[Advertisements⬇️]

KANDALA CHAPTER 3 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

KANDALA


CHAPTER 3
Wane k’allo k’ande tayi mata sannan ta dauk’a garin sauri sai taje ta bangaje mutum….. +

” k’e? wacece ke zaki bangaje ne?

” kayi hakuri!

” koba k’ande ce ke ba tasss ya wanka mata mari….

Ma k’wancin ta ta rik’e Amma Dai Nabaka hakuri ko?

” ko zaki rama ne jahila ‘yar kauye? Ai sai Dai kiyi aikatau agidan nan yadda kike haka babu mai iya k’allon ki…

” mtswe taja tatafi dak’inta tana shiga wane lalataccen kuka ta saki rabonta da kuka har ta manta wane tsaki tayi tare da fad’in Allah ya’isa mugu kuma sai na rama!

” farida ce ta dan tauna cingam tace sorry uncle yarinyar sai hakuri fa!

” don’t mind me dear ne tsoro take bani fa!..

” hmm manta da’ita zan koya mata hank’ali ya mum ya abuja?

” oll fine!…

” k’ada ido farida tayi tace nayi missing naka wallahi…

   ” same dear!..

” Tsayawa farida tayi tana kallon uncle matashi ne d’an shekara 32 bak’ine Amma yanada hanci kuma yanada ido, akwai shi da girman kai da tak’ama ga kudi agurinsa kamar mi, engineer ne, Yana son mace yar gayu me kuma ilimi, hak’an yasa farida take burgeshi har tayi tunanin sonta yake kullum yazo suna tare hajiya har kara girma ma hamza tak’eyi…

    ” Gurin 7 kowa yana palour a zaune sunata hira Dady ya shigo!

   ” firdausi ce tace sannu da zuwa dad..

     ” yauwa ‘yan gidan dad ina kanwar taku?

    ” hajiya tace wakake nufi Alhaji?

   ” k’ande mana!

        ” Au k’ande ka dakko? Kai amma abun yayi kyau tayi wata dariyar mugunta!…

     ” k’ande dake daki tana zaune ga sanyi ya’isheta fitowa tayi sanyi da bak’in hijjabi tayi sallama tasamu kusa da firdausi ta zauna hajiya ina yini?

   ” lpylou k’ande ya mutun k’auye?

   ” mutun kauye suna lpya kamar yadda kuke sannu da zuwa Alhaji!….

      ” yauwa ‘yata kinci Abinci? A’a banci ba kuma yunwa nakeji…

     ” kallonta sukayi su farida da hamza suka saka dariya!…

    ” shiru tayi bataci musu komai ba!..

      ” hajiya da Abincin ne?

     ” A’a Alhaji babu sai dai tasha kwak’i…

    ” ke farida dak’ko min indomie na dafa mata!

    ” suka hada bak’i k’anden zaka dafawa!!!

    ” Ke bazaki dakko bani?

    ” Aa alhaji kar nasaka wahala zan sha kwak’in..

    ” firdausi ce ta daka mata tsawa dallah matsa daga kusa dani wannan doyin kauyen naku baza arasa cuta ba!

   ” k’ande abun yayi mata ciwo tace to menene na yimun tsawa sai kace uwata, kauye kuma kowa yana dashi dadinta ma inda kaza ta fito da kwai anan take kashi!
useless kawai jahila!!! +

    ” dady ne yace toh daman ku bakusan Asalin ku bani ba? To nema k’afin nazama wane har da fitsari nayi yawo!…

      ” Hajiya tace shiga can zakiga kitchen ki dauki kwak’i a kofi!

    ” Toh tace sannan taje ta dakko tajika tadawo tace hajiya sukari…

    ” budar bakin hajiya tace ubanki ne yakawo sikarin? Dallah jahila sha haka a kauye da ubanki suke sha??

    ” Alhaji ne yafi to daga toilet k’ande lafiya naganki a tsaya?

    ” nace subani sukari sun tsaya suna ciwa asalin ka mutunci wai ban isa nasha zaki ba tunda ba yayanka ne ya kawo ba!!!

    ” Dariya Alhaji yayi yace kawo har madara zan zuba miki ya karba ya hada mata mai dadi…

    ” haruna yana shigowa yajiyo muryar k’ande yace Alhaji yakawo jaraba har gidan sa!

Babu Wanda ya kalla Sai hamza suka gaisa sannan ya shige dak’in sa!

