QADDARAR SUMAYYA CHAPTER 30

Advertisements

_____

QADDARAR SUMAYYACHAPTER 30Ba yadda ummee ta iya wani lokaci haka take biyewa tsiyar su’ad,ta lallabata,takan yiwa mustapha fada idan ya mata tsawa ko ya niyyaci dukanta,sam bai son sangartarta,bai shiga gidansu ma sabida halayyarta data uwarta da bata yi masa ba,ummee bata son yadda yake mata,takan ce yarinya ce fa mustapha su’ad har yanzj,cikin zuciyarta kuma bata ganin laifin kowa sai na uwarta,tunda ance ice tun yana danye…..,haka nan barewa bata gudu danta yayi rarrafe. +

Tun yana qaraminsa Allah ya zuba masa miskilanci,halinshi ne,halittarsa ce haka gado yayi,yaro ne shi mai zubin gidan sarauta,yana qaunar doki,kayan sarauta da duk wani abu daya danganci hawa doki,kusan yadda halayyarsa take tamkar babban mutum ya sanya abokansa yaran turawa ke tsokanarshi da sunan MAN,mukhtar baabaa prof shima yakan tsokaneshi lokaci lokaci,daga haka sunan ya bishi,son dokinshi ya sanya baabaa prof tun a lokaci yakan siya masa ticket yaje kallon wasan polo tun a american,yawan kallon wasan polo ya sanya su’ad itama wasan ya soma burgeta,bai da abokin tafiya duk sanda zashi kallon,sai ita ke nacewa zata rakashi,tun yana daka mata tsawa yana korarta yana cewa ba zata rakashi ba har ya fara barinta tana binsa,saidai har suje su dawo bai tanka mata,ita kuwa ta cikashi da surutu,abinda baiso kenan,yanzu kansa zai hau ciwo,don ciwon kai bai masa wuya.

Tsabar qwaqwalwa da Allah ya zuba masa ya sanya aka daukeshi daga nursery zuwa primary,a can din ma suka fuskanci basirarsa ta girmewa gurbin da suka bishi,tilas aka sake turashi ajin da zasu kammala secondry a shekarar, 6

   A shekarar ne baabaa yaga dacewar ajjiye aikinsa ya dawo gida ya tattara kan iyalinshi baki daya,anty maamaa dake abuja da ummee dake tare da shi a america,maida hankalinsa sosai yayi ya tasamma gina katafaren gidanshi a abujan,gini ne dashi kansa yasan cewa ya kashe masa maqudan kudade duk da ba komai bane abinda ya cira wajen ginin cikin irin dukiyar da Allah ya hore masa,a yanzu ya tabbatar baida wasu family na jikinsa sosai baya ga sauran dangi tsiraru da suka rage banda yaransa da ya haifa,wanda a yanzu sun zama su bakwai,ummee na da biyar
ADAM
MUSTAPHA
FARIDA(UMMAN HUSNA)
HUDA sau auta
SUMAYYA(AMIRA) +

Bilkisu anty maamaa na da yara biyu duka maza

MAHMOUD da
USAMA

       Gini yayi yana mai hasashen gaba,yana son yaransa maza su zauna da shi idan Allah ya hukunta hakan cikin gida daya,hakan ya sanya yayi sassa biyu,ko wane sashi akwai wasu sassan ciki,duk a lokacin ma adam da yake babba a lokacin yake ss two a can american,sanda suka tashu tafiya aka bar adam ya kammala secondry dinsa,yayin da uncle abdus samad mahaifin su’ad ya nemi alfarmar a bar masa mustapha,saboda ya lura da yadda su’ad ke daga hankalinta daga jin labarin tafiyarsu,da fari mustapha yaqi ya murje idanunsa,sabida asalan shi mutum ne da bai boye abinda ke ransa koda ba zai maka dadi ba,gaskiya ce zaya fadeta komai dacinta,saida baabaa prof ya jashi yayi masa fada kaca kaca,ya gaya masa abdus samad babansa ne kamar yadda shima yake babansa,yarone mai biyayya da bin umarnin iyayensa komai tsaurinsa,baison bata musu ko yaya,hakan ya sanya ya sunkuyar da kai,bai sake cewa qala ba har akayi aka gama suka tafi suka barshi hannun abdus samad da matarsa khaulat,murna cikin khaulat kamar tayi me,a take ta dinga hasasowa ranta hada mustapha da su’ad,tabbas ba zata bari ‘yarta tayi asarar babban gida irin wannan ba,zata so hada alaqa da gudan professor mukhtar muhammad,tabbas ba qaramin kankaro mutunci bane ku samu relation da attajirai irinsu,shu’umin murmushi ta saki,kusan ita ta qara kitsawa su’ad soyayyar mustapha,tunu yarinya ta hau turba,dama gata cikin turawa,batasan kunya ba ko kadan,a shekarun har tasan wani soyayya da i love you,a haka shekaru suka fara tafiya,adam ya kammala karatunsa yana niyyar komawa naijeria,yana son qasar tayi masa,ba kamar mustapha ba da ya lura tunda aka tafi aka barshi bai kuma zancan qasar ba,fushi ne ko ameriacn tafi yi masa oho?.
Koda ya koma nijeria adam makarantar gaba da secondry aka sama masa ya sake komawa,yayin da mustapha tuni ya shiga secondry,yana aji biyu junior suka daukeshi suka maidashi senior aji biyu saboda gifted ne na tashin hankali,kishinsa classmate dinsa suka musamman turawan nan,suna ganin bai isa ba yana asalin dan nijeria yace zaizo ya dokesu,kunsan mai jan kunne da shegen kishi da ganin kai baqar fata baka isa ba,to indai mustapha ne basu isheshi duba ba,karatunsa yake haiqan,babu wanda ya isa yayi gigin tabashiduk iskancinau,sunsan waye ubansa,ko baya ga haka ma suna sane da halin jarumta irin tashi,sau da yawa abubuwa na tsoro sai su kasa shike gabatar da su,baison raini ko kadan yana da zafi,bai shiga sabgar da bata shafeshi na,wadda ta shafeshin ma ba lallai ya bata muhimmanci ba,karatu ya zaunar da shi kuma shi yakeyi,tilas suma suka sallama masa,cikin qanqanin lokaci yayi fice yayi suna cikin makarantar,tare ake kaisu a daukosu shi da su’ad,saidai ko kadan basa shiri saboda yadda ta cika rawar kai da kule kulen maza,amininshi daya ne tal a duniya har ya zuwa yau din nan,HAMZA ABUBAKAR JAHUN,babansa aiki ne ya kawoshi qasar suke zaune,shi daya yasan ta kan mustapha,ya iya zama da shi hakan ya sanya tasu tazo daya. +

        Duk da wannan halayya tasa mutum ne shi mai tausayi,yana da tausayi ga mata tun asali yasan su masu rauni ne,sannan qananan yara musamman idan aka ce wannan maraya ne,Allah ya zuba masa tausayin maraya walau uwa ko rasa ko uba,ko kuma dukka baki daya,tun a sannan ya yiwa kansa alqawarin gina gidan marayu idan ya girma,yasan idan ya yiwa babansa maganar shi mai ginawa ne,to amma yafison ya gama karatu ya kama aiki,ya ginda da kudinsa daya nema da guminsa.

