[Advertisements⬇️]

QADDARAR SUMAYYA CHAPTER 23 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

QADDARAR SUMAYYA

CHAPTER 23Ungawa ce mai matuqar kyau da tsari,akwai nauikan mutane
daban daban cikinta,saidai akasarin mzauna cikinta din masu hannu da
shuni ne da kuma masu rufin asiri ko wadanda suke ma’aikatan
gwamnatin tarayya ta basu gida su zauna kamar su anty dije.
Sai da mansur ya fidda kayanta baki daya ya shigar mata cikin gidan
ta masa godiya sosai sannan ya ja motarsa ya shige wani katafare kuma
hamshaqin gida dake kallon nasu.
Dukka yaran gidan na nan kasancewar ranar qarshen mako ce,laila

ita ce babba,sai hafiz mai bi mata,sannan khalifa sai nasir sai auta
amina minal,a qalla laila zata yi shekaru goma sha hudu,ita ta fara
ganin shigowar sumayya falon,ihu ta sanya wanda ya janyo hankalin
yan uwanta ta nufi sumayya ta rungumeta,haka sauran suka baibayeta
wanda ya janyo musu faduwa a qasa dukansu suna dariya,da qyar ta
samu suka dagata suka koma saman kujera sannan ta soma
tambayarsu anty dijen don bata ji motsinta ba,dining laila ta nuna wa
sumayyan tana cewa
“Kinga yaya sumayya can duka abincinki ne,tun dazu mama ke jiranki
baku iso ba har ta gaji ta shiga gidan daddy prof,amma bari naje na
kirata” ta fada tana yafa dan yalolon mayafinta tayi waje da
sauri,khalifa sumayya tasa ya fara nuna mata toilet ta shiga tayi
alwala,tana kammala alwalar anty dije na shigowa
“Sai yanzu?,gaskiya kunyi nauyi a hanya kamar wadanda suka hau
motar haya inji hajiya bilki” murmushi sumayya tayi tana duban anty
dije wadda ta sake gogewa bisa dukkan alamu zaman garin ya karbeta
matuga,ta kuma zama yar gayu ita da yaranta baki daya
“Wallahi anty sai da muka biya kasuwa muka karbo wasu kaya sannan
har mun dau hanya wani oga ko yallabai ya maida ku zoo road karbo
dinki”
“Eh inaga man ne dinkunan su’ad ce,maza yi sallar kizo kici abinci kafin
mu zauna hirar yashe gamo” ta fada tana sanya su laila dauke
akwatunta zuwa wani daki da aka tanada saboda baqi irinta.
Sai da taci ta qoshi sannan suka baje a falon ana hiran yaushe

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

gamo,kusan haka suka qarar da wunin ranar,ko da malamar lesson din
yaran ma tazo guduwa sukayi suka qi zuwa sai tafiya tayi,da dare ma
yayi da qyar suka tafi dakinsu don cewa sukayi tare da sumayyan zasu
kwana,saida anty dije ta korasu saboda tana son suyi zance,sosai suka
sake kuwa don mai gidan ta baya nan sun tafi semina lagos,sosai anty
dije ta sake kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari ta rufe da
fadi cikin sigar tsokana
“Duk da nasan sumayyan tawa zuwa yanzu ta fara girma,hankali ya fara
zuwa mata” itama dariya tayi,sai wajen sha daya da rabi sannan ta fita
ta barta,to nan din ma lukman bai barta ba da hira sai data ce tana jin
bacci sannan yace
“Ki kula min da kanki to na baki amanar kanki my dear kinji”ajiyar
zuciya ta saki sannan ta amsa masa ta katse kiran,taso kiran halina taji
ya abdallah yake,amma ganin dare yayi nisa ya sanyata ta haqura ta
barwa gobe,duk sai taji tana kewar yaron nata.
****** ******
******
Kwanakin da tayi a garin kwanaki ke da suka yi mata dadi
sosai,kullum yaran na nanuqe da ita suna hira,sauqin abun sun gama
jarabawa hutu kawai suke jira,wani lokaci da yammaci anty dije kan
debe su da motar mai gidan da ya barta a gida ta kaisu park su dan sha
iska suyi ciye ciye su dawo,hakan na yiwa sumayya dadi,lallai ko yaya
ka motsa daga wani gu zuwa wani gu zaka samu sauyi zuciyarka zata yi
dadi.
Duk wani abu da ya kamata a yiwa amarya anty dije da kanta ta
yiwa sumayya,cikin kwana goma ta hadata tsaf
Ana ya gobe zasu koma kanon laila na kwance kan cinyar sumayya
sumayyan na tsefe mata kitsonta zasu wankin gashi da yamma anty
dije ta fito ta dubesu
“zan dan shiga gidan daddy prof zamuyi sallama da su,Allah baiyi dani
za’a yi sunan nan ba”sumayya ta daga kai ta dubi anty dije
“au haihuwa akayi halan?”
“Sai yau zaki tambaya kenan,kwana na nawa ina leqa su amma baki
taba karar ki shiga ku gaisa da mutanen ba,direban gidan ya dauko ki
daga kano fa,surukar gidan ce ta haihu” murmushi sumayya tayi
“To ai ban sansu bane anty”
“Ni ai na sansu kuma gashi na gaya miki,mutanen akwai tsabar
mutunci da karrama mutum,duk yadda Allah ya musu tsabar arziqi
amma basu raina na qasansu,mai gidan bakiga yadda ya dauki abban
khalifa ba kamar dan cikinsa,su khalifa kuwa ya maidasu tamkar
jikokinsa” jinjina kai sumayya keyi sannan tace
“Allah ya saka musu da alkhairi, kice ina musu barka”
“Zasuji tunda ba zaki din ba” inji anty dije ta fice tana mita sumayya ta
bita da dariya.
Basu jima da kammala tsifar ba anty dijen ta dawo hannunya dauke
da baqar leda, ta cillar kan cinyar sumayya
“Da baki iya zuwa gaida mutane ba gashinan haj bilkisu tace na kawo
miki kiyi fitar biki,ta yaba da zabin leshin ki wai kin iya zabar kala,ashe
tare kuka shiga shagon da mansur din”. Baki ta saki sanda ta fiddo
leshin taga daya daga cikin wadanda suka siya dinne
“Anty kinsan kuwa nawa ne farashinsa duk guda daya?”. Dariya anty
dijen tayi
“Hmmmmm,bakisan mutan gidan bane sumayya,kinga ku tashi ku
shirya ku wuce wankin kan nan kada dare yayi muku hanya “ta furta
tana miqewa ta nufi kitchen.
**
Sanda suka isa kwanaki biyu sukayi saura a daura aure don babu
wani event da sumayyan ta tsara yi.yaya abubakar ne kawai zaiyi
walima bayan an gama daura aure.
Kusa awa guda kenan da shigowarta gidan amma bata ga wulgawar
abdallah ba,tun tana kawaici bata tambaya ba har sai data magantu
“wai nikam ina abdallah ne?” Maimakon maman ta amsa mata sai tace
da ita
“Kije malam nason magana da ke” hakanan taji jikinta bai bata ba,ta
miqe ta zura hijabinta ta fice.
A ladabce ta gaisheshi ya amsa yana tsokanata abuja ta karbeta,sai
ya bata kunya ta sunkui da kai tana murmushi yayin da tausayinta
kuma ya darsu a zuciyar malam din
“Sumayya maganar da zamuyi da ke nasan ba zata miki dadi ba,domin
raba da da uwa sai Allah,saidai babu yadda muka iya,bayan tafiyarki
mukhtar yazo ya karbi yaronsa..”A firgice ta dago ta dubeshi muryarta
na rawa idanunta na fidda ruwan hawaye
“Amma malam me yasa zaimin haka,rabamu ken…”kaaa qarasawa
tayi tayi qas da kanta
“kiyi haquri sumayya,shi ya fiki a haqqu da shi,sannan ya riga da yace
baiso yaron yayi zaman a golanci gidan wani kamar yadda shima
yayi,kiyu haquri nasan ba wai ya rabaku bane na har abada saboda
yadda yazo mana bada nuna isa ko qarfa qarfa bane,abinda na lura
shine bazai iya jurar rashin ganin yaron bane,tunda idan har kika tafi da
shi bashi yiwuwa ya dinga binki gidan mijinki da sunan yazk ganin
dansa,kiyi haquri babu komai ai kuna tare,na tabbata za’a dinga kai
miki shi”malam ya fada cikin tausasawa. Haka malam din ya dinga
lallashinta yana bata kalamai har ta samu ta danji sauqin zugin
zuciyarta,saidai abinda take ji na game da kewar yaron har yau bai
sauya ba.
