[Advertisements⬇️]

QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 22 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

QADDARAR SUMAYYAH
CHAPTER 22

A tsakar gida zainab ta sake shimfida musu wata tabarmar suka
koma ciki.
Hira sosai suka dinga yi har da mama,abdur rahman na basu labarin
garin ma’aiki madinatul munawwara har aka kirayi sallar magariba,tare
suka fita sallar shi da malam da yaya abubakar,koda suka dawo ma bai
tafi ba tare suka ci abincin dare sannan ya musu sallama.
Hannunsa dauke da abdallah ya fito daga gudan,bahija da

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

sumayya na bayansa wadda ta fito don ta dan taka musu,a bakin
motarsa sabuwa da ya sauya qirar range rover yaja burki yana duban
sumayya
“Tsarabar abdallah bata qaraso ba,ko zaki dan rakamu waccan titin
dake gabanku naga akwai wami super market na dan masa siyayya
kafin su iso?”. Kai ta kada tana dubansa
“haba sabida dorawa kai wahala, mun yafe duk sanda suka iso ma
amsa”kunu ya dan sha yana dubanta
“Dorawa kai wahala kuma?,niba babansa bane?,ko kina so kice ba
yarona bane?” Baki ta bude tana dariya tare da dubansa tace
“Ni na isa in fadi haka,kai matsala ta da kai son girma fa”
“Ban kai naso girma ba ko sumayya?” Ya fada cikin wani irin salo da ya
sauya yanayin muryarsa idanunsa cikin nata,wanda ya haifarwa da
sumayyan rage farashin dariyarta,karon farko da taji duban qwayar
idonsa ya mata nauyi,sai ta janye idonta tana cewa
“A’ah,ai ko da sakan daya mutum ya girmeka ya girmemaka har abada”
dan shiru yayi sannan ya gyara tsaiwarsa yana miqa mata abdallah
“Karbeshi yau mun wunar muku,sai kuma gobe idan Allah ya kaimu” ta
amsheshi tana cewa
“Allah ya nuna mana goben” cikim zuciyarta ta dauka da wasa
yake,hannun abdallahn ya bude ya sanya masa ‘yan dubu dai dai guda
uku yana cewa
“Kasha sweet my son'”
“Habba abdur rahman..”
Katseta yayi ta hanyar cewa
“Shshshshsh!,ai bake na bawa ba ko?,kuma wai bakijin kunyar fadar
suna na haka gatsal?” Galala ta saki idanu ta bishi da kallo
“Kunyar kamar yaya?” Ta fada tana dubansa,murmushu kawai yayi ya
bude gaban motarsa ya zauna sannan yace
“Sai goben ko ‘yamma ta?” Murmushi ta saka mamakin abdur rahman
din na kuma kasheta
“Nice kuma yau ‘yammata abdur rahman ga yaro na a hannu?”
“Oh,kuma fadar sunan nawa dai kika yi?” Ya tambayeta yana kada
kai,shuru ta masa tana zagayawa wajen bahija ta dubeta
“Bahija ki gaida mama kinji,naga alama wannan yayan naki bayan
karatu sa ya tafi qarowa ya qaro yadda ake canjin hali” dariya bahijan
tayi tana amaa mata da zata ji,shima dariyar yayi sannan ya tada motar
tasa yayin da sumayya ta shige gida.
Tunda ya shigo da motarsa layin su sumayyan ya hagi tsaiwar wata
motar a qofar gidansu, har zuwa yanzu da motar tazo ta wuce ta gefan
tashi yana binta da kallo tare da qoqarin tantance waye a ciki,saidai
duk qwaqqwafinsa ya kasa gane waye a ciki saboda glasa din motar
mai duhu ne,hakanan sai yaji wani abu mai tauri ya riqe masa
wuya,rabin ‘yar walwalar da ya samu wunin yau ta kau baki daya,a
sannu yaci gaba da tuqa motar tasa har ya qaraso qofar gidan ya tsaya
ya fito ya samu yaro ya aikashi ciki,ba jimawa yaron ya fito dama sun
riga da sun saba duk sanda aka aika akace ana gaida mama to mukhtar
din ne kuma sun san me yazo yi,sai halima ko zainab ta kawo masa
abdallahnsa,nan cikin mota yake zama da shi su qaraci wasan su
sannan yayi horn su fito su karbeshi da abinda ya kawo masa sannan ya
wuce,sau tari yakanji sha’awar ganin sumayyan saidai babu wannan
damar,rabon da ya ganta ma bazai iya tantance adadin kwanakin
ba,tilas yaje danne komai don ya sani a yanzu ta fita a huruminsa.
Yau din ma kamar kullum hakan ce ta kasance,abdallahn nata masa
gwalanto saidai bai gane me yake cewa ba biye masa kawai yake,bai
wani jima ba ya maida shi ya tafi zuciyarsa na sakutarsa kan motar da
ya gani.ya mance cewa a yanzun sumayyan rabon mai rabo ce ba
mallakinsa bace
BAYAN KWANA BIYU*
Tun daga ranar abdur rahman ya maida gidan gurin hirarsa,wani
lokaci yazo shi kafai wami lokaci ya taho da bahija,da yake su biyu
Allah ya bawa mamansu, sukan dauki lokaci da sumayya suna
hirarsu,yayin da wani lokaci idan ya furta wata maganar sai ta sanya ta
a duhu,wani sa’in takan yi murmushi ta alaqanta hakan da girma da
abdur rahman din ya sake yi.ya fara zama babban mutum shi yasa
yanayin hirarrakinsa suke sauyawa,bata taba kawo komai cikin
zuciyarta ba saboda ita din rainon mutum daya ce da mutum daya ta
taba gina duniyarta wato mukhtar,ba komai take iya ganewa ba ko
fahimta game da wasu baqin al’amura a gun d’a namiji ba.
Sau biyu mukhtar na katarin ganin motar na tasiwa daga qofar
gidansu ta fice daga layin,saidai har yau bai samu nasarar gano waye
ba,lamarin ya tsaye masa a zuciya,duk da yasan baida hurumin hakan
amma zuciyarsa ta gaza daurewa,hakan ne ya sanyashi cin washin
zuwa ya tadda ko waye.
Tunda ta fito daga makarantar tasu ta lura yake bin bayanta cikin
mota wanda hakan ya matuqar tsorata ta musamman data lura yau
unguwar tasu babu yawaitar jama’a,hakan ya sanya ta qarawa qafarta
sauri.
