[Advertisements⬇️]

QADDARAR SUMAYYA CHAPTER 32 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

QADDARAR SUMAYYA


CHAPTER 32

Kafin su kai ga fita daga airphort din ruwan sama ya sauka,hakan ya hadu da duhun magariba ya kawo qarancin jama’a bisa titi,idanuwan sumayya qur bisa kwalta yadda ruwan ke sauka yana wanketa,a duk sanda ruwam sama zai sauka sai ya mata tunin mukhtar kamar ko yaushe. +

Rashin daukewar ruwan har suka isa gida shi ya sabbaba driban ya shige da su baki daya cikin gidan baaban ba tare da sumayya ta samu damar sauka ba kamar yadda taso,saboda Abdallah wanda ya jima da yin barci kan cinyar amira,ruwan na iya tabashi,da ita daya ce da da sauqi.

   Lema kubra ta shiga ta dauko musu sannan suka fito,suka taka har cikin gidan.

     Lallai kam wannan biki ba qarami bane,baki daya harabar gidan ko ina an kafa tempol,duk da gidan bai wani cika rana ba,duk da ruwan da ake tsulawa hakan bai hanaka ganin mutane na kai kawo daga wannan sashi zuwa wancan sashi ba,a haka suka qarasa bangaren ummee,falonta cike yake da baqi,yan uwa qawaye da abokan arziqi,ga ‘yan rano nan wanda ko ba’a gaya ma ba kana kallonsu kasan jinin ummee ne,jinin sarauta,ga ‘yammata nan ko ina zazzaune kowa na nashi harkan,shigar amiran ya sanya hanaklin sh dawowa kanta,masu tsokana nayi masu mata barka da dawowa nayi,da qyar ta yakice suka hau falon sama na ummee wanda tana can.

       Karon farko da sumayyan ta taba shigarshi,falo ne dan gaske,wanda ya mallaki duk wasu kayan alfarma,baki daya kwalliyar falon ta da duk abinda aka zuba mishi na sarauta ne,kama daga royal chairs zuwa fentin falon,yayi matuqar burge sumayyan ba kadan ba,ummen ma zaune kan daya cikin kujerun falon tana irga sabbabin kudi wanda suke daure a rafarsu,ita da wasu mata ne wadanda kusan cousin dinta ne da suka taso tare tun zamanin ‘yammatanci,qarasawa amira tayi ta kwantar da abdallah kan daya cikin kujerun,ummee ta dubeshi tana musu sannu da qarasowa ita da sauran ‘yan dakin,a ladabce sumayya ta qarasa gabanta ta duqa tana gaidata,ta amsa fuska sake tana cewa
“Amira ta hanaki sakat ko sai data daukoki” murmushi tayi kawai amiran tace
“Ummee ba’a shiga tsakaninmu”
“Au ai dama itaku amira” ta fada tana kiran daya daga cikin ma’aikatanta ta wayar hannu tana tambayarta an gama gyara dakin da tace,sai data gama wayar ta dubi amira
“Kije an gama gyara muku dakin,saiki sanya a kawo muku abinci,ki duba abinda kuke da buqata ki kira mama uwani ki sanar mata,su ummu salma ma ina zaton suna dakin tun dazun suke qorafin rashin dawowarki gashi gobe kamu”
“To ummee na” amiran ta fada tana miqewa
“Muje,ummee idan abdallah ya tashi ki bada shi a kawo mana shi” ta fada tana nuna abdallahn dake kwance yana baccinsa lakadan,kai ummim ta daga don bata son yin magana ta sake bata a lissafin.

        Dakina babba sosai wanda ya babu komai cikinsa sai carfet da aka malale shi da shi,katifune saman carfet din ko ina aka kwakwkwantar,yayin da aka lullube kowacce katifa da zanin gado abun rufa da filo qwaya daya alamar kowacce ta kwanciyar mutum guda ce,sai toilet qwaya biyu cikin dakim,da qaton madubi da ya kusa cinye rabin bango,mutum biyar suka taras a dakin,wasunsu na hira wasu na cin abinci,shewa suka sanya da ganin shigowar amaryar,kowacce da abinda zata fadi,nan suka zube aka gaisa suna ci gaba da surutaj,itakam sumayya na gefe tana kallonsu,rayuwar wayewa kawai ake a wannan familyn,kowacce ka gani tana ji da wayewa kyau da arziqin gidansu,akwai alama dake nuna suna da zumunci da kara,sannan akwai sabo da fahimtar juna tsakaninsh,wanda hakan baya rasa nasaba da yadda baabaa prof ya hadasu baki daya ya rungume kowa,duk sallah babba da qarama duk ‘ya’yan ‘yan uwan na gidansa,baya banbantawa da nashi dangin dana matansa,shi ya sanya kowa yasan kowa,’yammata ne hadaddu wannan na wace wancan ta fada a ranta tana murmushi. 

       Agogon fata na kamfanin gucci purple dake daure a hannunta ta duba ganin ruwan ya tsagaita sai yayyafi wanda take iya gani ta window din dakin albarkacin hasken lanatarkin da yake tarwai kowane lungu da saqo na gidan
“Zan wuce fa amira” inji sumayya ganin yadda amiran ta bararraje tana kwasar hira,duka sai hankalin su ya dawo kanta har taji nauyin yadda kowa ya dora mata idonshi
“Wasa fa kike amirah,kin manta alqawarinmu,ai ga gun kwanaki nan har na bar gidan nan” sai ta karyar da wuya tana murmushi
“Amma dai ai kya bari naje naga anty ko?”
“Eh,wannan kuma,kuma ai ban ma gama ganinki ba,muje part din anty maamaa akwai abinda zaki gani idan kin dawo na nuna miki sauran” ta fada tana miqewa,itama tashin tayi suka fito,har sun kai qofa tace
“One minute don Allah sis,bari na dauko kayan waccan jarababbar na kai mata,Allah yasa ya musty bai nan” kafin tace komai har ta juya da sauri ta koma,tsayawa tayi tana jiranta gabanta na faduwa,tana addu’an kada Allah ya sa tace sai ta rakatan,don gaskiya ba abinda zai hanata ce mata ba zata ba.

        Tana shiga ummu salma tace da ita
“Amira wai ina kika samu wannan babe din haka mai shegen class,wallahi tamun,ta burgeni da ganinta akwai nutsuwa”
“Ga kyau,muryarta ce ni kuma ta burgeni” inji hafsat,dariya suka bata,dukkansu ‘ya’yan yar ummee ne,tasu ta bala’in zuwa daya da amira saboda halayyarsu kusan daya ce,ba ruwansu suna da matuqar kirki
“Nan fa gidan anty dije wadda ta muku fried rice da sunan hanan,a nan take”
“Masha Allah wallahi tayi”
“Ai baku ma san tayi ba sai mu da muka je gidansu….” Eesha da hassada ta cikata tace
“Me tayi,mr suke da shi a gidan nasu” amira wadda har ta sanya qafarta zata fita ta fasa ta dawo jin abinda eesham tace,dama tana lura da take takenta akan sumayya,wadda bata ga ita sumayyan abinda ta yi mata ko ta tsareta mata ba
“Basu da komai,amma suna da rufin asiri,suna da wadatar zuci,basu taba kuma roqon wani ba,baya ga haka suna da karamci kyautatawa da girmama baqo,wadan nan abubuwa sun basu komai na rayuwa koda basu da shi din” inji amira ranta a bace sannan ta juya ta fita ranta a bace,humaida ce wadda itama ke jin haushin abinda eeshan keyi ta dora
“Arziqi ba kudi bane eesha,wadatar zuci sanin darajar kai,mutunci yakana da karamci sune arziqin,kana da cin yau kana fa na gobe jibi wata ko shekara ma,kana sanya suturarka ta mutunci,baka taba roqa a baka ba,baka tashi ka rasa abin kaiwa baka me kake nema?”
“Kinga malama,ni ba wani nace mata ba da zaku isheni da dogon wa’azi,ha’an…” Ta qarashe tana jan tsaki,caaa suka mata sun fita yawa ala tilas tayi shiru. 2

       A inda ta barta a nan ta taras da ita,suka ci gaba da takawa ba tare data nuna wa sumayyan akwai wani abu ba,bangaren anty maamaa suka soma shiga,itama bangaren nata masha Allah da mutane,suka gaisa sannan taja hannunta suka tsallake zuwa kitchen dinta,suna shiga tana yunqurin fitowa hannunta dauke da tray wanda aka jera tangaran mai garai garai guda daya wanda ke dauke da hadin salad mai kyau,sai wata qaramar butar shayi irin ta larabawa da cups dinta wanda ke dauke da baqin shayi wanda yasha kayan qamshi iri iri,su’ad ce,fuskar nan a hade tana faman kumburi,ko kunyar idon mutane bata ji,ta zama baturiyar qarfi da yaji,sanye take da dogon wando wanda ya kama jikinta da t.shirt mai gajeran hannu,kanta babu dankwali sai uban qarin gashi wanda aka dasa shi kamar nata na ainihi,ta sanya ribbom ta kameshi,takalmin qafarta kuwa irin mai igiyar nan je,wanda tsininsa ba kawai abun kallo ne,amma akace sabo da yi gawa da gatsine,da yake ta saba tafiya da abunta sam bai dameta ba,hannyenta kuwa farce ne wanda tasha nail polish,gefe suka janye bata ko kallesu ba ta wuce abinta,da kallo amira ta bita tana tabe baki kafin ta maida kallonta ga anty maamaa
“Kumburin banza kawai,shi wanda kike ma kumburin ma baisan kina yi ba,ba kuma ki isa kiyi masa a gabanshi ba,abincin ba bake zaki girki ba ki karba ki kai masa yaci kina baqinciki kamar da kudinki aka sarrafa,wallahi ni yanzu baiken ya musty ma nake gani,kana aure amma kamar ba magidanci ba,babu wani ci gaba da ka samu ko sauyi dangane da tsohuwar rayuwarka” daquwa anty maaman ta jefeta da ita tana fadin
“Sau nawa zan miki magana kan dauke ido daga rayuwarsu?,ke ke zaune da ita?,ko kinga ta kulaki sansa zata fita” shigin shagwaba amiran ke kumbure kumbure tana fadin
“Duk ku kuke sake bata su wallahi,ni da ganin wannan takacin gwara kayi aurenka ma kayi gaba a barku da su” dariya ma ta baiwa anty maaman sai ta dauke kanta tana duban sumayyan
“Qaraso amiran umman khalipha mu gaisa ki qyale wannan tuburarriyar qawar taki,rana iwar haka dai naga wanda zata yi mawa” dariya sumayyan ta saka itama tana qarasowa inda anty maman take,a ladabce ta gaidata tana tambayar yadda ta baro mutanan gidan,sai da suka gama gaisawa sannan tace
“Anty mama,bedroom dinki na bude,zamuga wadan nam kayan” kai ta kada mata suka juya suka fice.

