[Advertisements⬇️]

KANDALA CHAPTER 6 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

KANDALA


CHAPTER 6
To hamza nagaji da jiranka yau kusan sati biyu kana yimun wasa da hankali to nagaje umarni Nake baka!!!

” Dady yace baza’ayi haka ba kai hamza wakakeso?

” k’ande ya kallah itama shi take kallo lokaci daya cikin ta yakada…

” ba dakai ake magana ba…

” abi na samu wacce nakeso……

K’ande da kirjenta ke faman bugawa ahankali ta daga k’anta hakan yasa sukayi ido biyu da hamza!…

” Abi kadan karamin lokaci manah soonest zan kawo….

” kowanne lokaci abunda kake gayan kenan to let me tell u this is the last time da zan karayi mika magana!

” inshaaAllahu Abi…

” farida dake gefe tayi tsuru tazata Hamza zai ambace sunanta Amma sai taga ya basar…

” mumy ma abunda take tunani kenan!.

” firdausi da zuciyar ta keyi mata wasu wasi yadda taga hamza na kallon k’ande…

” Toh Alhaji ne zantafi Amma ina neman Alfarma guda daya?

” Haba Alhaji mahmuda ai tsakanina da kai babu wannan kafadi kome nine?

” yauwa daman kande nakeso tabine ta danyi kwana biyu…

” kande datayi maza gurin daga kanta sai dady yace uwata ke shirya to kutafi….

” cikin rashin jindadi tace toh…

” hamza dake faman jindadi domin shima campany suna nemansa wannan kuma dama ce dazai samu gurin nuna mata soyayya!…

” Toh hamza sai katashi mutafi muna jiranta a mota matan dady sai anjima…

” cikin hada baki sukace agaida mutan gidan…

” k’ande da hawaye ke wanke mata fuska ayayin datake hada kayan nata gashi bata sanar a islamiyya ba number uncle ta dauka tare da jan akwatin waje….

” aa harkin shirya..

” eh nashirya..

” to agaishe su dama hutun makarantar ku sati biyu ne ko?

” tohm ran lahadi driver zaizo ya dauke ki…

” takalli su hajiya ta ce natafi…

” Daga su har yayan banza sukayi mata!…

” Tunda suka shiga mota k’ala bataci musu ba tanajin dai uba da dansa suna tattaunawa Amma ita ido ta zuba musu…

Basu isa abuja ba sai gurin6 hakan yasa ta bude idonta dan kalli kalli gidanjen datake gani ne yasata cikin wane farin ciki shigarsu maitama babu wuya ta hango wane katafaren gida, aranta fada take aljannar duniya…

” remote din dataga hamza ya danna shiya tayar da hankalin ta nan da nan taga ya bude da kansa! Lokacin da suka shiga gidan katon fili tagani da motoci sai wane bangare da batasan sunansa ba!

” Ahankali hamza ya dauki akwatin ta Abi kuma yace fito Aisha…

” lokacin da suka shiga parlour suka tarar har kashi uku Anan suka zauna sannan hamza ya fita…

” ita kande datake ganin ta waye ashe ba wayewa tayi ba wannan Aljannar duniya haka lallai masu kudi sunanan…

Wasu Yan mata tagani su biyu sun sakko daga katafaren bine sai kowacce fuska babu annuri!…wata fara doguwa ce ta fara magana Abi har ka dawo? +

” yes am back!..

” d’ayar ce ta dakawa kande harara tace abi wa ka kwaso mana?

” kande data dauke fuskarta cikin tsanar su, Abi yace Aisha ga yayana fadila itace babba Amma tana Dubai ita da yan uwanta karatu! Wannan sunanta saddika waccen kuma sunanta maryam!…

” cikin murya a sanyi tace ina yinin ku?

” lou sukace sannan suka samu guri suka zauna…

” ummi ce ta sakko daga bine tana fadin abi kwashe kwashen ka yayi yawa wata yarinya kakawo mana?

” wacce irin magana ce wannan ummi? Yar ugurin kanwata ce tun farko ne naso abani ita ashe Alhaji hassan ya yi min fin karfi tazo ta kwana biyu ne anan!..

” okay ummin ta ambata batare da ta kara kallon su ba!

“Mikewa yayi yace maryam kushiga da ita dak’inku…

” sai data dan jima sannan tace okay!!!…

” kande dake guri daya tayi wane mugun tagumi cikin zuciyarta tace ina ina Ai bazan taba sonka ba uncle hamza wannan gida naku sai ku!

” ke kihau binne zakiga wane palour the first one shine namu akwai daki aciki so kishiga but karki haumana bed akwai kafet sai kizauna akai….

” toh tace sannan ta mik’i, tana shiga taga dakin ya hadu wane irin kafet dataki takawa akwatin ta ta ajiye sannan ta bude wane guri ashe bandaki ne haduwa tayi hadu tarasa inda zata kunna ruwa ahankali tasaka hannunta tanasawa taga yazo tana cirewa yadauke ikon Allah, bayan tayi alwala tayi sallah ta zauna tana tunanin rayuwa….

” after laasar hamza yashigo ummi ina yini!

” son so kakeyi nadinga fushi dakaine…

” maryam tace haba yaya kaje kawane zauna akano…

” saddika tace like irin house din nan nasu!

” dallah kuyimin shiru kusan dadin kano kuwa?