    ” k’ande ce ta shige dak’in datake zaune tana ta shan kwakin ta wata dariya ta saki sannan tace dole yan birni su dinga kiba wanga madara da sukari dadi…

    ” firdausi ce ta kalli hajiyar su tace wallahi ba zai yihuba kowanne kala da dutse sai dad ya kawo dubi yarinyar nan wata dirty da’ita Amma dady yana ji da’ita!

    ” hamza ne yayi murmushi sannan yace cooldown dear ai ku gaba takaiku kun samu mai aiki….

    ” mum tace thats true fa ai kuwa kuma ku kwantar da hankalin ku domin sai na azabtar da’ita!…

   ” yeap mum hakan za’ayi…

    ” hamza ne ya miki good night farida gobe kiyimin chips da egg kinji?

    ” oky!!!

     ” k’ande dake faman zaune ak’asan tahil ga katifa a gefen ta Amma ita tafeson sanyi sanyin kasa bandaki ta shiga taga ta kasa kunna ruwan gidan palour tafita ta ga babu kowa tafiya ta dinga yi har sai da ta’isa kofar gidan sannu baba tsoho dan Allah zo ka kunna min ruwan bandaki Alwala zanyi…

   ” Alhaji ya hana mu shiga cikin gidan!..

     ” haba dan tsoho Alwala fa nace zanyi haba!

    ” To muje..

     ” suna isa ya nuna mata yadda zatayi tace to nagode yana fita yaga haruna!…

     ” baba me kazoyi anan kuma?

    ” yarinyar nan ce tace in kunna mata fanfo bata iya ba!

    ” toh jika…

       ” k’ande ce ta murguda baki ko ba zaiyi sallar bani? Sai wane hararata kakeyi!…

    ” kallon ta yayi hijjabin jikinta baki ne Amma saboda kod’ewa har yazama baki!…

  ” Dak’in ta sayo tashiga tayi Alwala ta kwanta a kasa ahaka bacci ya kamata!

    ” Haruna kuwa kulle dakin yayi sannan yace ai bazan kulaki ba ballanta na aji k’anmu!…

    ” Da asuba dady ya shigo dak’inta azaune ya taddata k’an sallaya…

    ” ‘yata kin tashi?

   ” eh baba me kakeso adafa maka?

     ” kin iya soya dankali?

    ” eh na iya kasan muna cinsa muma sai dai ka koyamin yadda zan kunna abin dafawa!….

     ” To muje na koya miki…

      ” ya nuna mata komai da komai ta firayi mai yawa ta soya ta wanke wasu flask ta zuba ta dura ruwan shayi duk tajera akan dinning da yake dama tasan abinci ake durawa, ta wanke kwanuka ta shari dak’i ko’ina fafes sannan ta ji nata dakin ta wanke bandaki!..

   ” sai karfe 9 kowa ya fito duk suna zaune sunfara ci hamza yace chips dinnan yayi dadi fa dubi yadda yaje maggi!…

    ” kowa yayi shiru farida sai rawar kai takeyi!..

   ” haruna yana fitowa yasamu guri ya zauna firdausi ita alallai son haruna takeyi domin in ya zauna ta dinga kallon sa kenan!

    ” k’ande ce ta fito haruna kuma ya taso tace shi kuwa haruna haushin kallon firdausi yakeji!

    ” ina kwana? ko kallonta baiyi ba yace lpya! +

     ” hamza kuwa tun kafin ta karaso yace tsaya anan karki samu muyi amai!…

     ” Alhaji yace menene haka hamza? Ranka zai bace fa!

   ” baba ina ne dak’inka in gyara!

    ” Ai kuwa dakina ya dadi ba agyare ba!

    ” k’ande ta kalle su firdausi tace sai soyayyar ba’a neman lada!…

     ” kaikuma uncle kake kowa baruwanka dani tunda ne bana kulaka banson cin zarafi….

    ” yama kara yimiki ranki sai ya bace!

    ” farida tace kaje jahila kaje jahila!

    ” K’ande da ranta yayi dubu ya bace sai cewa tayi jahilai dai tayi ficewarta!

    ” dady ne yace kuna gab da fuskantar hukunci…

     “Tana gama gyara wa ta dawo ita kanta tasan wari takeyi kayanta ta duba ta shafa Alimun…

    ” fita sukayi da dady ya kaita prime anyi mata komai sukace ss3 zasu sakata ran monday ta fara zuwa,

    ” tun amota take godiya har aka sauke dady a office farida aka dakko…

     ” ke mekikeyi a mota dallah malama sauka!