     A can mustapha ke halartar wata makaranta,duk da yake aji guda ne saidai kowa da inda ake masa qari,alqur’ani ake koya musu da littafan addini wanda ya shafi fiqhu,tauhid/aqida,da kuma hadith,mutumin dan qasar pakistan ne,da fari su’ad na binshi suje,duk da ba wani abun arziqi take koyowa ba,daga bisani bayan shekara daya ta watsar,saboda a ganinta ta girmi zuwa makarantar islamiyya,tayi zamanta da jahilcinta tana yiwa wasu kallon gidadawa kidahumai,mustapha bai gushe ba yana zuwa makarantar har ya sauke bayan haddar izifi talatin cif da ya samu,wanda har zuwa yanzu tana nan a kanshi.
A hankali shekaru suka fara ja,girma yazo wa kowannensu,su’ada an zama budurwa,tana ss 2 a lokacin,yayin da mustapha ke universty,a duniya baida sha’awar kowanne karatu irin karatun likita,yana son karantar bangaren cututtukan yara,sai aka samu akasi kasancewarsa ba mai magana ba,uncle abdus samad ya cike masa fannin mata,wato gynocology,sam wannan fannin bai burgeshi ba,amma da sukayi magana da ummensa,ta nuna masa cewa bangare ne mai muhimmanci da irin adadin matan da zai iya taimaka,sai ya gamsu ya karba hannu bibbiyu,ya shiga karatu ka’in da na’in,kowa ya sani cewa karatun likita ba abu bane mai sauqi kamar sauran bangarorin,balle agun mutum mai daukan lamuransa da gaske irin mustapha,bashi da lokaci komai sai na karatunshi,fanni guda suke karanta shi da abokinsa hamza,a hankali suka hadu da abokai daidai su,wadanda karatu kawai suka saka gaba,cikin qanqanin lokaci group dinsu yayi shura,su shida ne cif,dukkansu babu baya cikinsu,ta fannin kyau,nasaba da dukiya,mustapha,hamza,usman,musaddiq,lamin,huzaifa,suna da ra’ayoyi iri guda ta wani fannin,yayin da kuma suka saba ta wani bangaren,abu guda dai wanda sukayi tarayya a kai shine,aqidun turawa da sukayi tasiri cikin gangar jiki da zuciyoyinsu,sakamakon dadewa da kowannansu yayi cikin qasar,lamin me kawai da musaddiq karatu ne ya shigo da su,ba wanda ke harkar banza a cikinsu anutse suke,saidai kama daga abinci,sutura zabi na irin matar aurensu,doka da qa’ida da mu’malaolinsu na yau da gobe dukka aqida da halayen nasara ya shiga cikinsu yayi kane kane.
+

                  SU’ADAH

     Yarinyar da tun tana qanqanuwarta aka nuna mata ta ginu ta kafu kan raina talaka,dukkan wanda bai da shi bai da qima baida daraja a idanuwanta,kai hasalima bata masa kallon cikakken mutum mai ‘yanci,yarinya ce mai yawan izza da jin kanta,yarinyar da bata mu’amala da dukkan mutumin da bai fisu arziqi ba,matuqar kina so ko kana so kuyi qawance ka tabbatar ka fito daga gidan da yafi nasu arziqi ko kake dai dai da ita,ta dauki kanta da girma,ta ajjiye kanta can nesa sama qololuwa,komai nata high class ne,komi da zata mallaka sai ta tabbatar yasha banban da na kowa,bata taba yadda wani ya fita ko ya shalle mata,bata lamunci kallon banza ba bare ka furta mata maganar banza,taku take iya qarfinta,jin kanta take tamkar diyar DONALTRUMPH ko kuma BILLGATE,kallon da takewa mutane ma dabanne,duban farko ga mai hankali zai fuskanci kallo ne na qasqanci da ganin kowa bai isa ba face ita din nan dai,masu hidimawa gidansu kallonsu take tamkar bayi da suka siyesu,babu wanda baifi qarfin ta takashi ba matuqar arziqinka ya gaza nasu,wayewarta ta wuce iyaka,ta wuce tunaninka,duk wani abu da baturiya zatayi shi a matsayinta na farar fata wadda bata da cikakken addini bare kunya shi su’adah zata yi ba,babu uban wanda take jin kunya,abu guda ne bata taba yiba bada 
mutuncinta,saboda ta riga ta sanyawa ranta bata da miji daya wuce mustpha,har yau batayi katari da namiji kamar mustaphan ba,duk wanda ta kalla sai taga mustaphan ya masa fintikau,tamkar yadda sama ta yiwa qasa nisa,bugu da qari ta tabbatar ta jewa mustapha a fanko babu abinda zaya hana wulaqanta duniyarta,babu abinda zai hana yayi fatali da dukkan wata qauna da take masa ya hukuntata mafi tsananin hukunci,tana yarfa tare da wulaqanta maza da yawa,kama daga hausawa har zuwa turawan,idan har kaga ta tsaya ta kulaka tofa ka tabbatar babanka an sanshi ya san wani shima,sunansa ya zama tambari a duk qasar da kuke da zama,su’adah bata san sanya atamfa ba balle daurin zani,dankwali kuwa saidai ta gani a kan wasu,yadda americans ke shigarsu itama haka yake,ta sanya rigarta da wando,ta fito da gashi ta fice abinta haka,a da har ra tsiri saka mini skert,mustapha yaci ubanta ya taka mata birki,tana qwafa tana kumburi bayan fitarsa tana ba zata daina ba,kaulat da take kira mom ta mata fada,ta fuskanci sam a cikin kaso dari na rashin nutuncin su’adah itakam ko arba’in bata yi ba,dama wai ance sai mai koyo yafi qwararre qwarewa
“Ke da kike son aurensa,ta yaya zaki qi yin abinda yake so,idan dai baso kike ki jawo mana asara ba,jira nake kawai ki gama secondry na qyasawa babanku maganar,don kada ma ya hango wata ya jawo mana asara” kan haka ya sanya ta daina sanyawa,ta kuma nemi dankwali take sanyawa akanta don dole wanda data fice yawonta zata figeshi sai kuma idan zata dawo gida.
       A irin zaman hostel da sukeyi idan jarabawa ta kusa,suna zaune su shidan bayan kowanne yayi karatu ya gaji,sai kuma suka barke da hira,mustapha dake kashingide gefansu yana duba handout,shi kadai ne bai ajjiye tasa ba,sun riga kusan da sun saba da irin wannan halayya tasa,yadda yake na daban komai nashi dabanne,bai gajiya sam da karatu,iskar gun nayi mishi dadi qwarai,saboda wadatar shuke shuken dake wajen,a hankali suka gangaro kan hamza,shi sukewa tsiya kan yaci baya,ya rasa wadda zaya aura sai ‘yar afrika,afrikan ma nijeria,nijeria ma yarinyar da kwalin secondry school kadai gareta,ra’ayinsa ne,don duk cikinsu ya fisu sassauqan ra’ayi,baiga dalilin da zai daukarwa kansa jangwam ba,yana mamakin yadda ‘yammatan da idanunsa ke bude tarwai suke burgeshi,shikam ya sheqa yaga babu qwaya gwara ya auri local ya wayar da abunsa,kusan mustapha yafi kowa jin baqincikin batun,shi gaba daya atsarinsa ma baijin zai iya auren matar da bata da kwalin degree zuwa sama,matar da tasan abinda take yi,yana jinsu suna ta kumfar baki,daga bisani da yaji sun fara cikashi ya miqe zai bar gun,don kada ma ranshi ya baci kan lamarin,bai son cewa komai,haka ya kwashe litattafansa ya sauya gu yana ganin baiken hamza,tare da mamakin meye amfanin wayewa da karatunsa da zai dauki irin wadan nan yaran a matsayin matar aure,wadda babu wayewa tattare da su,a ganinsa saidai kawai kasha kayan haushi,babu wata kulawa da zallar soyayya mai maqalewa zuciya da zasu iya yi ma,a yadda yake din nan mayen soyayya ne,mutum ne shi mai burin samun macen da zasu baje kolin soyayya,ta soshi tamkar ranta,ta kula da shi kamar sabon jinjiri,ta shagwabashi kamar dan auta,ta bawa lamuransa muhimmanci ta fifitashi fiye da kowa ina zaya samu wannan ga irin wadancan matan?.
Lokacin da mustaphan ya gama karatunsa baki daya har ya samu aiki a wani babban asibiti dake garin,wanda da gudu suka daukeshi,sun jima dama suna bibiyar irin qwazonsa,don a daliban da jami’ar ta yaye a shekarar banu dalibin da ya kai qwazonsa,ranar baabaa prof yayi farinciki da samun d’a kamar shi,ya runa kalaman mahaifinsa muhammadu,ba shakka suna ganin abinda malam ya gaya musu zahiri,mustaphan daban yake tun daga haihuwarsa zuwa yau,haka ma ummee don baki daya suka rankayo harda anty maamaa suka zo bikin yaye su din.
+