        Har bedroom din ta dangana da ita,aljannar duniya sumayya ta kira dakin,cupboard din antyn ta bude ta jawo wata akwati ta ajjiye gaban sumayyan,ta sake janyo wata ta ajjiye sannan ta fara hudewa tana fadin
“Ga kayan da zaki saka na biki baki daya,komai da komai,sarqa kawai zaki buqata bansan choice dinki ba” baki kawai sumayyan ta sake tana kallonta,ta soma ware mata wanda zata sanya gobe kamu,wani dandatsetsen lace ne brown mai yarfin milk wanda aka yiwa dinkin fitted gown,rigar ta dinku iyaka,sai takalmi milk na companyn vinci wanda ke da tsini dunduniya,sake dago wata doguwar riga tayi wadda ta tafi da imaninta,ire iren rigunan da baabaa ya basu da salla ita da laila mai dauke da tambarin companyn MM,itama da takalminta ruwan kwalliyar duwatsun dake jikin rigar tace wannan ta jibi ce ranar arabian night,sake janyo wani shegen yadi tayi wanda bata tantance wanne ba,baqi ne baki dayansa an masa ado da milk din zare tsalli tsalli da milk din qulalai a jiki,shima fitted gown ce,har tafi ta farko fitinuwa,sai wani shegen hill shoes mai igiyoyi ruwan adon jikin yadin da jaka purse mahadin kayan ga
“ankon dinner dinki” amira ta fada tana murmushi,rasa bakin magana kawai tayi tana duban amira,dariya ta sanya sanda ta motsa zata yi magana
“Wallahi idan kika ce wani abu sai mun bata,baabaa ne duka ya bada yace na zabi na dinkawa babbar qawata” kai kawai ta dinga kadawa kafin ta furta kalaman godiya,kunnuwanta ta tasihe da nufin bata son ji. +

       Daya akwatin kuwa baki daya kayan amarya ne da zata yi fitar biki,fadin irin kyawunsu ma bata baki ne,sai data daga mata su daya bayan daya sannan ta rufe ta maida ma’ajiyarsu tana cewa
“A nan zamu dinga shiryawa,don haka anan zamu bar kayanmu,sai muje kiga lefe dama baki gani ba” dariya tayi
“So kike dai dare yamin banje naga anty ba,ai basai na gani ba amira”.
” shikenan,muje ki rakani na miqawa waccan kayanta,sai na rakaki qofa kije ki dawi din”fuska ta narke,ta langabe kai duk don amiran ta haqura da wannan rakiya
“Habbaaa amira,muje dai ki wuce ki kai mata ni kuma na wuce gida”
“Ke kika ce sai na amso mata dinkin ina zaman zamana,saboda haka dole ki rakani” tayi maganar tana gyara nadin mayafinta,miqewa tayi jikinta babu qwari tabi bayan amiran suka fice.

        Daf da zasu shiga bangaren wanda ta baya suka biyo da yake qofofi biyu garesu,akwai qofar gaba wanda zaka shiga ta falo,akwai qofar baya wanda zaka shiga ta kutchen wannan qofar suka biyo,daga hannun hagu na bakin qofar,a qawace yake da wasu irin nau’in furanni da shukoki masu kaloli daban daban da kuma kyau,baki dayansu kansu daya babu wadda tafi wani tsaho,an qawata gun tamkar wani dan gurin hutawa,kaf gidan nan dinne kadai ke da irin wadan nan shukokin,wanda qilan mamallakin bangaren ne ya siyi abunshi yasa aka tsara masa su a haka,yara ne kusan su hudu,maza biyu mata biyu,a qiyasce zasuyi sa’annin juna baki dayansu,kowanne qananun kaya ne a jikinsa,sun kunna fanfunan suna ta faman wasan ruwa,amira ita ta fara hangosu,sai ta dakata tana daga murya
“Hibba!!,yayi muku kyau da wasan ruwa kunji ko” baki daya suka waiwayo suna dubanta,kyawawan yara ne wanda kallo daya zaka yi musu ka tabbatar jinin gidan baabaa prof ne,wadda aka kira da hibba ita ta matso
“Anty amira,gasar yin alwala muke,su hibban duk basu iya ba,zo kiga na fisu iyawa”
“Matsa ki ban gu,yanzu ban da lokacin shirmenku kinji,tawa ta isheni” sai ta karyar da kai fuskarta kamar mai shirin yin kuka tace
“Don Allah anty amira kizo ki gani” idanunta ta zaro tana dubanta
“Ina wasa dake ne,bakiga ina cikin hidima ba,matsa a wajen nace” sumayya na tsaye tana murmushi tana dubansu,yarinyar ta burgeta,zuciyar son yaranta ta motsa mata,dauke idonta yarinyar tayi daga duban amira ta maida kan sumayya
“Tunda ba zaki ba ai ga wata antyn ko?anty zaki je ki gani?”
“Me zai hana” sumayya ta fada tana murmushi,tsalle ta fara wanda hakan ya sanya sauran yaran qarasowa din jin me ya faru
“Ba inda zata,Allah hibba kin baci da yawa,itama tana da abunyi”
“A’ah,nifa sai naje” inji sumayya wadda dama hanyar kubuta take nema
“Kije ki fito kya sameni a nan” ta fada tana yin gaba din tuni yarinyar ta riqe mata hannu
“Anty muje waccan fanfon,wannan na uncle man ne,zai zanemu ya ganmu a gurin,amma idan mukayi kuka sai ya bamu chaculet yace mu daina” murmushi tayi kawai tace
“Allah”
“Allah anty,kuma duk yafi sona” hibba ta fada suna qarasowa wani waje wanda shima akwai fanfo saidai baikai wancan kyau ba.
         Jin muryar yara ya sanyashi daga idanunshi daga kan laptop din dake gabanshi yana duba wasu sababbin design na dogayen riguna da kamfaninsa ke son fitarwa a sabuwar shekara,gefanshi butar shayi ce da cup qwaya daya,a rayuwarshi yana son ababen nan,yanayi na damuna irin wannan bayan gama saukar ruwan sama,da guri wanda ke da wadatar korayen tsirrai,iskar wajen mai dan sanyi sanyi kadan hade da qamshin qasa da qamshin furanni na masa dadi qwarai,ganin yaran tare da wata ya sanyashi maida kanshi yaci gaba da abinda yake.
Daya yaron ne ya tabe fuska yana cewa
“Qarya ne anty,yafi sona,ko za’a tambaya ma” yatsanta ta dora kan lebenta tana zaro masu idanu alamun yayi abunda ba mai kyau ba
“Bakasan ba’a cewa babba qarya yake ba,lala ba kyau,kace Allah na tuba” kan kunnensa kalaman suka sauka sai ya daga kai ya sake duban inda suke tsaye,har yanzu bai gane wace ba,amma yana iya gane yaran saboda baki daya yasan muryoyinsu,hannunshi ya sanya ya tsiyayi shayin ya kai bakinsa yana ci gaba da sauraronsu,a rayuwa Allah ya zuba masa qaunar yara,zama cikinsu yana debe kewanshi a duk sanda ya samu kansa cikin kewa,hakan ya sanya wani lokaci yakan bata lokaci cikin gidan marayunshi,akwai yaran da suka shiga ransa da dama a gidan,baisan so yaushe ne zai daina rayuwar kadaici ba. +

     Murmushi tayi ganin yaron yayi saurin rufe bakinsa yana cewa
“Allah na tuba”
“To yanzu muje mu gwada inga alwalar kowa din,duk wanda yafi iyawa shi ya m…..” Sai ta kasa qarasa sunan
“Wanda duk yafi iyawa shi aka fi so” ta sauya salon maganar tata,tsalle suke har suka isa gaban fanfon,tana tsaye tana kallon kowa daya bayan hannayenta harde a qirjinta,kamar yadda yake zaune saman kujera yan kurbar tea mai zafi yana kallonsu,sai da suka kammala tsaf,tabbas hibba ta fisu iyawa,amma ita dinma akwai gyare gyare,a hankali ta yaye yalwataccen mayafin data suturce jikinta da shu,wanda hakan ya bayyana shape dinta sosai kasancewar riga da skert ne a jikinta,tun bayan zuwanta abuja kayan suka dan kamata kasancewar ta murje ta cicciko,idanuwanshi ya lumshe saboda gujewa kallin haramun dinshi,sai ya kasa sake bude idanuwan mashi ya barsu a lumshe yana sauraron ta tana fadin
“Sai kuyu haka,yauwa haka,haka” bai bude ba har sai da yaji tana fadin
“Idan kayi haka,kayi alwala mai kyau” a hankali ya bude idanuwan nashi,wannan karon fuskarta tarwai take ta haske qwan lantarkin da ta tsaya saitinsa,ya dan qura mata idanuwa yana son tuna inda yasan fuskar
“Mai kuka a uk mall” qwaqwalwarsa ta birkito file dinta,qaramin murmushi ne ya subuce masa,wanda idan baka kula da kyau ba na zaka gane hakan ba,saboda cije leban qasan bakinsa da yayi
“Tana acting kamar wata babba” ya raya hakan a ransa.