Ganin tana neman bace masa ya sanya shi faka motar sannan ya fito
ya biyo bayanta, gabanta taga an sha wanda ya hakan ya dan tsorata ta
taja baya taba dubansa,matashi ne wanda a qalla zaiyi shekara arba’ain
da biyu,dogo ne baqi maras jiki sosai,za’a iya karansa da chaculet
colour,babu laifi yana da kyau dai dai gwargwado, kana kallonsa kasan
yana cikin rufin asiri da wadata dai dai gwargwado
“Assalamu alaikum” ya fada yana murmushi wanda sallamar ta dauke
kaso mafi yawa daga cikin tsoron da ya cika zuciyarta,cikin qarfin hali ta
amsa masa
“Don Allah kiyi haquri,nasan ban tsaidaki a yanayin da ya dace ba,nidai
suna na lukman,na gaza daurewa zuciya ta ne shi yasa ni aikata
hakan,na lura kamar a darare kike da ni,idan ba zaki damu ba ki bani
lambar wayarki sai muyi magana” kamar kuwa ya sani a takuren
take,saboda wannan shine karo na farko da ta fara tsaiwa da wani
namiji.ga masu shugewa jifa jifa suna faman binta da kallo,hakan ya
sanya cikin rudewa ta karanto masa lambar halima don bata da niyyar
bashi tata,yayi serving yana murmushi gami da yi mata godiya, bata ko
jirayi amsa masa ba tayi gaba da sauri shima ya wuce ya tada motarsa
ya fice a layin.
Tun daga nesa take hangowa kamar shine sabe sa abdallah ya zuba
mata idanu, sai data qaraso gab da shi ta tabbatar shi din ne
kuwa,hannunsa dauke da leda wadda ta tabbatar abdallah ya yiwa
siyayya kamar yadda ya saba
“Waye wancan?” Ya tari numfashinta ya furta fuskarsa a dan daure ta
hanyar riga ta yin magana,dan galala tayi tana dubansa cikin
mamaki,sai kuma ta basar ta saki dariya cikin tsokana tace
“Bazawari na ne”
“Bazawarinki?” Ya tambaya cikin nanatawa har sau uku yayin da ta
tsaya tana sake dubanshi
“Eh mana” ta fada kanta tsaye,shiru yayi kamar zaiyi magana sai kuma
ya fasa ya sauya akalar abinda zai fada din da cewa
“Ok,muje qofar gida akwai maganar da nakeso muyi” ya fada cikin
magana ta gaske yana yin gaba, kamar an qulle bakinta sai ta ja
qafafunta ta bishi.
Qofofim gaban motar ya bude ya shiga nashi mazaunin yana dauke
da abdallah wanda baiko damu da ganin maman tasa ba,ya wani lafe
jikin abdur rahman din yana ta fama da biscuite,dubanta yayi ganin
tana tsaye qiqam a waje
“Bismillah shigo ki zauna” kafadunta ta daga
“Haba,ai kaima kasan bai kamata ba,mu shiga cikin gida kawai ko meye
ai ina ga sai yafi dadin tattaunawa ko ba cikin mota ba”
i nasan da cikin gidan,amma maganar bata cikin gida bace,idan
kuma kina da wani gu da zamu mu tattauna kuma to” kanta ya daure
tana mamakin wacce iriyar magana ce haka da yakeso suyi da sai su
kadai?
“To amma kuma malam fa,idan ya dawo ya ganni cikin motarka”
“Indai malam me baki da matsala,na gaya miki hakan da gaske” dan
shiru tayi sannan ta sake bude murfin ta shiga ta zauna ba tare data
maida murfin ta rufe ba,abdallah ne ya soma yunqurin tahowa gunta
hakan ya sanya ya miqa mata shi,sai da ta zaunar sa shi sosai ya nutsu a
gunta sannan ya soma magana
“Sumayya.
Yadda yayi kiranta ya sanya ta daga kai ta dubeshi
“Kinsan cewa tun kafin a haifemu Allah ke rubuta mana dukkan wani
abubda zai faru da mu har ya zuwa ranar mutuwarmu ko?”.kai ta jinjina
tana bashi dukkan nutsuwarta
“a gaskiya sumayya bazan cuci kaina ko na zalunci kaina
ba,sumayya….haqiqa na ga dukkan wasu halayya na mace ta gari,naga
dukkan wasu dabi’u na macen da za’a iya aure ta zama uwar ‘ya’ya,na
gamsu na nutsu,nagano alkhairai a tattare da ke sumayya,da haka
zuciya ta ta fara qaunarki sumayya,zuciyata ta gamsu da ke a matsayin
wadda zamu rayu tare,ina sonki ina qaunarki,ina buri ki zama mata
ta,ina kuma fatan zaki amince da maganganuna,kin san ko waye abdur
rahman sumayya tun ba yau ba,saboda haka mene ne ra’a yinki a
kaina?”
Dariya dariya ta saki duk da tarin mamakin dake cunkushe cikin
Zuciyarta
“Kai abdur rahman,Allah ka iya wasan kwaikwayo,kyanka dramer”
“Sumayyal!” Ya kira sunanta da dan qarfi wanda shi ya sake jan
hankalinta gareshi
“Dubeni da kyaul,kinga wasa a idanu na da fuska ta bare
kalamaina?,wallahi billahi babu wasa cikin lamari na,da qarfina nazo
gareki sumayya ko yau kika amince a shirye nake da a daura min aure
da kai”.
Sosai maganar ta daki qirjinta,sai ta shiga kada kai kamar
qadangaruwa,da qyar ta qwaci kalmar
” haba abdur rahman,ka rufamin asiri mana,ka manta kai waye ne?,kai
dan kawun mukhtar ne fa,ko ka manta mukhtar kamar yaya yake a gare
ka?,baya ga haka ma so kake duniya ta zage ni?,nifa bazawara ce har da
yaro na,kai kuwa matashin saurayi ne da ko auren fari baka yi
ba”murmusawa yayi yadda yaga tsantsar tashin hankaki kan fuskarta
kamar wadda aka ce za’a yanka,sai maganarta ta biyu data bashi
dariya,dududu ita din ma nawa take, yammata da yawa wasu masu
shekaru irin nata ma ba’a fara zancan aurensu ba,wasu kuwa sai a
lokacin suka isa auren ma,shekara ashirin kacal da take da su din,idan
ba ita ta fada ba babu mai yadda tayi auren fari ma bare haihuwa,kai ya
kada da ya tuna ita din farin shiga ce, baki daya ta rude,dole ya bita a
hankali har ta sake da shi
“Dukka wadan nan basu isa hujjoji a gareni ba sumayya,jeki gida ki
nutsu kiyi shawara,na baki nan da sati guda,amma kada ki manta ni din
ina sonki kuma in sha Allahu sai na aureki”. Har wani tsoro ta dinga ji
haka taja qafafunta da sukayi sanyi tamkar an buge mata su ta fita daga
motar ta rufe masa ita,sai ta kasa motsi har yaja motar ya soma fita a
layin tana jin motar da idanu.