        familyn tun a lokacin family ne mai ban sha’awa da burgewa,cike yake da qaunar juna da hadin kai,dukkansu daga ummee har anty maamaa sun tsarkake zukatansu,kowacce ta riqe ‘yar uwarta fusabilillab,sai Allah ya shiga lamarinsu ya kade musu dukkanin abun qi.

        Ana ya gobe su baabaa prof din zasu koma uncle abdus samad ya sanarwa baabaan niyyarsu ta hada auren mustapha da su’adah,ba qaramin farinciki baban yayi ba,yana ganin lokaci ne na qara danqon aminci da zumuncin dake tsakaninsu,ko a lokacin sai da ya tuna da sulenshi,inama ace diyar sulenshi ce zai aurawa mustapha?,kowa yayi na’am da batun sabanin mustapha daya shiga tashin hankali da bacin rai,tunda shi kam babu wata alaqa ta soyayya data taba shiga tsakaninsa da yarinyar sam,hasalima bata cika sharadan da yake so ba,don candy kadai tayi,kawai dai ya dauketa ne matsayin qanwarsa,amma da batun yaje kunnen abokan nasa su suka kwantar masa da hankali,a ganinsu babu komai,a daura auren taci gaba da karatunta,shima yaci gaba da aikinsa,idan yaso sai yayi rainonta har takai matakin da yake so ta kai,ya dorata kan dukkanin tsarinsa,tunda babe din ta hadu,abinda basu sani ba dukkansu shine su’adan ta girmi tunaninsu,shi sam shawarar ma bata yi masa ba,abu guda da ya sanyashi amincewa shine ranar wata lahadi da ya jiyo muryar kaulat na kururuwa,su’adah din ya dirki guba saboda ta lura mustaphan baya sonta,abun ya tsoratashi,ta dauki halayen yahudawa baki daya na rashin yadda da qaddara,ko data farfado cewa tayi zata kashe kanta,roqon sa da uncle din ke masa kan ya aureta shi ya masa nauyi,ba tare da bata lokaci ba ya amincewa aurenta,yana tunanin yayi amfani da shawarar abokansa kawai.

6

      Cikin iya duniyanci da gogewa sannu a hankali ta soma jan ra’ayinsa,sai ya sakar mata ya zuba mata ido,cikin kaffa kaffa take lamuranta,don tasan halinshi sarai bai daukar wargi,a hankali ta soma bude wata qofa daga cikin zuciyarsa,wanda hakan ya sanya ya dan sakar mata kadan,a wannan bigiren sukayi aure.
      Baki daya ta bata tsarinsa na yayi rainonta,abu guda ne ya dore ci gaba da karatu da tayi,don itama tana masifar son karatu,tana son tayi karatun da zata zama wata,watan da duniya zata dinga maganarta da kwatancenta,ta riqi karatunta da masifar muhimmanci,tana ganin shine tsanin mataki na biyu da zai sanya ta zama wata a duniya,bayan zamantowarta daya daga cikin iyalin PROFESSOR MUHAMMAD MUKHTAR MUHAMMAD ADAM GOMBE.
Rayuwar gidan aurensu rayuwa ce irin wadda suka ga mazauna qasar nayi,rayuwar ‘yanci,kowa yana da right,har wani lokaci mace tafi namiji dama,saidai a wannan bangaren mustaphan ya riqe kambunsa,yayi riqo da bahaushiyar al’ada,ya bata damarta,saidai fa bata isa ta tsallake umarni qa’ida ko dokarsa ba,wannan kadai take gani ya takura ta,shike bata mata rai,to amma ba komai bane a gunta saboda masifaffen son da takewa mustaphan,tanaji a acikin ranta ko ummee da tayi naqudarsa bata kama qafar son da takewa mustaphan ba.
+

       Tsakaninta da mustapha ya biya mata buqatarta,ta aure kota kudi,taci sa’a kuwa gwanin kyautatawa iyali ne,bata san cinsa ko shansa ba,batasan tsaftar muhalli data tufafinsa ba,suna da kuku suna da mai share share suna da mai wanki da guga,sam ita a rayuwarta ma baki dayanta bata taba shiga kitchen ba,shege ruwan zafi saidai ta ganshi kawai,rayuwa ce irin ta banasaren mutum zallah suke gudanarwa,shima bai damu ba,amma wani lokaci sai yayi mamaki idan yaje nijeria yaga yadda su umme ke dawainiya da majinsu,basu duba tsufansa ko girmansa ko kuma yawan ma’aikatan dake gidan,wanda duk abinda kake so daka fada ta cikin waya za’a gabatar maka da shi,sai ya watsar tare da dora hakan kan mizanin banbancin al’ada da dabi’a.