       Riqeta yaran suka sake yi,nurain daya daga cikin yaran yace
“Anty ki mana tatsuniya,baabaa lami mai aikin momi tana mana” murmushi ta saki,ta lura suma lallai yaran masu son mutane da sabo ne,saidai suna son riqeta gashi tana son tafiya gida ne
“Ban iya tatsuniya ba saidai na baki tarihi”
“Laaaah,irin wanda uncle man ya taba yi mana rannana?” Zaitun daya yarinyar ta ambata da salon tambaya,duk da bata sani ba amma sai ta daga kai
“Ita,amma yanzun inaso naje gida na gaida anty na,sai wani lokacin na muku ko?”
“Yaushe?” Inji hibban,kai ta girgiza qaramar dariya na son subuce mata,yaaraan akwai wayo,tana som tana yaro mai wayo da kaifin qwaqwalwa irin haka,ta tabbatar basirar da wayon bai tashi a banza,zai zama abu ne mai amfani a nan gaba
“Wataran in sha Allah”.

        A hankali ya janye idanuwanshi daga kansu jin qarar wayarshi,ya cirota daga aljihun black trouser din dake jikinsa yana duba mau kiran,su’ad ce,dan qaramin tsaki yaja,ba matsala yake so ta qara maishi ba,ya riga da ya yanke magana,ya gaji da auren asha ruwan tsuntsaye da sukeyi,ita tana kano shi yana daura,kusan tun jiya bayan isowarshi garin da yaje gidan hamza abun ke dawainiya da shi,kasancewar wanda amiran zata aura cousin suke da hamza,wata rayuwa ya gani ba irin tasu rayuwar ba,ba irin rayuwar gidanshi ba,yana iya tuna sanda hamza ya dagewa auren yarinyar suna ganin baikensa,ashe akwai abinda ya gano?.Rejecting call din nayi sannan ya maida kansa kan laptop dinshi da niyyar ci gaba da aikin da yakeyi,wani tsakin ya kuma ja ganin lokacin da ya bata yana kallon sha’anin da bai shafe shi ba,yayi asaran time dinsa a banza,saidai yadda take kiranshi a jejjere ya hanashi aiwatar da komai,wani wawan tsakin ya sake ja,a rayuwarshi ya tsani abinda zai takurashi,sai ya ciro wayar a fusace ya daga ya kara a kunnenshi,cikin shagwaba da karyar da murya ta soma fadin
“haba my man,please….please kada muyi haka da kai,ka duba fa ka gani duka duka shekara daya ya rage min na kasance tare da kai fa?”
“Keep quite su’adah please….na riga da na gama magana,idan zaki iya zama gu daya fine,idan ma ba zaki iya zama ba duk daya,amma kada ki zargeni nan gaba” ta tabbatar da cewa shi din kaifi daya ne,baha magana ya sauyata,mutum biyu ne tal a duniya ke sauya masa ra’ayi koda baiyi daidai da mizanin mashi ra’ayin ba,baabaa prof sai ummee,sanin baya qaunar kuka ko misqala zarratin,koda na qaramin yaro ne ya sanyata saka kuka har da sheshsheqa,sai ya lumshe idanuwansa yana sauraren sautin kukan nata,a hankali ya zame wayar daga kunnenshi sannan ya kasheta baki daya ya cillata aljihu,shutting down din system din yayi sannan ya miqe tsaye yana jira ta qarasa mutuwa,ya laluba aljihunsa yaji muqullansa na jiki,ya dauke system din sannan ya dinga takawa a hankali ya nufi inda yayi niyya,baki daya baya marmarin komawa bangaren bare taci gaba da jagula masa lissafi,saboda haka ya isa ga qarama cikin motocinsa ya bude ya ajjiye kayanshi ciki ya tada ta ya fice ba tare da ya nemi kowa ba.Mamaki ya kama anty dije ganin sumayya,dariya ta dinga yi tana cewa
“Maganinki,da kika qi dawowa ga mai gaba daya nan taje ta taho mana da ke ai” itama sumayya dariya take
“Hmmm,amira,amira rigima amira tabara,sai ganinta kawai nayi wallahi”
“Ina sane ban gaya miki ba ai” guri sumayyan ta samu ta zauna tana ci gaba da dariya. +

        Nan ta shantake suna ta hira da anty dijen,bata tashi farga ba sai taga har sha daya tayi,hakan ya sanya ta bude dakinta tayi kwanciyarta,anty dije je cewa
“Abdallah fa?”
“Barshi anty,babu lallai yayi rigima”

   ******     ******    *******

        Qarfe goma na safe tayi wanka bayan ta gama hada breakfast ta barwa anty dije sauran aikin gidan,doguwar riga ta saka ta wani irin yadi mai talewa,hijabi ta zura wanda ya saukar mata har saman tafin qafarta,niqabinta ta daura sannan ta fita ta tadda anty dije na goge kayan kallo a falo
“Anty zan wuce,nasan amira tana can ta cika fam,fashewa kawai take jira tayi” ta fada tana qyalqyalewa da dariya,dariyar itama tayi
“Ato,yau mai rabaku sai Allah” tana dariya ta saki niqab din nata ta fice a gidan.

       Ya kusan a qalla mintuna talatin zaune cikin corridor din dake saman benanshi,bata san sanda ya shigo ba,tun daren jiyan taje zaman jiran shigowarshi taji shiru,ta kira wayar babu adadi saidai duka amsa daya ce wayar a akashe take,tun tana kumbura har zuciyarta ta fara saukowa,ta sani cewa fushinsa bashi da dadi,tana shan wuya a duk lokacin da yayi fushi,hakan ya soma daga hankalinta,kusan ranar bata yi cikakken bacci ba,saidai duk da haka bata san shigowarshi cikin gidan ba.

        Cikin qanqanin lokaci zuciyarsa tayi fes,fuskarsa ta soma washewa,yaran dake shawagi kan idanunshi a harabar gidan,yaro daya tak yake hangowa cikinsu wanda bai sanshi ba baquwar fuska ne,saidai a yadda wasan da yaran ke gudana duka ya fisu kuzari da wayo,motsin yaron ya dinga bi da kallo yana sakin murmushin gefan baki.

          Sai data tsaya suka gaisa da baaba mai gadi kamar yadda suka saba sannan ta sanya kanta cikin gidan,tunda ta shiga gabanta ke wani irin faduwa,kusan yara sunfi yawa a harabar gidan suna wasanninsu,jifa jifa mutane na kai kawo,juyiwar da abdallah zaiyi ya hangota,duk da niqabin dake fuskarta da hijabinta hakan bai sanya ya kasa ganeta ba,da gudu ya tafi yana kiran
“Ammiiiii….amminaaaa” cak yaran suka tsaya suna kallonshi ganin suna tsaka da wasa ya bar gun.

       Da idanuwa yabi yaron ganin yayi wani guri da gudu,hannayenta ta bude baki daya duk da har yanzu niqabin na kan fuskarta amma murmushi ne kan fuskarta,durqusawa tayi ta daga shi tana nishi saboda nauyin da abdallahn ya dan yi mata sannan ta dage niqaf din,fararen jerarrun haqoranta a waje
“Wai abdallah,na kusa fara kasa dagaka,me kaci yau ka qara nauyi?” Dariya ya saki irin ta quruciya sannan yace
“Ammi,wata ummi ce,na kwana a dakinta,ta yimin wanka ta bani chips da qwai ni kadai na cinye,harda tea da suger sosai” dariya ta kamata,har sai data dora tafin hannunta kan bakinta,kafin tace wani abu hibba tayo gaba da gudu itama sauran yaran suka biyota,bata ankara ba taji an ruqunqumeta ana fadin
“Anty,kin dawo zaki mana labarin?” Waiwayowa tayi tana dariya,ta sauke abdallah tana fadin
“Kin manta yau ana bikin anty ameeraa?,sai idan an gama zan muku,muje ku rakani inda anty amiran take” gaba tayi yaran na binta a baya wannan ya riqe hannunta wannan ya riqe hijabinta a haka suka tafi.

        Baisan yana binsu da kallo ba sai da suka bacewa ganinsa,ya lumshe idanunsa sannan ya bude a hankali,abun ya burgeshi ya bashi sha’awa,yana son yara har cikin zuciyarsa,bayansa ya jinginar jikin kujerar yana fidda zazzafan huci daga bakinsa
“My man” yaji an ambata a tausashe,yasan ko wace hakan ya sanya yaqi waiwayawa,sannu a hankali ta tako gabanshi,sanye take cikin riga da wando,ire iren shigar da tasan yana muradi suna burgeshi qwarai idan tayi,jikinta na fidda wani irin qamshi mai dadi,duka hannayenta ta zuba a kafadarsa,cikin shagwaba salon da tasan yafiso tace My man,ka sanyani a damuwa jiya,kasan cewa ina buqatar ka,baki daya kwanakin da zamu kasance tare ba masu yawa bane,amma man ka qauracemin” ko kadan bai da buqatar maganarta,hakan ya sanya ya saka hannunshi ya sauke hannayenta dake kafadarsa sannan ya ture kujerar ya miqe tsaye ta juya yana shirin barin gun,ranta ne ya baci,hankalinta ya tashi,ta tabbatar cewa ya hau bigerin da shawo kansa zaiyi wuya,bata kuma isa ta sha gabanshi don hakan zai iya jawo mata wata matsalar,tilas ta janye jiki tana kallonshi ya wuceta,hannayenta ta saki zuciyarta na zafi,idanuwanta na neman tara qwalla,babu shakka idan banda mustapha mustapha ne da babu namijin da zata zauna a duniya yayi mata haka,saidai mustaphan na dabanne kamar yadda yake daban a zuciyarta,mafita daya gareta ta kaishu gaba inda za’a sashi tilas yayi mata abinda take so din,bama inda ta saba kaishi ba wannan karon na can zata kaishi ba,sai ta juya da dan sassarfa ta ratsa ta dakinsa zuwa falonsa ta sauko qasa ta nemi hanyar ficewa ba tare data damu da sauya kaya ko daukar babban mayani ta suturta jikinta ba ko don girman wanda zata gurinsa. 