” ummi tace abi dai yatada fada yace sai kafito da matar aure nan da 2weeks..

” murmushi yayi yace to ai ummi nasamu yarinya mai hankali da ilimi gata kyakyawa!…

” ummi tace bazan daina gayamaka ba banason yar talakawa kuma nafeson mai ilimi sosai kaga sisters dinka sungama service, masters ya rage..

” haba ummi how many times zangaya miki tarbiya itace ba kudi ba…

” yi mun shiru malam kaine first born yar gidan manya nakeso kadakko min…

” maryam ta hau sama tare da fadin kinsan yaya da kwashe kwashe sai kinyi da gaski…

” saddika ma tabiyota tare da fadin aikuwa dai, suna shiga dakin suka haye gado babu wanda ya kalle kande, maryam taga ta dau waya tave d’boy katawo?

” itama saddika kiran prince tayi tare da fadin maryam sai karfe biyu zamu dawo fa!

” mamaki ne yakama kande dataga suna saka wane shigun kaya…

” Ke dallah daina kallon mu idiot kawai…

Kano

Cikin gidan dady kuwa kowa jin jiki yakeyi, ba shiri mumy tasa aka kawo mata masu aiki..

” mama farida kuwa inba ran girkenta ba ba batayin girke…

” haruna kuwa tunda ya dawo yaje labarin cewa kande bata nan yakasa sukuni baisan ko soyayya bace ko kiyayya shidai yasan yana jin wane abu acikin ransa ga yunwa da ke dawainiya dashi…

” sister farida wallahi kidage akan uncle hamza dan akwai abunda nake zarge!…

” ke dai bari sis nema kinga nakasa sukuni gashi nakira wayarsa Amma akashe…

” da daddare aka sanar da shi iya habu batada lafiya tambaya yayi sannan yaje yasiyo mata magani…..

” cikin daren firdausi tashiga dakinsa Amma yariga ya fita…

” lokacin da haruna ya shiga kauyen direct gidan iya habu ya zarce tarar da ita yayi atabarma…

” aa sannu da zuwa haruna sunnu da zuwa…

” gidan murmushi yace ya jikin naki iya?

” jiki naje sauki inason inyi maka fadane haruna ka girma ya kamata aci kayi aure haruna ganin awannan yanayin bazan jidadi ba inaso kafin nema na mutu naga jikokina!…

” shiru yayi yace toh iyah…

” inaso kanemi auran kande!…

” murmushi yayi yace kande fa kikace?

” kwarai ita nake nufi…

” Tohm zan gwada naga in zata soni…

” yauwa haruna hakana keso naji….

Abuja..

Tunda su maryam da saddika suka fita tsoro ne duk ya baibayeta ahankali taje turowar kofa!

” kanta ta daga hamza tagane ya shigo…

” yar kanwata sannu da hutawa!

” Kallon sa tayi takau da kanta!DanAllah Aisha ki soni wallahi ina kaunarki rashin soyayyarki agareni zata iya haifar mun da matsala acikin zuciyata… +

” cikin masifa tave wai saunawa kakeso na sanar dakai bana sonka har Abada bazan taba sonka ba! Ba ciwo ba zuciyar ka ta Buga gaba daya but bazan soka ba!

” jikinsa na bare ya rike hannunta saboda me kande?

” sakar min hannu saboda na tsaneka…

” cikin salubewar jiki ya miki ya fita yana kokarin sakkowa abi ya ganshi…

” hamza what wrong…

” kuka ya fashi dashi tare da fadin banida lafiya…

” nace maka kadinga daure karmazama rago…

” a hankali ya dafe bango ya shige dak’insa…

Washegari yini guda hamza yana daki saddika ce takaimasa abinci da mamakinta ta ganshi kwance ahankali tace yaya miki damunka?

” yace babu komai riqeni mufita!…

” kande ma ta fito ganin gidan sukayi karo dasu wata muguwar harara tayi masa sannan ta huce…

” saddika tace yaya kadaina saka damuwa aranka please!

” wane mugun tari yafara sannan yace maidani ciki…

” tana kaishe kafin tafita taje ya miki ya dauke fitilar kusa da bed dinsa yana fasawa…

” yaya menene haka!…

” mudubin sa ya tararratsa yana fadin wallahi inasonki inasonki hannunsa duk jini nan da nan ya wadi luuuu…

” saddika ce tafita a guje tana Abi, ummi yaya! Yaya!! Yaya!!! tana kuka…Tana k’aishe k’afin ta fita taje ya mik’i ya dauke fitilar k’usa da bed d’insa yana fasawa…

” yaya menene haka?..

” mudubin sa ya tararratsa yana fadin wallahi inasonki inasonki hannunsa duk jini nan da nan ya wadi luuuu…

” saddika ce tafita a guje tana Abi, ummi yaya! Yaya!! Yaya!!! tana kuka…

Kiran da saddika takeyi ya tayar da hankalin kowa hatta maryam dake cikin daki mik’ewa tayi aguje ta sakko suna girgiza sa suna magana hamza hama karka mutu kabarni wayyo Allah nah hamza!!…

” Abi ne yashigo agigice ya daukesa sai mota duk’an ninsu suka shiga mota suka bi bayansa…

” Nan da nan ummi takirawo waya tare da sanar da asubitin ga sunan zuwa kuka takeyi su saddika suna bata baki kidaina damuwa zaije sauke….