        Yana tsaka da aikinsa wani babban asibitin kudi suka yi masa tayin aiki a asibitinsu,ya duba yanayin asibitin yaga yayi masa,akwai nisa sosai tsakanin jahar da suke da jahar da asibitin yake,hakan ya sanya ya duba gida mai kyau a can ya siya,bedroom biyu falo sai kitchen ya koma can da aiki,yayin da ya bar su’ada a nan tana ci gaba da karatunta,don cewa tayi ba zata bishi ba gaskiya taba tsaka da karatunta,shima bai wani damu ba yayi tafiyarsa,saidai sam baida lokacin zuwa inda suke,ita dince idan ta motsa mata zata kwashi kayanta ta bishi,tayi masa weekend ta dawo taci gaba da sabgoginta.

       Tafiya ta fara nisa,babu haihuwa wajen su’adah ba dalilinta,bata yi mamaki ba,don tuni ta jima da fara hadiyar qwayoyin tsaida haihuwa tun satin farko na aurensu,kusan tafi uwarta iya shege,don daga bisani ma zuwa tayi ita aka juyar da mahaifar,don tace bata ga me zata ci da haihuwa ba,ita da iyayenta suna da arziqin da basai ta nemi taimakon da ba,tunda dama don ya taimakeka kake haifarsa(a tunaninta),sam mustaphan bai san da wannan badaqalar ba ko kadan,ya dauka kawai Allah ne bai kawo ba,baya ga aikin da yakeyi yana kasuwanci sosai,wanda har yaso yafi baabaa prof qashin arziqi,cikin qanqanin lokaci dukiyarsa tayi haukatar ban mamaki,hakan ya sanyashi diban maqudan kudade ya zo nijeria,kowacce state din nan da muke da ita ciki harda abujan ya danqara asibiti,wanda idan da na private ne sai ka isa ma zaka iya zuwanshi,amma yace kyauta komai za’a dinga yi ciki,shi da kansa idan ya samu lokaci yazo nijerian yana zabar states din da yake ga zai iya zuwa ciki harda gombe wadda bai fashin zuwanta sabida tuna asali da tushe ya ziyarci a asibitocin,ya karbi cases masu girma da asibitin ya samu ya zauna yaga marasa lafiyan yayi musu abinda ya dace,asibitin abuja kuwa sati biyu yake yi yana ganin marasa lafiya kowanne iri matuqar lalurar ta shafi mata,hakan ne ya sanya kaf fadin najeria babu asibitoci mafiya inganci taimako da kula da marasa lafiya irin nasu asibitocin,girmamawa ta musamman gwamnati ta yi masa saboda taimako da gudun mawar da ya baiwa al’ummarsa.
1

        Baya ga wannan ya gina gidan marayu,kano daya gombe daya abuja daya,gidan marayu mafi girma da baiwa marayu tallafi da kulawa a nijeria,shike daukar nauyi da dawainiyar komai nasu,yana daga can yana turo duk wani abun buqata nasu,ya sake samun bunqasar arziqinsa ne lokacin da ya zuba hannun jarinsa cikin wani company dake dubai wanda ke saqa nau’in dogayen riguna na maza da mata masu tsada da kuma masu matsakaitan kudi,daga bisani masu hannyen jarin kowa yaso janye nasa,shi ya biya kowa ya mallakin company,ya zauna tare da taimakon hamza,musaddiq lamin da usman suka sake yiwa companyn garambawul ya sake tashi a aiki,suka sauya masa
suna wanda yake amfani da tambarin MM mustapha mukhtar,sai gashi ya zama company mai daraja ta daya dake sarrafa dogayen rigunan dai nau’i daban daban,kaloli daban daban,companyn na daya daga cikin zuciyar arziqin da ya mallaka.
      Rayuwa ta yiwa su’adah dadi,sai yanzu take sake kallon irin gatan da mamanta tayi mata na maqalewa tare da naqalta mata auren mustapha,tana jin dadi tana alfahari ta juya a duniya tace itace matar MUHAMMAD EL-MUSTAPHA,wanda ya kasance cikin jerin sahun farko na matasan shahararrun masu arziqin da nijeria ta mallaka.

        Rayuwa ta yi masa kyau,burikansa suna dab da cika,wannan karon yana yawan waiwayar nijeria,idan azumi ya kusa kamawa a nan zaizo yayi guda ashirin,goman qarshe su wuce umra shi da duk wanda Allah tsaga da rabonsa ko wanda baabaan shima ya biyawa,duk shekara bai dauke sunan ummensa babanshi da anty maamaa,sai autarsu sumayyatul amirah,shike biya musu,bai yadda suyi amfani da kudinsu wajen biyawa kansu ba saidai wanda suka ga dama cikin ‘ya’ya dangi ko surukai,idan ta rayawa su’adah tace zata bismillah,idan kuma ‘yan abun basa kusa taqi zuwa,wani lokaci da taje can ta gwammace ta siyawa kanta da qawayenta tikiti na maquden kudade su tafi kallon wani wasan a can wani shahararren gun kallon wasa duk inda yake a duniya saidai idan ba’a ginashi ba,hakanne ya sanya take matuqar qawance da qasar DUBAI,daga bisani Allah ya hukunta mustaphan aikinsa ya dawo dubai din,hakan ya masa dadi saboda yayi masa kusa da company dinsa,duk da dama bai da damuwa yana da abokai masu kama da ‘yan uwa dake kula da shi,kasancewar dukkansu basu kai budin mustaphan ba,sai dubai ta sake zamewa su’ad din gida,tana iya baro karatunta ta taho dubai din takanas kallon film ko wani wasan,daga nan ta shargalle agun mustaphan idan taga dama ta wuce,hakan ya sanya karatun nata ke kwan gaba kwan baya,har yau yaqi ya qare.