       A dakinsu na jiya sumayyan ta tadda su,tana qunshe dariya ta qarasa,dariya amiran ta saka tana harararta
“Wallahi kin maida ni wata iri amira,godiya nake”
“Afuwa namecy,afwa”ta qarasa ciki suna gaisawa da ‘yammatan dake ciki,gira ta daga
” to ya zanyi da ke,ni na kai kaina inda ba’a damu da ni ba,muje kimin rakiya wajen baabaa”
“Ya kamata,don nima ina son inje in gaidashi” eesha dake shan tea ta ajjuye cup din tana yiwa sumayyan duban ita kuma a wa?,kamar zata furta sai kuma ta fasa,ta miqe itama tana yafa dan yalolon mayafi kan kayan baccinta tana cewa
“Muje nima nayi rakiya”
“Owk” amira ta fada ta dubi su hibba
“Oya,ku wuce ku tafi wasanku” juyawa sukayi hibba ta tsaya ta karbi abdallah suka wuce.

        Sai da suka shiga wajen anty maamaa da ummee ta gaidasu sannan ta suka wuce zuwa sashen tsohon.

           Zaune yake gefan umminsa daga shi sai itayana kurbar coffee,idan da kowa a gun ta tabbata bazai sha ba,wanda ta shiga kitchen da kanta ta hada masa,dubanshi take qasa qasa,ita daya take iya gane mustaphan,tayi tsammanin idan yayi aure shikenan komai ya qare,matarsa zata fahimceshi fiye da kowa,saidai kash,sabanin haka ne ya faru,matarsa itace wadda bata fahimceshi ba fiye da kowa,a yanzun kallo daya tayi masa ta fahimci yunwa yake ji,bazai iya gaya mata ba,zai iya ci gaba da zamansa haka har sai an bashi,idan ya gaji ya kuma yana iya fita can wani wajen cin abincin yaci abinshi,time to time yakan sanya matarsa tazo ta karba masa idan yunwar taci tura,hatta da amira tafi matarsa sanin ko shi waye,wani irin mutum ne shi mai wuyar sha’ani,ba kowa ke iya fahimtarsa ba,bai iya sharing damuwarsa ko shawararsa da kowa idan ka dauke ummeen da baabaansa,tayi zaton idan yayi aure wannan zai zama aikin matarsa,saidai ina ma yaga matar bare ta dauki wannan responsibility din,saidai komai tana ganin ya kusa zuwa qarshe tunda gaf su’adan take da kammala karatunta,tana zaton idan ta gama din zata nutsu ta tara hankalinta waje guda ta kula da mijinta kamar kowacce matar aure.

        Yana tsaka da amsa waya ta shigo falon kai tsaye tare da sallamarta,a hankali ya daga kanshi don ganin waye,kansa ya kawai gefe yana jin kunyar ganinta a haka a matsayin surukarshi,baki daya babu al’adar bahaushe ko digi cikin jini da jijiyarta,komai nata na mai jan kunne ne,ko qanqanin bata jin kunyar keta gidan a haka,duk da tarin baqi dake gidan,yana yiwa yaronshi sha’awar sauyin rayuwa,duk abinda ke faruwa cikin rayuwar yaron shi da yakeso fiye da kowa cikin yaransa idan ka dauke amira yana sane,saidai baison jefa kanahi cikin sha’anin da ba’a nemi agaji ko tallafinsa,dattijon suruki ne wanda yasan ciwon kanshi da mutucinsa,amma tabbas mustapha ma cikin wani wadi daya cancanci a tallafeshi,tun fari laifinshi ne da bai ganin aibun rayuwar mai jan kunne,gani yake rayuwa ce ta burgewa,baisan babu komai cikinta face tsantsar wahala da rashin nutsuwa. +

      Cikin sheshsheqar kuka ta zube a gabansa
“Baabaa don Allah kayi masa fada,ka masa magana,yana son takurani,yana son tauyen ‘yancina” sosai yake dubanta,a nutse yace
“Nutsu su’adah,zauna,zauna sosai,gayamin,me ya faru?,me ya hadaku” zama tayi gabansa tana goge hawayen nata da tissue,don ko dan mayafin da zata kama ta goge hawayen babu a jikinta
“Baabaa,mustapha ne,haka kawai muna zamanmu yadda muka saba,shekaran jiya yaje gidan hamza,ya gano wata zamantakewa ta daban yace dole muma irinta zamuyi,bayan zamantakewar tasu sam babu ‘yanci ko walwala a cikinta,sai dinbim takura kai da rayuwa cikin duhu da rashin wayewa,lallai wai saidai na dawo nan qasar na zauna daku na qarasa karatuna don bai amince da duk qawaye na da abokaina ba,sannan wai idan na kammala na bishi dubai mu zauna tare na dinga kula da shi,don Allah baaba wannan ba takura bace,ni ban taba ganin inda da quruciyarki kike rayuwa irin haka ba,a gun africans kawai nake gani suma rashin wayewa ce da duhun kai” idanu baban ya runtse kafin ya bude,duka ta hadu ta zagesu su da iyayensy,babu shakka ba qaramin tasiri rayuwar yaro take ba a duk inda aka haifeshi ko ya taso,sai Allah ya taimaka iyaye sunyi tsaiwar daka sannan za’a samu yaro ya tashi da dabi’a halayya da al’adunshi. 3

      Cup din ya dire dai dai sanda wayarshi tayi tsuwwa,ya duba yaga kiran daga baabaa ne,tun kafin ya daga ranshi ya raya masa mishkilar su’adah ce,daya daga din kuwa ce masa baabaan yayi
“Kana ina?,duk inda kake kazo ka sameni a falo,ina jiranka” daga maganar tasa kawai ya fahimci mawuyaci ne ba qararsa ta kai wajen baabaan ba,duk da cewa hakan ba baqon lamari bane wajensa,amma abun yayi masa ciwo fiye da kullum,ranshi bace ya maida wayar aljihunsa yana duban ummee
“Baabaa na kira” ya fadi a taqaice
“Ok,ka qoshi kenan coffee kawai ya isheka,bayanshi banga kaci komai ba?”
“I’m ok ummee” ya fadi yana takawa ya fice daga dakin.
          Cikin sanyi da qasaita yayi sallama cikin falon baaban,wani kallo yajefa mata wanda ya sanyata sadda kanta qasa,take jikinta yayi sanyi,nadamar kawo qarar ta baibayeta,kwarjininsa kadai ya ladabtar da ita,cikin girmamawa ya isa gaban baaban ya zauna gami da lanqwashe qafafunsa,ajjiye takaddun hannayensa yayi sannan ya maida hankalinsa gareshi
“Mustapha,me ya shiga tsakaninka da matarka” shiru yayi na wasu daqiqu kanshi na qasa,idanunshi bisa carfet din dake dakin,a hankali ya motsa bakinsa
“Baabaa,ina da buqatar mata ta ne kawai kusa dani,na buqaci ta ajjiye karatunta ta zauna tare da ni” yasan a rina,mustaphan ba mai boyon abu bane cikin zuciya,komai tsaurin gaskiya ko dacinta sai ya fadeta,tabbas mustaphan bashi da laifi cikin maganarlaifinshi daya tun fari a haka ya tarbiyyanci matarsa,amma kowanne magidanci zaiso kasancewa da iyalinshi,bawai kowannansu da inda ya sanya kanshi ba sannan ace wai a haka za’a rayu,tausayinshi ya kama shi,yana jin wannan karon ya kamata yayi wani hobbasa cikin rayuwar yaron nashi
“Baka kyauta ba mustapha” maganar data sanyashi daga ido cikin mamaki ya tsare babaa da kallo,yayi zaton shine na farko da zai goya masa baya?,ya zaci shima yasan ba haka rayuwar ma’aurata take ba 
Tun farko haka ka dora bigiren rayuwarku kai da ita,ka manta ice tun yana danye ake tanqwarashi,basai ya bushe ba sannan kace zaka tanqwarashi” kai su’adah ke kadawa cike da jin dadi tare da alamun samun nasara cikin zancan baban ba tare data fuskanci dungun dake cikin maganar ba
“Mustapha,komai ya kusa qarewa,ka qyale matarka ta kammala karatunta a inda ta fara,shekara guda ya rage mata ta kammala,idan yaso koma meyw zai biyi baya sai ka zauna ku yanke” shiru ne ya ratsa falon,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarshi,zuciyar su’adah ciki fal da fatan samun nasara. +

      Bayajin a duniya akwai wani umarni da baban zai bashi ya tsallakeshi,ya numfasa a hankali sannan ya furta
“Na barta baabaa”
“Yes dad,thank you” sa’adah ta fada cikin daga murya,murmushi ya subucewa baabaan,addu’a yaje da fatan saisaituwar halayen su’adah ko kyakkyawar rayuwa zata samu ga diyansa,miqewa tayi cikin farinciki ta fice,fes taje jin ranta,don ta mustapha tana tunanin tasan yadda zata shawo kansa,don ko kadan bata jin zata iya tabbata cikin nijeria tayi rayuwa a cikinta.