” ummi da batasan lokacin datayi park cikin asubitin ba da sauri suka shiga suna biye da likitocin tuni anyi emergency dashi…

” Abi ne yace haba ummi cool down mana kukan ki bazaiyi miki komai ba u better pray for him…

” rungumesa tayi tana kuka haba Abi tayaya zanyi shiru bayan d’ana yana cikin rai ko mutuwa Alhaji mai yak’e damun hamza kagayamin cikin kuka takarasa zancen….

” bari doctors din sufito su zasu sanar damu Amma inshaa Allah babu komai…

” Duk suna tsaya sunata zagayi kusan awansu biyu kowannen su yakasa yiwa juna magana….

“K’ande ce ke faman tunani me yafaru suka fita agigice? wanene ba lafiya? To me yasamu hamza? Tambayoyi ne da suke ziyartar zuciyar ta can kuma tace me ruwana ma? Mekiwa tayi ta shiga kitchen nan ta tarar da kuku! Gaisawa sukayi cikin turanci sannan ta tambayi shi store nan ta dafa Abunda zataci tahaye sama!…

” Dr fabrick ne yafito yana tambayar ina alhaji Nan akayi masa Alamu da inda yake cikin muryar likitoci yace excuse me sir!

” uhm what wrong with him?

” kindly follow me to my office…

” nan ummi ta tashi dr yayi mata inkiya data zauna…

” cikin rauni ta rungume maryam tana fadin Allah yasa ba mutuwa yayi ba!

” cikin rawar murya saddika tace ummi cool your mind DanAllah, Allah yana tare da yayanmu…

” Acikin office din dr yabawa Alhaji hannu suka gaisa sannan yace hamza yana cikin matsanan cin hali, how many times naki gayamuku son yana da saka damuwa sosai acikin lamarin sa kudinga searching, yan haka zamuyi masa aiki!

” dr aiki fa kace…

” that’s the only solution da zaa cice ransa!…

” innalillahi wa’inna illahir raji’um, yanzu when za’ayi aikin?

” Tomorrow inshaa Allah bama nizanyi ba akwai dr victor shi zai gudanar da aiki gobe by 12:00…

” okay, tashi yayi jiki a salube ya fita zuwa gurin su ummi wacce kana ganinta kasan tana cikin damuwa…

” ya mutu ko ai daman nasani…

” cikin sanyin murya yace jikin nasa da sauki kuma gobe za’ayi masa aiki!

” Aiki kamar yaya? Haba Alhaji kafita dashi waje ayi masa ni banga likitan dazaiyi masa aiki a abuja ba…

” ummi Allah kibada lafiya ba likita ba kuma dr din gobe zaizo daga America so babban likitane bangarin heart…

“Oh Allah kabawa son dina lafiya, Allah kadubi shi, to me hamza yasa azuciyarsa haka?

” abunda nakasa fahimta kenan ina tunanin zancen Auren nan nasani…

” saddika tace yes abi shine domin naji yana fadin wallahi ina sonki inasonki, itace kusan kalmarsa takarshe….

” Shiyasa nace aikai kudin kafin ma yaji sauki…

” Dawa kuma za’a akai?

” ‘yar gidan Aminina mana farida ai dama ne ita nake hangi…

” Ne dai wannan nata tashi ba kabari ‘dana ya samu lafiya…kuzo muje kutawo da Abinci saddika da maryam suka mik’e.. +

” A hanya sukace anya abi yaya yana son farida?

” yana sonta mana naga suna shiri sosai fa domin har waya sukeyi!

” Gaskiya Abi kabari kaje ta bakinsa karkayi masa shigar gaggawa…

” To ya ambata…

Suna shiga gida saddika tasanar da kuka ya hada abinci da kayan tea!..

” ya Amsa mata da okay!

” k’ande tana zaune inda ta saba zama shigowar su maryam ce tasata gyara zama da nuna gajiyawar ta..

” sanadiyar basa kulata domin yanzu ma ko kallonta basuyi ba hakan yasa ita tayi fuska tana kallon su…

” sauri sauri sukayi sannan suka fita zuwa car!

” maryam ce tace sister gaskiya wannan Aisha din *Ta Dabance*…

” Wallahi kam what am telling in my mind kenan!..

” bayan fitar su zaman ya ishe kande hakan yabata damar fita gurin mai gadi tana sannu sannu….

” aa yana ganki anan?

” wallhi zuwa nayi muyi hira?

” cikin firfito sa ido yace dawa dani wai ina maigadin?

” haba baba me gadi ai mutum bai isa ya manta asalinsa ba, Ne da kaganne yar kauye ce sunana k’ande…

” hakan yasa yaji dadi yace kin hutawa rayuwarki domin bakida wulakanta dan Adam…

” La ai ita rayuwa in kanason kace ribarta to ka’iya zama da kowa!…

” hakane kam domin dazu aka fita da hamza rai ahannun Allah ko yaya suke cika oho…

” Basar da hirar tayi batare da ko gizau aranta ba sannan tashiga wata hirar…

Kauye

Haruna da sassafe ya sanar da iya cewa zai tafi…

” haba haruna Ai ka tsaya na dama koko ko?

” Tohm bari naji na gaida goggo..