Horn din da aka danne shi ya sanya ta dawowa daga karanta
wasiqar jakin data tsaya yi a qofar gida, abdallah na kafadarta duk ya
bata mayafinta da nashi bakin da burbushin biscuite amma sam bata
ma ankara ba,idanunta ta juya zuwa gabanta,mukhtar ne zaune cikin
motarsa yana dubanta,fuskarsa a hautsine kamar wanda aka kikkifawa
mari,a hanzarce ya fito daga motar ya zagayo zuwa inda take yana fidda
wani huci
“waye waccan?”ya tambaya yana mata nuni da motar abdur rahman
dake gab da qulewa zuwa kan babban titi,sai tabi inda yake nunin da
kallo kamar bata san motar da yake nunawa din ba,mamakin
tambayarsa da dalilin fusatarsa ya taru ya sake daskarar sa
qwaqwalwarta,cikin qarfin hali tace masa
“Gurina yazo,sai me?”, mamaki ya kamashi, shi sumayyan ke gayawa
haka,zuciya ta taso masa iya wuya, hannu yasa ya fincike abdallah daga
hannunta har ya dan tsorata ya tabe baki zai sa kuka,sai ya rungumeshi
a aqirjinsa,yayi luf kuwa abinsa don tuni ya jima da gane shi,akwai sabo
da shaquwa sosai tsakaninsu,cikin tsantsar bacin rai yace da ita
“sai me kuwa?,ba damuwata bace,saidai ki sani bashi da alaqa ya yaro
na,kiyita fitowa gunsa amma badai da yaro na ba”sai ya juya ya bude
motarsa ya shige ya tada ta ya bar layin.
Kuka ta saki ta shige cikin gida da gudu wanda ya ja hankalin mama
dake bakin qofar madafi zaune tana gyara kwanukan abincin daren
malam,tsaye ta miqe tana tambayarta lafiya
“Mama ya karbe abdallah ya tafi da shi”
“Waye?,waye ya tafi da shi” ta tambaya cikin rudewa
“Mukhtar mana” ajiyar zuciya ta saki hankakinta na kwanciya,tayi zaton
wani ne ma daban,harara ta balla mata
“Sai aka ce miki saceshi yayi?,ko ce miki akayi bazai dawo da shi
ba?”.kai ya gyada
” bazai dawo da shi ba mama”harararta ta sake yi
“Maras kunya,idan bai dawo da shi din ba sai me,ba ubanshi bane,ke
yanzu akan dan farin kika tsaya kina min kuka?, matsa ki bani guri”janye
jikinta tayi ta shige daki tana ci gaba da matsar qwalla,ta yadda lallai
har yau akwai sauran quruciya akan sumayyan,ko tsabar tabara ce oho.
Har maman ta gama abinda take bata iya yin shiru ba,ji take kamar ta
fita ta karbo yaronta.ganin bilhaqqi da gaske kukan take ya sanya
maman binta daki ta kwantar mata da hankali,ita dai jin maman take
kawai,gani take bazai dawo mata sa shi ba,da qyar ta fita ta dauro
alwalar sallar magariba ta dawo ta tada sallar tana kasa kunnen ta inda
abdallanta zai bullo,abun sai ya hadu ya dagule mata,ga zancan abdur
rahman ga kewar yaronta.
tofa masu karatu, nasan yanzu zamu fara raba team.ga team ABDUR
RAHMAN,ga MUKHTAR ga kuma wata sabuwa LUKMAN
Har ta idar sallahr isha’i babu abdallah ba mukhtar,sai ta rushe sa
kika ganin qarfe takwas na neman gotawa, komawa tayi ta jingina da
jikin katifa tana maida numfashi tare da sakin ajiyar zuciya.
Kamar daga sama taji muryar mukhtar din kamar daga can soro
suna magana da yaya abubakar,sai ta miqe zumbur ta zauna tana
saurare har zuwa sanda abubakar din ya daga labulen qofar dakinta ya
leqo
“Kije ki karbi abdallah,wai yau ni zaiwa rashin m yaga babansa yaqi
yarda na karboshi” ya qarashe zancan yana sakin labulen,tana ji yana
ma mama qorafi tana musu dariya,zumbur ta miqe kamar mai
jira,dama tun hijabin da tayi sallah shine a jikinta bata cireshi ba.
A soron ta tadda su tsaye yana rungume da abdallan,tana zuwa ta
miqa hannu alamar ya bata shi,banza yayi kamar bai gane me take nufi
ba.ya dubeta fuskar nan a dinke tsaf
“Duk randa kika sake gigin fitowa gun bazawarinki da yaro na,idan har
na tafi da shi ya tafi kenan har abada” ya qare maganan sannan ya miqa
mata shi wanda tuni bacci ya fara dibansa,hannu tasa cikin azaba ta
karbeshi,cikin hanzarin ta shige gida kamar wanda zaice mata dawo da
shi,binsu yayi da kallo har suka shige.ya jima tsaye cikin soron ba tare
da ya iya tafiya na a haka abubakar ya cimmasa sannan sukayi sallama
ya tagi,har yanzu bai cimma burinsa na ganin wanda ke zuwa gun
sumayyan ba,amma babu shakka ba zai guahe ba har sai ya gano waye.
Dare ya fara miqawa amma tana kwance idanunta biyu,abdallah na
jikinta yana ta barcinsa,a haka halima ta daga labulen dakin ta shigo
“Yaya sumayya wani ne keta kira tun dazu yana cewa sumayya yake
nema,nace masa ba ita bace amma yace ita ta bashi number din”
“Wani?” Ta tambaya cikin mamaki,don har ga Allah ta mance shaf da
luqman.
“Eh.yace dazu da yamma” sai a lakacin ta tuna da shi,don baki daya
abdur rahman ya hargitsa tunaninta,maganar sa ta mata girma,ga
mukhtar shima da yaso hautsina ta,kafin tace komai wayar ta sake
ruri,haliman ta kalleta
“Yaya gashi,shi ya sake kira” tsaki ta dan ja tana ganin baiken kanta tun
farko da bata bashi lambar bogi ba,kanta ta maida kan filo sannan tace
“Kice da shi nayi bacci”
“Amma yaya..” Haliman taso yin qorafi saboda ba sabonsu bane yin
qarya
“Don Allah ki fita ki bani guri ki gaya masa yadda nace din ko kisan me
zaki gaya masa” ganin sumayyan ta harzuqa har haka wanda basu saba
ganin hakan tattare da ita ba ya sanya ta juya ya fice ba tare data amsa
wayar dake ta faman kururuwa ba.
*******
*****
***
Cikin kwanakin da suka biyo baya gaba daya haka take wuni
sukuku,ga maganar abdur rahman dake mata amsa kuwwa a kai,gefe
guda kuma ga luqman daya matsanta da kiran waya ba dare ba
rana,duk da ko daya bata taba amsa wayarsa ba amma hakan bai sanya
ta gajiya ba.
Gani take baki daya abdur rahman ta shigo da maganar ne don ya
dagula lissafinta,domin shi kansa yasan yana magana ne kan abinda
bashi yiwuwa,ta yaya zata aure shi bayan ta auri dan uwansa?,ta yaya
zata yadda ta sake maida kanta cikin ahalin da bata da farinjini ko sau
daya a gunsu?,ahalin da tasha wahala tasha jinyar zuciyarta duk a
kansu,ahalin da basu ganin alkhairi tattare da ita?,duk a ture ta wannan
ma yaushe zata aure musu abdur rahman?,matashin saurayin da ko
auren fari baiyi ba?,sam bata jin zata iya wannan abu koda a mafarki ne
ballanta na kuma a gaske.