      Sukan dawo daga umra ranar sallar,daga nan idan baijin gajiya zai sake hawa jirgi a washegari ya taho rano wajen kakanninsa,da shi ake hawan sallah,abun na qayatar da shi,kusan tawagarsa daban take,duk sanda zai wuce sai ya ja hankalin mutane saboda kwalliyarsu daban take,bayan ya gama hawan sallah sannan ya dawo ya koma kan ayyukanshi,haka rayuwarsa take,kusan baida wani lokaci na banza a rayuwarsa,duk daqiqa daya mai amfani ce a wajensa,yana tafiyar da ita wajen ayyukanshi,hakan bai damu su’adah na wai bata samu cikakkiyar kulawa ba,arziqi dukiya da rayuwa mai aji da tsada take buri kuma ta samu,buqata ce idan ta taso mata duk inda yake zata siyi ticket ta bishi ta fansheta ta dawo.

      Hakanne yasa a hankali qannensa mata suka fara lura da irin rayuwar da yayansu yake,rayuwa ce mai kama data gauro,bai da wata mace a gefansa da zai dafa ta aduk sanda wani abu ya taso masa na gaggawa,bashi da wata mace dake tare da shi kullu yaumin da zata tsara masa lamuransa,lokutansa da rayuwarsa,ko da yaushe yana cikin aiki,aiki dai,shi yana gabas kasuwanci da aiki matarsa tana yamma karatu,sam baida wani family da zai nuna nashi kamar yadda sauran ‘yan uwansa ke da shi.

      Misali: babban wansu adam a yanzu haka yana da matan aure biyu,ta farko na’imah Allah bai bata haihuwa ba ya sake aure ya auri fahriyya,yanzun haka yana fa yara hudu,biyu maza biyu mata,yana aiki a legos cikin shima nashi company na qashin kansa,yana zuwa gida da su baki daya idan ya faru ko kuma daya tazo a bar daya a can,qanwarsa farida tayi aure,tana da yara uku,mai bi mata huda itama tayi aure yaranta biyu,mahmoud ya kammala karatunsa,yana juya dukiyar baabaa prof shi da dan uwansa usama,baaban baya komai sai kula da gidan gonan sulensa,har yau sule yana ranshi yana saka ran haduwarsu kafin mutuwa da ruski dayansu,gidan gonan da zuwa lokacin yayi rassa jahohi daban daban har nan abujar,duk da cewa usama akwai sauran nauyin karatu a kansa da bai kammala ba,amma daga can inda yake yana kasuwancin,thailand ne,shi da mahmoud din ke shigo da kayan su rarrabawa ‘yan kasuwa,kowannensu ya fidda macen macen aure,lokaci kawai ake jira,sosai baabaa yaga alfanun yiwa yaran nasa sashensu,don ya zame musu tamkar mahada ko masauki duk sanda suka baro wajajensu kowa nada bangarensa da zaya sauka cikin gidan kusa da babansu,akan ga kowa a gida akai akai amma ganin mustapha yakan zama aiki,balle madam din nasa,wadda lokacin bikin sallah ne take biyoshi don ta san cewa gidan nasu kan kasance cikin baqi ‘yammata da samari,takan biyoshi ne ta kasa ta tsare,abinda har yau bata sani ba kenan halayyar mijinta,itace shaida ta farko da zata fadi kan mustapha baida idanuwan kallon mata baki daya,amma ita sai take ganin hakan isarta ce tasa har yau ita kadai yake gani,ta sani cewa mustaphan nata irin mazan nan ne dake tsada,mazan da mata ke marmarin samu,ba wai saboda tsurar kyau kawai ba,a’ah,kwarjini haiba kamala da cikar zati da halitta,ita kanta ta tabbata Allah ne kawai ya kashe ya bata,tana sane da yadda ake farautar mustaphan,kama daga yammata kyawawa masu taqama da kyau da arziqi irin nata ko fiye da natan ma,zuwa manyan hajiyoyi masu juya naira,abun yakan bashi mamaki ganin yadda mata ke farautar d’a namiji,yakan jima yana jinjina lamarin,wasu na roqon aure ya hadasu,yayin da wasu ke roqo ko da harkar banza yazo suyi,son so ace yadda haduwar mustaphan take baida komai,da sun yaudareshi koda da dukiya ce,saidai kash,sai suka sameshi da arziqin da zai iya daukar nauyin danginsu ma baki daya.
   Sirrin samuwar nasararsa ta ta’allaqa ne ga biyayya da tsananin kyautatawa iyaye,bai iya tsallake umarninsu,uwa uba kuma tausayi da taimako.
Wannan shine cikakken tarihin familyn baabaa sumayya,na tabbata zuwa yanzu kin fahimci komai” murmushi sumayyan keyi tana gyada kai,sosai labarin asalin zuriyyar ya burgeta ya qayatar da ita,very interesting,ta tsinci darussan masu yawa a ciki,sunyi gadon karamci mutunci da halacci,qasan ranta take raya amma shi kam bata san inda ya tsinto nashi halayyar ba,tana masa duban mutumin da bai girmama mutuntaka ta dan adam,mutum mara saurin fahimta da dogon tsinkaye da bada hanzari
“Wa kenan”ta tsinci muryar anty dije na tambayarta
“Na’am”sumayya ta waiwayo da hanzari tana tambayarta,don bata tsammaci da ita take ba
“Idan na canka dai dai mustapha kike wa wannan yankan hanzarin ko?” Da sauri ta kada kai
“Ko kadan,me kika ji nace?” Murmushi antyn tayi ganin tana son musanta mata,cikin sigar tsokana tace
“Kiyi dai a hankali,kada kema ki fada tarkonshi,naga ba wuya ‘yammata sun zurma cikin komarsa” wata matsananciyar faduwa gabanta yayi,kai ta soma kadawa
“Allah ya sawwaqe anty,ya rufamin asiri duniya da lahira,yanzu kyamin wannan fatan haba anty?,na kai su’adah ina,baya ga haka ma wallahi baiyimin ba ko kadan,banga abun burgewar ba anan wajen” dariya antyn tayi sosai har su laila dake sit din gaba suka waiwayo suna dubanta sai data ce su juya
“Dukka yadda akayi kallon tsoro kika yi masa,kece mutum ta farko da naji kin ambaci haka,ko minal dake da qarancin shekaru cemin take,mami uncle man yana da kyau kamar na ‘yan india,ta yaya ma zaki gane shi bayan kallon mukhtar kika yi masa ba ainihin kamarsa kika gani ba,kuma ma meye na saurin rantsuwar baiyi miki ba?,kika san inda rana zata fadi?”
“A inda ta saba faduwa mana anty,komai kyansa bazan gane ba anty daga kan mukhtar an gama namiji” ta qarashe zancan fuskarta na nuna rauni da karaya da zuciyarta tayi,hakan ya sanya antyn yin shiru,yayin da itama tayi shirun tana maida numfashi tare da hadiye yawu da qyar.