” yauwa ko kaifa..

” Cikin Nutsuwa ya bude kofar ahanya suka dinga gaisawa da mutane a hankali yayi sallama…

” A’a muryar wa nakeji kamar ta haruna?

” Eh nine goggo durkusawa yayi har kasa yace ina kwana na sameku lafiya?

” lafiya lou ya mutan birnin?

” Duk suna lafiya ai tun jiya nazo duba jikin iya…

” eh wallahi tasa jiki jikin nata amma da sauki ai, ina kande kuna daita hakuri da’ita…

” a’a goggo ai k’ande ta canja!

” To ya zamansu da farida kuwa…

” uhm abun dai sai addu’a wallhi!

” toh kadinga yimata bada Dai…

” Ai kawu mahmuda yazo ya tafi da’ita..

” goggo dai bataji babu dadi sai ta dake tace toh Allah ya dawo da’ita lafiya..

” Ameen bari na tafi toh kashiga kugaisa da su abbas da Ali manah…

” Nan ya lika suka Dan taba hira bayan sunyi sallama sannan ya koma gidan iya habu yayi mata sallama ya huce birni….

Birni

Shigar sa kenan ya tarar da farida tana kuka zama yayi ya dubita lafiya?

” hamza ne bashida lafiya za’ayi masa aiki zuciyarsa…

” subhnlhi yaushe?

” gobe..” okay ma tafi goben dakkomin abincina! +

” Tana cikin daukar abinci mama farida tashigo to iyayen ci da kashi bakwa tabuk’a komai sai ci da barci to ajiye abincin tunda ba ku kuka dafa ba…

” karki zageni bane zanci ba yaya haruna ne zaici..

” muje nagani suna fita ta hadu da haruna yana zaune…

” gashi yaya cikin bacin rai yace Na koshi…

” mama farida ta mika hannu to bani abincina tayi gaba…

” firdausi ce ta sakko yayana mekakeso naji nadafa maka!

” Cikin kashe ido yace kome kika dafamin ‘yar kanwata zance…

” Cikin murna ta shiga kitchen…

” cikin awa biyu tagama komai sannan ta kirashi ta zuba meshi ya naci suna hira…

” haka dady ya sakko ya tarar dasu yaji dadi sosai sannan suka gaisa ya fita…

Abuja

Manyan likitoci sun taru Yau za’a gabatar da Aiki, su abi da ummi tun safe suke asubuti…

” Ummi ce tace wai saddika ina wannan bak’uwar ko tace zata biyoku…

” that’s what am saying ummi yarinyar batada kirki wallhi…

” kukyaleni da’ita bari naji gida nadawo…

” okay…

” k’ande tana zaune tana ta dariya sanadiyar film din datake kallo…

” ummi ce tashigo to asararriya mara mutunci, son yana can ba lafiya ke kinan kina dariya wane asararrin ne zai hada zuri’a dake, wallahi Na tsaneki kuma…..k’ande tana zaune tana ta dariya sanadiyar film din datake kallo… +

” ummi ce tashigo to asararriya mara mutunci, son yana can ba lafiya ke kinan kina dariya wane asararrin ne zai hada zuri’a dake, wallahi Na tsaneki kuma Yadda kika nunamin kiyayya ido biyu to kisane bashi kika dauka Dan iskanci kana gidan mutum ai ko tausayin d’ansa k’aje..

” zuciyar kande ce tafara tafasa nan zuciyoyin ta suka fara aiko mata da sak’o a hankali ta Daga kai tace kiyi hakuri ummi ne bahaka nake nufi ba kuma babu wanda yasanar dani akan bashida lafiya, saddika da maryam ba kulani sukeyi ba!

” Lafiya ce dai Allah zai bashi ko kinyi addua ko bakiyi ba dan haka kiyi duk abunda kikaga dama idiot kawai…

” cikin bacin rai kande ta dago idonta can kuma tace bamasa fatan rashin samun lafiya ba domin nema yaya yake agurina…

” ummi tace Dallah tafi can…

” kallonta kawai tayi sannan ta hau sama cikin tsaki tace ko mai ruwana da d’anku oh? Wama zai hada zuri’a daku bakusan darajar Dan Adam ba!…

     ” ummi ce ta dauki abinci sannan ta koma asubutin nan ta tarar abi yana ta hamdala…

    ” Cikin murmushin da yakusa kaiwa dariya tace anyi aiki lafiya ko!…

   ” maryam ce ta rungumeta suna murna…

    ” Alhamdulilah Allah yakara masa lafiya..

      ” suka ce Amin…

          ” abi yace kinga yanzu yana murmurewa sai ayi zancen auren sa da farida!.??

     ” haba abi yakakeso akamayar da jiya yau ai kawai kadaina wannan zancen ma…

    ” saddika tace what am telling him kenan…

    ” Anan Dr yafito ya sanar musu cewar tomorrow zasu iya ganinsa…

Birni…

    Mumy mumy kefa muke jira kiyi sauri…

    ” oh firdausi irin wannan kira haka ko haruna ne ya gaji?

     ” haba mumy to haka za’abarsa atsaye kema aikinsan bazai yihuba!

   ” sannu mai masoyi sannu nace miki toh ina faridar ta shiga?

