[Advertisements⬇️]

QADDARAR SUMAYYA CHAPTER 25 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

QADDARAR SUMAYYAH
CHAPTER 25

Bayan sallar isha’i ne,idarwarta kenan abdallah ya soma rigima tilas
ta kwantar da shi gefanta ta soma lallabashi,don kwanakin abinda ya
koya kenan rigima idan zaiyi bacci,ya Abbakar ne dake shirin wucewa
gidansa ya leqo
“Kinyi baqo sumayya”
“Baqo?,baqo kuma ya abbakar?” Ta tambaya cikin mamaki da faduwar
gaba,waye yake son jawo mata jarfa tana zamanta lafiyar Allah
“Eh baqo, kiyi ki fito kada ki zauna” ya fada cikin halin ko in kula da
yanayinta yana sakin labulen ya fice,magabar tayita juyawa cikin
ranta,sai ta banzatar da zancan jin yaya abbakar din na yiwa mama sai
da safe ya wuce gidansa.
Minti kusan goma da fitar tasa mama ta dago labulen ta shigo
“Wai ba yayanki ya fada miki kina da baqo ba” kamar zata saki kuka ta
dubeta
“Mama ban fa san ko waye ba”
“Idan kinje kya ga ko waye din yana sitting room din malam,tashi maza
ki wuce kuma saura kije ki yiwa mutane sakarci”,tilas ta miqe bayan ta
kwantar da abdallah a kan gado ko hijabin jikinta bata cire ba ta fito
zuciyarta fal quna.
Turus tayi bakin qofar ragowar sallamarta ta koma ciki,da hanzari ta
juya tana mai neman fita,cikin zafin nama ya sha gabanta wanda saura
kadan jikinsu ya hadu,sai ta ja baya tana dubansa, mukhtar ne sanye da
dinkim shadda ruwan sararin samaniya babu hula kansa,ta masa kyau
sosai saidai ramar da yayi ta bayyana, hancinta ya cika da qamshin
turarensa ya dinga tuna mata baya,saboda haka da sauri tace
“matsamin na wuce”
“Babu inda zakije sumayya yau sai kince wani abu game da ni,kin yafe
min ko baki yafemin ba,sumayya ya ina kike so na dora raina?,laifi ne na
aikatashi na nemi afuwarki sumayya amma kinqi kice komai,kinsan
kullum ya nake kwana ya nake tashi da rashin cewa komanki?,kinsan
me nakeji cikin qirji na” sai kuma ya sassauta murya cikin sanyi
“Kinfi kowa sanin wane mukhtar sumayya, kinfi kowa sanin wane irin
zama mukayi a baya,sumayya ki tausaya min koda ba zaki tausayamin
ba ki tausayawa abdallah,abdallah ya zama marayan qarfi da
yaji,abdallah na buqatar mu ni da ke a tare,idan baki tausayawa mana
ba sumayya waye zaiji tausayinmu duk duniya?,taba qirjina sumayya
kiji” ya fada yana fincikar hannunta zuwa qirjinsa,sosai taji zuciyarsa na
bugawa,gaza cire hannunta tayi sai da taji ya ambaci wash,da sauri ta
dubeshi sai taga yana dafe da kansa yana layi,batasan sanda ta riqeshi
ba a rude tana cewa lafiya?,ganin yana neman gun zama ya sanya ta
zaunar da shi tana masa sannu,tsahon mintina biyar sannan ya sauke
numfashi ya gyara zamansa tana zaune can nesa da shi ya dubeta
“Ciwon kai nake fama da shi,amma wannan duka ba damuwata bace
burina kawai ki yafemin” ya fada yana duban wayar idanunta, a
hankali ta janye idanuwanta zuciyarta na mata bitar waye mukhtar
agurinta,
“Na yafe maka” ta furta murya can qasa
“Allah ya yafe mana baki daya” wani wawar ajiyar zuciya ya saki,baki
daya jikinsa ya saki,wani farinciki yaji yana ratsa kowacce gaba ta
jikinsa, yana so yaje ga sumayyan amma sam jikinsa babu qwari ko
kadan,sai ya miqa mata hannu
“Taso sumayya kizo kusa da ni don Allah” sai ta girgiza kai ba tare data
motsa ba,tilas ya tattaro duk wani ragowar qarfinsa ya kiqe ya isa
gareta, kusa da ita ya zauna har tana gogar kafadarta,hakan ne ya
sanyata ta janye da sauri tana hada rai
“Meye haka,don nace na yafe maka ai hakan ba yana nufin kai mijina
bane ko zan sakw aurenka ba” da sauri ya sake matsawa kusa da ita
babu gun matsawa a gunta don ya kaita qarshen kujerar sai ya kama
hannunta ya matse cikin nashi
“Sumayya, na sake miki wani laifin don na bada sadakinki,amma bisa
sharadin matsawar baki amince ba zan karbi kaya na na haqura”
Wani abu taji yana ratsa zuciyarta mai kama da farinciki,zuciyarta ta
karye hawaye ya biyo kuncinta, cikin raunanniyar murya ta kwabe
fuskarta
“Ni nace maka ka kai sadakina ba tare da sani na ba?,ai kuwa sai kaje ka
karbi abinka don ni ban amince ba, kuma……” Bata ankara ba ya hade
bakinsu waje daya wanda hakan yayi sanadiyyar katsewar
maganarta,sun dauki kusan minti goma a haka sannan ya janye yana
dubanta,qasa tayi da kanta kan fuskarta qaramin murmushi na fita a
fuskarta
“Magana ta qare,na sanki tun ba yau ba,dukkan abinda zaki fada a
yanzun nasan aji ne kawai zala jamin ko ba haka ba” sake hade fuska
tayi kamar gaske
“Nidai na fada kaje ka karbi sadakinka,bana yi”
“Ok to bari na kira ya abbakar na sanar masa” ya fada yana fiddo
wayarsa daga aljihun gaban rigarsa,ganin da gaske lambar ya abbakar
yake nemowa ya sanyata qwace wayar
“Alah,ki bani mana na isar mishi da saqonki”
“Ni bance ba” ta fada a shagwabe,sai yayi jagale yana kallonta saboda
tuna masa da baya da tayi ta salon yanayin maganar da tayi