        Fitarta sukayi kacibus da su amira na niyyar shigowa,babu wanda ta kalla cikinsu tayi gaba abinta,yayin da eesha ta bita da harara kamar idanuwanta zai fado,babu wanda ta tsana a duniyarta sama da su’adah din,tana ganin baki daya ta kanainaye rayuwar mustapha,ta hanashi duban kowacce mace da qima,bayan ita din ba wata uwa take tsinanawa gareshi ba,abinda bata sani ba,abun a jininsa yake,tsaki ta ja wanda ya sanya amira waiwaya ta dubeta,tasan meke kai kawo a zuciyarta,saidai koma mene bata fatan Allah ya ida nufi,don qwaryar sama ke dukan ta qasa,banbancin ita da itan kadan ne. 4

       Bayan sallama da tayi ganinsa shine abu na biyu daya biyo baya bayan shigowarta falon,nutsuwarta yaji na nemam gushewa
“Bafa mukhtar bane,ba kuma zai taba zama mukhtar ba” wannan shine kalaman sa suka dawo mata cikin kwanyarta,sai ta lumshe ido taja dogon numfashi kafin ta ajiye nunfashi ta kuma daidaita nutsuwarta.

       Fuskarsa dauke da fara’a yake dubansu
“Mommies dina ne da kuma mai sunan uwar mumunai” ya furta cikin fara’a,su dinma fuskarsu washe take suka samu waje gefe da shi suka zauna,yayin da eesha tafi daura da mustapha,satar kallonshi take,baki daya man din ya sake tafiya da tunaninta,
“Allah ka mallakamin shi” ta fada cikin zuciyarta tana lumshe idanuwa tana ci gaba da satar kallonshi,wanda sam shi baisan ma tana yi ba,abinda ke gabansa kawai shi ya dameshi,gaisuwansun ma bai dago kai ba bare ya gane su waye ya amsa musu baki daya kudin goro,ba haka eesha taso ba,gaida baabaa sukayi baki daya ya amsa cikin fara’a
“Mutan kano,gaki ga mutuniyar dai,bata qyaleki ba,nan ta addabeni sai da na siya musu ticket ta taho” dariya suka dan saka baki dayansu.

       A hankali ya miqe yana shafa sumar kanshi,jin maganansu yake kamar a tsakiyan kanshi kasancewar bai son hayaniya,baabaan ya fuskanci me yake son fadi,saboda haka yace
“Shikenan,kana iya tafiya” juyawa yai a hankali ya fice a falon fuska a daure kamar ko yaushe,eesha ji take kamar ta bishi ta rungumeshi,saboda yadda kullum kwanan duniya yake sake tafiya da ita,yayin da sumayya kanta ke qasa tana wasa da yatsunta zuciyarta na bugawa,amira ta bishi da kallo kamar yadda baaba shima ya bishi da kallo,shiru yaci gaba da ratsa falon har ya fice din sannan baabaa ya dauke idanuwansa daga kanshi ya maida kansu,ya dubi amira
“Aishatu ta rakaki amira kuje ku amso min saqo wajen ummenku”
“To abba” ta fada tana miqewa,tasan babanta sosai,hakan ya sanya bata ce sumayya ta taso na,tunda taga haka tasan akwai manufarsa na aikensu su biyu,baki daya taji wani nauyi ya sake kamata bayan fitar tasu,falon yayi shiru ta kasa motsawa sai kanta dake qasa har yanzu
“Mamana,ki saki jiki mana,nima fa babanki ne ko ba haka bane” murmushi tayi Haka ne abba” shiru ya sake ratsa falon na wasu sakanni kafin ta sake jin muryarsa
“Mama na,wata alfarma nakeson na roqeki,saidai ina jin nauyin haka” mamaki ya kamata,ita din wace?,wacce alfarma babban mutum kamar baabaa prof din zai nema daga gareta,bayan ita din ba kowa bace,bata kuma mallaki komai ba
“Baabaa,yanzu kace kai abbana ne,kuma na yarda haka ne,me yasa uba zaiji nauyin bawa diyarsa umarni” sosai wani irin qima da darajarta ya qaru a idanuwanshi,ya jima baiga nutsuwa da hankali tattare da yarinya mai makamancin shekaru irin nata ba,nutsuwarta da kaifin hankalinta shine abu na farko daya fara bashi mamaki tattare da ita,tana da wani irin dattako kunya nutsuwa da ganin darajar manya,wanda zaiyi wuya a wannan zamani ka samu mace kamarta da wannan qualities din
“Allah yayi miki albarka maman,haqiqa iyayenki sunyi nasara wajen tarbiyyarki,sun rabauta da diya ta qwarai,mamana…..kinga yayankun nan da ya fice yanzu?” Gabanta ya buga,sai ta kasa daga kai ta kalli baabaan,Allah yasa ba wani sharrin yayi mata wajen baban ba,kai kawai ta kada
“Mamana,zaki taimaka min ki taimaka masa wajen inganta rayuwarsa?” Duburburcewa tunanunta yayi,sam bata gano me baban ke nufi ba,inganta rayuwarsa kamar yaya,ya manta bata da komai ne qarqashin wasu take itama,duk yadda taso ta fassara maganar tsakaninta da qwaqwalwarta ta gaza gano ainihin ma’anar maganar,har rudun hakan ya bayyana saman fuskarta. 12

     Murmushi baaban ya saki,ya yadda har yau ita dinma akwai sauran quruciya tattare da ita,baison rudata,saboda haka yace
“Baki fahimci baaba ko,shikenan,tashi kije kuci gaba da sabgoginku,idan kika fahimci ma’anar maganar ina son ganinki a lokacin,amma fa kada ki zurfafa tunani,kune qawayen amarya,kusha bikinku kinji mamana,Allah yayi miki albarka”
“Amin baabaa,na gode” ta fada tana miqewa,hakanan taji jikinta yayi wani mugun sanyi,rashin jin dadin kasa fahintar maganar baban ce har ya dago haka ko kuwa mene?. Qarfe biyar na yammacin ranar baki daya gidan ya sake dinkewa da jama’a saboda shirin fara gabatar da kamun amarya,sumayya na tare da amiran duk inda ta sanya qafarta sai ta janyota,kamar yanzu da suke can uwar dakan anty maamaa suna shiryawa,daga sumayyan sai amira sai humaida da humaira,amiran akewa kwalliya an kusa kammala mata,tayi kyau qwarai da gaske cikin wani irin yadin saqi na fulani mai azqbar kyau da daukan hankali,saqin fulani je wanda aka zamanantar da shi da kayan ado dana qawa,maroon ne sosai da yarfin kwalliyar golden a jiki,walwali kawai take zubawa,ta lura da yadda sumayyan ke yawaita shiru,saka bakinta cikim hirarta yayu qaranci sosai,hannu ta sanya ta tabota,ta daga kai ta dubeta tana murmushi,da hannu ta yi mata alamar lafiya,sai kawai ta girgiza kai ba tare data ce komai ba,duk yadda taso barin zancan da baabaa yayi mata abun yaqi barin kwanyarta,zuciyarta ta nace da son gano ainihin me maganar tashi ke nufi
“An gama min,saura ke” inji amira tana isa bakin mudubi tana duba kwalliyar tata,kai ta kada
“Powder kawai za’a shafa min a jamin jagira sun isa” idanu amira ga watso mata
“Bazaiyiwu ba wallahi,kina babbar qawar amarya?”
“Ki barni ayimin hakan don Allah,naga dai yau aka fara abin nan ko?,gaba a yimin” ta fada tana zama gaban mai kwalliyat,dariya humaida ta saka,yanayi da halayen sumayyan ke qara bata sha’awa,sam bata da rawar kai ko iyayi irin na ‘yammata. +

       Duk da cewa ba wani kwalliyar azo a gani aka mata ba amma tashi daya ta sauya,tayi wani sihirtaccen kyau mai sanyi wanda babu hayaniya a cikinshi,su kansu sai da suka yaba,biyar da kwata kiran ango saifudden ya shigo wayarta,yake sanar mata sun iso,da yake tare za’a kama su shi da ita,falon anty maamaan suka sauko sannan suka hadu sa sauran qawaye da ‘yan uwa suka fito.

       Qyashi da hassada fal ran eesha,duk yadda taso taga ta wuce sumayyan a kwalliya abun yacu tura,ira kadai ta tsone mata duk taton ‘yammatan nan,saboda kaf cikinsu bata ga wadda tayi ya kyawunta ba,duk da yake akwai wadanda suka saka suturar da suka fi nata kayan qaawa da tsada,amma ba’a nan take ba wai aj dannewa bodari kai,abinda bata sani ba baki daya sumayyan jinta take a wani mugun takure,karo na farko a rayuwarta data taba shiga makamanciyar wannan,qememe amira ta hanata sanya mayafi sai ratayashi kawai tayi gefan kafadarta guda daya,kayan sunyi masifar amsarta kamar wanda ya saqa su ya saqasu ne musamman saboda ita,takalmin ne kawai ya gagareta tafiya,subaleshi tayi ta nemi plat cikin na amiran ta saka,a ranar tayi adon gashinta wanda yasha gyara aka fito mata da shi cikin daurinta sai sheqi sa walwali yake,ta saje cikin ‘yammatan amaryar har ta zama kamar wata fitila ta daban cikinsu.