Data koma daki taga sauran kayayyakinsa kasa ci gaba da daurewar
tayi,ba shakka raba da da uwa ba qaramin abu bane,shi yasa aka ce ko
mutuwa tana shakkar idon uwa.yaya wadanda suka rabu da
‘ya’yayensu suke ji rabuwa ta har abada?,ashe da sauqi ita tunda yana
nan cikin duniyarta kusa da ita amma duk da haka ta gaza
daurewa,kuka tayi mai yawan gaske wanda shi ya haifar mata da
zazzabin da ciwon kai mai tsanani har ranar da aka daura auren, haka
aka tattarata aka kaita dakinta tana mai ci gaba da kuka mai
qunshe da abubuwa iri daban daban
****
*****
Lukman Bashir shine asalin sunansa,haifaffen garin kano cikin
qaramar hukumar kano municipal.yayi karatunsa iya N.C.E sai ya fada
kasuwanci gadan gadan,mahaifiyarsa hajiya kubra shi kadai tallin talta
haifa,hakan ya sanya ta dauki so da qauna da kulawa ta dora
masa,wannan shine dalilin da ya sanya duk lokacin da yayi aure ta
fuskanci yana mutuwar son matar take rabasu don wai ba zata bari a
mallake mata yaro ba tana kallo,kasancewar gidansu daya part guda
yayi mata da ya tashi ginin gidansa,a haka a haka ta sanya lukman ya
rabu da mata kusan hudu kenan duk da cewa yana dacen matan aure
masu matuqar haquri da biyayya saidai ita sam bata gani,haquri da
biyayyar da sukewa lukman din ita ke jawo musu qauna gunsa,amma
ita gani taje tsabar asiri ne matan suke yi,sam matan basu da
sukuni,hatta zanin daurawa idan zai musu ita ke karbar kudin ta siyo ta
bada adinka musu ita kuwa sai wanda ta zaba zata sanya,hakanan duk
cikin matan da yake aurowa mutum daya ce ta haihu da shi don na
wani dadewa take bari suyi ba,ita din ma a gidansu ta haife sai da ta
yaye hajiyan tasa aka karbota, ya mace ta haifa wadda ake kira da
nuwaira.
Hausawa suka ce alhaki kwikuyo ne,a irin haka ne Allah ya hada
lukman da KARIMA gogaggiya mai idanu a tsakiyar kaa wadda ita ta
haifa masa yara uku dukka mata zaitun marwa da radiya,da fari
kariman lumbu lumbu ta yiwa hajiyan har ta saki jiki da ita,sannan daga
bisani ta sanya gaba daya daga lukman din har hajiyan aka sanya su
qarqashin ikonta,daga lukman din har hajiyan umarni suke karba daga
wajenta,babu wanda ya isa ya tsallake abinda ta shimfida masa,sai a
bayan idonta su yita takaici da jimami amma a gaban idonta ko tari ba
wanda ya isa yayi, mutane da yawa sunyi murna sunyi shewa da
wannan sauyi domin ya zamewa hajiya kubra izina.
Tun bayan da ya auri karima bai kuma gigin qara wani auren ba sai a
yanzu da yake KUNDIN QADDARArsa na rubuce da auren
sumayya,sanda yake gaya mata zai qara aure a tsorace yake,ita kanta
tayi matuqar mamaki,a fusace ta shiga dakinta ta kira wayar malaminta
ta sanar masa,wayar tace ya kashe zaiyi bincike nan da awa guda zai
nemeta.ya kuwa nemetan ya sanar mata wannan aure ba makawa sai
an yishi saboda yarinyar nada addu’a hakazalika ‘yar gidan malamai
ce,wannan kalma ta sake tunzura karima ta sanya aka sake sabunta aiki
mai kyau akan hajiya da lukman don kada sumayyan ta samu kafar rusa
mata shirinta wanda ta riga ta qudurceshi cikin ranta,haqura tayi saidai
duk wani harkar biki kama daga lefe da sauransu ita tayi su,komai sai
data ninka kudinsa sannan kuma ta zuba abinda ranta yaga
dama,sauqin daya gidansu sumayyan gida ne na dattako babu wanda
ya damu dabtsada ko yawan abinda aka zuba cikin lefen.
Qarfe tara da rabi na daren bayan an kaita gun hajiya an gabatar da
ita yayin da ita kuwa hajiyan ke fadin tabi karima wanda ya baiwa kowa
mamaki sannan aka dawo da ita dakinta wanda falo ne guda daya
makeke sai dakunan bacci na kowacce mace da bandaki a cikinsa,sai
dakin yara da mai gida kitchen da bandaki duk cikin babban falon,cikin
falon dai ya kira sumayya don dama ita karima na zaune a falon tun kan
a kawo sumayyan har kowa ya watse
“TO sumayya wannan itace uwar gida na uwar ya’ya na,idan kika bita
kamar kin bini ne,na auroki ne ba don bana sonta ba,bana so kumaki
raina min ita, hatta hajiya farincikinta shine farincikin karima da fatan
kin gane” kanta ta cira a hankali tana dubansu baki daya,cikin zuciyarta
ta furta
“Ikon Allah.yau kuma da wacce kalar Allah ya hadani?”.
Miqewa kariman tayi cikin izza tana yatsina
idan ka gama ka sameni a daki,kada ka wuce minti biyar”
“T …to to” ya amsa cikin inda inda tare da binta da kallo har ta wuce
dakinta,da sauri ya dubi sumayya
“Amarya ta muje na rakaki daki kinji” ya fada cikin kwantar da
murya,ba musu ta miqe tayi gaba mamaki na kasheta,wai dama haka
lukman din yake?me yake shirin faruwa ne?.
Bakin gado ya zaunar da ita yana duba agogo don kada yayi laifi
“Zauna bari naje,in Allah ya yarda zanyi qoqarin dawowa,ga kaxarki
nan idan kina jin yunwa kici kafin na dawo” ya fada yana juyawa ya fice
da sauri,binsa tayi dakallo baki daya qimarsa da mutuncinsa da take
dan gani a da suna ficewa fit daga ranta,hawaye suka soma fita daga
kuncinta data tuna rayuwar gidan mukhtar makamanciyar
wannan,saidai sam da alamu bata kai qazancewar wannan ba,ita kuma
nata salon QADDARAR kenan?. Juyawa tayi ta kwanta tana faman zubar
da hawaye.
Har bacci ya soma fusgarta taji yana ambaton sunanta sama
sama,ta bude idanunta tana dubansa, murmushi yake yana kallonta
shima tare da duba bakin qofar dakin kamar wani ya biyoshi,ganin ta
tashi ta zauna ya sanyashi maida qofar dakin ya murza key,kamar
wanda ke sauri jirgi zai tashi ya barshi yake magana
“Tashi maza ki dauro alwala, ina fatan dai kinci abincin ko?…inyi
sallar isha’i?..dauro alwala sumayya babu lokaci..”ya fadi yana satar
kallon qofar dakin
Cikin mamaki take dubanshi duk ya wani firgice,lokaci kada ya qure
kamar yaya take tambayar kanta
” don Allah tashi mana sumayya kada ta…”bai qarasa fada ba aka fara
dukan qofar kamar za’a ballata
“Innalillahi wa inna aihi raji’un” ya fada yana dafe kansa.
“Zaka bude ko sai na sassaba maka,maci amana” inji mai buga
qofar.jiki ba qwari ya nufi qofar ya bude mai bugun ta fado dakin tana
raba idanuwa,kubra ce sai data qarewa dakin kallo ta fuskanci babu
abinda ya faru sannan ta kalleshi
“Ni zaka ci amana ka karya alqawarin daka yimun?,to wallahi ko kwana
a dakin baka yi butulu kawai, maye,tunda ni ban isar maka ba,wuce
muje nace ka tsaya ka kafeni da idanuwa” sai ya waiwaya yana duban
sumayyan har sai data ingiza qeyarsa sannan ya fice yana waiwaye.