“Kada ki hanani fa tafiya gida yau na kwana a nan”
“Bismillah mana ai ga guri nan” sai yayi kalar tausayi yana dubanta
“Yaushe zala tara shaidu sumayya ki koma dakinki” idanu ta juya ta dan
murguda baki
“Sai shekara iwar haka” qirjinsa ya dafe yana kallonta
“Mutuwa kike so nayi kafin lokacin sannan ko?” Rai ta hade
“Ka daina fadin haka mana ya mukhtar,ni kunya nake ji gaskiya ka bari
idan ja shirya zan fada maka ka sanarwa ya abbakar” hannunta wanda
ke cikin nashi ya sumbata yana fadin
“Na gode, na gode, na gode sumayya,na gode da karamcin da kika nuna
min a rayuwa,na gode da kika nuna ke mai qaunata ce har yanzu” sai ya
dakata yana fidda zoben azurfan dake yatsansa ya zura a nata,ya mata
yawa hakan ya basu dariya baki dayansu,sai ya cire ya sanya mata a
yatsan tsakiya duk da haka ya mata yawa
“Ina son zoben nan sumayy,amma sai naga yafi kyau a hannunki,ki
ajiyemin zan karba”
“Idan kuma naji dadinsa bazan maida maka ba”
Dariya ya danyi sannan yace
“Babu komai,ai da kai da kaya duka mallakar wuya ne” sallamar halima
ta sanya sumayya miqewa,shigowa tayi dauke da abdallah tana fadin
“Wallahi yaron nan ya koyi rigima,tunda ya tashi yaje zunduma ihu nayi
tsammani ma kin jiyo shi”
“Ina zata jiyoshi ta shiga kogin qauna” mukhtar ya fada cikin salon
zolaya yana miqa hannu ya amshi abdallah dake ta dokin zuwa gunsa
yana kiran abba na,murmushi halima tayi tana yiwa sumayya kallon
tsokana ta fice,ita kanta wani dadi taji don babu wanda yaji dadin
rabuwarta da mukhtar,qafarta har qaiqayi take taje ta bawa zainab
labari.
Yar kallo sumayya ta koma sanda mukhtar suka soma wasa da
abdallah,bata taba ganin d’a da uba irin haka ba,sai wajen qarfe goma
ya fito zai tafi,qin tafiya yayi har sai data masa rakiya bakin mota,har ya
shiga ya fito ya sake kallonta
“Ban son tafiya sumayya,banqi ace tare da ke zan tafi ba,don Allah ki
taimaka ki gama shirye shiryen da duk zaki da wuri,ni na amince ma
duk abinda baki qarasa ba ki qarasa shi a gida na zan baki wannan
damar.ji nake kamar lokaci na qure mana” murmushi tayi tana jin
maganar tasa na sauka sosai cikin zuciyarta
“Kada ka damu ya mukhtar,ka qarasa gida dare yanayi” ta fada tana
taka masa,sai da yaja motar ya bar layin sannan ta koma cikin gida.
*** *
***
Cikin abinda bai gaza sati biyu ba mukhtar ya sabunta soyayyarsa
baki daya,kullum yana tare da ita idan baizo ba kuwa ranar katin waya
zaici ubanshi,har tsokanarta su halima sukeyi,wai sai kace wasu masu
auren fari.ya dawo mata ya mukhtar dinta sak,sai ta samu kanta da
dokanta wajen ganin ta a gidanta cikin sabuwar rayuwa ita da mukhtar
dinta da yaronta.
Sati na zagayowa aka maida auren sumayya da mukhtar karo na
biyu ranar jum’a bayan an sauko daga masallaci,a ranar mukhtar ya
matsanta mata sai ta sanya ranar tariya,sati biyu tace ya tuburr mata
kan ya masa yawa,tilas ta haqura ta maida shi sati dayan,don dama
tana jiran aiken da anty dije tace zata yi mata nan da kwana goma.
***
*******
***
Juma’a asabar lahadi litinin kwana hudu da mai da auren ran litinin
mukhtar yace ta shirya da daddare zata masa rakiya zai yi siyayyar
kayan da yake son sauyawa cikin gidan,mama ta sanar,Allah ya tsare sai
kun dawo abinda maman tace kenan.
Tana idar da sallar magariba ta soma shiryawa,kwalliya tayi wadda
rabonta da yin kwalliya irinta har ta manta,tsaf ta shirya cikin material
na one million stone peach ne da adon mint green,fitted gown aka
mata da shi.ya masifar yi mata kyau,zainab ke dubanta tana cewa
“Kai yaya sumayya,sai kace zaki dinner,ai kya bari sai nan da kwana
hudu wannan kwalliyar,karfa ki sanya ya mukhtar yaqi maidoki”
daquwa sumayya tayi mata tana cewa
“Ni sa’arki ce,naga alama kin soma rainani” dariya ta sanya
“Yi haquri yayanmu,amma dai ba hijabi zaki sanya ba ko?,naga kina da
mayafi kalar kayan”
“Kyaji da shi” sumayyan ta fada tana feshe jikinta da turaruka,ita kanta
tasan cewa tayi kyau,sai da tazo fitowa sai taji kunyar wuce mama a
haka,da qyar ta fice kanta na sunkuye mama bayan ta barwa zainab
abdallah wanda yau yayi baccin wuri
Baki kawai mukhtar ya saki yana kallonta har sai data hure masa
idanu,dariya sukayi baki daya
“Ki amince kawai yau mu wuce gida my sumy”kicin kicin tayi
“amma dai unguwa kawai kace zan raka ko?”murmushi ya saki
“Afuwa ranki shi dade,na tuna,muje” suna tafe yana tuqi amma baki
daya ya wani narke mata bini bini ya kalleta har suka isa gun ya kashe
motar ya zuba mata ido ba tare da ya fita ba
“Sumayya, ina jin wata sabuwar gauna taki na dasuwa cikim zuciya
ta,da ace a yanzu ne wani ya aureki mutuwa zanyi wallahi,ina sonki
sumayya ina fata mu kasance tare har ABADAN” murmushi ta saki tana
kada kai
“Nima ina fatan haka ya mukhtar”
Sai da ya sumbaci goshinta sannan ya bude motar suka fita.