Ranar da ta fara amsa wayarsa suna zaune ne baki dayasu a falon
maman suna cin tuwon dare wayar haliman ta sake tsuwwa karo na
wajen uku kenan,mama ce da ringing din wayar ya soma damu ta dubi
halima
“Wai halima idan ba zaki daga wayar nan ba ki kashe ta mana haba”
“Mama bani ake kira ba yaya ake kira.yau kusan kwana hudu kenan wlh
taqi ta daga ko sau daya” sai maman ta juya tana suban aumayya
wadda ta cika tayi fam sabida halima ta gayawa maman
“Ke sumayya wake kiranki” cikin murya mai kama da shagwaba wanda
sau tari idan ranta na bace bata aon magana haka yanayin muryarta ke
komawa tace
“Wani ne nima mama ban sanshi ba”‘hade rai maman tayi sannan tace
“Ha’aa,baki sanshi ba kamar yaya?,ina cewa ke kika bashi lambar ko?”
Dan jim tayi sannan ta syada kai
“To maza bana son shashanci karbi ki amsa kirab,na gane take takenki
sarai,kuma kinfi kowa sani malam ya fara maganar baiga kina magana
da wani ba,kinsan halinshi sarai tun da can baya ma shi ba mai barin
yara su girme a gabanshi bane,su kansu su halima rashin tsayayye ye ne
ya sanya har suke gida iwar haka” gabanta ya fadi fargaba ta
lullubeta,wani irin aure kuma?,duka duka mutuwar auren nata da bai
wuce shekara biyu ba?,tilas ta karbi wayar ta miqe ta shige daki.
Sun dan dauki lokaci kan wayar yana qoqarin shigar da kansa a
gunta,ba yabo ba fallasa ta amsa masa duk wata magana da yayi
mata,da qyar ya shawo kanta ta bashi lambarta,yayi murna da godiya
sosai tare da alqawarin zai kirata gobe,tabe baki tayi tana bin wayar da
kallo bayan sun gama wayar,sai ta miqe nan saman katifa tayi
kwanciyarta taqi komawa falon don koda ma mama ta sake baro wata
maganar.
****
*****
******
Kullum ta Allah baya fashin kiranta,koda kuwa bata dauka ba zai
mata tex,qoqarin kafa kanshi yake sosai da gaske,duk da gaya masa ita
din fa ba budurwa bace har da yaronta,yace babu komai shi hakan ma
yake so,a haka har sati dayan da abdur rahman ya diba mata ya
cika,satin guda cif bai sake nemanta ko takowa gidan ba har cikar
wa’adin kwanakin.
Tun safe take addu’ar kada Allah ya dawo da shi,a haka har lokacin
tafiya makaranta yayi ta shirya ta tafi tare da abdallah wanda yau ya
tubure sai ya bita.
Yau sai kusan biyar suka taso,tun daga qofar gidan ta hangi
motarsa,a hankali ta dinga takawa jikinta a sanyaye har ta isa gab da
motar,qofar mazaunin direba a bude take alamun mamallakin motar
yana ciki,tuni abdallah ya gane motar waye.ya zame daga jikinta yayi
wajen motar yana kiran abba,hankalin abdur rahman yayo wajen ya
waiwayo yana murmushi sannan ya fito ya dage shi sama ya cafe suna
dariya,sanye yake da yadi irin na maza blue black,hula da takalminsa
sau ciki duka baqi,.yayi kyau sosai. Ya sauke idanunshi a kanta yana
kallonta
“Yau kam kin dade,kinsan tun nawa nake nan ina jiranki?” Kai ta girgiza
ba tare da tace komai ba,yatsun hannunsa ya daga guda hudu ya nuna
mata,sannan ya dora da fadin
“Shine yau kika dauke abokin hirar ko?” Kai ta sake kadawa sannan
tace
“Shine ya nace yau sai ya biji,nima bana son tafiya da shi”
“Mukam muna maraba da shi ko yaushe, shiga ki kintsa kafin naje can
qasan layinku na dawo na baki minti talatin”
“Amma dai da ka shigo ciki ko?”
“Amma dai kinsan gunki nazo ko?”ya bata amsa da salon yadda tayi
tata maganar,ta lura jan magana yake ji saboda haka ta sanya kanta
gida tana fadin
“A dawo lafiya”.
Salla kawai tayi wadda lokacinta ya kubce mata,ko abincin ta kasa ci
tanaa zaune tana nazarin hanyar da zata bi abdur rahman ya janye
zancansa salin alin ba tare da an kai ruwa rana ba,don gaskiya bata jin
zata iya maida kanta cikin familyn su mukhtar,an gudu ba’a tsira ba
kenan,ko kuma tsugune bata qare ba?,cikin haka zainab ta shigo dakin
ta gaya mata taje ya abdur rahman na waje ta karbi abdallah.
Kamar wancan karon wannan ma haka ya tilasta mata shiga motar
tasa,shuru ya ratsa motar na wasu daqiqu ba wanda ya sake cewa uffan
bayan abdur rahman ya gama jaddada bayanansa a gareta
“Da farko abinda zan fara cewa shine na gode na gode matuqa,na yaba
da qaunata da kace kana yi,har ka nuna sha’awar zamantowa abokiyar
rayuwarka duk da ban cancanci wannan darajar ba,amma abdur
rahman kayi haquri,bazan iya aurenka ba,saboda wasu dalilai wadanda
ni da kai duka mun sansu wasunsu kuma ni da ubangiji na ne kawai
muka sansu” kai yake jinjinawa yana dubanta sannan yace
“Ban gamsu da baya nanki ba ko kadan,babu wani abu da zai sanya ni
janyewa daga batun neman aurenki sumayya, ina sonki babu wanda zai
hanani”so take ya fahinceta bilhaqqi don su bar maganar sun wuce
gun,sai ta sake fuskantar sosai wani abu na taba zuciyarta na daga
abubuwa da suka faru da ita a baya
“ta yaya abdur rahman kake so na sake komawa cikin danginku,bayan
kaima kana daya daga cikin mutanan da zasu shaidi irin rayuwar da
nayi a cikinsu.ya kake so ka sake maidani rayuwar baqincikin da nayi
bankwana da ita?,ko kuwa zaka sauya dangi ne saboda zaka aureni ni
sumayya ‘yar gwal,ko ka manta waje mijina na baya,ka manta alaqar da
take tsakanin ku,don Allah abdur rahman muci gaba da mutunci mu
aijiye zancan soyayya a gefe “ta qarashe maganar tsohon mikin dake
zuciyarta na taso mata,sai ta sanyo qafafunta waje ta fito daga motar,da
sauri shima ya fito ya zagayo inda take tsayen, kafin yace mata komai
suka ji tsaiwar mota,waiwayawa sukayi dukkansu don ganin waye.