    ” To ina zanje?

      ” Hankada ta tayi sannan tace driver yaja mota!

    ” k’ande ce ta kalli kanta kuka tafarayi da kyar ta’isa gida!…

    ” shigarta ke da wuya hajiya ta wanka mata mari nan ta dinga duk’anta hakuri k’ande ta dinga bata, dan uwarki zakizo gidana ki dinga yimun iskanci banza jaka kawai hankada ta tayi luuuuu haruna ya riki ta mekikaye mata?

   ” tana kuka tace wallahi banyi mata komai ba wallhi ni ka maidani gurin iya habu kamaida ni…

    ” cikin wata sanyar yiyar murya yace daina kuka ina tare dake….

     ” kallonsa tafarayi sai kuma taje dadin maganar! Da gaske kana tare dani? …. Shigarta k’e da wuya hajiya ta wank’a mata mari nan ta dinga duk’anta hakuri k’ande ta dinga bata, dan uwark’i zakizo gidana ki dinga yimun iskanci banza jaka k’awai hank’ada ta tayi luuuuu haruna ya rik’i ta mekikaye mata? +

   ” tana kuka tace wallahi banyi mata komai ba wallhi ni ka maidani gurin iya habu kamaida ni…

    ” cikin wata sanyar yiyar murya yace daina kuka ina tare dake….

     ” kallonsa tafarayi sai kuma taje dadin maganar! Da gaske kana tare dani?

    Daga Mata Kai yayi alamar “eh”….

Murmushi tayi lokaci daya kuma hawayen ta ya tsaya dak’in ta ta shiga Alwala tayi tazo tayi sallah….

  ” hajiya dak’e fa man masifa da bala’i farida na zuga ta!

    ” au hajiya kallanta zaki dinga yi ne? Ta ci abinci tayi kashe? Ai kuwa bazai yihuba dan haka daga yau ita zata dinga dafa abinci…

    ” hakane ina zuwa shigar hajiya dak’in ba wuya ta tarar da K’ande tana kan sallah takalmin kafarta ta chilla mata!…..

   ” k’ande ce tace  innalillahi hajiya lafiya takalmi kika cilla min  fa?

    ” au ba’asi kike nema nayi din sai uban me? Ki tashi ki dafa shinkafa da miya kuma kada ki shigar min kitchen da takalmi kicere shi a kofar kitchen din i hope you understand me?

    ” k’ande ce tayi murmushi indai kunne ne yakeji to aikuwa na jiki…

    ” karma kije idan na rufe ki da duk’a za kije ai!….

    ” shiru tayi mata sannan ta mik’e hijjabin jikin tane yake ta wari gashi bata da wane hijjabin direct kitchen tatafi…..

” ita Kuma hajiya ta huce palour tana yar iskar yarinya ai baki isa ki mulki ne ba!

   ” farida ce ta saka dariya yauwa mumcy gwara da kikaye mata haka ai…

   ” k’ande kuwa tana kitchen abun duniya duk ya isheta haushin kanta ma takeji data biyo alhaji gidansa ta tuni tana tare da iya habu!

    ” haruna ne ya katse mata tunanin ta lpya k’ande?

     ” uhmmm bakomai…

           ” okay!

   ” cup ya dauka zai fita k’ande tace ya haruna katsaya Na karasa Abincin sai kaci!…

    ” never mind zansha tea ma!

     ” k’ande ta yamutsa fuska ga Abinci me tea zaiyi maka!…

     ” kinsan ciki ciki ne tea is okay for me!…

     ” yi tayi kamar zatayi kuka ita batasan me isa ta damu da ya haruna ba yanzu!  Chan kuma tace to ai shikenan tunda danuwa na ma k’yama tata yakeyi…

    ” any way so kike nace miki gurin matata zanje tanason gani na ne!

    ” matarka kuma dama kayi aure ne!…

    ” Banza yayi mata ya fita!….

   ” wane sabon tagumi ta saka chan taje kamar an dasa mata duk’a!.

   ” Dallah yar kauye yi sauri ki karasa mana abincin kafin ranki ya bace kuma kowa kisaka masa A plate!..

  ” Tohm mum!!! haka takarasa ta zubawa kowa ta kaimusu dinning tana kaiwa hamza ta ajiye masa!… +

    ” wata tsawa ya daka mata will you move away! Kina tunanin naci abincin ki? God forbid! Kalleki how dirty you are ware ko ta’ina look at your hijjab, yasaka dariya fuskarki kamar bakar daddawa, carry your jagwalgwalo and move away….