        Kai ta girgiza bayan ta gama wassafa ta yaya zata zauna zaman aure da wani bayan mukhtar din,sam,ji take ba zata iya ba,babu wannan mafarkin cikin rayuwarta,kamar soyayyar da take nuna masa bata cika ba kenan.

        Cikin hukuncin Allah suka isa qasar lafiya,tun daga airphort sumayya ta soma gane banbanci baro baro da tata qasar,haka tayi ta kalle kalle sanda taxi ke dauke da su zuwa masaukinsu,sai ta samu kanta da yiwa qasarta addu’a tare da fatan samun ci gaba kamar wannan qasar.

         Da suka isa a gajiye suke,gida ne wanda ke dauke da falo guda daya,sai kitchen,bedroom uku,kowanne da manne da toilet,sallolinsu kawai suka rama kowa ya kama makwancinsa,kusan ita ce qarshen bacci a gidan,ta jima tana juyi kan gadon,hakanan take da tsananin baqunta,duk sanda ta sauya muhallin data saba da shi tana dadewa kafin bacci ya dauketa.Tunda suka je uncle farouq bai zauna ba,yana ta zirga zirga kan abinda ya kawoshi tare da yi musu siyayyar abubuwan da zasu buqata na gida,sai da suka ci sati guda cur kafin komai ya daidaita,ya miqa laila da khalipha wata makaranta wadda ke nan cikin unguwar,yayin da ya samawa sumayya wata center ta manya dake karantar da su dukkan wasu karatuttuka irin na ‘yan secondry tun daga matakin farko cikin shekara guda su baka certificate dinka,itama babu nisa tsakaninsu,ko a qafa zaka iya zuwa,idan kana da buqata kuma kana fita bus zata zo ta daukeka ta qarasa da kai,da fari sumayyan ta tsure,tsoro take ji,tana tunanin ta yadda zata dinga zuwa wajen ita daya,ta zauna cikin baqin fuska,fararen fata,wadanda akwai banbancin addini harshe da al’ada tsakaninsu,kamar tayi qwalla saboda tsoro,anty dije ta dinga tuntsira mata dariya
“To ko ni zan dinga rakaki?” Ta zolayeta
“Dole fa ki saki jikinki sumayya,nan qasar babu ruwan wani da wani ce,kowa abinda ya kawoshi shi yakeyi,ki zama mai budadden kai,so nake a kasa ganeki duk sanda muka koma gida” da irin wadan nan kalaman ta qarfafi gwiwarta. +
       Ranar farko gabanta na dukan uku uku  haka taje,tayi tsurutsuru cikin ajin,sam bata fahimtar me suke fadi bata fahimtar turancinsu,a wani hade yake bare ta iya tsintar abinda zata iya tsinta din,tana nan zaune tsuru taji an dafa ta,ta waiwaya tana kallonta
“Sannu,ke baquwa ce ko?” Sai ta sake kallonta sosai,baqar fata ce ‘yar uwarta wadda a qalla zasuyi shekaru daya,amsa mata tayi,fuskarta sake ta nemi wajen zama kusa da sumayyan tana gabatar mata da kanta,kusan ita tayata zama har aka tashi suka taho tare,ashe basu da nisa saboda haka ta samu abokiyar tafiya tare suka taho,sunanta zulaiha ta sanar mata,itama baquwa ce a qasar bata kai shekara guda da zuwa ba.

       Cikin satittika suka soma sabawa da zulaihan,anan take gaya mata dan uwan mahaifiyarta ke ruqonta,mamanta na aure ne a kano qauyen sumaila,itace autarsu,tana da shekara sha takwas mahaifiyar tata ta rasu,babanta na son yi mata auren dole,yayan mamanta shi yaji labari yazo ya dauketa,ya taho nan da ita inda yake sana’ar drivern taxi,da yake qasa ce ta neman arziqi,jama’armu da yawa musamman daga qasashe na afirka kan tafi neman kudi irin wadan nan qasashe,idan zamanta ya karbeka duk sana’ar da kake sai kaga albarka cikin arziqinka,sam ba zaka ce yana tuqa taxi ba anan musamman idan yazo gida nijeria,matarsa daya dansu daya.

      Akwai banbanci tsakanin sumayya da zulaiha,zulaihan ta fita wayewa da gogewa qwarai,idan ka ganta ba zakayi tsammanin ga daga inda ta fito ba,mutumce mai son jama’a da faran faran,hakan ya sanya take da qawaye sosai,sai a lokacinne sumayyan tasan alfanun qawa da dadinta,musamman idan ka hadu da mai kyakkyawar halayya irin ta zulaiha mai sonka da zuciya diya,da fari sumayyan ta fara tababa kan yadda zatayi shiga ta fita ba irin wadda ta saba ba,zulaihan ita ta karbi kudi wajen anty dije ta rakata ta siyo irin sutturun qasar,wanda zaki sanya basu fidda tsiraicinki ba,wadanda zaka dace da zamani ba kuma tare da ka fidda tsiraicinka ka sabawa al’adarka ba da addininka baki daya,sau tari idan ta shirya zata makaranta laila kan tsokaneta
Wallahi anty sumy kin canza cikin watanni kadan,bakiga yadda kayan nan ke miki kyau ba,kamar ba sumyn malam ba,maman abdallah” anty dije na tayata
“Kin rigani a fili na rigaki a zuciya,ta koma wata qaramar baturiya,haskenki ne kadai ba qarasa nasu ba,inaga ma kafin mu koma fa kim saje da su,kayan sun amsheki” ita kanta ta sani amma sai ta saki dariya
“Ina wani kyau a kayan banasaren mutum anty,dadinta daya kawai basa fidda tsiraicin mutum” duk da haka bata bar hijabinta ba,don babu sutura mafi daraja a gunta irin hijabin,saidai duk sanda ta sanya kafin ta kai makarantar suna shan kallo ita fa zulaiha,har zulaihan kan ce
“Ke kuwa sumayya ki haqura mana”
“Babu abinda zai rabani da hijabi sai mutuwa,sai randa likkafani ya zama sutura ta ta qarshe” dariya zulaihan keyi
“Nima wasa nake miki”. +