Mukhtar ne,tun yana cikin motar tasa yake qarewa motar kallo,babu
shakka wannan motar yake tawan gani a qofar gidan su
sumayyan,kenan yau zai ga waye mamallakinta zaiga wake zuwa
gunta,amma idan idanuwansa na nuna masa dai dai kamar abdur
rahman yake gani tsaye tare da sumayya,to meye yake hakaa
gidan?,meyw hadinsu?,shine mai motar da yake gani kullum na ficewa
daga layin?,don samun amsaoshin tambayoyinsa sai ya balle murfin ya
fito bayan ya kashe motar ya nufosu idanuwansa a kansu zuciyarsa na
azalzala tare da ayyana masa wani abu wanda baya fatan
kasancewaraa.
Sallamarsa ita ta katse abdur rahman daga kallon sumayya da tuni
idanunta suka cika da qwalla,sannan suka katse shi dag fadar abinda
yake shirin fada,dukkansu waiwaya suka yi suka dubeshi,fuskar abdur
rahman din dauke da murmushi ya miqawa mukhtar hannu yana fadin
“Ah,ya mukhtar kai ne?” Baiqi miqa masa nasa hannun ba suka yi
musabaha yana fadi tare da tsareshi da wani irin kallo
“Eh.ya kawu da sauren mutanen gidan”
“Duka lafiya alhamdulillahi” ya fada yana sakin hannun mukhtar din
sannan ya juya ga sumayya
“Ki nazari a nutse,kada ki ruda kanki,kada ki cuci kanki ki cuceni,gobe
in sha Allah zan dawo” ya fada yana juyawa zuwa wajen
motarsa,dukkansu ita da mukhtar din suka yi masa rakiyar
idanuwa,saidai kowa da abinda ke kai kawo cikin zuciyarsa.ya bude
motar ya shiga bayan ya bawa abdallah ‘yar madaidaiciyar baqar leda
cike da biscuite da choculet ya saukeshi ya tada motar ya wuce.
Wani abu ne ya tokare masa wuya yana jin wani irin bacin rai na
taso masa,sai yayi qoqarin dannewa ta hanyar daukar abdallah da ya
nufo gunsa kai tsaye yana fadin daddy daddy,motsawa sumayya tayi
don shigewa cikin gidan cikin hanzari ya sha gabanta
“Me abdur rahman ke zuwa yi gunki?” Idanunta ta dora a kansa kanta
tsaye tace
“Alheri”
“Alheri wanne iri?,kada kice min gonata yake son shigowa?”wani irin
kallo ta masa
“Yaushe ka fara noma?,dama kana da gona ne?,alheri kuma duka alheri
ne babu wani banbanci” ta fada tana rabeshi zata wuceshi ranta a
bace,baisan ya riqo gefen hijabinta ba hakan ya sanyata waiwayowa
tana dubansa a mamakance
“Me yasa kike cutar da ni haka sumayya me na miki a rayuwa da zafi?”
Ya fada zuciyarsa na zafi yayin rauni ya bayyana qarara a fuskarsa
“Cutarwa?,ni nake cutar da kai ma mukhtar!” Ta fada tana nuna qirjinta
da yatsa cikin mamaki,sai ta juyo baki daya tana dubansa sosai
“Bance ka cutar da ni ba mukhtar ni da ka saka saki uku ina
kwance?,bance ka cutar da ni ba ni da ka yanke min hukunci kan zato
da zargi,ka yanken hukunci ba tare da kayi bincike ba?.”
“Wanne bincike sumayya bayan ba labari aka bani ba,na gani da ido
na,sannan bincike na likita ya sake tabbatar min da kinsha din wanne
bincike kike da buqata nayi bayan wannan” a kaikaice takw dubansa
sannan tace
“ok ko?,to shikenan.yayi kyau hakan ai,amma shawara zan baka ka fita
daga dukkan harkoki na,ko da maza dari zaka ganni da su wannan ba
damuwarka bane,tunda dai a yanzu ba qarqashin ikonka nake
ba,gashin kaina nake ci sai ka shafamin lafiya” tana gama maganar ta
juya tayi shigewarta cikin gida ta barshi da abdallah.
Binta yayi da kallo,taushe sunayya ta koma haka,yaushe bakinta ya
bude da magana haka?,saidai batayi laifi ba yana ganin baiken
kansa,tabbas ba shakka gaskiya ta fadi yanzun ita din ba huruminsa
bace,baisan me ya sanya ya shishshigewa lamarin rayuwarta har haka
ba.jiki ba qwari ya koma mota ya dauko siyayyar abdallah ya riqoshi har
bakin qofar da zata sadaka da tsakar gidan ya ajiyeshi ya wuce,cikin
mota yana tuqi yana tunanin yadda zai raba kansa da shiga
lamuranta,don bisa gaskiyarta take,wani sarawa kansa yayi wanda
hakan ya sanyashi yin parking motaraa gefan titi ba shiri.ya dauki a
qalla sama da mintuna talatin kafin yaci gaba da tafiya.
**************
Duk yadda taso abdur rahman ya fahimci abinda take nufi yaqi
fahimta,sai ta tattarashi ta janye masa jiki, sau tari takan qi dawowa
daga makaranta akan kari,tana kuma dawowar lokacin sallar magariba
ne,daga nan kuma suna zama karatu da malam wanda ya sanya musu
wasu litattafan addini wanda suke hadda ce wasu abubuwa a ciki,sam
ta daina bada wani gaf ko wata dama da zasu kadaice har suyi
magana,idan ana tare cikin jama’a zasu yi magana da shi kamar kowa.
Ta bangare daya kuwa luqman shima ya matsa lamba,tilas ta bashi
dama yazo gidan sau daya,a ranar malam ya dawo ya ganshi suka
gaisa,saidai malam din baice mata komai ba kamar yadda ta
zata,hakanne ya sanya ta saki jiki har ta sake bashi wasu damammakin
yazo wai koda hakan zai sanya abdur rahman ya janye daga
qudirinsa,saidai duk da hakan babu abinda ya girgiza shi,har mamaki
abun ke bata,cikin lokaci qarami ya sanyata ta saki jikinta da shi,mutum
ne mai barkwanci da yawan bada labarai,ko bata son magana sai ya
sanyata dariya.