Kayayyakin amfanin gida suka siya sosai,harda kayan kitchen sai da
ya siya wasu abubuwa daga ciki,motarsa ta cinye kayan a ciki aka zuba
masa sannan suka fito,sake tsayawa yayi a wani gu da saida kayab
qwalam da maqulashe ya sayi kaji biyu gasassu da ice cream,sai
damammiyar fura ya dawo ya tada motar yana dubanta, hira suke qasa
qasa duk ya wani sukurkuce,wani kallo yake jifanta da shi,sai taga ya
dauke kan motar ya sauya hanya shuru tayi ta kasa tambayarsa
hakanan sai ta biye masa har suka isa qofar gidansu,gidanta ne a da
wanda a yanzu ma ya sake zama mallakinta
“Bismillah muje ciki ko?”
“Ya mukhtar na bar abdallah a gida fa”
“Babu komai,minti talatin kawai ina son ganinki ne sumayya” nan ma
bata ce komai ba ta fita suka shiga gidan,tayi mamakim ganin komai a
tsaftace a killace,bai tsaya ko ina ba sai dakin gadonsa,ya dubeta sanda
yake cirw hularsa tare da tattare hannun rigarsa
“Nasan bakiyi sallar isha’i ba ki daura alwala muyi sallah sai mu wuce
ko?” Cikin shagwaba tace masa
“Wai nikam bansan gaggawar me kake ba ya mukhtar,saura kwana
hudu fa na dawo gidan baki daya” murmushi kawai yayi bai amsa mata
ba ya shiga bandakin.
Bayan sun idar ya matso inda take, hannunsa ya sanya cikin nashi
yana kallon qwayar idonta
“Sumayya,Allah ne kadai yasan yadda nake jin sonki a zuciyata”
murmushi tayi tana girgiza kai.”ya mukhtar,sai kace yau kasan
sumayya,sai sake jaddada qaunarta kake bayan ta riga da tasan
hakan”murmushin shima yayi
“Hakane fa ko sumayya,amma wannan karon wata qauna ta daban
nakeji,sumayya,ina so ki kasance tare da ni har qarshen rayuwata”
“Na maka wannan alqawarin”
“Na gode”
Sai kuma shiru ya biyo baya har ya qosa taji me zai sake cewa,sai daga
l. 3
8:05 AM OI
B/s
bisani yace
“Sumayya,zaki yimin alfarma na kasance tare da ke cikin wannan
daren?”idanu ta daj fiddo
“Ya mukhtar,kwana hudu fa ya rage”
“Na sani sumayya,amma so nake kimim wannan alfarmar indai ban
keta iyakar ubangiji ba”
“Na maka ya mukhtar” ta fada kanta tsaye
“Allah yayi miki albarka” ya fada yana janyota ta fada jikinsa
kowannansu cuke da kewar dan uwansa,kada ma mukhtar yaji labari.ji
yake kamar an masa bushara da aljanna.
Qarfe goma saura na dare ta fito daga bandaki,mukhtar tuni ya
kammala shiryawa yana zaune yana jiran fitowarta,binta ya dinga yi da
kallo,ji yake tamkar ya hadiyeta ya maidata ciki,har yanzu baiwar nan
da ya santa da ita na tattare da ita,ganin ta kammala ta yafa mayafi tana
saba jaka ya sashi saurin cewa
“A’ah,amarya guda bai kamata ace bata ci komai ba” sai ta saki
murmushi cikin jin kunya
“Ya mukhtar yau ka manta da abdallahnmu?,munfa barshi a
gida”miqewa yayi da sauri yana fadin
“Kai kai hakane fa,jikina ya bani ma fa ya farka” dariya ta saki
“Uhmmm,sannu masu ‘ya’ya”
“Wallahi kuwa,d’a ba wasa bane” ya fada yana kama hannunta suka
fice.
Ihu take so ta kwarara ko zataji sanyi a ranta amma zinatu ta hanata
don kada ta tara musu mutane,wadda ita ta kawo mata labarin
komawar auren sumayya da mukhtar,maimakon haka saita maida
dubanta ga zinatu cikin daga murya
“Wallahi wallahi sai na aikata abinda na qudurta babu mai hanani
aikatashi wallahi.mukhtar nawa ne,nawa ne ni kadai,bazan juri ganinsa
da wata ba ba ni ba” ta fada kamar zararriya tana mai ficewa daga layin
cikin qunar zuciya kamar zatayi aman zuciyar tata.
Ko da ya sauke ta ma sai da ya sake tsareta,kamar bazaya tafi ba har
sai dayaga giftawar malam da alama ya shigo gida kenan sai da safe
sannan sukayi sallama bayan ya cikata da kalamai masu tsayawa a
Zuciyar wanda ake so.
