zaici abinda ke cikin kwanon nan” hararsa tayi
“Haka fa,anqi aure anbi an takura mana miji,kunqi barinsa yayi auki,komai zaici sai kun tayashi” dariya ya sanya yana ficewa tare da fadin
“Wannan tsohon mijin naki anty ana ji da shi” itama dariyar tayi sabida tasan halin zolayar mahmoud,qarasa lissafa musu abinda ya dace tayi sannan ta dubi sumayya tace 
“Bismillah” ta soma qoqarin tafiya tare da daukar kwanon,ganin haka ya sanya sumayyan matsawa kusa da antyn ta miqawa yarinyar hannu,zubawa sumayyan ido tayi tana kallonta,dariya anty tayi
“Wannan uwar qyuyar,Allah yasa ta yarda,uwarta na can ta tafi yawon saloon din da ba’a yishi ba sai yau ta barni da rigimamma” kamar taji kuwa abinda antyn tace sai ta miqawa sumayyan hannu alamar ta dauketa,ba antyn ba har masu aikin ta basu dariya,saboda kowa yasan qyuyarta ba da kowa take yarda ba
Lallai kin ciri tuta mai sunan umma” ta kira sumayyan da haka saboda tuna sunan wace garesu,murmushi ta danyi tabi bayan antyn tana duban yarinyar,sai ta tuna mata abdallahnta,ko yanzu me yake?,tana kewarsa sosai,ta qagu lahadi tayi ta ganshi,sai kuma ta tuna yaranta wadanda ke tayata zama tun suna tsohon gidansu da mukhtar,su naana kam tasan yanzu sun girma,tana saka ran in sha Allah da zarar ta koma zata ziyarcesu,itakam tasan cewa son yara a jininta yake haka halittarta take,duk inda taga yaro ya dinga burgeta tana kallonsa kenan. +

       A hankali suke ratsa gidan anty maamaan na janta hira kadan kadan,jefi jefi suna gaisawa da mutane a kan hanya wanda da alama basu hadu bane tun safe sai yanzu,ba mamaki saboda girman gidan wanda ya iya hadiye duka baqin dake ciki,tun daga farkon sashen ta tabbatar da cewa akwai banbanci da sauran sasannin gidan,antyn dai na gaba tana bin bayanta,yarinyar na ci gaba da kallon sumayya tare da yi mata shirmen surutu irin na yaran dake son koyon magana ita kuwa na biye mata anty na binsu da murmushi har suka isa qofar da zata sadasu da babban falon dake mallakin mai gidan ne
Dattijo ne mai kimanin shekaru sittin da biyar zaune kan daya daga cikin kujeru na alfarma dake zagaye da falon,haiba kwarjini da kamala sun bayyana qarara kan fuskarsa,Allah yayi masa baiwar furfura tun daga gemu zuwa kansa,farin gilashi ke saye a fuskarsa baya ga shaddar dake jikinsa fala sol,dogon wando da riga mai gajeran hannu iya gwiwa,da alamu akwai babbar rigarsu wadda bai sanya ta ba,gefensa daga hannun dama samari ne guda uku,wanda ke daura da shi yana fuskantarsa sosai,bisa alamu magana suke mai muhimmanci,kyakkyawan matashine mai cike da kyau kwarjini izza da haiba,sanye yake da irin kayan tsohon bisa dukkan alamu anko sukayi,shi dinma fuskarsa sanye take da gilashin,daya hannun nashi ma wasu matasanne su biyu sai mata guda biyu. +