    ” mumy ce da Firdausi suka saka dariya….

   ” farida kuma tace dont mind her my dear bari na dafa maka indomie, ne bansan irin k’ande ba ita ta dabance bata ganin kazantar ta fa!..h

    ” K’ande tana shiga kitchen ta saka kuka mai ciki da tausayi, wanke fuskar ta tayi sannan tayi wanke wanke tazo ta huce….

     ” tsaki hamza yayi!…

        ” mumy wai ina uncle haruna ne?

     ” dazu yazo mun gaisa kinsan yana masters dinsa…

    ” wane murmushi firdausi tayi azuciyar ta kuma tace burina ya kusa cika…

K’ande tana zaune tunanin kauye kawai takeyi tunanin ma haifin ta tafara ahaka taga har 9 tayi gashi hijjabin jikinta ya dameta mik’ewa tayi tatafi bangaren baba!..

   Sallama tayi sannan tace baba in shigo?

   ” A’a ‘yar gidan baba shigo mana!…

    ” tsaya anan dan ubanki…

   ” menene haka hajiya!…

   ” bansani ba sai dai kai kaje kasameta amma kar ta sake ta shigomin dak’in mijina!

    ” baba ne yace hmm sannan yafita ‘yar gidan baba ya akayi?

   ” i’donta har yafara cikowa tace sanyi nakeji kuma babu bargo!

   ” mantawa nayi wallahi Amma zan bari na dakko miki wane!

    ” baba har da omo!

      ” jim kadan yafito to gashi gobe inkin dawo daga makaranta maje ki zabe abunda kikeso…

   ” Tohm tace sannan ta fita!

    Tana shigowa palour ya haruna yana danna waya firdausi kowa kallon sa kawai takeyi tana murmushi!….

    ” k’ande har ta huce haruna yace bargon wa kika dakko?

     ” banzs tayi masa tana kokarin hucewa…

    ” kaje dabba ko zata nuna maka halin yan kauye!…

     ” k’ande kuwa taje maganar har cikin ranta!

   ” haruna yace kardai gurin baba mai gadi kika karbo?

    ” dan dai banda imani yaza’ayi Na karbo gurin mai gadi…

   ” Ai nasan zaki ‘iya…

” D’akin ta ta shiga tafara wanke hijjabin ta sannan tayi dauren kirje tasaka wata doguwar riga sannan ta kwanta!…

   ” Da Asuba baba ya tashita bayan ya dawo daga masallaci yace K’ande?

   ” Naam baba!..

” yauwa magana nakeso muyi dake dama so nakeyi na aure mama farida!…

    ” k’ande tayi tiriss ta kauye?

    ” eh ita ya dabi’un ta yake?

   ” huu’ujun to dai gaskiya tanada hassada dakuma mugunta, Amma kuma tunda suke tare da goggo basu taba rigima ba kuma tasan darajar baban mu kafin ya mutu ni kadaice bama shiri da ‘itah Amma da kabar hajiya baba batayi maka komai fa?

    ” A’a inason na taimaki mama farida ne!..

   ” ai kuwa kamar kasan ba’kin jinin aurene dasu!…

    K’ande kenan ai komai na rayuwa Allah yariga ya rubuta tub kafin a haife ka! Kuma Allah shi yakeyin komai, Allah ke bada miji ba dan’adam ba kudaina jefan mutane da sunki samun miji inkunayin haka tamkar bakusan Allah ne kadai mai bayarwa ba A lokacin da kukaye wa wane bori kema bakisan karshen rayuwar ki ba, kuma zaki haihu in aka gayawa yarki kima zakije ba dadi….hakane baba Allah ya yafi mana! +

    ” Da daddare zab tafi china in nadawo za’ayi bikin ki koma barcin ki kafin lokacin makaranta yayi…

   ” Tohm..

” gurin karfe 7 na safe hajiya ta sirka kankara ta shigo dak’in ta kwarawa K’ande A fuskarta!

    ” firgen tatashi tana tare idonta da ya k’ada tace ina kwana hajiya!

  ” tashi malama kiyi mana breakfast…

    ” Toh tace sannan tatafi ta dorah…

K’auye

    Haba goggo kinbi kinsa kande aranki!..