Tana shirin kwanciya wayarta ta dauki ruri, mukhtar ne sai ta kumahe
idanu tana murmushi
“Na kasa bacci my sumy,ganinki nake kusa da ni”‘yar qaramar dariya ya
tasa tana fadin
” baban zumudi ka zama ya mukhtar ne?”shiru ya danyi sannan ya saki
ajiyar zuciya
“Bakisan me nake ji ba game da ke sumayya”. Hira suka kashe lokaci
suna yi,a nan yake gaya mata ran rakota tare da yaya yahanasu za’a
zo,har mamaki take idan taji yadda yaya yahasun ta sauya take nuna
mata qauna,basu suka rabu ba sai daya na dare,ta dubi agogo tana zaro
ido ganin lokacin da suka shafe tare,sai ta fita ta daura alwala tayi
sallah raka’a biyu sannan ta kwanta.
********
******
***
Shirye shiryen tariya sun kankama sosai,tayi gyaran jiki hadi da
qunshi da kitso,kayanta baki daya ta kammalesu.
Ranar alhamis ana ya gobe zata koma,da azahar suna falo ita da
halima da zainab suna hira ita kuma tana gugar ragowar kayan
abdallah da bata gama shiryawa ba,sai anty salma qanwar mama
wadda anam zata kwana,wayarta dake daki ta soma burari,abdallah ne
ya miqe da gudunsa ya dauko ya miqa mata,anty salma ta talle masa
geya tana cewa
” kaji dan jakar uba wai yasan kayan uwarsa,sai kace wani yace zai
dauki wayar ne”dariya sukayi dukansu halima tace
“Indai Abdallah ne kadan kika gani anty” ita kuwa sumayya miqewa
tayi ganin lambar mukhtar ce ta fita ta koma dakinta
“Lafiya abban abdallah naji muryarka can qasa?”murmushi ya saki
sannan yace
“lafiya qalau,a yanzu ma ina gida kwance ina hutawa,babu abinda nayi
amma wata gajiya nakeji sosai a jikina, kewarki nake sumayya goben
nan kamar ba zata zo ba”tamkar yasan abinda take ji jikinta itama
kenam,sai ta saki ajiyar zuciya tana masa murmushi
“Au dariya ma kike min?,naji na gode,amma da zaki taimaka min da
kinzo na ganki kinji my sumy” sai ta kasa musa masa,dama suna da
agender fita karbo dinkunan sumayya gidan wata mata bayan sallar
la’asar ita da anty salma
“Babu damuwa ya mukhtar,a mma sai bayan la’asar”cikin zumudi yace
“Da gaske sumayya ta?,kada fa ki shirgani”dariya ta qyalqyale masa da
Ita
” da gaske nake mana abban abdallah, ka jirayeni,amma fa gobe ba za’a
rakoni da wuri ba tunda yau ka sake gani na”
“Babu komai,ai goben ta Allah ce,Allah yayi miki albarka sumayya ta”
tana jin dadi ya sanya mata albarka don haka da sauri ta amsa da amin.
A gidan mai dinki ta bar anty salma tace zata je ta dawo,ta riga da
tasan inda zata din saboda haka tayi tayi abdallah ya zauna qememe
yaqi har da kukansa ammi zai bi tace madallah yayi ta binta din sai sun
dawo.
A qofar gidan mai adaidaita sahu ya sauketa,ji tayi ana malam ga
kudinka,tana waiwayowa sai taga mukhtar ne,cikin mamaki take
tambayarsa
“Ya akayi kasan na qaraso”
“Jikina ne ya bani” ya bata amsa yana amsar abdallah daga hannunta
yana masa cakulkuli suna qyalqyala dariya tana biye da su har zuwa
falon gidan,kallon gidan take ya sauya komai kamar wanda zai kawo
budurwa,komai fes gwanin sha’awa,zubewa sukayi kan kujera mukhtar
na biyewa abdallah suna ta wasanninsu yayin da sumayyan ke zaune
gefe guda
“Wai nikam ‘yar kallo kuka maidani ne,nazo amma ba’a tani,bayan
nemana akayi” ta fada tana murguda baki,dariya mukhtar din ya saki
yana duban abdallah.”lah,abdallah kaga mamanka na kishi da kai”sai
ya kada kai kawai yaron don bai fahimci me yace ba,juyawa yayi gunta
“Dama taimaka mana kika yi kika dafa mana wani abun madam”
“Kamar me?” Ta tambayeshi
“Abinci mai sauqi da dadi
“An gama” ta fada tana miqewa
“Ammm,madam,amma da kin taimaka kin cire wannan hijabin tunda
gaban mijinki kike ko?” Dariya ma ya bata yadda yayi maganar a
dake,bata ce komai ba ta cire din,sai ta miqawa abdallah hannu
“Muje kayi fitsari sai ka dawo ko?” Lafewa yayi jikin mukhtar din
qememe yaqi yarda da ita
“Barmin yaro na ana dole ne.yayi fitsarinsa babu komai cinyar babanshi
ce”.don haka ta juya zuwa kitchen ta barsu nan.
Tana tsaka da girkin mukhtar ya shigo goye da abdallah, saura qiris
ta dona hannunta cikin gas garin dariya
” ka ganka kuwa da goyon nan,don Allah tsaya na maka hoto”shi din
ma dariya yake,
“To ya zanyi.yaqi yarda na kwantar da shi kwata kwata”hoto ta musu
wajen kala biyar ta nuna masa suka dinga sheqa dariya,tex din da ya
shigo wayarta ya katseta,anty salma ce ke gaya mata ta wuce gida uta
kam sai ta taho,tana niyyar kiranta tace ta jirata tana tahowa mukhtar
ya rige hannunta
qyaletq ni da kaina zan maidaki”.qarshe tare suka gama girkin wajen
sallar magariba sannan ta karbi abdallah da qyar zata kwantar,sai ya
farka ya riqe mukhtar gam gam yana sakin kuka,tilas yace ta qyaleshi
suka dauro alwala sukayi jam’in sallar magariba tare sannan ta gabatar
masa da abincin.