Kan sumayya ta dawo da kallonta'”‘da sauran quruciyarki amma kin
zabi nakasta rayuwarki,idan don kwanciyar aure kika zo gidan nan to
kinyi babban kuskure don yadda kika zo haka zaki koma,don babu
wasu ‘ya’ya da za’a haifa a gidan nan sai nawa yaran,itama wadda aka
haifa din don uwarta ta rigani zuwa ne,wlh da ni na rugata zuwa da bata
isa ta haifeta ba,keda lukman kuwa saidai kallo”
“Ke lukman ya dama,kuma ta Allah ba taki ba,ni an bani ilimin yarda da
QADDARA mai kyau ko akasinta, hikinar ubangiji kuma yawa
gareta,hakanan sanin gaibu sai Allah,duk kuma nisan jifa wataran qasa
zai fado,mai yiwuwa ma idan ya tashi fadowar ya dawo tsakiyar kan
wanda yayi jifan”
“Ke ki iya bakinki wallahi idan baso kike kiyi kwanan gidanku ba”
“Idan kinso kina iya karbe aron numfashin ma da kika bani idan yaso
nayi kwanan kabari baki daya” sumayya ta fada hankalinta kwance,don
ya zuwa yanzu tana jin ta gama daukar haquri da rainin wayon
kishiya,bata cuce su ba don me su zasu dinga cutar da ita,tabbaa dafi
da gubar zainab har yau bata bar illata zuciya da gangar jikinta ba,don
kusan ita ta zama silar data sake cillota wannan muhalli da take ganin
wata rayuwa miji ke biyayya wa mata. Mamaki ya cika kariman don ta
jima rabon da a mayar mata da magana haka,sai zuciyarta ta tuna mata
daga inda sumayya ta fito,take gumi ya fara tsatstsafo mata,tabbas sai
ta sake shiri a kanta,qwafa taja sannan ta juya tana fadin
Da karimatu kike zancan lallai bakisan wace ni ba”bata yi nauyin bakin
maida mata amsa ba don kada ma ta fita bata ji ba
“hakanan bakisan wace sumayya ba,ki zuba ido kisha kallo”. Bayan
fitarta muqulli sumayya ta sanyawa qofarta ta shiga toilet ta daura
alwala,sam bata ji wata damuwa na barinta da angonta yayi ita daya a
dakin ba,kaya ta fiddo ta sauya wadanda zata sake a cikinsu sannan ta
sanya hijabi ta tada sallah,kyawawan nafiloli ta raya daren sosai da su
kafin bacci ya rinjayi idanuwanta.
asuba ta gari amaryar lukman”
Qarfe tara na safiya tayi wankanta,ta shirya cikin atamfa dinkin riga
da zani,ba wani kwalliya tayi ba amma tayi kyau,dakin ta sake
karkadewa ta goge sannan ta koma bakin gadonta ta sake
kwanciya,idanunta ta lumshe tana saqa da warwara,kewar abdallah
take ji sosai cikin zuciyarta har qwalla na shirin kawo mata,tunani ne fal
zuciyarta tana wassafa yaya rayuwa zata kuma kaya mata cikin wannan
gidan.
Hayaniya ta dinga jiyowa cikin falon da surutai,ta bude idanunta ta
kalli agogon dakin,goma tayi har da mintina arba’in da biyu,saita bude
sif dinta ta ciro hijabi ta zura kana ta sanya silifas dinta ta murda qofar
dakin ta fito.
Duk uban hayaniyar da take ji yara hudu ne cikin falon.yarinyar
farko wadda ita ta sake hautsina yanayin falon ma hakimce kan kujera
kamar wata babbar mace duk da du du du ba zata wuce shakara sha
uku ba,kallo take a tashar mbc three ta qure volume kamar ita da
mutum dari suke kallon,sai yarinya ta biyu wadda batafi shekara uku ba
dake zaune qasanta kan carfet taci uban indomie ta hadeta da ruwan
shayi tana wasa da ita,daga can wajen step na dining kuwa wasu yaran
ne su biyu,daya shekarunta goma daya takwas suna karyawa,su biyun
kadai sun dame gurin kamar qanwar tasu dai,ta sake wurga
idanunta,wata yarinya ce data tasamma zama matashiya wadda ta kusa
shekara goma sha hudu takure a saqon kujeru,kallo daya zaka mata
kasan daban take kamar yadda kamanninsu ya bambanta da sauran
yaran dake falon,don dukkansu kamarsu daya ita kadaice kamarta
daban kamar yadda ta fisu kyau baki dayansu.
Dukkansu sun ga fitowarta saidai babu wanda ya kulata,ta dubi
qofar dakin karima wanda ke garqame ta sake dauke kai
“Ina kwana anty”
Taji an ambata daga bayanta,saita waiwaya,yarinyar dake zaune ce
saqon kujera ta gaidata tana murmushi,maida mata murmushin itama
tayi tana mamakin zarnin dake tasowa daga jikinta
“Lafiya qalau,an tashi lafiya?,me sunanki?”
“Nuwaira”
“Sunan mai dadi” sai tayi murmushi tana cewa
“Na gode anty”
“Ko zaki rakani wajen kakarku?”
“Wa?,hajiya”
“Eh”
“Muje in rakaki anty” ta fada tana wucewa gaba sumayya na rufa mata
baya.
“Wallahi bari umma ta fito sai na gaya mata duk abinda kika yi,bata
ja mana kunne ba?” Yarinyar daje saman kujera ita ta ambaci hakan
tana jijiga kai,cak yarinyar ta tsaya kamar an ambata mata mala’ikan
mutuwa,idanunta na tara qwalla tace
“Kiyi haquri don Allah kada ki gaya mata”
“Wallahi sai na fada saidai ta kasheki” ta fada tana buga hannu alamun
babu fashi, wani abu ya tsayawa sumayya a wuya,takaici da mamaki
suka cikata,sai ta janye nuwaira tana fadin
“Muje babu abinda zai faru dake kinji kada ki damu” jikinta babu qwari
ta bi sumayyan suka fice.
Kafin su qarasa gun hajiyan sumayya ta dubeta
“Me yasa kinsan kina fitsarin kwance da kika tashi baki sauya kayanki
ba nuwaira?,kinsan fa ba’a son mace da qazanta” sai yarinyar ta fara
qwalla ta soma sharewa tana cewa
“Wallahi anty tunda bana fitsarin kwance,saddiqa keyi sai a hadamu
kwanciya gado daya,idan tayi duk sai ya jiqani,idan ta tashi ita sai
nuratu ta sauya mata kaya,ni kuma ba zan canza ba har sai umma ta
gama bacci tayi wanka ta fito sannan zata nunan wadanda zan sauya
din,koda asuba bana samu nayi sallah sai rana ta fito” ta fada da alamu
abun na ci mata tuwo a qwarya,shiru sumayya tayi tausayin yarinyar na
kamata,wannan wanne irin zalunci ne,tun kallon farko da ta yiwa
yarinyar ya nuna tana jin jiki a gidan,amma tana tunanin kamar ita ce
yarinyar nan daya da karimajiya ta gaya mata uwarta daban,don ta
tabbatar sai ta tambayeta
“Ina mamarki to?”
“Mama na tayi aure a wani gidan,tun kafin a yayeni aka karboni aka
bawa hajiya ni,to da abbanmu ya sake aure ya auro umma sai umman
ta karbeni nake gunta”take tsanar karima ta darsu a zuciyar
sumayya,lallai ba shakka bayan shirkar tsafi ma harda azabtar da
yarinyar da bata ji ba bata gani ba,wai me mutane suka dauki duniya
ne?,kowacce mace son kanta ya mata yawa?,burinta ta mallaki miji ta
rabashi da kowa nasa?,ta rabashi da ‘yan uwansa da tazo ta samesu
tare, yan uwa da suka zamar masa bango marufar asiri tun yana zanin
tsumma har kawo yau,ta rabashi da duk wani alkhairi uwa uba ta
rabashi da mahaliccinsa,ta sakashi a musibar da ranar gobe qiyama
bazai iya tsallaketa ba,ta rabashi da hankalinsa bare ya kula da
addininsa,wanda ya cancanci a bashi haqqinsa ta hana ya basu yanzu
duka wannan qauna ce?,sai tace sonshi take shi yasa ta aikata
haka,wannan ko babban maqiyinka ba shakka iya cutarwar da zai maka
kenan,da irin wannan tunani suka isa bangaren hajiyan
A duqe suka sameta tana snare talon nata dake matale da
carfet,kallo daya sumayya tayi mata ta fuskanci shekarunta basukai ace
tayi tsufar da tayi a yanzu ba,da sallama suka shiga ta dago tana a
musu riqe da qugunta wanda bisa dukkan alamu ciwo yake
mata,nuwaira ce ta gaisheta ta amsa babu yabo ba fallasa yayin da
sumayya ta qarasa tana amsar tsintsiyar hannunta tana
gaidata,amsawa tayi tana dubanta yayin da sumayya ke qarasa mata
sharar har ta kammala sannanbta dawo inda hajiyar ke zaune tana yiwa
nuwaira masifar sai zuba zarni take taje bandakinta ta wanke
jikinta,mamaki ya cika sumayyar,to ko batasan meke wakana bane cikin
gidan?,batasan ba laifin nuwairan bane karima ce ta cancanci fada idan
da duka ma ayi mata?,tashi yarinyar tayi ya shige bandakin hajiyar
sannan hajiyar ta maido kallonta ga sumayyan
“Ban gane fuskar ba wace ce ne?” Murmushi kawai tayi ta dan sad da
kai
“Oho,ko amaryar lukman ce” kai sumayyan ta gyada.
Shiru ne ya biyo baya,hajiyan na dan satar kallon sumayyan,sai taji
ta dan sake da yarinyar duk da ba hira suke ba zaman kurame ne,a haka
har nuwaira ta fito daga bandakin sanye da jiqaqqun kayanta wadanda
ta wanke bayan ta dauraye jikinta ta maida su a haka
“Wani nuwaira nikam bakuyu abin kari bane yau,gashi har sha daya na
shirin gotawa yau ba’a kawo kin komai ba,ko luba mai aikin bata zo
bane?”cike da madaukakin mamaki sumayya ke sauraron zancan
“Tazo hajiya,bansan ba’a kawo miki ba,don ko nima yau ban karya
ba,naga dai su nuratu na karyawa ni ma ba’a bani nawa ba”ta fadi babu
alamun damuwa tattare da ita bisa dukkan alamu ta riga da ta saba da
hakan.yamutsa fuska hajiyan tayi
“gaskiya na fara jin yunwa wlh,wannan abu Allah kayi mana
maganinsa”
“Amma hajiya ai naga kina da sauran kayan abincinki da kika ce bazaki
iya ci gaba da girki ba ai abba bai debe su ba ko?”
“To idan banda abinki ina fama da lalura ina zan iya,sharar ma don
bazan iya zama cikin qazanta bane nake daburtawa nake yinta” ta fada
ta muskutawa da alamu yunwa na sakadarta,tausayinta duka sai ya
kama sumayya ta dubeta
“To hajiya idan ba damuwa sai na shiga na girka miki ai ko? “haba ta
riqe
“a’a,har kya fara shiga madafi ta sanadina?,ki barshi babu komai idan
da sabo ai mun saba da irin wannan gashin,ke dai kawai Allah yayi
mana magani”murmushi tayi kawai ta miqe tana tambayar nuwaira
inda kitchen din yake.
Sallamar karima a gadarance ita ta maida hankalinsu bakin qofar,ita
ke gaba gogan na bintaa baya riqe da wani dan qaramin flask wanda
bako shakka abun karin hajiyan ne a ciki, idanunsa na kan sumayya
yana faman sakar mata murmushi ,wani takaici da haushinsa suka
qumeta saita dauke kai tana jin kamar taje ta shaqeshi, haka nan kawai
taji jarumin namiji yana burgeta,sai ta tuna sanda zainab ta fara murza
kambunta lokacin tana gidan mukhtar,tabbas ko a lokacin mukhtar din
kan tauna tsakuwa wani lokaci.
Hajiyan da za’a yiwa sannu a gaisheta ita ke faman yiwa kariman
sannu tare da gaisheta, lukman ya koma gefan hajiyan yana gaidata
cikin dari dari suke gaisawar kamar suruki da suruka duk don kada su
batawa karima rai,baki sumayya ta saki tana kallon abun mamaki
bayan hajiya ta bude flask din da aka kawo mata,wani gantalallen
soyayyen dankali ne da rabin wainar qwai babu ko tea amma hajiyan
sai godiya da sannu take mata
“Saidai yau kici haka hajiya don kafin na fito jikokin naki sun shanye
shayin”
“Ai babu komai,idan baka yiwa jikanka ba wa zaka yiwa” ta fada fara’a
kamar gonar auduga.
Kallon sumayya karima tayi bayan sumayyan ta gaida lukman
wanda ke faman binta da kallo kamar tsohon maye
“Ke baki iya gaida mutane ba” ta fada fuska a tsuke kamar wata
uwarta,waigawa sumayyan tayi ta watsa mata kallo
“Su waye mutanen?” Ta tambayeta bayan ta tsareta da ido,sai kawai
taji sumayyan ta mata kwarjini da irin kallon da take mata,janye idonta
yi ta dubi hajiya
“Hajiya kina gani dai a gabanki ko?” Ta fada cikin zafin rai,lukman yayi
saurin karbewa
“Bana son rashin zaman lafiya fa sumayya a gida na kinji ko?” Kallon da
wa kazo ta watsa masa sannan ta dauke kai,hajiya cikin rawarjiki tace
Ke yarinya, farincikinmu shine farincikin karima,saboda haka dole ki
mata biyayya ki kiyaye” girman hajiyan take gani,saboda haka ta dan
rusuna
“Insha Allahu hajiya kiyi haquri” ta fadi da sauri tana shigewa kitchen
din hajiyan don bata son ma ta sake kallon fuskar lukman bare ta
karima.
Tana kitchen tana hada girkin duk da wasu kayan buqatun
babu,mamaki da tunani fal ranta,a haka taji sallamar hajiyan,ta juya
tana amsa mata,qarasowa hajiyan tayi ta kama hannun sumayya kamar
zata saki kuka
“Kiyi haquri sumayya da abinda nayi miki dazu.yarinyar nan idan ta
umarcemu da abu daga ni har lukman bama iya musa mata,amma
nasan alhakin yaran jama’a ne yake bibiyata, haka kawai naji kin
kwanta min sumayya zan gaya miki wace ni me na aikata ga rayuwata
da rayuwar yarona”
Kafin sumayyan tace wani abu tuni hajiya ta fara bata labarin dukka
aure auren da lukman yayi wanda ita ce sila,da fari haushin hajiyan ta
dinga ji,amma daga bisani sai tausayinta ita da lukman ya baibayeta
baki daya,tabbas abu na farko data fuskanta ya janyo wannan matsalar
sakaci da rashin riqe ubangiji hannu bibbiyu,har qwalla sai data yiwa
hajiya da lukman din saboda aikin kariman ya shallake hankali.
cikin sanyin jiki ta riqe hannun hajiyan ganin tana zubda qwalla
“Kiyi haquri hajiya ki fawwalawa Allah lamarinki,ba shakka inna idan
ma alhakin ne ba mamaki,Allah na sonki shi yasa zai hukunta ki tunha
duniya,din hukuncin lahira da shi gwara na duniya sau babu adadi, in
sha Allahuni zanyi iya bakin qoqarina wajen ganin na daidaita lamarin
iya abinda Allah ya huwace min,ina so daga yau kisa a ranki ba zaki qara
jin tsoron karima ba,ba zaki sake bin umarninta ba sai abinda ya dace
shi zakiyi,a duk sanda kika ganta idan kika ji faduwar gaba ko tsoro ki
karanta ALLAHUMMAKH FINIHIM BIMA SHI’ITA matakin farko
kenan,sannan daga yau kada ki sake cin duk abinda ya fito daga
hannunta,ki umarci lukman ya kawo miki kayan abincinki a zuwan zaki
ci gaba da girki,ni kuma in sha Allahi zanci gaba da dafa miki” kai take
gyadawa cike da gamsuwa tana jin tamkar damuwarta na gab da
yayewa
“Sannan lukman danki ne hajiya, bakin uwa kaifi gareshi,ki dage da yi
masa addu’a,Allah ya yaye masa bala’in da ya fada ta sanadin abinda
ke kika aikata shi,bashi kadai ba,har ke dinma saikin dage da addu’a wa
kanki na neman tsari”
Kai ta sake jinjinawa
“Har na manta rabon da na sashi a addu’a ta,na gode da tunatar da ni
da kikayi,na gode sosai”
“Sannan hajiya,kinsan rayuwar da nuwaira take cikin gida kuwa?” Ta
tabo inda yafi mata qaiqayi
“Na sani sumayya na sani,saidai bani da ikon magana bani da ikon
gyarawa” ta fada cikin jimami,don har ga Allah duk cikin jikokinta tafi
qaubarta,din ta fita daban a cikinsu,nutsuwarta da komai da
komai,shiru sumayyan tayi sannan tace
“Babu komai,zanyi iya bakin qoqarina itama akanta kafin Allah ya kawo
qarshen lamarin”
“Na gode sumayya na gode, haqiqa kin zamo “HASKE cikin gidan d’ana
cikin kwana daya tal,ina miki fatan alheri sannan kuma ina miki fatan
samun nasara,Allah ya albarkaci rayuwarki da alkhairi masu tarin
yawa.ya tsareki” amin sumayya ta dinga cewa tana jin dadin addu’ar
har cikin ranta,ko da can ita din mai son wani na gaba da ita ne ya
albarkaceta, kusan tare suka gama aikin ta kammalewa hajiyan cikin
kula yadda tasan zai ishesu ita da nuwaira,tace zata turo mata ita taci
na rana dana dare,don ta lura bata samu albarakacin cin na safe ba,sai
na hajiyan da suka yayyafita.
Nan tayi zamanta gun hajiya,ita kanta hajiyan sai ta dinga jin dadi
cikin ranta,nuwaira ma ta dinga sato jiki tana leqowa har sanda
sumayyan ta koma bangarensu.
****
****
******
Cikin kwanaki hudu rak sumayya ta gama dukkan wani shiri nata na
tunkarar wakeken qalubalen data fuskanci yana danqare a gidan,ita
kanta mamakin kanta take yadda zuciyarta ta taurare baki daya har
take ganin zata qalubalanci karima wadda baki daya ta rusa rayuwar
gidan ta dora ta kan turbar da take so,sam sam yaranta irin yaran nan
marasa tarbiyya ko qanqani,su zagi babba duk girmansa ba komai bane
a gunsu,sam sam sumayya bata shiga shirginsu ko sakar muau fuska
tunda ta fuskanci inda tarbiyyarsu tasa gaba,hakan ya sanya suka faraa
shakkarta,sai kuma mai biwa babbar da ta soma son kula sumayya, sau
tari takan qwanqwasa qofarta idan ta bude mata tace ta shigo kuma sai
taqi,sai ta fuskanci shakkar mamarta take, hakan ya sanya ita sumayyan
ta fara qoqarin janyota a jiki,ga shegen gulma munafunci da iya kawo
labari,hatta da mahaifinsu suna iya dauko gulmarsa su kawo mata ita
kuma ta tuhumeshi kan haka,sumayyan na sha’awar hatta da tarbiyyar
yaran ta saisaita musu ita,don ta kula sam daga makarantar boko babu
kuma wata makaranta ta biyu da yaran ke zuwa wadda ake kira da
makarantar addini ko islamiyya,baki daya idan ka dauke sumayya banu
mai rayuwa kan ra’ayinsa sai abinda ta shinfida,tun abun na bawa
sumayya haushi har ya koma bata tausayi, ita sam ma baki daya bata ta
angon ko kadan,wanda zuwa yanzu hatta lokacin fita da dawowarsa
gida karima ta sauya masa duk don kada su hadu da sumayyan,ta saka
an qara narka masa aikin mantau akan sumayya wadda ko gefen silifas
dinta lukman din ma baije ba,sau tari takan tambayi kanta me yasa ta
auri lukman sai ta rasa dalili.amsa dava ke zuwa kanta
“Qila don kizo ki ceci rayuwar ‘yar gidan ne” ita kanta tafi gamsuwa da
wannan ce sahihiyar amsar
Cikin satittika qalilan shaquwa ta fara shiga tsakaninta da
hajiya,kusan koda yaushe can take wuni,ta yima haijan aikace aikace
sannan suyi girkinsu abinsu,sannu a hankali sauyi ya fara samuwa
tattare da hajiyan,sumayya ta zaburar da ita ta kuma koya mata
addu’o’i sosai,rana ta farko da suka fara fuskantar zuwan sauyi shine
randa kariman ta shigo da abincinta wanda aka saba sanwa hajiyan
don bazance bata ba,duk da hajiyan ta jima bata ci amma sumayya tace
ta dinga karba kada ta gaya mata idan yaso saita dinga bayarwa,tunda
ta shigo ta lura hajiyan sam bata rawar qafa yadda ta saba idan ta shigo
gunta,abu na biyu tana jiran taga hajiyan ta gaidata yadda ta saba sai
taga tayi fuska,ta maida hankalinta gun sumayya dake shafa mata man
zafi a gwiwarta data riqe mata take mata ciwo,wanda abaya bata da
wannan gatan saidai taci ciwonta ta warke don dolenta.
Kanta yayi masifar daurewa, abu na farko da yazo kanta aikin hajiyan
ya fara sako sako don dama kwana biyu tafi maida kai a kan lukman din
“Ga abinci nan” kariman ta fada a wulaqance,juyowa hajiyan tayi tana
duban flask din ranta cike da takaicin yadda ma ta dinga karbar
wannan abincin
“Wai ni?,ai da kinyi gaba da abinki don na jima banci abincinku ba,yata
na girkamin kullum” ta fada tana duban sumayya,take tsoro ya shigi
karima,ashe tayi sake har haka?,ashe fa diyar malamai wannan karon
lukman ya kwaso mata, lallai ba shakka shi yasa taga bata taba
tambayar abincinta ba a gidan duk yadda ta sha alwashi akan yi mata
kaca kaca duk sanda ta tambayi a bata abinci.
Hankalinta tashe ta fito daga bangaren ciken da tsoron lallai idan ta
gama da hajiya babu shakka lukman zata dawowa,kacibus sukayi da
nuwaira wadda ke dawowa daga gidan kitso da sumayya ta turata tayi
saboda ba zata iya mata ba jiya ta yanke da wuqa a hannunta,baki ta
saka tana duban nuwairan yadda ta canza cikin sati biyu kacal da
kariman tayi bata nan,ta tilasta lukman ya biya musu umra ita da shi
don har sai da yaci bashin wajen dubu dari biyar sannan ya cika
musu,su kuma yaranta da zata tafi ta tattarasu ta maida su gidan
iyayenta ta bar nuwaira ko oho,don dama ta saba yi mata irin
hakan,tsoro ya kama nuwairan sai ta rabe gefe sannan ta tattakura ta
sheqa da gudu sai bangaren hajiya,don kayan dake jikinta na waccar
sallar ne shekara uku da dinka su, bata barinta ta sanya su sai wani
abun ya tashi duk da cewa suna da lodin kaya harda wanda bata taba
sawa ba ma sababbi,ta riga ta saba kayanta koda yaushe haka suke
tamkar tsummokara,a haka ma sai an bata umarnin wadansa zata
saka,bayan ‘yan uwanta kullum cikin saka mai kyau suke.
Bata bi ta kan nuwaira ba don ba ita ce yanzu a gabanta, bangarenta
ta wuce hankalinta a matuqar tashe,tabbas lallai babu shakka idan
batayi wani abu ba ta lura duniyar rayuwarta gab take da girgiza koma
rugujewa baki daya,dole ne gidan ya koma yadda yake,dole kowa ya
koma yadda take so ciki kuwa harda sumayyan
k*
**
*******
******
Tunda ya karbeshi kusan shi ua zame masa uwa da uba baki
daya,yana matuqar debe masa kewa.yana sanyashi nishadi,wata qauna
ta yaron nasa yake ji cikin jikinsa da jininsa,sau tari ya kanyi mamakin
kansa yadda yake zama yayita kallon abdallan kamar babu gobe,babu
yadda yaya yahansu batayi ba akan ya bata shi amma ya qiya.ya bata
haquri don bazai iya bata shi din ba.
Da safe tare suke shiryawa ya bashi abinci su fita kasuwa tare da
shi,zuwa azahar zai bar kasuwa ya dan fita da shi su zaga gari su dawo
da la’asar,qarfe shida subar kasuwa su dawo gida, har gado ya siya na
yara ya sanya masa can cikin shagon, nan ma idan sun dawo sunyi
wanka sannan suci takeaway din da ya tsaya hanya yayo musu,daga
nan ya zube masa kayan wasansa yana tayashi yana kallon t.v har yaron
yayi bacci,wani lokaci yakan bata lokaci saman abun sallah yana wa
yaron nasa addu’a tare da yiwa kansa,wanda hakan ya sake samarwa
da ruhinsa nutsuwa,shikewa Abdallahn komai,dai dai da rana guda
mukhtar bai taba jin ya qosa koya gajiya ba,kai kanka idan ka kalli
yaron ba zakayi zaton bai tare da mahaifiyarsa ba,kusan kullum sabon
kayan mukhtar zai sanya masa,ado yake masa sosai, hakanan idan
shadda zaya sanya ko yadi anko suke abinsu,duk wanda ya gansu a
hanya zasu burgeshi,wata qauna ta musamman ce tsakanin d’a da
ubansa,wani lokaci idan ya soma rigiman mamansa sai ya kaishi gunsu
halima ya wuni don bai iya barinsa ya kwana,da dare yazo ya dauki
abinsa su wuce.
Sau daya yaya yahansu ta taba tuntubarsa da batun bazayayi aure
bane,murmushi kawai yayi mata yace tabar batun don ko sha’awar sa
bayayi,tilas ta ja bakinta ta tsuke,domin har yau tana tuhumar kanta da
cewa ita ce sila,zuwa yanzu itama ta fara gani,don kuwa yaron da jamila
ke ao kamar ta mutu shima yayarsa ta hana auren sam tace bata yarda
ba,ga fatima nan ma a gabanta babu wani bayani,fiddausi kuwa uwar
miji ta sakota gaba,yau tana gidanta gobe tana gidan yaya yahanasun
_KOMAI NISAN JIFA_
Tunda dukka ayyukanta suka kammalu wajen malaminta data
bawa hadin kai wanda har ta kaita da kwanciya da shi,ki a jikinta babu
abinda taji tunda har ya mata alqawarin tabbas tamkar ta samu kukhtar
ta gama koda kuwa zata sanar masa ita ta shirya duk abinda ya faru a
baya da sumayya,babu abinda zai iya aikatawa ba zaiga aibunta ba face
sabuwar soyayya da zata sake ballewa a tsakaninsu.
Ranar lahadi ta shirya zuwa har gida saboda ta tabbatar a ranar bai
fita kasuwa,dinki na musamman tayi sabo,baya ga sabon kitso da gidan
kwalliya da taje duka aka sauya halittar Allah,saboda tana rayawa
matuqar ciniki ya fada tofa ba lallai bane ma ta dawo gidansu ba saidai
a biyota da kayanta,tunda har yau a matsayin saki daya yayi mata haka
ta sanarwa mamanta,wanda koda sakin ukun tace an mata ta kuma ce
zata koma babu abinda uwar ta isa tayi don ba a bakin komai take a
gunta ba.
Qarfe sha goma na safe ta kammala komai,a nan cikin shagon masu
kwalliya wadda ta sanya fitowa tunda safen tayi mata ta sauya
kaya,double ta biya kudin makeup din hakan ya sanya ta yiwa jakarta
qarqaf,bata da damuwa tunda tana saka ran kome wanda zata fanshe
dukkan abinda ta kashe gun mukhtar,ba shakka sai ta rama wahalar da
ya bata ba zata sassauta masa ba.
Qarfe goma sha daya saura mintuna goma ta sauka qofar gidan
mukhtar din,wani farinciki ya lullubeta ta soma shaqar iskar komawa
cikin gidan,cikin sa’a tana tura qofar gidan ta taddata a bude,a hankali
take takawa saboda cogen dake qafarta har ta sada kanta da falon
gidan,a hankali take qarewa falon kallo yadda ya sake maidashi ya
gyarashi bayan barinsu gidan,sai abun ya sake burgeta,ko ina tsaf
kamar akwai mace a ciki kasancewar yana da mai share share da goge
goge,cikin kallon da takeyi ne idanuwanta ya saukan kan abdallah dake
zaune tsakiyar falon,sanye yake da jallabiya fara tas ta yara wadda ta
masa kyau kamar dan larabawa,wasansa yake da kayan wasa turmus a
gabansa nau’i daban daban.
Idanuwa ta zuba masa kamar yadda shima ya zuba mata idanuwa
yana kallonta tamkar ya santa,karkata kai take tana gano kamannin
mutum biyu tattare da shi,sumayya sumayya mukhtar mukhtar,ci gaba
tayi da kallon nasa tana son tantance dan waye?,miqewa yaron yayi
yana ci gaba da kallonta sai kuma ya saki kuka tare da juyawaa
shige bangaren baban nasa wanda ke ciki.
Nan gefan abdallah ya kwanta yana ci gaba da kuka tamkar wani
qaramin yaro,jin zuciyarsa yake kamar zata fashe,janyo abdallah yayi
cikin jikinsa yana magana qasa qasa mai cike da kalmomin nadama
yana ci gaba da kuka.
Sai da rana ta soma bugun naman jikinta sannan ta iya miqewa a
daddafe ta yafa mayafinta,takalmi kuwa basu sakuwa a hannu ta riqesu
hadi da jakarta,da qyar da jan qafa ta kai kanta titi ta tari adaidata sahu
ta hau duk da cewa bata da qwadalar da zata bashi,qofar gidansu ya
sauketa tace ya jira ta miqo masa kudin,tana sallama ta zube a tsakar
gidansu tana maida numfashi,mamarta dake wanki bakin fanfo ta dago
tana dubanta,mamaki ya cikata saidai bata da ikon tambayar ta abinda
ya sameta,murya can qasa da qyar ta qwalawa qanwarta kira
“Idan akwai naira dari jakarki fita waje ki bawa mai adaidaita
sahu,mama dora min ruwan zafi” kowannansu da to ya amsa
mata,maman ta saki wankin ta shiga kitchen.
Gashi tayiwa kanta sosai tamkar kai jego,tanayi tana runtse ido
zuciyarta na zafi da quna,tana tuna yadda mukhtar ya dinga jibgarta
kamar wanda ya sayi jaki mai taurin kai,dakinta ta koma ta shafe jikinta
da man zafi ta samu ta kwanta sannan ta janyo wayarta tayi kiran
abokiyar shawara da shaidancinta zinatu,tana dagawa ta buqaci
ganinta,cikin sa’a kuwa tana kusa.