   ” Abbas kenan k’ande fa ‘ya tace dole na damu da halin da take ciki nasan bata cikin kwanciyar hankali!…

    ” To yanzu me zakiyi mata ta riga ta tafi!…

   ” ya kabiru ne yace har garinnan yayi shiru annoba tatafi…

   ” mama farida tace eh wallahi datune tanata zanbada mana fitsara….

     ” koma menene Allah yatsre min ‘yata yabata ilimin datake nema!…

   ” ya Abbas yace oh su inna soyayyar k’ande ta tashi…

    ” dariya tayi tace wanga soyayya ta d’ad’e!

  ” ya kabiru yace Ai gwara goggo iya habu tana can zazzabin rashin k’ande!…

   ” Dariya suka saka…


Birni

  Yau sati daya kenan k’ande tanata zuwa makaranta kullum sai tayi wanke da guga Kullum sai sunci mata mutunci!…

   ” yau ma tana daki takasa yin maths din kuka ke kokarin zubo mata mik’ewa tayi ta dake tayi sallama a kofar dak’in haruna yaya na shigo?

   ” eh shigo..

” langwabar da kai tayi yaya dan Allah koyamin assignment dinnan!

   ” to yace sannan karbe bairon yafara koya mata!

   ” Suna gamawa tayi godiya ta huce dak’inta tana shiga bandaki tabar littafin ta ak’an gado…

   ” hajiya tana shigo tace yanzu kin mayar da littafan nan mafi mahimmanci to bari kiga tafara yagawa!..

   ” hajiya danAllah karki yaga danAllah…

    ” tsake taja tayaga sannan tatafi…

  ” kuka K’ande ta fashi dashi haruna duk yana jinsu!

  ” littafi ya dauka sabo yayi mata wane sai da tayi bacci ya saka mata acikin jaka!…

    ” Da safe tana hanya tanata tunanin dukan mr philips zaiyi mata abakin gate ta gadu dashi!

  ” Aisha where is your assignment??

    ” jakarta ta bude tana danyin dabara kiris tayi karo da sabon littafi taba budewa taga Assignment din ya haruna yakarayi mata!..

   ” mik’ewa tayi..

       ” heee Aisha  weldone! I have wrote some classwork group work so go and start solving it!

   ” okay sir wane tsalle tayi  har da juye ya haruna yayi ar……Jak’arta ta bude tana d’anyin da bara k’iris tayi karo da sabon littafi taba budewa taga Assignment din ya haruna yakarayi mata!.. +

   ” mik’ewa tayi..

       ” heee Aisha  weldone! I have wrote some classwork, group work so go and start solving it!

   ” okay sir wane tsalle tayi har da juye ya haruna yayi arayuwa, wane murmushi ta saka mai ciki da kauna…..

  Good morning class!

   ” morning esha!

      ” Where is the classwork?

    ”  look at the board!

        ” mujahid Ina nafeesa?

     ” I think tana hanya you’re lucky fa nazata bakiyi assignment dinki ba!

    ” hmm k’ai dai tunda nayi shikenan!

    ” Nafeesa ce ta shigo rai abace Yan group dinsu suka kalleta how comes bakiyi ba?

    ” Amma Aisha baki kyauta min ba ai nayi tunanin zakiyi min!

   ” kamar ya cewar mujahid bakiga a gate yake karba ba!

   ” am sorry nafeesa u can’t understand me right know so let start our class work!..

    ” karfi biyu An tashi daga makaranta sun fito ita da nafeesa zasu tafi oh nafisa please escort me to uncle isyak’u…

    ” okay let go…

      ” uncle isyaku yana hango k’ande yafara gyara zama k’allon kansa yayi gashi black gajeri ga ido da hanci yanada rufin asirin sa, arayuwar sa k’ande tana burgeshi tunda ta shigo skull din yaji ya kamo da sonta!…

   Assalam excuse us sir!..

    ” Nafisa ce takara kiransa uncle isyaku!!..

    ” yes nafisa idris ya akayi?

    ” k’ande ce tace uhm sir about ur assignment are we going to answer all or…

     ” katseta yayi yace answer one if u can’t answer just live it!..

    ” Nafisa ce tace but sir u ask us to answer All fa!…

     ” k’ande kawai yake kallo okay Aisha kibar naki zanyi miki!…

     ” k’ande ce tace saikace wane brother nawa just live it please my brain is not off is on!…

     ” but to me i have the right to do anything that can make you happy!…

    ” Nafisa taja malama let go wannan mutumin bashida hankali…

    ” Nafisa ce tace anya basonki yakeyi ba?