Tare suke ci baki dayansu,saidai duk daga kan da zatayi idanuwansa
na kanta,saidai ya sakar mata murmushi ta maida masa martani,sake
hada idanuwa sukayi karo na barkatai, sai ya kauda kallonsa ya maida
kan abdallah
“Na godewa Allah da ya sake gwadamin wannan lokaci cikin
rayuwata,lokacin da zan zauna ni da matata abar sona da kuma diyan
cikina,ina fata Allah ya rayamin kai” ya fada yana shafa kan abdallah,sai
yaron ya dago kai yana kallonsa kamar yasan ma’anar abinda yake
cewa
“Ina da buri kanka abdallah” ya sakw fadi,sai ya dubi sumayya
“Ki taimaka min wajen tarbiyyar abdallah don Allah” murmushi ta saki
zuciyarta na bugawa kadan kadan
“Banda abinka ya mukhtar ai saidai mu taimaki juna tunda tare zamuyi
tarbiyyarsa” girarsa daya ya dage
“Haka ne fa,to Allah ya bamu aron rai”
“Amin ya Allah” ta fada tana ci gaba da cin abincin, sai daga bisani ta
lura ba wani cin abincin sosai mukhtar din keyi ba sai aukin kallonsu
“Ai bama cin abincin kake ba fa yaya,wannan kallon duka na meye?”
Murmushi ya kuma saki.”kallon so da qauna nake muku”dariya ya bata
sOsai
“Naga alama sai na maka dura” ta fadi tana debo abincin da spoon tana
bashi,qarshe ita ta qarasa basu abincin dukansu sannan ta gyara
gun,kayan wasa taga yana ta hadawa abdallah sannan ya janye ta
bedroom yace zata tayashi wani aiki,bata fahimci wayo yayi mata ba sai
da labari ya soma shan banban.
Daf da kammaluwar komai sai ta tsinci hawaye na diga
idanunsa,tasa hannu ta shafo sai taji itama nata idanun na fidda ruwan
qwallar da batasan dalili ba
“Ya mukhtar ko na yi ma laifi ne?” Ta tambayeshi cikin sanyin jiki,sai ya
sake qanqameta yana sakin ajiyar zuciya tare da murmushi
“Babu abinda kika yimin, tsakani na da ke sai fatan alheri,Allah ya
haskaka rayuwarki.qwallar farinciki nake musamman idan na tuna
gobe zamu sake sabon zama sumayya” dariya tayi tana kwantar da
kanta a qirjinsa
“Na gode ya mukhtar”
“Nine da godiya sumayya,ina so ki sake yafemin ki dauka tamkar babu
abinda ya taba faruwa tsakaninmu mara dadi” cikin shagwaba tace
“Ni na manta ma fa ya mukhtar,ni babu abinda ya taba faruwa
tsakanina da kai,kai fa uban ‘ya’ya na ne”.
Da qyar ya yarda zai maidata gida,da sdrd yayi tayi zamanta meye
marabar yau da goben,ko a motar ma sai da ya gama yawo da su guri
guri ya loda uban siyayya sannan ya kaisu gida,riqe hannunta yayi
sanda take shirin fita ya sumbaci bayan hannun nata,itama sai ta maida
masa martani,ta jima tsaye a soronsu tana leqensa ganin ya tsaya bai
tafi ba,sai daga bisani taga ya ja motar ya tafi.
Tun mafarkin da taji daren jiya jikinta a mace yake,tana farkawa ta
kira mukhtar din ta tabbatar da lafiyarsa,har yana zolayarta kodai ta
qagu ne kawai a kawota,shi bacci ma yakw ta tasheshi,dariya tayi cikin
jin kunya sukayi sallama,har zuwa wayewar garin juma’ar jikinta a
mace yake,tun safe take kwance ta kasa katabus,tana jiyo koke koken
abdallah da yau ya tashi da rigima amma ta kasa cewa komao,har ya
shigo dakin ya gama kukansa da kawo mata qarar walida ‘yar anty
salma ya gaji ya fice ba tare da tace masa komai ba.
Qarfe hudu na yammacin ranar tana tsaye tana shiryawa cikin
dinkin atamfa riga da zani anty salma na tsaye kusa da ita tana bata
turare wayarta ta dauki kuwwa,sunan mukhtar ne ya bayyana gabanta
yayi mummunan faduwar har qafafuwanta taji sunyi sanyi,sai ta koma
bakin gado ta zauna tana amsa wayar cikin fargaba
“Assalamu alaiki amarya ta” muryar mukhtar ta ratsa dodon
kunannata,sai ta amsa masa tana lumshe idanuwanta,cikim salon
soyayya suka gaisa sannan yace
“Ina fatan kin fara shirin tahowa gidanki” dariya ya bata ta murmusa
“Yanzun haka ma shirin nake angom doki”
“Eh naji na yarda ina abdallah”
“Yana waje.yau tun safe yake ji da rigima wallahi” nemo min shi mu
gaisa”
“Bai kusa fa ya mukhtar” ta fada a shagwabe,tuburewa yayi tilas ta
qwalawa zainab kira ta kawo shi ta hadasu da wayar taci gaba da
shiryawa,sai da ta gama sannan ta karbi wayar
“Nima ina gun masu dinki zan karbi dinkuna na,SAI KIN TAHO?”
“To ya mukhtar,ka kularmin da kanka”
“To my sumy”. Ajjiye wayar tayi tana sakim ajiyar zuciya.
Bayan sallar magariba ‘yan rakiyar nata sukayi mata sallama kowa
ya kama gabansa,ganin har isha’i tayi shiru sai ta daura alwala tayi
sallar isha’inta,sam gidan ba,gabanta ke yawaita faduwa tana ambaton
hasbunallahu wa ni’imal wakil,ga abdallah na tare da mukhtar tare
zasu taho da shi,ganin shirun yayi yawa sai ta miqe ta kunna saudi
qur’an Allah ya taimaketa ma akwai wutar nepa ta zauna tana ci gaba
da saurara zuciyarta na mata wani iri babu dadi.