     Tunda suka shigo falon gabanta ke mugun faduwa,sosai ta dinga qoqarin baiwa kanta qwarin gwiwa saboda haka sai ta sadda kanta qasa har suka qaraso cikin falon suna sallama,dattijon ne ya amsa da wasu daga cikin mazauna falon,idonsa na kan antyn da sumayya har suka qaraso,gefe ta samu ta zauna daga qasan carfet din,da sauri baabaa yace
“A’ah,tashi ki koma saman kujera mana” murmushi tayi kanta na qasa,ta soma gaidashi tare da yi masa sannu da zuwa,fuska sake tamkar ya santa ya amsa mata,anty ta dubeshi
“Nasan baka santa ba” sake dubanta yayi yana gyada kai
“Gaskiya kam,koda na santa to ta kwanta min,kinsan shekarun sun fara turawa sai a hankali” sauran dake zaune sukayi danyi dariya banda mutum daya da tun shigowarsu ya dauke kansa ya maida hankalinsa kacokam kan wayarsa yana tura saqonni,hakanan ransa yake a bace.
“Itace wadda ka dinga bamu labari ka kwashi girki na kwana ashirin ka dinga zabga santi” baki daya dariya suka kuma saki wanda hakan ya dan ja hankalinsa,har ya sanyashi daga kai ya mata kallo daya tak ya sake maidawa kan wayarsa yaci gaba da abinda yake
Masha Allah,Allah yayi albarka,naji dadin abinci kam qwarai da gaske,Allah yayi albarka”
“Amin baabaa,na gode” ta fada cikin jin dadi bisa dabi’arta ta son na gaba da ita wanda take saka ran addu’arsa zata iya binsa ya sa mata albarka,hannu ya miqawa husna wadda ke hannun sumayya,ta kuwa lafe a jikinta tamkar ta santa,qememe taqi zuwa,sai ya zura hannunshi cikin aljihun rigarsa ya zaro alewa,kasancewarsa mai yawan kyauta,musamman a irin wannan lokaci da jikokinsa ke kasancewa a gidan tare da shi,hakan ya sanya baya rabo da alewa da sabbin kudi,miqa mata yayi take kuwa ta tafi gurin nasa,hannu yasa ya dagata yana dariya jama’ar falon na tayashi,tsaki ya ja qasa qasa yana miqewa,shikam bai san me yasa abun dariya bai yiwa su mu’azzam wuya ba,shi baki daya ma baiga abun dariya ba,yarinyar ma tunda ta shigo baki daya ma yaji ransa ya baci,musamman katse musu hanzarin da tayi kan muhimmin batun da suke tattaunawa,tun dazun dama yake addu’ar kada wani ya shigo saboda baison abinda zai katse masa bayanin da ya daukowa baban,ya san mutum ne shi mai mutunta baqo,kome yakeyi yana iya katsewa ya saurari baqonsa,sarai baaban ya ganshi amma sai ya qyaleshi,yasan halin kayansa sarai,da idanu ya rakashi har ya fice,ganin ya fita ya sanya sauran miqewa
“Baabaa kada fa ya tafi ya barmu”
“Jeku,don tsaf zai iya aikatawa,musamman da kun zo da tsarin da baiyi masa ba”dariya suka yi sannan sukayi sallama da baban suka fice,tattambayarta baabaa yayi kan wasu abubuwan tana amsa masa,har alokacin kanta na duqe,ta miqe bayan wasu mintuna ta masa sallama,sai anty ta ajjiye masa kwanon tana masa bayani,qwarai da gaske yaji dadi,domin shi mutum ne da baya raina alkhairi komai qanqantarsa,koda yafi qarfin abu ka bashi shi yana ganin girmansa abun agunsa,dakatar da ita yayi yana fadin
“bari na baki zamzam da bagaruwa ko”
“To” ta fada tana murmushi,antyn yama kwatance cikin dakinsa,cikin sakanni ta shiga ta fito da wata jarka