        Bata gane wautar data tafka ba sai bayan da suka iso gurin taron,wanda a cikin gidan aka shirya kujeru rumfuna da decoration na alfarma da kece raini,saika rantse da Allah wani event center ne mai tsada aka kama,ita ke riqe da amiran amma sai ta kusa faduwa saboda yadda idanuwa suka mata caaa,idanunta ta lumshe tana kiran sunayen Allah,ko ina abokan ango ne gogaggu kuma wayayyu tsaitsaye suna jira a qaraso musu da amaryar,hannun anty huda ta danqa ta sannan ta juya har tana hardewa saboda ido ta juya,su’adah na tsaye gefan huda din,india ta tafi baki daya,sari ne a jikinta wanda ya amsa sunansa,sak irin dinki ‘yan qasar hindun ne jikinya skert da ‘yar fingilar riga,sai mayafin kayan a jikin skert din ta nannade jikinta,yayin da kanta ke a bude kamar nasu,sai gashin dokin da aka dinkeshi da ainihin nata ya tashi tamkar nata,ta rabashi kafadar hagu da dama kakar yadda ‘yan qasar hindun keyi. Tana juyawa suka ci karo da anty farida umman husna,bakinta a washe take duban sumayya
“Wai wai,kunyi wuyar gani,ko diyarki baku hadu ba” murmushi sosai kan fuskarta cikin girmamawa ta gaida anty farida sanan ta wuce ummee dake cikin gida bata fito ba ta aikota wajen amiran. 

       Wayarta dake hannunta ta dauki vibration sanda amarya ta samu zama a gurbinta ita da angonta,sunan nafisa ta gani,mamaki ya cikata ganin number dinta ce ta nijeria,qarar lasifiqan wajen bazai barta taji ba,hakan ya sanya ta soma takawa don barin wajen tana duban kiran,can baya inda zata iya jin ta ta tsaya ta soma lalubarta saboda kiran ya riga da ya katse
“Am at home sisi” idanu ta fiddo waje
“Da gaske?”
“Suprise wlh naso baki,shigo gidan anty ki shigo dani yau traditional setting na amira ina lissafe dama”
“Wayyo sis,gani nan” ta fada cikin zumudi da murna ta kashe wayar,daidai sanda kida ya soma tashi daga inda ake gabatar da bikin,tsalle ta dan saki kadan farinciki fak ranta
“Yi a hankali gimbiya kada ki fadi ki batan kwalliyar” abinda taji an ambata kenan,da sauri ta waiwayo,alqasim ne tsaye sanye da shadda ya kawo hula gaban goshinsa yana qare mata kallo yana murmushi,daidaita natsuwarta tayi sannan ta juya da niyyar ci gaba da tafiya,saurin shan gabanta yayi,ya wani karyar da kai
“Haba sumayya,ko gaisawa i kya tsaya muyi ko?” shiru tayi tana dubansa ba tare data ce komai ba,ji take kawai zai bata mata lokaci ne,bata da buqatar wani abu a yanzu,tana cewa ta gama da babinsa,tunda tuni ta gaya masa ita din ba budurwa bace bare ya saka ran zata biye masa,idanunta tarufe tare da yin banza da shi,tana jinshi yana magana ci kanka bata ce masa ba.

       Tunda suka fara tashin kidan ya tashi ya shiga bathroom ya sake wanka,jin kidan yake kamar a tsakiyar kanshi,duk wani abu da zai zama tamkar hayaniya bai qaunarsa,ko qwaqwaran motsi ne ya fiya yawa yanzun zai dameshi,sau tari babban wansi adam kance
“Kai ko mustapha kamar mai aljanu,koyaya motsi yake sai ya dameka” amma hakan bai rasa nasaba da ciwon kan da yake fama da shi tsawon shekaru,wanda idan ya tayar masa baya masa ta dadi.

         Ta baya yabi don bai muradin haduwa da kowa bare a tsaidashi a cikashi da suruti,baki daya yau zucuyarsa a quntace take,saidai ko kai daka sanshi baka isa ka fadi hakan ba,sakamakon yadda ko yaushe haka fuskarsa take a daure koda cikin farinciki yake indai ba girmama farincinkin yayi ba shine zaka ga fuskar ta sake washewa fiye da yadda take da,yatsanshi saqale yake da maqullin motar da yake sha’awar fita cikinta,tun kafin ya shiga wankan ya turawa P.A dinsa ya shirya haduwarsa da mutanen da yace jiya bazai samu damar ganinsu ba qasa da awa daya yana hanya kada su wuce haka,sannan ya turawa driver dinsa shima ya shirya motar da zai fita,kanshi a qasa yake takowa cikin shigarsa ta qa’ida trouser da t.shirt v neck wanda ta fidda structure ta jikinsa sosai,kwata kwata saka manyan kaya bai cikin tsarinshi,duk wanda yasan mustapha cikin duniyarsa yasan ba ma’abocin sanya manyan kaya bane,kana iya gama mu’amalarka kaf da shi baka ganshi da manyan kaya ba,daidai gun da jiya suka zauna wasa ya tuna,yaron ya fado masa,ya tuna shegen wayonsa,wani qaramin murmishi da bai shirya masa ba ya kubce masa,a hankali ya daga kanshi sai ya hangosu,tsaye yake a gabanta yayi kane kane kamar zai hade gaf din dake  tsakaninsu,yayin da take tsaye hannayenta harde a qirji tana dubanshi,rashi ya baci,dan salaman da ya samu ta gushe,yana daya daga cikin abinda yasa kenan baison baqin ‘yammatan cikin gidansu,yana zaton daga daga cikin ‘yan matan family din nasu ne,sauya akalar tafiyar tasa yayi zuwa wajen,sai da yaje dab ya lura alqasim ne
“Itakam haka take,gobe wancan mutumin jibi wannan?” Ya qarasa bayansu,daidai sanda take fadin
“Na riga na gama magana da kai ko?,ba zaka taba samun abinda kake so ba,so don Allah ka qyale rayuwata” ta kammala fadi sannan ta juya a hankali ta soma barin wajen,burinta kawai ta isa ga nafisan gashi ya bata mata rai da lokaci baki daya,binta yayi da kallo har sai data bacewa ganinsa sannan ya juyo yana sakin ajiyar zuciya,sai suka hada idanuwa da mustaphan yana kallonshi,kunya ta kamashi,yana bala’in ganin girman almustapha da mutuncinsa,girmama shi yake qwarai da gaske,ya dan diririce yana fadin
“Barka da fitowa yaya” bai amsa ba ya qara taku zuwa inda yake yana dubanshi,haushi yakeji,hashi ya kamashi,ji yake kamar shi akawa haka
“Kan me ka tsaya mace na gaya maka irin wannan maganar ibrahim?,kai namiji ne ka manta?,so kayi maintaining dignity dinka,akwai mata da yawa a gari ka zabi wata mana,kar ka cusa kanka inda ba’a sonka,ba’a so dole,i hope ka fahimta?,ba ita daya bace mace akwaisu da yawan gaske” kai ya rusuna yana gyadashi alamun gamsuwa,cikin zuciyarshi yana cewa
“Ya mustapha kai baka hango abinda na hango ba,baka hango personalityn dana gani tattare da ita ba,hmmmm ke ka ganin so wani abu mai sauqi ne tunda kullum cikin neman son ake a wajenka”amma a fili sai yace
“na gode,Allah ya qara girma” kai ya jinjina ba tare da yace komai ba ya juya ya bar wajen. 

      Kamar ta goya nafisa haka taji lokacin data ganta,tayi ado sosai tana rungume da khalid,ta amshi khalid din kai tsaye suka koma wajen da ake kamu,sanda suka je tuni al’amura sun fara nisa,bayan gabatar da abubuwan da suka dace sannan aka kama amira kafin daga bisani a bada damar yiwa amarya da ango liqi,basu suka tashi daga kamun ba sai qarfe takwas na dare,kamu ya qayatar matuqa da gaske,tafiya nafisa tayi bayan sun gaisa da amira sama sama,taso riqeta tace a’ah tayi haquri abban khalid din ya iso,saidai zata zo dinner insha Allah wanda za’ayi ranar alhamis.

       Washegari akayi arabian night wanda aka gabatar da ita itama cikin gidan baabaa prof,gidane gari guda hakan ya sanya basu da damuwar sai sun kama waje,ba qaramin qawata wajen akayi da kayan ado ba,ranar duk wani ahali da ya shafi baabaa prof sanye yake da abaya ta mata,maza kuma doguwar riga ce da hirami,kai ka rantse a ranar baqin larabawa aka yi a unguwar.

 *******    ******     ********     

Washegari tana kwance tana baccin gajiya,kasancewar alhamis ce ranar babu event din da za’a yi sai gobe idan Allah ya kaimu,ji tayi an daka mata duka,tilas ta farka tana mutstsike idanu,amira ce zaune gefanta
“Sannu,ai wallahi bacci bai ganki ba bai kuma kamaki ba,qarfe hudu zamu lunching na maman saifullahi,kuma ba kowa ne zashi ba,bamu da yawa” zama tayi sosai tana hamma hannunta kan bakinta
“Shine zaki dakamin wannan dukan,badon inajin kunyar idanun saifullahi ba sai na rama” dariya ta qyalqyale da ita
“Ato bismillah,ni kinga ina da mai ramamin,ke kuwa nasan ko na dakeki na daki banza,waccan mutumin da na gani a kano babu abinda zaya iya” ta sani sarai da abdur rahman take,bata san meye hadinta dashi ba data saka masa tsama haka da yawa,harara ta jefa mata sannan ya shiga bandaki ta wanke bakinta ta dawo ta amshi katin tana dubawa,komai a tsare yake harda dress code na maza da mata,mata shigan baqi zasuyi maza shigan fari.
Kusan baki daya kayanta sai data baje su saman gado,ta rasa wanda zata zaba,a haka anty dije ta cimmata,dariya ta dinga yi mata
“Ato wallahi gwara ki qure adaka,don suma dangin saifullahin ba baya bane”sai data gama ruwan idonta sannan ta zabi wani shegen lace a cikin kayan wanda yake baqi ne an masa adon ja mai daukar idanuwa,zuba kayan tayi a jaka don ta nufi gidan baabaa don amira na can na jira,sanda ta isa an gama mata kwalliya,tayi masifar kyau cikin baqar wedding gown,sumayyan zama tayi itama aka soma yi mata tata. +

         Wani irin sihirtaccen kyau ke fita daga kwalliyarta hadi da tsumammen qamshi,kunya ta kamata da mamakin kanta,riga da skert ne wanda suka fitar da baki daya qirarta gaba da baya
” wow”abinda amira ta dinga fada kenan tana qarewa sumayya kalo
“Haka baqin kaya ke miki kyau amiran umman khalipha?,ya Allah” kai ta kada
“Ai kam cire kayan nan ya zamemin wajibi,ina zan iya fita cikin jama’a haka amira” ta fada tana yunqurin cire daurin dankwalin da aka bata lokaci ana mata shi,da sauri amiran ta riqe hannunta tayi kicin kicin da fuska
“Allah idan kika cire sai mun bata,ke komai ma bakison ya miki kyau,kina da kyau kina da aji kina da isar da za’a dama dake,kibar yin haka don Allah” yanayin yadda tayi maganar ta bata dariya,sai ta zame hannunta tana hada mata kayayyakinta data yi amfani da su kasancewar yau cikin dakinta ta shirya
“Bari na maida su sashin anty maamaan ko”
“Godiya namescy na” murmushi tayi ta fice a dakin.

       A shirye ta tadda anty mamman,kasancewar ita zata yiwa amiran rakiya,wani irin biki suke a tsarin familynsu,suna gayyatar amarya ne da manyan yayyenta da iyayenta,inda zasu kawo musu ita suyi mata nasu bikin ma musamman haka sukeyi,ta ajjiye kayan tana saukowa suka sake kacibus da anty maamaa wadda ke kai kawon hadawa baabaa kunun alkama,haka matan suke,duk rintsi basa wasa da cikin mijinsu
“Amiran umman khalipha zo don Allah ki kulamin da kunun nan in qarasa hadawa babanku hadin salad din nan”aladabce ta asawa ta bita kitchen din,cikin sauri sauri take hada komai saboda lokacin tafiya yayi,sau uku amira na aikowa sumayyan tazo su tafi,antyn bata sani ba,sai ana hudu taji aiken da ake mata ta dubeta
“Jeki amira,na qarasa na biyoku daga baya” murmushi tayi tana noqe kafada
“A’ah anty suje kawai,ma taho”.
     Cikin mintuna talatin suka gama,babu abinda jikinta yayi,saboda haka goge hannunta kawai tayi,sannan ta fidda kwalakcarta ta goga a hannayenta,ta sake shafe jikinta da turaren humrarta mai fidda wani sihirtaccen qamshi,wayarta dake ruri anty maman ta daga ta kara a kunnenta sannan tace
“Eh na gama,gani nan” ta dubi sumayya tana maqala kyakkyawar jakarta
“Muje ko amira” ta amsa.

       Tuni maman ta rigata yin gaba saboda hill shoes din dake qafarta wanda ya sake sauya yanayin tafiyarta,sannu a hankali take takawa,sai ka dauka wani salon tafiya ce ta daban,koko tsabar yanga ce da iyayi ga wanda baisan takalmin ne ya takurata ba,baqar rantsatstsiyar mota ce wadda har sheqi take da daukan ido saboda tsabar sabunta da kyau,ita daya ta rage tsaye a wajen,da alamu dukka an tafi,baya anty mamaan ta bude ta shiga,yayi kyau cikin farin qal din trouser da lallausar short sleeve t.shirt baqa mai adon fari a jiki,wadda ta fidda sirrin hannunshi na tarin gargasa wadda ta kwanta har saman tafin hannunshi,da wani sashi na murdadden dantsensa wanda kana gani kasan ya saba daga qarfe,daya daga cikin abinda ya sanya kenan bai fiya saka kaya masu gajeran hannu ba,black hight top snickers ne a qafarsa,tsintsiyar hannunshi daure da agogon fata na kamfanin gucci mai matuqar tsada da kyau,yadda jikinsa ke fidda wani sihirtaccen qamshin wani turare da mawuyacine ka gane wani iri ne haka motar ki fidda sanyayyan qamshin freshner,komai nasa mai kyau tsafta da aji ne,jin yana niyyar tayarwa ya sanya tace
“Tsaya,akwai mutum daya” a kasalance ya kashe motar,ka kadan baison tuqi da kanshi idan ba kamawa tayi ba kamar irin hakan,qarasowa tayi tana niyyar bude bayan anty maamaa tace
“Koma gaba amira” don tasan halinshi sarai,ya tsani ya dauko mutane su shiga baya baki dayansu,yana alaqanta hakan da sai driver,jin an ambaci sunan amira ya sanyashi juyowa,daidai sanda take daidaita zamanta gaban motar suka hada idanu,idanuwanta suka fada cikin nashi,tashin farko kowanne ya janye idanunshi,qirjinta na bugawa,qamshin turarenshi na ratsa qofofin hancinta,idanunta ta ragewa girma tana duban gaban motar,tana ji kamar ta zura da gudu ta bar motar,wani dabaibayi taji na daureta,kwarjininsa ya mata yawa,tana jin zamanta a bigiren bai dace ba,a kasalance ta sanya hannu zata rufe murfin motar taji kamar muryar laila na kiran sunanta,itace tafe riqe da hannun abdallah da yayi kyau cikin baqaqen suit na yara,sai baqin sau ciki na yara da baqar safa baki daya,suka qaraso bakin motar inda take zaune
“Anty,mami tace na kawo miki shi,kuka ya soma yaqi zama” dubanshi tayi cikin sigar lallashi
“Abdallah,ina cewa na gaya maka tun dazun bazanje da kai ba,ka koma gida ka zauna da su laila,yanzu zan dawo bazan jima ba” qafafunshi ya sa bubbugawa yana sakin kuka sosai kamar wanda ake yanka yana fadin
“Allah ni sai naje” ranta ya baci ganin yadda yake tsala kuka kamar tayi mishi wata uwa,sake lallaminshi tayi baiji na,maimakon haka ma sai ya buge hannun laila ya taho inda take ya shigo sit din da take,abinda bai taba yi ba kenan,yana qarasowa kuwa ta daga hannu ta kai masa mari,ta kuwa sameshi gefan fuskarshi,kafin anty maama ta furta maganar daga bude baki zata yi wata tsawa ta karade motar,tuni laila ta ja baya a tsorace,hannunshi ya miqo inda suke ya janyo abdallah wanda ke sakin kuka cikim jim zafin marin ya dorashi kan cinyarshi yana shafa inda ta mareshin
“U r very stupid,how dare you zaki mari qaramin yaro har haka?,saboda bakisan ciwonshi ba?,bakisan ciwon haihuwa ba?,idan baki iya riqeshi mai ya sanya ba zaki sa a maidashi wajen mamarshi ba,fice min a mota!” ya fada cikin bacin rai da zafin rai,bata ankara ba taji hawaye sun soma layi bisa kuncinta,ji take kamar mukhtar ke mata fadan,me ya fusata ta ta mari abdallah itama bata sani ba,hannunta ta sanya kan mabudin motar ta tura da niyyar fita anty maamaa ta dakatar da ita
“A’ah zauna,kuyi haquri mutapha,baki kyauta ba amiran umman khalipha,saurin hannu wa yaro bai kamata ba,ki kiyaye gaba”
“To maamaa” ta fada ba don taso ba ta koma ta zauna,so tayi ta qyaleta ta fita,wani nauyi taji zuciyarta tayi,tana jin hucin numfashinsu su biyun. 2

      Luf abdallah yayi kan cinyar mustapha wanda ya zaunar da shi suna facing juna ya rungumeshi cikin jikinshi yana ci gaba da shafa inda tayi marin,ci gaba da kallonshi abdallahn yayi,a hankali ya furta
“Abba!” Sannan ya sake narkewa cikin jikinshi,wani nauyi zuciyarta ta sake yi,sai ta kasa daurewa ta sanya kanta a tsakiyar qafafunta,tausayin abdallahn yasake qara yawan hawayen dake fita a idanunta. 
        Bubbuga bayan abdallahn yaci gaba dayi kadan kadan har sai da yaji alamun ya huce,hannun ya sanya gefanshi ya ciro gorar ruwan da ya dauko da niyyar sha ya bude mishi ya saka mai a baki,sai da yasha sosai sannan ya rufe ya maidata gurbinta,ya sake zaro wayarsa ya latso wasu lambobi ya kara a kunnenshi yayi magana a taqaice
“Eh,ka sameni gidan,ka tambaya adress din” ya katse kiran ya ajjiye,tada motar yayi sannan ya ya jata a sukwane abdallah na kwance jikinsa.

        Shiru ne ya ratsa motar ba wanda ya sake magana,sumayya na kife har yanzu kan cinyarta tana qoqarin control din hawayenta,ambaton sunayen Allah ta dinga yi daya bayan daya har ta samu hawayen suka tsaya saidai bata iya dagowa ba har suka isa wajem,anty maamaa ce ta soma fita,tuni tayi gaba saboda suna isowa taji ana nemanta ta lasifiqar dake cikin wajen taron.