       Wata baiwar qwaqwalwa Allah ya baiwa sumayyan,cikin wata biyu kacal harshenta ya fara juyewa,su kansu uncle farouq da anty dije mamaki suke,ganin tana ganewan ne ya sanya ya yanke shawarar sanyata wata makarantar dake training wa mata zamantakewar rayuwa,ciki harda nau’in girke girke na kowacce qasa,duk randa zakuyi girkin wata qasa tofa malamar ‘yar asalin qasar ce,makarantar akwai tsada don ko ita anty dije ta burgeta,ba don tayi tsada da yawa ba itama taso shiga,amma tunda ‘yarta ta samu tace ba komai ta dinga koya mata. 17

        Watansu biyu da daddare uncle farouq ya kwashesu suka fice suga gari karon farko tun bayan zuwa,don sam bai da lokacin zama a gida,awa biyu kacal sukayi suka dawo saboda yana da aikin da zaiyi,suna gab da shiga gidan ya tuna dawowar qanin abokinsa wanda gidansa ke daura da nasu,sunje ganin gida ne shi da matarsa sai shekaran jiya suka dawo,baki dayansu suka nufi gidan don a gaisa,anty dije ta riga data sansu dama,mai gidan na girmama uncle farouq kasancewarsa abokin yayansa.

       Gidane qarami kamar nasu,ga mamakin sumayya matar gida matashiya ce wadda kusan zasuyi sa’anni da ita,yaronta daya itama wanda ya kusa shekara hudu,nafisa asalin shuwa ce,tana aure da mijinta Dr auwal wanda qarin karatu ya kawoshi qasar,shekararsu biyu kenan,shekara biyu ya rage musu su koma gida,shekararsu hudu da aure,yaransu daya khalid wanda shima shekararsa hudun dai dai da shekarar aurensu,saidai har yanzu bata qara wata haihuwar ba,ita din ma karatu take,yanzu haka ta kusa hada degree dinta a fannin kasuwanci,abinda tafi sha’awa kenan tun tana yarinya,kusan gado tayi,sabida kasuwanci shine sana’ar mahafinta .
Ba qaramin dadi taji ba da ganin iyalan uncle farouq din,sai ta jita kamar a gida nijeria,nan kusa da su dama babu wani dan nijeria,duk a tsakiyar fararen fata ‘yan asalin qasar take,tun kafin su tafi ganin sumayya sa’a take a gunta ta dinga fadin
“Na samu ‘yar uwa”
“Lallai kam,wannan,ai sai kinyi da gaske nafisa,bata da son mutane,ga shegen qulafucin zaman gida,makaranta kadai ki fidda ta”
“Zamu saba ai ko sumayya,zaki zama qawata” ta fada tana kallonta,tashin farko taji sumayyan tayi mata,nutsuwarta ta burgeta,murmushi sumayyan tayi
“Insha Allah maman khalid”
“Kamar gaske” cewar anty dije
“Haba umman khalipha kada ki sage mana gwiwa mana” inji nafisan. +

        Sumayya kam ta gwada mata halinta,mutum ce mai yawan janye jiki ga baqin mutane,musamman wanda ta fuskanci rayuwa bata ajesu bigire guda ba,bata son sanya kanta inda zai zame mata matsala ko dana sani a gaba,ko kuma inda ya fi qarfinta,qwarya tabi qwarya haka nata ra’ayin yake,wanda ta gada ne daga wajen mahaifanta,mutane masu sanin daraja da qimar kansu,masu wadatar zuci da yakana,bata manta nasihan mama da kullum take gaya musu,kaso duniya mutane su qika,ka qi duniya mutane sai su soka,ka guji kwadayi,don shi din mabudin wahala ne,matuqar ka hau motar kwadayi to la shakka babu inda za’a saukeka sai tashar wulaqanci,mutunci yafi kudi,mutunci abu ne da idan ya zube qasa bai yiwuwa ka kwasheshi,mutunci abu ne da kudi ko wata isa basu iya siyanshi,ire iren wadan nan maganganu ke mata tasiri,takan zama mai tsantseni duk inda ta samu kanta,takan koma dora mutuncinta gaban komai nata. 1