    ” Ai tana mota ita da mama farida…

     ” fitarsu ke da wuya haruna ya shiga mota Nan dady shima ya shiga…

     ” cikin girmamawa haruna yace ince lafiya najika shiru?

    ” kaima kafada haruna anzo tambayar auren k’ande ne!…

     ” duk’an su suka kace k’ande…

      ” hankalin haruna yafi nakowa tashi cikin in ina yace wanene yaron?

    ” isyaku ne dan gidan alhaji datti yaro nutsatse…

       ” firdausi da murna ta isheta batasan lokacin da tace Alhamdulilah ba…

    ” haruna da brain dinsa take bugawa cikin zuciyarsa yace ai daman nasan narasata…

    ” dady ya kalli haruna yanaga kashiga damuwa ne ko yaron bashida tarbiya ne?

    ” Nan yayi murmushi yace nop ba haka bani ba ina tunanin anya tana sonsa?

     ” sosai ma kuwa yayin da dadi ya furta haka…firdausi tace toh yaushe za’akawo kudin ne…

    ” dady yace wata nagaba za’akawo…

    ” haruna ne kadai ya daure yace Allah yasa Alkhaire…

    “Ameen..

Basu isa Abuja ba sai karfe 8 nadare lokacin da suka shiga farfajeyar kowa kallon gidan yakeyi da dukiyar da Aka zuba…

    ” cikin palour suka karasa k’ande tana zaune tana shan tea sallamar su ta mik’ar da’ita tsayi tace sannunku da zuwa…

    ” farida tace oh yab kauye ansamu guri An zauna sai kace gidan su..

    ” dady yayi saurin katseta da cewa gidab sune mana oh kinga yadda kikaye kiba k’ande…

    ” Cikin murmushi tace Allah ko dady? Kasan nan bana aikin komai suna da masu aiki kala kala…

    ” haruna dake faman kallonta tunda suka shigo yakasa cewa komai…

    ” a’a harda kai yaya haruna? Ina yini…

    ” dauke kansa yayi, hakam yayiwa firdausi dadi…

    ” to yamai jikin cewar farida?

     ” Alhamdlhi jiki yayi sauki kam dan kuwa anyi aiki lafiya duk suna can asubutin…

       ” uwata me isa bakije ba?

     ” zuwana matsala ce dady…

    ” kowa ya zaro ido matsala kamar yaya?

    ” kamar yadda bazaku gani ba!…

     ” mumy tace kidai kije tsoron Allah…

      ” mikewa tayi ta kawo musu lemo tana mik’awa haruna yace am okay ba sai nasha ba…

    ” wane kallo tayi masa na tuhuma sannan tace bari naje nayi sallah sai na dawo…

    ” kowannen su ya mik’e ya nufi bandaki bayan sunyi Alwala kowa ya gabatar da sallah…

    Dady ne yace su mik’e sutafi Asubitin cikin murya mai karfi ya kira k’ande…

     ” Naam dady..

          ” banason sha shanci ki fito mutafi tare…

    ” cikin rashin jindadi tace toh mayafin ta ta saka sannan tafita zuwa motar…

    ” Direct asubutin suka isa nan Abi yafito ya tafi dasu sunata gaisawa…

     ” sannu da zuwan ku mumy farida sannu…

     ” cikin muryar girma tace ya mai jiki Abi?

     ” jiki Alhndlhi…

          ” tana shiga cikin dak’in su ummi suka fara sakar mata harara..

   ” ko kallonsu k’ande ba tayi ba ta samu guri daya ta zauna…

    ” cikin damuwa farida takara sa gaban gadon hamza tana kuka…

    ” kallon ta yayi da idanu wansa su kayi jajir sannan ya kau da kansa…

    ” farida ta rike hannun sa sannu dear Get well soon…

    ” Nan suka dinga hira dr ne ya shigo ya sanar dasu da sudan fita haka suka fita..

    ” kande da ke bakin kofar dak’in Dr yafito yace i think hamza na kirar wata acikin nan…

    ” mumy tayi saurin cewa bazai huce farida ba..

     ” ku barshi ya huta ku mik’a masa wannan towel din ya mikawa k’ande…” k’ande ce takalli kowa ba ma ummi da ta tsira mata ido, haruna ta kallah ta lurah bama kallon ta yakeyi ba… +

      ” Dr fabrick yace collect it mana!

     ” amsa tayi sannan ta bude dak’in ajiye masa towel din tayi batare da ta kalke shi ba…

     ” Ahankali hamza ya rik’e mayafinta yana kokarin yimata magana..

     ” fizgewa tayi tace karabu dani karabu dani!..

      ” bayan fitowar kande saddika ta shiga hawayen da taga idom hamza yana yi shine ya kara tsoratar da’ita…

     ” yaya kadaina saka damuwa cikin ranka please lafiyarka tafi komai fa…

    ” Nan ta sanar da ummi akwai question mark akan kande fa..

     ” ummi tace ke ba wannan ne problem din ba i think zafin aikin ne…

     ” okay saddika ta ambata tabar gurin…

Nan dady da abi suke tattaunawa akan yadda zasu hada auren…

     ” Abi yace aine yar gurinka nake kwadaye farida ita Nakeso ahada da hamza..