    ” hehhe ai ne wannan bai taba burgeni ba kuma son maso wane yakeyi!!!…

    ” you mean kinada wanda kikeso?

    ” murmushi tayi tace nema son maso wani nakeyi ban tunanin zai soni!…

     ” suna tafiya suna hira Nafisa tace bye zan shiga layin mu sai gobe!

    ” kande tace to ta dau hanya tana ta tafiya ta hadu da wane saurayi yatara gashi ya sabule wando sai k’anbo yakeyi!!!

    ” Dariya tasaka masa tace kai mai bishiya akansa!  Dani kike wai?

” to dawa nake? +

      ” kaikuwa me yayi maka Zafi kaja wanda ka kasa sai kace wanda akayi masa Allura a!

    ” hahaha yarinya wannan dakike gani gayu sunansa yanzu duk yammatan dasuka ganni sona zasuyi!

    ” wai ai kaine dama suru malam ka gyara kayanka kaje ayi maka aske in bahaka ba gaba kanka har ‘ya’ya sai yafarayi!

    ” shiru yayi sannan yaja wandon sa ya tafi…

  Tana isa gida ta tarar da maigadi a waje sannu baba!

   ” kice da sannu k’ande ya akayi bakya biyo driver?

   ” baya zuwa ya dauke ne na tambayi shi yace hajiya tace ya daina dakko ne kuma makarantar da nisa!!!

    ” toh Allah ya taimaka!

    ” Ameen baba!

Tana shiga palour taga uncle Hamza yana tsaye bata gama saka kafarta ba taje saukar mari ya kara mata wani!

   ” me nayi maka?

    ” uwarki kikaye min banaci kidinga gyaran daki naba!…

    ” kande da idonta ya ciko da hawaye tace to yaushe kagayamin? Yau da safe kagayamin…

    ” farida ce tace ke agidan namu zaki dinga mayar mana da martani dan ubanki?

    ” hamza yace ai wannan jahila ce naga karfin halin alhaji da yasata a makaranta da baba mai gadi ya aura mata sai su dinga yimana aiki!

    ” hahaha wallhi kam!..

    ” wata muguwar dariya k’ande tayi azuciyar ta tace bakusan k’ande ba!!!

     ” Hanyar dak’inta tayi wane funcikota yayi bazaki bani hakuri ba?

   ” kukane ya subuce mata tace yi hakuri!..
   
     ” Hank’ada ta ya karayi!

   ” Dak’inta ta shiga sauri tayi tacire kaya tayi sallah sannan ta fito tafara share gurin tana cikin mopping firdausi ta sakko tana sani ta zubar da abinci tayi tafiyar ta!

    ” farida tana fitowa ta farke omo agurin itama tafita…

    ” k’ande dai bataci k’ala ba ta kwashe takarasa gyaran ta wanka tayi ta saka doguwar rigarta ta zauna tana assignment!

   ” Alwalar da tashiga zatayi firdausi ta shiga dakin ta dauke littafin ahanya sukayi karo da haruna!

    ” uhm yaya sannu da zuwa!

    ” banza yayi mata sannan ya shiga dakinsa!!!

    ” ita kuma tayi sauri ta hau sama!

    ” k’ande na fitowa tanemi littafi ta rasa kofar dakinta ta lika kamar tayi kuka! Sai Kuma ta koma tadauki wane littafin tafara rubutu…

    ” haruna ne yace lallai k’ande ta dabance ta gwammace tasaki wane data tambaya!

Bayan sallar la’asar tana zaune tana biya alkur’ani tajiyo muryar mumy tana k’ande k’ande???

   ” da sauri tafita Naam mumy!

     ” uwarki ce mumy karki kara cemin momy kice min hajiya tunda bani nahaifi ki ba!

    ” tohm…Ga chicken can ankawo kije kigyara ki soya kiyiwa Alhaji farfesu da fried rice da salad! +

    ” firdausi tace be fast! Yunwa nakeji!

    ” k’ande kamar ta rufeta da duka tace okay!!!

    ” haka ta shiga kitchen shinkafar tafara soyawa kafin ta tsane taje ta yanka kajin ta dura ahuta! Kafin ya dahu ta yanka salad din ta…

    ” nafisa ce tatawo gidansu kande tana isa baba mai gadi yace ina zakije?

    ” tace gurin Aisha zanje!.. 
  
    ” Gidan nan babu Aisha!

   ” Nan nafisa ta dinga yimasa bayani…

    ” ai sai kice k’ande!

      ” Dariya tayi tace ai bansan sunan da ake gaya mata ba!

     ” tana shiga palour taga haruna a zaune ina yini?

    ” ko kallonta baiyi ba yace lpya!

    ” Aisha tana nan?

      ” Tana kitchen nan zaki shiga!

    ” lah nafisa ai bakici min zakizo ba!.

    ” wannan uban aiki Aisha ina yan matan gidan?

    ” suna daki ai su basa aiki!

   ” kece jaka ki zakiyi musu? Wallahi kiyi tunani…

    ” a kauye ma ninakeyi…

    ” kauye ai daban da birni kinsaka wane hijjabi duk ya mutu gaki da kyau duk kidinga boye k’yan naki!

    ” uhm kingama assignment dinki?

   ” zuwa nayi muyi tare mama na gaisheki..

    ” ina Amsawa amma bari nagama aiki na zan share dakin baba kuma zanyi wankin kayan uniform dina!

    ” ai mayi tare bani nakarasa miki salad din…

   ” tohm, tayaya kika shigo kinsan ba asanni da Aisha ba k’ande suke cimin…

    ” Ai sai danayi masa bayanin ki sosai, ya maganar islamiyyar zaki shiga?

   ” Eh gobe zan karbo form zan siya yadi…

    ” aa kibarshi nagayawa Abbana duk zaiyi miki…

    ” Tohm nagode…

Basu gama assignment din ba sai gurin 9 kwanciya tayi tana hutawa hajiya tace au abincin ma nizan zuba dan uwarki?

   ” mikewa tayi sannan tafita palour ta zubawa kowa banda hamza!

   ” har ta dau nata taje ance ubanki ne yasiya abincin da baku zuban ba?

   ” jiya ai gani nayi bakaci!

    ” idiot kawai dallah zubamin…

  ” farida tace ai bata yarda ba tafara zùwa makaranta!

   ” hamza yace asarar kudin makaranta ba!.

   ” ita dai bataci musu kala ba tashige dak’in ya haruna ta shiga yana ta waya da Amira!..

    ” ta dade a tsaye sannan yace lafiya?

    ” Abinci nakawo maka!

   ” Dazu naci agidan su Amira!..

    ” fita tayi ranta a bace tana shiga daki tafashi da kuka ahaka bacci ya dauke ta!..

  Da safe dady yadawo kowa ya zauna A palour sunata hira!…

     ” Firdausi tace oh uncle haruna dady kadai kake sakarwa fuska mubaka hira damu!…

    ” dady yayi dariya ainema labari nake bashi shiyasa, ina k’ande ne?

    ” farida tace ai tana can tana bacci…

     ” sannu da zuwa dady wallhi ina dak’i ne ina karatu exam zamu fara ne! yauwa uwata nasiyi miki tsaraba kalakala! +

   ” murmushi tayi ta samu guri ta zauna, baba ya china?

    ” lpylou hope kina lafiya bawani problem?

    ” eh babu duk muna lpya kallon haruna takeyi yadda yakara yimata kyau ya saka black yard dinsa….

    ” ga atamfa guda 12 ki kai dinki inda su firdausi suke kaiwa!…

    ” farida tace tabbijan can taje tasamu tailor dinta Amma walhi bazamu bawa namu ba!…

     ” haruna kakaita gidan hafsa sai tarakata tunda ne ban isa daku ba!

    ” Tohm Alhaji…

       ” yauwa akwai maganar danakeso muyi daku zankara aure!

    ” kutmar cewar mumy auren uban me to walhi bazata sabo ba!

     ” nagama komai yanzu haka lefen ta yana mota kima ga guda biyar can nayi miki!

    ” farida tace dady wazaka auro?

     ” mama farida ta kauye…

     ” Hajiya tace ai zata shigo ko? To wallhi zatasan tashigo gidan mulki….

    ” fuuuu suka hau sama itada ‘ya’yanta…

     ” k’ande kuwa murna taje tunda ran mumy ya bace, Dady please zanje kai lefen ….

    ” kiyi zamanki tunda jarabawa zaki fara!..

     ” Tohm tace masa sannan ta mik’e!…

Gurin karfe 4 an tafi k’ai lefe, haruna ya leko kin shirya?

    ” eh tun dazu na shirya…

     ” To tawo muje gidan gaba ta bude ta shiga yaya please ka kaine gidan su kawata nafisa sai na kaiwa tailor dinta banason zuwa gidan anty hafsa!!!