Firgigit ta dawo hayyacinta tana duba agogo,goma na dare ta dubi
wayarta dake ta faman ruri,sunan malam ta gani kam screen dinta,sai
taji gabanta yayi mummunan faduwa har sai da ta furta hasbunallahu
wa ni’imal wakil a bayyane sannan ta kara wayar a kunnenta
“sumayya kina ina?” Abinda taji malam ya fadi kenan,sai tambayar ta
bata mamaki
“Ina gida na malam”
“Yauwa to maza kashe wayarki ki fito qofar gida abubakar na
jiranki.yace yana ta bugu bakiji ba”sai ta amsa da to kawai tare da bin
umarnin malam din kawai tana jin wani yanayi nabin fata da tsokar
jikinta,hijabin data idar da sallah ta zira ta fito kai tsaye qofar gidan ba
tare data rufe gidan ba.
Ya abbakar ne tsaye jikin adaidaita sahu kansa a kife,qarar bude
gidan ya janyo hankalin sa,sai ya kalleta
“ya baki kulle gidan ba,malam ke son ganinki”
“To” kawai ta kuma cewa ta koma ta jajjanyo qofofin,tana fitowa ta
miqawa ya abubakar wayar tata don ji tayi ta fara yi mata nauyi a
hannu,kallonta kawai yayi ya sanya hannu ya amshi wayar ya sanya a
aljihunsa suka shiga adaidaita sahun ya jasu suka bar qofar gidan ba
tare da kowa ya sake cewa komai ba.
Cikin harabar asibitin mai adaidata ya faka ya abbakar ya biyashi
suka fito,binsa kawai take a baya ba tare da tasan inda take jefa qafarta
ba,tarin tambayoyi ke yawo kan kwanyarta amma ta gaza furta koda
guda?,shin waye a asibiti?,me ya faru ko meke faruwa?.gab da zasu
haura saman asibitin ta iya tambayarsa
“Ya abbakar,wai me yake faruwa?,waye ba lafiya?”
“Babu komai muje kawai”
Tun daga farkon barandar ta fara cin karo da mutane.yaya
yahanasu.malam,kawu mahaifin abdur rahman da hajiya
mahaifiyarsa.jamila yarinyar yaya yahanasu, sai mamanta da wasu
mutane uku da batasan su waye ba,tunda taga yaya yahanasu mukhtar
ko abdallah ne suka fado ranta,jikinta ya fara rawa sai ta fara qoqarin
faduwa sanda suka had ido da yaya yahanasu taga ta saki kuka,da sauri
hajiyan abdur rahman ta qaraso ta tareta ta zaunar da ita kan kujera
tana fadin
“Yi a hankali sumayya, babu komai in sha Allah Allah zai bashi lafiya,kiyi
masa addu’a”
“Waye hajiya me ya sameshi” malam ne ya qaraso yayi mata
bayani,hatsari mukhtar din ya samu yana hanyar tahowa gida shida
abdallah gab da sallar magariba,yanzu haka mukhtar din na tare da
likitoci amma sunce yanzu zasu fito da shi saidai ICU zasu kaishi,wani
irin tauri taji zuciyarta tayi
“La haula wala quwwata illa billah” ta dinga maimaitawa,jin jikinta take
kamar ba nata ba.
Bata ce komai ba har zuwa sanda aka bude qofar wani daki aka turo
gadon,mukhtar ne kwance tamkar gawa,babu abinda ke aiki a jikinsa
sai numfashinsa dake fusga duk bayan wasu daqiqu,kansa nannade da
bandeji fari wanda jinin da ya ci gaba da ratsowa ke barazanar sauya
masa kala,a haka ma sun gyarashi sun dan gogeshi,wani kalar tashin
hankali ya ruftowa sumayya,sai ta miqe tsaye har suka wuce da shi
intensive care unit din,kukan yaya yahansu na haduwa da nata tashin
hankalin yana yamutsa qwaqwalwarta,qunshe bakinta tayi cikin hijabi
ta saki wani irin kuka qasa qasa ta soma furtawa
“Ya ubangiji na,na roqeka kada ka sanya wannan ya zama cikin KUNDIN
QADDARA ta,Allah na tuba,na tuba ubangiji na” abinda ta dinga
maimaitawa kenan qasa qasa,hajiyan abdur rahman ita ta dinga
lallashinta,saidai babu abinda ke qara mata sai tashin hankali ahaka
sha biyu na dare ya cimmasu dai dai lokacin da likitocin suka
fito,bayani suka yi masu kan dakin bai buqatar shigar mutane ciki, haka
nan mutum daya suke da buqata wanda zai zauna da mara lafiya
“Don Allah don annabi malam ku qyaleni na kwana,wallahi bazan iya
tafiya gida ba” sumayya ta fada tana fashewa da kuka,babu wanda
tausayinta bai kama ba anan,ganin babu yadfa za’ayi a barta ita daya
kawu da ya abbakar zasu kwana cikin asibitin,ita kuma ta kwana gun
mukhtar din.
A hankali ta dinga takawa har gaban gadon da mukhtar din ke
kwance,ko ina na’ura ce ke aiki a jikinsa,baki daya fuskarsa ta sauya
kamar ba mukhtar ba,kallo daya zaka masa kasan lallai ya bugu sosai a
kansa don tuni har ya kumbura kan nasa,kujera ta ajiye bakin gadon
tana qoqarin danne zuciyarta tare da tuna nasihar da malam yayi kata
kafin su tafi
“Kuka baya maganin komai,addu’a ita ke magani” abinda ya gaya mata
na qarshe kenan,kanta ta girgiza tana sake baiwa kanta qwarin
gwiwa,sai ta kama tafin hannunsa ta sanya cikin nata,a hankali murya
can qasa mai cike da rauni ta soma karanto ayoyin qur’ani wadanda su
suka dinga debe mata kewa tsawon daren, saidai abinda ke daga mata
hankali dai dai da second daya babu wani abu da taga ya motsa daga
jikinsa,wanda likitocin sunce ta kula ko yaya taga ya motsa ta sanar
musu,duk da lokaci bayan lokaci suna shigowa suna sake dubashi.