       A hankali ta daga kanta ta gyara yafen mayafin dake kanta sannan ta bude murfin motar ta fice,ta gefan ido yake dubanta har ta bace a wajen,gajeran tsaki ya ja,yana jin bazai iya ci gaba da zama a wajen ba,daga yarin yayi ya dubeshi har ya soma bacci,sai yaji tausayinshi ya kamashu,haushinta ya sake qumeshi,cikin zuciyarshi ya dinga masifa shi kadai,bude motar yayi ya saba abdallah a kafadarsa suka koma sit din baya,kwantar da shi yayi sannan ya zauna gefansa.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


       Tana tsaye bakin get din gidan jingine jikin motarta hannunta harde a qirjinta,sam wajen bai dace sa tsarinta ba kasancewar a gargajiyance suka tsara komai,bugu da qari ranta a jagule yake,yadda almustapha ke ninka nuna hakin ko in kula da lamuranta,shigowar motar yaso ya dan ja hankalinta kadan,saboda irin motar mustaphan da take mutuwar so,wadda a yau ita taso hawa amma yaqi bata hadin kai,dauke kai tayi daga kallon motar don kada ta zubda ajinta,a dauka ‘yar matsiyata ce kamar yadda take rayawa a ranta,ganin fitowar anty maamaa daga ciki shi ya sake maida hankalinta kan motar
“Kada dai ace almustaphan ne?,yazo ya dauko maamaan a ciki amma ni ina matsayin matarsa ya watsan qasa a ido?” Take raya haka a ranta tana qarewa motar kallo,bata jin mustaphan ne,don tunda itama yaqi daukota ya kawota tabbas babu wanda zai kawo koda kuwa iyayenshi ne(a tunaninta),ita kanta motar bai taba hawanta ba sai yau,hakan yasa ta yin kwadayin ace ita ya fara dauka a ciki,mutum ce ita mai son taga tafi kowa,komai a gunta aka fara ganinsa,bata gama wannan tunanin ba sumayyan ta bude murfin motar itama ta fito cikin salon wata tafiya da zaka tsammaci ta yanga ce,saidai tsabar kasala quncin zuciya da tsinin takalminta ya haifarwa da mai kallonta ganin cewa yanga take kai tsaye,wani bala’i ne ya dirarwa zuciyarta,take ta tattara kallonta baki daya a wajen,ci gaba tayi da kallon sumayyan wadda sam hankalinta bai wajen taci gaba da yi har ta wuce,zuciyarta na tsaka da bata shawarar zuwa ta duba matuqin motar don tabbatar da cewa mustapha dinta ne cikin motar ko wani ne daban mai farcen susa ya yaci nasarar mallakar irin motar mijin mata,hutassheta akayi saboda fitowar da yayi ya koma gidan baya yana sabe da abdallah,ta gane yaron,yaron data cuccusawa zagi jiya da daddare saboda ya gyara mata gyaran alwalarta,huci ta soma fitarwa saboda wani zafi da taji qirjinta yana yi,me kenan?,me hakan ke nufi?,ba bata lokaci ta soma takawa zuwa bakin motar. 1

      Bude murfin motar tayi sannan ta cusa kai cikin motar kai tsaye,hannunshi na saman kan abdallah yaji shigowarta,juyowa yayi ya dubeta sannan ya dauke kai yaci gaba da abinda yake kamar bai santa ba,ta sani sarai bazai tanka mata ba idan in zata shekara matuqar ba ita tayi magana ba,ko ita din tayi bata da tabbacin amsarsa
“Tsakani da Allah ka kyauta kenan man,naci burin hawa motar nan ka watsan qasa a ido amma sai naga ka kawo wasu,har wata banza can ka baiwa damar zama gefanka wanda ni kadai ke da wannan matsayin?” Ta fada cikin son dai daita fushinta don kada ta fita daga hanya ta jawa kanta wani sabon lamarin,ta san duk sabida zancan qarasa karatunta ya sake zame mata wani badadde,ilai kuwa shiru ne ya biyo baya,kishin sumayya data gani yaci gaba da mintsinin zuciyarta
“Wai shin ma meye alqarka da ita waccan yarinyar da har ta samu matsayin daukota cikin motar da koni ban taba shigarta ba,sannan ko kai kanka yau ka fara shigarta?” Bai da ko niyyan waiwayowa ya dubeta bare ta saka ran samun amsa,wayarsa ce tayi tsuwwa ya saka hannu inda ya ajjuyeta ya dauko yana dubawa tare da amsa kiran da ya shigo din
“Bude ka shigo a bude take” ya gayawa drivern nasa a taqaice,dama shi yake jira,sauke wayar yayi still bai dubeta ba yace
“Idan kin gama kina iya sauka ko?”wani abu ya tokare mata wuya,sai ta zuba ido tana kallonshi,sonshi kamar ta lasheshi,haushi kamar ta hafiyi zuciyarta,idanunta ya cika taf da qwalla,cikin rawar murya da son karya lagonsa da kuka ta soma cewa
” ni kake ma haka mustapha?”hannu yayi saurin daga mata wanda dole ta shanye sauran maganarta,sai ta bude murfin ya fice da hanzari,budewa drivan yayi ya shiga cikin girmamawa ya russuna bayan ya zauna ya gaidashi,a taqaice ya amsa mishi,sai da ya tayar da motar suka bar layin suka hau kwalta sosai sannan cikin girmamawa yace da shi
“Ranka ya dade ina zamuje?”
“Maitama” ya bashi amsa a taqaice,baice komai ba ya qara gudun motar suka lula titi. +

         Sosai lunching din ya qayatar,ba qaramin qauna iyalin saifullahi suka nunawa amira ba,basu tashi ba sai qarfe bakwai na dare,wannan karon tare da su amiran suka koma,saidai ko kadan bata da walwala,a takure take jim zuciyarta baki daya,hatta da amiran ta lura,amma bata ce mata komai ba saboda ta tambayi anty mama abdallah taje gaya mata abinda ya faru,ana saukesu ta dubi amira
“Kimin afuwa zan wuce gida sai gobe,kaina ke mij ciwo sosai” ba qarya take ba da gaske kan nata ciwo yake mata,sai ta daga kai
“Na miki,Allah ya bada lafiya,ya tashemu lafiya” ta bude murfin motar ta fice.

        Wanka ta fara yi sannan tayi sallolinta,anty dije tace mata ga abinci tace sai anjima,duka abinda take hankalinta bai wajen yana wajen abdallah,ina yake?,ina ya kai mata shi,tun tana kasa kunne da ido har ta kwanta saidai shiru kake ji,kasa haquri tayi ta miqe da hijabin sallarta ta qwanqwasa dakin anty dije ta mata izinin shiga,kwalliya ta tadda ta tanayi
“Uhm,ya akai amara qirjin biki” murmushi ta danyi wanda yafi kama da yaqe
“Anty wannan yayansu amiran ya amshi abdallah tun dazun,har yanzu ban ganshi ba bashi ba abdallahn” cikin ko in kula tace
“Wa?,wai musty,kada ki damu kisa a ranki kamar kina tare da abdallah ne,ai mayen yara ne,indai mustapha ne a rina” hankalinta ya dan kwanta da jin hakan,sai ta koma daki tayi shirin kwanciya,don ita kadai take da buqata a yanzh,tun tana sauraren ta ina abdallahn zai shigo har bacci ya sureta.

         Washe gari sam bata shiga gidan ba ma sai da yammaci tayi aka soma shirin tafiya dinner,nan ka bata ga abdallan ba,ba kuma wanda ya mata maganarsa,haka taci gaba da daurewa har sanda anty maamaa ta dan tsokaneta
“Abdallah kam anyi wuyar gani anyi sabon daddy” murmushi kawai ta danyi ta basar.

       Wani qayataccen event center suka kama,hmmm masu abu da abinsu,kada kaso kaga yadda gun ya qawatu yayi matuqar tsaru,ranar sumayya anyi abun gani,ita ta zauna mazaunin babbar qawar amarya,tayi komai yadda zata faranta ran amiran duk da a takure take matuqa,idanuwan maza bisa kanta sunyi yawa,kai har ma wasu daga cikin matan,sai da guri ya gama tumbatsa sannan su’adah ta iso,a nan tayi burgar data saba,tsakiyan abokan ango cikin dinkim riga da skert na wani shegen leshi mai azabar tsada wanda aka ci mutuncin tsadar tasa aka yi masa dinki na ganin dama,tsagar skert din har kusan gwiwarta,dinkin ya kamata dam,banda dankwalin da aka tsarawa dauri babu komai a kanta,don ko tuna sunan mayafi bata yi ba,liqi ta shiga yi da ‘yan dubu dubu sabni kar wanda ita kanta bata san nawa ta barar ba,abin nema ya samu ta dauki idanuwan jama’a,ta kuma qona zukatan ‘yan baqinciki wadanda bas son tarayyarta da mustapha,to su gani ya tsaya mata,sai data yi mai isarta sannan ta sauka daga step din ta koma mazauninta. Sai sha daya na dare aka tashi kowa ya koma inda ya fito. +

*******    *******    ******

        Tun qarfe goma na safe layin nasu ya tumbatsa ya dinke da jama’a kasancewar goma da rabi ne daurin auren,bacci ranar tayi sosai dakin anty dije,bata tashi farkawa ba sai qarfe tara da rabi na safe,tarin missed call ta taras duka na amira,da hanzari ta miqe ta fada toilet tayi wanka,a gurguje ta fito ta shirya cikim shaddar da sukayi anko wadda tayi masifar haduwa,kamar yadda dinkin doguwar rigar ya dace da jikinta,komai da tayi amfani da shi kalar zaren da akayi aikin shaddar da shi ne,ta fito fes mashaAllah,daidai sanda laila ta shigo,baki ta sake tana kallon sumayyan,ta qaraso dakin ta samu bakin gado ta zauna
“Wai dama don Allah anty sumayya haka kike da kyau” dariya yarinyar ta bata saboda bihaqqi ta fada
“Sai an tambayo” ta fadi hankalinta ka can gidan baba,saboda hayaniyar data dinga jiyowa na tashi ta tabbatar layin yayi tumbatsar da babu damar ta fita,valcony din saman benan anty dije ta bude ta fita ciki,layin ya shaqara da mutane ya cika masha Allah,kai ta dinga kadawa don tasan dole ta haqura har sai an ragu.

      Kujeta ta ja ta zauna daga gefe yadda zata iya hango komai,ta bude wayarta ta soma lalubar lambar amira don ya bata uzurinta,hakanan taji yana yinta ya soma sauyawa kamar ba ita daya bace a gun,kamar fisgar mayen qarfe haka idanuwanta suka jata zuwa inda yake tsaye tsakiyan wasu zaratan samari kamarshi.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]