Ba ita ba,zamzam din da nayi dawafi da shi” mamaki antyn tayi,don irin wannan zam zam din ba kowa yake bawa shi ba,dashi yaje dawafi da addu’o’i,yakam zama magani cikin ikon Allah ga duk wanda ke jin lalura ya bashi yayi amfani da shi,duk da kasancewarsa tantagaryar dan boko amma akwai ilimin addini mai yawa tattare da shi,jarka ce guda tayi tsawon ta faro qarami ya zuba mata,sannan ya cika mata leda da bagaruwa da dabino,godiya tama baban sosai ta kuma ji dadin kyautar tasa,tare suka fito da antyn
“Anty zan koma”
“Haba daga shigowarki,kodai tsoron kike ji kamar yadda mahmoud ya fada,naga ko mutuniyar taki amira baki gani na,bayan ita tunda muka dawo take maganarki,na tabbata baqi ke suka hanata fitowa da tuni kin ganta,sannan baki shiga kin gaida ummee ba” sam bata so antyn ta debo mata wannan bayanin ba,amma sai ta sadda kai tace
“To,bari na shiga”
“Yauwa,ki gaida ummam khalipan don Allah idan kin koma,nasan itama baqi ke suka hanata leqowa,dukkanmu irin wannan lokacin sai haquri baqi muke ba dauke qafa”
“To zataji” ta furta sanda antyn ke yunqurin amsar husna,nan ma qi tayi,dariya antyn ta dinga
“Shikenan kuje da ita kin samu qanwa,idan tayi kuka ko laila kaya bada ta kawota”
“To anty” tafada tana dariya tare da yin gaba. 1
        Baki daya falon ya sauya ba kamar waccan karon data shigo shi ba,da alama gyaran azumin ne,komai ya canza a falon,saidai tun kafin ka kai ga qarasowa cikin falon zaka jiyo muryarta,tana tsaye tsakiyar falon hannunta riqe a qugu tana zuba masifa,bisa alamu da ‘yanmatan dake zaune a falon take,sun kusa su hudu harda amira dake gefe tana shan ice cream hankalinta kwance kamar ma bata falon
“To bani cike da iskanci,ran kowa sai ya baci wallahi,bazan dauki raini ba,kuma wanda ya fasa karbo greeting cards na ‘yammata yana kawowa bai cika ba mu zuba ni da ku,aikin banza kawai” tana gamawa ta juya a fusace tana taku kan tsireren takalminta mai igiya,kowa sanye da suturar al’ada banda ita,wando ne a jikinta irin straight leg din nan,sai riga one shoulder a jikinta,gefe sumayyan ta janye tana dubanta,dariya taji ‘yammatan suka saki bayan fitar tata banda amira fake ci gaba da abinda take,daya daga cikinsu tace Duk wayon amarya wallahi sai an sha manta”sai a lokacin sumayyan ta maimaita sallamarta,amira ce ta amsa cikin fara’a ta miqe
“amiran umman khalipha kinsan kina raina,sannu ga guri zauna” tana mata nuni da wata kujera dake can gefe babu kowa,qarasawa tayi tana zaman amira ta sake cewa
“Ina kika tsinto wannan uwar qyuyar,daina kallona kina wani saukar da kai ban daukanki zanyi ba nima” ta fada tana dan daga murya da zaro ido da alamu tana jin haushin irin qyuyar husnar,murmushi sumayya ta saki tana dafe kan husna wadda ta kwantar da kanta aqirjinta
“Dole fa ta miki qyuya,kina mata irin haka”
“Allah bata da kirki” gaisawa sukayi ta mata sannu da zuwa sannan ta tambayi ummin
“Ummi na sama,bari na miki kiranta”
“To” ta amsa,satar kallonta ‘yammatan suka ci gaba da yi itakam hankalinta na kan husna tana mata wasa a haka amira ta dawo ta tadda su,ba dadewa ummin ta sauko,abinda sumayya ta dan lura da shi shine,ummen irin mutanen nan ne da basu son hayaniya da yawan surutu. 1