        Nafisa ‘yar gata ce gaba da baya,itace auta a gidansu baya ga maza yayye da take da su guda hudu,ita daya ce diya mace qwal daya tilo da iyayenta suka haifa,hakan ya sanya take ganin gata,baya ga arziqi da Allah ya yiwa mahaifanta,nafisa irin mutanan nan ne masu son jama’a,sakin fuska da jan mutane a jiki,ko kadan ba zata taba yin wani aiki da zai nuna maka ga daga inda ta fito ba,saidai idan kai idanuwanka suka kai ka gani,tunda taga sumayya taji tayi mata,take jin ta samu ‘yar uwar data rasa a baya,duk da cewa tana da tarin qawaye amma sai taji sumayyan ta zame mata daban.
Tun sumayyan na janye jikinta har ta saki jiki,nafisan ita ta soma koya mata cumputer,ta naqalceta sosai,itama halayen nafisan sun burgeta,yadda ta tsammaci halin masu kudi duka guda ne ashe ba haka abun yake ba,taga misali daga kan nafisa da kuma amira,a yanzu haka amiran ko yaushe na kan kiran sumayyan,har tana mamakin bata ganin kudin da take qonewa wajen kiran nata?,kullum nafisan na kan qorafi da mitar yadda sumayya taki sakin jiki da ita bayan ta dauketa ‘yar uwa,kan hakan har tasowa sukayi takanas ita da mai gidanta suka zo suka kawowa uncle farouq qarar sumayya wai bata sonsu,wanda tilas hakan ya sanya ta soma sakin jiki da itan,shima mijin nata auwal da yake dan taya bera bari ne ya biye mata,akwai tsantsar qauna shaquwa da fahimtar juna tsakaninsa da matarshi,qauna ce mai yawa da tsafta tsakaninsu,wani lokaci idan sumayyan taje taga yadda ake zuba soyayya kunya kamata take,takan ce bari naje gida,bazan iya wannan badalar taku ba,dariya nafisa ke saki
“Wallahi sister(haka take ce mata)sai kin fini tsula tsiya,bari kiyi auren” kyabe baki sumayya keyi
“Wane aure,ai mu mun bar muku shi,mu da shi sai a qiyama” kalaman da sun jima suna daurewa nafisa kai,ga tsammaninta sumayyan budurwa ce bata taba aure ba,sau tayi yunqurin tambayarta sai kuna taja bakinta ta tsuke,ba kasafai take son yiwa mutum shishshigi cikin lamuransa ba,randa taga sumayyan na waya da abdallah a ranar ta kasa daure tarin tambayoyinta
“Ke wallahi baki isa ba,kullum ki sani a duhu ki gudu,to yau kam sai kin gayan wace ke” nafisan ta fada cikin yin kicin kicin,dariya tayi mata
“Wace kuwa ni din bayan sumayyan da kika sani” sakinta nafisan tayi tayi baya ta zauna
“Shikenan tunda haka kika ce,na fuskanci baki daukeni yadda ni na daukeki ba,inda kin daukeni yadda na daukeki da ba zaki boyen komai dangane da ke ba,tunda dan uwa bai boyewa dan uwansa sirrinsa,naga har shawara nake dake sumayya kuma ina ganin haske cikin dukkanin shawarar da kika bani” shiru tayi ganin yadda fuskan nafisan ta nuna rashin jin dadi qarara,babu shakka dukkan wata qauna ta fisabilillahi nafisan ta nuna mata,bata shayi ko shakkar yin kowacce shawara da ita,ajiyar zuciya ta saki
“Shikenam kiyi haquri mom khalid,yanzu ki bari naje gida na yiwa anty abincin dare kinga bata nan sun fita da uncle,amma na miki alqawarin idan na kammala zan dawo na baki labari na” sake hade rai tayi don ta nuna mata gaskiyan abinda take fada
“Na amince saidai da sharadin idan kinzo nan gidan zaki kwana,tunda kin sani yau dadyn khalid bai gida kwanan makaranta zaiyi” dariya sumayyan ta bushe da ita ganin yadda ta hade rai tana mata muzurai kamar wadda ta hadiyi kunama
“Idan anty ta barni zan kwana” 
“Zata ma barki saidai baki so ba” bata qara cewa komai ba ta miqawa khalid hannu dake kallonta,jira dama kawai yake tace su taho,wani shaquwa sukayi sosai da yaron,ganinsa take kamar abdallanta,ta sabi khalid din suka fice nafisa na binsu da kallo,murmushi ta saki tana jin dadi,jin sumayya take kamar ciki daya suka fito,Allah shike hada qauna da soyayya a tsakanin mutane har ma da jinsin dabbobi,haduwar jini wani abu ne na daban daga Allah. Tana zaune kan sofar dake dakin baccin nafisan sanye da nata kayan bacci cotton masu kauri riga da wando wadatattu,khalid na saman cinyarta yayi bacci,hannunta na saman sumar kanshi tana shafawa don bai jima da yin baccin ba,lokaci lokaci takan daga kai ta dubi nafisa dake tsaye gaban madubi tana ta faman shafe shafe da goge goge bayan fitowarta daga wanka,mamaki duka ya cikata bacci akewa wannan hidima haka,gaskiya mana ko yaushe fatar nafisan kamar ta dan jariri,duk da fara bace choculet ce,har haqurin sumayyan ya qare ta tanka
“Wai duka wannan wankan naki meye amfaninshi bayab wanda ake mawa baya nan mrs auwal kamar zaki sauya fata?” Murmushu tayi tare da ajiye body mist da ta fesa ta dubi sumayyan
“Au sai noor yana nan sannan zanyi haka,ai ya riga da ya zame min al’ada ta”
“To ai saiki bada himma,nikam na fara jin bacci,ina jin labarin nan bai yiwuwa sai gobe” ta fada tana gyarawa khalid kwanciya saman gado,da sauri ta zura ‘yar saman rigar baccin nata ta qaraso inda sumayyan take itama ta haye gadon tana cewa
“Sorry,na kammala,kema dab kike daki fara wannan sanaben ai” baki ta kama
“Niii,rufan asiri,ku din dai sai kuyita yi,haka naga laila ma ‘yar qwailarta da ita ta fara daukan course” dariya nafisa tayi
“Wallahi da gaske nake,jiya na hau internet,naga D&G sunyo sabbin mai na gyaran fatar fararen mata,set ne harfa perfume,sure,da subulunshi,na riga ma da na siya miki,jiran isowarsa kawai zamuyi,a yadda suka ce gobe zasu kawo min” shiru tayi tana saurarenta,wannan wace irin qauna nafisan ke mata haka?,daga ganin abu babu wanda ta tuna sai ita din?
“Am ready fa,ke nake jira” ta katsewa sumayyan tunani tana dubanta. 1

       Gyara zamanta tayi bayan ta jingina jikinta da bango,a hankali ta soma warware mata wace ce ita,babu abinda ta boye mata,sumayya kuka nafisa kuka,babu wanda zai rarrashi wani,bala’in tausayin sumayyan ya kama zuciyar nafisa,yayin da sumayya ta tsokano wani danqararren tabo da dama har yau bai ida warkewa ba,janyo sumayya tayi ta kifa kanta saman cinyar nafisan tana ci gaba da kukan tana bubbuga bayan itama tana tayata ba tare da ta tsaidata ba,cikin zuciyarta taba cike fal da mamakin irin rayuwar da sumayya tayi,bata taba hasashen zata iya yin rayuwa irin wannan ba,shi qunci da matsin rayuwa gami da QADDARA hadi da JARRABAWA kenan babu ruwansu da girma ko qanqantar shekaru?. 1

        Sai da zuciyarta ta samu salama sannan nafisa ta soma magana
“Ashe akwai irin wannan rayuwar a duniya?,rayuwar da mutum mai kimanin shekaru kwatankwacin nawa zaya fuskanceta da tsanani har kamar haka?,na jinjina miki sumayya,Allah ne kadai yasan me ya tanadarwa rayuwarki,irin wannan yarda da qaddara da karbarta hannu bibbiyu bau tashi a banza,Allah ya jiqan mukhtar ya raya mana abdallah,kici gaba da haquri,amma kada ki sake hasashen ba zaki sake yin aure ko jin dadin rayuwarki ba,kin sani kowanne bawa da yadda Allah ya tsara masa zai rayu,dole kowa ya rayu bisa tsari da doron da mahalicci ya QADDARA,kici gaba da addu’a,zan tayaki da yardar mai duka,yayi miki zabin kyakkyawar rayuwa,ya cire dukkan qunci da damuwa da kika taba tsintar zuciyarki a ciki”,ta jima tana fidda hawaye masu dumi wadanda suka dinga wanko zafi da radadin dake cikin zuciyarta maganganu ta dinga bata masu kwantar da hankali har ta samu nutsuwa cikin zuciyarta. 1

        Washe gari ta tashi fuskarta ta dan tasa saboda kukan data raba dare jiya tana yi,baki daya nafisa sai ta damu tana ganin kaman laifinta ne,murmushi sumayyan ta dinga tana girgiza kai tana qoqarin nuna mata ba laifinta bane,dole ne ga duk mutumin da yake da miki cikin rayuwarsa ya koka duk sanda wannan ciwon ya motsa.

Advertisements

_____

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 29

Advertisements _____ QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 29 Shuru amiran tayi tana duban sumayya cike da qwarin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *