QADDARAR SUMAYYA CHAPTER 26

QADDARAR SUMAYYA

CHAPTER 26
Cikin kwana daya tal amma ji take duniyar ta mata daurin huhun goro,babu abinda qwaqwalwarta keyi sai bitar rayuwarta da mukhtar,idanunta sunqi dakatawa da zubda hawaye dai dai da second d’aya,cikin kwana gudan tal ta rame ta fige ta fita hayyacinta,ba ta cewa uffan sai ido kawai,ko gaisuwa aka yi mata saidai ta amsa da ka,daga jiyan zuwa yau babu abinda ta kai bakinta illa ruwa da take kurba lokaci zuwa lokaci idan an matsa mata,sam abincin bai iya wucewa ta maqogaronta balle ya kai ga uwar hanjinta,a washegarin ranar anty dije ta iso hankali tashe,sai sabon kuka ya balle tsakaninsu,ba qaramin tausayawa sumayya take ba,yarinya qarama amma taga jarabtar rayuwa iri iri,da qyar aka sha kansu. +
      Bayan sallar la’asar tana saman abun sallah tana lazumi cikin dakin gadonta,anty salma ya yahanasu antu dije da mama ne zaune a dakin sai ita ta biyar,sai yaran ‘yan uwa dake gefe suna wasa,idanuwanta da hankalinta na kansu
“Abdallah” sunan da ya fado kanta kenan,cak ta tsaya da lazumin tana lissafin ina abdallah yake?,bata ga abdallah ba duk cikin kai komon yata,haka bata ganshi gaban gawar mukhtar ba
“Ina Abdallah” lokaci na farko da tayi magana tun bayan tsawon awanni kusan talatin,dif dakin sukayi don babu mai amsar bata,tuni hawaye ya cika idanuwan anty dije ta sanya mayafinya ta soma sharewa,mama tafi kowa shiga cikin taraddadi,don ba’ayi minti goma ba malam ya kirata yace suna gun ‘yan sanda,sumayyan dai bata yi maganar sa ba ko?tace masa eh
“Ina abdallah yake?” Ta kuma tambaya wannan karon tana dubansu hawaye na bin kuncinta
“Don Allah kuce min wani abu kunyi shiru,ko shima ya mutu ne?,shima yabi sahun mukhtar?,ku daina boyemin ku gaya min don Allah”
“Abdallah na nan a raye bai mutu ba,kiyi haquri kinji sumayya” inji yaya yahanasu ta fada tana share hawaye,murmushi mai dauke da hawaye tayi wanda ya sanyasu yin jagale suna kallonta
“Meye na boyemin idan shima ya mutun,ban isa nayi komai ba saidai nayi haquri,ku fadan don Allah na sashi cikin addu’ata idan har ya mutun” mama ce cikin hawaye ta taso ta iso gabanta ta soma share mata qwallar
“Haka ne sumayya,kiyi haquri kan wanda kika yi,a iya binciken da jami’an tsaro sukayi abdallah bai mutu ba,saidai ya bata an rasashi ba’a san inda yake ba,amma in sha Allahu ana gab da samunsa ‘yan sanda na nan suna bincike kan inda yake” shiru sumayyan tayi tana duban maman,sai ta sake qas da kanta bata sake cewa komai ba sai taci gaba da jan carbinta,ta riga ta sallama abdallah ya riga ya tafi kamar yadda mukhtar ya tafi ya barta,kasa zama anty dije tayi sai ta miqe ta fice tana hawaye,ba’a yi sallar magariba ba wani zazzafan zazzabi ya rufeta.
      Zazzabin shi yaci gaba da jigata ta da wahal da ita tsahon kwanaki biyu har ranar sadakar bakwai,qarin ruwa kam ta shashi har ta godewa Allahi,idan ka ganta baka cewa itace sumayya,ita kadai tasan me take ji a gangar jikinta da zuciyarta,ta riga data sallamawa rayuwa baki daya.
     *****   *******  *****
     Zaune take a falon gidan sanye da hijabi da carbi,idarwarta kenan daga sallar walha,gidan ba kowa sai yaya yahanasu wadda ke zuwa kullum ta wuni ta tafi anty dije halima da matar kawun abdur rahman,tun shekaran jiya da akayi sadakar bakwai kowa ya watse aka barta da su.
     Anty salma ce ta fito daga kitchen dauke da cup ta qaraso inda sumayya ke zaune
“Ungo ai kin idar da sallar karbi kisha” kai ta gigirza hawaye fal idanuwanta
“Bazan iya sha ba anty salma,babu dadi,tsayamin yake a wuya”

“Haba sumayya,haba sumayya,ana yabonki sallah kuma ya haka,kowa na yabawa tawakkalin da kikayi,akwai ciwo rashin miji da batan da’a,amma kinsan babu yadda za’ayi rayuwa ta yiwu ba abinci,tunda abun nan ya faru baki sake sanya abu cikinki ba,mu kanmu da muke tare da ke kinsan ba zamu ji dadi ba,daure ki karba kisha don Allah ko kurba uku ce” hawaye na bin kuncinta ta karba ta kafa kai tare da rintse ido kamar wadda zata sha guba,kurba uku tayi masa ta dire kofin tana maida numfashi,dai dai lokacin da aka yi sallama bakin qofar falon amsawa sukayi halima ta duba tace ‘yan sanda ne,anty dije tace eh abban laila ne ya turosu su shigo suke bincike kan batan abdallah da musabbabin hadarin mukhtar,gaban sumayya yayi mummunan faduwa idanuwanta kan qofar falon har suka shigo,suka samu gu suka zauna,tambayoyi suka yiwa sumayyan suna saurarenta har ta gama,daya daga cikinsu wanda da alama shine babbansu ya fiddo wata leda wadda kana iya hango abinda ke ciki ya miqo musu
“Kince gab da lokacin da abin zai faru kunyi waya,munga komai nashi cikin motar saidai bamu ga wayar tasa ba,ko akwai wanda yayi kiran lambarsa tun bayan rasuwar?” Anty yahanasu dake zaune gefe tace
“Gsky a’ah”
“Ok,ko zamu iya samun lambar wayar tasa?”
“Eh” anty dije tace,ita ta karanta masu lambobin yana rubutawa,ya kammala rubutawa sannan ya latsa kiran,cikin second uku kiran ya shiga,tsit dakin yayi kamar babu wani mai numfashi suna sauraren shigan kiran wayar
“Waye me magana” wata murya ta fada daga can bangaren
“Am,mukhtar nake nema don Allah” wata dariya aka saki wadda cika falon kasancewar a hands-free ya sakata
“Ai mukhtar ya dade da wulawa barzahu,idan ma qarin bayani ake nema bari nayi maka,mun kashe mukhtar,hakanan d’ansa yana hannunmu mun daukeshi,zamuyi masa irin tarbiyyar da muka ga dama mu kuma moreshi sannan mu aikashi inda babansa ya tafi,na tabbata wannan ya ishi babbarsa itama tabi sahunsu” qit aka katse kiran,salati suka dauka baki dayansu,basu ankara ba sai ganin sumayya sukayi ta sulale a gurin,tashin hankali sabo,a rude baki dayansu sukayi kanta. 2
      A hankali ta bude idanuwanta tana fadin
“Allahumma la sahla illa ma ja’altahu sahla,wa anta taj’alik hazna iza shi’ita sahla” idanunta ya sauka cikin falon,wannan karon mutane sun dadu sabanin dazu,malam ya abbakar kawu da mijin anty dije wato umar farouq duka suna cikin falon,sai ta sanya kuka tana kiran sunan Allah,tausayinta ya kama kowa,wannan karon babu wanda ya hanata,don sunsan cewa abun ya mata yawa,dole ta zubda hawaye ko zata samu sauqin radadin dake cikin zuciyarta,a qalla kimanin minti goma tana kukan mai fidda sauti kafin ta koma yin na zuci,sai a sannan ‘yan sandam suka samu damar yin magana,wanda yayi magana dazun wannan karon ma shi ya maganta
“Alhamdulillahi mun gode Allah,ba shakka wannan bincike ya zo mana cikin sauqi,cikin ikon Allah sun sauqaqa mana wahalar bincike”
Haka nace cikin zuciyata ASP,yanzu me kake ganin za’ayi,don ya kamata cikin gaggawa a nemo yaron kada  su samu nasarar cutar da rayuwarsa” cewar mijin anty dije cikin tsananin takaici da zaquwa
“Hakane alhj farouq,ina ganin zamuyi amfani da hikimar tracing layin har don mu gano indo suke”
“Good,hakan yayi,kamar zuwa yaushe kenan ?”alh farouq ya sake fada
” daga yau zuwa gobe in sha Allahu zamu aiwatar da komai”
“Na gode ASP,na gode qwarai” alhj farouq ya fada yana bawa ASP hannu,sukayi sallama daga nan suka fice. +
     Hankalinsa ya maida ga su malam
“Malam,sai mu dage da addu’a,Allah ya bada nasara a gano ko su waye,ba shakka idan aka ganosu ba zamu qyalesu ba,sai mun bi haqqin ran mukhtar da yardar Allah….sumayya saiki qara haquri,Allah ya baki juriya ya baki ladan haqurin da kikeyi”. Godiya sosai su malam ya yiwa farouq gajin yadda yayi uwa yayi makarbiya kan lamarin,bai gari ma sanda abun ya faru amma ya dawo ya karbi ragamar al’amarin,a nan sukayi sallar azahar sannan suka tafi bayan ban baki da suka sake yiwa sumayyan.
A hankali jerin gwanon motocin jami’an tsaron suka dinga kutsa kai cikin hanyar don baza’a kirata layi ba,saboda sabuwar unguwa ce wadda ba’a kammala ginin nikan dake cikinta ba balle a samu sukunin gabe layuka,kana iya bi ta ko ina,cikin gonaki ko filayen dake daura da wajen wucewarka,motar dake gaba mutumin dake kusa da mazaunin direba wanda shine shugaban ‘yan sanda shi ya dauki wata waya da jami’an tsaro suke magana don bada umarni zuwa sasanni dabaj daban ya kara a bakinsa yana bada sanarwa ga sauran motocin dake biye da su a baya a kan su kashe jiniya,sannan ko wannensu ya shrya don suna gab da qarasawa gidan da na’ura ta musu nuni cewa a wannan gun layin wayar mukhtar ke aiki. +

      Sosai suka dinga rage gudu har suka qaraso daura da gidan inda suka faka motocinsu,ogan nasu ya sauka ya bawa kowanne umarni kan inda zai tsaya,kafin wani dan lokaci sun zagaye gidan baki dayansa,daya daga cikinsu wanda ke sanye da kayan gida saidai akwai qaramar bindiga boye a aljihunsa ya nufi qofar gidan kai tsaye,yayi bugu kusan sau goma kafin ya jiyo wata kakkausar murya na tambayar wane,nine yace aka sake maimaitawa da cewa kai wane
“Gun oga nazo,idan na baza’a bude ba ai harkar ba dole bace sai na koma akwai masu jira na”ya fada cikin zafi zafi
” bari na sanar masa”mai maganar yace yana mai juyawa zuwa cikin gidan,a falon gidan ya samesu harda ZAINAB dake zaune tana dakon zuwan mutumin da zata saidawa abdallah da shi,wanda abdallah ke zaune gefe daya a falon cikin kashi da fitsari,kwanukan da yake cin abinci da su suma sun gauraya cikin qazantar,yana sanarmusu baqo yazo oga ya bada umarni a bude masa ga zatonsu mao siyan yaron ne yazo.
      Yana kammala bude qofar yayi caraf ya damqeshi,bindiga ya nuna masa saitin kansa yana cewa
“Duk wani motsi da zaka yi wanda zai alamtawa abokan aikinka akwai matsala dai dai yake da harba alburushi cikin kwanyarka,muje ka nuna mana inda suke” kai ya kada idanuwa a warwaje kamar an shaqe mujiya,alama ya yiwa sauran jami’an tsaron da zasu shiga ciki suka biyo bayansu.
       Kusan su biyar ne a falon,ganin an taso dan uwansu da bindiga ya sanyasu saita tasu
“Ku ajjiye makamanku,idan ba haka ba ku baqunci lahira” cewar wani gabjejen dan sanda cikin kakkausar murya,da fari sun so suyi gardama,amma daga bisani da suka ga yawan jami’an tsaron ya sanya su ajjiye makaman nasu aka tattarasu gu daya sannan aka fara aikin daure musu hannayensu don yin gaba da su.
      Tuni cikin zainab ya duri ruwa,ta tabbatar cewa matuqar batayi wani abu da zata wanke kanta ba tun anan babu shakka tata ta qare,saboda haka tayi hanzari ta faki idanuwansu ta zagaya inda abdallah ke zaune cikim qazanta yana kallon kowa ta kunceshi ta qanqameshi a jikinta duk wari da zarnin da take shaqa ta hadiyeshi,sai ta saki kuka mai gunji tana fadin Allah na gode maka da ka kubutar da mu daga hannun wadan nan azzaluman,Allah abin godiya” kukan nata na qarya yaja hankalinsu,wannan kakkauran dan sandan daya gama qullesu ya kalleta yana zare ido,cikin daga tsawa yace
“Kefa?,daga ina?”ance mara gaskiya ko cikin ruwa gumi yake,take jikinta ya kama rawa cikin rawar murya tace
” nice….nice uwar dannan,sato mu sukayi”baki dayansu ‘yan sanda suka zuba mata ido,kowa dai yasan case din rasa abdallah,hakanan sunsan uwa da ubanshi,to ita wannan din wace da zata ce uwarsa ce
“Wallahi qarya take yallabai,ita ta bamu kwangilar kashe…….” Wanda ya bude musu qofa wanda da alama duk ya fisu tsoro ya fara rattabo bayani cikin rawar jiki
“Qarya ne sharri zai min” zainab ta fada cikin daga murya tare da yunqurin hanashi tona mata asiri,take sai musu yaso ya balle tsakaninta da shi,shi yana son bayyanawa ita tana son hanawa,yayin da ogan nasu haushin zainab ya tsaya masa a wuya,ya tabbatar koma meye wannan kama sun yana da alaqa da aikinta da suka aiwatar mata,ji yake ina ma bai ya da bindigarsa ba,da babu shakka sai ya fasa mata kai da harsashi a take,amma babu komai,idan kere na yawo zabo na yawo zasu hade,tsawa shugan ‘yan sandan ya buga musu wadda ta sanyasu yin tsit
“Lawan,dauke abdallah,idris ka sanya mata ankwa itama,ko meye ma ya kawota nan din muje bincike zai nuna” ya fada yana ficewa tare da yi musu umarnin su tafi,zainab na zare ido na komai aka buga mata ankwa aka hadata da tsagerun aka tura cikin mota,sun fara tafiya kenan ogan ya faki idon dan sandan dake tsare da su ya daga kafceceyar qafarsa ya daki ta zainab cike da jin haushinta da ganin ta jaza musu masifa,ji kake qasssssss zainab din ta saki wata razananniyar qara ta sume,shugaban ‘yan sanda shi yace aci gaba da tafiya kada a tsaya idan anje station a mata duk taimakon da za’ayi,yayin da yasa suka qara dora kula a kan oga don gudun kada ya subuce musu.
Tun safe da taga fitar malam alhj farouq da kawu hankalinta ya kasa kwanciya,duk da cikin damuwa take sai damuwar tata ta ninka ta da,jan carbi take wanda shi ya zamo mata abokin hirarta tana share hawaye,har aka yi sallar la’asar babu labarinsu,abunda ta kula da shi shine lokaci lokaci anty dije na daga waya tana kiran mai gidanta,saidai babu wanda ta tambaya kamar yadda babu wanda ya yimata bayani. +
      Cikin dakinta tayi sallar magariba tana jiran isha’i,ta zurfafa a cikin tunani anty dije ta shigo
“Kizo inji su malam”
“To” ta fada ba tare da ta iya motsawa ba,gabanta ne ya tsananta faduwa,zuciyarta ta ta cire tsammani ,wala’alla ba’a samu nasara ba,wala’alla ta rasa abdallanta kamar yadda ta rasa mahaifinsa,shikenan haka Allah ya tsarama rayuwarta,sai ta kife kanta jikin gado ta saki kuka
“A’ah,subhanallahi sumayya kuka dai?,ke da nace kije su malam da abban laila(alhj farouq)na jiranki,tashi don Allah ki bar kukan nan haka” anty dije ta fada tana qoqarin dagata,ita ta dafa don ba cin abinci take ba balle ta samu qwarin jikinta a haka har suka isa falon. 1
     Bata san ta saki anty dije ba,bata san kan qafafunta take tafiya ba sai data isa gaban abdallah ta zube wanda ke kan cinyar ya abbakar,wani sabon kuka ta saki tana yunqurin daukar yaron ganin yadda ya sauya cikin kwanakin da basu wuce goma ba,yayi baqi ya rame goshinsa har da ciwo,a haka ma sai da aka kaishi wajen mama tayi masa wanka ta bashi abinci yaci aka sauya masa sababbin kaya,qanqameshi tayi tana sake sakin kuka mai cin rai,kowa tausaya mata yake tare dayi mata kyakkyawar addu’ar yankewar qaddarorinta haka nan,a hankali alhj farouq ke bayani
“Alhamdulillahi an kama Abdallah tare da wasu wadanda babu shakka su sukayi sanadin mutuwar mukhtar kamar yadda sukayi iqirari da kansu,tunda an kamasu da wadansu abubuwa dake sake bayyanar da hakanne,cikin wadanda aka kama harda wata ZAINAB wadda da fari ta musu iqirarin cewa itace mahaifiyarsa” da sauri sumayya ta dago kai tana maimaita zainab cikin ranta gabanta na ci gaba da faduwa,alhj farouq ya dora
Amma abinda su yaran suka ce shine ita ta dauki ta basu aikin kashe mukhtar,sannan daga bisani da taga ba zata iya biyansu sauran kudin ba ta sauya shawarar daukar abdallah ta tafi neman kudi da shi,taga gwara su saida abdallah ta biya kudin sauran tayi harkar gabanta” ba sumayya ba wannan karon,baki daya jama’ar dake falon ba qaramin girgiza sukayi ba,wannan waccw iriyar masifa ce,tamkar ba diyar musulmi ba,tamkar babu digon musulunci a jikinta,wannan karon cak kukan sumayya ya tsaya,sunayen Allah ta dinga kira,tsoron zainab na kamata kamar tana wajen,kisa zainab,kisa?,kisan mukhtar?,daga bisani wani hawayen ya sake subuce mata,har ta gaji da kuka haka nan,ko da yaushe idanunta zafi suke mata saboda kuka,har wani lokaci take gani hatsa hatsa,sai ta rufe idonta tana godewa Allah daya QADDARA mata sake rayuwa da d’anta,ya kubutar mata da d’anta cikin aminci da salama,bata san da wanne baki zata godewa uncle mukhtar mijin anty dije ba,ta sake jinjina masa da yadda yayi zumunci irin haka sanda taji yana fadin idan aka kammala bincike cikin ‘yan watanni qalilan insha Allah za’a soma shari’a,don dole abi kadin haqqin rai a kuma hukunta duk wanda ke da hannu cikin lamarin,tabbas babu shakka indai har da zainab cikin wadanda suka aikata wannan aiki mutum ya zama abun tsoro,to idan babu sa hannunta shin me ya kaita wajen?,har tana iqirarin abdallah danta ne?,ita ce mamarsa?
“Ya Allah ka yimin gata,ka shigemin gaba,ka yimin jagora cikin al’amuran rayuwa ta” abinda ta dinga fadi kenan tana maimaitawa rungume da abdallah a jikinta,shi kansa yaron kallonta yake tayi yana kiran ammi lokaci zuwa lokaci,haka yayi luf a jikinta jikinsa a sanyaye yana jin dumin mahaifiyarsa.
*GIDAN LUKMAN* +
      Baki daya rayuwar gidan ta yiwa karima baqi,kusan ita kadai ke rayuwarta cikin gidan,yaran baki daya sun kwashe kayansu sunyi qaura zuwa bangaren hajiya,tsakaminta da su kallo daga nesa,suna dai shigowa su gaidata su kuma tambayeta mai zasuyi mata na aiki,hakanan duk abinda tace suyi matuqar bai sabawa addini ko al’ada ba hajiyan na umartarsu suyi mata,lukman kam tunda ya hada kayansa yayi tafiya zuwa legos tsawon watanni rabonsa da gida,saidai yakan kira wayar hajiya wanda ya siya ya ajjiye musu a bangaren hajiya,yana kira suyi hira da yaran ya kuma gaisa da hajiyan,sau tari idan tace ba zai dawo ba haquri yake bata,yace sam yaji gidan ya fice masa ne a rai tunda sumayya ta bar gidan,hakanan yana zama yana bata ran hajiyan,amma tayi haquri lokaci ne idan yayi zai dawo,sam karima bata san ya sauya lamba ba saidai idan ta kira tayi ta jin is switch off,hakanan a yanzu ba zata iya cewa ga inda lukman din yake ba,sai dai lokaci lokaci tana jin alert na transper din kudi daga account dinsa zuwa naga,kudin buqatunta na yau da kullum,sannu a hankali hankalinta ya fara tashi,wannan karon saboda rashin lukman din a kusa bata da isashshen kudi gunta da zata koma wajen malaminta. 1
   ********  *****  ********
    Sannu a hankali rayuwa ta dinga juyawa,kwanakin takabarta na raguwa,ta fawwalawa Allah lamarinta baki daya,hakanan ta karbi QADDARArta hannu bibbiyu,saidai ba’a raba zuciya da tuna abubuwa masu d’aci da suka gabatar mata,yanayin sumayya ya sauya baki daya,ta sake zama mai yawan shiru shiru,sai kallo da idanuwa,har yau jikinta ya kasa komawa dai dai,ta rame,sai uban fari data sake yi sanadiyyar ramar da tayi,anty dije ta koma sai ita a gidan da zainab da halima,su kawu sukace ta zauna tayi iddarta a dakinta don haka addinin musulunci yafi so,lokaci lokaci ya abbakar da matarsa da suke kira anty sukan leqosu.
Ranar wata asabar wanda ya kama wata biyu da rasuwar mukhtar alhj farouq ya iso kano,cikin falon sumayya suke zaune kamar yadda suka saba idan zama irin wannan ya kamasu,bayan gaishe gaishe da qarin wani jajen alhj farouq ya soma gabatar da maganar data tarasu
“Bayan dukkan wani bincike da jami’an tsaro suka gabatar ya bayyana cewa zainab ita ta dauki nauyi ta kuma bada umarnin kisan mukhtar” duk sa suna zargin hakan amma sai da maganar ta sake razanasu,kuka yaya yahanasu ta sanya tana salati da kalmar shahada tare da ambatar sunan zainab,alhaj farouq bai kula ba ya dora
“Ta bayyana dalilinta na yin hakan da cewa bacin ran wulaqancin da mukhtar ya mata ne na saki uku kuma yaqi maidata bayan kaahe kudaden da tayi wajen bin malamai amma babu nasara,qarshe ma ya bita da dukan kawo wuqa,daga bisani kuma ta tsinci labarin ya maida aurensa da sumayya bayan ita ta kamu da cuta mai karya garkuwar jiki ta sanadinsa,tunda taga haka ta tabbatar bazai mayar da ita ba,sai taga gwara ayi biyu babu kowa ya rasa,baya ga haka dama tana jin haushin sumayya na tsallake rijiya da baya da tayi har ta haifi abdallah”alhj farouq ya saurara yana maida numfashi cike da bacin rai,ji yake kamar ya shaqe zainab a lokacin da take wannan bayanin,tun asali shi mutum ne mai tausayi da jin qai,baya qaunar zalunci sam a rayuwarsa
“La ilaha illa anta,yanzu sakayyar da zainab kika yi mana kenan,ashe kece ajalin muntari?” Yaya yahanasu ta fada tana sakin kuka mai qarfi har da sheshsheqa,tana jin cewa itace da alhakin mutuwar mukhtar,durqushewa tayi sannan ta ja jikinta da qyar ta isa gaban sumayya wadda abdallah ke zaune a kan cinyarta tana dubansh,idanuwanta sun gaji da kuka sai na zuci take wanda yafi ciwo
“Sumayya,don girman Allah,don darajar ma’aiki da iyayenki ki yafemin,babu shakka ina ji a raina nice sikar ajalin muntari,Allah ya bawa muntari mace ta gari,ta daga hankalina na hanaku zaman lpy don kawai baki samu abinda Allah ne kadai ke da ikon bawa bawa ba,na yi masa aure na farko suka rabu bai isheni ishara ba,na sake dauko masa wata na tsaya kai da fata sai da ya kawota cikin rayuwarku,ashe ita ce ajalinsa,itace silar tarwatsa rayuwarku,nayi gaggawa na shiga hurumin ubangiji,idan da na haqura ashe akwai rabon mukhtar bazai taba barin duniya ba sai ya haifi abdullahi,sumayya ki yafemin,kimin afuwa,wallahi na tabbatar idan baki yafemin ba haqqinki bazai taba barina cikin rayuwa ba…..” Sai ta kasa qarasa abinda take da niyyar cewa muryarta ta sarqe kamar idanuwanta zash tsiyaye saboda kuka.
Dubanta sumayya keyi kawai,ita yanzu a rayuwa me ya rage mata?,me zai bata mata rai?,mene ribar taqi yafewa yaya yahanasun tunda mai afkuwa ta afku,babu mai goge abinda ya faru,idan ta qullaceta mai hakan zai maganta mata?,koba komai taci darajar mutum biyu MUKHTAR da ABDALLAH
“Allah ya yafe mana baki dayanmu” abinda ta fada cikin raunin murya,babu wanda hakan bai burgeshi ba,godiya ta dinga jerawa sumayyan tare da binta da kyawawan addu’o’i sannan ta juya ga malam
“Malam kaima ina neman afuwarka,abinda na yiwa diyarku da kuka bamu ita cikin aminci da amana tun tana shekara sha uku amma naci amana,na bada gudun mawa wajen mutuwar mijint….” Nan ma kasa qarasawar tayi saboda yadda lamarin ke mata ciwo cikin zuciyarta
“Ya isa yahanasu,babu mai rayawa ko kashewa sai ubangiji,komai akwai sanadiyya amma kuma Allah ya riga ya tsara komai,abinda ake so ga bawa dama shine,a duk sanda ya fahimci yayi wani kuskure to ya nemi afuwa ya kuma guji aikata laifin a gaba,Allah ya bamu dacewa baki daya”
“Amin ya Allah,amin” duka suka amsa,sumayya ta miqe don komawa ciki,haka take bata son zama cikin jama’a balle tayi doguwar magana,a nan alhj farouq ya sanar musu cewa ranar litinin za’a miqa zainab da sauran yaran kotu,amma basai sumayyan taje ba insha Allahu tunda sun amsa laifinsu ba wata doguwar shari’a za’ayi ba. +
    *******   ******   ********
     Kwana goma ya rage mata ta kammala takabarta aka gama shari’ar wadda ta dauki wata biyu ana yinta,bincike ya nuna zainab na da hannu dumu dumu wajen mutuwar mukhtar,ita ta biyasu suka kunce tayar motar mukhtar a sanda yake shagon dinki zai amso kayan dinkin sa,yayin da yaran data dauka aiki anjima ana nemansu,irin mutanen da ake hayarsu ne suyi kisa,sun kashe mutane da dama hakan ya sanya aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya,zainab kuwa aka yanke mata hukuncin daurin rai da rai,aka fara wucewa da ita asibiti,sabida a lokacin cuta mai karya garkuwar jikin dake jikinta ta fara mata tasiri,zaman gidan kurkuku da tayi ba tare data fara shan magani ba ya sata bayyana lokaci guda,alamominta duk sun gama bayyana,sannan qafarta da oga ya daka ta karye aka mata dori dorin baiyi kyau ba,don da aka kwance gun har ya fara ruwa yana neman lalacewa……
  ******     ******    *******
Ranar da ta kammala takabarta a washegari malam yace su dawo gida,kawun abdur rahman shi ya nemi alfarma gun malam din yayi haquri a gama tattara dukiyoyin muntari a raba gado,shikam yace babu komai duk abinda suka zartas dai dai ne amma kawun yace a masa alfarmar dai,cikin qanqanin lokaci aka kammala hada komai na mukhtar din,aka raba gadon kamar yadda ubangiji ya tsara,kusan dukiyar baki daya abdallah ya cinyeta kasancewarsa d’a namiji qwaya daya tal wajen mahaifinsa,kawu ya tattaro dukiyar baki daya ya kawo gaban malam,sam malam yace yaje ya riqe ya kula da ita amma qememe kawun yaqi,daga qarshe suka yanke shawara aka danqawa ya abubakar ya juya masa cikin kasuwancinsa da yake na saida atamfofi,addu’a sosai suka yiwa abubakar din kan Allah ha tayashi riqo +
     *SABUWAR RAYUWA*
     A kullum ta kebe kanta ita daya tunani take yi yaya rayuwa zata kaya mata?,meyw kuma kundin qaddararta na gaba?,wanne shafi kundin zai bude mata kuma?,amma a zahiri ta saki jikinta ko don yadda ‘yan uwa da iyayenta suka damu da ita,burin kowannansu ya faranta mata ya sanyata dariya,kowa tausayinta yake,tana ganin bai kyautu ba taci gaba da zama cikin damuwa har ta sanya wasu,mukhtar dai ya riga ya tafi ba kuma zai taba dawowa ba har abada duk kuwa yadda take qaunarsa,qauna daya ce tsakaninsu kada ta manta da yi masa addu’a,hakan yasa ta rungumi rayuwarta ta kuma rungumi danta,a lokacin cikin kudinta na tumunin takaba ya abbakar ya ware mata wani abu yace ta fara sana’a,dama can sumayya ta iya sana’arta,saboda haka babu bata lokaci ta shiga kasuwar kurmi ta saro kayan humta turaren wuta na daki kaya dana tsugunno sai kwalakca ta koma tsohuwar sana’arta,mutum ce ita mai nasibin sana’a,duk abinda ta sanya kanta ta fara saidawa sai Allah ya kama mata,cikin ikon Allah kuwa sai wannan karon abun nata ya sake bunqasa,cikin abokan ya abbakar akwai mutum uku da iyayen gidansh ke da supermarket,suka buqaci ta kawo su gwada cikin shagon,ta samu kwalabe masu kyau da tsari ta zuba,ba’ayi sati ba suka qare suka kawo mata kudinta suja sake nemam wasu,cikin lokaci qanqani abun ya habaka,sai ta sanya halima da zainab ciki sukeyi tare,tunda ta aikama anty dije itama take karba ta amfanin gida,wani lokaci ta saida ko tayi kyauta.
      Sana’ar da take yi ta dauke hankalinta sosai,ta rage mata zaman tunani da kuka,saidai duk da haka babu wani abu da ya ragu na tunanin mukhtar cikin ranta,hakanan duk dare kafin bacci ya dauketa sai tayi kuka mai isarta.
   ******    *****   ********
    *_Bayan shekara daya_*
     Koda kwana daya ne ya ratsa cikin rayuwar bawa ta iya yiwuwa kaga sauyi tattare da rayuwar nan tasa,walau a sarari ko a boye,hakan ce ta kasance ga rayuwar gidan su sumayya,wanda a wannan shekara guda din an sauya fasalin gidansu san sake musu gini mai kyau da tsari cikin ribar kudin abdallah sumayya tasa aka yi wannan aiki,sun sake samun rufin asiri sosai,babu abinda ta nema a rayuwarta ta rasa,ci da sha da sutura baki daya,don har taimako takanyi cikin ribar sana’arta wanda bai gaza dubu hudu zuwa qasa ba,an kawo kudin auren zainab wanda ba’a sanya rana ba ana jira zuwa wani lokaci kafin na halima ya gama shiryawa kamar yadda yace a bashi lokaci.