       A mutunce ta gaidata ta amsa mata fuska a sake itama tana son daukar husna,saidai itama husnar ta watsa mata qasa a idanu kamar sauran,tilas ta barta sumayya na mamakin qyuyar yarinyar,bata wani jima ba tayi musu sallama ta fice sabida yadda ‘yammatan ke kallonta.

       Anty dije ma tayi mamakin ganinta da husnar,goyata tayi bayan ta bata abinci,ba jimawa kuwa tayi bacci a bayan nata,gab da magariba sukaji sallama a falon,sumayyan ce ta fito goye da husnar tana amsawa,magidanciya ce wadda zata doshi shekara talatin da hudu,fuska a sake sumayya tayi mata sannu da zuwa,leqa bayan sumayyab tayi tana riqe baki cikin fara’a
“Wai lallai raino yayi dadi,ashe kam da gaske tana nan din,ni ina can hankalina na kanki uwar qyuya ashe ke kin haye bayan mutane kina bacci abinki” dariya sumayya ta danyi sai alokacin ta fuskanci mamarta ce,yunqurin saukota tayi tana fadin bari ta bata ita
“A’ah,barta mana idan ba’a matsa miki ba,haba sai kace bare,da nan da gidan baabaa ai duka daya ne,kawai dai idan ta tashine nasam zata taba miki darunta,sai azo a dauketa”
“To” ta amsa tana gyara goyon
Ina anty dije” ta ambaceta da sunan da suke kiranta a kano sabanin yadda taji mutan gidan na kiranta da umman khalipha
“Yanzun nan ta shiga wanka”
“Sarkin kwalliya wa miji,idan ta fito kice ina gaidata” ta fada da sigar zolaya,bisa alamu sun saba sosai. +

      Bata farka ba sai bayan magariba sumayyan ma na shirin tada isha’i,daukota tayi daga kan gadon ta cire mata pampers tare da zuba abinci ta bata,sai da taga ta qoshi sannan ta sabata a kafada ta zura hijabin sallarta wanda ke kusan sharar qasa tace khalipha yazo ya rakata.

        Tarwai gidan da haske kamar kowanne lokaci,saidai yau akwai yawaitar mutane a harabar gidan,sashen anty maamaa ta shiga tacu sa’a ko ta tadda maman husnar,amsarta tayi tana yiwa sumayyan sannu tare da godiya.

       Tunda ta tako daga sashen anty maaman ya zuba mata idanu,haske gidan kadai ya wadatar masa ya gane wace ita,mahmoud da ya gaji da yi masa magana ya dafa kafadarsa wanda hakan ya sanyashi daga kai da sauri yana dubansa
“Mahmoud,sumayya ta nake gani a gidanku” waiwayawa yayi zuwa inda yaga alqasim din na kalla,tabbas sumayya ce ke tahowa
“Wannan sumayyan ce sumayyarka dama?”
“Wallahi itace” alqasim ya fada a rude,dariya mahmoud ya saki
“Ai tazo gidan sauqi,amma fa ba abune mai sauqi ba shawo kanta haka na fuskanta”
“Please mahmoud” alqasim ya fada cikin damuwa yana hade hannayensa ganin sumayyan na gab da su
“Don’t mind”mahmoud ya furta yana waiwayawa yadda zata iya ganinsa idan ta qaraso,sam bata lura sa su ba duk da hasken da ya wadatar da gidan tamkar raba,hanakalinta na gefe can inda wasu ‘yammata ke zaune suna hira,kusan basu suka dauki hankalinta ba ma yaran dake wasansu kusa da su ne,wanda daya daga cikinsu keta kiran abbanaa da alama labarin abban nasu yake basu,tana ganin sa’o’in abdallah a ciki,cikin ranta ta raya suna cikin farinciki da gata,sabanin abdallah da take fatan zai tashi cikin farinciki saidai baisan dadin uba ba,qwalla ta taru idonta sai tayi hanzaru sadda da kai da qara sauri a tafiyarta don ficewa daga gidan.tun jiya ranta a jagule yake,hakanan ta wuni da tunaninsa cikin ranta,wanda ya haddasa mata kasala da mutuwar jiki wunin baki daya,shi ya qara mata qyuyar fitowa waje
Yi a hankali kada ki fadi” mahmoud ya fada yana dubanta,cak ta tsaya tana dubanshi tare da qaqaro murmushi
“Hala sauri ake a fice daga gidan namu”dariya ma yaso bata saidai bata yin ba sai murmushi saboda damuwar da zuciyarta ta shiga daga tuna mukhtar
” kadai camfani”
“Ko kadan,to daina saurin,ga baqo kinyi,yanata nemanki wata da watanni sai yau Allah ya qaddara haduwarku” a zabure kamar wadda ta yiwa sarki qarya ta daga kai,suka hada idanuwa da alqasim,farinciki yake ji sosai cikin ransa,takowa yayi gefanta yana dubanta
“Zakaran da Allah ya nufa da cara sumayya,mai yiwuwa Allah ya qaddara wani lamari ne mai girma tsakaninmu,shi yasa ya kado hankalina abuja gidansu abokina mahmoud,ashe rabon na ganki ne” ba shakka tana ganin girma da qimar mahmoud,tunda shi ya soma tsaidata,banda haka da tuni ta yankawa alqasim warning cikin daqiqun nan tare da kaucewa. 
        Saye yake da quater zip sweater mai dogon hannu ta kamfanin armani maroon colour saboda sanyin da ya soma busawa sakamakon hadarin da ya hadu dazu bai zub da ruwa ba sai ya bada sanyi wa garin baki daya,wandon jeans baqi,sai high top sneakers,hannayensa saye cikin aljihun wandonsa ya fito zuwa harabar gidan yana duddubawa,kusan al’adarsa ce wannan a lokaci irin wannan,kafin yaje ya kwanta sai ya dudduba ko ina saboda baqin dake gidan,ya tabbatar babu yarinyar data fita yawo balle akai ga zuwan saurayi zance gidan,yace duk mai buqatar hakan ta bari idan ta koma gidansu tayi abinda taga ya mata amma ba cikin gidansu ba,tsarin ya yiwa baabaa prof saboda haka baice komai ba,a irin hakan wasu daga ‘yammatan wadanda suke zaton wayewa ce garesu,iliminsu da gogewarsu ta kai wani mizani,sukan fita ciye ciye ko siyayya da samarinsu,wani lokaci sukan kai goma ko tara na dare basu dawo ba,yayin da wasu sukan maida harabar gidan filin baje kolin gayyatar saurayi suyi zance,hakan ne ya sanyashi sanya wannan doka wadda ta yiwa manyan dai dai saboda tsaron tarbiyyar kowacce yarinya har ta koma gidansu,hakanan duk wanda ke kawo ziyara gidan a irin wannan lokaci ya san da dokar,walau mace ko namiji.
Cikin izza da ginshira yake takowa tsakiyar harabar gidan yana qarewa kowacce kusurwa ta gidan kallo da idanunshi,tuni hayaniyar wajen ta soma raguwa kowa ya soma shiga taitayinsa,wasunsu suka shagala da kallonsa,masu gulmarsa qasa qasa nayi. +