     ” uffan baice mata ba wayansa yafara ringing dauka ya dauk’a hello sweety!

    ” kana ina ne nayi kwalliya kazo ka gani kaje!

    ”  haha tohm ganinan juyawa yayi bai tsaya ko’ina ba sai kofar gidansu Amira! Nazo fito to!

   ” ita dai k’ande taga ikon Allah sakar baki tayi taga Amirar nan fitowarta keda wuya taga ai tafi Amira komai sai dai ta nuna mata fari!

    ”  irin wannan kyau Amira!.

      ” Da gaske nayi kyau?

    ” sosaima

         ” kace abinci kokuma na zubo maka?

     ” Naci kinyi mun zobon!

     ” yeap gashi nan..

    ” yauwa sweety, Ga sister ta nan ku gaisa!

    ” ina yini..

     ” k’ande tace lpya lou matar yaya kinyi kyau fa!

    ” Nagode!..

      ” bari mutafi…

         ” Tun yanzu? Cikin wata murya mai cike da tausayi…

” haba sweety kuka zakiyi? Ai da night zan dawo…

    ” okay tohm bye dear…

     ” kande tace ikon god kalle yadda suke tararrayar juna!

   ” tunda yashigo mota yaketa murmushi…

   ” can kande ta saka dariya murmushi kai kadai?

    ” ke kuwa naga abokiyar rayuwata dadi nakeji!

   ” cikin gyatsene tace Allah sarki…

    ” ya kaita shagon me dinkin nan ta shiga ta basa bashi dubu goma…..

   ” Kai masa tayi…

     ” Nagode yaya rannan ma kayi mun asignmnt thank you!..

     ” Ai dama Nace miki ina tare dake….

    ” kayi sauri please kada bunkusar mumy tafara duka na…

     ” Ai itace daidai dake!!!

    ” hmm haka kagani ai…

     ” suna komawa tayi sallah tace hajiya me za’a dura?

    ” k’an uwarki dana ubanki zaki dafa mana!

     ” kande tasaka dariya a ina zan siyosu sai na dafa?

      ” firdausi tace naga taki takin ki gurin uncle haruna so kiyi hankali…

     ” lah ai dazuma gidan su budurwarsa narakasa suka sha soyayyar su, kinsan yanzu maza sun waye basa son jahila sunfison mai addini…

     ” zama tayi tace oh my god ya zanyi da son uncle…

    ” kande kuwa haushin firdausi taje lallai da aiki agaban ta….

  Ranar lahadi aka daura auren mama farida karfe 4 aka kawota gidan part dinta aka kaita ya hadu sosai…

     ” hajiya tana daki tana rusa ihu Alhaji ya cuceta kuka takeyi sosai..

       ” kande kuwa tana palour a zaune tanata karatu…

  ” baba mai gadi ne yayi sallama ga zobon ya siyo nan ta sarrafa shi sai kamshi yakeyi ta saka acikin jug guda biyu ta dafa taliya da sauces, kowa da kowa suna zaune har hajiya…

    ” Dady yace toh dai ga Antyn ku nan itama Amatsayin mahaifiyar ku take!

     ” To sukace kande ta fito aa mama farida sannu!

    ” baki iya gaisuwa bani?

      ” Ai kinsan lokacin danake gida baki koya min ba!ni zakiyiwa fitsara!… +

       ” kinsan inkayi sai an maka!..

    ” mumy da farida mamaki ne ya kamasu dama kande tanada zafi…

     ” daga hannu tayi zata wanka mata mari kande tace maza mayar maza mayar, kafin nakai miki nawa!…

     ” kukan karya mama farida tasaka Alhaji kana k’allon yadda tayimin ko?

    ” so what? Cewar kande kingansu duk basu san halina bani ba  na kyale su ne kawai so kowacce tayi control din kanta!

    ” zata shiga dak’inta haruna yarike hannunta menene haka!

    ” soyayya ce!

     ” kamar yaya?

     ” bazaka fahimta ba tunda kai kanada wacce kakeso!

    ” oya tell me wanda kikeso zan taimaka miki, ya riga yafada soyayyar wata…

    ” gayamin toh har ta bude bakin ta…

    ” firdausi tace uncle kazo inje dadi…

    ” okay yace..

Firdausi ta nuna kande da hannu!!

     ” kande a zuciyar ta tace indai akan haruna ne yanzu zamu fara (game) din….

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]