Sai da suka saitu sosai kan hanya sannan mama tace
“Ina abdallah” tofa,sai lokacin hankalin kowa ya dawo jikinsa,duk
cikinsu babu mai amsar tambayar,don hatta jama’ar da suka ceci
mukhtar dim babu wanda yace yaga yaro,take wani sabon tashin
hankalin ya samesu,mama kam kasa daurewa tayi saboda tsananin
tausayin sumayya sai kawai ta sanya kuka,kai tsaye malam ya nemi
alfarmar mai abun hawar ya canja akalarsa zuwa policestation wanda
tafi kusa da inda al’amarin ya faru don si shigar da report cike da
matsanancin tashin hankali.
Kiran sallar asubar fari sanyi ya fara busowa,sam bata lura ba tana
gyara zamanta,tana daga kai suka hada idanu.ya bude idanuwansa tar
yana kallonta,wani farinciki ya dinga zagaya ta,ga mamakinta taji sai
taji ya kita sunanta,ciin matsanancin farinciki ta amsa
“Qarfe nawa?”
“An kusa sallar asuba”
“Daura min alwala sumayya banyi sallar magariba da isha ba” girgiza
kai tayi
“Ya mukhtar jikinka duka kayan aiki ne,ka bari likita yazo sai ayi maka”
tubure mata yayi hakan ya sanya ta lallaba ta shashshafa masa ruwan
iya inda zai yiwu,.yana daga kwancen ya dinga halarto da sallar yana yi
har ya kammala baki daya tana zaune tana kallonsa,yana sallamar
qarshe kansa saitinta ne sai ya zuba mata idanu,murmushi tayi tace
“Sannu ya mukhtar” kai ya kada mata sannan yace
“Ina abdallah” abdallah,ta dinga nanatawa,idan kunnuwanta basuyi
mata qarya ba ance tare suke da abdallah,to ina yake ina yayi?
“Ina fata lafiya yake babu abinda ya sameshi” tabbas lafiya yake idan da
ba lafiya ba da sun gaya mata
“Lafiya yake ya mukhtar” ta fada cikin salon son kwantar da hankalinsa
“Alhamdulillah” taji ya fada sai ya maida kansa,cikin farinciki da tada
sallah itama.
Shaquwa taji ya soma yi wadda kan ta idar da sallar ta qara
yawa,tana sallamewa tayi kansa tana masa sannu,da hanzari ta dauko
ruwan roba ta bude ta fara bashi a hankali,sosai ya sha ruwan kuwa
sannan ta cire roban daga bakinsa ta qulle tana masa sannu,minti biyar
tsakani shaquwar ta dawo,ta sake matsawa gunsa tana riqe da
hannunsa tana masa sannu cikin tashin hankali ganin yadda qirjinsa ke
dagawa wannan karon
“Bari na qara maka ruwan” ta fadi tana shirin juyawa inda gorar ruwan
take,sai taji ya damqe hannunta,juyowa tayi tare da tsayawa cak kamar
an kafeta,idanuwansa taga sun fara juyewa,jikinta ya hau rawa ta
qanqame hannunsa tana fadi a fili
“La’ilaha ilallah,muhammadur rasulullah” abinda ta dinga maimaitawa
kenan a fili babu qaqqautawa,a hankali taji ya kama yana
maimaitawa,kusan minti biyu yana fada shima cikin fusgar numfashi
sai taga idanunsa na lumshewa,riqon da ya yiwa hannunta tsaurinsa ya
sassauta
(Abinda ake so ga kowanne majinyaci kenan,mutuwa na da sa gigita da
daga hankali,amma gata ake so ka yiwa mamaci wanda shine qarshen
qaunar da zaka nuna masa,a yayin daka fuskanci wasu alamu na fitar
ruhi daga gangar jikin majinyaci,bakinka ya dinga ambaton la’ilaha
ilallahu muhammadur rasulullah ko za’a dace mamaci ya kama,ba
cewa ake fadi abinda na fada ba,ko kuma cene la’ilaha ilallah,a’a ka
dinga fadi yadda kunnuwansa zasu iya ji,idan Allah ya qaddara
bawansa ne na gari sai ya kama ya kuma cika da ita,Allah kasa mu cika
da wannan kalma mu da daukacin musulmi baki daya,amin).
Hannunta ta zare qirjinta na fat fat fat, hawaye ne ke bin
kuncinta,wasi wasi ya cika zuciyarta,fata take ba abinda take zato
bane,wannan tunani ya sanyata fita da gudu tayi ofishin likitan.
A rude ta fada ofishin likitan tana kiransa,likita ne mai kirki.yq gane
ko wacece saboda haka ya kiqe kawai ya biyota,zata fada dakin ya
dakatar da ita yace ta jira a waje
“Sumayya.jikin muntarin ne?” Kawu wanda idar da sallarsu kenan daga
masallaci suka yo cikin asibitin suka tambayeta
“Kai kawai ta iya daga musu hawaye na bin kuncinta,don bata jin zata
iya cewa komai.jiri ta faraji yana neman kayar da ita saboda tashin
hankali da mintinan da suka kwashe a tsaye,sabida haka sai ta daddafa
ta zauna kan kujerar sake barandar dakin.
Likitoci biyu ne suka zo suka sake shigewa dakin suna nan
zaune,awa guda ta kusa shudewa dai dai lokacin da mama halima da
zainab suka iso,yayin da malam ya fara biyawa ta police station ko an
samu labarin abdallah.jikin mama ta jingina kawai ta kwantar da kanta
a kafadarta ba um ba um-um,sannu maman ke mata tana tambayar
jikin mukhtar din,kawu ne ya amsa mata da cewa da sauqi don baki
dayansu hankalinsu bai jikinsu.
Budewar qofar dakin ne ya ja hankalinsu, likita na farko ya wuce
baice musu komai ba,na biyu ma haka, na ukun ne ya tako gabansu a
hankali sannan ya dubesu
” dukkan mai rai mamaci ne wannan alqawarin Allah ne babu mai zama
cikin duniya sai ya taf,ina mai baku haquri,Allah ya yiwa mara lafiyanku
cikawa,sai kuyi masa addu’a”,kuka ne da salati ya gauraye wajen, wani
dogon numfashi sumayya ta ja,cikin daga murya wadda bata san ta yita
ba ta furta
“INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN,ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI
WA AKHLIFNI KHAIRAN MINHA” tun daga haka bafa dada ba bata rage
ba,don ba sosai take ganewa ba,bin kowa kawai take da idanuwa.
Isowar yaya yahanasu shi ya sake ruda gurin,zubewa tayi a qasa tana
kuka kamar ranta zai fita,daga bisani ta sume a nan,sai da aka bata
taimakon gaggawa sannan ta dawo hayyacinta,zuwa lokacin an
kammala settling na tafiya da gawar mukhtar,motar asibiti suka basu a
kaishi ciki(ambulance)itakam sumayya ido kawai take bin kowa da
shi,sai ajiyar zuciya da take ta faman saki har suka isa gidansu na
aure,gidan da suka tanada domin sabunta rayuwar aurensu,gidan da
suka ciwa burin sake gina kyakkyawar alaqa da danganta har gaban
ABADAN,ashe wannan mafarki nasu bazai cika ba,ashe wannan buri
nasu yankakke ne,ashe sunyi zaman qarshe da mukhtar kenan a daren
jiya?,abinda ya dinga bijiro mata kenan,kallon mutane take suna
kuka,sai ta dinga jin dama itace su,dama itama zatayi kuka,domin kuka
ya fiye mata sau dubu akan bala’i da sukar da take ji a qirjinta.
Cikin uwar dakanta aka wuce da ita aka zaunar da ita,har lokacin
babu um ba um um sai ido kawai,a falo aka kwantar da mukhtar,aka
bawa makusantansa dama suka wanke shi aka maaa suttura sannan
aka buqaci ‘yan uwansa suje suyi masa sallama,take gidan ya sake
rudewa da koke koke,hakanne yasa anty salma tace a bar kowa ya
gama shiga sannan sumayya ta shiha daga baya,da qyar aka fidda su
yaya yahanash, ku ka take tana ya yafe mata,itakam ta yafe masa dan bai
taba saba mata ba,tsakaninsu biyayya ce irinta d’a da uwarsa tunda ta
fara riqonsa har ta aurar da shi.
A hankali take takowa cikin falon da taimakon hajiyan abdur rahman
wadda ta riqeta,gaban gawar mukhtar ta durqusa wadda ke lullube
cikin likkafani aka sake rufeta da wani mayafin,kanta ta duqar zuciyarta
na suya tana jin zafin yana ratsa dukkan sassan ilahirin jikinta,tana daga
kai suka hada idanu da malam,da idanu ya mata nuni ta masa
addu’a, hakan ya qwarara zuciyarta,a hankali ta soma fadin
“Allah ya jiqanka ya mukhtar ya gafarta maka,ya Allah ka tsareshi daga
azabar qabari da fitinarsa,ya Allah gashinan yana mai buqatuwa izuwa
rahamarka,kai mawadaci ne daga barin azabtar da shi, idan ya kasance
mai kyautatawa ya Allah ka qara masa kan kyawawan ayyukansa,idan
ya kasance mai sabo ya Allah kayi masa afuwa,ya ubangiji ga mukhtar
nan,bawanka ne Allah ka gafarta masa kayi masa rahama,ka yalwata
masa makwancinsa,ka wankeshi daga laifuffukansa da ruwa da
qanqara kamar yadda ake tsaftace farin tufafi daga dauda,ka sauya
masa gida wanda yafi gidansa,da iyali wadanda suka fi nasa,da mata
wadda tafi tasa..”sai ta sake yin qasa da kai,karo na farko da hawaye
ya samu gurbi cikin idanuwanta,babu wanda bata burgeshi ba a gun da
irin jarumtarta,kamar yadda babu wanda tausayinta bai ratsa shi
ba,alfaharin haifar diya irin sumayyan ta kama malam, Numfashinta ne
ya yanke,duhu ya fara mamaye idanuwanta, kunnenta ya daina jin
komai,daga nan ta daina gane komai sai daukarta akayi aka fita da
ita,kamar yadda aka dauki gawar mukhtar zuwa gidansa na
gaskiya, gidan dake jiran kowanne bawa.
13
Bata sake sanin inda kanta yake ba sai gab da sallar la’asar,har ana
shawarar kaita asibiti idan aka kammala sallar la’asar din bata farfado
ba,da kalmar shahada ta farka,daga bisani kuka ta sake qwace
maga,qanqame anty salma tayi tana rusa kuka mai tsuma
zuciya,wanda hakan ya sake sanya wadanda ke dakin fashewa da
kuka,babu wanda bai tausaya mata ba,ba shakka mutuwar miji babban
al’amari ne gun diya mace,mijin ma irin mukhtar,shiru kam yaqi ywuwa
a gurinta,har sai da malam ya shigo da kansa ciki wanda basu jima sa
dawowa daga wajen ‘yan sanda ba,hankalinsu a tashe yake don babu
labarin abdallah,baiso wannan labari ya kai kunnen sumayya,so yake
kafin komai ya lafa a ga abdallahn a duk inda yake,ya jima da ita a daki

kafin ya fito,tayi shiru amma har hanzu hawaye basu bar bin kuncinta
ba,haka nan bata fasa ambatar innalilahi ba cikin zuciyarta.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]