       Kamar ta sanya kuka haka sumayyan keji,yayin da alqasim kuma ya dage wajen ganin komai ya daidaita kafin barinta wajen,idanunsa ya sake wurgawa wani sashen,a can saka masa kamu,maca ce tsaye da hijabinta har qasa da wani saurayi tsaye a gabanta,sai wani saga gefanta,ranshi ya matuqar baci,ya tsani ya sanya doka a karya masa,a ganinshi wannan daya ne daga cikin alamun raini,idanu ya zuba sosai sai ya dinga hango kamar mahmoud ne dayan dake gefe,cikin bacin rai ya soma takawa idanuwansa na wajen,sam mahmoud bai ankara da fitowarsa ba shakka da tuni ya sallameta,ya riga da yasan halinsa sarai mutum ne mai doka da qa’ida,bazai karya dokar wani ba so shima kada a karya tasa shine zaman lafiyar mutum.

       “Mahmoud” ya ambaci sunanshi bayan isowarshi gun,wani abu taji ya caketa tun daga tsakiyar kanta zuwa tafin qafarta da taji muryar mukhtar gab da ita,kuma a bayanta,kamar mai ciwon wuya haka ta dinga waiwayawa a hankali har ta kammala juyawa baki daya,tsaye yake harde da hannayensa yana yiwa mahmoud da alqasim magaba cikin bacin rai,idanuwansa na kansu,wanda sam bata iya jin abinda yake gaya musu illa bakinsa da take gani yana motsawa,muryar ce taci gaba da yi mata amsa kuwwa cikin kunnuwanta,a hankali ya dinga juye mata zuwa mukhtar dinta,sannu sannu jikinta ya soma rawa tamkar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi,bata ankare ba taga yana qoqarin juyawa ya bar gurin,batasan lokacin da ta daga murya cikin qaraji daya sabbaba har wadanda ke daura da su jin sautinta ta ambaci
“Mukhtar!” Cak ya tsaya tare da waiwayowa yana dubanta,kallonsa take tana takowa zuwa gurinsa a hankali,tsayawa kawai yayi yana dubanta,tun dazun haushi ya tsaye masa a wuya,tunda ya tsaya gun ya lura da yadda ta zuba masa udanuwa,abinda ya tsana kenan cikin kafatanin halayen ‘yammatan wannan qarnin,kallon tsiyawa d’a namiji,babu wata kunya tattare da su
“Mukhtar kai ne?,kaine mukhtar!,dama kana nan,dama baka mutu ba?” Cikin bacin rai da yi mata kallon mai tabin hankali ya dubi mahmoud
“After All ma ashe da mai lalurar tabin hankali kuke tsaye?,sai kuzo kusan yadda zaku fidda ta tun kafin ta soma yiwa mutane barna”
Mukhtar nice fa,sumayyarka ce mukhtar,nike da tabin hankali?” Har yanzu bai gasgata mai hankali bace,amma sai ya nutsu tsaf ya dubeta,babu alamu na hauka tattare da ita,ayyanawa yayi kawai tsabar rainin wayo ne da son samun guri,wanda ba tun yau ba ya gama haddace kissa ta son samun guri na ‘yammata masu cusa kai kala daban daban,wani tsaki ya ja,sannan cikin dakakkiyar muryarsa wadda ta sake taimakawa wajen sawwara mata surarsa zuwa ta mukhtar yace
“Ban ciki da hauka da gidadanci kinji ko,ki kama kanki tun bai gudu ya barki ba,kama hanyarki ki koma inda kika fito” ya juya yana yunqurin barin wajen,a zabure ta bishi har ta samu nasarar riqo dantsensa,cikin tsananin bacin rai ya juyo yana dubanta cikin ido,wani kallo ya jefe ta da shi wanda tabbas da cikin hayyacinta take tuni ta sake shi saidai sam ko a jikinta
“Sake tafiya zakayi ka barni?”
“Sakeni!” Ya daka mata tsawa
“Bazan sake ka ba” itama ta fada cikin tsawa da bacin rau,take zuciya tanzuroshi,marinta yaso yi amma yaga rashin dacewar hakan,maiyiwuwa akwai tabin qwaqwalwar da batasan tana da shi ba,yaga kuma alama matuqar yaci gaba da tsaiwa zata iya ma rungumeshi kaban wadan nan yaran ta zubda masa mutunci,saboda haka sai ya fincike hannunshi tare da tunkudata yayi gaba,wani irin zafi yake ji da haushinta,baya tayi cikin rashin qwarin jiki,sun tsammaci zata turje ta tsaya sai kawai suka ga ta sulale ta zube baki daya,cikin firgici da tashin hankali mahmoud ya soma qwalawa amira kira don babu damar taba ta wadda fitowarta kenan shan iska batasan ma meke faruwa ba,ganin sumayyan kwance ya daga hankalinta ta koma ciki a sukwane,nan sukayi kacibus da anty farida mamar husna ta kamo hannunta suka yo wajen.
Ba amira da anty farida ba,hatta mahmoud da alqasim hankalinsu tashi yayi,kowa mamaki yake,meke faruwa ne haka,abu kamar dramer cikin sakanni qalilan,tana ta faman kiran mukhtar shi kuma wannan ALMUSTPHA ne abinda suke tunani kenan,cikin hanzari anty farida ta soma yunqurin dagata da taimakon amira,idan ka dubi fuskar wasu dai daikun ‘yammatan dake gun jimami da tausayi ne bisa fuskrsu,addu’a suke mata kan Allah yasa ba qoshin wahalar da suka afka bane itama ta afka cikinsa,yayin da wasu dadi ya rufesu kamar su taka rawa,ko banza basu zama su kadai ba cikin wadanda suka rasa wannan damar. +

        A hankali ta ja numfashi tana ambaton sunan Allah,idanunta ta bude,jinta take kamar wadda ta tashi daga bacci,idanuwanta ta sake lumshewa take abun ya sake fado mata,kalamansa da muryarsa suka fara yi mata amsa kuwwa cikin kunne,take idanuwanta suka tara hawaye masu dumin gaske suka soma bin gefen kunnenta,sake rintse idanuwanta tayi,kamanninsa suka fara dawo mata ganin farko data yi masa kafin idanuwanta su rudeta,da sauri ta bude idanuwanab tana girgiza kai,tabbas ba mukhtar bane,babu kamannin mukhtar ma tattare da shi idan ka dauke murya,me ya shiga kanta ta aikata haka sai kace wadda jinnu suka juyawa tunani?. 4

        Saitin fuskarta taga an turo screen din waya,idanuwanta ta bude kan screen din,shine,shine wanda ta gani dazun,sanye yake da qananun kaya kyakkyawar fuskarshi qunshe da murmushi,hotonsa ya cika fuskar wayar baki daya,a yanzun ta sake tabbatarwa bata ga kama tsakaninsa da mukhtar dinta ba,sai ta waiwaya don taga wanda ke haska mata hoton,amira ce zaune gefanta,idanuwa suka hada sai ta janye wayar tata ta kasheta tana duban sumayya
“Wannan yaya nane,mama da baabaanmu daya,ummee ita ta haifemu,sunanshi MUSTAPHA ko ALMUSTAPHA duk daya ne,anty dije ta bani labarin waye mukhtar a gunki,matuqar suna kama da mukhtar kuma yayi miki na miki alqawarin zaki zama mallakinsa,duk da nasan babban aiki na daukawa kaina saboda sanin waye YAYA MAN,amma abinda yayi miki ya bata min rai,ina jin tamkar ni aka yiwa,ko don saboda wannan indai kina sonshi amiran umman khalipha na miki alqawarin aurensa”.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]