     ” kai mashaa Allah kaga kuwa sai ahada haruna da firdausi tunda naga suna san junansu…

    ” Aikuwa hakan yayi…

      ” Lokacin da suka koma gida anata hira kande dai na dak’e tuna nin ta daya yaya rayuwar zata kasance agaba? Wanne irin matsala ce take tunkarone? Amsar data kasa bawa kanta kenan…

    ” Dr Ne ya kira ummi..

          ” gaskiya hamza yana matsala over thinking yakeyi yakamata asan menene matsalar sa?

   ” several times ina tambayar sa dr but amsar daya ce kullum hawaye..

     ” okay karki damu nan da 4days zamu sallame shi ….

        ” okay likita nagode…

       Da safe ma abi da kande ne su kadai kuka je asubutin a yayen da ummi ta dawo gida…

      ” Sannu son yajikin naka?

     ” cikin wane yanayi na ban tausayi yace Abi babu sauke!..

    ” haba hamza mai isa kake mai da kanka baya…

     ” Abi indai zan kasance a haka wallahi bazan taba gaba ba yakamata ku dube halin danake ciki in bahaka ba ina gab da mutuwa…

    ” hamza kadaina fadin irin kalaman nan domin ita mutuwa sai lokacin ka yayi kuma bana tunanin akwai soyayyar data huce ta iyaye…

    ” k’ande dake tsayi agurin tana kallon su, Abi yace bari naje guri. Likita nadawo…

     ” bayan fitar Abi kande tayi hanyar kofa…

    ” hamza ne yace ki taimaka kitsaya domin na sanar dake sakon zuciyata, taimakon sona da zakeyi kamar ceton raini, ki tsaya kije kalamai daga bakina…

    ” cikin hawaye tace ne yar talakawa ce kuma ma abociyar wari da doyi gani dakikeya, kai kuwa me zakiyi da irin maccen nan?farida itace daidai dakai classy, gentle..lady…

        ” aisha ki sone, karki gujeni barina ni kadai ba karamin hadari bani ba, ko da ba kyasona ki daure ki aure ne…

     ” mai isa kakeson sakani cikin matsala? Kanason rayuwata kullum baya da gaba karka manta akwai bamban ci atsakanin mu dan haka rabuwa da soyayyata shine yafi yi maka Alkhairi ta buga kofar ta fita…

Bayan kwana uku an sallamo hamza bakomai ke damun ummi ba illah rashin walwalarsa yau su mumy suke shirin komawa gida farida ce tace mumy tabbas hamza ya chanja min ba kamar da ba, idan zai fadi sunana sai yace Aisha..

     ” Too karki damu komai zaiyi sauki inshaa Allah..

     ” k’ande dake faman shirin kayanta saddika tace ai naga sai yamma zaku tafi ai…

    ” cikin rashin fara’a tace eh…

     ” hamza dake faman kwara amai ummi nayi masa sannu cikin damuwa da jin kai irin na uwa tace hamza?..
  
   ” Naaaam..

        ” me ke damunka ne wai?

     ” cikin hawaye yace soyayyar yar kauye…

    ” bangani ba…

” zaki gane amma not soon!!..K’ande ce ta shiga dak’in haruna domin ansar wayarsa… +

     ” mik’ewa yayi ya matsa daf da’ita cikin murya tana sarkewa yace me isa kikeson yaudarar zuciyar da ta dadi tana rainon soyayyarki? Me isa kikeso ke butulci wa tsohowar soyayya? Ina sonki k’ande, ina sonki Aisha zan fito na sanar da duniya akan soyayyata…

    ” idonta ne yafara zubda hawaye…

      ” hannunsa yasa yace ki daina kuka ke *Ta dabance*ina kuma tare dake k’ande… kafin ya karasa maganar farida ta shigo….” K’ande ce ta shiga dak’in haruna domin ansar wayarsa… +

     ” mik’ewa yayi ya matsa daf da’ita cikin murya tana sarkewa yace me isa kikeson yaudarar zuciyar da ta dadi tana rainon soyayyarki? Me isa kikeso ke butulci wa tsohowar soyayya? Ina sonki k’ande, ina sonki Aisha zan fito na sanar da duniya akan soyayyata…

    ” idonta ne yafara zubda hawaye…

      ” hannunsa yasa yace ki daina kuka ke *Ta dabance* ina kuma tare dake k’ande… kafin ya karasa maganar farida ta shigo….

Shigowar farida d’akin nasa bai hanashi cigaba da maganganu masu mutukar tsoratar wa ba….

      ” farida da ta tsaya daga bakin kofa tace yaya haruna kaine kake hawaye…

      ” hannun kande ya rike dake faman kuka yace wallahi wannan itace mahadin rayuwata inasonta ina kaunarta farida kisanar da ita ta soni danAllah, mafarkin ta yazama kamar ruwa agurina kullum sai nayi kamar yadda tunanin ta ya hanani sukuni, Nazo abuja kawai dan dai naganki, zancen aurenki da isyaku pls ki tureshi ki kasance matata DanAllah….

     ” k’ande dake faman kuka hakan yasa ta fuzge hannunta sannan ta bar dak’in…

    ” farida dake cikin duniyar tunani anya ba kande asiri tayiwa haruna ba? Fita tayi tahuce dak’in direct dakin mumy ta shega cikin haki da damuwa…

    ” mai yafaru farida…

           ” mumy wallahi akwai babbar matsala fa…

     ” matsalar me?