Abinda bata sani ba malam din na sane da komai,bata san da hakan
ba sai ranar da aka kai kudin auren abubakar da saka rana wanda baki
daya aka tsaida watanni biyu,washegarin ranar malam din yayi kiranta
falonsa,bayan ya kammala duka abubuwan da yake ya dubeta
“Am sumayya,nasan cewa kinsan tsarina da al’ada ta gidan nan,sannan
alhamdulillah kin san mutuncin mace dakin mijinta,baki da inda yafi
nan daraja,dukkan wani abu da ya faru a baya mu aijiyeshi gefe haka
Allah ya tsarama rayuwarki.cikin KUNDIN QADDARARKI yake,babu
wanda ya isa ya goge miki ko ya kautar miki da shi”
“Haka ne malam” ta fada kanta na duqe zuciyarta ba bugawa kamar
zata bullo,addu’a take kada Allah yasa malam ya bullo mata da zancan
da bata da bugatar jinsa a yanzu
“Sumayya,yaron nan abdur rahman yazo guna ya gabatar min da kansa
a matsayin manenin aurenki,to amma kasancewarki bazawara a yanzu
addini ya baki damar zabawa kanki mijin aure ya sanya nace sai na
tambayeki naji mene ne ra’ayinki,kada ki zalunci kanki a yanzu kina da
dama,sannan zaman aure zama ne bana yau ko gobe kawai ba,zama ne
na har abada”. Wani tashin hankali ne ya rikito mata,abubuwan da suka
dinga faruwa da ita zamanin tana auren mukhtar tsaf suka dinga dawo
mata,a hankali ta bude bakinta muryarta na rawa
“Kayi haquri malam,abdur rahman dan uwa ne ga mukhtar dan wan
babansa ne nasan kasan haka malam” murmushi ya saki
“Sumayya,sumayya kenan,wannan duka ba abun damuwa bane tunda
dai aure ya halasta a tsakaninku ba haramun bane” tashin hankali ta
fada cikin zuciyarta, yan uwan mukhtar fa sune dai ‘yan uwan abdur
rahman,ba’a canzawa tuwo suna
“Malam,ina tsoron sake kasancewa da ahalin su mukhtar.” Sai tayi
shiru ta kasa qarasawa,shima shirun yayi yana nazarin
maganarta,tabbas sumayya yarinya ce mai matuqar zurfin ciki,a iya
zamanta na aure bazai iya fadar ranar data kawo matsalarta ba,saidai
idan an fahimta a maganta mata.
“Ke kike da zabi a hannunki ai,ba zan miki auren dole ba”
“Malam,ina so abdur rahman ya janye daga qudurinsa, bana son sake
shiga ahalinsu” ta fada zuciyarta na raurawa muryarta na rawa
“Shikenan zancansa ya wuce,sai ki fidda miji ina son hada aurenki da
na yayanki abubakar idan ta kama har da su halima baki daya”
“Amma malam ba..”
“Sumayya,bana son qorafi ko wata magana,kinsan ba zaiyiwu kici gaba
da zama a gida ba,shekara nawa,shekara daya ana gab da cika ta biyu”
shuru tayi don tafi kowa sanin waye malam,amma ina mafita meye
mafitarta?,
“Sumayyan luqman fa?” Taji ya jefo mata tambayar wadda ta sanya
dago kanta ta dubeshi,murmushi ya kuma yi yana dubanta
“Mamaki kike yadda na sanshi?,ya fara zuwa gunki ba da izini ba ya
karya doka ta,hakan ya sanya nayi bincike a kansa,na samu gamsassun
bayanai a kansa,mutumin kirki ne bakin gwargwado” sai ya dan ja fasali
yana dubanta kafin yaci gaba da cewa.
“Lukman na da matar aure daya da yara hudu,hakan shike nuna
zaiyi riqon Allah tunda har yana da wata matar ya saba riqon macen
aure,bawai zaiyi aurensa na fari bane,amma kije kiyi tunani kina da
sauran lokaci har kwanaki talatin,Allah ya zaba mana abinda yafi
alheri,tashi kije”.
Tamkar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka take tafiya har ta isa
dakin ta,kusan ranar baki daya akwance ta yita,tana jin abdallah yana
qiriniyarsa har ya gama yayi bacci anan wurin.
**** *****
****
***
Mukhtar bai fasa zuwa ganin yaronsa ba kamar yadda abdur rahman
bai fasa zuwa gidan ba,saidai baki dayansu ganinta ya musu wahala, ba
wanda take yarda ya ganta saidai bacin rana,ta bangare daya lukman
naci gaba da nacin sake zuwa wajenta,saidai ko sau daya taqi yarda ya
kuma zuwa din,wani irin so lukmam din ke mata wanda ke bata
mamaki kuma ya fara sanya mata tausayinshi,duk randa baiji muryarta
ba yakan zamo kamar wani soko ko zautacce.yayi ta jera kiran kenan
har sai ta gaji ta daga,hakan ya sanya sau tari takan dan sassauta masa.
Lokaci ne yaci gaba da tafiya,kwanakin da malam ya diba mata na
kuma tafiya,a haka har aka cimma kwanaki talatin din cif,saidai s
run
da taji malam din bai tada mata maganar ba ya sanya ta kwantar da
hankali ta ta kuma sake sakankancewa abinta, har aka fara sabgar
shirye shiryen auren yaya abubakar da ita.
Ranar wata juma’a da wani yammaci wanda ya tasamma kwanaki
arba’in da yin maganarta da malam bayan sakkowa sallar juma’a
malam din ya dawo gida yaci abinci sannan ya sanya aka kira masa ita.
Tunda taji kiransa hankalinta yayi mummunan tashi,a lokacin suna
dakin mama suna shirya akwatin kayan lefan yaya abubakar da ake
saka ran kaiwa satin sama.
“Ya ake ciki sumayya,kwanakin da na diba miki sun shude har da
doriya ba tare da naji komai daga bakinki ba”.
Cikin yanayi na daburcewa tace
“eh malam dama….dama.”
“Unhmmm,dama mene?,kin haqura kin zabi abdur rahman dinne” da
sauri ta girgiza kai
“Ok lukman din ne?” Nan ma kai ta girgiza,sai malam din ya sauya
fuska sosai sannan yace
“Ki bude baki kimin magana sosai,idan ba haka ba zan bawa abdur
rahman dama ya turo,saboda daga shi har lukman din babu mai aibu a
cikinsa,aure kuwa mutunci da kamala shine abu mafi muhimmanci da
za’a fara nema a cikinsa” tuni hawaye ya fara wanke mata fuska
“Malam bana son sake hada zama da su abdur rahman ka yimin afuwa”
karo na farko da ta fara yima malam din musu,duk sai tajita wani
iritana jin kamar tayi ba dai dai ba
“Shikenan,a bawa lukman din dama ya fito kenan?” Shiru tayi kamar
wadda ruwa ya cinye,ta yaya zata sake musa masa bayan ba al’adata
bace?,baya ga haka kuma yayi bincike halayyarsa ta yi masa me zata ce
kuma?,ganin batayi magana ba ya sanya ya sake maimaita tambayar
tasa saidai nan ma shiru ne ya biyo baya bata ce komai ba,a bisa ga
abinda addini ya nuna shiru alamar amincewa ce da hakan malam ya
dauka cewa ta amince
“ShikenanAllah ya tabbatar da alkhairi,Allah yayi miki albarka ya
albarkaci aurenku,tashi ki tafi” abinda taji malam din ya fada kenan.
Ita dai bata san yadda aka yi ta kai kanta dakinta ba,sai tsintar kanta
tayi saman katifarta tana malelekuwa hawaye na malala daga idanunta
“Shikenan,shikenan lukman cikin KUNDIN QADDARATA?,” abinda ta
dinga nanatawa kanta kenan,kuka tayi na fitar rai a ranar,sai ta dingajin
wani banbarakwai wai yau ita zata sake auren wani?,su zauna suyi
rayuwar aure da shi.