  *****   **********   ******
Sanye take da dogon hijabi mai hannu wanda har jan qasa yake,qafarta na sanye da safa sai niqabi daure a fuskarta,wannan itace shigar data koma yi tun randa ta taba fita wani ya biyota ta yiwa kanta alqawarin canza shiga,duk da dama can ma’abociyar sanya hijabi ce,daga ranar ta bada kudi aka dinka mata su kaloli masu kyau har kala biyar,ko ina zata su take sanyawa duk tsadar suturar dake jikinta,ko yaushe kar suke a goge cikin tsafta da qamshi,shigar na matuqar yi mata kyau qara mata kwarjini da kuma boye kyawun sufarta baki daya,dawowarsu kenan daga gidan anty salma ita da halima ta kai mata humra da turaren wutar da ta yiwa wata amarya da za’a yiwa aure ‘yar maqotanta,daga nan ta tsaya aka musu lalle ita da haliman bayan ta shiga kasuwa ta sayi kayan humra,saboda anty dije tace sati na sama tana nan zuwa kano,har tana tsokanarta da ita zata koma abuja don ta fuskanci bata qaunar zuwa abujan ko kadan,dariya sumayyan ta dinga yi tana tsokanar anty dijen itama da cewa zaman garinku sai wanda ya saba,haka kawai kaje a qunsheka cikin gidan ba motsin yara bana maqota saidai idan kai ka shiga. +
      Sam bata damu da sabuwar motar da ta gani ajjiye qofar gidansu ba suka wuce zuwa cikin gidan ita da halima suna ‘yan hurarrakinsu,tun daga soron gidan su qamshin turare ke dukar hancinsu ba kuma irin turaren humrarta ba da ya kama gidan,daga bakin qofar falonsu ta hangi takalma sau ciki na maza bata kawo komai a ranta ba tadage niqaf dinta tayi sallama cikin falon. 1
       Abdur rahman ne zaune cikin daya daga cikin kujerun falon sanye da shadda ruwan madara wadda ta haska fatarsa,kansa hula ce zanna,hankalinsa na kan mama suna taba hira da alama labari yake bata,sallamar su ce ta maido hankalinsa bakim qofar,baki ya saki yana kallonta cikin mamaki kamar yadda ta saki baki itama tana kallonsa cike sa mamakin yaushe ya diro nijeria
“Kai kam baka da aiki sai zuwan bazata?”
“Kawai kice yaushe a gari inji maqi baqo” ya fada yana murmushi,sai data samu gu ta zauna sannan ta dubi mama
“Wai don Allah mama yaushe yazo?”
Fitarku ba dadewa” sai tayi murmushi tana gaida shi,amsawa yake shima cikin sakin fusakar suka fara dan tsokanar juna yadda suka saba,halima ce ta shigo wadda sai da ta tsaya ta daura alwala,a ladabce ta gaidashi ya amsa yana dubanta
“Wai shekara daya tal naga duk kum qara girma,halima ke kam ashe ke kika debo kamar sumayya”dariya tayi ta shige daki don tada sallah,mama ta miqe jin zainab na kiranta tazo taga ruwan miyar tuwon daren data tsayar ya isa. 3
     Maida dubansa yayi ga sumayya
“sumayya ya kuma bayan saduwa,bayan tafiyata lamura masu yawa sun wakana,Allah ya jiqan yaya mukhtar,ya gafarta masa ya masa kyakkyawan masauki a aljanna yasa ya huta”
“Amin ya Allah” ta fada wani miki na neman motsuwa a zuciyarta,zuciyar na son karyewa hawaye na neman zuba,shuru ya ratsa dakin yana nazarinta,ya fuskanci ya taba mata mikin dake zuciyarta
“Tunda nazo nake tambaya ina mutumina ashe yana gidan gwaggwo yahanasu,da yake ban leqa gidan ba,jiya na shigo qasar” sai ta murmusa tana cewa
“Ayyah,ai da ya samu hutu sai tazo ta daukeshi da kanta” idanu ya zaro
“Kice abdallah an fara makaranta,lallai an girma”murmushi ta kuma tana bashi amsa sanda mama ke dawowa cikin falon
“eh,ai yana cika shekara ya abbakar ya sanyashi”
“Wacce makaranta ce?”
“New egypt international” kai ya kada
“Masha Allah” hirar sai ta koma gun mama sai ta miqe itama tayi sallar la’asar,bashi ya bar gidan ba sai da yayi magariba suka gaisa da malam sannan ya ajjiye musu tsaraba dangin alawoyi da jallabiya ta maza data  mata tasu sumayya zainab da halima,sai tarin qananan kaya na abdallahnsa.
Yanayin sanyi ya fara ja baya,yayin da zafi ya fara sako kai,wannan shike nuna alamu na tahowar damuna,mafi yawanci lokutan zafi bata iya bacci mai yawa,hakan shi yake sanya ta tashin wuri,qarfe goma tuni ta kammala ayyukan gidab,bata ma jirayi tashin zainab ko halima ba,wanka tayi ta sanya kaya sa’annan ta debi kayan kari daga kitchen ta shiga falon mama,a zaune ta sameta itama tana gyara mafitai tunda lokacin amfaninda su ya zo,kasancewar ba ko da yaushe ake samun wuta ba,nan ta zauna tana karyawa suna hira da mama,bayan ta kammala ta dauko kayan hadin humrarta tana fadin
“Mama bari kiga na fara hadawa anty dije tata,saura kwana biyar tazo kada lokaci ya quren”
“Ai kam don idan tazo baki matan ba ke da ita,ya taku kada ku sakani ciki” dariya sumayyan ta danyi tana bude robar ruwan turare
“Ai ba’a shiga fadan uwa da d’a mama,Allah mama tun ina mamakin irin qaunar da anty dije kemin har naxo na daina” murmushi mama tayi
“Ko sanda muna gida tamu tafi zuwa daya ai,dana haifi abubakar lokacin bata yi aure ba cewa tayi da sai ta karbeshi,sanda na haifeki kuma basa garin nan ita da farouqu da tuni gunta zaki tashi,kinga kuma kina da shekara sha uku aka aurar da ke” kai take jinjinawa tana hadin humrar tare da jin dadin labarin da mama ke bata. +
      Halima wadda bata jima da tashi a bacci ba ta shigo dauke da wayar dake burari sumayya wadda gunta wayar ta kwana tana miqa mata
“Yaya ana kiranki” kanta ta daga ta dubeta
“Waye?”
“Baquwar lambace” ta daga mata kiran sannan ta miqa mata,karawa tayi a kunnenta tana mai sallama daga daya bangaren aka amsa mata sannan ta buqaci sanin waye,ajiyar zuciya ya saki yana lumshe idanuwansa
“Amma kam banji dadi ba da har cikin sauri haka kika manta da ni sumayyah” gabanta ne ya fadi,idan ba gixo kunnenta ke mata ba muryar lukman ce,dakewa tayi cikin qarfin hali tace
“Ba abun mamaki bane don na mance muryar wanda ban sani ba” dariya ya dan saki sannan yace
“Lukman ne sumayya,lukman tsohon mijinki wanda kuma yake fatan sake zamantowa mijinki a karo na biyu” jikinta ne ya dauki bari,sai kawai ta katse wayar tana duban halima da ta zuba mata ido tana kallonta,mamanta shiga uwar daki maida mafitan
“Halima lukman ne wai” ta fadi muryarta na rawa
“Mene?,me ya gaya miki?”
“Ba komai”
Shine kuma duk kika bi kika rude yaya,har yau kamar mune yayun kece qanwar wlh,kinga,ki tsaya kiji me zai fadi bawai ki katse waya ba”
“Cewa yayi tsohon mijina mai kuma fatan sake zama mijina”
“Dole aka ce haka ce zata tabbata?” Ta tambayeta tana kallonta,shiru tayi bata amsa mata ba,ganin bata da alamar ansawa ya sanyata juyawa zata fice,sai sumayyan ta niqa mata wayar tace ta tafi da ita. 2
       Gabanta ne ya dinga faduwa,sai aikin nata ya koma sukuku sabanin dazu da take yinsa cikin karsashi,har mama ta ankara saidai bata tambayeta ba,tana zaton ko mukhtar ta tuna,da yake yawancin lokuta haka na faruwa da ita idan ta tuna shi,tana shirin miqewa ta adana kayan haliman ta sake shigowa riqe da wayar,idanuwa ta tsareta da shi
“Ya aka yi?”
“Ba lukman bane wannan karon ya abdur rahman ne” tsaki ta ja tana ci gaba da ayyukanta,ta gama lura da take takensa
“Duk kanwar ja ce,dauki kice bana kusa”
“To” haliman ta fada tana daga wayar gami da ficewa daga dakin. 1
      Sai bayan kusa awa daya sannan ta dawo dakin tana dariya ta dubi sumayy
“Wlh yaya kin ban kunya,kinga ya abdur rahman ya gane fa,cewa yayi har da ni a yi masa qarya ko,yace zaya zo anjima zamu hadu” shiru tayi ba tare da ta ce komai ba,bata fata ko buri abdur rahman ya dora daga inda ya tsaya wajen yada manufarsa,domin a yanzu bama abdur rahman ba,bata buri kowanne namiji ya sota,don kwata kwata bata ji a rayuwarta zata iya sake yin aure,idan tayi tana jin kamar taci amanar mukhtar ne,gwara taci gaba da rayuwarta a haka har itama tata tazo ta tadda ita ta hadu da mukhtar dinta a jannatul firdausi.
Idanu ta dinga zubawa tana addu’a kada yazo,addu’arta kuwa taci don baizo ba din har suka kwanta,saidai washegari da yammaci ta gama wanka kenan tana shafa mai taji muryarsa a tsakar gida,yau duka a kasalance ta wuni cikin mutuwar jiki,saboda yadda lukman ya matsanta mata da kira da turo saqonnin ban haquri yafiya da kuma yunqurin dawowa gareta,baki daya ya birkita mata kwanya,baisan yadda ta tsani batun aure ba yanzun,sam ya fice mata a kai,ta yaya zatayi marmarin abunda tasha wuya cikinsa,baki daya tarihin rayuwarta wahalar aure ce wadda ta cimmata ta jigata ta cikin qananun shekaru. +
      Ta kammala sanya kayanta tana shirin tada sallah wadda zata yita ne a makare don lokacin ya fita zainab ta shigo wadda ta gama shiryawa zasu yinin biki ita da mama
“Ya sumayya kizo inji yaya abdur rahman”
“Ina zuwa” tace tana yunqurin tada sallah
“To mu mun tafi inji mama,tace ki kula da yadfa halima zata sa sanwa kada tayi yawa tunda yau banda malam” kai ta gyada mata don ta riga ta tayar din.
       Falo zuwa tsakar gida ta duba duka baya nan,hakan ya sanya ta leqa soronsu a bakin sitting room ta hangi takalmansa,sai ta sanya silifas ta fita zuwa can,da sallama ta shiga ya daga kamsa daga wayar da yake daddannawa ya dubeta,gefe can ta samu ta gaidashi ya amsa idanuwansa na kanta,kallon ya fara mata yawa saboda haka ta kau da kai tana shirin magana sai kuma ya rigata
“Nima sai an ja min aji sannan za’a fito?” Idanu ta watsa masa wadanda suka sanyashi lumshe nashi idon,sau tayi murmushi ba tare da ta dubeshi ba tace
“Wanne irin jan aji kamar saurayin da yazo zance gurin budurwarsa”
Ai hakanne,saurayin ne yazi zance gun budurwarsa ko kin manta?” Sai ta sake dubansa,Maganar ta taba ta duk da ta tsammaci haka,shima ita yake kallo,cikin son maida maganar wasa tace
“Ah ko?,to ai kayi kuskure,ka manta ni din ba budurwa bace,saboda haka saidai bazawari yazo guna ba saurayi ba,saurayi sai budurwa ai”
“A haka na gani nake kuma matuqar so” shi kuma ya fada ba tare da alamun wasa ba,ganin yanason maida zancen gaske sabanin yadda take son maidawa saita waske da cewa
“Yau kuma tsurfa ce ta tashi daga toge a sitting room maimakon ka shiga ciki yadda ka saba?”
“Neman aure nazo,kinga bai kamata naci gaba da shiga cikin falom surukai ina zama ba” sai ta danyi dariya duk ason bagarar da zancan
“Ah wai…auren halima ko?”ya fuskanci da gangan take watsi da manufofin da yake son yadawa,hakan ya sanya ya kira sunanta wanda ya tilasta mata dubansa
“kinsan ko a da idan na fadi magana irin wannan da gaske nake ko?,to har yau din ma hakan take,da gaske sumayya na dawo neman aurenki ke karo na biyu babu wasa,kuma ina fata wannan karon ni zan jefa qwallon”shuru tayi tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,mukhtar dinta ta tuna,ta daga kai tana kallon abdur rahman idanuwanta fal qwalla
“yanzu kaima sai ka yarda naci amanar ya mukhtar?” Cikin rashin fahimta ya tsuke gira
“Cin amana kamar yaya,da aurensa ne a kanki?,ina cewa koda yana raye halas ne na aureki bare ya rasu?”