          ” can kuma tayi shiru sanadiyar wasu yan tunanuka da tayi…

      ” common tell me know…

      ” wane murmushi mai ciki da tashin hankali tayi sannan tace lah tsokanar ki nakeyi fa…

       ” aa farida tunda kika furta to akwai matsalar…

     ” karki damu zaki sane a hankali…

     ” k’ande dake faman kuka a dak’i can kuma sai cewa tayi Ya Allah, you are truly merciful, please forgive me Choose for me,what is best….

     ” maryam tace ke kuma ke dawa?

    ” cikin masifa kande tace nayi miki magana ne?

    ” Dallah malama daga tambaya?

     ” malamai dai wane yace kiyi tambayar aikin banza kawai…

       ” ke yar talakawa gyara bakinki kafin nace miki mutunci wallahi…

      ” harara kande ta zabga mata sannan ta fita daga dak’in…

Shirya shiryan tafiya sukeyi kande takasa hada idanun ta dana haruna balle uwa uba hamza da bata kaunar ganinsa!

   ” oh kande kin wane rabi sai kace mage…

    ” ummi tace ai wannan yarinyar ta dabance…

      ” mama farida tace abun dariya ma sai ku rantse irin mumina ce…

    ” sai da ta gama jinsu dukk’an nin su sannan tace ai rabewa itace daidai ga mutumin da ake k’yararsa…

     ” kamar yaya cewar mumy…

       ” dady ne ya katsesu da cewa kuyi maza kufito haruna baya jindadi dan haka ni zanyi driving din….

     ” firdausi ce tace dady me ke damunsa?

       ” kije ki tambayi shi mana…

     ” K’ande dake faman daukar ledarta adaki farida ta shigo tace wallahi kande kije tsoron Allah yanzu kirasa wanda zakiyiwa asiri sai yaya to bari in gayamiki kizuba ido kigane auren firdausi da haruna babu fashi…

      ” dariya kande tayi tace ai kinsan komai nufin Allah ne na firdausi ne ya fito…

     ” maryam tayi saurin fadin dady na jiran ku fa…

    ” Nan suka sakko Abi sai fada yakeyiwa kande ai kwanakin sunyi kadan…

    ” Acikin zuciyarta tace wa’zai iya zama da bakar kaddara…

    ” au kinajina?

         ” zandawo abi karka damu…

      ” suna kokarin shiga mota kenan hamza yafito tare da dafe bango….

    ” dady yayi saurin fadin me zangani haka?

     ” please kutafi dani zanfi samun sauke fiye da da…

    ” Dady ne yace kayi hakuri kasamu sauki hamza, after that ma akwai company uku suna jiran sign dinka katsaya ka gina sana’arka…..

     ” hawayen da yafara zuba a idonsa yasa ummi cewa haba nafa gaje wannan wacce irin cutace abu kadan hawaye….

    ” abi yace to ko farida ta zauna…

      ” hararar da hamza yayi mata yasa tace inada lectures….Haka sukayi sallama tare da godiya… +

Abi ne yaruke hannun hamza suka shiga ciki suna zaune a palour ummi tace ne dai ankar dani wallahi wannan wacce irin cutace?

    ” saddika cikin yamutse fuska tace wallahi soyayya ce ummi….

     ” maryam ma tace ai gashinan zai maida kansa kamar mahaukaci yanzu haka yarinyar dayake so din ba clss dinsa bace ba…

      ” Abi yace hamza kagaya min gaskiyar abunda ke damunka…

     ” Abi to zaka magance mun ita?

     ” indai zan iya zan magance maka son…

       ” wata yarinya nakeso nake kuma so a aura min ita!..

      ” ummi tayi saurin cewa wacece?

         ” hamza ya kalli abi tare da rungume sa yace Abi bata sona bata kyaunata!…

    ” abi yayi hanzarin cewa what yar gidan uban wacece?

     ” ba yar kowa bace ba…

      ”  okay karka damu bari naje office ana jirana when am back zamu tattauna son but kadaina saka damuwa aranka….

      ” ummi tace hamza kenan Allah yabaka Mata tagare….

      ” kallon ta yayi yace ai Allah yabani ma…

Su k’ande suna komawa gida kowanne ya shiga d’akin sa..

      ” wanka kande tayi sannan ta dau littafan islamiyyar ta duk da ta makara amma hakan bai hanata zuwa ba bata tarar da kowa a palour ba hakan yasa tayi hucewar ta suka gaisa da baba mai gadi har yayi mata ban gajiya…

     ” sauri sauri takeyi dan ta karasa tana karasawa taga malam umar ne aciki gashi tambayoyi yakeyi sai da cikin ta ya dan k’ada dan batayi karatu ba…


     ” malam ina yini?

” lafiya lou sai yanzu zakizo makarantar?

      ” wallahi munyi tafiya ne malam yanzu muka dawo…

     ” tohm jiki zauna…

” Fatima tace sannu kunshaa hanya amma kika tawo yau…

     ” ke ne inba dole ba mai zaisa nabar makaranta , tsorona daya yanzu banyi karatu ba..