Washe gari lukman ya kirata,murna kamar ya taka rawa cikin
waya,daga qarshe yace mata jibi yana tafe in sha Allah bayan masu
kawo kudi sun tafi.
Washe garin kuwa iyayen lukman suka iso,naira dubu dari suka
kawo kudin har da kudin sa rana,sannan suka ce sati na sama za’a
kawo lefe,duk yadda malam ya dakatar da bidi’ar da ya lura suna shirin
yi amma sunqi.ganin cewa ko aurenta na fari bai karbi kudin aurenta
har haka ba bare yanzu,sunce angon keson hakan tilas ya haqura.
Qarfe takwas ya kira wayarta ya shaida mata ya iso,ba wani abu da
ta sanya ko ta sauya, kayan dake jikinta da hijabinta duka da su ta
fita,fuskarnan duka a kode saboda kuka,mama na lura da ita amma sai
ta alaqanta hakan da cewa wata qila tsananin sabo da rayuwar da
sukayi da mukhtar ya sanyata take jin duka ba dadi zata sauya sheqa,ita
dai da addu’a take binta tare da fatan alheri.
Yana zaune cikin motarsa sanye da shadda cream colour sai maiqo
take,ta masa cas tare da yi masa kyau ta kuma haska kwantacciyar
fatarsa kalar choculet,fuskarsa kawai zaka kalla kasan cike yake da
farinciki da annashuwa,murmushi ne zallah kan fuskar tasa kadan
kadan,lukman na cikin sahun tsaka tsaki na kyawawan maza,waqa ce
ke tashi a motar tasa wadda aka ragewa sauti sautinta can qasa,wanda
kalaman soyayya me kawai zalla cikin baitukan waqar.
A jikin motar ta tsaya hannayenta harde a qirjinta,wani banbarakwai
take jin ta baki daya,bai lura da tsaiwar tata ba sai da ya daga kai da
nufin ganin ko ta fito saboda yadda ya zaqu yaga abar qaunar tasa,da
hanzari ya fito daga cikin motar ya rufe sannan ya zagayo zuwa inda
take
“Ranki ya dade da kin shigo ai saboda kada ki gaji da tsaiwar”
“A’ah na gode, nan ma ya isa” ta fada tana gyara tsaiwarta,gaisheshi tayi
don gajarta maganar.ya amsa a tausashe
“Naji dadi qwarai da gaake da kika aminta dani a matsayin mijin da
zaki aura,ina fata Allah ya sanya alkhairi a tsakaninmu amin,kuma in
mai miki albishir da cewa da yardar Allah zan baki dukkan wata kulawa
data dace,Allah ya tabbatar mana da dukkan alkhairinsa”
“Amin ” ta amsa can qasa,haka ya dinga janta da hira tana
saurarensa,ba shakka ya iya kalamai na soyayya da jan hankalk,ta kasa
kunnuwa tana saurarensa saidai duk yadda yaso bata farinciki ta kasa
jin farincikin dai dai da qwayar zarra,a haka suka shafe mintina talatin
kafin wayaraa tayi tsuwwa ya daga ya kara a kunnensa
“Allah ya taimakeki gani nan zuwa” ya fada yana maida wayar
aljihunsa,sai ta lura kamar duka hankalinsa yayi gaba ya dubeta
“Uwar gida tayi kira ni zan koma sai wajen jibi haka” bata damu ba ko
kadan tace
“Allah ya kaimu” duk yadda yaso ta karbi kudin da ya mata kyautarsu
taqi karba haka ta juya ta shige gida.
Bakin katifa ta zauna tana sauke ajiyat zuciya, kafin qwaqwalwarta
takai ga tuno wani abu wayarta ta fara tsuwwa,ta sanya hannunta ta
dagota ta duba mai kiran,sai taga anty dije ce,ji tayi kamar an mata
rahama,tun kafin ta kai ga dagawa zuciyarta ta karye,da dake ta amsa
kiran nata, bayan sun gaisa anty dijen tace
“Ance min kina nan kina ta kuka saboda zaki sake aure ko?,ince dai ba
mukhtar kikewa kukan ba?” Girgiza kai tayi kamar tana gabanta ta rasa
me zata ce mata don ita kanta bata san me takewa kukan ba
“A’ah anty”
“To baki son angon ne?”
“Nima ban sani ba anty” ta fada da gaskiyarta,shuru anty dijen tayi tana
nazari,tana tunanin har yau zuciyar sumayya a kulle take,babu mamaki
har yanzu batasan soyayya ko qiyayya ba duk da tayi zaman aure na
wasu shekaru
“Indai har baki sani din ba ina son ki kwantar da hankalinki,mai yiwuwa
ki koyi yadda zaki soshin tunda baki tantance mai kike ji a kansa
anason ki dinga daga hankalinki sumayya kinji,kiyi addu’a kibi
komai a sanni,duk abinda kika ya zowa bawa ya dauka hakan
MUQADDARI ne daga ubangijinsa”
“To anty in sha Allah” ta fada tana jin qaunar anty dijen na ratsata,duk
cikin ‘ya’yan ‘yan uwa anty dijen tafi sonta, haka nan Allah ya hada
jininsu tana jin sumayyan ne kamar diyarta saboda irin halayyar da take
sa ita wadda ta banbanta da ta sauran
“Maman ta gaya min sati na sama za’a kawo lefe,sati biyu masu zuwa
zq’a fara biki har da na abubakar ko?”
“Eh” ta amsa a sanyaye
“To shikenan babu damuwa,cikin satin nan kamar naji hajiya bilkisu
matar professor zata aiko direbansu kano zai mata siyayyar wasu
kaya,zan tambayi hajiyan idan zai iya qarasowa nan sai ya daukoki ya
kawomin ke,idan yaso satim bikin sai mu taho baki daya ko?” Duk da
bata sha’awar zuwa abujan amma bai kamata taqi ba sai ta amsa mata
“To anty na gode a gaida min da minar dita(amina ne sunan kakarsu ce
ake ce mata minal sumayya ke tsokanarta da minar)” dariya anty dije
tayi tana cewa
“Zataji,nasan babu zama indai taji kina zuwa abuja” itama sai ta dan yi
murmushi saboda tana son qiriniyar yarinyar.
***** *********
Qarfe goma na safiya dai dai kamar yadda anty dije ta gaya mata
direban ya iso,da qyar lukman ya bar tafiya dan dai yaji anty dije ce
amma cewa yayi baiso ta masa nisa,ta bari next week sati daya saura
bikinsu zashi abujan shima kaiwa wasu abokansa katin daurin aure sai
su tafi tare tayi kwana biyu gidan anty dijen ya dawo da ita,tilas ya
haqura da yaji antin ce.
Tana tsaye gaban motar wadda saboda azabar kyau tana ganin
kanta a jikin motar,yaya abubakar da direban na sanya mata akwatinta
a bayan motar,bayan sun gama shigarwa ne sukayi sallama direban ya
bude mata bayan motar ta shiga a hankali ta rufe murfin motar tana
kallon su halima ta gilashin motar mai duhu wanda ya nuna su basa
ganinta har suka fice daga layin,wani sanyin ac da qamshi ya ziyarceta
lokaci guda,ta dan lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya,sanyin har
yaso ya dan mata yawa amma hijabin dake jikinta ya taqaita haihawar
sanyin
“idan ba damuwa zan dan tsaya a kwari bakin wani shago zan karbawa
hajiya saqon wasu kaya”
“Babu komai” sumayyan ta fada a hankali,ni da za’a yiwa alfarma ma
sai an nemi shawara ta ta fada cikin zuciyarta.
Sai da suka iso bakin kwarin ma sannan ta lura saboda sam
hankalinta bai kan titin bugu da qari kuma lafiyayyar motace da bakajin
kwaram kwaram din titi,bayan ya kashe motar har ya juya zai fita sai ya
juyo
“Hajiya ko zaki taimaka min muje ki zaba musu kala sabida gaskiya ni
bansan kalar mata ba,gashi hajiya ta jadda da min na zaba musu mai
kyau ta riga da ta biya kudaden”. Dan jim tayi tana nazari,ita da bata
sansu ba ta yaya zata san kalolin da suka dace da su?,amma duk da
hakan bata musa ba ta amsa masa da to ta fito tabi bayansa.
Wani lafiyayyen shago ne da kana kallonsa kasan na qananun kaya
suke saidawa ba,kai tsaye mansir dire ba ya nufi inda manajan gun ke
zaune wanda tun daga nesa da ya hangoshi ya fara washe baki,hannu
ya miqa masa suka gaisa yana tambayarsa su hajiyan yace kowa lafiya
qalau sannan ya masa jagora zuwa inda lesukan suke.
Kallo daya zaka musu kasan ba kowa ke iya siyansu ba,inda suke a
ajiye ma na daban ne,a nan manajan ya juya ya barsu don su zabi
wadanda sukayi musu,ta kai mintuna wajen biyar kafin ta juya ta dubi
mansir
” guda nawa za’a zaba?”ta tambayeshi
“Guda shida ne” ya bata amsa,cikin hikima da dabara ta dinga zaben
kaloli masu dauke da pattern mai kyau har ta kammala,washe baki
mansir yayi yana yaba kalolin data zaba din duk da bata ce komai
ba,suna shirin barin wajen idanunta ya qyallaro mata farashinsu,tayi
mamakin yawan kudin amma daga bisani mamakin nata ya ragu duba
da irin kyansu.
Cikin mintinan da basu gaza arba’in ba suka saitu sosai kan
hanya,tafiya ce mai dadi saboda yadda na cikin motar baijin rana ko
gajiyar zama balle ya jigata,suna tamburawa wayar direban ta dauki
tsuwwa,a hankali ya gangara gefen titi saboda ganin mai kiran nasa
sannan ya daga,cikin tsantsar ladabi ya fara gaida mai kiran nasa ,waya
sukayi na ‘yan mintuna yana mai amsawa sa to to yallabai cikin ladabi
sannan ya kashe kana waiwayo baya inda sumayya ke zaune
“Hajiya yallabai ya katse mana hanzarinmu ya sake maida mu baya,sai
mun koma zoo road mun karbo dinkunan madam,kiyi haquri bansan
zamu karbo su ba sai yanzu yake sanar mini” agogon wayarta ta duba,a
qalla sun kashe kusan awa biyu da rabi kenan daga fitowarsu daga gida
amma basu dau hanya ba sai yanzu.yanzun kuma gashu zasu sake
komawa cikin gari,duk da ta danji babu dadi amma ba yadda ta iya
tunda ‘yar alfarma ce,
“Kiyi haquri fa” direban ya sake fada yana juya kan motar”
“A’ah babu komai ai”. sai kusan qarfe daya da rabi sannan suka dauki
hanya sosai.
Gab da zasu shiga garin zaria wayarta ta dauki burari,sai da gabanta
ya fadi hakanan da taga sunan abdur rahman,kasa dagawa tayi har sai
da ya kirata kusan sau biyu ana ukun ta daga
‘Sumayya har abun yayi zafi haka?,ba wani abu bane kiranki nayi na
miki sallama,naje gida ban sameki ba ance kin tafi abuja wajen anty
dije,koba komai ai akwai kyakkyawar alaqa tsakaninmu ko sanarmin
kyayi,kin yaye abdallah ma duka ban sani ba sumayya haka rayuwa
take?,cewa da nayi ina sonki ban sameki ba bashi zai bata zumuncinmu
ba” muryarta a matuqar sanyaye tace
“Kayi haquri don Allah,duka banyi hakan bane da wata manufa,kawai
bansan da fuskar da zan kalleka bane”
“Da fuskar da kike kallona sumayya,ni na yarda da QADDARA na yarda
cewa hakan na cikin KUNDIN QADDARARMU ba wai don baki qauna ta
ba duk da bansan zahirin zuciyarki ba”
“Haka ne abdur rahman,bana qinka wallahi har ga Allah, kawai
QADDARA ta riga fata ne, bansan dalilin da yasanya zan auri lukman
ba,amma nasan cewa QADDARATA ce ta rubuta hakan kuma sai ya faru”
“Na fahimceki sumayya,Allah yayi mana zabi mafi alkhairi a dukka
rayuwarmu shine fatanmu,na kiraki na sanar miki in sha Allah jibi zan
koma inda na fito,tunda ban samu cikar buri ba,nasan kafin na sake
waiwayowa najeria kin jima a dakinki,ina miki fatan kyakkyawar
rayuwa,na bar miki saqo a hannun halima”
“Na gode qwarai da gaske, haqiqa ka jima kana bada gudun mawa a
rayuwata tun ba yau ba abdur rahman,ina maka fatan kyakkyawar
rayuwa fiye da tawa fiye da wadda ka roqamin,ina roqa maka alkhairin
ubangiji a duk wani motsi na rayuwarka,Alla h ya haskaka rayuwarka
karatunka da duk wasu harkokinka, na gode na gode”
“Nima na gode sumayya,saduwar alkhairi” ya fada yana katse
layin,sauke wayar tayi daga kunnenta tana bin wayar da kallo,sai kuka
ya kufce mata tayi azamar rufe bakinta saboda tuna a inda take,kanta
ta kifa saman cinyarta tana tunanin mai ya hanata zabar abdur
rahman?mutumin da babu abinda ya rasa na nagata da kyawawan
halaye saboda wasu dalilai dake gefe guda?.
QADDARA CE babu shakka qaddara ce tana kuma fata wannan karo tazo
mata da kyakkyawan sakamako,kifan kan da tayi bata sake dagowa ba
bacci ya kwasheta bata kuma farka ba sai da suka tsaya bakin qofar
gidan anty dije cikin kyakkyawar unguwar tasu.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]