cikin mintuna qalilan zinatun ta iso,su ka gaisa da maman wanda ke
zaune tsajar gida tana shirin dora abincin rana,da kallo tabi zinatun har
ta shige dakin,
“Lafiya?,na zaci zaki cemin gaki gidan mukhtar anyi kome sai nazo na
sameki kina tashi da qyar haka?”baqinciki ya sake tokare zainab,cikin
bacin rai ta soma fadin
” ni malam zai ciwa kudi zinatu,ni zai ha’inta?,kalli jikina ki ga abinda
mukhtar ya yimin duba zinatu”
“La la lal” shine kawai abinda zinatu ke fada tana gyada kai
“Garin yaya haka zainab” tas ta kwashe yadda komai ya faru ranta na
quna ta qunduma ashar sannan ta dora
“Ba sai na warke ba gobe gobe zamu koma wajen malam,wallahi sai na
nuna masa ni ‘yar tasha ce,duk abinda ya buqata nayi masa,kwana nayi
yana sasukata duk warin dake tashi a jikinsa amma ban damu,shine ni
kuma zai rainamin wayo an gaya masa ni gara ce,to wallahi Allah ya
nuna mana gobe shege ka fasa” haka ta dinga bambami zinatu na
tausarta da haka sukayi sallama da niyyar gobe da sassafe zasu dirarwa
malam
0.**
Tana zaune bakin gadonta tana ninke kayan sawarta a
hanakali,tunanin abdallah na kai komo cikin ranta tun safe,tunda ta
haifeashi basu taba rabuwa daidai da kwana guda ba banda sanda ta
yayeshi sai wannan lokacin,yanzu haka watanni kusan shida kenan
bata sanyashi a idanunta ba,gidan nasu yau shiru yake tun safe har
yammaci,hajiya na bangarenta yau bata jin dadi,tunda ta kammala
mata girki sai ta barta ta dan kwanta ta huta, karima ta hada kan yaran
sun tafi sunan qanwarta data haihu,bata kuma bar nuwaira ba haka ta
kada ta suka tafi tare.yaran baki daya sunci ado banda ita,a haka da
sauqi tunda sumayya ta tattara dukkan yagaggun kayanta ta boye ta
hanata sakasu tafiddo mata da wasu,haka karima ta haqura bayan
sa’insar da suka sha da sumayyan,a yanzu bata da goyon bayan hajiya
lukman kuma bai gari yayi tafiya bare ta hadata da shi.
Hudu da rabi na yammacin taji sallamarsa bakin qofar dakinta,a
hankali ta daga kanta tana dubansa,ta mance yaushe rabon data
sanyashi a idanuwanta tun kafin yayi tafiyar nan wadda ita kanta
satinsa biyu kenan baya nan,sanye yake da shadda dinkin tazarce da
hula saman kansa sai takalmi sau ciki,kafadarsa rataye da jaka ta
matafiya,kallonta yake yana mata murmushi
“Sannu da zuwa” ta fada tana gyara daurin dan kwalinta
“Yauwa sumayya,ya gidan?” Ya fada yana zama gefanta yana mai ci
gaba da kallonta
“Lafiya qalau” ta fada tana hada kayanta waje guda tare da miqewa ta
zura hijabinta tana shirin ficewa
“A’ah.ya haka kuma,ya zaki fita ki barni”
“Au da dawa nake barinka” ta fada tana gyara zaman hijabinta gami da
kallonsa
“Amma dai ai yau gidan babu kowa ko?,wa zai kula da ni?”
Qugu ta riqe tana duban idanuwansa
“Sai babu kowa cikin gidan sannan nake da amfani a gunka?,to gun
hajiya zani na dubata na barota bata jin dadin”damuwa qarara ta gani
ta bayyana kan fuskarsa karo na farko kan maganar da ta shafi
mahaifiyarsa
” subhaballahi tun yaushe?, muje na ganta”‘ya aijiye jakarsa ya miqe
yabi bayanta.
Ganin yadda ya damu qwarai ya sanyata cewa
“Ba wani ciwo me mai zafi ba,qafarta ce kawai ta motsa”tayi furucin
tana kallon gabanta, ajiyar zuciya yayi bai sake cewa komai ba har suka
qarasa dakin hajiyar.
Tana kwance a falo da alama sallah ta idar,sosai tayi mamakin ganin
lukman din wai tazo dubata,saidai bata nuna masa ba,suka gaisa
fuskarta a sake,shi da itan duka wani dadi suke ji,sai gashi suna hira
kadan kadan, hatta da sumayya sai data dinga jin dadi,ta dade da sanin
dadin da iyaye ke da shi a gun d’a,hakanan zuwa yanzu tasan yadda
uwa ke jin dadi a duk sanda ta daga ido ta kalli danta ko diyarta cikin
kyakkyawan yanayi.
“kaje ka huta lukman ka dawo daga baya idan hirarce”hajiyan ta
fada qasan zuciyarta a karye,don tasan ita kanta fada kawai tayi,saboda
babu lallai ya sake zama da ita irin haka matuqar karima baqar daga ta
dawi cikin gidan,ta fada ne don kawai kada ta shiga haqqinsa shi da
iyalinsa,saboda zuwa yanzu ta yarda kura kuran da ta tafka a baya
zunubinsu ke bibiyarta,amsawa yayi da to don shi kansa yanason
kasancewa da matarsa, miqewa yayi yayi gaba wanda tilas sumayyan
tabi bayansa don tana kunyar hajiya da ganin girmanta,bata son ta
fuskanci komai daga gareta.
Gaba ya sanyata har zuwa dakinsa, karo na farko data fara taka
dakin tun zuwanta gidan,kan gado ya zube yana dubanta
“Hadamin ruwan wanka na gaji sumayya,sai ki yo alwala idan na fito
zamuyi sallah”
“To” kawai tace masa tana tunanin lokacin sallar magaribar ai baiyi ba
aqalla akwai kusan awa guda nan gaba,sai daya shiga wankan sannan
tayi alwalar kamar yadda ya buqaceta,a nan gabanta ya shirya duk da
dauke kai da tayi sannan ya umarceta da tatashi suyi sallah,bata
fuskanci abinda yake nufi ba sai suka idar da sallar taji yafara
addu’a,take jikinta yayi sanyi,tsoro kuma ya cikata,tana jin ta yaya zata
sake wata sabuwar rayuwar da wani sabon mutumin na daban ba
wanda ta saba da shi ba?,saidai babu yadda ta iya din saboda tana da
cikakkiyar masaniyar cewa da mijinta take tare wanda ya biya
sadakinta shaidu kuma suka shaida,to shi kansa kamar baqo haka ya
bijiro mata,sai daga bisani ya fara warewa a hankali,hawaye ne suka
dinga gangaro mata,ambaton Allah ta dinga yi cikin zuciyarta.
Tana gaban madubi tana gyara gashin kanta bayan ta gogeshi tare
da maida masa ribbom dinsa,shi kuma na zaune bakin gado yana
kallonta,talbbas babu shakka kyauta Allah ya masa,a cikin mata hudu
da ya aura har da karima cikon ta biyar din bai taba cin karo da mace
kwatankwacin sumayya ba cikin duniyar ma’aurata,babu abinda ke kai
kawo cikin qwaqwalwarsa sai yadda ya samu sumayyan cikin sahun
mata na musamman wadanda suke ‘yan kadan ne cikin daruruwan
mata,amma sai ya fuskanci babu wata fara’a ko walwala sam a
fuskarta,wanda hakan sai yaji sam bai masa dadi ba,a hankali ya kira
sunanta ta amsa gami da waiwayowa tana daura dankwalinta ba tare
da ta dubi qwayar idonsa ba
“Sumayya,naga kamar bakya farinciki da ni ko?,nasan fushi kike da ni
haushina kike ji,nasan dole kiji haushi bake bama koma wacece,don
Allah don annabi kiyi haquri sumayya,wallahi ba laifina bane, bansan
dalilin da ya sanya idan karima ta bani umarni ba nake kasa bijire
mata,bansan me ya sanya ba nake tsananin tsoronta,duk da cewa a
yanzu cikin kashi dari inajin babu kashi hamsin yana raguwa
sosai,kiyimin haquri sumayya ina saka ran in sha Allahu komai ya kusa
dai daita,ina miki godiya kan namijin qoqarin da kike kan gyaruwar
gida na,ina sane kuma ina lura da komai,wasu kuma karima ta
sanarmin sa niyyar na na taka miki birki,wallahi sumayya ban taba
ganin mutumin dake taka karima itama kuma take shakka shakkarsa ba
saike,kiyi haquri kici gaba da yin haquei komai mai wucewa ne in sha
Allah” yanayin yadda yake maganar kawai ya isa ya sanar mata bilhaqqi
da gaske yake, sai taji tausayinsa ya kamata,mutum cikakke kamar
lukman amma sharrin mace ya maidashi wani iri
“Babu komai,kowanne bawa da irin tasa QADDARAR a rayuwa,Allah ya
mana magani ya shige mana gaba,ka riqe addu’a kaima insha Allahu
HASKE na nan zuwa…
Bai kai ga bata amsa ba suka soma jin bugun qofa mai tsananin qarfi
“ka bude lukman bude,ina fatan ba abinda nake zargi bane,wallahi idan
har shine ka kuka da kanka”idanuwansa ya runtse gabansa na
faduwa,sumayya dake zaune a nutse abinta ta soma nazartarsa da
nazartar yadda ya tsorace,babu laifi da sauqi,tunda idan da dane da
tuni ya arta da gudu yaje ya bude din
“ka ambaci Allah cikin ranka hakan shi zai cire maka tsoron dake cikin
ranka”
“Allahumkhfinihim bima shi’ita”ya fara ambata daya daga cikin addu’ar
da yaji hajiyansa na ambata tun bayan zuwan sumayya gidan aduk
lokacin da taga karima.
Sumayya ce ta tashi ta isa bakin qofar dakin ta murza key din ta
bude,karima ce tsaye bakin qofar rataye da jaka,shigowarta gidan
kenan ta hangi motar lukman fake,ta tambayi mai gadi ya sanar mata
kusan awanshi biyu da kenan da dawowa,dama tun tana gidan sunan
taji hankalinta yayi gida,abun mamakin shine dukka yaranta na tsaye
bayanta harta da qaramarsu, abinda ya sake daurewa sumayya kai
kenan,nufinta a gabansu zata tijara babansu?,da yanayin da tazo mata
taso itama ta tarbeta,amma ganin yaran ya sanya sumayyan murmushi
“A’ah,maman nuratu,kece kuma da yaran baki daya haka? “harara ta
balla mata sannan tace
munafukar Allah bake nake nema ba,babban magulmacin nake
nema,matsamana mu shige”murmushi ta kuma yi tana gyada kai
“Mai zai hana na barki ki shiga, ke da dakin mijinki,amma bai kamata ku
dunguma baki daya ba,saboda bakisan a yanayin da zaku ruskeshi ba”
ta fadi maganar tata ta qarshe qasa qasa yadda kariman ce kawai zata
iya ji
“Bismillah” sumayyan tace sa ita bayan ta janye mata jiki,sai data ja
tsaki sannan ta wuce kamar zata bangajeta,yaran suka yunquro zasu
shiga ta sha gabansu,ta dubi nuwaira wadda ta tabbatar itace mai
hankalin cikinsu
“Nuwaira,maza ku tafi dakinku ku sauya kaya,mamanku na
fitowa,kama hannun basma ku wuce ko?”
“To anty” ta fada tana kama amma da nuratu sukayi gaba,tsare sauran
tayi da idanuwa tilas duk rashin kunyarsu suka bi bayan nuwaira daidai
sanda maganganun karima cikin ihu suka soma tashi
“Na shiga uku na lalace,yanzu lukman sai da ka kwanta da
matarnan,lallau namiji d’an kunama ne,wayyo Allah yau naga ta kaina”
ta fada tana dora hannu a ka tare da qarewa gadon nasa kallo,tsaye
sumayya tayi harde da hannayenta tana kallonta,wato badon ta kora
yaran ba nufinta gabansu zatayi wannan tambelan?,gaskiya ne dole
wasu matan su janyo a dinga kiran mata masu naqasun hankali,takawa
tayi ta dafa kafadarta wanda ya sanya karima waiwayowa tana dubanta
“Meye na tashi hankali haka?,tun ranar farko kenan?,bakisan somin tabi
bane yanzu aka soma?,ki godewa Allah ma da bakizo kin samu ana
third round ba” ta fada tana kewayeta tare da komawa bangaran gadon
ta soma gyara bedsheet din tana murmushi.
Ashar ta lailayo ta danqarawa sumayyan irin wadda bata taba jin
irinta ba
“Wallahi kinyi qarya kin kwana da yunwa duk malantar ubanki baki isa
ba,duk wanda yaci tuwo da ni miya ya sha,wallahi sai kin gane
kurenki,saikin gane shayi ba komai bane face ruwa,sai na cusa miki
baqinciki fiye da wanda kika cusa min” sai ta waiwaya inda lukman ke
zaune,tayi tsammanin ganin tashin hankalinsa qarara yadda aka saba
sai ta ganshi zaune ko gezau
“Kai kuma tashi mu wuce dakina” ta fada a tsawace
“Ba inda zanje” ya fada yana jin shakka shakka na tasowa can qasan
ransa yana qoqarin danneta,idanuwa ta zaro.jikinta ya soma bari,ba
shakka alqadarinta gab yake da karyewa,kasa magana ma tayi sai
kallonsa da takeyi
“A’ah,ki wuce mana kije tunda dai shi din yace bashi zuwa” a fusace ta
waiwayo ta tunkuda sumayyan wadda bata zata ba,hakan yayi sanadin
da tayi taga taga zata fadi lukman din ya tareta,sai ta miqe daga jikinsa
tana murmushi kamar ba ita aka yiwa ba
“Babu komai,duk cikin haushi ne” qwallar baqinciki ce ta fara qoqarin
zubo mata,da hanzari ta juya ta fice a dakim saboda batason sumayya
ta gani har ta gane ta soma samun rauni,qofar sumayyan tabi ta kulle
sannan ta dawi ga lukman wanda ta lura hankalinsa ya soma
tashi,sosai ta zauna gabansa tana karanta masa abubuwan da suka
dace har ya soma daidaita,sannan suka tashi suka sake komawa duba
jikin hajiya wadda mamaki ya sake kamata ganin sun sake dawowar
duk da taji shigowar karima gidan.
Qarfe goma da rabi suna dawowa daga wajen hajiya suka ratso ta
falon,islam suka gani na matse hawaye ta tari gaban uban tana cewa
“Abba kaga kasa mamanmu ta hada kayanta ko ta tafi, kuma tace ba
zata dawo ba” wani matsanancin faduwar gaba ya ziyarce ya zaro ido
yana dubanta
“Tun yaushe?”
“Dazu,naje dakinka baka nan” duk sai sumayya taji babu dadi, kada dai
abinda ya faru dazun ya sata bar musu gidan,sai ya kama hannun
yarinyar yana fadin
“Ya isa,kada ki damu mamanku gobe zata dawo kinji,sumayya jeki da
su suna dakinsu ina zato” amsa masa tayi,saidai qememe yarinyar taqi
yarda ta kama hannuwanta haka suka tafi,koda ta shiga dakin suna
zaune baki dayansu tsuru tsuru,duk sai taji tausayinsu ta dinga jin babu
dadi,da fari duka qin sakin jikinsu sukayi da ita sai nuwaira
kawai,amma ganin nuwairan ta saki jiki sai basma qaramar cikinsu
itama ta ware,daga baya nuratu ta sake itama,sai islam kawai da tayi
kicin kicin taqi shiga sabgarsu,ba ita ta barsu ba sai da taga sunyi bacci
sannan ta musu addu’a ta bar dakin.
Sumayya na wucewa wayarsa ta dauki ruri,lambar karima ce hakan
ya sanyashi dagawa cikin hanzari yana cewa
“Haba karima,haba karima,meye haka din da zaki bar yaranki ki kwashi
kaya,yaji da girmanki da komai”
“Saurara ba wannan na kiraka ka gaya min ba,kiranka nayi na gaya ma
ka sanar da wannan matar taka diyar malamai masu kwanan buzu
cewa,ta bar murna karanta ya kama kura,babu inda zani ina nan
dawowa,kuma dawowata ba zata yi mata dadi ba wallahi wallahi sai ta
gwammace kida da karatu,don babu wata ‘ya da zan bari ta shigarmin
rayuwa ba tare da na nuna mata kuskurenta ba,kuma kada ka soma
wahal da kanka kace zaka nemeni don ba samuna zaka yi ba,har sai
randa na dawo da karan kaina,ina fata ka gane”‘qit ta datse kiran sai
yabi wayar da kallo yana kada kai aljihu ya maidata yana amsa sallamar
da sumayya tayi masa.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]