    ” karki damu zaki haye inshaa Allah…

    ” Abdullahi uba ga tambayar ka akwai hadisi mai lamba 6846,6406 bukari da muslim ne suka rawaito Amma lafazin hadisin na muslim ne me hadisin yake  magana akai…

      ” hadisin yayi magana akan kalmomin da Allah yakeso ne.. An karbo
daga gareshi -Abi Huraira Allah ya qara yarda a gareshi- daga Manzon Allah SAW yace: (( Kalmomi guda biyu masu sauki akan harshe, masu nauyi akan mizani -ranar alqiyama-, Allah mai Rahama yana sonsu :
*SUB-HÃNALLAHI WA BI HAMDIHI, SUB-HÃNALLAHIL AZÊM ))*

” jazakallah…

    ” Aisha ga tambayar ki, wacce addu’a ce sayyadl istigfari? A wane hadisi aka kawota? Wanene ya rawaito? Da kuma falalarta…

    ” sai da cikin kande ya kada sannan ta mike cikin rashin kuzari tace 
Bukari ne ya rawaito cikin hadisin sa mai lamba 6306, itace shugaba cikin zikran neman gafara kamar yadda yazo acikin hadisi cewa : An karbo daga Shaddad bin Aus daga Annabi SAW yace: “Shugaba cikin zikran neman gafara mutum yace: *(( ALLÃHUMMA ANTA RABBY LÃ’ILAHA ILLA ANTA, KHALAQ-TANY WA ANA ABDUKA, WA ANA ALA AHDIKA WA WA’ADIKA MAS-TA’DA’ATU, A’UZU BIKA MIN SHARRI MA SANA’ATU, ABUU’U LAKA BINI’IMATIKA ALAYYA,WA ABUU’U BI ZANBY, FAG-FIRLY, INNAHU LÃ YAGFIRUZ ZUNUUBA ILLÃ ANTA))*

  Kuma yace: (( Duk wanda ya fad’eta a yini yana mai sakan-kancewa da ita, kuma ya mutu a wannan yinin kafin ya kai yammaci, to yana cikin ‘yan aljanna, kuma duk wanda ya fad’eta da daddare, alhali yana mai sakan-kancewa da ita, sai ya mutu kafin sãfiya, to yana cikin ‘yan aljanna…

    ” barakallahu fiyki…Mumy ce ke faman masifa da zagi a palour wannan yar iskar yarinyar ina ta shiga haka zata barmana palour kacha kacha….

    ” mama farida ce ta sakko daga sama to mekike nufi idan batanan Ne zangyara…

     ” karkiyi min rashin kunya wallahi…

     ” rashin kunya ta nawa kuma ai sai dai in bakiyi abunda za’ayi miki fitsarar bani kin sangarta ‘ya’ya basayin komai basu iya komai ba sai kwanciya ko kina tunanin ba gata kukeyiwa kande ba?

     ” gidan uban su ne babu abunda zatayi…

       ” itama gidan uban nata ne tunda kawunta ne….

    ” k’ande ke faman tafiya ita kadai burinta taje tayi sallah ta kwanta wata sallama taje sai da kirjinta ya buga…

    ” a hankali ta amsa tare da fadin ina yini?

      ” lpy ba lafiya ba kinbarni cikin k’ewa da damuwa, gaskiya ya kamata ki samu waya Aisha…

      ” Allah uncle isyaku?

          ” Allah kuwa wannan kwanakin dakikayi duk sun hargetsani wallahi kullum tattausar muryarki kemin yawo acikin kaina, soyayyar ki ta faskara kuma nan da next mouth za’akawo kudi fa…

     ” kamarya?

      ” cikin murmushi da mazan taka hace ai an aiko gidan ku…

      ” dakewa tayi tace Allah ya zabama abunda yafi alheri…

      ” Ameen matas, k’insan Allah ina masifaffan k’aunar k’i ne bikin ma banaso yakai 5mouth wallahi nagaji….

     ” Dariya tasaka tace ne wallahi kunya kake bani uncle…

      ” zan ma daina baki ayayin dana fara kashe ki da kalamai na…

     ” bye bye ni dai nazo gida…

     ” shigar kande kenan mumy tace toh tam badaddiya, mai bin maza, daga dawowa har kin ja hijjabi kin fita wa zai gyara miki gidan?

    ” mumy makaranta fa naje…

     ” Aa ilimin kika jawo dallah shige ki gyara gidan ki kuma dora girke…

    ” tohm ta Ambata sannan ta shiga dak’in ta…

    ” gurin karfe tara tana kasan dak’in ta a zaune sai ga haruna ya murda kofar ya shigo…

    ” zama yayi kusa da’ita ga takeaway na siyo miki nasan bakyacin couscous…

     ” kallonsa kawai takeyi…

     ” kanwata please kidaina saka damuwa kikuma daina zama da yunwa kinje?

     ” Tohm, yaya waya nakeso kacika kasiyamun please….

    ” ban yarda ke riki waya ba!…

       ” shiru tayi tace to…

              ” wayannan mayafan ke daina saka su zankaro miki hijjabai…

    ” ita dai kawai da to take binsa takasa fahimtar inda ya dosa…

     ” cikin rashin fara’a tace yaya ina Amira?

       ” yanzu kice Amirata…

     ” har yafita tana kallonsa…

      “Da safe cikin ta ke  danyi mata ciwo bata gyara dak’in da huri ba…..

    ” Tana fita mumy ta wanka mata mari…

      Cikin kuka zata koma dak’in ta haruna ya rikota…

      ” rungumesa tayi tana kuka…

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]