Kalmar ta mata ba dadi sai ta miqe
“A gunka mukhtar ya rasu amma ni a cikin zuciyata rayayye ne tamkar yadda kake a raye” sai ta juya ta fice kuka na qwace mata,sam bayi tunanin wannan maganar ta isa bata rai ba,amma da ya tuna cewa har yau tana cikin zafin mutuwar uban danta sai ya mata uziri,hakan ya sanya daga sitting room din ya wuce ba tare da ya dawo ciki ba,har dare ranta na a jagule,tana zaman zamanta yana neman jagula mata lissafi,tana ganin kiransa ta share shima da yaga bata daga ba sai ya tura mata tex ya qyaleta. +
  *******    *******   ********
Batasan cewa ana shirin jagula mata lissafi ba sai washegari da azahar data tsinkayi sallamar su nuwaira a tsakar gidansu,baki daya yaran ne cikin kyakkyawar kaka data bayyana mata har yau basu sauya kan turbar data dorasu ba,zuciyarta ta dinga bugawa tsoro ya cikata,duk da a bangare guda tayi farinciki da ziyarar tasu. +
       Sosai taji dadin zuwan yaran,basma ta dubeta
“Anty abbanmu ne ya kawo mu,yace wai kema zaki dawo gidanmu ko?” Yarinyar ta tambayeta,murmushi tayi tana shafa kanta
“Basma,har yau surutu na nan kenan” ta fada da sigar son bagarar da maganar,tare suka wuni da ita,suna zagaye da ita suna bata labarun gidansu da yadda lamura suka sauya,inda sukayi dai dai ta yaba musu,inda suka kuskure ta gyara musu ta nuna musu yadda akeyi. 1
     Da yamma bayan sun gama sallar la’asar sun sake cin abinci nuwaira ta dubi sumayya
“Anty,don Allah ki daure ki dawo gidanmu,abba yace mu roqeki,muna sonki wallahi anty,baki ga yadda hajiya ma ke son ki dawo ba,naji tana cewa ne ba zata sanya baki ba tun yanzun,kada nauyinta ya sanya kiyi abinda bakiyi niyya ba ta shiga haqqinki,don Allah anty ki dawo” ta fada tana karkatar da kai,sai islam ma ta matso
“Eh wallahi anty tunda kika tafi baki daya gidan babu dadi,ko abba ma barin garin yayi,baifi wata daya da dawowa na,da ya dawo kuma kullum masifa suke da mama,gidan ba dadi muna gun hajiya ko yaushe,ki dawo anty don Allah kinji” kasa magana tayi baki daya,wato lukman kwaso mata yaransa yayi kenan su masa campaign ko su daure ta da jijiyar jikinta?
“Anty baki ce komai ba” cewar nuwaira wadda ta qagu taji sumayyan ta amsa,murmushi ta sanya ta kama hannayensu ta hade waje guda
“Kunsan komai nufin Allah ne,kuma ko wanne bawa da irin tasa qaddarar,to ku yita addu’a idan akwai alkhairi zan dawo in sha Allah kunji?”
“To anty” suka fada jikinsu a sanyaye,duka sai suka bata tausayi,babu shakka yaran abun tausayi ne,su masu uwa ma kenan bare mara uwa a gidan,ko da yake dace da uwa ta qwarai shine jigon farinciki da jin dadin rayuwar ‘ya’ya duniya da lahira. 3
       Qarfe biyar saura yaro yayi sallama gidan yace su nuwaira su fito,tuni basma ta sheqa da gudu ta gano abban nasu sannan ta dawo
“Abba ne,yace ku fito”,kyautar humra da kwalakca ta yiwa kowannansu,sannan ta zuba wata da yawa ta hada da turaren wuta tace su kaiwa hajiya.
       A bakin qofar soro ta ja tunga tana musu sallama,nuwaira ta dubeta tana narai narai da idanuwa
“anty iya nan ko qofar gida ma ba zaki rakamu ba?”dariya tayi,ta fuskanci wayo wai yarinyar keson yi mata
shikenan muje”ta fada don faranta musu,yana tsaye bakin mota ya bubbude qofofin,da dai dai yaran suka dinga shiga tana musu sallama sannan ta rufe musu qofar motar,tana dagowa suka hada idanu
“Ku gaida gida ku gaidamin hajiya” ta fada tana juyawa da niyyar shigewa ciki,da sauri ya tari gabanta
“Haba mana sumayya,ko gaisuwa ai kya tsaya kuyi ko?” Ta tabbata idon yaran yana kanta hakan ya sanyata tsayawa tana dubansa
“Don girman Allah sumayya kimin alfarma ki koma gida na,kimin alfarma ko don rayuwar yara na”
“Ni kuma tawa rayuwar fa?” Ta masa tambaya kai tsaye
“Sumayya gida na ya sauya a yanzu,da qafafuna nake tsaye,hijabin dake lullube da idanuwa Allah ya yamin shi,ki taimaka ki koma gidana ki sa cikasa mana sauran haske da farincikin da muke da buqata,kowa a gida na na buqatarki sumayya,don Allah kada ki gujemu”. Kai ta kada 
” lukman,bani da buqatar nayi aure har na koma ga mahalicci na,domin ina fata naje na hadu da mijina uban ‘ya’yana,ina mai baka shawara tun wuri kayi haquri da ni”ta qarashe zancan zuciyarta na raurawa ta kewayeshi ta wuce ciki,jiki babu qwari a sanyaye shima ya koma cikin motar ya tada ita ya bar layin.
+
       Tana shiga zainab na miqa mata waya,bata san ko waye ba haka bata tambaya ba,tama yi tsammanin anty dije ce don tace anjima zata kira ta,wayar ta maqala a kunne,muryar abdur rahman ta mamayi dodon kunnen nata
“Ba mukhtar kadai ba,ashe har lukman ma na raye a zuciyarki?” Tambayar da ya fara jefo mata kenan wadda ta sanyata saurin janye wayar daga dodon kunnenta,yaushe abdur rahman ya ganta da lukman?,tambayar data yiwa kanta kenan,kawai sai ta tsinci kanta da fashewa da kuka,saman katifarta ta fada tana kife kanta a saman filo,baki daya cikin kwanaki hudu zuwa biyar kacal suna son lalata zaman lafiyar zuciyarta ruhinta da ma gangar jikinta?,wa yace musu tana da buqatar aure a yanzu?,wa yace musu tana buqatar wani daga cikinsu?,akan me zasu yi mata kutse cikin rayuwar data lallabata ta fara samun nutsuwa da dangana?su suke suce ta mance da mukhtar ta fara sabuwar rayuwa da su?,ta mance da mutumin da shi ya fara gina tunani da zuciyarta?.
Qarar wayarta karo na biyu ya sake katse mata tunanin da ya karade ilahirin qwaqwalwarra,kamar ba zata daga ba sai taga lambar anty dije ke yawo bisa fuskar wayar,qara fashewa tayi da kuka da taga sunanta,zuciyarta ta sake karyewa,tasan a irin wannan yanayin babu wanda take budewa damuwarta irin anty dijen,taso ace a yanzu tana kusa da ita,sai ta daga kiran da sauri,saidai maimakon sallama da anty dijen ta tsammata sai taji sautin kukan sumayya ya karade kunnuwanta.

About Ismail

Check Also

QADDARAR SUMAYYA CHAPTER 30

QADDARAR SUMAYYA CHAPTER 30 Ba yadda ummee ta iya wani lokaci haka take biyewa tsiyar …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *